Ticker

6/recent/ticker-posts

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (5)

NA

HIZBULLAHI ƊANLAMI

 

birkila

BABI NA HUƊU:

TASIRIN SANA’AR GINI GA BUNƘASA ARZIƘIN KWATARKWASHI

4.0 Gabatarwa

            Wannan babi zai tattauna ne akan tasirin sana’ar gini ga Bunƙasa arziƙin kwatarkwashi, wanda a ƙarƙashinsa za a yi bayanin ci gaban da aka samu ta ɓangaren samar da aikin yi ga matasa, da bunƙasar kiyo da Noma da kuma saye da sayarwa (kasuwanci) a garin kwatarkwashi.

            A gargajiyance akwai hanyoyi da yawa da Bahaushe ke bi don haɓaka ko kawo ci gaban arziƙinsa. Waɗanda suka haɗa da sana’o’i tare da yanayin tsarin zamantakewarsa. Idan aka dubi wannan sai a ga cewa wasu muhimman hanyoyi ne da Bahushe ke bi don bunƙasa hanyoyin arziƙi.

            Sana’o’in gargajiyar Hausawa su ne mafi yawa da bunƙasa arziƙi da Bahaushe ke bi ya samar wa kansa abubuwan da yake buƙata don gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum.

            A bisa haka ne, sana’ar gini da magini (Birkila) ta taimaka ƙwarai da gaske a yankin garin kwatarkwashi a bisa ga tasirinta wajen bunƙasa arziƙi. Sana’ar ta yi ƙoƙari ainun wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi ta hanyoyi kamar haka: -

 

 

4.1 Samar da Aikin yi ga Matasa

            Haƙiƙa, sana’ar  gini da magini (Birkila) ta ba da gudunmuwa ta musamman wajen wanzar da ayyuka mabambanta, a dai dai lokacin da ake fama da rashin ayyukan yi, musamman ga matasan da suka kammala karatu a makarantun gaba da firamare (Primary), waɗanda ba su sami wucewa ba zuwa manyan makarantun gaba da sakandare. Sabod rage raɗaɗi na zugin talauci da kuma zaman kashe wando a cikin gari.

            Sana’ar gini da magini (Birkila) a garin kwatarkwashi ba ta tsaya a nan ba, har ma da waɗanda suka kammala karatun N.C.E, a cewar Musa Ɗanbarno Sankalawa inda ya ba ni misali da ɗansa. Kuma ya tabbatar mini da cewa matasan da ya koya wa aikin gini a ƙasar kotorkoshi da ma wajenta kamar irin su Damɓa da Gusau, to bai san adadinsu ba.

            Har ila yau, sana’ar gini da magini (Birkila) a garin kwatarkwashi ba ta tsaya a kan waɗancan matasan ba a’a, har ma da marasa ilmin zamani duk sana’ar ta janyo su a jiki domin samar da aikin yi ga matasan domin rage zaman banza da bangar siyasa da shaye-shaye da sata da fizge da fyaɗe da kuma faɗa wa wasu ƙungiyoyin ta’addanci da sauransu.

            Tabbas, bayanai sun nuna cewa a halinm da  ake ciki a garin kwatarkwashi da wuya a sami wata sana’a ta gargajiya ko ma ta zamani da ta kwashi kason jama’a mai yawa kamar sana’ar gini da magini (Birkila). Saboda sana’ar ba ta buƙatar fidda wasu kuɗi masu  yawa wajen yinta, ba kamar irin sauran sana’o’in ba.

4.2 Bunƙasa Kiyo a Garin Kwatarkwashi

            Kiyo/kiwo: sana’a ce ta sayen dabbobi  domin a kula  da abincinsu, lafiyarsu, a kuma ririta su domin samun naman ci da kuma biyan buƙatun rayuwa.

Sana’ar kiwo/kiyo daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, kusan sana’ar ta na kafaɗa da kafaɗa da tsohuwar sana’ar nan ta gargajiya wato Fawa (hwawa) ko ma ta ɗan girme mata.

            Kasancewar ƙasar kwatarkwashi shimfiɗaɗɗiya ga kuma sarari da ciyayi a ko’ina ya sa kusan kowane gida ana kiwon dabbobi ko tsuntsaye. Mutanen  kwatarkwashi na tsare dabbobi da tsuntsaye a gidajensu ta hanyar ba su abinci ko kuma a kora su  zuwa daji don su sami abinci a can. Ire-iren  dabbobin da mutanen kwatarkwashi suke kiyo/kiwo sun haɗa da shanu, da  Tumaki da Awaki don cin namansu da kuma sayarwa. To haka su ma maginan (Birkilan) ƙasar kwatarkwashi ba a bar su a baya ba, duk suna yin wannan sana’a domin bunƙasa arziƙin garin ko yankin na kwatarkwashi.

            Sannan kuma, ana sayar da fatunsu da ƙiragansu don yin amfani da su. Ana kuma ɗaukar kashin da suka yi don kai wa gona a matsayin takin da zai ƙara wa gona albarkar  ƙasa.

            Bayan dabbobi, mutanen ƙasar kwatarkwashi suna kiwon tsuntsaye irin su kaji da agwagi da zabbi don cin namansu da ƙwaya-ƙwayinsu da kuma sayarwa. Maginan (Birkilan) ma suna a sahun gaba wajen kiwon ire-iren wɗannan  tsuntsayen domin bunƙasar arziƙin garin na kwatarkwashi ta hanyar kuɗaɗen da suke samu daga tasu sana’ar.

