Nazarin ra’i a mizanin ayyukan adabi na Hausa abu ne da bai daɗe da bayyana ba. Wasu masana suna ganin wasu nau’o’ukan ra’in kamar ba su da muhalli a nazarin ayyukan adabi na Hausa. Wannan ne ya sa aka yi ƙoƙarin ƙalailaice ra’in lalatattun lamura (Quee Theory) da sigoginsa a wasu fina-finan Hausa. A wannan aiki an diba siffofi da sigogi da yanayi yadda ra’in yake wanzuwa a cikin ayyukan adabi, musamman finafinan Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen wannan aiki, musamman zabo fina-finan da suke da ruwa da tsaki da wannan aiki. Binciken ya tabbatar da yiwuwar nazarin fina-finan Hausa ta hanyar amfani da ra’in lalatattun Lamura. Haka kuma binciken ya gano sigogin ra’in lalatattun lamura da yadda ake samun su a fina-finan Hausa. A ƙarshe binciken ya gano cewa irin waɗannan fina-finai suna da matuƙar tasiri akan abubuwan da suka shafi tarbiyar al’umma. Sannan kuma an ɗora wannan aiki ne bisa ra’in lalatattun Lamurra. (Quee theory).
Ra’in Lalatattun Lamura A
Finafinan Hausa: Nazari Daga Fim Ɗin Kare Jini Biri Jini
DAGA
ABDURRAHMAN ALIYU
08036954354
ksarauta@gmail.com
1.0 Gabatarwa
Wannan bincike an gabatar
da shi ta hanyar yin nazarin ra’in
lallatattun lamura a fim ɗin Kare Jini Biri
Jini, da kuma irin haɓakar da
ya samu da ci gaba ta hanyar gudanar wa da gabatarwa a fina-finan Hausa. Irin hikimomin da ake samu cikin fina-finan Hausa a yayin ƙoƙarin isar da
saƙo ga masu kallo sune suka ƙara fito da nazarin
ra’in lalatattun lamurra fili.
Sanin
kowa ne cewa, finafinan Hausa reshe ne
na adabi kuma fasaha
ce mai bayyana yanayi da tsarin rayuwar al’umma.
Ta hanyar fina-finan Hausa za a iya
ganin hoton rayuwar wata al’ummar da ta gabata, haka kuma za a
iya fahimtar tsarin rayuwar waɗannan mutane da ɗabi’unsu
da tattalin arziki da zamantakewarsu. Za a iya ganin
hoton abin da ke faruwa a cikin al’umma, har ma wani lokaci a iya kirdaden abin da zai
iya faruwa a cikin al’umma.
Finafinan Hausa hanya ce ta bayyana tunanin mai shirya fim ɗin,
ko marubuci, ko kuma irin falsafarsa
game da rayuwa. (Malumfashi, 2002).
Duk da irin kallon da
ake wa wannan fannin na lalatattun lamurra na rashin samun tagomashi a cikin
ayyukan adabin Hausa, sakamakon wasu tadodi da al’adu na al’ummar hausawa da
suka yi wa fannin shinge, amma a zahirin binciken da aka yi a yanzu kusan kashi
69% na ayyukan adabi da suka shafi fina-finan Hausa suna ɗauke da wannan nau’i a yanzu haka, kuma
duk aikin da bai tafi da wannan nau’i ba kusan ana kallonsa lami.
Wannan aiki zai fito
mana da wannan ra’in fili domin fitar da aya daga tsakuwa.
1.1 Wanzuwar Ra’i a Duniyar Adabi
Masana
sun yi kai-koma dangane da samuwar hanyar nazarin adabi musamman daga larabawa
da Turawa da Hausawa
Dangambo
(2008:6) ya bayyana cewa mazahabobi na tarke sun fara kunno kai tun wajen ƙarni
na 16 zuwa 17 a ƙasashen Turai, wanda hakan ya yi tasiri ƙwarai wajen ginuwar
ayyukan adabi masu inganci. Su kuwa Larabawa sun fara bincike kan ayyukan adabi
da rayuwar ɗan Adam tun zaman farko na Jahiliyya. Sun mayar da hankali kan
nazarin ayyukan gargajiya da suka danganci maganganun azanci da waƙoƙin baka da
labaru da al’adu da sauransu. An samu bunƙasar nazarin musamman a daulolin
Umawiyya da Abbasiyawa.
