Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Ingausar
Yarbawa Da Hausawa A Garin
Gusau, Jihar Zamfara (5)
NA
ADAMU SANI
BABI NA HUƊU
INGAUSA.
4.0 SHIMFIƊA
Yabo da
godiya sun tabbata ga Allah (S.W.A) mai rahama da jinƙai ga
bayinsa, wanda ya bada ikon cigaba da wannan bincike. Tsira da amincin Allah su
tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa, har
zuwa ranar sakamako.
Wannan babi
zai yi bayani a kan Ingausa kamar yadda muka gani a taken babin inda za a
tattauna abubuwa kamar haka: Ma’anar harshe da bayani akan harshen Hausa da na
Yarbanci. Bayan haka za a duba ma’anar Ingausa da nau’o’in Ingausa. Haka kuma
za a dubi dalilan da ke haifar da ingausa. Bugu da ƙari za a
bayyana amfani da illolin Ingausa. Daga ƙarshe za a
kawo Ingausar Yarbawa da Hausa a garin Gusau wanda shi ne sakamakon wannan
bincike, sai naɗewa.
4.1 MA’ANAR
HARSHE
Harshe wata
kafa ce wadda mutane ke amfani da shi domin sadarwa. Masana da dama sun tofa
albarkacin bakinsu game da ma’anar harshe, daga cikinsu akwai:
Skiba R.
(1997); Ya bayyana cewa “Harshe hanya ce ta bayyana yanayin yadda muke tunani,
da kuma yadda muke bayyana kawunanmu, tare da mu’amularmu, kuma shi ya raba mu
zuwa ƙabilu mabanbanta”.
Auer, (1998);
Cewa ya yi “Harshe ba wani abu ne ɓoyayye wajen koyo ba, amma abu ne
wanda yake bayyane a wurare kamar; aiki, da buƙatu, da jindaɗi, da kuma
damuwa da sauransu. Bugu da ƙari da sharuɗɗa da wasu
dokoki da ke ƙarƙashin kowane
harshe”.
Mukhtar A.B
(2017), ya ce “Harshe shi ne hanyar sadarwa da ta zama ruwan dare domin yana ba
wa mutane dammar su zanta da junansu da kuma damar rubuta tunaninsu da
ra’ayinsu”.
Ibrahim N.A
(2019); cewa ya yi “Harshe hanya ce ta sadarwa tsakanin al’umma ko dai da sauti
da alamomi ko da ishara.
A taƙaice
za a iya cewa harshe hanya ce wadda mutane ke amfani da ita wajen bayyana
tunanen su ta hanyar furuci ko rubutu ko kuma amfani da wasu alamomi.
4.2 HARSHEN
HAUSA
A nan za mu
yi tsokaci game da harshen Hausa, dangane da ra’ayoyin masana a kan harshen.
Haka kuma za a duba rukuni da zui’ar da harshen ya faɗa, tare da
duba yankunan da aka fi amfani da harshen. Bugu da ƙari za a
bayyana kason mutanen da ke magana da Hausa a Nijeriya.
Harshen Hausa
na ɗaya daga
cikin rukunin harsunan Chadic, kuma a ƙungiyar
Chadic yana cikin iyalin harshen (Afroasiatic).
Hausa na ɗaya daga
cikin manyan yarukan Nijeriya. Hausa ita ce yare mafi girma a Nijeriya, masu
magana da yaren Hausa a ƙasar sun kai
kashi hamsin da biyar (55%). Harshen Hausa yana yaɗuwa ne ta
hanyar ƙaurace-ƙaurace daga ƙasar
Hausa zuwa sassa daban-daban domin kasuwanci da neman ilimi, da yawon buɗa ido, da
sauransu. Saboda haka wannan ya ƙara ɗaukaka
harshen Hausa a faɗin duniya (Wikipedia 2019).
