Ticker

6/recent/ticker-posts

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (3)

NA

ABDULRAHMAN BALA

Taubasantaka

BABI NA BIYU

DANGANTAKAR BAZAMFARE DA BADAKKARE

2.0 GABATARWA

Zamfarawa da Dakarkari wasu al’ummomi ne masu alaƙa da juna. Dukkansu sun ɗauka cewa dangin juna suke, sai dai mafi yawan Zamfarawa da Dakarkari ba su da cikakken bayanin yadda dangantakar ta kasance. Idan har buƙatar a san haka ɗin ta taso, sai dai a zurfafa bincike a waɗansu manyan gidajen sarautu ko kuma a wurin manyan malamai masana tarihi. To ya abin ya ke ne? shin ko akwai wata alaƙa ta dangantaka a tsakanin waɗannan mutane? Ko kuwa sam babu, kawai maƙwabtakace tsakaninsu? Ko kuma launin fata ne ya haɗasu?

 

Akan haka ne wannan babi zai yi nitso sosai a cikin waɗannan al’ummomi don yin bincike tuƙuru a kan irin dangantakar da take tsakaninsu.

 

2.1 MA’ANAR DANGANTAKA

Dangantaka na nufin kwatanta wani abu da wani abu domin a ga dacewar kamanninsu da juna. Kowace al’umma tana da al’ada ko al’adu waɗanda suka yarda da su ko suka dogara da su, kuma suke alfahari da su (Haruna: 2002).

 

Dangantaka dai tana samuwa ko afkuwa ne a tsakanin al’ummomi guda biyu ta sanadiyar wurin zama inda wani kan yi tasiri a kan wani ta hanyar harsunan da suke amfani da su, da halayya ko al’adu, ko hulɗa ta kasuwanci ko fatauci da dai sauransu. Wani lokaci ma kwatsam sai ka ga sun zama abokan wasan juna (Taubasai), sakamakon faruwar waɗansu abubuwa a tsakaninsu, kamar irin auratayya da yaƙi da dai sauransu (Adam: 1978).

 

Saboda haka, wannan bincike zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajen binciko ko gano asalin abin da ya haifar da dangantakar da ke tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa, tare da taimakon sanin tarihin waɗansu ƙabilun da waɗannan al’ummomi suka yi maƙwabtaka da su.

 

2.2 WANE NE BAZAMFARE

Bazamfare dai mutum ne shi ma kamar irin sauran mutane. Sannan kuma Bazamfare shi ne ɗan ƙabilar Hausawa mai magana da harshen Hausa, musamman Karin harshen Zamfara (Gusau: 2005).

 

Bazamfare mutum ne mai son ɗan uwansa, ga shi da jinƙai gas hi da son zumunci. Haka kuma yana da ladabi da biyayya ga shi kuma mutum ne wanda ya mayar da hankali wajen neman ilimin addinin musulunci da na zamani.

 

Har wa yau, Bazamfare mutum ne mai son baƙi ga shi da taimakon kai da kai. Wannan na cikin dalilin da ya sa dangantakarsa da Badakkare ta yi ƙarfin gaske har ta yi ƙarko.

Sauda yawa Bazamfare yakan raba gidansa kashi biyu, ya ba baƙo ya zauna don girmamawa gare shi da taimakonsa. Shi ya sa za a ga cewa ƙasar Zamfara cike take da baƙi daban-daban, ƙabila-ƙabila, kuma su zauna zaman lafiya da jin daɗi. Ta haka ne ya sa duk wanda ya zo Zamfara  ko da kwana ɗaya ne ba zai so ya barta ba. Idan ma ya barta, to Zamfara za ta zame masa abar so ko da yaushe. A duk inda ya tafi sai ya ji yana son ya dawo mata (Kabiru; 1988).

 

Tarihi ya tabbatar da cewa Bazamfare, mutum ne ƙaƙƙarfa mai yaji, jarumi kuma haziƙin manomi, Jangwarzo ne a fagen yaƙi. Haka kuma ya kan iya tunkarar kowace runduna ta mayaƙa ba tare da fargaba ko razana ba. Bazamfare mayaƙi ne wanda ya sha kai hari zuwa ƙasashen Zabarma da Katsina da Kano da Yawuri da Kabi da kuma Adar. To haka ne Bazamfare ya sha gwabzawa da wasu dauloli maƙwabtansa tun ma ba Katsina da Kabi da Ƙwanni ba (Haruna 2002).

 

Don haka za mu iya cewa Bazamfare tun asali shi mutum ne mai son baƙi, tare da tarbon baƙo cikin halin karamci da girmamawa. Shi ya sa za mu ga a kodayaushe ƙasar Zamfara cike take da baƙi ta ko’ina. Haka kuma Bazamfare mun fahimci cewa shi mutum ne jajirtacce a fannin noma da kuma kiyo. Haka zalika jarumin gaske ne a fannin yaƙi, wato a filin daga wanda ba ya shakkar tunkarar abokan gabarsa. Kuma a cikin bayanan da suka gabata za a fahimci cewa Bazamfare mutum ne wanda bai son lalaci da raggwanci da rashin sanin ciwon kai. Yakan yi faɗa matuƙa a kan mutum wanda aka lura bai kula da rayuwarsa ba, ko marar tanadi da rashin aikin yi.

