Ticker

6/recent/ticker-posts

Adashen Mata A Garin Gusau (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Adashen Mata A Garin Gusau (3)

NA

AMINA ABUBAKAR

 

Adashe

BABI NA BIYU

TARIHIN GARIN GUSAU DA SANA’O’IN SU

2.0 GABAARWA

Wannan babi na biyu zai tattauna a kan abubuwa kamar haka: Taƙaitaccen tarihin Garin Gusau, Bugu da ƙari kuma zai yi duba zuwa ga ire-iren sana’o’in mutanen Gusau, tare da duba muhimmancin sana’a. Daga ƙarshe kammalawa.

 

2.1 TAƘAITACCEN TARIN GARIN GUSAU

Garin Gusau shi ne babban birnin jihar Zamfara wadda aka ƙirƙiro a ranar (1/10/1996), daga tsohuwar jihar Sokoto. Garin Gusau na kan titin Sakkwato zuwa Zariya. Daga gabas ya yi iyaka da ƙasar Ƙaura Namoda ta wajen yamma kuwa ya yi iyaka da ƙasar Bunguɗu, ta kudu ya yi iyaka da Ɗansadau.

 

Tarihi ya nuna cewa, an samu kalmar Gusau ne daga kalmar “Gusa”, dalili a nan shi ne, lokacin da malam Sambo Ɗan’ashafa ya sara garin ‘Yandoto, bayan kammalawa ne, sai ya ce bari mu “gusa”, daga nan sai ya zo a nan, inda ya sara garin Gusau, cewar da ya yi bari mu ‘gusa’ shi ne asalin samuwar wannan suna na Gusau.

 

Tarihi ya nuna cewa, babban abin da ya sa ya gusa shi ne, domin kawo ci gaba a wannan ƙasa baki ɗaya. malam Sambo Ɗan’ashafa shi ne ya kafa garin Gusau a shekarar (1799), shi kuwa malam Sambo Ɗan’ashafa, asalinsa mutumin garin ‘Yandoto ne, ta ƙasar Katsina, ƙasar garin kuwa na da shinfiɗaɗɗen yanayi maras kwararan duwatsu, sai jefi-jefi, kuma a kan tudu yake, kuma kafin kafuwar wannan gari, mutanensa na farko sun sha fama da yake-yaƙe.

 

Al’adun jama’ar wannan gari, al’adu ne, na musulmi zallah, kwararar baki garin, na daga dalilan habbaƙarsa. Haka ma, an taɓa zagaye garin da ganuwa mai kofofi tara. Daga baya garin ya ƙunshi ƙabilu daban-daban kamar Fulani, Katsinawa, Zamfara, Gobirawa, Garawa, Ibira, Yarbawa, Barebari da sauransu.

 

Ta fuskar kasuwanci kuwa, garin Gusau ya zama cibiyar kasuwanci a ƙarni na goma sha tara (19), zuwa na ashirin (20). Daga lokacin da aka kafa wannan gari zuwa yau, an yi sarakuna goma sha biyar (15) takwas daga ciki sun fito ne daga zuri’ar malam Sambo Ɗan’ashafa, a yayin da sauran (6) sun fito ne daga waje wato tun daga (1906 - 2005) Sarkin da ke ci a lokacin yanzu shi ne Sarkin Katsinan Gusau Alh. Ibraim Bello, wanda aka rantsar a ranar, 5th /4/ 2015.

 

Haka kuma, kamar yadda aka yi wa wasu garuruwa da wurare kirari- don yi masu zuga da fito da su fili ga jama’a a ƙasar Hausa, Gusau ma ba a barta a baya ba, tana da nata kirarin ga wasu misalai daga cikinsu.

·         Gusau ta Sambo kanwar daji

Daga gare ki sai ai ɗamara

·          Gusau ta Sambo Dandin Hausa

Kowaz zo Gusau abinai shi gusa

·         Gusau ta Sambo ƙwarya mai kasha akushi

Takarda mai kasha turmin lailai

·         Gusau ta Sambo ba a kai maki yaƙi ta Sambo garkuwa mutanen Sambo.

 

2.2 IRE-IREN SANA’O’IN GUSAU

Sana’o’in gargajiya su ne sana’o’in da Hausawa suke yi tun kafin saduwar su da baƙin al’ummomi kamar Larabawa da Turawa da sauransu. Hausawa sun tashi tsaye da yin sana’o’in gargajiya daban-daban, kuma kowace ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa akwai sana’o’in da suka fi shahara da su. Gusau ta kula ainun tare da ba da himma wajen yin sana’o’in gargajiya iri-iri. Daga cikin sana’o’in da mutanen Gusau suka fi shahara da yin su akwai.

