Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwadayi Mabudin Wahala: Nazarin Kwartanci Da Ayyukan Kwarto A Mahangar Danladi Mai Kidin Kwartaye

Wannan muƙala mai suna “Kwaɗayi Mabuɗin Wahala: Nazarin Kwartanci da Ayyukan Kwarto a Mahangar Makaɗa Ɗanladi Mai Kiɗin Kwartaye”, an bayyana wasu dalilai da ake ganin suna daga cikin abubuwan da ke haddasa wasu mutane yin kwartanci. An samo hujjojin abin da aka faɗa daga waƙar kwartaye ta Ɗanladi. Dalilan da aka hango da ke sanya wasu mutane zama kwartaye sun haɗa da kwaɗayi da gado da kasancewar mutum hariji da yin abota da kwarto da mallakar magani da sauransu kamar yadda aka ciro daga waƙar kwartaye ta makaɗa Ɗanladi. Haka kuma an bayyana wasu ayyukan da kwartaye ke aikatawa da suka haɗa da kwartanci da gudu da fasa darni da neman magani da neman matan maƙwabta da sauransu. An yi hira da wasu mutane da dama da ba a ambaci sunayensu ba da sunayen garuruwan da suke domin guje wa ta-da-zaune-tsaye, domin idan aka ba da bayanin wani ta hanyar ambatar sunan wanda aka yi hira da shi, zai ga an ci mutuncinsa. Domin guje wa hakan aka sakaya sunayen waɗanda aka yi hira da su da sunayen garuruwan da suke. An kawo abubuwan da muƙalar ta hango a matsayin sakamakon bincike da shawarwarin da ake ganin za su taimaka wajen rage matsalar kwartaye da kwartanci

Muhimman Kalmomi: Kwaɗayi; Kwartanci; Kwarto; Kwartaye

Kwaɗayi Mabuɗin Wahala: Nazarin Kwartanci Da Ayyukan Kwarto A Mahangar Ɗanladi Mai Kiɗin Kwartaye


Bello Bala Usman
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
08027459617

And

Dano Balarabe Bunza
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
07035141980

Kwarto 

1.0    Gabatarwa

Masana da manazarta da suka feɗe biri har wutsiya a harakar waƙoƙin baka na da yawa. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Gusau, S.M. (1988) da Abba da Zulyadaini (2000) da Bunza A.M. (2009) da sauransu. Kiɗin kwartaye kiɗin tonon silili ne da ake yi wa wanda asirinsa ya tonu a lokacin da ya tafi wajen aikinsa na neman matan wasu mutane, a garin da yake ko a wani gari. Kiɗin kwartaye kiɗin kunya ne da ake yi wa makunyatan da abin kunya ba ya ba su kunya. Kiɗi ne da ake yi wa wanda aka kama ko aka tayar a gidan da ba nasa ba, da niyyar neman matar wani domin ya yi lalata da ita. Babu magidancin da ke murnar wani mutum ya yi wa matarsa kwartanci ko da kuwa shi kwarto ne. Kiɗan da ake yi wa kwartaye ba da ra’ayinsu ba ne. Wannan ke sanya kwarto ba makaɗi komai domin kar ya kaɗa masa gangar kunya. Idan dai yadda ake so bai samu ba, tilas a yi haƙuri da abin da aka samu. Kwarto da ayyukansa duk abin ƙyama ne ga kowace al’umma. Takardar za ta kawo bayanin abubuwa da dama da suka shafi kwarto da ayyukansa da suka haɗa da dalilan da ke haddasa yin kwartanci da ayyukan kwarto kamar yadda muka hango a cikin waƙar makaɗa Ɗanladi mai kiɗin kwartaye. Za mu kuma yi amfani da hirarrakin da muka yi da waɗansu mutane sai dai, ba za mu ambaci sunan waɗanda muka yi hira da su ba, da na kwartayen da muka sami labari daga hirar da muka yi da su ba. Za mu kafa hujjoji da ɗiyan waƙar Ɗanladi waɗanda ya rera wa kwartayen da ya ambaci sunayensu a cikin waƙarsa.

 2.0 Dalilan Bincike

Kowane bincike na da dalilin da ya sanya aka yi shi sai dai, dalilin ya kasance mai karɓuwa ko raunana. Dalilin aiwatar da wannan bincike shi ne, ba mu sami takardar da ta kalli kwarto da kwartanci ta fuskar nazarin waƙar kwartaye ta Ɗanladi ba, face ta Aliyu Muhammad Bunza. Shi ma Aliyu ba waƙar ya nazarta ba domin ya yi amfani da ɗiyan waƙar kwartaye uku kacal a cikin takardarsa sai kuma ratayen waƙar da ya kawo. Hasali ma, taken takardarsa shi ne: Kwartanci: (Fashin Baƙinsa, Mafarinsa da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin Bahaushe). Ita kuma takardarmu ta kalli kwarto da kwartanci yadda makaɗin ya fito da su a cikin waƙarsa ta hanyar kafa hujja da ɗiyan waƙar. Ƙarin da aka samu shi ne hirarrakin da muka yi da wasu mutane a kan kwarto da ayyukansa kuma, ya sanya armashi a takardar. Na biyu shi ne, makaɗin ya rasu, waƙar na a kan hanyar ɓacewa kai tsaye ko kuma a rasa samun wanda ya yi tunanin rubutu a kan kwarto da kwartanci. An yi wannan bincike domin ciyar da al’amarin adabi gaba da masu tasowan da ba su san kwarto ba, balle kwartanci. A fahimtarmu idan aka yi bayanin kwarto da kwartanci a rubuce, wanda bai san shi ba idan ya karanta zai fahimta.

 

3.0  Dabarun Bincike

A cikin kowane bincike akan sami dabarar da aka yi amfani da ita, ko a faɗa ko kar a faɗa. A lokacin rubuta wannan takarda mun yi amfani da dabarun binciken da suka haɗa da sauraro da nazarin waƙar da kuma bincike a ɗakunan karatu tare da yin hira da masana fannin adabi da al’adun Hausawa. Sai dai kuma, ba mu sami aikin da aka yi kacokan a kan kwartanci ba, balle nazarin waƙar kwartaye ta Ɗanladi. Haka ba mu sami kwarton da ya ba da haɗin kai domin a yi hira da shi ba, face waɗanda suka san abin da ya faru dangane da kwartanci a gabansu. Wannan na da alaƙa da kasancewarsu cikin garuruwan da tashin-tashinar kwartanci ta faru a gaban idonsu.

4.0   Hanyar Bincike

Hanyar da aka aza wannan bincike a kai ita ce karin maganar Hausawa da ke cewa “Kwaɗayi mabuɗin wahala”. Takardar ta lura da duk rayuwar kwarto a ɓangaren kwartanci wahala ce da babu ranar hutu face an daina. An lura daga gudu sai gudun ceton rai kwarto ke fama da shi bayan barazanar halakarwa da yake fuskanta daga al’ummar da yake taɓa matansu. Idan ba ya da rabon mutuwa, zai sha kasha tamkar damen dawa na ƙarshe da aka fitar a cikin rumbu.

5.0   Kwarto

Masana sun bayyana wanda ake kira kwarto a cikin rubuce-rubucensu gwargwadon hali. Ga bayanin wanda ake kira kwarto kamar haka:

 A ganin wasu masana kwarto na nufin mutumin da yake neman matar wani (CNHN, 2006:267).

Aliyu Muhammadu Bunza cewa ya yi, kwarto shi ne wanda yake da aure, kuma ya yi hulɗar ɓatanci da matar aure a cikin takardarsa, (Kwartanci: Fashin Baƙinsa, Mafarinsa da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin Bahaushe).

A fahimtarmu duk bayanan da suka gabata sun yi wa ma’anar kwarto susa gurbin ƙaiƙai kuma, sun wadatar da mai neman ma’anar kwarto. Tare da haka muna da ra’ayin cewa kwarto na nufin mutumin da ya yi ko ke hulɗa da mata/matan wasu ta hanyar saduwa cikin ɓoyo/sirri ba tare da buƙatar sanin kowa ba. Aliyu Muhammadu Bunza ya bayyana cewa babu mace kwartuwa domin mai zuwa ake ba suna ba wanda ake je wa ba. A tunanin takardar wannan a da ne kuma a al’adance, ba kamar yau da aka waye ba, inda wasu matan aure ke kai kansu a gidajen wasu maza domin a yi hulɗar kwartanci da su. Idan a da namiji ke zuwa wurin mace shi ya tabbatar masa da sunan kwarto, to yanzu kuma da mace ke kai kanta wurin namiji kuma duk domin buƙata iri ɗaya, me zai hana a kira ta kwartuwa ko kwartanya?