Bunza (2018);
ya bayyana cewa “Hausa tana da ma’anoni da dama daga ciki akwai; Hausa tana ɗaukar harshe
ne wanda ake magana da shi domin sadarwa da juna, ko dabara, ko hikima ta
aiwatar da wani abu domin nuna gwanewa”.
Bugu da ƙari,
Hausa kan iya zama sunan wata ƙabila wadda
take zaune a ƙasar Hausa. Bayan waɗannan, Hausa
na iya zama ƙasar da Fulani ke mulki, amma ba tasu ba ce
ta kabawa ce ko ta Gobirawa ce, to ana kiranta Hausa.
Daɗin daɗewa Hausa kan
iya zama al’ada, watau hanyar gudanar da rayuwar al’ummar Hausa. Dubi da waɗannan
ra’ayoyi, mukan iya cewa Hausa harshe ne da wata al’umma ke magana da shi, kuma
suke bayyana fasahohinsu, haka kuma da shi suke bayyana al’adunsu da ƙasarsu.
Bugu da ƙari sukan bayyana kansu da shi.
4.3 HARSHEN
YARBANCI (YORUBA)
Kamar harshen
Hausa a nan za a duba yankunan da aka fi amfani da Yarbanci, da kuma ƙiyasin
masu magana da shi. Haka kuma za a duba zuri’ar harsunan da yake, da kuma duba
harsunan da ke da alaƙa da Yarbanci daga ƙarshe,
za a bayyana dalilan da suka sa harshen ya kasu zuwa karuruwa daban-daban.
Yarbanci harshe
ne da ake magana da shi a Afrika ta yamma. An fi samun masu magana da wannan
harshe a Nijeriya da jamhuriyar Benin da sauran ƙasashen
Afrika. Harshen Yarbanci yana da alaƙa da
Ishekiri, da kuma Igala, a tsakiyar Nijeriya.
Harshen
Yarbanci yana cikin zuri’ar harshen Niger- Congo. A tarihance ana kirdadon
harshen ya yi shekara 15,000 tun ƙarni na huɗu kafin
haihuwar Annabi Isah ake tsammanin Yarbawa suna, zaune a Ife (Ile – Ife).
A Nijeriya
ana samun kare-karen harshen Yarbanci ta la’akari da shiyoyin ƙasar
guda biyar (5) kamar haka:
i.
Arewa maso yamma
ii.
Arewa maso gabas
iii.
Tsakiyar Nijeriya
iv.
Kudu maso yamma
v.
Kudu maso gabas
Waɗannan
bambance- bambancen muhallin zama ya kawo ‘yan bambance-bambance ga harshen
wanda ba ya hana fahimtar juna sai dai can ba ka rasa ba.
A taƙaice
Yarbanci harshe ne daga cikin manyan harsunan Nijeriya, harshen yana da
daidaitacciyar hanyar rubutu, kuma ana nazari da koyar da shi a makarantun
yankunan Yarbawa, da wasu sassa na arewacin Nijeriya.
4.4 MA’ANAR
INGAUSA
Ingausa ta samu
ne dalilin walwalar harshe wadda ake nazari a fannin ilimin kimiyyar harshe na
walwalar harshe (sociolinguistics). Masana ilimin harshe sun tofa albarkacin
bakinsu game da ma’anar Ingausa, daga cikinsu akwai:
Dahl da
Amudsen (2010). Sun bayyana ingausa da cewa: “nau’in harshe ne wanda ake yi a
bayyane inda mai magana yake nuna gwanewarsa wajen haɗa harsuna
biyu saboda zantawa ko hira”.
Brice da
Anderson (1999). Sun bayyana “Ingausa ita ce gauraya harsuna biyu lokaci guda a
cikin zance ɗaya, ko kuma
wani yankin jumla”.
Kia da Wasu,
(2011); Sun kalli ingausa a matsayin “gauraya wasu ababe na harshe kamar
kalmomi, da yankunan jumla, haka kuma da ganguna, da mahaɗin jumloli a
cikin zance guda”.
