Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zababbun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (5)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (5)

    NA

    NASIRU HASSAN 

    Siyasa

    BABI NA HUƊU

    4.0 GABATARWA

    YANAYIN SALAILAN JAWABIN KAMA AIKI NA GWAMNONIN JIHAR ZAMFARA

    Jawabin kama aikin da zaɓaɓɓun Gwamnoni ke yi, al’amari ne mai matuƙar muhimmanci ga al’umma, domin a wannan jawabin ne zaɓaɓɓen yakan fito da tsare-tsare da gwamnatinsa za ta sa gaba domin jin daɗin al’ummar da zai mulka. Saboda haka wajen gabatar da jawabi irin wannan gwamnoni kan yi amfani da salailai daban-daban domin jawo hankalin jama’a su yarda da abin da suke faɗa ko suka ƙudurta yi zuwa ga al’umma. Saboda haka ne ma wannan babi zai mai da hankali kan salo da siyasa da lafuzzan yan siyasa ta yadda suke sarrafa harshe. Sai kuma nazari kan jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun gwamnonin jihar Zamfara daga shekara ta 2007 zuwa ta 2019.

     

    4.1  MA’ANAR SALO

    Salo muhimmin abu ne a rayuwar al’umma, musamman dangane da maganganun siyasa. Wannan ne ya sa aka kawo shi a cikin wannan aiki na jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun gwamnonin jahar Zamfara, salo na taka muhimmiyar rawa a ɓangarorin rayuwar ɗan – adam.

     

    Ɗantumbishi, (2005 da 2007) ya ce, salo na taka muhimmiyar rawa a ɓangarorin harshe da waƙa da kuma al’ada. Saboda haka, tun da akwai shi a harshe, kuma ya kamata a duba shi, domin fayyace muhimmancinsa a wannan aiki na siyasa. Salo shi ne hanyar gudanarwa wato mai jawo hankali ya tara shi gu ɗaya.

     

    Yahaya (2001); ya kira salo da cewa “Shi ne asirin waƙa. Waɗannan bayanai na nuna mana cewa salo na da muhimmanci ga waƙa da kuma magana. Salo na taka rawa a dukkan harkikin rayuwa. Wannan ne ya sa aka ga ya dace a duba salo da alaƙarsa a siyasa. Saboda haka ‘yan siyasa na amfani da salo ne domin isar da saƙonninsu na siyasa.

     

    4.2 SALO DA SIYASA

    Jawabin kama aiki na gwamnoni wani fage ne a cikin da’irar siyasa, wanda ke zaman kansa. Duk lokacin da masana suka zo bayani kan siyasa a ɓangaren jawabai, yana da salo na musamman. Masana da manazarta da masu bincike kan siyasa, na lura da jawaban ‘yan siyasa.

     

    Salon magana ga ‘yan siyasa na taka rawa wajen isar da saƙonni ga jama’a. Wato dabaru na iya tsara zanttuka na jawo hankalin mutane ta yadda za su fahimci manufar da mutum ke ɗauke da shi, domin samun goyon baya. Yin haka ga ‘yan siyasa shi ke ba su dammar samun tafiyar da mulkinsu, ta salon da suke ganin ya dace.

     

    Siyasa ta ƙunshi maganganu da lafuzza domin neman amincewar jama’a. Wannan dalili ya sa ake samun salo na musamman wajen gudanar da wasu harkoki na siyasa, kamar wajen kamfe. Jam’iyyun siyasa kan shirya kamfe, domin samun damar yi wa jama’a bayanai kan manufarsu da ayyukan da suke da niyyar yi masu. Saboda haka, suke samun lokaci na yi wa jama’a bayanai ta hanyar tallata ‘yan takararsu tare da yin suka ga jamiyyun da suke adawa da su. Wannan ɓangare shi ne ke nuna gogewa da basira da hikima da ‘yan takara ke da ita. Jangebe (2015).

     

    4.2.1 SALO DA LAFUZZAN SIYASA

    Magana ta ƙunshi fitar da sautuka ta hanyar amfani da kalmomi cikin tsari da wannan harshe ya aminta da shi. Muhimman abubuwa sun haɗa da zaɓen kalmomin da suka dace, da kuma amfani da su inda ya dace.  A wannan lokaci mai magana shi ne wakilin jam’iyyarsa, idan ya nuna bajinta a yi karuruwa, ko a dara a mayar da martani.