6.0  Kwartanci

Kamar yadda masana suka bayyana ma’anar kwarto, haka sun bayyana kwartanci kamar haka:

A wani wuri cewa aka yi, kwartanci na nufin neman matar wani (CNHN, 2006: 267). Shi kuma wani cewa ya yi kwartanci na nufin immorality between adults (zina). Haka kuma ya bayyana cewa kwarto na nufin 1. Aprofligate, immoral p., a paramour. (Bargery).

Har yanzu an sami wani masanin al’adar Hausawa ya bayyana ma’anar kwartanci da cewa, hulɗar soyayya tsakanin mace mai aure da wani namiji ma’auraci ko yana tare da matarsa ko sun rabu sunan namijin kwarto. Sunan wannan soyayyar ko da ɓatanci bai bayyana ba, aka kama su, sunanta “kwartanci”. A al’adar Bahaushe, da an yi aure an katangance ango da amarya. Hulɗa da wani miji da ba nata ba, ko hulɗa da wata matar aure da ba tasa ba, shi ne kwartanci. Wanda duk aka samu cikin wannan ƙazanta sunansa kwarto.

A fahimtarmu, kwartanci na nufin zuwan wani namiji ga matar da ba tasa ba a cikin gidanta ko gidansa ko wani wuri da amincewar juna domin yin lalata tsakaninsu. Bayan haka ana iya cewa, kwartanci shi ne haɗuwar mijin wata da matar wani a kan wata yarjejeniyar biya wa juna buƙata kuma, akan sami hakan ko ba tare da yarjejeniya ba a wasu lokuta. Je wa mace ba tare da yin yarjejeniya da ita ba, shi ake kira shige. A taƙaice, kwartanci shi ne hulɗar fasiƙanci tsakanin wani mijin aure da matar auren da ba matarsa ba da saninta ko ba tare da saninta ba, an gan su ko ba a gan su ba.

7.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Ɗanladi

Ba a sami tarihin makaɗa Ɗanladi ba domin ba a taɓa aikin bincike a kansa ba a matakin digiri na farko ko na biyu ba balle na uku. Haka kuma ba a sami wani aikin NCE da aka gudanar a kansa ba. Abin da aka sani game da shi kawai shi ne abin da ya ambata a cikin waƙarsa ta kwartaye. Ba a san waƙarsa ba sai da baya-bayan nan kuma, manazarta ba su ahama da yin rubutu a kan waƙar kwartaye ba sai da baya-bayan nan. Abin da aka sani dangane da shi kawai shi ne, mutumin ƙasar Neja ne kamar yadda ya ambata a cikin wani ɗan waƙarsa kamar haka:

Bari in koma ƙasarmu in mai da bilata dai,

Garba sana’a na Salka bai bak kasada ba,

Kasuwad daji Garba yay yi gaba da Hilani,

……………………………………………

A cikin ɗan waƙar da aka kawo a sama, makaɗin ya faɗi cewa, a bari ya koma ƙasarsu ya faɗi wani abu dangane da wani kwarto mai suna Garba Sana’a na Salka. Garin Salka na cikin jihar Neja a yankin Kwantagora. Yana can gaban garin Nasko idan an fito daga Yawuri. An ƙuduri a haɗu da makaɗin domin yin hira da shi, sai aka sami labarin ya rasu. Wannan shi ne ƙarshen tarihin da aka samu na makaɗa Ɗanladi mai kiɗin kwartaye a taƙaice.

8.0  Dalilan Da Ke Haddasa Yin Kwartanci

 

Ko a hankalin tuwo bai dace a yi tunanin faruwar abu ba tare da dalili ba. Idan aka sami mutum na sata (ɓarawo ne) tilas a sami sanadin kasancewarsa ɓarawo. Hausawa dai cewa suka yi “Ruwa ba ya tsami banza”. Ma’ana, ba a san ruwa da wani ɗanɗano ba. Idan aka ji su da wani ɗanɗano akwai abin da ya faru gare su. Haka idan aka tarar mutum maye ne ko mai yin fashi ya ƙwace kayan mutane ko ma wane iri, tilas a sami dalilin kasancewarsa hakan. A kan haka ne takardar ta duƙufa don gano dalilan da ke haddasa mutum ya kasance kwarto har ya yi kwartanci. Ba shakka an sami wasu dalilai daga bakin Ɗanladi a cikin waƙarsa da ya kawo wasu dalilai da takardar ta yanke hukuncin cewa su ne suka yi sanadin kasancewar kwarto da wannan aiki. Ga dalilan kamar haka:

8.1 Kwaɗayi

Kwaɗayi na nufin tsananin son wani abu, musamman abin da za a ci ko za a sha, wanda mutum bai mallaka ba. Haka kuma yana nufin sha’awar ci ko shan wani abu. Bayan wannan an ce kwaɗayi na nufin son karɓar wani abu cikin sauƙi a wajen mutane (Ƙamusaun Hausa, 2006:260).

Makaɗin kwartaye ma ya bayyana abin da ake nufi da kwaɗayi a cikin wani ɗan waƙarsa inda ya ce:

Shekaranjiya Kawoje yag ganan yay yi kira na nit tai,

Yarinya tai madaddake ta yi magarzai,

Kuma ga dogon wuya kamat ta yi ma kanta,

Ta sa lallen ga nata daidai da idon swai,

Kitson kiliya ag ga kanta mai jehwa mazaje,

Alhaji Mamman da yag gani yaɗ ɗahwa rainai,

Ya ce min dalumag ga ab ba ta wuce shi,

Lahira in ya tai matambayan nan su kashe shi.

 

Idan aka yi la’akari da layuka uku na ƙarshen ɗan waƙar da aka kawo a sama, makaɗin ya bayyana abin da ake nufi da kwaɗayi a fahimtarsa a kuma fahimci abin cikin sauƙi. Ya ce mutum ya ga abu ya ɗahwa (sanya ransa gare shi) kuma ta kowace hanya sai ya sami abin daga baya duk abin da ke faruwa gare shi ya faru. Haƙiƙa wannan shi ne kwaɗayi. Wannan yasanya Hausawa faɗar “Ƙuda wajen kwaɗayi aka mutuwa”.

A fahimtarmu kwaɗayi na nufin tsananin buƙatar wani abu a rayuwa da mutum bai mallaka ba da ƙoƙarin ganin ya same shi ta kowane hali. Ana iya cewa, kwaɗayi na nufin ƙallafa rai (Ɗahwa rai) ga abin da ba a mallaka ba da nufin a same shi ta kowane hali. Abin na iya kasancewa abinci ko abin sha ko wata ƙawar duniya da Sheɗan ya ƙawatar da zukatan bil Adam da ita.

A binciken da aka yi an sami makaɗin kwartaye ya kira kwarto makwaɗaici a cikin wasu ɗiyan waƙarsa. Wannan ya sa aka sanya wa takardar suna “Kwaɗayi Mabuɗin Wahala”. Hausawa sun ce “Idan da kwaɗayi da wulaƙanci”. Makaɗin da kansa ya kira su makwaɗaita a cikin waƙarsa, duk da yake shi ma makwaɗaicin ne. Ga wuraren da ya kira kansu makwaɗaita:

 

Ina sarkin raɓe-raɓe kwarto makwaɗaici?

Kwarto mai shan jinin jikinai ya bi darni.

 

Allah hi kiyaye,

To ko can sai sha biyun dare za ta rabawa zak kyau,

Yakin in sa kiɗin mazana makwaɗaita

 

An ce min ɗan alaru ya kai makwaɗaici Audi,

To bari in tai buhuhuwa can in hwake su,

Ana son a yi ɗandako mutane na ƙiya min,

An ce Sarkin alaru ya rataya darni.

 

Shekaranjiya Kawoje yag ganan yay yi kira na nit tai,

Yarinya tai madaddake ta yi magarzai,

Kuma ga dogon wuya kamat ta yi ma kanta,

Ta sa lallen ga nata daidai da idon swai,

Kitson kiliya ag ga kanta mai jehwa mazaje,

Alhaji Mamman da yag gani yaɗ ɗahwa rainai,

Ya ce min dalumag ga ab ba ta wuce shi,

Lahira in ya tai matambayan nan su kashe shi.