 

2.3 ASALIN BAZAMFARE

Bahaushe na cewa “Duk wanda bai da asali to shege ne.” Don haka Bazamfare mutum ne mai cikakkaen asali. Bazamfare kamar yadda muka sani dai cewa shi mutum ne kamar kowa. Bazamfare Kalmar tillo ce, jam’in Kalmar ita ce Zamfarawa kuma mutanen ƙasar Zamfara. Saboda haka domin samun sauƙin sanin asalin Bazamfare za mu yi amfani da Kalmar jam’in sunan wato Zamfarawa; domin mu ji sauƙin gano asalin Bazamfare.

 

Da farko dai ƙasar Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata ɗaya daga cikin Banza bakwai, waɗanda ba hausawan asali ba ne. Dalilin haka shi ne ana ganin bare-bari ne asalin Zamfara. Wani masani yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. Ya cigaba da cewa Zamfarawa suna danganta asalinsu daga maguzawa maharba waɗanda suka zauna a yankin ƙasar Kano kafin zuwan Bagauda a Dutsen Dala. (Gusau:2005).

 

To a nan a fahimtata za mu iya cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun fil azal, domin mun fahimci cewa sun dai sami asalinsu daga Maharba maguzawa. Wani kuma an ce sun samu ne daga tsatson Bare-bari a tarihance.

 

Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manyan manyan mutane ne masu girman jiki da yadda ake danganta asalinsu daga samudawa. Akwai wasu manya-manayn kaburbura guda shida a Dutsi an ce kaburburan Sarakunan Zamfara ne na asali. Saboda girman kaburburan ana kiransu da Kaburburan samudawa. Ga alamu Zamfarawan asali na da girman jiki sosai (Kabiru: 1988).

 

Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a ƙasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan sarkin Zamfara. An ce Zamfarawa sai da suka kwashe shekaru bakwai ba su naɗa sarki ba a Dutsi, daga nan sai suka naɗa Sarkinsu na farko mai suna Dakka. Dakka ne sarkin Zamfara na farko Don haka sarkin Zamfara ana masa take da “Gimshiƙin gidan Dakka”. Sarakuna huɗu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniya ‘yar Goje, an ce ‘yar Goje ta yi mulki a tsakiyar ƙarni na sha uku (13) miladiyya. Kuma ta shahara a lokacinta, domin har a dajin Kuyam Bana da ke ƙasar Ɗansadau ta jahar Zamfara ta kai ziyara. Takan zauna da majalisarta tana yanke hukunci a kan lamurran da suka shafi al’ummarta. A yanzu haka akwai wata fitilarta da ke ajiye a gidan hukumar adana kayan tarihi da al’adun gargajiya na jihar Zamfara da ake dangantawa da ita.

Bayan rasuwarta a Dutsi sai aka naɗa ƙanenta mai suna Baƙuruƙuru a matsayin sabon Sarki. Kuma shi ne wanda ya ƙirƙiri sabuwar Hedikwatar Zamfarawa, mai suna “Birnin Zamfara” (Birnin Alƙalawa) daga ƙarshe- ƙarshen ƙarni na goma sha uku zuwa farkon ƙarni na goma sha huɗu. Shi ne dalilin da yasa Zamfarawa suka tashi daga Dutsi zuwa can Birnin Al-ƙalawa. Birnin Alƙalawa wata gonar Alƙalin Zamfara ce wadda aka mayar hedikwatar Zamfara. Wasu kuma suna ganin cewa sarkin Baƙuruƙuru shi ne Sarkin Zamfara na bakwai, amma masana tarihi sun haƙiƙance cewa sarakuna ashirin da uku ne aka binne a garin Dutsi. Sai dai Sarki na bakwai daga cikin waɗannan sarakunan shi ne wanda ya kafa Birnin Zamfara (Birnin Alƙalawa) (Muhammad: 1982) da (Haruna: 2002).

 

Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya haɓaka sosai, sun katange shi da ganuwa. Har yanzu a ƙofar tsohon garin na Alƙalawa akwai rusasshiyar ganuwa mai tsawon mil goma sha uku da ƙofofin garin hamsin (Gusau 1995).

 

A nan za mu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara. Don haka za mu iya dogaro da ɗan wannan taƙaitaccen bayanin da muka samu daga wurin masana, kuma muna sa ran cewa zai taimaka musan asalin kowa ake ce ma Bazamfare.

2.4 ƘASAR ZAMFARA

A wannan fanni kuwa za mu yi bayani ne a kan abin da ya shafi ƙasar Zamfara. Kuma za mu duba tun daga irin yanayin ƙasar da kuma irin abubuwan da ta ƙunsa; kamar yadda bayanai suka gabata a cikin rubuce-rubucen masana.