     

    Ana buƙatar zaɓen kalmomi waɗanda ke iya jan hankalin mutane. A yanayin jawabi irin wannan na ba da damar yin amfani da gaɓɓan jiki wajen ƙara bayani kamar amfani da hannaye ko kai ko ido da sauransu. Harshe na taka muhimmiyar rawa wajen jawabin siyasa, saboda haka, akwai buƙatar ƙwarewa sosai ga harshen da ake amfani da shi wajen gabatar da jawabi (Jangebe 2015).

     

    Dole ne mai gabatar da jawabi ya taɓɓatar ya san abin da wannan jamaa suke buƙata. Kamar duba ɓangaren sana’a, noma, ilimi, lafiya, hanyoyi da makamantansu, wannan shi zai jawo hankalin mutane nan take, domin ɗan adam na son a damu da abin da ya dame shi. Wannan ya nuna cewa dole a yi amfani da hankali domin fahimtar inda ake, domin kar a yi tuya a manta da albasa. Duk abubuwan da ɗan siyasa zai faɗa, idan ya manta da buƙatar al’umma, za su ɗauke shi sauna, kuma su ƙyamace shi.

     

    Duk da cewa jawabi ko lafazi ake magana a kai, a irin waɗannan wurare sutura na da tasiri, domin ita ma na ba da saƙo dangane da mutum. Wannan ya nuna cewa salo na da alaƙa da abubuwa da yawa. Don wani shigar da ka yi ita za ta bashi sha’awa kafin lafazinka. (Jangebe 2015).

     

    4.2.2 SALO DA SARRAFA HARSHE

    Idan muka dubi ma’anar salo za mu ga cewa mutane da yawa sun yi ta tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar salo, domin kuwa idan muna son mu fito da ire-iren salon da muke da su a cikin magana ko a rubuce, to yana da kyau a yi ƙoƙarin fitowa da ma’anar salo don a fahimci inda aka dosa.

     

    Nazari ya nuna cewa, salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo. Za a iya fassara salo kamar haka, (Jangebe 2015). Salo wani abu ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin amfani da wata kalma ko lafazi ko yanayi ko hanya ko tunani a maimakon wani zaɓin da duk mutum ya yi wajen isar da saƙon da yake so ya isar zai yi tasiri ga wanda ake isar da saƙon gare shi. Salo ƙari ne na daraja a cikin rubutu ko furuci. A bisa wannan ma’ana ana iya cewa ba lalle ba ne a sami salo cikin kowane irin rubutu ko furuci ba.

     

    Haka ma salo iri- iri ne, akwai miƙaƙƙen salo; wato salo ne kai tsaye, mai sauƙin ganewa da isar da saƙo. Salo mai armashi mai karsashi, shi ne salon da ya gamsar ta hanyar karsashi ko ƙaƙale da burgewa. Raggon salo; shine mai kashe jiki kuma marar gamsarwa. Tsohon salo da sabon salo; shi ne wanda ake amfani da tsofaffin hanyoyi ko sababbi don isar da saƙo. Yana iya zama mai gamsarwa ko akasin haka. Akwai salo mai sarƙaƙiya ko mai tsauri, shi ne mai wahalar ganewa saboda tsarin saƙar manufofi ko tsauraran kalmomi.

     

    Nazari bai tsaya nan ba, sai da ya sake duba salon nazari a matsayin sarrafa harshe da dabara ta jawo hankali ta amfani da salon sarrafa harshe. Shi ya sa ake amfani da kalmomin Larabci da Turanci da Fulatanci da sauransu domin nuna ƙwarewa da ƙawata jawabinsa ga masu sauraro ko karantawa.

     

    Salon adabi shi ne adon harshe wanda ake samu cikin rubutattun waƙoƙi ko na baka. Irin waɗannan dabaru suna faruwa cikin waƙoƙi ko jawabi. Adon harshe kuma ya shafi azancin magana. Irin wannan ya haɗa da kirari da ƙarangiya ko gagara-gwari da habaici da Karin magana da sauransu (Jangebe 2015).

