Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamfarci Da Rabe-Rabensa (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Zamfarci Da Rabe-Rabensa (4)

NA

AHMAD MUHAMMAD KABIR

 

BABI NA UKU

KARE-KAREN HARSHEN HAUSA

 

3.0 SHIMFIƊA

Babi na biyu ya kawo bitar ayukkan da suka gabata, ya kuma duba rubutattun littafai da muƙalu da kundayen bincike da gudummuwar aiki ga ilimi, daɗin-daɗawa ya kawo tsarin gabatar da aiki.

 

Wannan babi na uku kuwa zai yi bayanin harshe da kare-karen harshen Hausa. Bugu da ƙari, zai yi bayanin karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma.

 

3.1 MA’ANAR HARSHE

Masana da dama sun bayyana ra’ayinsu a kan ma’anar harshe daga cikinsu akwai:

 

Sapir (1956), ya bayyana ma’anar harshe da cewa “Wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulɗa tsakanin mutum wadda dabbobi ba su da irin ta”.

 

Lado (1964) ya ce “harshe ya zama shi ne rai ko zuciyar duk wani tunani da aiki na Ɗan-dam musamman dangane da abin da mutum ke ji game da ƙabilarsa ko ƙasarsa ko addininsa ko kuma yadda shi kansa ya ɗauki kansa”.

 

Yakasai (2012) ya bayar da ma’anar harshe da cewa “Furuci ne mai ma’ana da mutane ke yi ta hanyar magana domin su isar da saƙon da zukatansu suka ƙudurta da irin mutanen da ke iya fahimtar wannan nau’i na sarrafa harshe ba tare da ishara da hannu ba”.

 

Ɗantumbishi (2004) ya ce “harshe shi ne magana ko furuci wanda ya bambanta mutum da dabba”.

 

Ta la’akari da ma’anonin da masana suka bayar ana iya cewa, harshe wata muhimmiyar hanya ce wadda Ɗan-adam yake amfani da ita wajen isar da saƙo ta hanyar magana ko rubutu ko kuma ishara. Kuma ya nuna cewa harshe shi ne tushen mu’amala tsakanin al’ummomi daban-daban na duniya.

 

3.2 KARE-KAREN HARSHEN HAUSA

Masana ilimin harshe irin su Sani (2001) sun yi ƙoƙarin kasa kare-karen harsuna zuwa gida biyu wato karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma. Karin harshen gabas karin harshe ne na mutanen gabacin ƙasar Hausa. Kafin mu shiga ƙasar Hausa ya dace mu san ina ne ƙasar Hausa? A ƙoƙarin gano ina ne ƙasar Hausa abu ne da masana ilimin tarihi da kuma masana nazarin ƙasa suka daɗe suna tafka muhawara a kai. Sai dai kowane masani yakan yi ƙoƙarin kafa hujja dangane da dalilin da za su kare ra’ayinsa.

Ƙasar Hausa: Ainihin ƙasar ta asali tana Afrika ta yamma ne, a farfajiyar nan da ke tsakanin hamadar sahara da dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun Atlantika daga kudu, kuma ana kiran ƙasar da sunan sudan ta yamma, wato tsakanin tafkin Cadi da gwiwar kogin Kwara a can yamma. In aka duba taswirar Afrika, za a sami ƙasar Hausa a tsakanin layi na goma sha biyar (15N) zuwa na goma sha takwas (18N) na arewa da Ikwaita. Kuma ƙasar tana tsakanin layi na takwas (8E) dana goma sha biyu (12 E) a gabas da layin Greenwhich.

Taswirar ƙasar Hausa

 

Taswirar kasar hausa

A bisa bayanin Shaihi malami Mahdi Adamu, ƙasar Hausa ta asali ta faro ne tun daga lalle da Asodu, can arewa maso gabas da Agades. Daga nan ne Gobirawa suka taso, da kaɗan kaɗan har suka zo inda suke a yau a Nijeriya.

 

A yanzu kuma, Hausa tana yaɗuwa ne, tana ƙoƙarin komawa har zuwa gidanta na Jiya, ƙasashen iyakar ƙasar Hausa a kudu kuwa shi ne, Yawuri da Zariya, da inda Bauci ta yi iyaka da Kano. (Mahadi 1998).

 

Gurun gabas (wato Birom) ita ce iyakar ƙasar Hausa daga gabas. A yamma kuwa bakinta Filingue. A bayanin Shaihi malam Mahadi Adamu (1988), ƙasar Hausa ita ce inda ba a buƙatar naɗa Sarkin Hausawa. Wato wannan bayani ya ware duk wasu zango-zango, inda ake magana da Hausa. Amma idan ana maganar inda harshen ya yaɗu ne, ya zama harshe na ɗaya ko na biyu abakin mutane, to wuraren da aka ambata a nan ba su fi rabin ƙasar Hausa ba.

 

Ƙasar Hausa galibinta shimfiɗaɗɗiya ce, mai yawan sarari. Akwai ta da tsaunuka da tuddai jifa-jifa, kuma duk yawan wannan ƙasa, manyan koguna biyu ne suka ratsa cikinta, da kogin Rima da kogin Haɗejiya. Haka kuma kogin Kwara ya zama kamar iyaka ne daga yammacin ƙasar.

 

Kogin Rima shi ne ya taso daga ƙasar Zamfara, ya gangara ya yi arewa zuwa Nijar, sa’annan ya karkata kudu, ya bi ta yamma da Sakkwato, ya je ya faɗa cikin kogin Kwara. Shi kuma kogin Haɗejiya, masominsa, a ƙasar Kano ne. Daga nan ne ya gangara gabas, ya bi ta Gashuwa ta Gaidam, ya je ya faɗa ta tafkin Cadi.

 

3.3 KARIN HARSHEN GABAS

Kamar yadda muka faɗa a baya cewa masana ilimin harshe sun kasa kare-karen harsuna zuwa gida biyu wato karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma. A nan za a yi tsokaci ne a kan karin harshen gabacin ƙasar Hausa. Kare-karen harshen gabacin ƙasar Hausa su ne Kananci da Zazzaganci da Dauranci da Bausanci da Haɗejanci da Guddaranci, waɗannan kare-karen harsuna mutanen gabashin ƙasar Hausa su ne ke amfani da su wajen mu’amalarsu ta yau da kullum.

 

3.4 KARIN HARSHEN YAMMA

Bugu da ƙari, akwai kare-karen harsunan yamma. Kare- Karen harshe na yammacin ƙasar Hausa su ne:

 

Sani (2001), Sakkwatanci da Gobiranci da Zamfarci da Katsinanci da Aranci. Bugu da ƙari, akwai Kurhwayanci da Kabanci da Adiranci. A taƙaice waɗannan kare-karen harsuna su ne masana suka kasa zuwa gida biyu wato karin harshen gabas da karin harshen yamma.


 

3.5 NAƊEWA

A wannan babi na uku kamar yadda bayani ya gabata ya kawo muna ma’anar harshe da ra’ayoyin masana daban-daban bayan nan an kawo kare-karen harshen Hausa, an kuma kalli karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma, sai kuma daga ƙarshe an zo da naɗewa.

Post a Comment

0 Comments