Ticker

6/recent/ticker-posts

Sharhin Littafin Matar Mutum Kabarinsa

Idan an yi tsai an lura za a ga hoton da ya bayyana da sunan littafin ta fuskar jigo-jimla a iya cewa saƙo ko jigon wasan na soyayya ne, bisa manufar da marubucin wasan ya tsara. Idan muka yi nazari ta jigo-tahaƙiƙi ma, za a ga hakan.

Sharhin Littafin Matar Mutum Kabarinsa

Ali Usman Umar
Translation Unit – News and Current Affair Department
Kano State Radio Corporation
alusumshariff@gmail.com

Matar mutum kabarinsa

Marubuci:                         Bashir Faruk Roukbah

Sunan Littafi:                  Matar Mutum Kabarinsa

Rukunin Adabi:            Wasan Kwaikwayo

Harshe/Kari:                 Hausa/Daidataccen Karin Harshe

Maɗaba’a:                        Northern Nigeria Publishing Company

Wurin Ɗab’i:                   Zaria, Nigeria

Shekarar Wallafa:       1974

Yawan Shafuka:            48

Marubucin wannan littafi, Bashir Faruk Roukbah, tun daga hoton bangon littafin ya nuna saurayi ɗaya da ’yanmata biyu. A inda ko mutum bai shiga cikin littafin ba, zai fahimci ruhin soyayya da aure cikin wannan littafi. A gaba ɗaya marubucin ya tafiyar da ruhin wasan ta hanyar nau’in wasan tir-madalla inda Nura ya ja zaren wasan tun daga farko har zuwa ƙarshe a matsayin jangwarzo. Da farko rayuwarsa ta ƙuntata cikin wahalar soyayya da ya yi ta fama har ya haƙura, amma sai ya kasance a ƙarshe ya sami farin ciki. Idan aka duba za a ga marubucin ya tsara wasansa daki-daki ta kan lokaci-miƙe wato mai jeriya kamar cikin sarka—daga farko sai tsakiya sannan ƙarshe. An nuna cikin littafin cewa kafin a fara aure abu na farko tsakanin saurayi da budurwa shi ne, fara jan hankalin juna ta hanayar kwarkwasa da jefa kalmomin yabo da kuma so da ƙauna a tsakanin juna. Daga nan, sai a tsunduma cikin kogin soyayya wanda zai kai ga yin aure. Wannan ita ce rayuwar da Bashir Faruok Roukbah ya kalla, tare da nuna irin tankiyar da ke dabaibaye masoya a kan turbar soyayya. Kuma wannan littafin wasan kwaikwayon ƙirƙirarsa mawallafin ya yi.

 

Jigo

Idan an yi tsai an lura za a ga hoton da ya bayyana da sunan littafin ta fuskar jigo-jimla a iya cewa saƙo ko jigon wasan na soyayya ne, bisa manufar da marubucin wasan ya tsara. Idan muka yi nazari ta jigo-tahaƙiƙi ma, za a ga hakan.

 

Warwarar jigo

A nan ne za a fito da jigo-tahaƙiƙi, ta hanyar haƙiƙance cewa jigon soyayya ne ko kuwa. Haka ma idan da wasu ƙananan jigogi za a yi ƙoƙarin tabbatar da su. Idan aka duba waɗannan wurare a cikin littafin za a ga yadda aka ayyana ƙwayar jigon soyayya cikin wannan littafi. Misali:

 

NURA: Jimmai za ki karɓi tawa gudummawar. Ko wannan ta ishe ku?  (shf. 6).

 

NURA: Haka kika faɗi a fili, amma kuma ina matuƙar samun haka. (shf 8).

 

JIMMAI:   Ai babu komai idan ya ji ni da ma can ban damu da shi ba, don ba na son sa (shf 9).

NURA: Mai yiwuwa ne ki ji mamaki idan na faɗa miki irin soyayyar da na… (shf 10).

 

Daga abin da za a gani na ƙwayar jigon soyayya akwai bayar da kyauta sai kuma a zo kan yaba kyauta da kalmomin soyayya. Kai a taƙaice duk fitowar da ta nuna Nura da Jimmai akwai irin waɗannan kalamai na soyayya. Haka ma, idan muka je ga kalaman Nura da Asabe. Misali:

 

NURA: Dalili shi ne soyayya wacce ba abin da ya gagara ta sa mutum ya yi… (shf 30).