Ho, (2007) ya
ce “Ingausa ita ce canzawa daga wani harshe zuwa wani a cikin zance guda na
magana ko rubutu”.
Ajibade A.C
da wasu (2017); sun bayyana cewa “Ingausa ita ce haɗa harsuna
biyu ko fiye a yayin zance ba tare da sauyawar ma’ana ba”.
Mukhtar A.B
(2017); ya bayyana Ingausa da cewa gamin gambizar harsuna biyu lokacin zance
domin isar da wani saƙo”. Ta la’akari da
ma’anonin da masana suka bayar za a iya cewa ingausa ita ce gaurayar harsuna
biyu ko fiye lokaci guda a cikin zance, rubutacce ko a magance domin isar da
wani saƙo na musamman.
4.5 NAU’O’IN
INGAUSA
Ingausa ta
kasu zuwa manyan nau’o’i guda biyu, dangane da yadda aka gina zancen. Waɗannan nau’o’in
sune:
i.
Surkin farko ko tsakiya -
(Code – miɗing)
ii.
Surkin ƙarshe - (Code
- Switching)
i. Surkin
farko ko tsakiya (Code – miɗing). Wannan nau’in ingausa ce wadda mai magana
ko rubutu kan surka harsuna biyu ko fiye a farko ko tsakiyar zance. Misali:
S/N |
Yrb/Hau |
Hau |
1.
|
Aso fari
mofe wo |
Farin kaya
zan sa |
2.
|
Pan mi si tulu
funmi |
Zuba ruwa
cikin tulu |
3.
|
Malam ni bo inwa |
Malam Ina
ka ke? |
ii. Surkin ƙarshe
(code – switching). Wannan nau’in ingausa ce wadda kan zo daga ƙarshen
zance. Tana iya zuwa tsakiyar jumla, inda Kalmar mahaɗi kan zo a ƙarshen
jumla ta farko a cikin jimla. Misali:
S/N |
Yrb/Hau |
Hau |
1.
|
Fun mi kuɗi |
Ba ni kuɗi |
2.
|
Orun po
bami mu lema |
Akwai rana
sosai ba ni lema |
3.
|
Bami tan fitila
|
Kunno mini
fitila |
Idan za mu
dubi waɗannan misalai
za a ga cewa surkin kalmomin Hausa duk ya zo ne a ƙarshen
zantukan. Bayan waɗannan nau’o’in ingausa.
Mukhtar
(2017) ya kalli ingausa ta fuska biyu kamar haka:
1. Surkin ciki
2. Surkin waje
1. Surkin
Ciki:
Wannan shi ne wanda yake faruwa a cikin harshe guda, inda mai magana zai surka
karin harsuna biyu cikin zance guda. Misali kamar ingausar Sakkwatanci da
Kananci.
2. Surkin
Waje (Hargitsa – Balle)
Wannan kuma
yana faruwa ne inda mai magana ko rubutu zai haɗa harsuna
biyu ko fiye a cikin zance guda. Misali haɗa Turanci da
Hausa, da kuma Arabic a cikin zance guda.
4.6 DALILAN
DA KE HAIFAR DA INGAUSA
Mafi akasarin
al’amurran rayuwa a kan gudanar da su ne bisa wasu dalilai. Haka abin yake a
wannan fannin, domin akwai dalilai da dama waɗanda ke sa a
yi ingausa daga cikinsu akwai:
1. Taƙaitattun
Kalmomi: Ingausa
tana faruwa saboda ƙarancin sanin kalmomi
a ɗaya daga
cikin harsunan da mai magana ke amfani da su, misali.