     

    Dangane da waɗannan ma’anoni a iya cewa salon sarrafa harshe hanya ce da mutum kan zaɓa wajen sarrafa harshe cikin wani yanayi da manufa ta daban, ta yin amfani da kalmomi masu jawo hankali tare da burgewa da kuma nuna gwanintar harshe. Don haka, za a iya fahimtar cewa sarrafa harshe na wanzuwa ta fuskar rubutu, wato yadda mutum zai zaɓi wasu kalmomi na gwaninta da burgewa ta la’akari da wau kalmomi da amfani da karin magana ko salon magana da kamantawa da kinaya da mutuntarwa da kuma kambamawa; haka ma duk waɗannan yanayin sarrafa harshe a cikin rubutu sukan zo da kuma adabin baka.

     

    4.3 NAZARIN JAWABIN KAMA AIKI NA ZAƁAƁƁEN GWAMNAN A 2007.

    JAWABIN GWAMNA MAHMUD ALIYU SHINKAFI

    “Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW).  Ina fara wannan jawabin da godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya nuna mana wannan rana mai cike da tarihi, wato lokacin karɓar mulkin Jihar nan, inda aka samu tarihin da ba’a taɓa samu ba a siyasar ƙasar nan, inda aka samu gwamna mai barin gado ya miƙa wa mataimakinsa mulki.

    Ina ƙara miƙa godiyata ga al’ummar jahar Zamfara da kuka bamu goyon baya ganin mun samu nasara ta hanyar jefa mana ƙuri’unku a jam’iyyarmu ta ANPP, inda aka zaɓi dukan ‘yan takararmu a kowane mataki.

     

    Ya ku masu girma mahalarta wannan taro goyon bayan da kuka ba gwamnatin da ta gabata. Ina fatar ku ci gaba da bani shi domin kawo ayyukan raya ƙasa da na haɓaka tattalin arzikin wannan jiha. Zamu ci gaba da shirye-shiryen tsohuwar gwamnati ta “Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura” tare da fito da wasu sababbi kamar inganta noma duba da irin gudummuwar da yake bayarwa wajen haɓaka tattalin arziki.

     

    Zamu ba da kulawa ta musamman a ɓangaren ilimi wajen gina ajijuwa da ɗakunan karatu a firamare da sakandare. Haka ma zamu yi ƙoƙarin gina jami’a mallakin Jiha. A ɓangaren kiwon lafiya, za mu inganta asibitoci tare da samar da ƙwararrun likitoci da samar da magunguna domin ba da kyakkyawar kulawa ga al’ummar wannan jiha.

     

    Haka kuma za mu gyara dukan hanyoyin wannan jiha tare da gina sababbi. Haka ma za mu inganta tare da samar da ruwan sha a karkara da birane, musamman a Gusau babban birnin Jiha.

    Mun yi tanadi na musamman don inganta rayuwar mata da samari (matasa). Don haka, ina kira da ku bamu goyon baya domin samun nasarar shirin.

    Ina tabbatar wa da iyayenmu sarakuna cewa; wannan gwamnati za ta yi aiki da ku, tare da karɓar shawarwarinku. Haka ma za mu taimaka wa ‘Yan kasuwa domin inganta kasuwanci a wannan jiha.

     

    Daga ƙarshe, ina ƙara godewa Allah da ya nuna mana wannan lokaci mai albarka. Haka ma ina ƙara miƙa godiyata ga dattijan wannan jam’iyya tamu mai albarka da ɗaukacin al’umar jihar Zamfara”.

     

    SHARHI

    Manufar wannan jawabi shi ne, ƙulla dangantaka tsakanin gwamna “Mahmuda Aliyu Shinkafi” da kuma al’ummar jihar Zamfara, tare da gabatar masu shirye-shiryen da aka tanada domin su da nufin amincewarsu da goyon bayansu zuwa ga gwamnati.

     

    Shi dai wannan jawabi an gabatar da shi ne a ranar 29, ga watan Mayu, 2007. Bayan karɓar rantsuwa da gwamna “Mamuda Aliyu Shinkafi” ya yi.

     

    TSARI

    An tsara wannan jawabi a zube kuma ya zo ne a gaɓa – gaɓa da nufin isar da saƙon gwamnati zuwa ga al’ummar jihar Zamfara. Saboda haka, jawabin a tsare yake, kowane batu na bin ɗan uwansa. Wato an tsara shi daki – daki ba wai kara zube ba, wato an yi shi bisa tsari mai kyau mai jan hankali da ba da nishaɗi ga mai sauraro.

