Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zababbun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (4)

     Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (4)

    NA

    NASIRU HASSAN

    Siyasa

    BABI NA UKU

    4.0 GABATARWA

    Taƙaitaccen Tarihin Jihar Zamfara, Jihar Zamfara na cikin jihohin Nijeriya masu amfani da harshen Hausa. Hausawa na cikin manya ƙabilun ƙasar nan; ba shakka irin wannan nazari, yana da matuƙar muhimmanci ga kowace al’umma da ke da burin inganta al’amurranta da tabbatar da kyawawan al’adunta na gargajiya da nufin ɗora jama’arta bisa wani amintaccen tafarki wanda zai shimfiɗu a kan wata halattaciyar aƙida. Muhimman abubuwa dangane da bunƙasar al’umma, sun haɗa da ilimi da sana’a da al’ada da kuma zaman lafiya. Koda yake siyasa na cike da hanyoyi da ce-ce-ku-ce da tarzoma, Zamfara na cikin kwanciyar hankali da lumana.

     

    4.1 TAƘAITACCEN TARIHIN JIHAR ZAMFARA

    Jihar Zamfara ta yi suna tun ana cewa “Bature zaki”. Ma’ana tun tana a matsayin daula. Daular Zamfara daɗaɗɗiya ce, tarihi ya nuna cewa daular Zamfara ta kafu ne tun a ƙarni na goma sha uku (ƙn 13), kuma tana ɗaya daga cikin daulolin ƙasar Hausa tsofaffi (wato waɗanda suka daɗe da kafuwa). Haka tarihi ya nuna cewa daular Zamfara wani yanki ne daga daulolin da suka taru suka haɗa tsohuwar daular Usmaniya a shekarun baya. Jangebe (2015).

     

    Tarihi bai tsaya nan ba, sai da ya bayyana mana cewa, an sami bayani a wajen Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da sauran Malaman tarihi a addini cewa, “Yankin ƙasar da ake kira Zamfara tana ɗaya daga sanannun ƙasashen Bilad  al-Sudan da Musulunci ya yi ƙarfi a ciki”.

     

    Bilad al-Sudan ta haɗa da ƙasar Kano da Daura da Katsina da Zazzau da Barno da Gobir da Zamfara da Kebbi da Yawuri da Nufe da Gulma da Bargu da ƙasar Ilori. Ko da yake tarihi Bayajida ya sa wasu masana suna ɗaukar ƙasashen Zamfara da Kebbi da Yawuri da Nufe da Ilori ƙasashen Banza Bakwai, amma wannan bai hana a ce masu Hausawa ba.

     

    Zamfarawa kamar sauran mutanen daulolin sudan ta tsakiya sun ɗauki kansu Hausawa ne kuma sun fito daga Gabas, suka ratso ƙasar Barno, suka isa mazauninsu na farko a Dutse.

     

    Nadama G. (1977) ya ce, Zamfara haɗi ne da Katsinawa da Gobirawa. Kamar yadda Muhammadu Bello ya ce; Gobirawa su ne uwa, Katsinawa kuwa su ne Uba. A wata ruwaya kuma asalin Zamfarawa daga Gobir suke inda aka samu auratayya tsakanin “Fara” ɗiyar Sarkin Gobirawa suka shiga a Birnin Zamfara a ƙarƙashin riƙon sarkin Babari a lokacin sarkin Zamfara Maroƙi. Gusau (2008), Daular Zamfara ta rayu kafin mulkin Gobirawa, tana da mazaunin mulki inda sarkin Zamfara yake zaune watau Birnin Zamfara.

    Babban Birnin Zamfara ya rushe, saboda ɓulluwa da haɓakar Daular Gobir a ƙarni na goma sha takwas (ƙn. 18) da kuma wargaza al’adu da jama’ar Zamfara suka yi wanda ya ƙarawa al’amarin wahala. Kuma saboda nasarar jihadi a ƙarni na sha tara (ƙn.19) an lalata tare da rushe manyan Garuruwan Zamfara kamar su kiyawa da jata da Banga da wasu ƙananan garuruwa.

