Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (3)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (3)

    waka

    BABI NA UKU

    TARIHIN KABIRU KILASIK

    3.0 GABATARWA

    A wannan babi za a yi cikakken bayani a kan rayuwar Alh Kabiru Yahaya Kilasik. Da dalilin fara waƙarsa da jigon waƙoƙinsa da ire-iren waƙoƙinsa. Haka kuma za a duba yadda yake tsara waƙarsa da kuma salon waƙoƙinsa, da irin matsayinsa a yau.Da yadda yake amfani da hikimarsa wajen haɓaka adabin Hausa.

    3.1 Tarihin Rayuwar Kabiru kilasik

    An haifi Alh Kabiru Yahaya kilasik a shiyar Ɗangawo cikin garin Talatar Mafara, a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba’in da takwas (1978). Sunan mahaifinsa Malam Yahaya. Sunan kakansa na wajen uba Malam Ibrahim  Sunan mahaifiyarsa Safiya, sunan kakansa na wajen uwa Mahammadu Macciɗo.Ya yi karatun allo a makarantar Malam Bawa a garin Sabon Birnin Gobir da ke jihar Sakkwato. Haka kuma ya shiga makarantar Boko a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da huɗu(1984) a garin Talatar Mafara, a makarantar Abubukar Tunau Model Primary School wacce ya kammala a alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in (1990). Kuma ya samu nasarar zarcewa zuwa makarantar Shiekh Abubakar Gummi Memorial College Sakkwato a wannan shekara. Haka zalika, ya samu nasarar kammala wannan makaranta a alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da shida (1996). Daga nan ya wuce makarantar fasaha da ƙere-ƙere ta Abdu Gusau Polytechnic Talatar Mafara a shekarar dubu biyu inda ya yi”certificate” a wannan shekarar..Kamar yadda mawaƙin ya nuna a cikin waƙarsa mai taken “Anpp Bani da Kowa”  asalinsu  fulani ne.Kuma ba nan kaɗai ya tsaya ba domin a waƙarsa ta Gwamnanin Arewa cewa ya yi,

    Jagora:            Kabiru ne tsatson ƙayatawa al’adarmu cin furen daji,

    Gwamnonin arewa dan Allah yazan kuna kwatanta adalci,

    In kune yau Kabiru Kilasik gobe takan yu ba yazan ku ba.”

    Ashe kenen idan aka yi la’akari da waɗannan ɗiyan waƙoƙin asalinsa Bafualatanin Maradun ne, makaƙera yadda ya bayyana da kansa.A yanzu Kilasik yana da mata uku, ga sunayensu kamar haka:-

    Matarsa ta farko sunanta Hajiya Lubabatu.

    Matarsa ta biyu sunanta Shafa’atu.

    Matarsa ta uku sunanta Hauwa’u.

    Yana da ‘ya’ya tara ga sunayensu kamar haka:

    Na farko shi ne mai sunan mahaifinsa Yahaya,

    Ta biyu  Khadija,

    Na uku Ibrahim,

    Ta huɗu Zainab,

    Na biyar  Muhammadu,

    Ta shida Fatima,

    Ta bakwai Hauwa’u,

    Na takwas Ahmad,

    Ta tara Safiya.

    Waɗannan su ne iyalan Alhaji Kabiru Yahaya Kilasik,kamar yadda muka gani yana da mata uku da ‘ya’ya tara a halin yanzu.

    3.2  Fara waƙarsa

    Babu wani abu da za a gudanar face akwai dalili ko mafarin yinsa ba. Wato,dukkkan lamari da ake yi akwai manufa ko maƙasudin aiwatar da shi. Gaskiyar masu hikima da ke cewa,”Ða walaki goro a cikin miya”   wato komi ka ga an yi akwai dalili.Don haka Kilasik ya fara waƙa ne tun shekarar alif dubu ɗaya da  ɗari tara da casa’in da shida, (1996), a loƙacin da yana ɗalibi, a wata dirama da suka shirya  a lokacin da suka ƙare makaranta.Ya fara da waƙa mai taken “Wargaji uban noma ba ka yin tsiyar gero” wato, waƙar noma inda yake cewa,

    Jagora:                                    Wargaji Uban Noma,

    Ba Ka Yin Tsiyar Gero

    Wargaji Ka Yin Dawa,

    Shi Ka Yin Buhun Maiwa.