    SARRAFA HARSHE 

    Sarrafa harshe ya danganci irin yadda mai jawabi ya yi amfani da kalmomi da jimloli, wato jerantuwarsu a wannan jawabin mai girma gwamna ya yi amfani da sauƙaƙan kalmomi da jimloli da salale daban-daban masu sauƙin fahimta ga kowane mai sauraro.

     

    SALO

    Abubuwan da aka nazarta a ƙarƙashin salo wanda kuma daga kansa ake yanke hukunci a ce salon jawabin ya ƙayatar ya yi armashi ko kuma ragon salo ne. Wannan ya haɗa da nazarin kalmomi da mai jawabi ya yi amfani da su wajen gina jawabin da kuma adon magana kamar Karin magana, maganganun hikima da tsarin gina jimloli a jawabin. Jawabin ya ƙunshi salele kamar haka:

     

    Mai jawabin ya fara da salon buɗewa inda ya yi yabo ga Allah da salati ga Annabi Muhammad (SAW) inda yake cewa:

    “Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Tsira Annabi Muhammad (SAW)”

     

    SALON TUNATARWA / GODIYA

    Ya yi amfani da tunatarwa ga al’ummar jiha da ƙasa cewa ba a taɓa samun wannan tarihi ba sai Zamfara.

    “Ba a taɓa samun wannan tarihi ba a siyasar ƙasar nan, inda gwamna mai barin gado ya miƙa mulki ga mataimakinsa ba”

     

    Ya ƙara godewa al’ummar jiha, inda ya ce.

    “Ina ƙara godewa al’ummar jihar Zamfara da kuka bamu goyon baya domin samun nasara ta hanyar jefa mana ƙuri’unku a Tutar Jam’iyyar ANPP”

     

    Ya fito da ragon salo a jawabinsa inda ya ce,

    “Zamu cigaba da shirye-hiryen tsohuwar gwamnati, tare da fito da sabbi”

    A nan yana nufin zasu yi ƙoƙarin gina Jami’a mallakin jaha, da inganta samar da ruwan sha a babbar birnin Jiha, kamar yanda tsohuwar gwamnati ta ƙudurta amma ta kasa. Wannan ragon salo ne

     

    SALON KIRA DA BA DA GOYON BAYA

    Mai jawabin ya yi amfani da salon kira da neman goyon baya inda ya ce:

    “Ya ku masu girma mahalarta wannan taro, goyon bayan da kuka ba gwamnatin da ta gabata, ina fatar ku cigaba da bamu shi domin cigaba da ayyukan raya ƙasa da haɓaka tattalin arzikin jiha”

    SALON TABBATARWA

    Ya tabbatar wa da al’ummar Zamfara da ɗorewa ga ayyukan ci gaba inda ya ce:

    “Zamu cigaba da shirye-shiryen tsohuwar gwamnati, tare da fito da wasu sababbi kamar inganta noma, hanyoyi, ruwan sha, kiyon lafiya, ilimi da sauransu.

     

    Haka ma, ya ƙara fito da wannan tabbaci a gaɓar ƙarshe na jawabin inda ya tabbatar wa mata da samari da sarakuna da kuma ‘yan kasuwa:

    “Mun yi tanadi na musamman don inganta rayuwar mata da samari. Haka ma ina ƙara tabbatarwa sarakuna cewa zamu yi aiki da su da kuma karɓar shawarwarinsu. Haka ma zamu taimakawa ‘yan kasuwa domin ganin an inganta kasuwanci a wannan jiha”

    Idan aka dubi tsarin wannan jawabin za a ga cewa jawabi ne da aka gabatar kai tsaye daga gwamna “Mahmuda Aliyu Shinkafi” zuwa ga al’ummar jihar Zamfara. Jawabin ya ƙunshi gaisuwa da godiya da jan hankali da kuma tabbaci. Kuma an yi amfani da kalmomi da suka dace a jawabin. Haka ma Jawabin bai taɓo zantukan da suka shafi adon harshe ba. Kamar Karin magana, habaici da sauransu. Wannan ba zai rasa nasaba da cewa gwamnati ce ta gida ma’ana mai gida ne ya miƙa wa yaronsa ragwamar mulki.

     

    Daga ƙarshe ya rufe jawabinsa da ƙara godiya ga Allah maɗaukakin Sarki da dattijan jam’iyya da kuma al’ummar jihar Zamfara.

