Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Zamfarci Da
Rabe-Rabensa (2)
NA
AHMAD MUHAMMAD KABIR
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
1.0 SHIMFIƊA
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, mai kowa mai komi, wanda ya ƙaga
halittar Ɗan - adam, ya kuma sanar da Ɗan-
adam abin da bai sani ba.
Salati da ɗaukaka su ƙara
tabbata ga jagoran wannan al’umma wato Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da
sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa ranar tsayuwa. Ina ƙara
godiya ga Allah da ya ƙaddara gudanar da
wannan bincike a fannin ilimi, domin kammala karatun digiri na farko
A wannan babi
mai suna “Gabatarwa” za a yi bayanin ababe muhimmai kamar haka: Dalilin gudanar
da bincike domin babu wani aiki da za a gabatar ba tare da dalili ba. Saboda
haka wannan aiki akwai dalilin gabatar da shi idan aka nutsa a cikin babin za a
ga dalilin. Haka kuma, za a yi tsokaci a kan muhallin bincike, daga bisani a yi
sharhi a kan hanyoyin gudanar da bincike. Bugu da ƙari, za a
kammala babin da matsalolin bincike, daga ƙarshe naɗewa.
1.1 DALILIN
GUDANAR DA BINCIKE
Kamar yadda
rayuwa take babu wani abu da Ɗan-adam zai
yi ba tare da manufa ba, ko dalilin yin aikin. Babu shakka na daɗe ina
sauraren yadda kare- karen harshe yake a tsakanin al’umma mabambanta, musamman
Karin harshen Zamfarci a yankin Zamfara. Saboda haka ana lura da yadda kowane
yanki yake amfani da irin nasa karin harshe.
Dalilin
gudanar da wannan bincike shi ne domin kawo sauƙi ga ‘yan’uwa
na ɗalibai da
kuma masu nazari, la’akari da cewa akwai ƙarancin
littafai da suka yi bayani a kan kare-karen harshe musamman Zamfarci. Wannan
dalilin ya sa na ga ya dace a gudanar da wannan aiki domin kawo sauƙi
a tsakanin ɗalibai da
kuma masu bincike, don wayar da kan al’umma game da kare-karen harshen
Zamfarci, kuma ina kira ga ɗalibai da masu nazari su ci gaba da
rubuce-rubuce don samar da ababen karatu ga ɗalibai ‘yan
gaba da firamare domin su samu abin karantawa.
Haka kuma za
a fito da ma’anar wasu kalmomi da kuma yadda suke a cikin waɗansu
kare-karen harshe, da kuma nuna wa ‘yan baya hanya domin ƙara zurfafa
bincike musmaman dangane da karin harshen Zamfara.
Daga cikin
dalilan sun haɗa da gudanar
da wannan nazari domin neman takardar shedar kammala digirin farko na Sashen
Nazarin Harsuna da Al’adu.
1.2 MUHALLIN
BINCIKE
Kafin shiga
cikin aiki ya kamata mu leƙa taskar
masana domin mu san ma’anar muhalli. Soba (2015) ya ce “Muhalli shi ne mazaunin
da ke kewaye da mutum da dukkan abubuwan da suke taimakawa rayuwarsa ta yau da
kullum, muhalli ya samu ne ta hanyar hikima da basirar da Allah Ubangiji ya yi
wa Ɗan-adam”.
Muhalli shi
ne wani abu da ke kewaye da mutum kuma wanda ya shafi rayuwarsa, kuma muhalli
kan iya zama wurin zaman ka da al’ummar da ke tare da kai da kuma dukkan abin
da ya shafe ka. Muhalli a wannan bincike shi ne wuri ko bagiren da aka gabatar
da wannan bincike.
Wannan bincike
an gudanar da shi ne a jihar Zamfara da kuma wasu yankuna ko kuma garuruwa da
ke cikin jihar Zamfara. Haka kuma za a shiga ɗakunan karatu
na makarantu domin faɗaɗa bincike, musamman ɗakin karatu
na Jami’ar Tarayya Gusau da makarantar horas da malamai ta kimiya da fasaha da ƙere-ƙere
ta gwamnatin tarayya da ke Gusau wato (FCET). Haka kuma za a yi amfani da ɗakin karatu
na ma’aikatar yaɗa labaru da
gidan tarihi duka mallakar Gwamnatin jihar Zamfara. Haka kuma za a leƙa
ofishin ‘yan jarida na jihar Zamfara.