    Da ya yi wannan waƙa shi ne Shugaban makarantarsu (principal)  Malam Ibrahim Liman ya nuna masa cewa yana da hazaƙa sosai, kuma ya sani ilimi bashi zai sa mutum ya ce bai iya saran icce ba, ko turin baro.Saboda haka  ya kamata ya jaraba ya gani. Wannan yana  ɗaya daga cikin dallilin fara waƙarsa.

    Haka kuma yana nuna cewa shi bai gadi waƙa ba sha’awa ce, inda ya nuna cewa sha’awar waƙoƙin Alh  Musa Ɗan Ba’u Gidan Buwai ta ja sha’awarsa ya fara waƙa.

    Daga nan bai sake waƙa ba sai da aka fara siyasa a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da tara (1999). A  lokacin da aka koma dimukuraɗiyya inda aka nemi ya yi wa jam’iyar NPN waƙa mai taken “Wurin Bindiga Wane Ƙyastu”  inda yake cewa,

    Jagora:                        Yarana ko da bayani ciki,

    Ina waƙa ba ku tanka ba,

    Karɓii:                  Lallai da bayani Kabiiru,

    Ka ƙi taɓo mana zancen baba.

    Kilasik ya yi waƙoƙi ɗari uku da hamshin  da tara (359). Ya ce a ranar  sha biyu ga watan uku shekara ta dubu biyu da goma sha takwas  (12-03-2018) , zai yi waƙa ta ɗari uku da sittin (360). Inda ya ce yana gab da  aje waƙa.Daga cikin waƙoƙinsa, waƙar Walin Kurya ita ce ta fi haskaka shi a idon jama’a. Kuma ta zama silar ɗaukakarsa a duniya. A taƙaice dai ita ce bakandamiyarsa. Kamar yadda ya nuna wannan waƙa abun al’ajabi ce  domin bai tsara ta ba , a wani lokaci kawai ya ji batocin waƙar na zo masa, nan take. A cewarsa kalmomin waƙa zuwa suke yi loƙaci ɗaya da kuma sun zo dole a rubuta su, don gudun kada su tafi domin da zarar sun tafi ba za su dawo ba.

    3.3 JIGON  WAƘOƘIN  KILASIK

    Jigo shi ne, manufa ko maƙasudi, ko saƙo da waƙa ke ɗauke da shi. Jigo shi ne saƙo da mawaƙi ke son isarwa a cikin waƙrsa. Masana da dama sun bayyana ma’anar jigo ta fuskoki daban-daban.Daga ciki akwai;

    Yahaya da wasu (1992), sun bayyana ma’anar jigo kamar haka, “jigo dai shi ne manufar waƙa wato saƙon da take ɗauke da shi a dunƙule”

    Shi kuwa Gusau (1993), cewa ya yi, “jigo shi ne abin da waƙa take magana a kansa ya ratsa ta tun daga farkonta har ƙarshenta”

    Amma Yahaya (1997) , ya bada ma’anar jigo da cewa,”wani muhimmin tubali ne na sharhi a kowane hali.”  Haka kuma sharhi kan jigo kan bayyana fahimtar da manazarci ya yi wa waƙar gaba ɗaya.

    Dunfawa (2008) cewa ya yi, “A rubutattar waƙa marubuci yakan ambaci jigon waƙarsa tun a farkon waƙa ko a tsakiyar waƙa ko a ƙarshenta”

    Murjanatu (2012) , ita ma ta yi ƙoƙarin kawo ma’anar jigo a daidai fahimtarta kamar haka: “Idan ana maganar jigo ana magana ne a kan

    a.      Saƙo da ke ƙunshe cikin adabi.

    b.      :Manufar ƙaga ko shirya abu.

    c.       Abubuwan da take karantarwa

    d.     Muhimmman abubuwan da ya bada haske a kansu.

    e.      Jigajigan abubuwa da aka tunkara ko aka fayyace a waƙa.

