Sarkanci sana’a ce ta kambaɗar kifi da wasu halittu na cikin ruwa. Yawan shiga ruwa da tu’ammali da shi abu ne mai wuyar gaske musamman idan aka yi la’akari da irin haɗurran da ke tattare da haka kama daga sanyi da zai iya kama mutum da sauran cututtuka da ake iya ɗauka a ruwa kamar ƙaiƙayin jiki, haɗarin gamo da iskoki don kuwa ruwa babban muhalli ne da iskoki ke tattaruwa. Dalilin sabo da shiga ruwa yau da kullum, Sarkawa sun shahara kuma sun ƙware ƙwarai da gaske wajen bayar da maganin ciwon sanyi. Ciwon sanyi kuwa nau’i biyu ne. Akwai sanyin fadama da kuma sanyin mata, wanda shi ma ya kasu zuwa farin sanyi da jan sanyi. Alamomin kamuwa da ciwon sanyi sun haɗa da zazzaɓi mai tsanani da bushewar leɓɓa da kumburin jiki da ƙaiƙayi a matsamatsi. Sanyin mata kuwa kan haddasa jin matsanancin zafi a al’aura yayin da ake yin fitsari. Wannan muƙala wani yunƙuri ne na nazarin yadda sarkawa ke kallon ciwon sanyi da kuma irin maganin da suke bayarwa domin samun waraka daga cutar. Magungunan sanyi da Sarkawa kan bayar sun haɗa sayyu da saƙe-saƙe da ma ganyaye na itatuwa daban.
Naƙalin Ciwon Sanyi A
Mahangar Sarkawa
DR. MUSA
FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983
1.0 Gabatarwa
A sha’anin kiwon
lafiya irin na gargajiya a al’ummar Hausawa, masu aiwatar da sana’o’in
gargajiya musamman waɗanda suka ƙware a kan sana’ar,
galibi waɗanda suka gadi
sana’ar daga kaka da kakanni[1]
suna daga cikin rukunan masana maganin gargajiya.[2]
Sana’ar Sarkanci tana ɗaya daga cikin manyan
sana’o’in gargajiya a ƙasar Hausa musamman a yankunan da ke da
wadatar ruwa na koguna da gulabe da tafukka da ƙoramu da ma duk wani
ruwa inda kifi ke
iya rayuwa.
Sana’ar Sarkanci ta
jiɓinci shiga ruwa domin
kambaɗar kifi da wasu
halittu na ruwa kamar kada da ayu da dorina, waɗanda ake kamawa domin a ci ko a sayar
a sami kuɗin biyan buƙatun rayuwar
yau da kullum, da kuma sarrafawa wajen yin magani na gargajiya.[3] Yawaita shiga
ruwa yau da kullum abu ne mai wuyar gaske domin
akwai haɗarin kamuwa da wasu
cututuka musamman sanyi. Dalilin sabo da shiga ruwa da kuma irin barazanar da
cutar sanyi kan yi ga lafiyar Sarkawa da Masunta, Sarkawa sun shahara matuƙa wajen bayar da tasu
gudunmuwa ga sha’anin kiwon lafiya irin na gargajiya a cikin al’ummar Hauswa.
Sarkawa sun bambanta da masunta. Sarkawa ƙwararri ne ga sha’anin ruwa saboda ‘yan gado ne. Ba
su da wata sana’a da ta shige kamun kifi, rani wa damina. Masunta kuwa ba ƙwararri ba ne kuma ba
koyaushe suke aiwatar da sana’ar kamun kifi ba. Hasali ma,
galibinsu haye suka yi wa sana’ar. Ƙwarewar Sarkawa ga sha’anin ruwa ne ya ba su damar sanin magunguna. Don haka suke bayar da magungunan sanyi da
na cututukan daban-daban da aka iya ɗauka a ruwa. Ire-iren cututukan sun
haɗa da ciwon tsagiya
da cututukan
fatar jiki da cire ƙayar kifi a wuya, idan ta maƙale. Cizon
kifi ko sukar ƙayar kifi, da farfaɗo da mutumin da ya galabaita sakamakon nutsewa cikin
ruwa, na daga cikin ayyukan Sarkawa na kula da lafiyar al’umma.