Barry
(2002:11) ya ce, “Turawan da suka fara share fage nazarin ayyukan
adabi, sun yi rubuce-rubuce da dama inda aka samu ayyukan Plato (427-347 BC) da
Aristotle (384-323 BC). Dagan an aka ci gaba da bayyana ra’ayoyi dangane da
tarken adabi, masana irin su Horece (65-8 BC) da Sidney (1554-86) da Barcon
(1561-1626) da Wordsworth (1770-1850) da Coleridge (1772-1834) da Sauransu da
dama, duk sun bayyana hanyoyin nazarin adabi dangane da tunane-tunanensu don
nazarin matani”.
Daga
ƙarshen ƙarni na 19 aka samu gwagwarmayar siyasa da tattalin arziƙin abin da ya
haifar da samuwar marubuta adabi irinsu Kalmarɗ da I.A Richard da sauransu. A shekara 1920 nazarin ya shiga
jami’o’i da cibiyoyin ilimi. A wannan lokaci I.A Richard ya rubuta littafi mai
suna “Principle of Literary Critcism (1924). Daga wannan ƙoƙari ne aka samu ƙungiyar
“New criticism” (1945-1950) wato sabbin matarka, da suka fara amfani da nazarin
Ƙwaƙƙwafi (Close reading) wannan ya sa ake wa wannan ƙungiyar kallon ta farkon
wajen tarken adabin.
Gusau, (2008:30-33) Ya bayyana malaman
da suka fara nazarin adabin Hausa zuwa rukunoni daban-daban, wato rukunin
Turawa irin su D.W Arnolt da Neil Skinner da M Hiskett da Paul Newman da Grahm
Furniss da sauransu ya kuma rarraba ‘yan ƙasa zuwa rukunoni biyar dangane da
lokutansu, sannan ya rarraba masana ta fuskar ɓangarorin nazarin Hausa wato
adabi da al’ada da kuma harshe. A ƙarshe ya ambaci makarantun nazari na farko
da lokuttan da aka buɗe su da malamansu na farko da marubuta masu sha’awar
nazarin Hausa.
Ɗangambo (2008:5-6) ya bayyana cewa tun
kafin Turawa su miƙa mulki, nazarin Hausa ya kankama cikin Turanci, kuma
tsofaffin ‘yan mulkin mallaka su ne malaman farko da ke koyar da dabarun
nazarin Hausa waɗannan manazarta su ne suka je suka yi sansani a wata makaranta
da ke ƙarƙashin Jami’ar Landon (SOAS), wasu suka tafi Oɗford wasu kuma Amurka da Jamus da sauransu. To daga can ne fa
suka yi ta horar da malaman da ke dawowa Nijeriya su koyar da harsunan ƙasar,
cikin har da Hausa.
Don haka, aka samar da manazarta adabin
Hausa da tsarin nazarin ra’o’in tarke na duniya. Sun tasirantu da adabin Turawa
wajen nazarin, wannan ya sa adabin Hausa ya cuɗanya da abubuwa da dama. da
farko akwai adabin gargajiya kafin Hausawa su cuɗanya da baƙi, sannan akwai
adabin Hausa wanda ya tasirantu da zuwan Larabawa, wanda yake ɗauke da
tarsashin addinin Musulunci, ga kuma tasirin adabin Turawa
2.0 Ra’in Lalatattun Lamura (Queer Theory)
Ra’in Lalatattun Lamura ya haɗa abubuwa mabambanta a wuri guda. Da farko, akwai masu neman maza (homoseɗual) sannan akwai ‘yan maɗigo (lesbianisms) da kuma sauran abubuwa irin su
batsa da karuwanci da tsafi da bore da sauran al’amura. Wannan ra’i ya
tsiru ne daga ra’in matantaka (feminisms) wato masu rajin kare ‘yancin mata.
Bayan boren Stonewall a Newyork (1969) inda aka samu haɗuwar mata ‘yan maɗigo
da maza ‘yan luwaɗi a wannan lokacin wani ɓangare na masu neman ‘yancin mata
suka haɗu da maza ‘yan luwaɗi (Plain Da Sellers, 2007:183) domin tabba tar da
wannan tunani.