     

    A madadinsu kuma aka sami wasu sababbin garuruwa. Daga cikin garuwan da suke ƙarƙashin Zamfara akwai Zurmi da Mafara da Bakura da Maradun da Anka da Gummi da Zoma da Kagara da sauransu.

     

    Zamfara sun daɗe suna neman da a yi musu jiha, amma haka bata samu ba, sai a lokacin mulkin soja na janar Sani Abacha, ɗaya ga watan Oktoba na shekarar 1996, Zamfara ta yau, tana da ƙananan hukumomi goma sha huɗu (14) waɗanda suka haɗa da.

    ·         Anka

    ·         Bakura

    ·         Bukkuyum

    ·         Birnin Magaji

    ·         Bunguɗu

    ·         Gusau

    ·         Gummi

    ·         Ƙaura – Namoda

    ·         Maru

    ·         Maradun

    ·         Shinkafi

    ·         Tsafe

    ·         Talata Mafara

    ·         Zurmi

    A ɗaya ga watan Oktoba ne 1996, a ka ƙirƙiro jihar Zamfara a lokacin mulkin Janar Sani Abacha. Inda gwamnan soja na farko shi ne “Lieutenant Kanal Jibril Bala Yakubu”. Jihar Zamfara ta samu Gwamnan farar hula na farko a shekarar 1999. A ƙarƙashin mulkin Ahmad Sani (Yariman Bakura). Daga nan sai mulkin siyasa ya ci gaba har zuwa yau.

     

    Wani muhimmin abu shi ne kasuwanci, wanda ke bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Duk da cewa kasuwanci na da faɗi, domin ana saye da sayarwa na abubuwa iri – iri. Jihar Zamfara na da matsayi da daraja wanda sana’ar noma ya samar mata. Jihar Zamfara ta shahara wajen noma kayan abinci iri – iri da suka haɗa da shinkafa, Gero, Dawa, Masara da wake da sauransu. Ana kuma noma kayan Lambu kamar Tumatir, Tattasai, Attarugu da albasa da sauransu. Wannan harka ta noma na cikin manyan abubuwa da ke haɓaka tattalin arzikin Zamfara. Jangebe (2015).

    3.1.1 YAWAN JAMA’A

    Yawan Jama’a shi ne adadin yawan jama’a ko al’ummar da ke zaune a wuri, ta haɗuwar jinsuna daban-daban. Jihar Zamfara ƙasa ce wadda Allah ya albarkata da yawan jama’a. Jihar Zamfara dai tana da ƙananan hukumomi guda goma sha huɗu (14) kuma a ƙididdigar da aka yi ta shekarar 2006, hukumar ƙidaya ta ƙasa ta gano yawan jama’ar da ke kowace jiha.

    Jihar Zamfara tana da adadin yawan jama’a kimanin 3,278,873, inda suka ƙunshi maza da mata. Ga jadawali yawan Jama’a a kowace ƙaramar hukuma, inda suka ƙunshi maza da mata.

    S/N

    Ƙaramar hukuma

    Maza

    Mata

    Jimla

    1.       

    Anka

    72,456

    71,181

    143,637

    2.       

    Bakura

    92,369

    95,772

    187,141

    3.       

    Birnin Magaji

    90,824

    93,259

    184,083

    4.       

    Bukkuyum

    108,812

    107,536

    258,048

    5.       

    Bunguɗu

    128,831

    129,813

    258,644

    6.       

    Gummi

    102,682

    104,035

    206,721

    7.       

    Gusau

    198,682

    185,030

    382,712

    8.       

    Ƙaura Namoda

    145,548

    139,815

    285,363

    9.       

    Maradun

    106,403

    101,160

    207,563

    10.   

    Maru

    146,920

    146,221

    263,141

    11.   

    Shinkafi

    66,51

    96,452

    133,964

    12.   

    Talata Mafara

    107,516

    108,134

    215,650

    13.   