 

Ɗanladi ya kira kwarto makwaɗaici kuma, shi ne makaɗinsu. Ya san su domin mutanensa ne. Hasali shi ma kwarto ne. A taƙaice, ya san kansa kuma ya san waɗanda yake tare da su. Idan aka lura kwaɗai da ɗahwa rai ga abu, duk ɗaya ne. Kwaɗayi irin na Audi ya kai gaya saboda ya amince wa kansa komai zai same shi ya same shi idan dai ya cim ma buƙatarsa ga dalumad da makaɗin ya siffanta. Mutum ya amince wa kansa halaka a lahira saboda wani abin duniya, ba shakka kwaɗayi ne kuma wanda ya kai gaya.

8.2 Ɗan Burgu/Gafiya Bai Rasa Farin Bindi (Gado)

Gado na nufin muƙami ko hali ko sifa ko kaya da mutum ya gada (Ƙamusun Hausa, 2006:149). A fahimtarmu, gado a nan na nufin a sami mutum ya ɗauko hali ko ɗabi’a ko aikin da wani ko wasu daga cikin iyayensa ko kakanninsa ke aikatawa, har idan aka gani a fahimci halin ya samo shi daga gare su. Wannan ya sa Hausawa suka ce “Gado ba ya wofinta”. Ma’ana tilas a sami wani ya ɗauko halin wani daga cikin iyaye ko kakanninsa. Wannan ya sanya Hausawa faɗar “Kyawon ɗan ƙwarai ya gadi ubansa”. Wannan ya sanya muka yi wa kan labarin suna ‘Ɗan burgu ba ya rasa farin bindi’. Idan akwai kaka ko uba da ke wata ɗabi’a mai kyau ko akasinta, aka sami daga cikin ‘ya’ya ko jikokinsa/ta wani ya tashi da ita kuma yana aikatawa, ba shakka gado ya tabbata. Dangane da wannan ba sai an je nesa ba domin makaɗin ya faɗi cewa yana da wani tsoho (mahaifi) a gidansu da ya tsufa yana kwartanci bai daina ba. Haka kuma ya nuna ya sha jan hankalin tsohon ya rage ko ya bari baki ɗaya domin kar ya bar musu abin faɗi/faɗe. Amsar da tsohon ya ba shi ita ce, abin da duk za a yi musu faɗe da shi sai dai ya kashe su, ba zai bar wannan jaraba ba. A sanadiyyar gado sai aka sami ɗan (Ɗanladi) ya yi aron hannu (ya gadi) ɗabi’ar kwartanci daga wannan tsoho. Wannan shi ya sa aka ce ɗan burgu ba ya rasa farin bindi/wutsiya. Ga wuraren da hoton gado ya fito a cikin waƙar kuma, shi abin ya shafa kai tsaye ba wani ba. Dangane da haka ga abin da ya ce:

Daɗa yaƙi ya ci gwamna ‘yan soja a watsu daji,

Ganga ta ci mai gari ta ci talakka,

Kiɗi daɗa ya ɓaci tunda ya kai ga su baba.

 

Akwai wani tsoho gare ni bai bak kasada ba,

Kullum nit tai gida ina zai masa horo,

Baba baƙin kwaɗan ga na so ka rage shi,

Yac ce, tai taka haraka ni in yi tawa,

Ka san horonka bai hana min jarabag ga,

Tsoho in kam mace ɗumi mu aka wa shi,

Sai yac ce min yawan ɗumin nan shi kashe mu.

 

Daɗa tsoho na zaton kiɗin ba ni buga mai shi,

Da nic ce kasa kunnuwanka in ba ka tahwashenka,

Lalle bana ban hana ma tsoho ya ji ganga,

To baba ka sha kiɗinka don ɗanka ka yi nai.

 

Yarinya ta da tay yi laihi ga mijinta,

An ce tsoho maji kira zo tahi bikon ta,

Baba da yash shigo dawa yac cire wandonai,

Ko da ta waiwayo dawa ya zube wando ƙasa,

To sun sha kewayal labaye da ƙahwahu,

Ai babban azzikinta sayyu na tare shi,

Da niz zo can inda yai gudun anka gwada min,

Jama’a swan baba gun labu ba hi ɓacewa,

Mata kwalhen ruwa sukai nan bisa swan nan.

 

Idan aka duba Ɗanladi ya yi amfani da kalmar tsoho da baba a wuri goma sha ɗaya a cikin ɗiyan waƙar da aka kawo a sama. Babu kwarton da ya kira baba in ba wannan ba don haka, wannan ya nuna mahaifinsa ne ba wai tsufar haihuwarsa ko yawan shekaru kaɗai ba. Haka kuma ko makaɗa ya fi shi shekaru yana zama ɗansa saboda dangantakar da ke tsakaninsu. Idan aka dubi ɗan waƙa na biyu da na uku da aka kawo a sama za a fahimci haihuwar gaske ce ke tsakanin Ɗanladi da tsohon. A taƙaice, makaɗa ya yanke hukuncin ana gadon kwartanci daga iyaye kamar yadda ya tabbatar a cikin ɗiyan waƙar da ke sama. Bayan haka, daga cikin kwartaye talatin da biyu da Ɗanladi ya ambata a cikin waƙarsa babu wanda ya kira baba/tsoho sai wannan tsoho kurum. Wannan ya nuna gado na ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya a sami mutum ya zama kwarto kai tsaye.

8.3 Harijanci

Hariji shi ne mutum namiji mai tsananin jarabar son saduwa da mata. Ita kuma harija, ita ce matar da ke da tsananin jarabar son saduwa da namiji (Ƙamusun Hausa, 2006:197).

A fahimtarmu, hariji shi ne mutumin da Allah ya jaraba da ƙarfin yi da yawan son jima’i da kuma ƙoƙarin yin sa kuma wannan daga jini ne ba ta hanyar shan wani magani don aiwatar da hakan ba. A taƙaice hariji shi ne wanda mace ba ta gane kasawarsa a wurin jima’i. Ita ma mace wadda aka halitta da wannan haka take.

A cikin waƙar Ɗanladi an sami wurin da ya ambaci wani da sifanta shi da zama hariji a cikin wasu ɗiyan waƙarsa. Ga abin da ya ce:

To bari dai in kiɗa ma sarkin majarauta duka,

Kwamandan ‘yan nema ko tawa ba hi ragawa,

Bari in koma ƙasag gabas inda Namanke,

Na Nabara anne na Bawa kura a ci wawai,

Jan anne ya biya ni jingaj jarabatai,

Ya sai doki da keke ya ba ni Namakau.

 

Ga shi mata huɗu ag gare shi bai baj jaraba ba,

Mata huɗu ba isan Namakau suka yi ba,

Wai dub bakin karin kumallo ya aje su.

 

Tun farko makaɗin ya ba kwarton sarauta ko shugaban kwartaye na zama kwamanda. A layi na biyu ya ce matar kowa ba ya bari idan ya samu. A ɗan waƙa na biyu ya bayyana cewa mata huɗu mutumin ke da amma ba su hana shi neman wasu mata ba ta hanyar kwartanci. Ma’ana, duk matan huɗu ba su isarsa ko gamsar da shi, hasali ma a matsayin karin kumallo ya aje su. Idan haka ne, ina na rana da na dare? Harijanci halitta ce, ba girman jiki ba ne ko rashinsa. A nan makaɗin ya bayyana mutumin da cewa hariji ne musamman idan aka yi la’akari da ma’anonin da aka bayyana a sama.