Wasu masana kuma irin su Ado (2017)
sun bayyana cewa wannan ra’i ya tsiru ne daga ra’in Fanɗarewar daga Keɓaɓɓun
Al’adun Al’umma (Deɓine Theory) in da
ya bayyana cewa wani bature mai suna Geoffry Leach ne ya fara batun ra’in Fanɗarewa
a wajen nazarin harshe da adabi a
shekarar 1969.
Wannan rai’i bai samu zama da
gindin sa ba sai a 1990 bayan wata mujalla mai suna “A Jornal of Feminist cultural studies” ta fitar da rahoton taron da
aka yi Jami’ar Calfornia mai taken “Special Issue of
Differences. Bayan fitar wannan rahoton a watan Fabarairu na 1990
sai aka samu rubuce-rubuce na samuwar wannan ra’i daga Lauren Berlant Gloria
Anzaldua da Eɓe Kosofsky
Sedgwick da kuma Judith Butler. Waɗannan su ne waɗanda suka ƙirƙiri wannan
mazahabar a matsayin hanyar nazarin wani matanin adabi. A taƙaice dai an ƙirƙire
ta ne a 1990.
Tun
bayan taron Jami’ar Calfonia wannan ra’i ya ci gaba da watsuwa an samu marubuta
irin su, Annamarie Jagose wanda ya rubuta littafin Queer theory: An Introduction in (1997) bayan shi kuma sai Janik Bastien-
Charlebois wanda ya ruba ta wani littafi mai suna Realities of the Interseɗ eɗperience. Daga nan marubuta irin su Mathew Lewis da Lorda Byron da Walf Whitman
da Katherine Mansfield da sauransu da dama suka yi rubuce-rubuce kan wannan
ra’i.
A
yankin Afirka wannan ra’i ya samu bunƙasuwa ta hannun ‘Yan Afirka da suka je ƙasashen
Turai suka koyo waɗansu munanan ɗabi’u. Marubuta irin su Maddy mai littafin No Past, No, Present No Future (1973) da
littafin Our Sister Killjoy (1977) na
Aidoo da Frantz Fanon mai littafin Black
Skin, White Mask (1952) da Wale
Soyinka wanda ya rubuta Interpreter (1965)
da Dillibe Onyeama wanda ya rubuta littafin Seɗ is a Nigger’s Game (1976) da sauran su da dama duk sun
samo ɓirɓishin wannan tunani tun kafin ra’in ya zauna da gindinsa.
A
ƙasar Hausa Marubuta da dama sun yi rubuce-rubuce kan irin wannan ra’Iimisali
Littafin ‘Yartsana na Ibrahim Sheme
da Littafin Kyan Ɗan Maciji na
Bilkisu Ahmad Funtua da littafin Butulu
na Auwal Anwar da Littafin Tashin Hankali
na Rahma Abdulmajid da sauransu da dama. Wannan ra’i na da manufofi da dama
da suka haɗa da:
*
Bayyanar da kalaman tayar da sha’awa
* Kare
haƙƙin tsirarru
*
Yin fito na fito da hukumomi
*
Bayyanar da sha’awar jinsi
* Ƙarfafa
mabiya yin alfahari da aƙidunsu
*
Bayyana manufofinsu fili
*
Bijirewa tanade-tanaden addinai
*
Barin tsarin al’ada da zamantakewar al’umma
*Neman
‘yancin aiwatar da alfasha da gurɓatattun al’amurra da sauran su.
2.1 Dangantakar
Ra’in Da Wasu Fina-finan Hausa
A
fagen adabi babu maganar adabi mai kyau ko marasa kyau, sai dai a yi duba kan
abin da al’umma ke kallon nau’in adabin, domin shi aikin adabi abu ne da ke
kallon yadda al’umma suke gudanar da rayuwarsu, saboda haka duk yadda ya zo
wajibi ne a karɓe shi, sai dai a fagen
nazari ne kawai aka iya rarrabewa, tsakanin ɗanɗanon wannan da wannan.
Irin alaƙar da adabi ya ke da shi da
al’ada shi ya sa wasu ke yiwa wasu ayyukan adabi kallon lallatattun ko kuma fanɗarraru,
amma a zahiri ba lallatattun ba ne ba kuma fanɗararrun ba ne, domin in aka yi
duba kan manufofi na ra’in lalatattun lamura ba wai ya ta fi ba ne kai tsaye
kan yadda za a riƙa aiwatar da ɓanna a cikin al’umma.