Wannan muƙala wani yunƙuri ne na nazarin
ciwon sanyi a mahangar Sarkawa. An yi ƙudurin kawo yadda
Sarkawan ke kallon cutar wato nau’ukan cutar, abubuwan da ke haddasa ta,
alamomin kamuwa da cutar, illar da cutar ke yi wa jikin mutum da kuma
magungunan da ake sha domin samun waraka daga cutar.
Kafin a duƙufa wajen kawo
bayanan da muƙalar ta ƙunsa, ya dace a yi waiwaye dangane
ma’anar kalmomin cuta da magani a mahangar masana domin yin haka zai ba da
haske a kan aikin Sarkawa game da kiwon lafiya na gargajiya kamar yadda ya
shafi cutar sanyi da maganinta.
1.1 Wane ne Basarke?
Bisa asali, kalmar Basarke an samo ta daga kalmar ‘Sarkanci’. Asalin kalmar kuwa ba
Bahaushiya ba ce. Tushen kalmar daga ‘Sorko’ ne, wata al’umma ta daular Sanwai
(Songhai). Al’ummar Sorko mutane ne da suka shahara matuƙa ga sha’anin su a kogin Kwara
wanda ya ratso ƙasashe da dama na yammacin Afirka. Sana’ar su ce ta kawo wannan al’umma
ta Sorko a daular Kabi. Sannu a hankali suka saje da al’ummar da suka tarar a
Kabi.[4]
Domin Hausantar da wannan kalma ta
“Sorko” an yi mata kwaskwarima ta hanyar cire wasalin /o/ a gaɓar farko aka musanya shi da wasalin /a/, wata ƙila domin a sami sauƙin furuci. Haka ma an yi mata ƙarin ɗafa goshi na ‘ba’ ta yadda za a sami sunan wanda ya
fito daga wannan al’umma ta ‘Sorko’, kafin daga baya ma’anar ta sauya zuwa ga
duk wani mai gudanar da sana’ar. An kuma cire wasalin /o/ na ƙarshe, aka musanya shi da
wasalin /e/, aka sami ‘Basarke’. Dangane da sunan sana’ar kuwa, tushen kalmar nenta ‘sark’ aka yi wa ƙarin ɗafa ƙeya na ‘anci’ aka
sami kalmar ‘Sarkanci’.
Bisa ma’ana, masana sun tofa
albarkacin bakinsu dangane da abin da suke ganin ake kira Basarke. Bargery
(1934:92) a ƙamusunsa ya bayyana wanda ake kira Basarke. A cewarsa,
Basarke shi ne masunci ko mai
fito da kwalekwale[5]
Wani sashe na wannan zance na Bargery yana da rauni domin aikin jirgi
(kwalekwale) domin fito[6]
da su ba shi ke sa mutum ya zama ‘Basarke’ ba duk da cewa akasarin Sarkawa suna
amfani da jiragen ruwa a wajen aiwatar da sana’arsu. Basarke ba shi ne mai fito
ba. Ma’anar tana da naƙasu domin kuwa aikin Basarke bai tsaya ga su ba kawai. Bayan kamun kifi, Basarke na kuma ba da
magani na Iskokin ruwa da cizo ko sukar wata dabba ta ruwa da sauran cututukan
ruwa. Ba wannan kaɗai ba, Basarke shi ne wanda ya
gadi Sarkanci ya kuma ba da muhimmanci ga sana’ar fiye da kowace, rani da
damina. Tare da haka, ga kuma zancen ƙwarewa kan sana’ar.