-          Noma

-          Saƙa

-          Rini

-          Ƙira

-          Jima

-          Aski

-          Dukanci

-          Kuɗa

-          Kiwo

-          Sassaƙa da sauransu

2.3 MUHIMMANCIN SANA’A

Yin sana’a a ƙasar Hausa muhimmin abu ne, domin ba a girmama mutum idan har ba shi da wata takamaimiyar sana’a. Wani lokaci ma mutum kan rasa aure idan ba shi da wata sana’ar yi, domin za a ga ba zai iya riƙa matar ba, ba zai sami biya mata buƙatunta na rayuwa ba. Al’umma kan daɗa ginuwa da bunƙasa ta hanyar aiwatar da sana’o’i, unguwa ko gari kan kafu a sanadiyyar tsayar da sana’o’i (Yahaya, 1992:53).

Muhimmancin da sana’a ke da shi yana da yawa, amma ga wasu daga ciki kamar haka:

·         Bunƙasa tattalin arzikin ƙasa

·         Samar da abin masarufi

·         Samar da aikin yi

·         Haifar da wasu sana’o’i

·         Raya al’adun gargajiya

·         Samar da magunguna na musamman

·         Cuɗanya da sauran jama’a

·         Tarbiyyar sana’a

·         Samar da kyakkyawan tsaro ga ƙasa

Yanzu za a ɗauki waɗannan batutuwa ɗaya bayan ɗaya domin a ga abin da suka ƙunsa:

1.      Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa: A yayin da aka ji al’umma na magana a kan tattalin arzikin ƙasa, to fa ana nuni ne da yadda za a kawar da talauci da yunwa da fatara waɗanda suka addabi al’umma. To bisa wannan dalili ne, sana’a ta zamanto tafarkin bunƙasa tattalin arziki na al’umma da kuma ƙasa baki ɗaya. Sana’a ɗaya na buƙatar hannu ashirin na mutane. Duk al’ummar da ta zama ba ta sana’a sai zaman banza, to fatara da talauci da yunwa da rashin zaman lafiya da ƙiyayya da hassada da ƙyashi su za su addabi wannan al’umma. Daga ƙarshe kuma sai yaƙi na ƙabilanci ko rikicin addini ya wanzu tsakanin wannan al’ummar. Wannan kuma shi zai haifar da rashin ci gaba da kuma koma baya a rayuwar wannan al’umma.

2.      Samar da Abin Masarufi: Sana’a kan haifar da tafarkin dogaro da kai, domin tafarki ne na samun abubuwan masarufi da suka haɗa da ci da sha da sutura da kuma mallakar iyali. Duk mutumin da yake da sana’a zai kasance mai rufin asiri da samun sauƙin gudanar da duk wasu al’umuran da suka shafi tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum cikin sauƙi, saɓanin mutumin da ba shi da wata daraja ko matsaya. Lallai marar sana’a, idan ba a iske shi ɓarawo ba, zai zama shawararsu guda da ta ɓarawo. Domin dole ne ya kasance yana da buƙatu kamar ci da sha da sutura, amma kuma ga shi ba ya sana’a. Saboda haka sana’a kan taimaka wajen samar da abin masarufi na rayuwar yau da kullum.

3.      Samar da Aikin Yi: Daga cikin muhimmancin sana’o’in Hausawa na gargajiya akwai samar da aikin yi. Misali, dukkan sana’o’in Hausawa kamar noma da ƙira da gini da saƙa da dukanci da fawa na samar da aikin yi ga al’umma. Idan Ɗan’adam yana da abin yi, to zai kasance koda yaushe cikin tsarkin zuciya da kuma kuɓuta daga saƙe-saƙenta. Sannan duk mutumin da ya kasance yana da sana’a za a same shi da wadatar zuci da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma. Dalili shi ne yana da aikin yi wanda kan haifar da ƙima da daraja da ɗaukaka a idon al’umma. Sannan mutum ba shi da wata fargaba a kan duk wata buƙata da za ta taso masa musamman ta kuɗi, domin yana da sana’a.

4.      Haifar da Wasu Sana’o’i: Dangane da hayayyafar sana’o’i za a ga cewa kowace sana’a aka ɗauka ta gargajiya, za a tarar ta samar da wata sana’ar ko kuma kayayyakin aikinta. Misali sana’ar fawa kan haifar da sana’ar jima, jima kuma ta haifar da dukanci. Haka kuma, idan aka ɗauki sana’ar ƙira tana haifar da kayayyakin gudanar da aikin gona kamar ruwan gatari da fartanya da lauje da sauransu. Haka abin yake ga sana’ar sassaƙa, su suke sassaƙa ƙotocin da ake zura ruwan fartanya da gatari da lauje domin gudanar da sana’ar noma. Saboda haka, babbar fa’idar sana’o’in Hausawa na gargajiya ita ce haifar da kayayyakin gudanar da wasu sana’o’in.

5.      Raya Al’adun Gargajiya: Idan muna maganar raya al’adun gargajiya, ana magana ne a kan wasu abubuwa kamar tufafi da kayan abinci da na adon ɗaki da makamantansu. Misali, waɗannan kayayyakin ana samar da su ne daga sana’o’in Hausawa na gargajiya. Kowace sana’a aka ɗauka za a tarar tana raya al’adun gargajiya. Misali idan aka ɗauki sana’ar sassaƙa da dukanci za a iske suna raya tare da adana wasu al’adun Hausawa na gargajiya, musamman wajen samar da kuma raya kayayyakin ƙawa da adon ɗakuna, misali zubuka[1] da ɗan goshi[2] da bishiri[3] da jalala[4] da huffi[5] da sambatse[6] da sauransu.