 

Da farko dai ƙasar Zamfara tana da muhimman garuruwa waɗanda suka haɗa da Dutsi da kiyawa da Jata da Banga da Tumfafi da Alƙalawa da sauransu. Ƙasar Zamfara ta mallaki faɗin ƙasa wanda ya kama tun daga Kogin Rima a shiyar Arewa zuwa gulbin Zamfara a ɓangaren kudu. A ɓangaren gabas kuma ta yi iyaka da Dajin Rugu zuwa Dutsin Disau. A sashen yamma, wannan farfajiya ta Zamfara tana sashen yamma na ƙasar Hausa, kuma ta sami matsayi babba na jaruntaka kamar yadda sauran dauloli na wannan lokaci suka samu waɗanda suka haɗa da Katsina da Kano da Daura da Kabi (Nadama G: 1986).

 

Ƙasar Zamfara ƙasa ce shimfiɗaɗɗiya wadda take a kan tudu, ba ta da yawan kwararra. Har wa yau ƙasar tana da tsaunuka jefi – jefi a wurare daban-daban kamar tsaunukan da ke tsakanin ‘Yandoto da Langa- Langa. Akwai wasu kuma a Mada da tsaunin Tutari. Ita kuma Wanke dukkanta tsauni ce, sannan akwai su a Labbo mai Komo. Manyan gulaben da suka ratsa cikin ƙasar Zamfara su ne, gulbin Sakkwato wanda ya fito daga ƙauyen Ɗandume ya biyo ta Kwaren Ganuwa da Rijiya da Gidan Fakkan da Gidan Malamai ya faɗo Gusau ya zarce zuwa Bunguɗu da Maru har zuwa Sakkwato. Sai gulbin Gagare wato na Wonaka wanda ya kama har Ƙauran Namoda. Akwai ta kuma da yanayin ƙasar noma mailaka da fadama da mai damɓa- damba. Akwai kuma inda take da jar ƙasa da wadda ba a rasa ba mai Jigawa (Gusau 2002).

 

Haka kuma akwai tsameku (tsamiyoyi) da suke da muhimmanci a ambace su saboda abubuwan tarihi da suka auku a wajensu. Misali Tsamiya Hausa ta Dabbakal wadda “Ƙauran Hausa,” Sarkin yaƙin Sarkin Maraɗi Ɗan Baskore ya ajiye sansamin yaƙinsa a ƙarƙashinta lokacin da ya kawo yaƙi Gusau inda ya kwana goma sha huɗu bai sami nasara ba ya tashi. Sai kuma tsamiya tara ta hanyar Rawayya, nan ne dogarai ke zama masu rakiyar Jama’a zuwa Rawayya, saboda kare kai daga ‘yan samame da ‘yan fashi. Akwai kan wurin Goga wanda yake babban zango ne na masu zuwa Lokoja da Ikko. Sai kuka mai sheƙa wadda ta zama kamar rimi a tsakar gari duk inda aka ɓullowa Gusau sai an gan ta, ta shanye sauran itatuwa. Waɗannan itatuwa da wasunsu akan yi musu Camfin ajiye iskoki, irin su Ɗantsatsumbe da jita- kuku da sauransu. Ƙasar Zamfara, sarkin Zamfara, shi ne jagaba wanda yake da wuƙa da nama a wajen zartar da hukunci a al’ummar Zamfarawa, shi ya ke da iko mai cin gashin kansa ga gudanar da mulkin jama’a. Amma duk da haka, sarkin Zamfara yakan naɗa wasu mutane waɗanda suke taimaka masa da ake kira masu sarauta (Kabir: 1988).

 

Ta ɓangaren sana’o’i waɗanda ake gudanarwa na yau da gobe, to a nan ma ba a bar ƙasar Zamfara ba, domin har akwai wasu sarautu na musamman da ake naɗawa wasu masu sana’a waɗanda suka shahara a fannin sana’ar tasu. Misali, sarkin Noma, Sarkin Aska, Sarkin Maƙera, Sarkin Fawa, Sarkin Marina, Sarkin Magori kuma dukkaninsu suna da nasu yankuna da suke gudanar da ayyukansu na mulki (Isma’il G: 1989).

 

Idan muka kalli bayanan da suka gabata da idon basira za mu iya fahimtar wani abu dangane da ƙasar Zamfara, wadda ke da faɗin gaske da ta ƙunshi abubuwa daban–daban, kamar irin su al’barkatun ƙasa, masana’antu, noma, kiyo da dai sauransu.

 

Ta ɓangaren ilimin addinin musulunci kuwa ƙasar Zamfara ta yi zarra musamman a fannin Hardar Alƙur’ani mai girma domin kuwa bincike ya nuna mana cewa mafi yawancin mahaddatan Najeriya masu ƙananan shekaru suna fitowa ne daga Jahar Zamfara (Fira da Malam Kanoma).

 

Ta fuskar Kasuwanci kuwa, ƙasar Zamfara ta cigaba sosai, domin idan muka duba za mu ga irin tarin kamfanonin gurzar auduga da ake da su, ga kuma irin tarin Fulazoji (Plazas) da ake da su, ga kuma tarin gidajen kiyon kaji da sauransu. Irin waɗannan abubuwa duk cigaba ne da ƙasar Zamfara take samu.

 

25 WANE NE BADAKKARE

Badakkare shi ne mutumin da ke magana da harshen Dakkarci, kuma shi ɗan asalin ƙabilar Dakkarawa ne. Idan ana son a gane Badakkaren asali to za a iya yin amfani da waɗannan bayanai da za su biyo baya.