    4.4 NAZARIN JAWABIN KAMA AIKI NA ZAƁAƁƁEN GWAMNA A 2011.

    JAWABIN GWAMNA ABDUL-AZIZ YARI ABUBAKAR

    MANUFA DA TSARI

    Shi wannan jawabi, jawabi ne zuwa ga al’ummar jiahar Zamfara bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2011. Wato gwamna Abdul-Aziz Yari Abubakar. A ranar 29 ga watan Mayu, 2011 ne aka rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan inda ya fara da cewa:

    “Ina matuƙar godiya ga Allah maɗaukakin Sarki da kuma godiya ga Shuwagabannin Jam’iyya, musamman jagora Alh. Ahmad Sani Yariman Bakura, ina ƙara godewa al’ummar Jihar Zamfara da kuka fito ƙwanku da ƙwarƙwatarku kuka zaɓe ni a wannan matsayi da nake kai a yau. Wannan babu ko shakka nasara ce tamu baki ɗaya. Bayan haka, ina kira ga waɗanda suka sha ƙasa a wannan tafiya (‘Yan adawa) da su zo mu haɗa hannu waje ɗaya domin cigaban wannan jiha tamu baki ɗaya ta kowane fanni. Dukaninmu Zamfarawa ne, babu abin da ya fi mana Jiharmu. Don haka, dole mu haɗa kanmu domin ba za mu bari ‘ya’yanmu da jikokinmu su lalace kan siyasa ba”

     

    Da wannan shimfiɗa mai aika saƙo ya kulla dangantaka tsakanin gwamna Abdul-Aziz Yari da kuma al’ummar Jihar Zafmara ta amfani da kafar jawabin, kuma dangantakar mai fa’ida. Wannan dangantaka ce ta tanadar wa wannan jawabi hurumi cikin manufa ta sadarwa. Dangane da jerantuwar jigo kuwa madosar ita ce Abdul-Aziz Yari da Al’ummar jihar Zamfara halin da jihar Zamfara take ciki. Saboda haka, ga jerantuwar jigon jawabin kamar haka.

    a.      Tabbacin dangantakarsa a matsayin ɗan Zamfara

    b.      Maƙasudin Jawabin na nuna irin yadda tattalin arzikin Jihar ya taɓarɓare.

    c.       Abubuwan lura da jan hankali

    d.     Rashin iya shugabanci, tattare da matsalar talauci da tsaro da almubazziranci.

     

    JAN HANKALI DA SARRAFA HARSHE  

    Tsokaci cikin ma’anar wannan jawabi yana da fa’ida, domin ta haka ne gaskiyar bayanan da suka bijiro a cikin jawabin za su share fagen fahimtar saƙonnin da ke ƙunshe a jawabin.

    “Na yi matuƙar nuna damuwata dangane da ayukan wasu ‘yan siyasa a jihar nan, siyasa wani tsari ne na aikin al’umma, haka ya ja ra’ayina ga shiga siyasa, domin yi wa al’umma aikin cigaban rayuwarsu a jiha da ƙasa baki ɗaya. Ina kuma nuna damuwata dangane da yadda aka kwashe shekaru, duk da ɗimbin albarkatun da Allah ya hore wa jihar nan bai amfani talakawa ba kasancewar noma shi ne abin tinƙahonmu, amman babu isasshen taki babu iraruwa, babu bashin da ake ba manoma domin samar da isasshen abinci a jiha”.

    Waɗannan batutuwa da suka gabata suna ɗauke da bayanai na aiwatarwa wato jimloli masu ƙarfafawa da mutuntawa. Da farko dai an ƙarfafa jimlolin rashin iya mulki, ko shugabanci yana tattare da wasu ɗimbin matsaloli. Don haka, rashin iya shugabanci yana ɗamfare da ɗimbin matsaloli a wannan jaha.

     

    Dangane da amfani da salo da sarrafa harshe kuwa, ana iya ganin ƙarfin amfani da harshe kamar yadda ya bijiro a jawabinsa, inda ya yi amfani da takaici da baƙin ciki, sannan ya yi ƙoƙarin canja tsarin shugabancin jihar Zamfara da siyasarta da ma tattalin arzikinta baki ɗaya

    “Za mu maida hankali ganin an dawo da ɗaliban da suka bar makarantunsu a sanadiyar rashin biya masu kuɗaɗen makaranta tare da basu ilimi kyautata a faɗin jihar nan. Haka ma za mu jawo masana’antu da masu hannu da shuni da su saka jari a wannan jiha domin cigaban tattalin arziki a wannan jiha, Wannan gwamnati ba za ta ɗauki sakaci da almubazziranci da dukiyar jama’a ba.

