Kudin Kammala Karatun Digiri Na Farko (B.A. Hausa) Da Aka Gabatar A Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Bambanci Da Kamanci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci Da Katsinanci (4)
NA
NAZIRU MUHAMMAD ALKALI
BABI NA UKU
JUMLOLI A KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
3.0 SHIMFIɗA
Wannan babi shi ne babin da ya ke ɗauke da nazari kan karin harshen Sakkwatanci, kuma a cikin sa ne za a ga ire-iren kalmomi da jumlolin da karin harshen Sakkwatanci yake da su. Waɗanda suka haɗa da azuzuwan kalmomi da Sassauƙar jumla a karin harshen Sakkwatanci, da kuma jumlar tambaya da ta umarni, tare da jumlar korewa duk a cikin karin harshen Sakkwatanci. Za a kawo su ne kamar yadda aka kawo na daidaitacciyar Hausa a babi na biyu. Kafin a yi duk waɗannan bayanan sai an waiwayi abin da masana suka ce game da karin harshen Sakkwatanci.
3.1 KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Idan ana maganar karin harshen Sakkwatanci za a ga cewa karin harshe ne mai babban kaso wanda ya ƙunshi karuruwan harsunan yammacin ƙasar Hausa. Idan aka yi la’akari da ra’ayoyin wasu daga cikin masana waɗanda ke ganin cewa, karin harshe ya kasu kashi biyu wato Karin harshen gabas wanda ya ƙunshi Kananci, Zazzaganci, Katsinanci da makamantansu, sai kuma karin harshen yamma wanda ya ƙunshi Sakkwatanci, Kabanci, Zamfaranci, Arewanci, da sauran kare-karen harshen yamma. Saboda kasancewar garin Sakkwato a matsayin babbar mahaɗa ga sauran karuruwan harsunan yamma. Saboda haka sai masana ilimin kimiyyar nazarin harshe suka zaɓi karin harshen Sakkwatanci ya zama jagora ga sauran karuruwan harshen Hausa da suke da alaƙa da juna ta fuskar furuci da tsarin sauti da yanayin gini jumla da ma’ana. Akan samu dangantaka ta fagen karin harshe da al’adu da auratayya, addini da kuma kasuwanci. Wasu kaɗan daga cikin masanan da suka tofa albarkacin bakinsu game da karin harshen Sakkwatanci su ne:
Hamma'ali, (1985), ya nuna cewa "Sakkwatanci Karin harshe ne na Sakkwato. An samo kalmar Sakkwatanci ne daga sunan garin Sakkwato. Sakkwatanci karin harshe ne na mutanen Sakkwato. Sai dai kuma ba ana nufin Jihar Sakkwato gaba ɗaya ba. Wasu na ganin tsagwaron Sakkwatawa su ne, waɗanda ke garuruwan da ke kusa da Sakkwato, wato Zamfarawa, Kabawa da Arawa, musamman waɗanda aka kafa ko ciyar da su gaba, bayan jihadi.
Wasu masana na ganin cewa, Sakkwatanci karin harshe ne na mulki. Dalilin da ya sa suke ganin Sakkwatanci a matsayin karin harshe na mulki shi ne, saboda kasancewar Sakkwato cibiyar daular Usmaniyya. Wadda bayan ƙare jihadi ita ce ke faɗa a ji a ƙasar Hausa, har zuwan Turawan mulkin mallaka. Bisa la’akari da ra’ayin wannan manazarci ana iya cewa karin harshen Sakkwatanci ya samo asali ne daga ginuwar garin Sakkwato a zamanin jihadin Shehu ɗanfodiyo, inda aka zaɓi garin Sakkwato don ya zama babbar fadar mulki ta masu jihadi. Wannan zaɓen da aka yi wa Sakkwato sai ya samar da dama ga mutanen garin Sakkwato na mallakar kalmomi da ƙwayoyin sautukan sauran kare-karen harshen da suke maƙwabtaka da garin Sakkwaton wajen ginin kalma da samar da jumla zuwa fahimtar ma’ana da take ƙunshe cikin zantukan yau da kullum.