 

Mafi yawan Dakkarkari ko in ce Badakkare za a gan shi da hakora masu kaifi da tsini (Feƙaƙƙu), ƙananan za a gan shi ko a same shi da tsananin haƙuri. Bai cika fushi ba ko (bai faye fushi ba), idan aka tsokane shi (Haruna 2002).

 

Badakkare za a gan shi yana da tsagar gado kusan ko’ina a fuskarsa da kuma dukkan sassan jikinsa, domin yakan yi zanen ƙaɗangare ko wani abu a hannunsa da sassan jikinshi (Sani 1986).

 

Badakkare yana da ra’ayin cin nama sosai don haka ake yi mashi kirari da “Na zuru komai nama”. Don haka ko da yaushe za ka tarar haƙoranshi fiƙaƙƙu ne, wato ana fiƙe ma shi su a yi musu tsini da kaifi (Haruna: 2002).

 

Badakkare jarumin mutum ne mai ƙarfin hali da ƙwazon aiki. Yana da juriya kan komai duk irin wahalar da ke cikin abu, kowanne iri ne kuwa, to Badakkare yana iya jurewa. Wannan ya sa Dakarkari suka yi yawa a cikin aikin soja. Duk irin wahalar horar da jami’an sojojin da ake yi, Wannan dalilin ya sa ake cewa “Shiga ba fita shiga, sojan Badakkare.

 

Sakamakon haka ne Dakarkari suka yi yawa sosai a aikin soja, har akwai lokacin da aka hana a ɗauki sabbin ma’aikata (Sojoji) Dakarkari. Saboda sun yi yawa sosai (Fira da Hajiya Fatima Zuru).

 

Badakkare bai cika damuwa da yanayin sanyi ko zafi ba, don haka bai cika yawan sutura (tufafi) ba yakan yi amfani da warki kawai, komai tsananin hunturu ko sanyi. Idan har aka tambaye shi (Badakkare) amsar da yake bayarwa ita ce “Kai ka damu da shi". Duk inda aka samu Badakkare za a tarar ba shi da kasala, mutum ne mai ƙarfin jiki kuma bai cika jin gajiya ba.” Ga himma kuma duk abin da ya sa kansa ko aka sa shi yakan yi bakin ƙoƙarinsa. Haka kuma manya da ƙanana, maza da matansu ba su da ƙyuiya ko kasawa ga dukkan lamurra, (Robins 1967).

 

Wasu daga cikin Dakarkari mazauna ƙauye, za a same su maras tsafta ga jiki da kuma tsaftar gidaje. Basu damu da sai sun tsaftace gidajensu da kuma jikinsu ba. Haka kuma ga su masu sauƙin rayuwa, ba su da girman kai. Ga su da ladabi da biyayya da kuma girmama baƙo, kamar yadda na tabbatar a kauyen Gamji na ƙasar Zuru (Ziyarar Gani da ido, 18/08/2019).

 

Wannan shi ne taƙaitaccen bayanin da za mu iya bayarwa amsar da za mu iya badawa akan wane ne Badakkare, kuma ina sa ran zai zama wani ɗan haske da zai taimaka ma mai nazari ko mai bincike.

 

2.6 ASALIN BADAKKARE

Duk ka ji an ce asalin abu, to fa so ake aji tarihin abun, domin cikin tarihin za a samu gamsasshen bayani ko bayanai da za su bayyana asalin abun. A taƙaice dai ana so a san tarihin Badakkare, saboda a cikinsa ne za a zaƙulo asalinsa na gaskiya. Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba, muddin ana son haƙa ta cimma ruwa” Wato a samu cikakken tarihin na Badakkare, to dole sai an yi amfani da jam’in Kalmar Badakkare. Yin amfani da Kalmar Dakarkari ya fi sauƙi sosai wajen bincike asalin akan yi amfani da Kalmar tillo ta Badakkare, don haka za a yi binciken ne akan tarihin Dakarkari.

 

Da farko Dakarkari kamar sauran al’ummomi suke su ma, suna da hanyoyin da suke bayar da tarihinsu. Kuma kowace hanya tana da madogara ta musamman da ake ganin cewa wannan bayanin yana iya zama gaskiya. A wannan ɓangare za a yi bayani ne game da tarihin asalin Dakarkari ta la’akari da ra’ayoyin masana. Akwai wasu tsofaffin mutane Dabai (Wato hediƙwatar Dakarkari) sun bayar da tarihin su kamar haka.

 

Dakarkari sun samo asali ne daga Bukkuyum ta cikin ƙaramar hukumar mulkin Bukkuym ta Jahar Zamfara. Sun ce wani mutum ne ya fito zuwa yankin wanda ake kira Dabai. Ya fito ne yin farauta har ya kawo wurin, in da ya zauna a wurin da iyalansa har zuriyarsa ta bunƙasa.