 

8.4 Zama da Maɗaukin Kanwa (Abota da Kwarto)

Akwai abotakar kusa da ta nesa cikin sha’anin zamantakewar yau da kullum tsakanin mutane ‘yan ƙabila ɗaya ko akasin haka. Sanin sirrin zamantakewa tsakanin mutane ya sa Hausawa suka ce “Zama da maɗaukki kanwa ke sa farin kai”. Su kuma Hausawa faɗa kaɗai suka yi ba maganarsu ba ce. Wannan zance daga Annabin rahama ya samo asali a inda ya ce “Ɗabi’a na satar ɗabi’a”. Abin nufi a nan shi ne, matuƙar mutum biyu na zaune tare, tilas ɗabi’ar ɗayansu ta yi tasiri a kan ta ɗaya. Wannan ya ƙara sanya Hausawa faɗar cewa “Abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa” Dangane da wannan maganar babu tantama domin an sheda ba ɗaya ba, ba kuma biyu ba. Mai abota da mai shaye-shaye ƙarshensa ya zama ɗan ƙwaya. Abokin ɓarawo, ɓarawo ne inji Hausawa. Idan aka sami abota tsakanin mutane babu shakka akwai wani al’amarin da suke gudanarwa tare mai kyau ko akasinsa. Bayan haka, Hausawa sun ƙara da cewa “In hali bai zan ɗaya ba ba a yawo tare”. A taƙaice abin nufi a nan shi ne, abota da kwarto na daga cikin dalilan da ke sanya aboki ya ɗauki ɗabi’ar kwartanci ya ci gaba da yi. Ana ɗaukar ɗabi’un ƙwarai daga abokai kamar yadda ake ɗaukar waɗanda ba na ƙwarai ba. A hirar da na yi da wani ya gaya min cewa aboki na farko kwarto ne. Na biyu ba kwarto ba ne. Yau da gobe har kwarton ya janye ra’ayin abokinsa ya sanya shi cikin kwartanci. Wannan misali ne da ke tabbatar da maganar zama da maɗauki kanwa shi ke sa farin kai. Ma’ana, duk mai ɗaukar kanwa ba ya rasa fari a kansa, don haka wanda duk ya yi abota da shi, kansa zai yi fari shi ma, domin zai taya shi ɗaukar ta wata rana. Sanadiyyar abota Allah kaɗai ya san waɗanda suka ɗauki ɗabi’ar kwartanci, suka zama kwartaye. A taƙaice, zama da kwarto ta hanyar abota na sanya aboki ya zama kwarto kamar abokinsa musamman aiki ne na kunya da duk mai yin sa ya yi bankwana da kunya, ba ya jin ta, ba ya gudun ta domin gonarsa ce dole ya nome ta. Allah ya kare mu.

8.5 Mallakar Magani

Magani na nufin abin da ake sha ko shafawa a jiki ko ɗurawa a jini ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya. Haka kuma an ce magani na nufin abin da samuwarsa ke kore wani abu daban. An ƙara da cewa, magani na nufin sammu, wato harhaɗa wasu abubuwa da yin surƙulle da nufin cutar da wani, musamman abokin gaba. Har wayau an ce magani shi ne harhaɗa ko yin wasu abubuwa don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu (Ƙamusun Hausa, 2006:316). Irin maganin da takardar ke magana kansa shi ne ma’anar ƙarshe da aka kawo ta Ƙamusun, wato harhaɗa ko yin wasu abubuwa don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu. Wannan ma’ana ta yi canjaras da maganin da kwartaye ke nema domin ganin sun biya buƙatarsu da duk matar da suka ɗahwa ransu gare ta. Wannan dalili ya sanya makaɗin ambatar wasu kwartaye haɗi da kansa a fagen neman magani da amfani da shi ga ayyukansu na fasadi a bayan ƙasa. Ga abin da ya ce:

Ina Sanin Sani magani sai da gwadawa,

Daɗa Sani ka biya mawaƙin makwaɗaita,

Da mai mata nab bige shi yar rama bugunai,

Kuma an amshe zanenshi ya amso zanenai,

Sani bai ɗaɗɗaka ba bai kau da ƙahwatai ba,

Nic ce tai ka yi ɗam maza hag ga uwaye.

 

Bari ni ma mai kiɗinsu bam bak kasadab ba,

Bana na kwan Unashi can anka tare ni,

Sauƙi don na ci baduhun kau da ido na,

In ba don na ci baduhun kau da ido ba,

Da ko am ba ni rai dubu na rasa raina,

Mai mata na bugun gado na tahiyata,

‘Yag gangata ta dauri can sunka kashe ta.

 

Akwai Mamman ɗan Amina kura a ci wawai,

Mamman mai kankare idanunka da kwalli,

Amina ki ja ɗanki kam maƙwauta su kashe shi.

 

A ɗiyan waƙa uku da aka kawo a sama makaɗin ya yi bayanin kwartanci ba ya yiwuwa sai tare da magani, kuma maganin da aka tabbatar da aikinsa ba wanda ake tababa ba. A ɗan waƙa na farko da aka kawo makaɗin ya yi wa wani kwarto kirari a kan maganin da ya samu na yin buga in buga da mai mata ba tare da mutanen unguwa ko gari sun kawo wa mai matar agaji ba. Zanen da mai matar ya karɓe hannunsa, ya karɓi abinsa, duk a sanadiyyar tambayar (maganin) da yake da. Haka a ɗan waƙa na biyu makaɗin ya nuna shi ma an taɓa rutse shi a cikin wani ɗaki, inda ya bayyana cewa da ba ya da ba-duhu a wannan rana da kwanansa sun ƙare, ko da kuwa rayukkansa sun kai dubu balle ɗaya ne. Idan ba aiki da magani ba, yaya mai mata ke rutse kwarto cikin ɗakinsa kuma a ce ya fita lafiya? Wani aiki sai magani! Kamar faɗar da aka yi a cikin wata ma’anar magani cewa, ana shafawa. Kwartaye na amfani da kwalli/tozali ta hanyar haɗa magani mai suna idonki-idona. Wannan ya sa ake kyautata zaton mutumin da ke amfani da tozali (kwalli) idan ba rashin lafiyar idanu gare shi ba, a hukunta masa kasancewa kwarto, face idan ya yi domin koyi da Manzon Allah (S.A.W.).

Mun yi hira da wani mutum dangane da tabbacin ko kwartaye na neman magani? Sanadiyyar haka ya ba ni labarin wani ma’aikacin gwamnati kuma kwarto da aka kai wani gari aiki, sai ya gane matar wani. Da mutumin ya ji labari kuma ya tabbatar da abin da ke faruwa, sai ya tafi ya nemo maganin da kullum yake buƙatar matar ma’aikacin zai same ta. Idan ya je wajenta ya yi, idan bai je ba ita ke kai kanta domin a yi da ita. Abin ya kai ko ƙaƙa, har mutumin ya faɗa wa ma’aikacin cewa ai ba irinsa ake yi wa haka ba, don haka wallahi kullum sai ya hau matar ma’aikacin matuƙar tana cikin garin. A ƙarshe, ma’aikacin ya gaji da wannan ta’asa tilas ya mayar da matarsa wani gari domin ya raba ta da mutumin. Me zai sa haka in ba magani ba? Za a kawo wasu misalai nan gaba a cikin ayyukan kwarto danagane da neman magani domin wannan na cikin dalilan da ke sanya wasu mutane yin kwartanci.

9.0  Ayyukan Kwarto

Ayyukan kwarto na da bambanci da dalilan da ke haddasa yin kwartanci da aka yi bayani a lamba ta 7.0 da sauran abubuwan da suka biyo bayansa. Duk da haka suna da alaƙa saboda mutum ɗaya suka shafa. Misali, kwaɗayi na daga cikin dalilan da ke sanya mutum ya zama kwarto sannan yana daga cikin halayen da aka san kwarto da shi da wasu abubuwa da suka yi kama da hakan. A kan haka takardar ta hango akwai wasu ayyukan da kwarto ke aikatawa kafin da kuma lokacin da ya je kwartanci kamar yadda makaɗa Ɗanladi ya bayyana a cikin waƙarsa ta kwartaye sai dai, mafi yawan ayyukan ba su bayyana sai a wurin kwartanci kamar yadda za a gani a cikin bayanin da ke tafe .

9.1 Gudu

 

A wani wuri an ce gudu na nufin fyalle ko ruga (Ƙamusu Husa, 2006:171). A tamu fahimta gudu shi ne rugawa da hanzari saɓanin tafiya mai nuna mai yin sa na cikin wani uzuri sanadiyyar faruwar wani abu da ya fi ƙarfin tafiya sannu. Ba a yin gudu sai buƙatar yin sa ta kama. Babu shakka gudun da kwartaye ke yi na uzuri ne da ceton rai. Duk kwarton da aka rutsa da shi har aka kashe shi wajen kwartanci tamkar an kashe kare ne. Domin tabbatar da haka ga abin da wani kwarto ya faɗa da bakinsa inji makaɗinsu kamar haka:

Barmu mesin da yai gudu anka hwaɗa min bana,

Yuƙag gina ga ƙyasuwa munka ishe ta,

Ka dubi yawan kuwara ta kai ga cikewa,

Kaw wani baƙon kada hi taso hi haye ka,

Yac ce “Ba ta kada nikai ba in tcira da raina”.