 

ASABE:…ina ganin shiga gidan masoyi ba wani abin mamaki ba ne…(shf 31).

 

Kusan duk haɗuwar Nura da Asabe, kamar irin haɗuwar Nura da Jimmai ce.

Akwai wasu ƙananan jigogi da suka fito cikin wannan wasa, kamar al’adun bikin aure da kuma lalacewar tarbiyyar, musamman a tsakanin iyaye da ’ya’yansu. Misali, irin yadda suke bijire wa ra’ayin iyayensu. Su kuma kafe a kan wanda suke so. Wannan a taƙaice kenan game da jigo da warwarar jigo.

 

Zubi da tsari

Marubucin wasan ya tsara wasan cikin kashe-kashe guda takwas inda ya nuna matsayin Nura da Jimmai da Asabe da kuma Sambo waɗanda labarin ya fi karkata a kai. Sannan kowane kashi yana da fitowa-fitowa.

1) Kashi na farko na da fitowa uku. An nuna haɗuwar Nura da Jimmai a gidan Mudi da kuma kan hanya. A cikin kashin an nuna matsalar munafurci da al’adun biki na zamani.

2) Kashi na biyu na da fitowa biyar, inda aka nuna soyayyar Nura da Jimmai da kuma tankiyar/matsalar da ke tsakanin wannan soyayya, wato Abdu wanda shi ya kasance a matsayin ma’aurinta tun na farko.

3) Kashi na uku na da fitowa huɗu, inda magabatan Jimmai ke yi mata faɗa kan kada ta sa su zama ƙananan mutane. A inda ita kuma ta matsanta kan cewa Nura take so ba Abdu ba.

4) Kashi na huɗu na da fitowa biyu. A ciki an nuna duk da irin matsananci halin da Nura da Jimmai suka shiga, Allah bai ƙaddara za su yi aure ba. Amma sai ga Jimmai da Abdu a matsayin ma’aurata.

5) Kashi na biyar na da fitowa biyar. A nan aka nuna irin darajar da aure yake da ita. Kuma an nuna mana sabuwar alaƙar Nura da Asabe, kuma an nuna yanayin soyayya irin ta baya ne, wato Nura da Jimmai

6) Kashi na shida na da fitowa uku. An nuna soyayyar Nura da Asabe ta fara ƙarfi tare da cewa tana da ma’aurinta na fari, Sambo.

7) Kashi na bakwai na da fitowa uku – sha’anin Sambo da Asabe na tasamma lalacewa. Amma ita Tabawa Mai Tuwo ta tsaya kai da fata kan cewa Sambo take so Asabe ta aura. Nura kuwa, ya fara ƙosawa da halayyar Tabawa Mai Tuwo.

8) Asabe ta ƙi sambo fafur, yayin da Nura ya fitar da rai da Asabe, masu magana kan ce “matar mutum…” Dawowar Nura daga rangadi ya zo ya ishe sabuwar amaryarsa a ɗaki.

Duba da irin yadda marubucin ya tsara tunaninsa, za a ga zubin ya tafi daki-daki cikin tsarin lokaci mai jerangiya. Watau daga wannan batu sai wancan: daga farko sai tsakiya sannan ƙarshe. Kuma idan an duba za a ga hakan daga yadda kowanne kashi ke ƙulluwa da kashi mai zuwa, haka ma kowace fitowa take nunawa – daga wannan batu sai mai biye masa. Sai dai, akwai buƙatar a kawo jerin sunayen ’yan wasa da bayanin fage da sauransu. A don haka, za mu ga cewa marubucin ya bayyana mana yanayin ala’adun soyayya da neman aure da zamantakewa a ƙasar Hausa cikin wasan.

 

Salo da sarrafa harshe

Kamar yadda za a gani marubucin ya yi amfani da salo mai ban sha’awa da jan hankali cikin kalmomi da jumloli sauƙaƙa. A taƙaice dai, solonsa ya yi armashi cikin sassauƙar zantarwa da ’yan wasa suka aiwatar – wato babu kalmomin aro ko kalmomi masu tsauri. Haka ma zaɓen kalmominsa ya dace da yadda marubucin ya ba wa kowane ɗan wasa. Misali, Nura da Jimmai da Asabe da Abdu da Sambo an nuna cewa matasa ne kuma dukkan kalmomin zantarwarsu na matasa ne. Haka ma Mudi da Kallamu da Mal. Hashimu sun zo a matsayin manya kuma kalmominsa sun dace da matsayinsu cikin wasan.

