Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Zamfarci Da
Rabe-Rabensa (3)
NA
AHMAD MUHAMMAD KABIR
BABI NA BIYU
TSARIN
GABATAR DA AIKI
2.0 SHIMFIƊA
Da sunan
Allah mai rahama mai jinƙai. Godiya ta
tabbata ga ubangijin talikai mai kowa mai komai a nan za a gabatar da wannan
babi na biyu tare da bayyanawa a taƙaice abubuwan
da ya kamata a nazarta a cikin wannan babi, waɗanda suka haɗa da bitar
ayukkan da suka gabata. Haka kuma idan aka nutsa a cikin babin an dubi
rubutattun littafai, bugu da ƙari an dubi
maƙalu tare da kundayen bincike domin ƙara
wa aikin armashi.
2.1 BITAR
AYUKKAN DA SUKA GABATA
Harshen
Hausa, harshe ne mai faɗin gaske musamman a fagen nazari, wanda ya ƙunshi
ɓangarori uku,
muhimmai; akwai ɓangaren
nazarin harshe da ɓangaren nazarin al’adu da kuma ɓangaren
nazarin adabi. A wannan aikin za a yi tsokaci a kan abin da ya shafi harshe.
Idan za a yi tsokaci a kowane ɓangare to ya zama dole a yi bitar
ayukan da suka gabata domin samun haske ga abin da ake son a yi magana a kai.
An gudanar da
ayuka da yawa waɗanda suke da
kama da wannan aikin. Wasu daga cikin waɗannan ayuka da aka ci
karo da su sun haɗa da:
2.2
RUBUTATTUN LITTAFAI
A cikin
nazarin littattafai an duba littafai da dama da za su ƙara mana
haske domin gudanar da wannan aikin, kaɗan daga ciki sun haɗa da;
Mukhtar A.B
(2017) Hausa da “Karorinta” a cikin littafin ya yi bayanin Karin harshen Hausar
Zamfarci da al’ummar Hausawa mazauna Zamfara suke amfani da ita. Wannan aiki
yana da kama da wannan bincike da za a yi mai taken “Zamfarci da Rabe-Rabensa”.
Abdullahi G.
(2005) a cikin littafinsa babi na biyu ya yi bayani a kan ma’anar karin harshe,
bai tsaya a nan ba, marubucin ya yi bayani a kan ire-iren kare-karen harshen
Hausa. Wannan aiki ya yi kama da wannan aikin da za a gudanar. Alaƙar
aikin da wanda ake gudanarwa shi ne, tarayya a Karin harshe, domin wannan aikin
zai nazarci Zamfarci da rabe-rabensa.
Zarruƙ
da wasu (2010) sabuwar Hanyar Nazarin Hausa sun yi bayanin harshe da
kare-karensa. Ahmadu Bello (1992), Kare-karen Harshen. Wannan aiki nasu yana
magana game da kare-karen harshen Hausa, yana da alaƙa da wannan
bincike mai taken “Zamfarci da Rabe-Rabensa” domin shi ma karin harshen Hausa
ne.
2.3 MUƘALU
Masana da
dama da ɗalibai
‘yan’uwana sun yi rubuce-rubuce da dama a kan abin da ya shafi kare-karen
harsuna. Saboda haka an samu maƙalu masu
daman gaske a kan kare-karen harsuna, musamman karin harshen Zamfarci da
rabe-rabensa. A nan za a dubi waɗansu maƙalu daga
cikinsu waɗanda suka yi
kama da wannan aikin.
Halidu (2016)
ya bayyana ma’anar harshe da muhimmancinsa ta
fuskokin sadarwa, tattalin arziki da al’ada da yaɗa addini da
siyasa. Ya kuma yi bayanin irin Hausar Zamani (wato irin Karin Harshen Zamani).