    Sanin kuwa ne cewa, duk abin da aka tsara to da manufarsa, don haka jigon waƙoƙin Kilasik shi ne  siyasa.A wata tattaunawa da aka yi da mawaƙin a gidan Talbijin na  RTƁ, dake cikin garin Sakkwato a shirin su na ‘Daga Bakin Mai Ita”  Mawaƙin ya bayyana cewa ‘yan siyasa yake yiwa waƙa, kuma su ne abokan hulɗarsa. Wannan zance haka yake domin kashi casa’in cikin ɗari na waƙoƙinsa duk na siyasa ne. Duk da a kan ɗan sami wasu da ba na siyasa ba. Kamar na Sarauta irn waƙar Sarkin Musulmi da ta Sarkin Gusau, da Sarkin Jabo da sauransu.

    Haka kuma ya yi wata waƙa wadda ta sauya mashi salon shi na zama maƙikin siyasa ya dawo wani, domin yara ne ya yi wa waƙar ‘ya’yan masoyinsa Barade. Ya bayyana cewa a halin yanzu babu wata waƙa da yake so a cikin waƙoƙinsa kamar wannan waƙar. Kuma waƙar ta samu karɓuwa. Waƙar ita ce,

    Jagora :          A watse kashi a sake rabo,

                         Fahad da Abubakar ku sani,

                         Duk Sakkwato wa ya kai ku uba,

                         Ɗiyan Ahmed Barade ubammu,

                         Ƙane ga Alu na har abada.

    Wannan waƙa Kilasik yana son ta sosai.Kamar yadda bayani ya gabata kilasik mawaƙin siyasa ne,Kuma mafi akasari ‘yan siyasa yake yi wa waƙa.

    Amma duk da haka a ‘yan siyasar ba kowa yake yi wa waƙa ba sai wanda ya yarda da halinsa da mutuncinsa. Kuma, ko a wacce jam’iya yake  ba sai a jam’iyar pdp yake ba.

    Akwai jigogi da dama da waƙoƙin Kilasik suka ƙunsa, musamman yabo da zambo da habaici da gugar-zana da arashi da makamantansu. Ga misalan wasu daga cikin jigogin waƙoƙinsa:

    -Gaskiya Mugunyar magana

    -Rumfar kara da ɗoriyar garwashi

    -In an ba albasa ruwa mugunyar

    --Jijjihin bubbukuwa

    -Iya ruwa fidda kai

    -Ruwa kar da bakin ƙwarya

    -Angulu da kan zabo

    -Ciki da gaskiya

    -Ramau ta fi farau zafi

    Wato mafi akasarin waƙoƙinsa tun a sunayensu yake buɗewa da zambo ko yabo ko habaici ko gugar zana domin isar da manufarsa ga al’umm

    3.4 Yadda Kabiru Kilasik Ke Tsara Waƙoƙinsa

    A nan za a duba yadda wannan mawaƙi ya ke tsara waƙoƙinsa, A haƙiƙanin gaskiya komi yana buƙatar tsari domin idan ba a tsara yadda za’a gudanar da shi ba dole ne za a cikaro da matsaloli.Tsari ya zama wajibi musamman ma a waƙa domin kowane mawaƙi yana da yadda yake tsara waƙarsa ko kiɗansa. Idan muka duba ƙarfin tunanin wannan mawaƙi, za mu ga cewa mawaƙin yana tsara waƙoƙinsa ta hanyar sigogi daban-daban.

    A wasu waƙoƙin yakan fara gabatar da lambar wayarsa sannan kiɗa ya biyo baya. Amma a wasu waƙoƙin sukan fara da kiɗa ne. Wasu kuma a gabatar da sunan waƙar ko takenta, sannan kiɗa ya biyo baya. Kuma yana sadaukar da waƙoƙin ne ga wasu mutane.

    Haka kuma wani lokaci sai ya gabatar da jigon sannan ‘yan amshi su ci gaba. A ya yin da ƙalilan daga ciki ‘yan amshi ke farawa. Haka kuma mawaƙin kan yi amfani da salon buɗe waƙarsa da addu’a bayan ya gabatar da jigon duk da kasancewar ba ya amfani da addu’ar wajen rufewa sai dai ya rufe da kiɗa.