 

Irin gudun da kwarto ke yi ba irin na kai ceto wurin da aka yi gobara ba ne, ba ceton wasu mutane ba ne, gudun ceton rayuwarsa ne don kar a kashe shi. Haka kuma duk lokacin da kwarto ya ruga da gudu, an tayar da shi ne a wurin aikinsa na kwartanci. Idan ba a tayar da kwarto ba to, batun gudu bai taso ba. Saboda haka gudu aikin kwarto ne da yake yi a kan tilas domin ya tsira da rayuwarsa kar a kashe shi. Wannan ya sanya makaɗin faɗar:

 

Ashe kwac ci abin gudu jiyoji ka biyanai,

Da duy yac ce bai gudu jikinai ya hwaɗa mai,

In kag ga gudu da waiwaya ce na ba’a na,

Gudu in ya ɓaci ko gida ba a biyawa.

 

A fahimtar makaɗin duk kwarton da aka tayar ya ƙi gudu ya amince da ya sha kashi tare da tonuwar asirinsa ko ma a kashe shi baki ɗaya. Ya ƙara bayyana cewa, idan mutum na gudu yana waiwayar bayansa ba na rashin gaskiya ba ne kuma, ba kwarto ba ne. Hasali ma idan aka biyo kwarto ba ya waiwaya kuma ba ya shiga gidansa domin kar a kama shi. Yadda ɓarawo ke gudu domin tsoron a kashe shi, haka kwarto ke yi domin duk gudun ceton rai ne suke yi. Ga wani ɗan waƙa da makaɗin ya ce:

Wai kura ta yi lahiya Daudu Madangyal,

Bari Daudu mutan Halala nak kama wuyanai,

Ni ban aza Daudu na gudu don wahala ba,

Sai ga hi sharaf-sharaf da laka ga ɗuwayya.

 

Wani kwarto ne mai suna Daudu Madangyal da mutanen garin da ake kira Halala suka kama lokacin da ya je kwartanci a wani gida. Makaɗin bai zaci Daudu na gudu don wahalar duka ba amma, da ya sha dukar da ta fi ƙarfinsa dole ya ara daga cikin na kare. A lokacin da ya ji an fi ƙarfinsa sai ya yi shawarar rugawa da gudu kar a kashe shi. Tare da haka shawarar gudu ba ta kama shi ba sai da ya sha kashi, ana bugu yana faɗuwa ƙasa cikin laka sannan da ya fahimci babu sarki sai Allah ya ce ƙafa mi na ci ban ba ki ba? Shi ma makaɗin da kansa ya bayyana cewa an taɓa tare shi a wani gari mai suna Raha lokacin da ladan mai kiran salla na assalatu amma, kafin mutane su tashi da safe su wanke ido ya kai garin Bena saboda bala’in gudun da ya yi. Ga abin da ya faɗa da bakinsa ganin babu mai gudun da ya fi kwarto. Ga ɗan waƙar duk da yake bayaninsa ya gabata a sama:

 

Garin Raha nis san gudun kwarace da iyawa,

Ladan na assalatu sai anka tare ni,

Ka diba sai ga ni Bena ba a wanke ido ba.

 

Bayan haka akwai wani kwarto mai gudu sosai da an yi biyar sa babu adadi ba a sami kama shi ba da makaɗin ya bayyana kamar haka:

Guntu na guntuwar kwana ba a riƙe shi Yellow,

Jama’a guntun mutum hina kyau bisa danni,

Yellow bana in kab buwaya karnai aka sa ma.

 

Bayanin layin ƙarshe a ɗan waƙa na sama shi ne, an sha bin Yellow ba a kama shi a shekarun da suka wuce. Don haka bana ko da ta kai a yi masa aji (A haɗa shi da karnu domin a kama shi) sai an yi domin a ga cewa an kama an halaka shi. Mutum ne mai gudu sosai da ba a taɓa kamawa a wurin aikinsa na kwartanci ba. A lura sosai a nan cewa, gudun kwartaye ba irin na sauran mutane ba ne. Mun yi hira da wani mutum, ya gaya muna cewa kwartaye na shan maganin da ke sa su yi gudu sosai wanda idan suka shiga gaba, babu mai iya cim musu balle ya kama su. Daga cikin abubuwan haɗa maganin gudu da kwartaye ke amfani da shi akwai shalla. Don haka takardar na ganin Yellow na amfani da wannan magani har ya sa ya buwaya a ɓangaren gudu inda mutane ba su iya kama shi, sai dai a sa masa karnuka. A gaida uban gudu kwarto!

9.2 Fasa Darni

 

Darni na nufin shingen kara ko zana (Ƙamusun Hausa, 2006:99). A wani wuri cewa aka yi darni/danni na nufin karan gero ko dawa ko maiwa da ake tsarawa a gewaye gida (Aliyu Muhammadu Bunza, 2020 a cikin takardarsa mai taken Kwartanci: Fashin Baƙinsa, Mafarinsa da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin Bahaushe). Duk ma’anonin da ke sama sun bayyana abin da ake nufi da darni/danni, duk da haka a fahimtarmu darni shi ne tsarin gewaye gida ta hanyar amfani da kara kuma mafi yawa karan gero ko na dawa ko duka ta hanyar yin killiya-killiya (sashe-sashe) kafin a gewaye gida. Mafi yawan masu amfani da darni su ne manoma da talakawa saboda rashin ƙarfi.

Fasa darni ko yakuce shi na daga cikin ayyukan kwarto kamar yadda makaɗinsu ya ambata a cikin wasu ɗiyan waƙarsa kamar haka:

 

………………………………………

Don yanzu guda-guda ina ba da mutane,

Kwartaye sun jima suna yaƙuce danni.

 

Bana lisafi gida-gida ukku yana nan,

Daɗa kowane yab biya gidan ya hwashi danni,

Gidan Manu Tcirare yab biya ya hwashi danni,

Gidan Malam Sani ya biya ya hwashi danni,

Gidan Sarkin hwawa ya biya ya hwashi danni,

Mugun ya ɗauko killiya ukku ga bainai,

Hay ya iske Ɗanhaɗeja ya take ƙahwatai.

 

Kwartaye na fasa darni a kan tilas ba da son rai ba. Hakan na faruwa a lokacin da aka tayar da su cikin gidan wani lokacin da suka je kwartanci. Idan aka tabbatar da suna cikin gida ko ɗaki, akan tsare hanyar fita gidan domin a sami damar kama su. Kwarto ya tsani a kama shi don haka, ya zaɓi fasa darni ya fita ba tare da ya bi hanyar shiga da fita gidan ba domin gudun a kama shi. Idan ƙofar shiga gida na ɓangaren gabas da mutane suka fake idan ya zo a kama shi, zai fashe darnin yamma domin ko an biyo shi akwai tazarar da da wuyan gaske a kama shi saboda tsananin gudun da yake da kamar yadda aka bayyana a baya.

A ɗan waƙa na farko da aka kawo a zancen fasa darni makaɗin ya bayyana cewa akwai kwartaye da dama da ke wannan aiki. Hasali ma, cewa ya yi sun jima suna yakuce danni. A nan ana iya fahimtar cewa, duk wanda ya jima (daɗe) yana yin abu, babu shakka aikinsa ne. Yakuce danni aikin kwartaye ne kamar yadda takardar ta ciro daga bakin makaɗinsu a cikin ɗan waƙan da ke sama.

A ɗan waƙa na biyu kuma, makaɗin ya ba da labarin wani kwarto da ya shiga gidaje uku lokaci ɗaya ta hanyar fashe wa masu gidajen danninsu. Wannan ya faru sanadiyyar biyo shi da aka yi domin a kama shi. Babu abin da kwarto ya tsana irin a kama shi hannu da hannu domin ya san makomarsa halaka ko kashewa idan haka ta faru. A taƙaice fasa darni na daga cikin ayyukan kwartaye na dole-uwar-na-ƙi da suke yi. Da yawa akan ga kussuwa ga sabo ko tsohon darni a yi tsammanin dabbobi suka yi su don ɓarna amma kwartaye ne ba dabbobi ba. Wani lokaci idan kwarto ya ga fasa darni na da wuya, sukan canza dabara su hau killiya su ƙetare. Wannan ya sanya makaɗinsu faɗar cewa suna kyau bisa darni kamar haka:

Guntu na guntuwar kwana ba a riƙe shi Yellow,

Jama’a guntun mutum hina kyau bisa danni,

Yellow bana in kab buwaya karnai aka sa ma.