Alaƙar
wannan aiki da wanda ake gudanarwa ita ce karin harshen zamani da ya yi magana
domin marubucin ya taɓo ire-iren kare-karen harshen Hausa wanda
yake da alaƙa da wannan aiki na nazarin karin harshen
Zamfarci da rabe-rabensa.
Hashim (2015)
ya yi tsokaci a kan yadda al’ummar Hausawa mazauna yankin masarautar Gumel suke
Hausar su, musamman wajen kore magana. Wannan yana da mukusanciyar alaƙa
da aikin nazarin karin harshen Zamfarci da rabe-rabensa domin marubucin ya yi
nazarin karen harshen Gumalanci ne da mutanen Gumel ke yi, inda marubucin ya
haskaka irin abubuwan da aka yi amfani da su wajen wannan bincike.
Fadama (2012)
Marubucin ya yi bayanin a kan ‘yanayi da tsarin musayar gurbi a Karin harshen
Zamfaranci”. Wannan aikin yana da kama da wannan mai taken Zamfarci da
rabe-rabensa, domin ya fito da kalmomin karin harshen Zamfaraci ƙarara.
2.4 KUNDAYEN
BINCIKE
Za a duba
kundaye iri daban-daban domin gano irin gudummuwar da suka bayar, a game da
karin harshen Zamfarci. An lura cewa ta haka ne za a iya samun ainihin cikakkun
bayanai a kan wasu ayukan da suka rigaya suka shuɗe, sannan ana
ganin ta haka ne za a iya gano irin nasara ko gudummuwar da suka bayar a cikin
bincikensu sannan kuma shi wannan aiki ya san inda zai ɗora domin ƙarin
bunƙasa iri-irin wannan nazari.
Bugu da ƙari,
har kullum masana suna bunƙasa fagen
ilimi ne ko nazari yayin la’akari da ayukan da aka rigaya aka yi a wannan fagen
da nufin bunƙasa shi, musamman ta fuskar kawo sababbin
abubuwa ko gyare-gyare a inda ake da buƙatar haka.
Yakasai
(1999) a kundin digiri na uku mai taken “Hausar kan iyaka; nazari a kan Hausar
Illela da Ƙonni (Janhuriyar Nijar)” Wanda ya gabatar a
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayaro, Kano. A wannan aiki ya
nazarci yadda ɗaiɗaikun harsuna
da kare-karen harshe da ke haɗuwa a kan iyaka ta Illela da Ƙonni
(Jamhuriyar Nijar) kan samar da wani karin harshe na daban. A cikin aikin ya yi
nazari a kan tasirin wasu harsuna kan wasu sanadiyar haɗuwarsu wuri ɗaya da kuma
abin da dangantakar ta su ta haifar na sauyi a cikin harshen Hausa. Alaƙar
wannan aiki ita ce tarayya a fagen nazarin karin harshe, inda marubucin ya
nazarci karin harshe na kan iyaka, inda wannan aiki ya nazarci karin harshen
yanki wato yankin Zamfara.
Abida da wasu
(2018) Nazarin Fitattun sigogin karin Hausar Zamfarci. A cikin kundin sun yi
bayanin yadda sigogin karin Hausar Zamfarci. A nan wannan aiki yana da kama da
binciken da a ke yi, amma a nan za a yi aiki ne a kan Zamfarci da rabe-rabensa.