    Alhaji Kabiru Kilasik na amfani da ƙafiya a dukkan waƙoƙinsa. Akwai amsa-amon ciki da na waje,wato babban amsa-amo da ƙarami a waƙarsa.

    Gaskiyar masu iya magana da suka ce, “yabon gwani ya zama dole” Kilasik na amfani da wani irin tsari na musamman mai burgewa da ƙayatarwa da kuma ban sha’awa da ba kowane mawaƙi ke amfani da shi ba a mawaƙan zamani. Ba a yi laifi ba idan aka ce karɓeɓeniya ita ce  ƙashin bayan waƙoƙinsa.Mafi akasarin waƙoƙinsa duk suna da karɓeɓeniya, ƙalilan ne babu ta a ciki.Duk da cewa magabata da suka yi aiki a kan wannan mawaƙi sun nuna cewa yana amfani da karɓeɓeniya iri biyu,  wato, karɓeɓeniyar baiti sukutum da kuma karɓeɓeniyar cikin baiti ɗaya. Haƙiƙa sun yi ƙoƙari. Amma hausawa na cewa “Abin da wayo ya ɓoye hankli ke gano shi”  wato a duk lokacin da mutum ya duƙufa a kan binciken wani abu ta hanyar bin diddiƙinsa tare da tonon silili da nazarin ƙwaƙƙwaf a kan wanan abin zai gano duk wani sirri da ke cikinsa.Ta haka ne na fahimci cewa Kilasik na amfani da karɓeɓeniya iri uku ne ba biyu ba, kamar yadda waɗanda suka gabace ni suka fahimta. Tsarin kaɓeɓeniyar shi ne, karɓeɓeniyar baiti sukutum, da karɓeɓeniyar cikin baiti ɗaya da kuma karɓeɓeniyar ɗango ko layi ɗaya. Saboda haka wannan tsari ne da ba kowane mawaƙi ke amfani da shi ba.Misali a waƙarsa   “In an ba albasa ruwa”

    Jagora:                 Rabbi Allah sarki ka maida jam’inmu guda,

    Har haɗa kawunan musulmi mu zamo har abada,

    Tunda kai ke baiwa ka fid da mu gun maraɗa,

    Dukka musulmi na duniya mu kauce tarkon sababi.”

    Amshi:                Musɗafa manzona Annabi madalla da kai,

    Ni a ƙyaleni a bar ni ka isan in yi da kai,

    Karramammen bawa na matsu in sadu da kai,

    Mai kamala Ahmadu Annabi tushen ladabi.”

    Idan aka lura a waɗannan baituttuka za a ga baiti sukutum take karɓewa.Haka kuma akwai karɓeɓeniyar cikin baiti in da zai faɗi layi ɗaya ta faɗi ɗaya. Ga ƙarin misali:a waƙarsa  mai taken”Baba dawo baba dawo”

    Jagora:     “Kusu ya tsare turbar kyanwa ya ce, “shege ka bi wajenga,

    Karɓii:      Ashe kare ya yi mai katanga da shi da kusu sun ka yi jinga,

    Jagora:       In ban cin faɗa da mai rabo ya ya turu za ya ja da ganga,

    Karɓii:       Kowa dai ya tsaya matsiyi nai in ba neman yawan faɗa ba”

    A nan Kilasik ya yi amfani da tsarin karɓeɓeniyar cikin baiti, bayan ya faɗi na ɗaya sai ta faɗi na biyu.Akwai kuma karɓeɓeniyar layi ɗaya. Ga misali a wata waƙarsa da ya yi wa Hajiya Sarutun Mamuda fes ledi.

    Jagora:            “ Ya Allahu gagara misali,

                              Mai Nijeriya mai Itali,

                               Waƙoƙi ala kulli hali,

    Jagoara:                Zan yo wa ga matar ubana ka sa idonta ba su kau ga ran ba,

    Karɓi:                 Zan yo wa ga matar ubana ka sa idonta  ba su kau ga ran ba.”