3.2 KALMOMIN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Waɗannan kalmomi da za a gabatar a nan kalmomi ne, da ake tattaunawa a kan su cikin shirin zauren Sakkwatanci na gidan rediyo vision F.M. waɗannan kalmomin za a adana su ne don gudun salwantar su nan gaba. Ga jerin kalmomin:
Kalmomin Sakkwatanci Ma’ana a Daidaitacciyar Hausa
Al’amurra al’amura
Agalemi buzu
Akaihwa farce
Alkwato dodonkoɗI Alloba annoba
Anka aka
Arbiƙi unguwarzoma
Assibit asabar
Awo Ee
Batu magana
Basilla allura
Biɗa nema
Burgu gafiya
Bugu duka
Rwarwaka raraka
Hwara fara
Wanga wannan
Wargi wasa
Shigihwa ɗaki
Biɗa nema
Ragaita shiririta
3.2.1 KALMOMI MASU BAMBANCIN FURUCI AMMA MA’ANA ɗAYA
Bargery (1934) shi ne ya yi ƙoƙarin kawo waɗannan kalmomin na Sakkwatanci tare da kwatanta su da na Daidaitacciyar Hausa. Saboda haka, ga wasu kaɗan daga cikin su bisa tsarin gidan rediyon Vision F.M. tare da ma’anar su cikin daidaitacciyar Hausa. Ga misalin su:
Karin Harshen Sakkwatanci Katsinanci
Agalemi buuzuu
Alkwatoo Koɗi
Akaihwa Farcee
Arbiiƙii Unguwarzoma
Badaraa Tsuntsu
Bagajaa Kwatamii
Bundii Wutsiyaa
ɓartakee Abaawaa
ɓaaci Zaagi
ɓaace-ɓaace zage-zage
Hwarcee Yaatsaa
Gambuu ƙyaure
Gulbii Koogii
Gujjiyaa Gyaɗa
Guroo Kuɓeewaa
Gidan bisa Beenee
Habɗii Tookaa
3.2.2 KALMOMI MASU MA’ANA ɗAYA, AMMA SAUTI BAMBAN
A nan ƙasa, in an za a ga Sakkwatatun kalmomi waɗanda ma’anarsu ɗaya da na Daidaitacciyar Hausa, amma sautin su ya bambanta da na Daidaitacciyar Hausa. Ga misalan kaɗan daga cikin su:
Sakkwatanci Daidaitacciyar Hausa
Allooba Annooba
Al’amurraa Al’amura
Attanin Litinin
Anguwaa Unguwaa
Assibit Asabar
Bahwaadee Bafaade
Busshiyaa Bishiya
Bukii Bikii
Ciyyoo Ciiwoo
Jibjii Juujii
Laahiyaa Laafiyaa
Laƙyas Laƙwas
Lallai Lalle
Mussai Mushee
Sabkaa Saukaa
Saashee Saashi
Shibkaa Shuukaa
Shidda Shida
Sihilii Sifirii
Suuraa Suumaa
Swaɓaanii Saaɓaanii
Swaahwaa Saafaa
Sakkwatanci yakan yi amfani da waɗansu kalmomi waɗanda shi kaɗai ya keɓanta da su, sai wasu daga cikin kare-karen harshen yammaci wato ‘yan dangin Sakkwatanci, waɗanda su ma ba kowace kalma ce daga cikin kalmomin suke amfani da ita ba. Amma wannan ba ya haddasa bambancin ma’ana a kan ire-iren waɗannan kalmomi da sauran kare-karen harshen Hausa ke amfani da su.
Wannan na nufin idan Sakkwatanci ya yi amfani da wata kalma, to akwai irinta a Daidaitacciyar Hausa da sauran kare-karen harshen Hausa sai dai akan sami bambancin ƙwayoyin sautuka a tsakanin su. Sannan kalmar ba ta da bambancin ma’ana da takwarar ta, da ke samu a cikin sauran kare-karen harshen Hausa ko a Daidaitacciyar Hausa. Alal misali, Sakkwatanci yakan yi amfani da kalmar ‘katattara’ wato wani sashe na ƙafar mutum mai tattare da nama, wanda ya taso daga guiwa zuwa ɗuwawu). Amma a Daidaitacciyar Hausa da wasu kare-karen harshen Hausa sukan yi amfani da kalmar ‘cinya’ a maimakon katattara. A nan, ma’anar katattara da cinya ba bambanci. Akan iya a sami bambancin tsarin kalmomin, amma ma’anarsu ɗaya. Ko kuma bambancin furuci, amma ma’ana ɗaya tsakanin Sakkwatanci da Daidaitacciyar Hausa ko ma da sauran kare-karen harshen gabashi.