 

A wancan lokacin Dabai daji ce, wanda ya ke cike da itatuwa da kuma namun daji. To sai mafarauta suka riƙa shiga don su yi farauta. Lokacin da Dabai ya zauna sai wurin ya zama gari. A cikin wannan bayanin sun cigaba da cewa; har zuwa farkon ƙarni na goma sha tara sarkin Bukkuyum shi ke naɗa hakimi a Dabai, wanda daga baya aka fi sani da suna Marafan Dabai (Kasancewarsu asalinsu daga Bukkuyum ne  (Bugaji: 1985).

 

Wani bayani shi ne, na “Dakka” wasu masana tarihi irin su (PG da Haris: 1938) sun ce Zamfarawan Dutsi a gundumar Zurmi, ‘yan uwan Dakarkari ne, su kuma Dakarkari jikokin Dakka ne. Wato mai yawon farautar nan da aka faɗi a ƙasar Bukkuyum, ya zama ɗa ne ga Dakka wanda ya yi ƙaura zuwa ƙasar Dakarkari. Ya kuma sawa mutanensa suna “Dakka” don riƙo da sunan Kakansa.

 

(Gujiya M. 1987) ya ce: Duk ƙabilun da ke Zuru ban da Achipawa sun samo asalinsu ne daga Tawayen da Zamfara ta yi wa ɗaular Kebbi ne, inda suka gudu daga garuruwan daular. Bayanin ya cigaba da cewa su Dakarkari asalinsu sojojin ƙasar ne na Sarkin Kebbi har ana kiran su Dakarkarun Kebbi.

 

Sai kuma al’ummar Dakarkari na yankin Wasagu a arewa maso gabashin zuru da ta ƙunshi garuruwa irin su Bena da Ribah da kanya da Waje da Macika. Tarihin ya nuna Katsinawa ne farkon zama a wannan gunduma, kuma sun taso ne daga kudancin Katsina suka zo suka zauna a wasagu ta yau, sun zaɓi zama a Wasagu ne saboda waɗansu muhimman abubuwan da suke cikinta. Waɗanda suka haɗa da ƙasar noma maikyau, da dajin farauta, sai kuma hanyar kasuwanci da ta haɗa Wasagu da wasu wurare, musamman Katsina da Zamfara da ƙasar NUPE  da abubuwan da ake samu a wurin aikin ƙarfi.

 

Katsinawa laka sun fara zama a “Kangon Wasagu” daga nan suka zarce Wasagu kai tsaye. Dalilin tafiyarsu ana danganta ta ne da burinsu na faɗaɗa ƙasa da inganta rayuwarsu.

 

Tarihi ya nuna cewa yayin da mutanen Riɓah (Ƙasar Zuru) suka baro Katsina, sun fara zama ne a wani ƙauyen ne a Arewacin Gusau wanda ake cewa Riɓe. Don haka zancen ya tabbatar da cewa waɗannan Dakarkari na yankin Wasagu akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu da Katsinawa da kuma Zamfarawa (Muhammad (1982).

 

Idan aka dubi waɗannan bayanai na masana, da suka gabata, za a fahimci cewa Dakarkari sun samo asali ne daga ƙasar Katsina, dalili shi ne, Asalin Dakka, (Kakan Dakarkari) mutumin Katsina ne. Kuma mafarauci wanda yawon farauta ya kawo shi ƙasar Zamfara a garin Bukkuym, inda ya fara zama na ɗan wani lokaci. Daga baya kuma sai ya koma ƙasar Zuru da zama a gain Dutsem inda ya ɗauko iyalansa ya dawo da su nan. Ya cigaba da gudanar da rayuwarsa a nan, sannan a hankali wurin ya fara zama gari. Sakamakon mahalba da ke ya da zango a wurin. Akwana a tashi, sai ɗaya daga cikin ‘ya’yan Dakka, ya shiga daji don yin farauta ko yawon farauta. Ya kutsa kai cikin daji sai da har ya kai ƙasar Kebbi (wato Zurun) da ya yada zango a nan, sannu a hankali sai Zuriarsa ta fara yawaita a wurin, to shi kuma saboda riƙo da sunan Baban shi, sai ya sa ma Zuri’arsa suna “Dakka.” Wannan shi ne sunan mahaifinsa, su ne a yau aka wayi gari ake kira da ƙabilar Dakarkari. Suna zaune ne a ƙasar zuru da ke cikin jahar Kabbi. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin asalin badakkare.

 

2.7 ƘASAR BADAKKARE/ MAZAUNIN BADAKKARE 

Ƙasar Badakkare ko Dakarkari maƙwaɓciyar ƙasar Zamfara ce mai cike da mutane iri-iri ‘yan asali da kuma baƙi. Wasu jama’ar kan shiga cikin ƙasar su zama tamkar su ne ‘yan asalin ƙasar domin daɗewarsu a cikinta.

 

Ƙasar Badakkare ƙasa ce mai faɗi wadda ta ƙunshi garuruwa daban-daban a cikinta. Kamar irin garin Gamji, Bogaɗi, Peni da Senchi da garin Zuru, inda a nan ne babbar hediƙwatarsu, take sai kuma garin Dabai da Wasagu, da Bena da Ribah da Waje, da macika da Kanya. Waɗannan garuruwa ne da al’ummar Dakarkari ke zaune a cikinsu, kuma a nan ne suke gudanar da rayuwarsu. Suna gudanar da kasuwanci, auratayya, farautunsu, da sauransa. Ba za a ce duk mutanen da ke zaune a cikin waɗannan garuruwa Dakarkari ne ba, ba kowane mutum ba ne Badakkare a cikinsu, saboda ba za a rasa baƙi ba (Bugaji: 1985).