    A nan Kilasik yana amfni da karɓeɓeniya ta cikin layi ko ɗango guda.

    Tsarin da Kilasik ke amfni da shi a cikin jerin gwanon waƙoƙinsa ya sha banban da na sauran mawaƙan siyasa na zamani.Ba don kar na cika baki ba da na ce a duk mawaƙan  siyasa na wannan ƙarni da muke da su a yau, a kasar Hausa,babu mawaƙi mai azanci da hikima da tsari da jera tinani a waƙa da ya taka sawun Kabiru kilasik.

     

    3.5 IRE-IREN  WAƘOƘIN  KILASIK

    Duk da wasu na ganin cewa ba jinsi da kilasik yake yi wa waƙa in ban da ‘yan siyasa, amma akwai iren-iren waƙoƙinsa da ba na sisaya ba. Kamar yadda muka gani cewa ya fara da waƙar noma ne ta dirama da suka yi a lokacin ƙare makarantarsu. Daga baya ya koma waƙoƙin siyasa, haka kuma Kilasik yakan yi waƙoƙin sarauta da na aure, amma ya nuna baya waƙar aure sai in an matsa mashi, amma ya nuna bai iya waƙar aure ba. Yana waƙoƙin faɗakarwa kamar waƙar “Gwamnonin Arewa” inda yake cewa

    Jagora:       Kabiru ne tsatson ƙayatawa al’adarmu cin huren daji,

                       Gwanonin Arewa dan Aallah ya zan kuna kwatanta adalci,

                       In ku ne yau Kabiru Kilasik gobe takan yu ba ya zan ku ba.

    Yanzu haka ya yi waƙoƙin bege na yabon Annabi Muhammad( SAW)..Daga cikin waƙoƙin begen day a yi akwai wannan:-

    Jagora:             Ga alƙawalin da niɗ dauka,

                             Yau za ni cika shi ba shakka,

                              Na yi alwashi na baitukka,

                              Na begen daha mai makka,

                             Buwayi tsalkake ruhina sa in yi shi domin Allah

    Jigo:       ( Fiyayye Annabin rahama na Kadijatu Manzon Allah)

    Duk da  kasancewar kilasik mawaƙin siyasa wani loƙaci yakan yi waƙar aure. Daga cikin waƙoƙi da ya yi na aure akwai waƙar, Ibrahim IB da Habiba.Inda yake cewa:

    Jagora      Manzona sunnarka na yi,

                    Na bi umarnin yadda ka yi,

                    Sa mu gidan rahama Nabiyi,

                     Ya baban ma’asumiyarmu Fatima-Zara dab a ta ƙarya.

    Akwai wata waƙar auren Sabo Anka da Amaryasa Samira. Yana cewa:

    Jagora:      Ya Allah mamallakina mai ikon dare da rana,

                     Ka ba ni daman a raya sunnah aure ne a zuciyana,

                     Wannan sunnah ta Manzo ce bani bari a bar ni baya.

    Haka kuma wajen waƙoƙin siyasa ya fi yi wa ‘yan fi di fi waƙa, domin shi ɗan jam’iyar fi di fi ne kamar yadda yake faɗa a waƙoƙinsa da dama. Misali a waƙar I.O. Cigarin Ƙaura yana cewa:

    Jagora:   Fi di fi Kilasik yake yi kuma ita nir riƙe ko yaushe,

    Amshi:   Ko a mafalki nic ci tuwan masara sai na matsa na maishe”

             Ga abin da yake faɗa a wata waƙa da ya yi wa A.A. Yari..

    Jagora:   Wasu da sun ga na yi ma Shehi waƙa za su ga fi di fi nika yi,

    Karɓi:     Bara na ƙara faɗawa mutane Kabiru fi di fi yaka yi”

    Haka ma bayan gama zaɓen shekara ta dubu biyu  da goma sha ɗaya, bayan jam;iyar ANPP ta yi nasarar lashe zaɓe an ta raɗe raɗIn Kilasik ya koma ANPP, don haka ya yi wata waƙa dan tabbatarwa al’umma cewa yana nan a pdp, in da yake cewa:

    Jagora:ANPP ba ni da kuwa,

    Kuma kun san ba ku da niya,

                                           `Kar muka kallon juna,

    Kabiru nai maku kallon mai bisa ruwa”

    Ba a nan Kilasik ya tsaya ba, akwai wata waƙa da ya yi wa Mamuda mai taken “Baba dawo baba dawo” yana cewa:

    Jagora:    Fi di fi Kilasik yake yi an ja an ja na ƙi barin ta,

    Karɓii:   Jam’iyata ta yi mini komi kowace waƙa ina yaba ta.”