    Gwamnatin da ta gabata ta bar ɗimbin bashin biliyoyin kuɗi kama daga na bankuna zuwa na ‘yan kwangila wanda ya kawo sanadin taɓarɓarewar tattalin arzikin jiha.

    Daga ƙarshe, ina kira ga al’umma da ku bamu goyon baya domin fito da wannan jiha halin da take ciki”.

     

    Daga abin da ya gabata na jan hankali da sarrafa harshe, jawabin ya ƙara fito da waɗannan abubuwa:

    ·         Rashin iya shugabanci

    ·         Matsalolin talauci da tsaro da almubazziranci sun dabaibaye jihar Zamfara

    ·         Abin takaici da baƙin ciki

    ·         Alamurran siyasa da tattalin arziki da zamantakewa sun dagule.

    SALO

    Mai jawabin ya yi amfani da salale daban-daban.

     

    SALON BUƊEWA

    Ya yi amfani da salon buɗewa da fara godiya ga Allah inda ya ce:

    “Ina matuƙar godiya ga Allah maɗaukakin sarki……

     

    SALON JAN HANKALI

    Ya yi amfani da salon jan hankali kamar haka

    “Na yi matuƙar damuwa dangane da ayukan wasu ‘yan siyasa a jihar nan……..

     

    SALON KASAWA

    Ya yi amfani da salon kasawa inda ya ce;

    “Ina matuƙar nuna damuwa ta kasancewar noma shi ne tinƙahonmu, amma babu isasshen taki……

     

    SALON TABBACI

    Ya yi amfani da wannan salo na tabbaci inda ya ce;

    “Za mu maida hankali ganin an dawo da dalibban da suka bar makarantunsu a sanadiyar rashin biya masu kuɗaɗen makaranta……”

     

    SALON BAN TSORO

    Ya yi amfani da salon ban tsoro inda ya ce;

    “Wannan gwamnati ba za ta ɗauki sakaci da almubazziranci da dukiyar jama’a ba”.

     

    Daga ƙarshe, abin da ya gabata a wannan jawabi nazari ne na harshe a jawabin gwamna Abdul-Aziz Yari Abubakar da ya yi na kama aiki a shekarar 2011. Salon sarrafa harshe tare da jawabi ko batu na jan hakali da tausayi ya sa aka fahimci manufar jawabin a mahallin gabatarwa da shi.

     

    4.5 NAZARIN JAWABIN KAMA AIKI NA ZAƁAƁƁEN GWAMNA A 2019,

    JAWABIN GWAMNA BELLO MUHAMMAD MATAWALLEN MARADUN

    Ina godiya ga Allah Subhanahu wata’ala da ya nuna mana wannan rana da na zama gwamnan Zamfara.

     

    Yau rana ce mai cike da tarihi gare ni da jam’iyyata ta PDP wanda ba a taɓa samu ba a tsawon shekara ashirin (20) ana gudanar da mulkin wannan jiha.

     

    Jama’ar Zamfara zaɓe ya ƙare don haka, mu aje duk wani bambancin siyasa mu haɗu mu ciyar da jiharmu gaba. Alhamdulillahi! Yau ni ne Gwamnan Zamfara don haka zan yi aiki da kowa domin gudanar da mulki a wannan jiha insha Allah!

     

    Ina sane da ƙalubalen da jihar nan take fuskanta, jama’ar Zamfara na buƙatar gwamnati da za ta kula da matsalar tsaro da ke addabarsu. Zamu yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin jihar nan. Zamu tabbatar an samu tsaro da kwanciyar hankali a wannan jiha.

     

    Jihar Zamfara ta yi ƙaurin suna a ƙasar nan da duniya wajen ayukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa. Zamu shawo kan matsalolin cikin lokaci da yardar Allah. Don haka, ina kira ga ‘yan bindiga da su miƙa makamansu, su rungumi zaman lafiya. Haka ma ina kira ga ‘yan sa kai da su kauce wa ayyukan da suka saɓawa doka, saboda gwamnati ba za ta lamunci kisan al’ummar da basu ji basu gani ba. Za a yi doka duk wanda aka samu da ta’addnci zai fuskanci hukuncin kisa.