 

Ƙasar Dakarkari ƙasa ce mai tarin itatuwa, ga dazuzzuka ga kuma ƙasar noma mai kyau wadda duk abin da aka shuka a cikinta muna sa ran za ta karɓeshi. Ga ta da daɗin zama babu tashin hankali a cikinta, sai zaman lafiya (Firaka da Sakina Kinfa).

 

Daga cikin wasu yankunan ƙasar Dakarkari tsarin gidajensu ya sha bamban da na sauran al’umma. Misali a wasu ƙauyuka kamar Gamji da Bogaɗi tsarin gidajensu  daban ne. Za ka ga katangun gidajensu guntaye ne, ba su cika tsawo sosai ba, za ka iya hango ginin ɗakunan da ke cikin gidajen daga waje. Amma na cikin gidan ba zai iya hango na waje ba, har sai ya ɗan taka wani abu (Fira da Hajiya Fatima Zuru).

 

Ta ɓangaren noma kuwa, ƙasar Zuru tayi fice wajen noma shinkafa, dawa, masara, gero, sai dai an fi noman dawa sama da komai. Sai kuma shinkafa, domin daga cikin nau’o’in shinkafar da muke da su akwai wadda ake kira da suna (Shinkafa yar Zuru). Dakarkari suna kiran mutumin da ya shahara sosai ta fannin noma da suna Daudu (wato sarkin noma), saɓanin Hausawa da suke amfani da Kalmar wajen kiran ɗan sarki (mai jiran gado) da ita. Haka zalika a ƙasar Dakarkari ba’a ba da sarauta kowace iri dole sai ɗangidan sarautar misali; irin Sarki, Waziri, Ɗan iya, Sarkin Fada da sauransu. Haka kuma ta fannin farauta, ita ba mai yinta sai ɗan gado, wanda a ƙasar Zuru ana kiransu da suna mahalba. (Fira da Sarkina Kinfa).

 

A ƙasar Dakarkari akwai wata al’ada da mutanen ƙasar ke yi, wato idan za a yi aure tsakanin Namiji da mace, akwai wani noma da ake yi a shekara bakwai (7) sunan wannan noma (Gwalmo) kuma namiji (mijin da zai auri yarinyar) shi ke yin wannan noman tsawon shekaru (7). Amma yanzu, tunda zamani ya canja an rage yin noman, sai dai a biya sadaki a yi aure. Sannan kuma a al’adar ƙasar Zuru aurensu bai mutuwa da an ɗaura, shi kenan babu rabuwa, sai in ɗaya daga ciki ya mutu. Haka zalika, matan Dakarkari ba su dogara da sai mazajensu sun ciyar da su ba. Idan Allah ya hore ma mata abu za ta yi amfani da kuɗinta, ko abun hannunta ta yi cefane ta haɗa abinci kowa da kowa ya ci. Suna yin haka ne saboda rufa ma juna asiri, ba su son ‘ya’yansu su yi ta gararanba a gari (Fira da Alh. Danƙo Osabu Zuru).

 

Ƙasar Dakarkari mutanen cikinta mutane ne masu son junansu da kuma taimaka ma juna a kan al’amuran rayuwa na yau da kullum. Dalili shi ne akwai wata al’ada da mutanen ƙasar ke yi, wato idan miji ya mutu ya bar mata da ‘ya’ya, mutanen unguwa da sauran ‘yan uwa da abokan arziki sukan haɗa gudummawa ta hatsi da sauran kayan amfanin gona su baiwa iyalan mamacin; kamar haka, wasu su ba da masara tiya biyu biyu, wasu dawa tiya biyu biyu, wasu shinkafa, wasu gero. Duk dai hatsin da Allah ya hore maka to tiya biyu za ka ɗebo ka ba da, wasu kuma kuɗi, wasu manja da sauransu. Haka za a haɗasu aje a kai ma iyalan wannan mamaci, (Fira da Sakina Kinfa). Ta cigaba da bayani cewa, Aladu sun fi yawa a ƙasar Dakarkari, sannan baccin yawa ma, sunfi awaki daraja a ƙasar, domin akwai Kirstoci da arna waɗanda sun fi cin naman Aladu da na awaki.

 

Sakamakon waɗannan bayanai da suka gabata dangane da ƙasar Dakarkari, mun fahimci cewa ƙasa ce mai tarin abubuwa, kamar yadda bayanai suka nuna mana, cewa ƙasace mai ɗauke da tarin mutane ‘yan gida da kuma baƙi. Haka zalika ƙasar ta samu cigaba sosai sakamakon zuwan addinin musulunci da na kiristanci, duk da cewa tarihi ya tabbatar da cewa shekaru masu yawa da suka wuce mutanen ƙasar Dakarkari ba su da wani addini bayan ‘yan tsafe-tsafe da su ke yi, sai daga baya wuraren shekara alif ɗari tara da tamanin da biyu (1982) ne aka fara ɗora tubalin kira ga al’ummar ƙasar Zuru da su shiga addinin kiristanci, wato lokacin da Turawa suka fara kutso kai (Adam 1978).