    Kenan waɗannan dalilai sun isa su gamsar da mu cewa Kilasik ɗan jam’iyar pdp ne, kuma ita ce ya fi yi wa waƙa.Har ma yakan kirata jam’iyarsa kamar yadda muka gani. Kuma jam’iyar ta tsayar da shi a matsayin ɗantakarar majalisa a (2015). Yanzu haka an ba Alh kabiru Yahaya kilasik SA a ƙaƙrƙashin tutar Apc wanda ya ba shi shi ne mai gidansa Alh Mamuda Aliyu Shinkafi.

    3.6 SALON WAƘOƘIN KILASIK

    Salo na ɗaya daga cikin ginshiƙan gina waƙa domin duk waƙar da ba ta da salo ba za ta samu karɓuwa ba a wajen jama’a. Kasancewar Kabiru Kilasik mawaƙin siyasa yana da salailai da yake amfani da su don waƙoƙinsa su samu karɓuwa ga jama’a kuma su yi armashi/Yana amfani da salo daban-daban domin jaddada manufarsa, musamman abin da ya shafi adon harshe da gwanintar harshe,da kuma salon sarrafa harshe.

    Ɗangambo.A (2006) Ya bayyana cewa: “Salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci.Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma .lafazi, yanayi, hanya ko tunanin a maimakon wani”

    Bunza A.M (2013) Ya ce salo shi ne “Dabara da fasaha da wayon tafiyar da wani abu cikin basira da natsuwa domin a kai ga wata manufa ta musamman.Matakan da za a bi wajen sarrafa hikimomin baka ko rubuce ko a aikace ya kasance mai jan hankali ne da burgewa ga mai sauraro ko karatu ko kallon aikin”.

    Ɗangulbi (1996) ya ce; “Sslo na nufin duk wata hanya da mawaƙi ke bi domin  isar da saƙo a cikin waƙarssa.

    Kamusun Hausa na CNHN, cewa suka yi: “Yayi ko sauyi ko launi ko fice”

    Nulic (1971) Ya ce; ‘salo  hanya ce da ake bi wajen isar da saƙo ko manufa”

    Leech (1981), Ya bayyana cewa: “Salo shi ne kwalliyar tunani wajen isae da saƙo”

     Zaɓin da duk mutum ya yi wajen isar da saƙon da yake so ya isar zai yi tasiri ga wanda  ake isar da saƙon gare shi.Salo dabara ce da mawaƙi kan yi amfani da ita domin jawo hankalin mai sauraran waƙa, ya fahimci saƙon da ake so ya isa gare shi..

    Kuma yana amfani da salon aron kalmomi, daga wasu harsuna, musamman

    a harshen Larabci da Ingilishi.

    Haka kuma yana amfani da karin harshen Sakkwatanci da Zamfarci domin shi Bazamfare ne.Wannan ma shi ya haifar da Nazarin Ginin Kalmomin Zamfarci A Wasu Waƙoƙin Kilasik.

    3.7 Kammalawa

    Alhaji Kabiru Yahaya kilasik, ya fara waƙa tun tsawon shekara ashirin da biyu (22), da suka shuɗe. Ya fara ne da waƙar was an kwaikwayo. Kamar yadda bayyani ya gabata. Mun ga tarihinsa da ire-iren waƙaoƙinsa da kuma salonsa da yadda yake jera tunanesa a cikin waƙoƙinsa. Mun ga irin matsayinsa da ɗaukakar da Allah ya yi masa a fanninsa na waƙa. Kuma waƙa ita ce babbar sana’arsa, ya kuma samu ɗaukaka a cikin harkar waƙa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.