    Tsafe

    129,010

    137,919

    266,929

    14.   

    Zurmi

    145,054

    148,923

    293,977

    A jimlace idan an duba za a ga cewa jihar Zamfara tana ɗauke da yawan jama’a kimanin 3,278,873 a wannan ƙidaya.

     

    3.1.2 ALBARKATUN ƘASA

    Allah (SWT) ya albarkaci jihar Zamfara da wata ƙasa ta noma da bishiyoyi ko itatuwa da ma’adinai iri-iri. Zamfara na da manyan gonaki da fadamu da ƙoramu da ke taimakawa wajen noman rani. Ana yin noma iri biyu a Zamfara wato noman damina da na rani.

     

    A noman damina aka fi noma mafi yawan abinci kamar gero, dawa, maiwa, wake, da sauransu. A noman rani kuwa an fi noma kayan marmari. Don haka, noman da Zamfara ke yi, ya ƙunshi na ci da na sayarwa. Kayan marmarin sun haɗa da tumatur, tattasai, tarugu, albasa, barkono da sauransu. Akwai irin su lansir da ayayo da karas da kabeji da dankali da rogo da mankani (Gwaza) da sauransu. Bishiyoyi da ke jihar Zamfara duk masu amfani ne, akwai na ci kamar tsamiya da kanya, ɗoruwa da kaɗanya da faru da sauransu. Akwai kuma waɗanda ake amfani da su wajen yin ababen amfani a gida da magani da sauransu.

     

    3.1.3 SANA’O’I

    Dangane da sana’o’i ko tattalin arziki, jihar Zamfara ta faro ne daga tonon kuza ko haƙarta, wanda idan muka duba kusan duk garuruwan da suka ci gaba da zama birane suna zaune ne a yankin da ake haƙar tama ko kuza. Kuma abu mafi muhimmanci a jihar Zamfara shi ne noma, saboda ta kasance tana da rayayyar ƙasar noma. Saboda tun ƙarni na sha-shidda (ƙn 16) an san da cewa ƙasar Zamfara ƙasa ce ta noma, wadda kusan shi ne ya haɗa ƙasar da sauran makwaftanta.

     

    Jihar Zamfara ta samu ci gaba ta hanyar kasuwancin fatu da ƙiraga da rini da dukanci da kuma sassaƙa. Haka ma tattalin arzikin Zamfara ya haɗa da sana’ar noma da kiwo da ƙira da jima da saƙa da ɗinki da kaɗi da fawa da gini da kitso da ƙwadago da koda da dillanci da dako da sauransu. Don haka, al’ummar Zamfara kowa da sana’ar da ta jibance shi, kamar yadda Hausawa ke cewa “Kowa da bikin da ya karɓe shi, wai makwafcin mai akuya ya sa yi kura”. Mutanen Zamfara suna da sana’o’i daban-daban, wannan ya zama al’ada ta mutum, wato samun abin yi don biyan buƙatar kai. Jangebe (2015).

    3.1.4 YANAYINTA

    Jihar Zamfara ƙasa ce mai ɗauke da yanayi iri biyu, rani (dry season) da kuma damina (rainy seasons). Yanayin jihar Zamfara yana da ɗumi ƙwarai duk tsawon shekara in ban da watan Fabareru zuwa watan biyar da ake sanyin hunturu (harmatan). Damina kan fara daga watan maris/Afrilu zuwa Satumba/ Oktoba har zuwa watan ɗaya na Hausa. Don haka ƙasa ce ta ciyawa mai itatuwa jefi-jefi masu ƙaya da masu faɗin ganyaye daban-daban.

    A jihar Zamfara rani na kamawa daga watan Oktoba ya ƙare watan Mayu. Daga nan sai a samu yanayin ya rabu gida biyu wato hunturu (harmatan) da kuma bazara (hot period).

     

    3.2 MA’ANAR HARSHE

    Masana da yawa sun yi bayani kan harshe da muhimmancinsa da sigoginsa da dangantakarsa ga rayuwar al’umma. Waɗannan masana sun ƙunshi al’ummomi iri-iri, domin wasu daga turai suke, wasu daga Amurka wasu kuma daga Afrika.