 

A halin yanzu ƙasar Dakarkari; ƙasa ce mai cunkoson gidaje da dama na mutane, yawancin gidajensu na laka ne, daga baya suka kwaikwayi na zamani wato ginin suminti. Sai dai ba su cika yawa sosai ba, kuma gidajen lallaƙe da juna suke. Haka zalika akwai yawan ‘ya’yan itatuwa kamar mangwaro, ayaba, gwaba, da icen kashuna, wanda shi ke yawancin gidaje akwai shi.

 

2.8 ALAƘAR BAZAMFARE DA BADAKKARE

Bazamfare da Badakkare sun sami kansu ne a mazauni wuri guda masu alaƙa da juna. Dukkansu sun ɗauki cewa dangin juna suke, shi ya sa suke kallon junansu a matsayin taubasai. Sai dai mafi yawan Zamfarawa da Dakkarawa ba su da cikakken bayanin yadda dangantakar ta kasance. Idan har ana buƙatar a san hakan to, sai dai a zurfafa bincike a manyan gidajen Sarautu ko wurin masana tarihi; domin a binciko ko a gano alaƙar da ke akwai a tsakanin waɗannan ƙabilu guda biyu.

 

Kamar yadda tarihi ya nuna cewa su waɗannan ƙabilu suna da alaƙa mai girma sosai a tsakaninsu. Alaƙar ma ba ta wuri guda ba, a a akwai ɓangarora da dama da ke nuna yadda alaƙar ta ƙullu tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa. Kamar ɓangaren kasuwanci, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu; sai dai ba haka kara zube ya kamata in cigaba da zayyano bayanai ba, yana da kyau a kawo hujjoji ƙwarara domin ba za a rasa wasu bayanan masana ba dangane da ita wannan alaƙa ta Bazamfare da Badakkare. Duk da dai an san cewa “Tatsuniyar Gizo ba ta wuce ƙoƙi.” Wato a tarihiance, babu makawa a kowane irin bincike a ka yi, za a tarar cewa akwai alaƙa a tsakanin waɗannan ƙabilu guda biyu. Matuƙar za a yi lakari da daɗaɗɗen tarihin asalin waɗannan ƙabilu, to dole ne a sami bayanai masu inganci a kan dangantakar dake tsakaninsu ta jinni da ta zamantakewa.

 

Adam (1978), ya nuna a cikin wani aikinshi cewa, Zamfarawa da Dakkarawa ‘yan ‘uwan juna ne tun asali, inda ya kafa hujja da cewa, Dakkarawa sun samo asali ne daga Wani mutum mafarauci mai yawon farauta mai suna “Dakka.” Saboda ɗaya daga cikin ‘ya’yanshi ne ya yi hijira zuwa wani daji mai suna “Dabai” inda ya zauna a nan tare da iyalinsa suka haifi ‘ya’ya masu yawa. Suma ‘ya’yan suka yi aure har suka hayayyafa sosai, sai zuria ta samu. Dabai sunan ɗan ɗan Dakka ne, kuma sunan shi ne aka saka ma dajin. Dabai shi ne ya sa ma zuri’arsa suna “Dakka” saboda riƙo da sunan Babanshi.

 

Shi wannan masani mai suna Adam, da wannan ne yake kafa hujjarsa a kan yarda da cewa Bazamfare da Badakkare ‘yan uwa juna ne. Wannan ra’ayi yana da alaƙa sosai da ra’ayin wani masani mai suna Haris, Wanda ra’ayinshi ya gabata a can baya cikin bayanai. Idan kau har masana biyu za su yi taro a kan ra’ayi guda to akwai ƙamshin gaskiya a cikin wannan ra’ayi. Saboda in dai za a ce Bazamfare da Badakkare ‘yan uwan juna ne, to wannan wata babbar alaƙa ce mai girma tsakaninsu.

 

Akwai wani masani da ya ce “akwai auratayya a tsakanin Dakarkari da Zamfarawa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka a ƙasar Hausa, don ya ƙara tabbatar da hakan sai ya ba da misali ya ce “Daga cikin iyalan sarkin Zuru da na Dabai akwai Zamfarawa a cikinsu, wanda sanadin aure ne ya kai su ƙasar Zuru da Dabai, kuma cikin iyalan Sarakunan, (Idris 1946).

 

A wannan ra’ayi za mu iya cewa akwai ƙamshin gaskiya a cikinsa, dalili aure yana daga cikin manya- manayn ginshiƙan da ke ƙulla ko haɗa alaƙa a tsakanin al’ummomi ma banmbanta. Saboda za ka ga Bazazzaga ta auri ba Kano, ko Basakkwata ta auri bazamfare, don haka, wannan ba abin mamaki ba ne don an ce Badakkare ya auri Bazamfara. Saboda haka wannan ma za mu iya cewa alaƙa ta ƙara haɗa waɗannan ƙabilu guda biyu.