Malumfashi
(2013) ya rawaito cewa, “daga binciken da na yi kan wanna fanni sai na fahimci
cewa yawancin irin wannan adabi, na batsa ne ko na sata ko na karuwanci ko na
daudanci ko na bore ko na tashin hankali, ana ɗaukar
sa a matsayin karkataccen adabi, shi ya sa nakan tambayi kaina, Wa ko Me ya
karkatar da shi, amsar da nakan ba kaina ita ce ba wanda ya karkatar da irin
wannan adabi face al’umma da ya samu kansa a ciki, domin ita ce ta samar da yabanyar
da adabin ya rayu cikinta, ba wannan ba ma ai muna sane da cewa ita kan ta
al’ummar ai kala biyu ce, ko dai wadda ke tafiya
da rayuwar masu danniya ko kuma wadda ke janye da karikitan waɗanda ake
dannewa. A cikin wannan zubin rayuwa guda biyu ake samun adabawa da ke riƙe da
kowane hannun riga guda.”
Shi ma Ado (2017)
ya bayyana cewa fanɗarewa iri biyu ce akwai mai amfani akwai kuma marasa
amfani, ya danganta da yadda marubuci ko kuma al’umma suka kalleta.
Za
mu kalli wasu daga cikin manufofin wannan ra’i waɗanda suka yi daidai da
binciken da ake gudanarwa kan fina-finan Hausa domin mu nazarce
su muga yadda suka yi alaƙa da wannan aiki da kuma in da suka shafe shi.
2.2 Nazarin
Ra’in Lalatattun Lamura a Fim Ɗin Kare Jini Biri Jini
Nazarin ra’i a cikin kowane
irin aikin adabi
yanayi na nuna tsarin labari wanda ya kan
jero manufofi ko kuma siga ta yadda aka gudanar da adabin.
A cikin fina-finan Hausa akwai masu wannan yanayi, na lallatattun lamurra wanda suka ƙunshi sata ko fashi ko madigo ko luwadi
da sauran wasu abubuwa makamanta waɗannan.
An dai yi nazari fim mai suna Kare Jini Biri Jini a wannan maƙala domin fito da misalin yadda wannan ra’i yake wanzuwa a
cikin finafinan Hausa da kuma irin yadda yake samun gindin zama a adabin Hausa.
Fim
ɗin
Kare Jini Biri
Jini na KamfaninGirma Film Production yana da kashi na ɗaya
da na biyu. A kashi na farko akwai fitowa fitowa har guda talatin da ɗaya.
A kashi na biyu kuma an sami fitowa fitowa har guda talatin, an sami jimillar
fitowa har sittin da ɗaya minti ɗari da huɗu, (sa’a ɗaya da minti arba’in da huɗu) a takaice ga yadda labarin yake.
An gina labarin ne a kan wani ƙauye ne guda ɗaya wanda ya rabu zuwa gida biyu wato shiyyar gabas ta yamma,
kuma matasan shiyoyin biyu ko alama basa jituwa da juna. Akwai matasa guda biyu
da suka shahara a kowane ɓangare a
shiyyar yamma Goje shi ne babban ɗan dabar garin kuma ɗan mai garin ne a ɓangaren
gabas kuwa Mai Arna shi ne jagoran yan dabar yankin.
A gefe guda kuma ƙanin Mai arna
yana soyayya da wata yarinya da ke
shiyyar gabas,
mai suna Rabi wadda Goje ya yi alƙawarin ba ami aurenta sai shi. Ita
kuma yarinyar sam bata ƙaunar sa. Wannan soyayyar ta haddasa rigima mai tsanani
a tsakanin shiyyar Gabas da ta yamma
wadda ta sa ranar da za a ɗaura wa yarinyar sai Goje ya zo wajen ɗaurin auren
ya tarwatsa wajen ya shiga har gidan uwayen amarayar ya hana a tafi da amaryar kowa ya watse daga ƙarshe aka je
aka faɗawa uban angon shi kuma ya sanya aka tado ma shi Mai Rrna wanda ake tunanin ya mutu ya tura shi ya je ya ɗauko mashi amaryar da
ango.
Mai Arna ya zo shiyyar yamma ya yi gumurzu da Goje har ya kashe shi daga ƙarshe shi kuma jami’an ‘yansanda suka tafi da
shi.