Taƙaitattun
Kalmomi
Gbe ƙafa kiro / Janye ƙafarka
2. Halin gajiya
ko damuwa: Ingausa
tana faruwa idan mai magana yana cikin wata gajiya ko damuwa. Misali
Wallahi I am annoyed/ Wallahi ina
cikin damuwa
3. Ɗabi’un
Magana: Mutane da dama sukan surka kalmomi ko yankunan
jumlolin harsuna biyu yayin wani zance. Wannan yana faruwa saboda kasancewar sa
ɗabi’ar magana
tsakanin mutane. Misali
Ekaro Sir / Malam Ina Kwana
4. Saboda
bayyana wani yanayi; Ana amfani da Ingausa, saboda bayyana wani
yanayi da mai magana yake ciki kamar: jindaɗi, ko
soyayya, ko fushi da sauransu. Misali:
Wayyo! I sympathised him / Wayyo! Na
tausaya masa.
5. Yanayin Mai
Magana: Wani
lokaci mai magana kan gaji, ko kasala, ko murna da sauransu. Muna iya fahimtar
yanayin mai magana ta hanyar amfani da harshensa. Misali:
Thank you abokina / Na gode abokina
6. Katin Shaida:
Ana
amfani da ingausa a matsayin wani muhimmin abu na katin shaidar ga daga yankin
da mai magana ya fito, ko ga addininsa. Misali:
Ƙaƙa?
Me ya faru? / Yaya? Me ya faru?
7. Bayyana
Sana’a: Ingausa
aba ce da ake yi domin bayyana sana’ar da mai magana yake yi dangane da sarrafa
harshensa a cikin al’umma. Misali
I want to go gida don in ɗanko barho
(Wuƙar rundawa)
8. Bayyana
Zumunta da girmamawa: Ana yin ingausa domin girmamawa ga wani,
wanda ke nuna wanda ake magana da shi ya kamata a girmama shi. Misali:
Ekasan baba mi / Baba ina wuni
9. Tasirin wata
al’umma: Ingausa
tana faruwa sanadiyar tasirin wata al’umma a kan wata ta hanyar amfani da wasu
kalmomi waɗanda ba na
harshen uwa ba.
4.7 AMFANIN
INGAUSA
Fahimtar
harsuna da dama yana da matuƙar muhimmanci
ga mai magana da harsunan. Daga cikin amfanin ingausa akwai:
1. Saukaka
sadarwa tsakanin iyalai domin karantarwa ko tarbiyantarwa ga yara.
2. Ana ingausa
domin nuna naƙaltar magana da harsuna biyu
3. Masu ingausa
suna da cikakkiyar dama ta magana da harsuna biyu
4. Ana amfani da
ingausa domin ɓoye sirri
kada wani ya fahimci abin da ake magana.
4.8 ILLOLIN
INGAUSA
Dukkanin
al’amura na rayuwar yau da kullum akan samu amfaninsu, amma kuma a wani gefe
akan samu illoli can ba a rasa ba. Haka abin yake ga ingausa domin tana da matuƙar
muhimmanci, amma kuma akwai illoli daga cikin illolin ingausa akwai:
1. Tana sa wasu
kalmomin harshen uwa su ɓata.
2. Tana mayar da
harshe baya
3. Tana canja ɗabi’un
maganar harshen uwa
4. Takan shafi
al’adun wasu harsuna da kan yo aron kalmomi
4.9 INGAUSAR
YARBAWA DA HAUSAWA A GARIN GUSAU
A wannan
bagiren za a bayyana ingausar Yarbanci da Hausa a garin Gusau tare da bayyana
mece ce “Ingausar Yarbanci da Hausa, da kuma rakiyar wadatattun misalai na
ingausar Yarbanci da Hausa. Idan aka ce ingausar Yarbanci da Hausa ana nufin haɗa harshen
Hausa da na Yarbanci a cikin zance guda, ko a magance ko rubuce. A kan surka
ababe a cikin zancen kamar kalmomi, yankunan jumloli, da mahaɗi da
sauransu. Wannan ingausa ta samu sanadiyar tasirin zaman da Yarbawa ke yi a
garin Gusau ta sanadiyar mu’amuloli kamar:
1. Mu’amalar
kasuwanci
2. Abokantaka
3. Neman ilimi
4. Sana’o’i
5. Ayukan
gwamnati
6. Muhallan zama
(unguwanni)
7. Auratayya da
sauransu.