 

Tarihi ya bayyana cewa a lokacin yaƙin Nagwamatse alaƙar Bazamfare ko Zamfarawa da Dakkarawa ta ƙara yawa sakamakon bayin Dakarkari da mayaƙan Zamfarawa suka riƙa kamawa. Mafi yawan yara daga cikinsu sun tashi ne a hannun Zamfarwa. Wannan dalili ya sa Hausa ta zama harshensu, haka kuma wasu Zamfarawan da mayaƙan Dakarkari suka kama a matsayin bayinsu, suka tafi da su ƙasar lelna don yi masu bauta. (P.G. da Haris 1938).

 

Wannan ma wata hujja ce da za mu iya cewa ta ƙulla alaƙa a tsakanin Bazamfare da Badakkare, sakamakon yaƙe- yaƙen da suka faru, a wancan zamanin da ya gabata.

 

(Haruna 2002) shigowar Turawan mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya, Zamfarawa sun haɗe kai da ƙabilar Dakarkari inda suka riƙa yin tawaye suna fanɗare wa buƙatun Turawan domin tumɓuke ko (cire) wasu sarakunan asali, waɗanda ba su yi biyayya garesu ba. Kamar yadda ta faru a lokacin da suka yi wa sarkin sakaba, da kuma sarkin Zuru.

 

Akwai wani sarki da ake kira Bogaji, Sarkin Bukkuyum na jahar Zamfara. Yana cewa, “Dakkarawa sun haɗu da Zamfarawa da kuma Katsinawa tun lokacin da Bazamfare ba Hausa ce harshen da ya ke amfani  da shi ba na asali. Domin Bazamfare ya sami harshen Hausa ne a matsayin harshen Kasuwanci, saboda kasancewar ƙasar Zamfara cibiyar Kasuwanci ce, tun kafin jihadin ƙarni na goma sha tara a ƙasar Hausa. Duk da ya ke Badakkare bai faye son yin kasuwanci zuwa wurare masu nisa ba. An tabbatar da yanayin kasuwanci ne da ƙasashen da yake kusa da su, daga cikin su har da ƙasar Zamfara (Sakaba, 1974).

 

Wannan bayani za mu iya amincewa da shi, idan aka yi la’akari da waɗansu abubuwa. Misali kamar sarkin Bukkuyum wanda asalin dakarkari daga can ne suka fito. Bayan haka gidan sarauta gida ne da ake aje kayan tarihi sosai a cikinsa. Don haka za mu iya cewa anan ma kasuwanci ya ƙara ƙulla alaƙa a takanin Bazamfare da Badakkare.

 

Waɗannan ra’ayoya da suka gabata za su iya taimaka mana sosai wajen fahimtar ko tabbatar da cewa akwai alaƙa a tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa. Irin hanyoyin da masana suka kafa hujja da su duka babu hanyar da ba ta iya ƙulla alaƙa a tsakanin al’umma mabambanta. Misali kasuwanci, auratayya, yaƙi, ‘yan uwantaka, dukkan waɗannan suna iya ƙulla alaƙa, kuma babu wanda babu a tsakanin Bazamfare da Badakkare. Waɗannan abubuwa su suka ƙulla alaƙa mai ƙarfi a tsakanin Zamfarwa da Dakkarawa. Hakan ya sa wata Badakkara mai suna Hajiya Fadima Zuru ta yi ikirarin cewa za su iya wasa da kowane Bazamfare, kuma su faɗa mishi magana son ransu tun daga gwamna, Sarki, Ciyaman da sauransu. Domin su taubasansu ne, don haka akwai wasa a tsakaninsu. Sannan ta ƙara da cewa idan Bazamfare ya kashe ɗan Badakkare ko Badakkare ya kashe ɗan Bazamfare babu abin da zai faru, saboda yan uwantakar da ke tsakaninsu. Don haka dole su yi haƙuri da juna. Alaƙa ce ta ba ta ƙwarin guiwar furta waɗannan maganganu, domin da babu ita da hakan ba ta faru ba.

 

2.9 NAƊEWA

Bayanan da suka gabata a cikin wannan babi sun ƙunshi abubuwa daban-daban, kuma masu alaƙa da juna. Har na so in ce wannan babi za a iya ce mishi “Tumbin Giwa” saboda irin muhimman bayanan da ya ƙunsa. Yawancin bayanan duk tarihi ne, kuma kusan shi ne tsani ko gadar ko ƙashin bayan wannan bincike. Hakan ya sa ya ɗauki tsawon lokaci ana tattara bayanansa.

 

An yi amfani da ra’ayoyin masana da kuma firarraki da wasu mutane, tare da ziyarar wasu wurare kamar wasu garuruwa, da kuma ɗakunan karatu don tattara bayanan. Babin dai ya yi magana ne akan ma’anar dangantaka, tare da bayyana ko wane ne Bazamfare da kuma asalin Bazamfare, sai ƙasar Zamfara, daga nan kuma aka yi bayani a kan wane ne Badakkare da asalin Badakkare, sai mazaunin Badakkare, da kuma alaƙar Bazamfare da Badakkare. Waɗannan su ne muhimman bayanan da Babin ya ƙunsa.

Post a Comment

0 Comments