     

    An san jihar Zamfara da noma, abin damuwa ne idan aka yi la’akari da sunan da ta yi a ƙasa da duniya baki ɗaya. Don haka, zamu farfaɗo da noma ta hanyar tallafawa manoma da inganta noman zamani na (ZACAREP). Zamu ba da kulawa ta musamman ga Dam ɗin bakalolri domin haɓaka noman rani don samar da isassen abinci a jiha.

     

    Ilimi gishirin zaman duniya, don haka, za mu bunƙasa ilimi wajen ganin duk yaranmu sun shiga makaranta. Haka ma za mu biya kuɗin jarabawar da tsohuwar gwamnati ta kasa biya, zamu fito da tsarin bayar da ilimi kyauta a faɗin jihar nan, zamu dawo da biyan kuɗaɗen tallafi ga ɗalibanmu (Schoolarship) da ke karatu a manyan makarantun ƙasar nan.

     

    Za mu tallafa wa harkokin kiwon lafiya a karkara da birane. Haka ma ɓangaren ruwan sha za mu tabbatar ana samar a isassun ruwan sha kuma masu tsafta a karkara da birane.

     

    Zamu fito da hanyoyi don samar da gine-gine musamman a babban birnin jihar, mun lura da cewa an barmu baya duk shekarun da aka ɗauka ana gudanar da mulkin dimokaraɗiya a wannan jiha.

     

    Gwamnati za ta gina hanyoyi domin ganin an yi amfani da albarkatun ƙasar da Allah ya hore mana don kakkaɓe talauci da samar da walwala a faɗin jihar nan, tare da kula da ‘yan gudun hijira da suka bar muhallansu sanadiyar rashin tsaro a yankunan su.

     

    Kafin kammala jawabina sai na yi godiya ga jama’ar Zamfara, bisa goyon bayan da kuka bamu har muka samu nasara a jam’iyyarmu ta PDP. Ina godiya ga duk wanda ya ba da gudummuwarsa da goyon baya wajen samun nasararmu.

     

    Daga ƙarshe, ina addu’a ga Allah subhananu Wata’ala da ya bamu damina mai albarka da yabanya mai yawa amin”.

     

    SHARHI

    Manufar wannan jawabi shi ne ƙulla dangantaka tsakanin mai jawabi da mai sauraro, wato gwamna Bello Muhammad Matawalle da kuma al’ummar Jihar Zamfara, tare da gabatar masu da manfofi da shirye-shiryen da aka tanada domin cigabansu da nufin amincewarsu da goyon bayansu zuwa ga Gwmanati.

     

    Wannan Jawabi, Jawabi ne da aka gabatar da shi a filin baje koli da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara a ranar 29, ga watan Mayu, 2019. Bayan karɓar rantsuwar kama aiki da gwamna Bello Muhammad Matawalle” ya yi.

     

    TSARI

    An tsara jawabin ne bisa tsari na gaba ɗaya (zube). Haka kuma jawabi ne aka tsara gaɓa-gaɓa da nufin isar da saƙon gwamnati zuwa ga al’ummar Jihar Zamfara. Don haka, jawabin a tsare yake kowane batu na bin wani. Wato tsarin daki-daki ba wai kara zube ba. Wato an yi shi bisa tsari, mai kyau mai jan hankali da ban tausayi da ma nishaɗi.

     

    SARRAFA HARSHE

    Sarrafa shi ne yadda mai jawabi ya yi amfani da kalmomi da jimloli, wato jerantuwarsu. A wannan jawabin mai girma gwamna ya yi amfani da sauƙaƙan kalmomi da jimloli da salele daban-daban domin sauƙin fahimta ga masu sauraro tare da jan hankali da nishaɗi.

     

    SALO

    Abubuwan da aka nazarta a ƙarƙashin salo wanda kuma daga kansa ne ake yanke hukunci a ce salon jawabin ya ƙayatar. Wannan ya haɗa da nazarin kalmomi da mai jawabi ya yi amfani da su wajen gina jawabinsa da kuma adon magana kamar Karin magana, maganganun hikima da tsarin ginin jimloli a jawabin. Za’a iya duba salele a ƙarƙashin jawabin kamar haka.