3.3 JUMLOLIN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
A babi na biyu an kawo nau’o’in jumlar daidaitacciyar Hausa, tare da misalan su, har nazarin ya fitar da tsarin azuzuwan kalmomin da kowace jumla ta ƙunsa. A wannan babin an kawo jerin wasu daga cikin kalmomi mallakar karin harshen Sakkatanci tare da taƙaitaccen bayani dangane da karin harshen Sakkwatancin kansa. Sannan an waiwayi yadda tsarin nau’o’in ginin jumlolin karin harshen Sakkwatanci tare da nazartar su daki-daki. Ga yadda nazarin ya gudana:
3.3.1 SASSAUƘAR JUMLA A KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Kamar yadda Sassauƙar Jumlar daidaitacciyyar Hausa ta ƙunshi yankin Suna da kuma abin da aka faɗi a game da suna; haka ma Sassauƙar jumlar Sakkwatanci ta ƙunshi yankin suna da kuma yankin abin da aka faɗi a game da suna. Misali wasu daga cikin jumlolin Sakkwatanci.
a- Bala ya c canye abinci.
Sn aik maf lokt Aik Sn ƙb
S A K
b- Musa na ya s sha ruwa
Sn aik maf lokt Aik Snƙb
S A K
c- Musa ya k kaama Zaki
Sn aik maf lokt Aik Sn ƙb
S A K
d- Ali ya k kashe Kare
Sn aik maf lokt Aik Sn ƙb
S A K
3.2.2 JUMLAR TAMBAYA
Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake yi domin tambaya. Saboda haka Sakkwatanci yakan canja wasu daga cikin kalmomin na tambaya, amma kuma wasu basu canjawa, kamar yadda daidaitacciyar Hausa take faɗinsu haka Sakkwatanci shi ma yake faɗinsu. Ga wasu daga cikinsu.
- Shi ina Maryam tat tahi ?
klm tmb almtmb
- Shin waa aŋ ka aika ?
klm tmb almtmb
- Shin yaushee na za a dawo wa aiki ?
klm tmb almtmb
- Shin ƙaƙaa za a yi ?
klm tmb almtmb
- Yayaa Audu yah hwaɗi jarabawa ?
klm tmb almtmb
- Mii Ali yas saye ?
klm tmb almtmb
- Wa suŋka zo ɗazu ?
klm tmb almtmb
3.2.3 JUMLAR UMARNI
Jumlar umurni kamar sauran jumloli ita ma jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci daidai take da jumlar umurni ta daidaitacciyar Hausa. Haka ma takan zo da kalma ɗaya rak, a matsayin jumla, kuma ta ba da ma'ana cikakkiya, kalmar da take zuwa da ita, itace kalmar aikatau. Ga kaɗan daga cikin misalan jumlar umurni a karin harshen Sakkwatanci.
- Ali tashi !
- Kabiru rubuta !
- Musa Karanta !
Haka jumlar ya kamata ta kasance amma saboda wasu dalilai sai ta koma kamar haka:
Misali:
Tashi !
Rubuta !
Karanta !
3.2.4 JUMLAR KOREWA
Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci ita ma daidai take da jumlar korewa ta Daidaitacciyar Hausa. Sai dai kuma ita wannan jumlar ta korewa ta ɗan bambanta da ta daidaitacciyar Hausa a wasu baƙaƙen haruffa na Sakkatanci da suka saɓa da na daidaitacciyar Hausa. Ga wasu daga cikin su:
- Baa Ali yas sayee ba.
- Rabi ba ta tahi makaranta ba.
- Baa kuɗɗi banki.
- Agwagwa ba ta tashi sama sosai.
- Baabu ruwa a randa.
- bai dace a hana bara ba.
- Kaada kaa tahi/kar ka a tahi.
- 3 NAɗEWA
Wannan babi wato babi na uku inda aka bayyana karin harshen Sakkwatanci a bisa ra’ayoyin masana da kuma ire-iren jumlar Hausa karin harshen Sakkwatanci, tare kuma da kawo wasu misalai daga ciki. A sassauƙar jumlar Hausa ta karin harshen Sakkwatanci an yi bayani cewa ita ma jumlar ta ƙumshi yanki biyu wato yankin suna da kuma yankin abin da aka faɗi a game da suna, haka ita ma jumlar karin harshen Sakkwatanci tana bias tsarin S.A.K, kamar haka sassauƙar jumlar daidaitacciyar Hausa. Jumlar tambaya ta karin harshen Sakkwatanci ita ma kamar jumlar tambaya take ta daidaitacciyar Hausa, jumla ce da ake yi domin tambaya. Jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar umurni take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne akan umurni. Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar korewa take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne a kan korewa sai dai ta bambanta da ta daidaitacciyar Hausa kaɗan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.