Ta la’akari
da waɗannan ababe
ne sakamakon bincikenmu ya samo wasu misalan ingausar Yarbanci da Hausa ta
hanyar zanta wa da Yarbawan garin Gusau mabambanta waɗanda suka ƙunshi
matasa da dattijan Yarbawan garin Gusau. Daga cikin misalan akwai:
S/N |
Yrb/Hau |
Hau |
1.
|
Bami mu buta
|
Ba ni buta |
2.
|
Gbe ƙafa kuro
|
Jaye ƙafarka
|
3.
|
Ra sabulu
funmi |
Sawo sabulu
|
4.
|
Bamogbe kujera |
Ɗauko
mini kujera |
5.
|
Mode hula |
Na sa hula |
6.
|
Se wa mu kunu? |
Za ka sha
kunu? |
7.
|
Mo fe mu ƙanƙara |
Ina son in
sha ƙanƙara |
8.
|
Fi cibi ge
|
Ka ci shi
da cibi |
9.
|
Mo fe wo takalma
|
Ina son in
sa takalma |
10. |
Mota tuntun ni |
Sabuwar mota
ce |
11. |
Bami lo masara |
Miƙo
mini masara |
12. |
Fi gari si |
Ka sa gari |
13. |
Mo fe je ƙuli |
Zan ci ƙuli |
14. |
Aso fari
mofe wo |
Farin kaya zan sa |
15. |
Aso mi ti datti |
Kayana sun
yi datti |
16. |
Orun po
bami mu Lema |
Akwai rana
sosai ba ni lema |
17. |
Pan rijiya
funmi |
Ɗebo
mini ruwan rijiya |
18. |
Ori giya
ni |
Mai giya
ne |
19. |
Bami tan fitila
|
Kunno mini fitila
|
20. |
Pan mi si tulu
funni |
Zuba ruwa
cikin Tulu |
21. |
Bomi Si kofi
funmi |
Ɗauko
mini kofi |
22. |
Mun fake
panawa |
Kawo fallen
kwano guda |
23. |
Bawo ni aboki |
Aboki ya ya dai? |
24. |
Malam ni bo Inwa |
Malam ina kake? |
25. |
E barika |
Barka da arziki |
26. |
Se lafiya ni |
Lafiya dai? |
27. |
Mi oni mashin
|
Ba ni da mashin |
28. |
Oni hankali
|
Ba ka da hankali
|
29. |
Odi gobe |
Sai gobe
|
30. |
Oro duniya
|
Maganar duniya |
31. |
Ban zo
makaranta ba, tori ora mi oya! |
Ban zo
makaranta ba, saboda ba ni da lafiya |
32. |
Mofe je Shinkafa |
Ina son in
ci Shinkafa |
33. |
Je ka lo
gba ƙwallo |
Mu tafi mu
yi ƙwallo |
34. |
Tun jiya motin
retire |
Tun jiya nake jiran ka. |
35. |
Omo Hausa
ni mofe fe |
Ni Bahausa
zan aura |
36. |
Je kalo si Makaranta
|
Zo mu tafi makaranta
|
37. |
Mofe ra abinci
Ebin kpami |
Ina son in
sayi abinci yunwa nake ji |
38. |
Shugaban
ajinmu omo
Yoruba ni |
Shugaban
ajinmu Bayerabe ne |
39. |
Alh. Audu
ne mai unguwa Adugbo wa |
Alh. Audu ne
mai unguwar shiyarmu |
40. |
Tuwo ati
obe kuka ni mofe se laleyi |
Tuwo da
miyar kuka zan dafa yau da dare |
41. |
Sarkin
Gusau
Olowo ni |
Sarkin
Gusau mai kuɗi ne |
42. |
Akeko wa
omo ihu Zamfara ni |
Mahaifinmu ɗan Zamfara
ne |
43. |
Monlo si garin