 

Layi na biyu da ke cikin ɗan waƙa na sama na nufin bayan fasa darni da kwartaye ke yi, akwai dabarar hawa darni a ƙetare musamman idan kwarto ya shiga rutsi.

9.3 Neman Matan Maƙwabta

 

Maƙwabci shi ne mutumin da gidansa ko wajen zamansa yake kusa da na wani (Ƙamusun Hausa, 2006:327). Wannan ma’ana ta yi daidai da zancen da takardar ke yi domin, akwai maƙwabtakar da kwarto ke yi da maƙwabtansa da ta shafi gida da wurin zama. A nan, babu shakka kwartaye mutane ne marasa kunya da rashin jin tsoron Allah dangane da cin amanar maƙwabtaka. Ana samu a cikin gida ɗaya wani ya nemi matar wani ko a sami ya nemi matar maƙwabcinsa da lalata. Kai! Akwai wani mutum da ya nemi matar ɗansa. Wannan maganar ba zaɓi-faɗi ba ce, makaɗin kwartayen ya faɗi haka ga wani maras kunya kamar haka:

 

Akwai sheri Nabangu ya ja wata darga yap pashe,

Auwal don ka jima kana cuta mutane,

To tsoho yo ma ɗanka aure ku ci tare,

Sai nic ce ka ga hurhure za ni gama ku,

Tai ka ci mai ƙurciya ka turo masa tsohhi,

Don mataɗ ɗanka ta hi matanka ɗuwayya,

Amma ci guminka kai kai wahalakka.

 

To! Ga wani uba saboda tsananin nisa cikin sha’anin kwartanci har da sarukansa (Matan ɗansa) bai bari ba. Makaɗa ya faɗa cewa, mutumin ya yi wa ɗansa aure amma, kowannensu na amfani da matar. Haba! Wannan rashin kunya da rashin tsoron Allah har ina? Ba abin mamaki ba ne domin na yi hira da wani ya gaya min cewa akwai irin wannan da ya taɓa faruwa a wani gari inda uba da ɗa suna noma tare amma, ɗan yana da mata biyu kuma su ke kai musu abinci/abinsha a daji. Idan ɗaya ta kai yau, gobe ɗayar ta kai. Daga cikin matan biyu ɗaya ta amince uban ya yi amfani da ita, ɗayar kuma ta ƙi amincewa. Duk lokacin da suka kawo abincin/abinsha (hurar) sai ya ce su tafi can bakin dutsi ya sama musu iccen huri su koma da shi gida. Yau haka, gobe haka har ɗan ya fara zargin akwai abin da ke faruwa. Wata rana wadda ke amincewa da uban ta kawo hura, suka tafi wajen icce bakin dutsi. Jim kaɗan ɗan ya bi sawunsu. Isarsa ke da wuya sai ya tarar da uban saman matarsa. Ganin haka ke da wuya sai ya juya ya koma gona ya ci gaba da aikinsa. Ana komawa gida, ɗan ya gaya wa mahaifiyarsa abin da ya faru kuma ya ce lallai ya bar wa uban matar har abada. Mutumin ya gaya muna cewa, ɗan bai dawo ba tsawon lokaci sai da ya ji labarin uban ya mutu.

Wani ya ba mu labarin wani kwarto da ke neman matar wani ɗan uwansa. Mutumin da ake neman matarsa basarke ne. Mai neman matar kuwa ba ya neman matar sai ya tabbatar da mutumin ya tafi wurin kamun kifi. Ana nan wata rana aka ba shi labari, ya ce babu komai a bari kawai. Har wurin da yake kwanciya da matarsa an gaya masa. Wata rana ya fita zuwa wurin kamun kifi sai matar ta fita zuwa wurin mutumin. Ana cikin haka kafin a jima ga mutumin ya komo gida. Yana dawowa bai tarar da matarsa ba, ya san wurin da ta tafi. Da ma an gaya masa wurin da suke sha’aninsu, bai tsaya ko’ina ba sai can yana riƙe da mashi. Yana laɓaɓe har ya isa a kansu ba tare da saninsu ba, sai da ya kai gare su kwarton ya kula da shi. Yana ƙoƙarin ya ruga sai mai matar ya nashe shi da mashin. Nashinsa ke da wuya sai ya juyo ya komo gida, ya bar mutumin da mashi. Daga wurin da aka nashi mutumin da mashi har cikin ɗakin matarsa jini ke zuba. Kafin ya shigo gari ya karya gorar mashin, ya shigo da ƙarfen mashin jini na tsiyaya. Matarsa na ganin haka sai ta tafi ta gaya wa ‘yan uwansa. Suka zo suka gani, suka tambaye shi wanda ya yi masa wannan karen aiki, sai ya ce ɗan uwansa ne. Ana cikin haka sai mutumin da aka nasa wa mashi ya ce ga garinku. Aka yi ta shari’a daga ƙarshe aka raba wannan darga saboda akwai ɗan uwantaka kuma, mamacin ba ya da gaskiya. Duk da haka har yau gabar wannan abu na tsakanin ‘yan uwan wanda aka nasa da mashi da na wanda ya yi nashin. Haka kuma makaɗin ya ambaci wani kwarto da ke neman matan maƙwabtansa kamar haka:

Akwai Mamman ɗan Amina kura a ci wawai,

Mamman mai kankare idanunka da kwalli,

Amina ki ja ɗanki kam maƙwauta su kashe shi,

 

A cikin ɗan waƙar makaɗin ya ambaci sunan kwarton da mahaifiyarsa tare da ba ta shawarar ta hana ɗanta aikin da yake yi kar maƙwabta su kashe shi. Wannan ya tabbatar da cewa, akwai kwartayen da ke neman matan maƙwabtansu da lalata. Wasu ma har na ‘yan uwa suke nema a cikin gida ɗaya. Don haka neman matan maƙwabta na ɗaya daga cikin ayyukan kwartaye da takardar ta hango a cikin waƙarsu. Ba wannan kaɗai ba, dangane da haka akwai haddasa mugun zama tsakanin ‘yan uwa da kwartaye ke yi. Allah ya kare mu ya kare muna.

9.5 Neman Magani

 

An bayyana ma’anar magani a lamba ta 7.4 mai taken “Mallakar Tambaya (Magani)” a cikin dalilan da ke sanya mutum ya zama kwarto. Kwartanci aiki ne da ba ya yiwuwa sai tare da mallakar magani don haka, neman magani na cikin ayyukan da kwartaye ke fara yi kafin su fita fage a san su. Ƙaryar kwarton da duk aka kama yana kwartanci ta ƙare, ta hanyar yi masa mummunan duka ko kashi ke sanya kwartaye neman magani. Daga cikin magungunan da kwartaye suka shahara da nema sun haɗa da ba-duhu da na gudu da ba-sanyi da idonki-idona da sauran irinsu. Tilas kwarto ya nemi maganin shiga da fice da yake yi a ɗakunan wasu magidanta domin, ko ba komai ya san da ana haƙon sa. Ba wannan kaɗai ba, idan birinsa ya yi kuren reshe, aka kama shi sai wani ba shi ba. Makaɗin kwartaye ya san da kwartanci ba ya yiwuwa sai da tanadar magani domin, shiga kwartanci babu magani tallar rai ne. Haka kuma, maganar da ya faɗa cewa, magani sai da gwadawa gaskiya ce domin, Hausawa ma cewa suka yi “Sai an gwada akan san na ƙwarai”. Wannan ya sa makaɗin faɗar cewa:

Ina Sanin Sani magani sai da gwadawa,

Daɗa Sani ka biya mawaƙin makwaɗaita,

Da mai mata nab bige shi yar rama bugunai,

Kuma an amshe zanenshi ya amso zanenai,

Sani bai ɗaɗɗaka ba bai kau da ƙahwatai ba,

Nic ce tai ka yi ɗam maza hag ga uwaye.