Dangane da dabarun sarrafa harshe kuwa, an sami wurare masu ɗan dama da marubucin wasan ya ba wa, musamman ’yanmatan ko budurawoyin cikin wasan damar yin karin magana da baƙar magana da habaici d.s. Misali tsakanin Jummai da Abdu da kuma tsakanin Asabe da Sambo an sami irin waɗannan adon harshen ko dabarun sarrafawa. Ga misalansu kamar haka:

 

Baƙar magana:

JIMMAI:…ka faɗa mini nan gaba…(shf. 19).

 

JIMMAI :…idan ya zama fa? Sai kuma ƙaƙa? (shf. 19).

 

ASABE:…Amma ai kai ne ka fara fito… ka san kuwa idan kiɗa ya sauya rawa ma… (shf. 39).

 

ASABE:…Da haƙuri ta mutu sadakar me ka yi mata? Kai malam ba na son tsotsogulon…(shf 39).

 

 Karin magana:

JIMMAI:…A yi dai can matar kaɗaici ta jiyo guɗa a bayan gida… (shf 23).

NURA:…son maso wani ƙoshin wahala…(shf 27-28).

 

ABOKI NA UKU:…komai nisan dare gari zai waye…duk sa’ada da ta yi tsami ma ji 929).

Adon magana:

ASABE:…labarin zuciya a tambayi fuska(shf 31).

SAMBO:…Da ma an ce dokin mai baki ya fi gudu (shf  30).

 

Siffantawa:

SAMBO: …kukan kurciya ma jawabi ne… (shf.45).

 

Habaici:

JIMMAI:…da ma an ce gwano baya jin warin jikinsa. Ko an manta da zafin rana ne saboda yanzu ana cikin hunturu? Ba a san komai daɗewa, bazara za ta sake dawowa ba? (shf. 22).

 

Kurman zance:

TABAWA MAI TUWO:…Ba shakka. Ai kamar mace ce mai ciki, babu wanda ya san abin da za ta haifa sai ran da Allah ya sauke ta. Mu dai fatanmu shi ne Allah ya tabbatar da abin da ya fi alheri. (shf. 34). d.s.

 

Waɗannan kaɗan ne daga cikin adon harshe ko kwalliyar magana da aka zaƙulo daga cikin littafin.

 

’Yan wasa

Wannan wasa na ƙunshe da ’yan wasa da yawa amma biyar daga ciki, su wasan ya fi son nunawa. Tun da an ce jigon soyayya ne, an tafiyar da shi ta kan ruhin wasan tir-madalla.

Nura, Jimmai, Asabe, Abdu da Sambo su ne manyan ’yan wasa. Amma za a iya cewa uku daga ciki su ne muhimman ’yan wasa wato: Nura da Jimmai da Asabe.

Kowanne daga cikin ’yan wasan ya taka rawa muhimmiya. Kuma ta kansu ne aka ga jigon wasan ya fito da kuma manufofin da ake son a nuna wa mai karatu. Bisa la’akari da rawar kowanne daga cikin ukun nan, za a iya fahimatar Nura a matsayin jangwarzo a wasan, wanda amonsa ya ja wasan tun daga farko har ƙarshe – wato dai, shi ne ya yi dakon manufar da ta yi mamaya cikin littafin.

 

Wasu dabaru cikin littafin Matar Mutum Kabarinsa

Baya ga manyan tubalan nazarin da aka bayyana a sama, akwai wasu dabaru da wannan littafin ya ƙunsa. Idan aka zurfafa wajen nazari wannan littafi na Matar Mutum Kabarinsa za a iya fitar da abubuwa masu yawa da suka haɗa da yanayin zantarwa da tufafin wasa da yadda ake tafiyar da wasa. Sai dai, a nan za a duba yadda aka tafiyar da wannan wasa kamar haka:

 

Tankiya

Dole ne wannan dabara ta bayyana a cikin kowane irin nau’in wasan kwaikwayo. A cikin wannan wasan an sami tankiya a wurare biyu waɗanda kuma su ne suka ja hankalin mai karatu.