     

    Wannan ya nuna cewa harshe al’amari ne na kowa (bil adama). Mutum shi ke amfani da harshe wajen harkokinsa na yau da kullum, domin samun biyan buƙatu na zamantakewa. Don haka, a bayyane yake cewa mutum kaɗai ke iya sarrafa shi (harshe) ta hanyar amfani da kalmomi.

     

    Rabi’u M. Zarruƙ da A. Kafin Hausa da Bello Y. Alhassan (1986). Sun ce, Harshe magana ce wadda ake ji a fahimta. Harshe shi ne abin da ya bambanta ɗan adam da sauran dabbobi. Harshe a wurin ɗan adam linzami ne na tunani. Sauran dabbobi kuma sai dai su yi kuka ko gurnani ko haushi ko haniniya don su nuna fushinsu ko murnarsu ko wuyarsu ko daɗinsu. Mutum ɗai ne ke iya riya abu a zuciyarsa ko ya gani da idanunsa ko ya ji da kunnuwansa, sannan ya faɗa da fatar baki. Duk lamurran rayuwa harshe ne abin kwatantasu da adanasu a ka ko a rubuce da kyautatasu.

    Harshe baiwa ce da ɗaukaka da Allah ya ba ɗan’adam, da shi mutum ke sadarwa da mu’amala. Ba a fahimtar wannan baiwar sai an dubi irin faman da ake yi kafin a fahimci abin da bebe ko jariri ke buƙata.

     

    Harshe shi ne maƙunshin ilimi da tarbiyyar al’umma da hikimominsu ilimi da tarbiyyar al’umma da hikomominsu da abubuwan sonsu da na ƙinsu, duk da harshe ake faɗarsu da adanasu har zuwa ga na baya. Ta haka ne al’umma ke renon ‘ya’yanta bisa kyawawan al’adunta, saboda haka, harshe ne taskar ilimin al’umma da tarihinta.

     

    Skinner (1977), ya ce: Harshe shi ne magana” shi kuwa “Noam Chomsky” kamar yadda Fromkin da Rodman (1976:1) cewa ya yi, harshe shi ne “Mutuncin ɗan’adam wanda ya sa ya yi fice”. Haka kuma a wannan ruwaya, an fassara harhe da cewa babbar alfarma ce ga mutum wadda ta bambanta shi da wasu halittu.

     

    Masana da dama sun yi bayani kan harshe irin su Dyelaran, O.O (1990:22) cewa ya yi harshe muhimmin abu ne wajen bayyana al’adar mutane.

    Bisa waɗannan bayanai na masana da suka gabata a iya cewa harshe wata riga ce ta alfarma wadda ɗan’adam ke sawa domin ta bambanta shi da wasu halittu.

     

    4.3 MA’ANAR SIYASA

    Masana irin su Bargery (1984) da Yakasai (2012) da ƙamusun Hausa (2006) da sauransu sun bayyana ma’anar siyasa kamar haka.

     

    Bargery (1934) cewa ya yi siyasa na nufin rangwame ko farashin kowane abu ko kuma tausayawa a cikin al’amura. Yakasai S.A (2012) kowace rayuwa tafe take da abin da ke yi mata jagora domin samun nasarar gudanar da al’amuranta na yau da kullum. Wannan jagoranci shi ake kira shugabanci. Wannan shugabanci ya fara tun daga maƙamin Sarauta ta gargajiya har zuwa shugabancin ƙananan hukumomi da jahohi da kuma ƙasa baki ɗaya. Ƙamusun Hausa (2006), siyasa ita ce tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwarinsu.