2.3 Dacewar Ra’in da Fim Ɗin
Wannnan fim ɗin ya fito da manufofin ra’in
lallatattun lamurra ta sigar bore da tayar da hankali, haka kuma wasu daga
cikin manufofin wannan ra’i sun yi matuƙar dacewa da wannan fim ɗin waɗannan
manufofin da suka dace da fim ɗin sun haɗa da:
*
Yin fito na fito da hukumomi
*
Bayyana manufofinsu fili
*
Bijirewa tanade-tanaden addinai
*
Barin tsarin al’ada da zamantakewar al’umma
*Neman
‘yancin aiwatar da alfasha da gurɓatattun al’amurra
Waɗannan su ne wasu daga cikin
manufofin wannan ra’i da suka bayyana a cikin wannan fim ɗin karara, bari mu ɗauke
su ɗaya bayan ɗaya domin gani dacewar su a cikin fim ɗin.
2.3.1.Yin Fito
na Fito da Hukumomi
A cikn wannan fim an nuna yadda
su Goje suke yin fito na fito da dokokin hukuma, wanda ta kai a wata fitowa sun
je har garin yamma sun yi kisan kai, amma da suka dawo suka faɗawa Goje sai ya
ce ai hanyar da aka bi aka yi kisan ba haka aka tsara ba saboda haka, an ɗauko
gawar da tsaron mutanen gari da hukuma, amma suka tare gawar da mutane suka ce
dole sai an ajiye gawar sun sake kashe ta domin yanka ta zasu yi ba suka ba, kuma haka suka karbi gawar rigima ta
barke a wajen.
Ƙoƙarin
da lilamaman garin da masu gari suka yin a su hana su aiwatar da wannai aiki na
su, amma suka kiya suka yi fito na fito tsakaninsu da hukumomin gari da kuma
sauran jami’an tsaro a bayyanar jama’a ga dai abin da suka gaya wa hukumar
kafin su fara ɗauki ba daɗin:
“….Kai lku ajiye
mana gawar nan, yanka ta zamu yi. Domin mun yi alƙawarin cewa yanka ta zamu yi,
bamu samu dama ba, amma yanzu a ajiye mana mu yanka ta. Kai malami nekasan
darajar alƙawari saboda haka sai mun yanka ta….”
Ko shakka babu wannan yin fito na
fito da hukuma ne domin an nuna rashin karfin hukuma da kuma tasirinta wanda
shi kuma wannan ra’in yana bayyana wannan manufa.
2.3.2 Bayyana Manufofinsu Fili
Bayyana manufofin munanan ayyuka
a fili na daga cikin manufofin ra’in lalatattun lamurra, a cikin wannan fim ɗin
an nuna yadda masu aikata munana ayyuka suke bayyana
manufofinsu a fili. Domin a cikin fim ɗin mun ga
yadda mahaifin Goje mai Gari ya kira shi domin yi masa nasiha ya bar abubuwan
da ya ke aikatawa, amma sai ya mayar ma shi da murtanin kamar haka:
“…. A wani abu aka
zo aka ce ma na yi? Duk waɗanda ke ma maganar nan sa’idanawa ne fa kuma akan ka
ne, kuma kare martabarmu na ke, kare martabar gidanmu, amma munafukai ‘yan sa
idpo sai su zo suna maka cara baba kana kyalesu? Ka dinga yi masu lakum
kawai….”
Daga ƙarshe ma sai ya tambayi mahaifin nasa cewar, “ ka gama” da ya amsa masa
da cewar ya gama sai ya tashi kawai ya shige cikin gida ba tare da ya kara
sauraren sa ba.
Haka ma a fim ɗin an nuna yadda
Mai arna ya sa aka kamo mashi wani matashi bayan da wata yarinya ta kowa masa ƙararsa na ya ci mata kayan sana’a bai biya ba, ya sa aka yi masa hukunci da
kuma gargaɗin sa, sannan ya bayyana mashi cewa su basu zalunci irin wannan.