Tankiyar farko ita ce tsakanin Nura da Abdu a kan Jimmai. Masomin wannan tankiya ya faro tun daga shafi na (6) inda Mudi yake cewa:

 

MUDI: … Da ba don tana makaranta ba, ai da tuni an yi mata aure. Ka ga sa’o’inta duk suna ɗakunan mazarsu.

 

NURA: Cikin hanzari: Ashe a halin yanzu ba ta da miji tukunna!

 

MUDI: Wa ya faɗa maka? Ai ba za ta kasa shekara biyar da ɗaurarren aure ba. Ka tuna da yaron nan Abdu, malamin makaranta?

 

Daga ɓangaren Abdu, kuwa ya fara tun daga lokaci da mutum na uku ya ishe shi har gida ya ba shi labarin abin da ke faruwa tsakanin Nura da Jummai:

 

JIMMAI:   Ai babu komai idan ya ji ni da ma can ban damu da shi ba, don ba na son sa (shf 9).

 

MUTUM NA UKU: Abin da zan faɗa maka shi ne Nura, wan matar surukinka…. suna ƙulle-ƙullen warware auranka   da Jummai don Nura ya aure ta… kusan duk mutanen unguwarmu sun sami cewa Jimmai tana zuwa gidan Nura. Idan kana shakka, to ka yi bincike bisa wannan. (shf. 16-17).

 

ABDU:.. Yanzu Nuran da muka tashi tare gaba ɗaya ne har yake yi mini wannan aiki? (shf. 17)

 

Wato duk da irin taurin kai da bijirewar Jimmai sai ga Abdu a ƙarshe shi ne ya yi rinjaye kan Nura. Wannan tankiya ba ta zo wa Nura da sa’a ko nasara ba, don kuwa bai yi rinjaye kan Abdu ba.

Tankiya ta biyu kuwa ta faru tsakanin Nura da Sambo a kan Asabe. To, idan an duba littafin za a ga hakan.

 

Waraka

Duk inda aka sami tankiya, to, akwai yiwuwar a sami waraka daga ƙarshe. Duk inda tankiya ta mamayi zaren labari, lalle za ta zo ƙarshe. Wato, idan an duba sha’ani Nura da Jimmai, bikin aurenta shi ne batun da ya kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Nura da Abdu. To, amma masomin waraka a nan ita ce tun daga lokacin da Mutum Na Uku ya ankarar da Abdu; sai kuma matakin da Kallamu da Mal. Hashimu suka ɗauka na sanya ranar aure Jimmai da Abdu. A tsakanin Nura da Asabe kuwa, sakamakon sawwaƙe wa Asabe da Sambo ya yi ne, ta kawo ƙarshen tankiyarsa da Nura.

 

Zancen zuci

Marubucin ya nuna wannan dabara a inda ya nuna Abdu a shafi na (16) da Jimmai a shafi na (23). Abdu ya yi wannan lokacin da Mutum Na Uku ya zo masa da labarin matarsa Jimmai. Ita kuma Jimmai ta yi wannan cikin tunani, yayin da ta dawo daga kiran da Mal. Hashimu ya yi mata, wato lokacin da take dawowa gida ita kaɗai a kan hanya. 

 

Arashi

Wannan dabara ta faru ga Nura a kashi na ƙarshe fitowa ta II, game da abin da ya faru gare shi amma bai sani ba. Wato bayan ya dawo daga rangadi sai ji ya yi ana yi masa guɗa ana kiransa ango. Nan ne fa ya iske ɗakinsa ya tarar da amaryarsa ciki zaune.

 

Ba waɗannan kaɗai ne ba. Akwai sauran abubuwan da suka shafi zantarwa (kamar taɗi da sambatu da muryar wasiƙa) da ba a faɗe su cikin wannan ɗan ƙwarya-ƙwaryar nazari ba. Haka kuma, akwai buƙatar a duba lokaci ko zamani da tufafin wasa da aukuwar lamura da isharori; tare da nazartar tasirinsu a cikin wannan wasa. Amma idan an so, za a iya narzarta wannan littafi na wasan kwaikwayo ta mabambanta fuskoki yayin da aka buƙaci yin tarken-waje. Alal misali, za a iya kwatanta shi ta mahangar zahiriyya ko kuma mararanci d.s.

Post a Comment

0 Comments