     

    Idan aka ce siyasa to akwai ɓukatar a san mene ne siyasa? Wannan kalma ce ta Larabci wace a halin yanzu an mayar da ita Hausa. Wadda kuma ke nufin sauƙi ko rangwame ko jinƙai. A da can, idan aka cewa mutum ɗan siyasa to ana nufin mutum mai jinƙai, mai rangwame, mai nasiha, watau mutum mai kyautata wa al’umma. A Hausance siyasa tana nufin wani tsari na jawo ra’ayin mutane da su haɗa ƙarfi wuri ɗaya su zaɓi wasu ko wani mutum don ya shugabancesu bisa ga tsarin dokokin ƙasa. Siyasa wata dabara ce ta neman mutane su zama masu ra’ayi ɗaya domin su zaɓi wakilinsu ga shugabancin ƙasa ko jiha ko ƙaramar hukuma.

     

    4.4 YAƊA LABARUM SIYASA

    Dangane da yaɗa labarai, a jihar Zamfara, an fi tallata duk siyasar da ke kan karagar mulki, wato ta gwamnati domin a daɗaɗawa Gwamna. Dalili shi ne, ma’aikatan gidan redoiyo da Talabijin da Jarida, suna ganin kamar wannan gwamnati suke yi wa aiki ba jama’a ba, ganin cewa gwamna ke naɗa shugabannin waɗannan kafafe. Wannan ne ya sa sai abin da gwamnati ke ra’ayi suke yaɗawa, musamman a nan jihar Zamfara.

     

    Alal misali gidan rediyon Zamfara wanda ake faman tallata Gwamna da manufofinsa da waƙoƙinsa tare da barin na ‘yan adawa. Haka abin yake a gidan Jaridar “The Legacy” (Legacy, 2011).

     

    Wannan jarida mallakar jihar Zamfara ce, wanda duk abin da ke faruwa a Zamfara “radiyo” na siyasa, irin sa ne ke faruwa a gidan jaridar “The Legacy”.

     

    4.5 KAFUWAR JAM’IYUN SIYASA

    Siyasa a Nijeriya ta kafu ne bisa hanyoyi guda uku (i) Siyasar gargajiya ta (ii) Siyasar Musulunci ta (iii) Siyasar dimukraɗiyya. Siyasar gargajiya ita ce, ta sarauta, watau ta gado, wadda yan gidan sarauta ne kawai ke da damar neman muƙami. Siyasar musulunci kuwa na aiki da Al’ƙur’ani mai girma da Hadisai na Manzon Tsira Muhammad (SAW).

     

    Rukuni na uku shi ne siyasar dimokuraɗiyya, wannan ita ce siyasar zamani, wannan siyasa ta ra’ayi ko ta zamani ta kasu kashi da dama kamar haka; (Jangebe: 2015).

     

    Akan yi ta don kishin al’umma ko kishin jam’iyyu ko aƙida ko siyasar ƙasa ko ta ƙabila. Siyasar dimokuraɗiyya ce ta fi fice a yau, kuma tana amfani da jam’iyyu. Irin wannan siyasa ta fara kankama a Nijeriya tun lokacin da ‘yan kishin ƙasa suka farga da irin zalunci da danniya da Turawa ke gudanarwa a ƙasarsu. Wannan shi ya fara kawo siyasar gwagwarmayar neman ‘yanci. Mashi (1986) ya ce; a shekarar (1920) aka kafa kungiyar ƙasashen Afrika renon Ingila (National Congress of British West Africa (NCBWA).

     