 

A cikin ɗan waƙar da ke sama, makaɗin ya jinjina wa wani tauraronsa saboda ya nemo magani har ya je gidan wani ya gwada ingancin maganin inda maigida ya buge shi, shi kuma ya rama. An karɓe zanen da ya je da shi wajen kwartanci amma, bai bar zanen can ba sai da ya karɓi abinsa. Wannan ya nuna neman magani na daga cikin ayyukan kwartaye kamar yadda bayani ya tabbatar dangane da ɗan waƙar da aka kafa hujja da shi daga waƙar kwartaye. Bayan haka akwai iza mai kantu ruwa da makaɗin ya yi wa tauraronsa a inda ya ce “Tai ka yi ɗam maza har ga uwaye” dommin idan duka ne ko kashi, kwarton ake yi wa ba makaɗin ba. Ga kuma wata hujja da ta tabbatar da neman magani na daga cikin ayyukan kwartaye kamar haka:

Bari ni ma mai kiɗinsu bam bak kasadab ba,

Bana na kwan Unashi can anka tare ni,

Sauƙi don na ci baduhun kau da ido na,

In ba don na ci ba-duhun kau da ido ba,

Da ko am ba ni rai dubu na rasa raina,

Mai mata na bugun gado na tahiyata,

‘Yag gangata ta dauri can sunka kashe ta.

 

A cikin ɗan waƙar da aka kawo makaɗin ya tabbatar da shi ma kwarto ne kuma, ya nemi magani domin aikinsa aikin tallan rai ne. Ya ce wata rana ya kwana garin Unashi inda ya tafi kwartanci wani gida aka rutse shi cikin ɗaki. Yana cikin ɗaki maigida ya tarar da shi bisa gadonsa kwance, kai tsaye maigida ya ci gaba da bugu tsammaninsa kwarton yake bugu. Shi kuma kwarton ya riga ya fita ɗakin, ya bar mai mata na bugun gado domin yana da maganin ba-duhu. Idan bai nemi maganin ba yana samun sa? Kwarton ya faɗa da bakinsa cewa, in ba domin ya ci ba-duhun ba da ko rai dubu gare shi da ya mutu a ranar. Domin rainin wayo har da gangarsa ya tafi da ita cikin ɗaki wajen kwartanci. Duk da ba a sami sa’ar kashe shi ba, an kashe gangarsa da ya bari a ɗakin. To, da ba ya da ba-duhun fa? Wannan kaɗai na tabbatar da kwartaye na neman magani kamar yadda bayani ya tabbatar a sama. Haka kuma, mun yi hira da wani a kan neman magungunan da kwartaye ke yi inda ya gaya muna, dole ne su nemi magani domin aikin tallan rai suke ciki kuma, sun san da zarar sun shiga hannu sai dai idan da kwana gaba. Ya ƙara da cewa, akwai wani kwarto ba ya zuwa kwartanci sai gidan mutumin da ke bugun gaba da babu kwarton da ya isa ya yi masa kwartanci cikin gida. Shi kuma ya fi son irinsu, ya zo ya gaya maka da bakinsa cewa yana nan tafe gidanka rana kaza kuma lokaci kaza. Mutumin ya ce ko mutum na kwance da matarsa kwarton na zuwa ya yi amfani da ita ya wuce saboda samun baƙar tambaya (Magani). Irin wannan maganinsa mugu ne domin, an ce da zarar ya taɓi mutum shi ke nan sai ya kama kwana ba tare da ya san inda yake ba, ko an tada shi ba ya iya tashi. A nan, mun zaci maganin ba-sanyi ke gare shi. Idan ba a nemi magani ba ba a samun sa. Gaskiyar Hausawa da ke cewa “Mai nema yana tare da samu”.

9.5 Neman Mafaka (Wurin Ɓuya)

Kwartaye na neman wurin fakewa idan aka tayar/koro da su a wurin kwartanci. Duk wanda aka kama ƙaryarsa ta ƙare. Wanda aka tayar aka biyo shi ba a cim masa aka kama shi ba, shi ke neman mafaka (Wurin ɓuya) domin ba ya zuwa gidansa kai tsaye. Wannan ya faru domin gudun a gane shi/ko a waye da shi, duk da ai ana fahimtar/gane wanda aka tayar domin zamantakewarsu da jama’a. A cikin waƙar makaɗin ya sha faɗin an koro wane ya laɓe (Tsuguna) gindin ƙyasuwa ko a masussuki kuma sauro na cizon sa babu halin korewa don gudun asirinsa ya tonu a gane wurin da ya laɓe. Domin tabbatar da wannan magana ga abin da makaɗin ya ce dangane da neman mafakar da wani mai shari’a ya yi cikin wani ɗan waƙa:

Shari’a ta anka sa ka ba banye zane ba,

Ga shari’a ta tashi ban ga kundin shara’atai ba,

Sai nac ce gobe kotu can za ni da gangata,

Ga Alƙali ga ƙyasuwa ya yi tsugunne,

Ga shi sauro na cin shi babu halin ya bige shi.

 

A cikin ɗan waƙar da ke sama makaɗin ya tabbatar da kwartaye na neman wurin da suka laɓe idan an koro su daga wurin kwantanci kamar yadda ta faru ga wani alƙali, inda ya nuna alƙali ya sami ƙyasuwa ya tsuguna ƙarƙashinta domin kar waɗanda suka biyo shi su gan shi. Dalilin da ya sa makaɗa na yawan kawo ƙyasuwa a matsayin wurin ɓuyar kwartaye shi ne, ƙyasuwa haki ne da ke da tsawo sosai da kuma duhun da ke hana a ga mutum ko yana ciki idan ba shigansa aka gani ba, domin da dare suke aikinsu. Akan sami haka idan magani ya kwanta ko kuma babu shi. Ba alƙali kaɗai ke kwartanci ba kamar yadda makaɗin ya faɗa. Akwai nau’in mutane da dama da ya bayyana cewa suna kwartanci wanda idan aka saurari waƙar ko aka karance ta, za a tabbatar da kwartanci ruwan dare ne game duniya. Wannan zai ba mutum mamaki har ya yi niyyar musantawa idan da ba ga bakin makaɗin ya ji maganar ba. Allah ya kare mu, ya kare muna.

 

9.6 Idan ba a Bar Zuwa Ruwa ba, ba a Barin Ɓari (Faɗawa Cikin Tarko)

Yadda ake haƙon ɓèra da gafiya da sauran namun daji, haka ake haƙon kwarto domin a kama shi. Idan aka kama ɓera da gafiya ko naman daji kashe shi ake yi sai wanda Allah ya kuɓutar.

Kwarto ma haka ake yi masa, face in ba a kama shi ba. Idan Allah bai nufi a kashe kwarto ba, sai ya ƙaddari a tayar da shi ya ruga ya tsere, ya nemi wurin ɓuya. Ba wannan kaɗai ba, akan kama kwarto a gwada wa jama’a cewa kwartanci aikinsa ne, ko ana sake shi daga baya a sake bayan kowa ya tabbatar da matsayinsa na mai neman matan mutane. Akwai tarkon da aka haƙa wa wani kwarto da makaɗin ya ce ba a taɓa kamun kwarto da ya kai munin wannan ba. Ga abin da makaɗin ya ce:

Bakin Lanjeriyag ga in dai a riƙe kwarto na,

Kamun kwarton Nabasa ab babu irinai,

Basarke kwash shige shi ya cimma iyaka,

Da yag gane kussuwad da kwarto ka shigowa gidansa,

Ga mamurra cikin gida anka haƙe su,

Mangariba ta wuce kurum anka yi kora tai,

Da yaz zo zai kurɗa kussuwa sunka riƙe shi,

Ɗan mamari ga su sui ɗari bakwai nan bisa bainai,

Har rana tay yi tsakkiya ga hi tsugunne.

 

Makaɗa Ɗanladi ya ce a cikin Nijeriya baki ɗaya ba a taɓa kama kwarto irin kamun da aka yi a garin Nabasa ba. Wani kwarto ne da ke zuwa kwartanci a gidan wani basarke da maigida ya gane sai ya yi wa kwarton tanadin yadda zai kama shi, bayan ya gane hanyar da yake bi ya shiga gidansa. Basarken bai yi wata-wata ba sai ya ɗauko mamari ya haƙa a cikin gida kafin magariba. Bayan magariba dare na yi sai kwarton ya shigo gidan. Ana ganin sa sai aka kore shi ba tare da ya san an haƙa mamari ba. Yana tasam ma kussuwar da ya saba fita gare ta, bai kai can ba sai haƙo ya kama shi. Makaɗin ya ce ɗiyan mamarin da suka shige wa kwarto ga jiki sun kai ɗari bakwai. Da maigida ya tabbatar da kwarto ya kamu, bai yi masa komai ba, bai ce masa komai ba sai da kowa ya gama ganinsa. Kwarton na nan sai da rana ta kai tsakiya sannan aka zo wurinsa domin kowa ya gan shi. Idan mamari ya kama kifi, duk lokacin da kifin ya motsa mamari ƙara shiga jikin kifin yake yi. Haka mamurran suka rinƙa shiga jikin kwarton duk lokacin da ya motsa, kuma aka fita batunsa sai da rana ta kai tsakiya. Ga abin da makaɗa ya ci gaba da cewa:

 

Da yaz zaka shi bai bugai ba yat tarda mutanenai,

Ai ko an ɗauko wanzami nashi na kainai,

To sai tcaga akai ana hid da ɗiyan nan,

Mugun ya zo ta Bauci ya sake kamannu,

Bana sun maisai Bakambare ba hi ɓacewa.