Abbas (2000)
a kundin digirinsa na farko da ya gabatar a sashen koyar da harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, mai taken “Karin Harshen Hausa na
Zamfarci”. A wannan aiki marubucin ya yi ƙoƙarin
bayyana yadda karin harshen Zamfarci yake da kuma siffofin da suka bambanta shi
da Daidaitacciyar Hausa. Alaƙar aikin da
wannan ita ce tarayya a fagen nazarin karin harshen Zamfarci, amma marubucin ya
kalli banbancin karin harshen Zamfarci da Daidaitacciyar Hausa ne, amma wannan
aiki ya kalleshi ta fuskar rabe-raben karin harshen Zamfarci
Sheshe
(1986); a kundin digirinsa na farko wanda ya gabatar a sashen koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato mai taken: Nazarin Lahajar Haɗejanci da
Daidaitacciyar Hausa” Wannan aiki ya yi shi ne don fito da bambance bambance a
tsakanin Hausar Haɗejanci da Daidaitacciyar Hausa, inda ya raba
aikinsa a kan daidaicin furuci da bambancin wasula da ƙirar kalma da
jumloli da kuma ma’ana. Alaƙar aikin da
wannan ita ce, marubucin ya yi nazarin karin harshen Haɗejanci ne ta
fuskar furuci da ƙirar kalma da kuma ginin jimloli, inda wannan
aikin ya nazarci karin harshen Zamfarci da rabe-rabensa. Alaƙa
ita ce tarayya a nazarin karin harshe.
2.5
GUDUMMUWAR AIKI GA ILIMI
Gudummuwar
aiki ga ilimi, kasancewar bincike wata hanya ce ta gano ko neman wani abu domin
warware wata matsala ko bayar da gudummuwa a wani fagen ilimi na musamman,
wannan bincike ne na ilimi wanda zai bayar da gudummuwa ta musamman a fagen
ilimi. Daga cikin gudummuwar da wannan bincike zai bayar a fagen ilimi ta haɗa da:
i.
Samar da abin karatu ga ɗalibai ‘yan
gaba da sakandare domin warware wasu matsaloli na karatu kamar jinga ko gabatar
da muƙalu da sauransu.
ii.
Fito da karin harshen Zamfarci a sarari yadda
yake da kuma yadda ake yinsa. Haka kuma domin samun sauƙin fahimtar
karin harshen ga ma’abota bincike.
2.6 TSARIN
GABATAR DA AIKI
Tsari a nan
yana nufin yadda za a gudanar da aikin domin sauƙaƙawa
ga mai karatu. Wannan bincike zai gudana ne cikin babi biyar. Babi na ɗaya shi ne
gabatarwa, wanda ya ƙunshi dalilin gudanar
da bincike da muhallin bincike da hanyoyin gudanar da bincike. Bugu da ƙari
za a yi tsokaci a kan muhimmancin bincike da kuma matsalolin bincike sai kuma
daga ƙarshe naɗewa.
Babi na biyu
zai yi magana ne a kan bitar ayukkan da suka gabata inda aka mai da hankali a
kan ababe muhimmai kamar haka; rubutattun littafai da muƙalu da
kundayen bincike. Haka kuma gudummuwar aiki ga ilimi da tsarin gabatar da aiki
daga ƙarshe kuma naɗewa.
Babi na uku
mai suna “kare-karen harshen Hausa”, inda zai yi magana ne a kan ma’anar harshe
da kare-karen harshen Hausa. Bugu da ƙari, za a yi
tsokaci a kan karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma, sai naɗewa.
Babi na huɗu mai suna
“Zamfara ƙasa” yana magana ne game da ƙasar
Zamfara inda zai dubi tarihin Zamfara da karin harshen zamfarci da rabe-raben
karin harshen Zamfarci. Daga bisani a yi tsokaci a kan Daidaitacciyar Hausa, ƙarshe
naɗewa.
Babi na biyar
kuwa shi ne kammalawa, inda za a taƙaita aikin
sannan shawarwari da kuma ta’arifin wasu kalmomi, sai naɗewa.
2.7 NAƊEWA
A wannan babi
na biyu mai taken; “Tsarin Gabatar da aiki”. Daga farko ya zo da bitar ayukkan
da suka gabata, inda ya kawo rubutattun littafai da muƙaloli da kuma
kundayen bincike. Haka zalika gudummuwar aiki ga ilimi daga ƙarshe
ya bayyana tsarin yadda za a gabatar da aikin.
0 Comments
Post your comment or ask a question.