2.3.3 Bijirewa Tanade-tanaden Addinai
Wannan na ɗaya daga cikin manyan
manufofin ra’in lallatattun lamurra, wato a samu aikin adabi da aka nuna yadda
mutane ke bijirewa tanade-tanaden addinai saboda biyan buƙatar kanasu. A cikin wannan fim mai suna Kare Jini Biri Jini an
samu irin wannan tsarin ya fito raɗau. Domin an nuna yadda yaran Goje suka tare
al’ummar gari su ka hana su kai gawa a kushewa kamar yadda
addini ya tsara suka buƙaci da aba su gawar domin
suna da wata buƙata ta musamman da ita. Haka ma kuma, an nuna yadda Goje ya zo ya tayar da taron ɗaurin aure ta hanyar sarar mutanen duk da
cewa iyayen yarinyar sun zaɓa mata wanda suke ganin shi ne mafita a
tare da ita, kamar yadda addini ya basu dama, amma sai su Goje suka bijirewa
wannan umurni suka hana a ɗaura auren. Wannan manufa kusan ta mamaye wannan fim
ɗin sosai.
Ga abinda Goje ke faɗa a lokacin da suka tayar da taron daurin auren.
“….. da nag a angon
nan idan bad a sai uwarsa ta haifi wani ba Allah ya tsine man, an tashi daga
bikin, ina masu bikin an daina bikin nine Goje, ni ne nan, ni ne mijin Rabi,
wallahi duk Duniya ba wanda ya isa ya aure ta, wallahi Allah akan rabi sai na
kasha mutum an daina bikin, ina angon da ka fito da sai na yanka ka, kuma bari
in gaya ma naga dan iskan day a isa ya zo ya ɗauki amaryar zan tsare in raka,
zan tsare in raka…”
Ko
shakka babu wannan kalamai na Goje bijirewa tanade-tanaden addini ne, domin
addini shi ya bada dammar a ɗaura aure kuma a bayar da yarinya ga mutumen
kirki, sannan wanda take so, amma a gefe guda ga wasu sun fito sun hana bikin
da rana tsaka ba tare da wani ya taka masu birki ba.
2.3.4 Barin Tsarin Al’ada da Zamantakewar Al’umma
Gabaki ɗaya fim ɗin Kare jini Biri Jini ya bar tsari al’adu
da zamantakewar al’umma musamman yadda aka shirya fim ɗin domin a nuna ƙarfin
daba a tsakanin wannan yanki da wannan yanki, irin zage-zagen da ake a cikin
fim ɗin da irin suturu da yanayin maganganun taurarin fim ɗin ga baki ɗaya sun saɓa tsari da zamantakewa ta al’umma, domin ba haka al’umma
suke gudanar da rayuwarsu ba. In ka ɗauki rin suturar da Mai arna da yaransa ke
sanya wa sam basu yi kama da sutura irin ta al’adar Bahausheba, haka ma irin mu’amulla da maganganun da ke fita bakin Goje da
yaran sa sam sun saɓawa zamantakewar al’umma baki ɗaya. Dubi irin zagin
da Goje ya yi a maƙabarta duk da n an karar das hi maƙabarta ce ba a zagi amma
buɗar bakin sa sai ya ce.
“……kutumar durin
uwar nan kai, wato Mai arna salon yaƙin da ya zo da shi ke nan….. amma zan nuna
ma ni shege ne naci uwarka, idan ba sai na haifar da abin da zai bayyana a
cikin garin nan ba shege nake…”
2.3.5 Neman ‘Yancin Aiwatar da Alfasha da Gurɓatattun Al’amurra
Baki ɗaya shirin fim ɗin Kare Jini Biri Jini an tsara shi ne bisa
neman ‘yancin alfasha da aikata gurɓatattun al’amurra, domin fitowa ta farko a
fim ɗin ma an nuna yadda Mai arna yazo gidan wani malami ya ja masa kunne a kan kar ya yarda ya aura ma kanensa ɗiyarsa, saboda suna yankin Yamma, in kuma
har ya ɗaura auren to zai ɗauki mataki kansa. Shi ma a ɓangaren Goje an gwada yadda ya zo zance wajen masoyiyarsa Rabi ya tarar da wani
saurayi ya zo wajenta, amma ya bashi rata ta gudu ya yi alƙawarin in ya tarar
da shi sai ya aika shi lahira, kuma haka aka yi da ya bishi ya tarar da shi
gaban jama’a ya sare shi da niyyar ya mutu Allah ya tsare shi.