1.3 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
An bi hanyoyi
da dama don samun nasarar gudanar da wannan bincike, domin neman sauƙin
gudanar da wannan aiki kamar haka:
Da farko an
fara bincikar littattafai waɗanda suka yi shige da wannan aiki
domin fahimtar yadda za a tsara wannan. Daga nan kuma an shirya yin hira da waɗansu ɗaiɗaikun mutanen
cikin wannan jiha ta Zamfara domin fahimtar bambance-bambance da ake samu a
tsakani ta fuskar karin harshe. Haka kuma za a tattauna da wasu malamai masana
kuma gogaggu musamman a fagen harshe domin su ba da irin tasu gudummawa, haka
kuma za a yi bincike a waɗansu makarantu maƙwabtan wannan
jaha kamar Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da
makarantar horar da malamai ta Shehu Shagari duka a jihar Sakkwato.
1.4
MUHIMMANCIN BINCIKE
Kasancewar
duk wani aiki ko wani abu da mutum zai gudanar ko kuma zai gabatar ya kasance
yana ɗauke da
muhimmin abu a cikinsa.
Wannan bincike
ya kasance ba shi ne bincike na farko da aka gudanar ba game da karin harshen
Zamfarci, sai dai a wannan bincike za a ƙara zurfafa
bincike da nazari don taimakawa ƙwarai da
gaske ga ɗalibai ‘yan
asalin jihar Zamfara da ma sauran jihohin wajen Zamfara su fahimci fitattun
kalmomin karin harshen Zamfarci a cikin sauƙi.
Wannan aiki
zai taimaka ƙwarai wajen ɗalibai masu
karatun harhse, musamman na makarantun gaba da Sakandare domin ya taɓo fannoni da
dama masu ɗauke da
muhimman abubuwa musamman tunawa na baya wasu riƙaƙƙun
kalmomi waɗanda za su
fahimtar da su ainihin Hausar Zamfara da garuruwa da ake kira Zamfarawan asali,
da dai sauransu.
1.5
MATSALOLIN BINCIKE
Kamar yadda
mai karatu zai gani a nan matsalolin bincike sun fara tun daga lokacin da aka
aminta da wannan batu da za a magana a kai, kafin shiga cikin aikin za a kawo
ma’anar “matsala” kamar yadda masana suka yi tsokaci a kai, inda suke
cewa: Fulani da wasu (2014) “Matsala na nufin duk wani abu da ya zo ya takura
wa rayuwar Ɗan-adam, ya hana mutum ya kasa cimma burinsa ɗari- bisa ɗari”.
Matsala tana
iya zama tawaya ga duk wani abu da mutum zai yi ko ya yi ko kuma yake yi. Bisa
ga wannan ra’ayin za a iya cewa “matsala na nufin duk wani ko wata ƙuntatawa
da rayuwa kan shiga ta fili ko ta ɓoye.
Bahaushe ya
ce “Ko wattuna bara bai ji ɗaɗin bana ba”.
Wannan bincike da ake gudanarwa ya yi karo da matsaloli da suka taso haiƙan,
ta fuskoki dadama, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:
Matsala ta
farko da aka fara cin karo da ita, ita ce tun lokacin da aka aminta da batun da
ake son a yi bincike a kansa, tun daga nan aka fara tunanin hanyoyin da za a bi
domin gudanar da wannan bincike da yadda za a tsara shi da kuma inda za a samun
kayan gudanar da wannan binciken.
Sai kuma
matsalar rashin wadatattun littafai da za a yi amfani da su a ya yin gudanar da
wannan bincike.
1.6 NAƊEWA
Wannan babi
na ɗaya shi ne
gabatarwa, babin ya kawo muna dalilin gudanar da bincike da muhallin bincike da
hanyoyin gudanar da bincike da muhimmancin bincike da matsalolin bincike da
kuma yadda masana suka tattauna game da muhalli da muhimmanci da kuma
matsaloli, daga ƙarshe babin ya zo da naɗewa.
0 Comments
Post your comment or ask a question.