6.      Samar da Magunguna Na Musamman: Wannan na ɗaya daga cikin muhimmancin sana’a a Bahaushiyar al’ada. Misali sana’ar rini kan samar da tokar katsi da matan Hausawa masu juna biyu suke amfani da ita wajen zubar da zaƙi da ke daskarewa a mararsu, domin samun sauƙi wajen haihuwa. Sana’ar ƙira na samar da maganin wuta da na ƙuna da sauransu. Sana’o’in sun samar da maganin sanyi. Sana’ar aski na samar da magungunan ƙarfe da na ɗan wuya. Haka abin yake a sana’ar farauta, inda mafarauta ke samo nau’o’in itatuwa da saiwoyi iri daban-daban domin samar da wani magani na musamman.

7.      Cuɗanya da Sauran Jama’a: Sana’o’in suna taimakawa wajen cuɗanyar Hausawa da sauran ƙabilun duniya, ta fuskar cinikayya da kasuwanci. Haka kuma, sana’o’in gargajiya suna taimakawa wajen bunƙasa da daɗa ɗaukaka martabar Hausawa a fuskar wasu ƙabilu da al’ummun da ake hulɗa da su. Daga nan aka sami dangantakar kasuwanci da cinikayya tsakanin Hausawa da wasu al’ummun duniya, musamman waɗanda ke kewaye da ƙasar Hausa.

8.      Tarbiyyar Sana’a: Wannan wata hanya ce ta koyar da mutane halaye na gari ko kuma wani tafarki ko gwadabe ko turba da a kan ɗora mutum a kanta domin samun madogara dangane da tafiyar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Wajen koyon sana’o’i dole a sami yaro da ubangidansa, inda yaro kan sami tarbiyyar sana’a daga wajen ubangidansa. Wannan na daga cikin muhimmancin sana’o’in Hausawa na gargajiya. Ma’ana turba ce ta dogaro dangane da abubuwan rayuwar yau-da-kullum. Wannan dalili shi ne ya haifar wa Hausawa tafiya da ‘ya’yansu tun suna ƙanana wajen sana’o’insu. Misali manomi a Bahaushiyar al’ada kan rinƙa tafiya da ɗansa ko ‘yarsa ko ‘ya’yansa tun suna ƙanana gona, domin su riƙa kallo da kuma kula da yadda ake tafiyar da harkokin noma. Haka abin yake ga kowace sana’a tun yara suna ƙanana iyaye ke tafiya da su wajen wannan sana’ar tasu, domin ta zama shiriya ko tarbiya ga yaran in sun girma su gaji iyayensu wajen aiwatar da wannan sana’ar.

9.      Samar da Kyakkyawan Tsaro ga Ƙasa: Sana’o’in Hausawa kan taimaka wajen samar da kyakkyawan tsaro ga ƙasa, babu yadda za a yi baƙo ya shigo ya cuci al’ummar ƙasa, ba tare da an gano shi ba. Domin duk wanda ya zo a matsayin baƙunta, za a tambaye shi sana’ar da yake yi, sannan a kai shi wurin shugabanta. Shugaban sana’a ne zai saukar da shi, ya sa ido a kansa, ba za a saki jiki da shi ba, sai an ga kamun ludayinsa. Wannan yakan taimaka wajen rage kutsawar miyagu cikin ƙasa, kuma ya sanya duk wanda yake yin wata tafiya sai ya tabbatar yana da wata sana’ar da yake yi. Daga nan aka kashe zaman banza da yawon ba gaira ba dalili.

 

2.4 KAMMALAWA:

Wannan babi na biyu ya yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau, da yadda yanayin garin ya ke ta fuskar kasuwanci. Bugu da ƙari kuma ya yi bayani a kan asalin inda aka samu Kalmar Gusau, haka kuma ya yi bayanin lokacin da aka ƙirƙiro jahar tare da kawo shekara rana da kuma watan da aka samar da jahar kamar yadda ya gabata.

 

Bayan nan kuma duk a cikin babin an yi tsokaci a kan ire-iren sana’o’in Gusau, tare da kawo wasu daga cikin sana’o’in. Haka kuma an ɗan yi tsokaci a kan muhimmacin sana’a tare da kawo wasu abubuwa da ke da muhimmanci a sana’a, daga ƙarshe kuma an yi bayaninsu ɗaya bayan ɗaya.[1] Wani tin-timi mai taushi da ake ɗaurawa a ƙasan sirdin doki

[2] Wani naɗaɗɗen zare mai ƙullutu da ake maƙalawa a goshin doki

[3] Yanki ne mai ja da baƙi da ake rufe sirdin doki da shi

[4] Mashinfiɗi mai ado da baza da ake shimfiɗawa a kan sirdin doki

[5] Safa ce ta fata

[6] Takalmi ne mai adon jar fata da Sarakuna suke sakawa

Post a Comment

0 Comments