A gefe guda kuma mun ga yadda
mahaifin Mai arna ya bashi umurnin ya tafi ya ɗauko fansar tare kanansa da aka
yi, a maimakon ya gaya wa hukuma sai ya bashi dama har ma ya riƙa kuranta shi
da nuna cewa shi jarumi ne kawai ya je ya ɗauko fansa. Irin waɗannan abubuwan na neman ‘yancin alfasha
da aikata gurɓatattun ayyuka sun taka muhimmiyar rawa a cikin wannan fim na Kare Jini Biri Jini. Kai ko salon waƙar fim ɗin ma tana aiwatar
alfasha a fili, ga kaɗan daga cikin ta.
“Kare jinni biri
jinni,
Ba zan ce ku daina
ba,
Ba zan ce ku fasa
ba,
Wai ina mazajen
suke?
Goje ya tsare gida
Ya maida daji
gida”
2.4. Sakamakon Bincike
Babu ko shakka duk wani bincike da aka gudanar to
daga ƙarshe akwai buƙatar a ga wane irin sakamako wannan bincike ya samar
musamman ga al’ummar da aka yi binciken domin su. Don haka, bincike kan “Ra’in Lalatattun Lamura: Nazari daga fim ɗin Kare Jini Biri Jini, shi ma akwai sakamakon da aikin ya samar wanda ya haɗa da:
·
Wannan aiki ya gano cewa, tun kafin Hausawa su haɗu
da baƙi suna amfani adabinsu
na gargajiya wanda cike ya ke da duk wasu fannoni na nazari da .kowane irin
adabi ya ƙunsa, haka kuma suna nazarin ayyukan adabinsu a gargajiyance, ta fuskar
yabawa ko kushewa ko kuma nuna ƙyamar abun, sannan kuma suna da mazahabobi ko
kuma hanyoyi da suke aiwatar da wannan nazarin cikin tsari. Don haka koda
ilimin nazarin ayyukan adabi suka same su a zamanance basu sha wahala ba wajen
karɓar tsarin tare da ɗora ayyukan adabinsu bisa wannan sabon tsarin.
·
Binciken ya gano cewa duk wani adabi wanda ake ganin karkatacce ne ki
kuma bai da kyau ba haka abin yake ba shima adabi ne mai ruhi kamar sauran
kowane adabi sai dai kawai yanayin saar da shi ne ya mayar da shi marasa kyau
ko kuma karkatacce.
·
Haka an gano cewa duk wasu ayyukan adabi da aka ɗora bisa
ra’in lallatattun lamurra ba ana nufin a riƙa aiwatar da aikin bane a zahiri ko
kuma aikin abu ne mai kyau, shi ra’in lalatattun lamurra ra’i ne da ke nunan manufar
aikin adabi da kuma karɓuwarsa ga al’umma, sannan ba manufar ra’in bane a riƙa
aikata abubuwa marasa kyau ba, babban abin da ra’in ke yi shi ne ya haskawa
alumma irin yadda adabin su ya ke da kuma yanayin ƙarfin tasirin shi ga
al’ummar.
·
Daga ƙarshe an gano cewa a wannan lokaci mafi yawan finafinan Hausa da
ake aiwatarwa suna ɗauke da manufar ra’in lallatattun lamurra, kuma ra’in ya
zama kamar gishiri ne a cikin fina-finan wanda in babu shi ba miya in kuma yai
yawa ya ɓata miyar.
3.0 Kammalawa
Nazartar
ayyukan adabi da fasahar al’umma
yana da alfanu musamman ga al’ummar da aka yi domin ta. Wannan bincike ya yi bayani
gwargwadon game da ra’in lalatattun lamura a adabin Hausawa
wanda
ake samu a fina-finan Hausa. Manufar wannan bincike mai ƙokarin tabbatar
da samuwar ra’in lalatattun lamura a fina-finan Hausa da kuma yadda tarihin nazarin ra’i ya fara wanzuwa a adabin Hausa. A ƙarƙashin wannan aiki an kawo taƙaitacen
tarihin samuwar ra’o’in tarke na duniya da yadda nazarin adabin Hausa ya cuɗanya
da irin waɗannan ra’o’i. Daga bisani aka kalli ra’in lalatattun lamurra aka yi nazarin sa a cikin fim ɗin Kare Jini Biri Jini sannan aka rufe
aikin da sakamakon da binciken ya samar.
Manazarta
Tuntuɓi mai
takarda.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.