Kano to ba ti dola |
Zan tafi
garin Kano gobe |
44. |
Iyawo re wallahi
arewani |
Wallahi
matarshi kyakkyawa ce |
45. |
Yami ni dubu
kan |
Aro mini
dubu guda |
46. |
Je ka losi masallaci |
Zo mu tafi
masallaci |
47. |
Mofe jade amma
ba lokaci |
Ina son in
fita, amma ba lokaci |
48. |
Je ka losi Kasuwa
|
Zo mu tafi
kasuwa |
49. |
Monlo si Makaranta
|
Zan tafi
makaranta |
50. |
Funimi ni Kuɗi mi |
Ba ni kuɗina |
51. |
Omo Yaro
Ole ni |
Wancan
yaron ba ya da kuzari |
52. |
Mo nife Yarinya
na |
Ina son
yarinyar |
53. |
Mowe Laroyi
amma ni ana inwe |
Na yi wanka
yau da safe amma jiya ban yi ba |
54. |
Wa ta canja
oba iluwa |
Sun canja
Sarkin garinmu |
55. |
Moje Shinkafa
ni ana |
Na ci
shinkafa jiya |
56. |
Mo lo gida
ni ana |
Na tafi
gida jiya |
57. |
Olulufemi zan
so na san sanda kake mini |
Abin
kaunata ina son in san irin son da kike mini |
58. |
Kosi ciniki
|
Babu ciniki
|
59. |
Kosi wahala
|
Babu wahala
|
60. |
Don Allah e mo no mi |
Dan Allah
kada ka buge ni |
61. |
Mofe lo barci |
Zan tafi na
yi barci |
62. |
Bani ra gyaɗa |
Sawo mini
gyaɗa |
63. |
Bami gbe agogo
sinu ile |
Kai min
agogon nan cikin gida |
64. |
Gidanmu okurin
lopoju |
Gidanmu
maza sun fi yawa |
65. |
Maigidanmu oti de ni
ana |
Maigidanmu
ya dawo jiya |
66. |
Mofe mu omi
amma babu sanyi |
Ina son
shan ruwa, amma babu sanyi |
67. |
Eba ati miyar
ganye |
Taiba da
miyar ganye |
68. |
Matata ta
iya obe |
Matata ta
iya miya |
69. |
Bani ogu e
fan |
Bani
maganin sauro |
70. |
Eni yi baba
mi |
Wannan
babana ne |
71. |
Mi ma wa ni
kullum |
Na dinga
zuwa kullum |
72. |
Moti se alƙawali |
Na yi alƙawali
|
73. |
Bami ra
Ohunje mai yaji |
Sawo min
abinci mai yaji |
74. |
Mama ni
tilo ra mangyaɗa |
Mamata ta
tafi ta sawo mangyaɗa |
75. |
Mora jaka
tuntun |
Na sawo
sabuwar jaka |
4.10 NAƊEWA
A taƙaice
wannan babi ya yi magana ne a kan ingausa, inda aka buɗe shi da
shimfiɗa, sai kuma
ma’anar harshe, sai kuma taƙaitaccen
bayani a kan harshen Hausa da na Yarbanci, haka kuma an waiwayi ra’ayoyin
masana game da ma’anar ingausa, bayan wannan kuma an duba nau’o’i da dalilan da
ke haifar da ingausa, bugu da ƙari, mun
kalli amfani da illolin ingausa, sai kuma gundarin aikin wato ingausar Yarbawa
da Hausawa a garin Gusau. Daga ƙarshe naɗewa ta biyo
baya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.