     

    SALON BUƊEWA

    Mai jawabin ya yi amfani da salon buɗewa inda ya fara da cewa

    “Ina godiya ga Allah subhanahu wata’ala da ya nuna mana wannan rana da na zama gwamnan Zamfara”

     

    SALON TUNATARWA DA NEMAN HAƊA KAI

    A wannan salon mai jawabin ya yi amfani da tunatarwa da neman haɗa kai inda ya tunatar da al’ummar jihar Zamfara cewa zaɓe ya ƙare inda ya ce:

    “Jama’ar Zamfara zaɓe ya ƙare, don haka, mu aje duk wani bambancin siyasa, mu haɗu mu ciyar da jiharmu gaba”

     

    SALON JAN HANKALI DA SARRAFA HARSHE

    Tsokaci cikin ma’anar sassan jawabin yana da fa’ida don ta haka ne gaskiyar bayanan da suka biyo cikin jawabin za su share fagen fahimtar saƙonnin da ke ƙunshe a jawabin, kasancewar shi ne abin da ya addabe al’ummar jihar Zamfara a wannan lokacin. Saboda haka ne ma ya yi amfani da salon jan hankali da harshe inda yake cewa:

    “Ina sane da ƙalubalen da jahar nan ke fuskanta, jama’ar Zamfara na buƙatar gwamnati da za ta kula da matsalar tsaro da ke addabarsu”

     

    A nan ya jawo hankalin al’ummar Zamfara zuwa ga abin da suke jira ya fito daga bakin gwamnan da matakin da zai ɗauka game da lamarin. Ya ci gaba da cewa:

    Zamu yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin jihar nan. Za mu tabbatar an samu tsaro da kwanciyar hankali a wannan jiha. Jihar Zamfara ta yi ƙaurin suna a ƙasar nan da duniya wajen ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a don neman kuɗaɗen fansa”

     

    Waɗannan batutuwa da suka gabata, suna ɗauke da bayanai na aiwatarwa wato jimloli masu ƙarfafa juna. Da farko an ƙarfafa jumlolin rashin tsaro da ya addabi wannan jiha, tare da rashin kulawar gwamnatin da ta gabata.

     

    Dangane da amfani da salo da sarrafa harshe ana iya ganin ƙarfin amfani da harshe kamar yadda ya biyo a jawabin, inda ya nuna takaici da baƙin ciki na rashin tsaro, sannan ya yi ƙoƙarin dawo da martabar Zamfara ta fannin tsaro da siyasa da kuma tattalin arziki.

     


     

    SALON DAMUWA DA TABBATARWA

    A nan ya yi amfani da salon tabbatarwa inda ya tabbatar wa manoma da ɗaliban ilimi da ɓangaren kiwon lafiya da ruwan sha da ma gine-gine tabbacin walwalarsu da jin daɗinsu inda ya ce:

    “An san jihar Zamfara da noma, abin damuwa ne idan aka yi la’akari da sunan da ta yi a ƙasa da duniya. Don haka, zamu farfaɗo da noma da ilimi da sha’anin samar da ruwan sha da kiwon lafiya da gine-ginen hanyoyi don amfanin al’ummarmu”

    SALON KASAWA

    Mai jawabin ya yi amfani da salon kasawa, inda ya nuna kasawar tsohuwar gwamnati musamman ta fannin ilimi inda ya ce:

    “Za mu biya kuɗin jarabawar da tsohuwar gwamnati ta kasa biya”

     

    SALON GODIYA

    Ya yi amfani da salon godiya a jawabin inda ya ce:

    “Kafin kammala jawabin sai na yi godiya ga jama’ar Zamfara bisa goyon bayan da kuka bamu har muka samu nasara a jam’iyyarmu ta PDP

    SALON RUFEWA

    Ya yi amfani da salon rufewa inda ya ce;

    “Daga ƙarshe, ina godoya ga Allah subhanahu wa’atala…..”

    Idan aka dubi wannan jawabi za a ga cewa, Jawabi ne da aka yi cikin damuwa da baƙin ciki duba da abin da ke faruwa na rashin tsaro a jihar Zafmara.

     

    4.6 KAMMALAWA

    A taƙaice, wannan babi na huɗu, shi ne jigon wannan aikin ko nazari gaba ɗaya, inda ya yi bayani ne kan Gabatarwa da ma’anar salo da siyasa da lafuzzan siyasa da sarrafa harshe da kuma kacokam nazarin jawabin kama aiki na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara daga shekara ta 2007 zuwa 2019, sai kuma kammalawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.