 

Da maigidan ya zo wurin kwarton bai buge shi ba amma, ya kira mutane domin su zo su gan shi. Kwrton na tsugune kuma ga mamurra cikin jikinsa babu halin motsi saboda kaifinsu ga jiki, sannan ba su ciruwa da hannu sai da aka kira wani wanzami domin ya cire wa kwarton. Dalilin tsagar da aka yi wa kwarton ana ɗebe masa ɗiyan mamari har canza kama ya yi, ya koma kamar Bakambare. Dangane da wannan akwai tabbacin faɗawa cikin tarkon masu gidaje da kwartaye ke yi ba da saninsu ba. Wannan ne dalilin da ya sanya aka sa wa kan labarin suna “Idan ba a bar zuwa ruwa ba, ba a barin ɓari”. Wannan na nufin matuƙar kwarto na zuwa kwartanci wata rana sai ya shiga hannu a wulaƙanta shi bainar jama’a. Babu shakka wannan kwarto ya faɗa tarkon maigida kuma, da wannan aka sami asirin kwarto ya tonu da aka kama shi.

10.0 Sakamakon Bincike

Binciken ya gano cewa ana sa kwarto hurumi sanadiyyar ƙyamar da ake yi masa kamar yadda makaɗinsu ya bayyana abin da ya faru tsakanin wani kwarto da wasu Fulanin ƙasar Neja. Wannan ya faru saboda tare wata Bafullata da ya yi a daji ya yi fasiƙanci da ita, duk da yake ina da tunanin fyaɗe ne ba kwartanci ba domin, taron ta ya yi a daji ba gida ya tarar da ita ba. Ga abin da makaɗin ya ce da ke tabbatar da sanya kwarto hurumi:

 

Bari in koma ƙasammu in maida bidata dai,

Garba sana’a na Salka bai bak kasada ba,

Kasuwad daji Garba yay yi gaba da Hilani,

Bahullata yat tare dawa yac ci tsakanta,

Daɗa ya yi hwaɗin dara, dara taƙ ƙi tsayawa,

Kai misallike kwangyal ga ƙyasuwa za ya nasa ta.

 

Ko ga nono cikin gida ba a saye mai,

Sai ya biɗo tsamiya ga ƙwarya ya jiƙa ta,

In ba hi da tsamiya ƙwame za ya hwashewa,

Nic ce ɗau anniya da mata na Hilani,

Ga Hillani na Salka kau sun game kansu,

Amma a yi langaru ka’ a sarai da takobi,

Ka san langaru bai barin kaɗo da hulla.

 

 Haka kuma an gano cewa ana gadon kwartanci kamar yadda makaɗin ya nuna a cikin wasu ɗiyan waƙa cewa yana da mahaifi kwarto, shi kuma ɗa kwarto ne. Bayan haka binciken ya gano kwarto matsoraci ne kuma matsoraci, ba ya tsayi ya fuskanci jama’a idan aka tayar da shi, sai dai ya ruga domin ya tsira da ransa. Akwai ɗiyan waƙa da dama da suka tabbatar da haka daga bakin makaɗin. Wani hali da binciken ya gano shi ne, kwarto bai kula da addini ba a wurin da makaɗinsu ya ce, kwarto bai kula da wankan janaba ba. Domin koyaushe suna cikin rashin tsarkin jiki da na tufafi bayan zuciyar ma ɓatatta ce. Wannan na nufin ba su kula da yin salla ba. Wani abin da binciken ya ƙara ganowa shi ne, kwarto ya yi ban kwana da kunya, bai san ta ba kuma bai yi kusa da ya san ta ba. Bayan haka akwai rashin ƙyamar kowace irin mace ga kwarto inda aka nuna yana yi da mai ido da makauniya da mai ji, har kurma bai bari ba. Wannan shi ya tabbatar da kwaɗayin kwarto. Ga ɗan waƙar da makaɗin ya tabbatar da kwaɗayi da rashin ƙyamar kowace irin mace ga kwarto:

To bari dai in kiɗa ma sarkin majarauta duka,

Kwamandan ‘yan nema ko tawa ba hi ragawa,

Bari in koma ƙasag gabas inda Namanke,

Na Nabara anne na Bawa kura a ci wawai,

Jan anne ya biya ni jingaj jarabatai,

Ya sai doki da keke ya ba ni Namakau.

 

Ga shi mata huɗu ag gare shi bai baj jaraba ba,

Mata huɗu ba isan Namakau suka yi ba,

Wai dub bakin karin kumallo ya aje su.

 

Tun yana ciyo mai kunnuwa hi dawo ma kurame,

Nic ce wata ran ham mar’ ido ba hi barin ta.

 

 

Haka kuma binciken ya gano kwarto maci amana ne inda yake neman matan abokansa da na ’yan uwansa da na maƙwabta na kusa da nesa. Wannan ya nuna kwarto azzalumi ne na ƙoli a cikin harakar zamantakewa. Kaɗan daga cikin abubuwan da binciken ya gano ke nan dangane da kwarto da kwartanci.

11.0 Shawara

Shawarar da muƙalar ke bayarwa ga al’umma ita ce, a ƙyamaci kwarto da aikinsa, sannan a ƙyamaci zuriyarsa domin duk inda ɗan burgu yake ba ya rasa farin bindi. Kar a auri ‘ya’yan kwarto kuma kar a ba su auren ‘ya’yan al’umma domin ɗabi’ar raɓo take yi face idan an tabbatar da rabuwarsa da wannan ɗabi’a. A ɓangaren hukuma kuma ya dace a hukunta su daidai da shari’a. Idan aka yi haka, an ɗauki matakin da ke kai al’umma ga tudun-na-tsira. A ƙarshe, kowa ya yi addu’a ya roƙi Allah tsari daga kwartanci domin ganin al’umma ta gyaru baki ɗaya har a wayi gari a sami ɗabi’ar kwartanci da kwartaye sun yi rauni. Haka kowa ya kula da iyalinsa da waɗanda suke hulɗa da su. Abokai da ke kai abokansu cikin gidajensu su yi hattara kar abota ta zama masifa gare su. Bayan haka, kowa ya kula da lalurorin iyalinsa, kar ya bar su cikin halin ƙaƙa-nika-yi domin gudun kwaɗayin abin hannun wani har a faɗa halin ƙuncin rayuwa da kuma da-na-sani. Allah ya kiyaye.

12.0 Kammalawa

An fara muƙalar da gabatarwa, aka kawo dalilan bincike da dabarun da aka yi amfani da su a wajen rubuta muƙalar. An kawo hanyar bincike da bayanin ma’anar kwarto da kwartanci dangane da abin da masana suka faɗa da taƙaitaccen tarihin makaɗa Ɗanladi a taƙaice ƙwarai. Bayan haka an bayyana dalilan da ke haddasa (sanya) mutum ya zama kwarto da suka haɗa da kwaɗayi da gado da harijanci da abota da mai yin kwartanci da mallakar magani da aka kafa hujjoji daga ɗiyan waƙoƙin makaɗin. Takardar ta kawo wasu ayyukan kwarto da suka haɗa da gudu da fasa darni da neman matan maƙwabta da rashin ƙyamar abokiyar fasiƙanci da neman magani da neman mafaka da kuma faɗawa tarkon magidanta. An yi haka ta fuskar tsamo ayyukan daga waƙar kwartaye ta makaɗin.

Manazarta

Tuntuɓi Masu takarda (Lambobin wayoyinsu na sama).

Post a Comment

1 Comments

  1. Jafar Jikamshi4 March 2021 at 11:17

    Masha Allah. Malam Abu Ubaida kana kokari sosai. Allah ya taimaka.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.