    Daga wannan lokaci ne al’amurran siyasa suka fara kankama har zuwa lokacin da aka ba da mulkin kai da zaɓaɓɓun wakilai bisa jam’iyyu a 1960). Haka aka ta yin gwagwarmayar kafa jam’iyyu da siyasa har zuwa lokacin Janar Sani Abacha da ya yi yunƙurin mayar da ƙasar nan kan turbar siyasa, inda ya nemi ‘yan siyasa da su kafa jam’iyyun siyasa inda gwamnati ta yi wa jam’iyyu guda biyar rigsta a watan Satumba 1996. Daga cikinsu akwai NCPN da UNCP da DPN da GDM da kuma NCNC, sai dai kafin a gudanar da zaɓe Allah ya yi wa Janar Sani Abacha rasuwa 8, ga Yuni, 1998. Wannan ya kawo rushewar jam’iyyun da shirin mai da mulki hannun farar hula. Bayan wannan janar Abdussalami shi ne ya gadi Abacha inda shi ma ya yi alƙawarin miƙa wa farar hula mulki. Abdussalami ya buƙaci a sake gabatar da kundin tsarin mulki na ƙasa da zai halattar da miƙa wa farar hula mulki cikin nasara. Kundin tsarin mulkin na 1998, wanda ya fara aiki a 1999 ya samu karɓuwa a ƙasar nan. Dagan an aka buƙaci ‘yan Nijeriya da su ƙirƙiro jam’iyyun siyasa da suke so. An ƙirƙiro jam’iyyu da dama waɗanda suka haɗa da jam’iyyar AD, da APP da PDP inda hukumar zaɓe ta sanar da yi wa waɗannan jam’iyyu uku rigista. Inda Jam’iyyar PDP ta kafa Gwamnati a matakin ƙasa wato “Chief Olesugun Obasanjo” ya lashe zaɓe. A Jihar Zamfara kuma Jam’iyyar APP ce ta kafa Gwamnati inda Alhaji Ahmad Sani (Yariman Bakura ya lashe zaɓe. An rantsar da sabuwar Gwamnati a ƙasa da Jihar Zafmara ranar 29, ga Mayu, 1999.

     

    4.6 LAFAZIN SIYASA DA MANUFARTA A SIYASANCE

    Lafazi ko magana shi ne wani furuci da ɗan’adam zai furta da bakinsa a bisa wata manufa. Wanda idan maganar ta fito shi ke nan ba ta komawa, Waɗannan maganganu manufarsu daban ne a siyasance. Wasu na ɗaukar maganganun siyasa a matsayin ƙarya ko yaudara. Saƙonnin siyasa a magance ko a rubuce na ɗaukar hankalin jama’a, domin siyasa ke tafi da ƙasa. ‘Yan siyasa suna maganganu a wajen yaƙin neman zaɓe suna kuma rubutawa a fastoci da laƙawa kan allunan kamfen. Amma abin dake rubuce ba shi ne ke jagorantar abin ba a siyasa wani abin ya zama aiki ba cikawa. Kamata ya yi a ce manufasto na siyasa shi ne ke jagorantar ‘yan siyasa sai za a yi zaɓe sannan ake faɗin za’a yi ayyuka kaza, amma da zarar an gama zaɓe shi ke nan kaji shiru kamar an shuka dusa. Irin waɗannan lafuzza ne za a ji ‘yan siyasa suna faɗa, (Jangebe, 2015).

     

    Maganganu suna fitowa, uwayenmu da babanninmu, za mu baku takin zamani, mu samar maku da ruwan sha, da hanyoyi, da ɗakunan shan magani. Idan kuka zaɓe mu za mu gina maku asibitoci masu gadaje hamsin hamsin. Ina manoma za mu samar maku da bashin shanun noma, da iraruwan shuka da galmunan shanu da takin zamani, domin inganta noma a wannan yanki da kuma jiha baki ɗaya.

     

    Waɗannan kaɗan ne daga cikin lafuzza ko maganganun da ake yi a siyasance, domin samun nasarar jawo hankalin masu zaɓe da su jefawa ɗan takara ƙuri’a domin ya ci zaɓe saboda gudanar da mulkinsa na dimokuraɗiyya. Daga cikin waɗannan lafuzzan suna cika wasu, wasu kuma yaudara ce.

     

    4.7 KAMMALAWA

    A wannan babi na uku, an yi magana a kan taƙaitaccen tarihin jihar Zamfara, yawan jama’a, albarkatun ƙasa, sana’o’i, yanayinta, ma’anar harshe, ma’anar siyasa, yaɗa labarum siyasa, kafuwar jam’iyyun siyasa da lafuzzan siyasa da manufarta a siyasance duk a cikin wannan babi na uku.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.