4.3 BUNƘASA NOMA A GARIN KWATARKWASHI

            Noma hanya ce ta amfani da ƙarfe domin a zafafa ƙasa a gino ko tono amfaninta ta hanyar shuke-shuke tare da amfani da ruwa domin a sami tsiro na ci  da na tsotsawa da kuma wanda za a sarrafa zuwa kayan tufafi ko kayan ado.

            Noma wata daɗaɗɗiyar sana’a ce ko safara wadda Bahaushe ya fara yi a doron ƙasa. Ana amfani da dabbobi ko ƙarfi wajen aiwatar da ita wannan sana’a.

            Noma sana’a ce wadda Bahaushe yake bugun gaba da ita, tun daga kaka da kakanni. Domin kuwa babu gidan  Bahaushe da ba a noma. A ƙasar Hausa a kan fahimci mutum mai arziƙi ne idan yana da ‘ya ‘ya  da yawa, masu taimaka masa ga yin noma a gonaki (wannan bisa ga al’ada ke nan) (Gusau, G.U.  2014).

            Hausawa kan ce “Noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Wannan kirari yana bayyana sana’ar Noma daɗaɗɗiya ce a wannan duniya ba wai ga Hausawa ba. Wannan ya sa idan ana maganar bunƙasar tattalin arziƙin al’ummar garin kwatarkwashi to noma ne za a fara kawowa  don kuwa shi ne ƙashin bayan bunƙasar tattalin arziƙin wannan gari (kwatarkwashi). Inda sana’ar gini da magini (Birkila) ta yi tasiri sosai wajen haɓaka da bunƙasar noma a garin (kwatarkwashi). Wannan ya faru ne saboda sana’a ce wadda kowa da kowa yake yi talaka da saraki, attajiri da matalauci, maza da mata, babba da yaro, don a sami abin da za a ci da kuma wanda za a sayar don yin hidimomin yau da kullum. Tasirin da birkilanci ya yi ga noma shi ne idan matasa suka sami kuɗi wajen gini sai su je su ƙara faɗaɗa noma da waɗannan kuɗi da suka samu ga aikin gini. Ta haka har noma ya bunƙasa a Kwatarkwashi kowa ya sami abinci da abin sayarwa/  sana’a.

            Al’ummar garin kwatarkwashi na yin noma iri biyu na ci da na sayarwa. Kayan  noma na abin  ci sun haɗa da gero da dawa da masara da shinkafa da sauransu, na sayarwa kuma sun haɗa da auduga, da gyaɗa da waken suya da sauransu. Haka, a ɓangaren magina (Birkila) sana’ar  gini ta yi tasiri sosai, wajen noma ire-iren waɗannan amfanin gona domin bunƙasa arziƙi mai ɗorewa a garin kwatarkwashi.

4.4 BUNƘASA SAYE-DA-SAYARWA A GARIN KWATARKWASHI

            Saye-da-sayarwa: wata hanyar hulɗa ce, ta kasuwanci tsakanin jama’a.

            Saye-da-sayarwa (Kasuwanci) yana ɗaya daga cikin muhimman sana’o’in garin kwatarkwashi, domin ta hanyarsa ne kusan dukkan sauran kayayyakin buƙatar rayuwar ɗan Adam suke shiga hannun jama’a.

            Tun kafin wannan zamani al’ummar Hausawa suna da irin nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci su. Wannan tsari ana iya dubansa ta fuska biyu; kasuwancin cikin gida da kuma na waje. A cikin gida akwai kasuwanni na garuruwa waɗanda ake  tafiyar da harkokin kasuwanci ana musayar abubuwan sayarwa ne, misali Manomi ya ba masaƙi kayan gona don ya amshi kayan saƙa, ko ya ba makiyayi don ya amshi wata dabba da sauransu. An daɗe ana yin irin wannan tsari na cinikayya a ƙasar Hausa har zuwa ƙarni na goma sha takwas da aka shigo da kuɗin wuri da biringizau don yin saye da sayarwa a  duk faɗi n Afrika ta yamma (Nadama, 1977: 137-138 cikin Sallau, 2017).

            Babu shakka wannan nau’in kasuwanci na cikin gida na saye da sayarwa, al’ummar garin kwatarkwashi suna gudanar da shi, wanda hakan ya sa  sana’ar gini da magini (Birkila) ta yi tasiri matuƙa wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi.

            Sannan kuma, hanyoyin kasuwanci suna da yawa a wajen mutanen garin kwatarkwashi, yawancinsu na saye da sayarwa ne. Kowane abin sayarwa yana da  tasa hanyar da ake bi a sayar da shi. Sai dai kasuwancin yana da wani mataki ɗaya, wannan kuwa shi ne jari da mai sana’a yake  son ya mallaka kafin  ya fara kasuwanci, saboda haka  ta hanyar gini matasa sun sami jarin yin  kasuwanci ta wannan hanya.   

            A cewar Gusau, G.U. (2012) “Jari wasu kuɗi ne da mai niyar yin kasuwanci ko sana’a ke tarawa, domin gudanar  da kasuwancinsa ta yadda zai ɗore ta hanyar jujjuya shi”.

            Haƙiƙa, sana’ar gini ta yi tasiri sosai ga magini (Birkila) ta hnayar samun jari na gudanar da kasuwanci irin na saye da sayarwa domin ƙara bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi.

4.5 NAƊEWA

            Wannan babi ya tattauna ne game  da  tasirin sana’ar gini ga bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi, wanda a ƙarƙashinsa aka fara bayyana gabatarwa, aka  shiga cikin bayanin muhimman abubuwan da suka yi tasiri wajen bunƙasa arziƙin garin kwatarkwashi, kamar irin su: samar da aikin yi ga matasa da bunƙasa kiyo da noma da kuma bunƙasa saye da sayarwa duk a garin  kwatarkwashi. 

Post a Comment

0 Comments