Alkali, (1969) ya bayyana abin
yake gani ake kira Sarkanci a inda yake cewa,
Tun ƙarni na goma sha
tara kalmar Sarkanci ta ɗauki ma’anar ƙwarewa
kan sana’ar
su, don haka duk Bakaben da ke yin wannan sana’a ake
kiransa
‘Basarke’
Wannan ma’ana da Alkali ya kawo ta yi daidai don
kuwa ba kowane masunci ne ake kira Basarke ba. Basarke masunci ne ƙwararre, wanda ba ya da wata
sana’a da ta shige su, rani da damina. Irin wannan masunci ne za a tarar yana
iya sarrafa ruwa da ma halittun da ke cikinsa ta duk yadda yake so. Ta fuskar
ba da magani kuwa, Basarke ba kanwar lasa ba ne kuma ƙwararre ne, masani ga sha’anin
ruwa. Yana iya hana shan ruwa, ko ya sa ruwa ya kasa dafa kifi, wato kifi ya
kasa dafuwa. Yana iya sa ƙayar kifi ta laƙe wa wani idan aka takale shi. Yana kuma iya hana a kama kifi a wani ruwa
idan aka ɓata masa rai. Basarke masanin
asirai ne na ruwa matuƙa.
1.2 Ma’anar Naƙali
A asali, kalmar an aro ta ne daga Larabci. A Larabci, ‘an naƙal’ na nufin tushe
ko salsalar wani zance. Misali, wane ya ji daga wane, shi kuma ya ji daga wane,
har a kai ga salsalar farkon inda zancen ya sami asali. Haka tana ɗaukar ma’anar cusa ko natata wani kalami ga wani (misali
yawaita yin kalmar Shahada ga majinyaci har sai ya kama, shi ma ya faɗa) har sai ya faɗi kalamin.[7]
A Hausa kuwa, Bargery, (1934:812) da Abraham, (1975:696) cewa suka yi naƙali na nufin bayani
dangane da yadda ake amfani da magani. A CNHN (2006:299) kuwa, cewa aka yi naƙali ko laƙani na nufin asiri da
ake bayarwa na yin wani magani, ko bayanin yadda za a bi a yi wani magani. Haka
kuma kalmar tana iya ɗaukar ma’anar magani. Ta la’akari da abin da masana suka faɗa, ana iya cewa kamar naƙali na nufin ko dai bayani game da
yadda ake amfani da magani, ko ma magani kacokam.
1.3 Ma’anar Cuta
Wasu na kallon cuta a matsayin kalmar da
ke nufin rashin lafiya ko ciwo.[8] Wannan
ma’ana ta shafi rashin lafiyar jiki ne kawai to amma ita cuta ba ga lafiyar
jiki kurum ta tsaya ba. Wannan ne ya sa Bunza, (1989:132) ya kawo bakandamiyar
ma’ana ta kalmar cuta. Masanin ya ce cuta wata damuwa ce da ta shiga jikin ɗan’adam don raunana
lafiyarsa ko kuma ta shafi zuciyarsa ta fuskar buƙatocinsa na jin daɗi ko ɗaukaka darajarsa da
sunansa.[9]
Idan an lura da kyau
za a ga cewa kalmar cuta kamar yadda masana suka faɗa ta shafi damuwa
wadda kan kawo cikas ga lafiyar ɗan’adam da kuma damuwa irin wadda ke tauye
walwalar mutum domin rashin biyan wasu buƙatunsa ko rashin ɗaukaka na darajarsa
da ƙimarsa.
Wato dai cuta ba wai lafiyar mutum kawai take shafuwa ba, ta shafi zuciyarsa
musamman idan wasu buƙatocinsa na rayuwa ko wani buri nasa ya kasa biya.
1.2 Ma’anar Magani.
A cewar masana, kamar Hamza, (1977:7), da Bunza, (1989:135), da
kuma Bunza, (1995:82) asali ko tushen kalmar magani hatsin bara ce daga wasu
kalmomi na ma- yi- ma- gani, wato za a jarraba a gani ko a dace, a sami biyan
buƙata. Sannu
a hankali, yau da gobe ta yi halinta har aka sassaƙe
kalmomin na wannan zance suka koma magani.
Dangane da ma’anar kalmar
magani kuwa, mutane da dama sun rubuta ra’ayoyi game da abin da suke ganin ake
nufi da magani. Waɗannan
ra’ayoyi na nan ƙunshe a cikin ayyukan Bunza, (1989:132-134), da kuma (1995:83-85). Don haka
nake ganin ba sai an sake maimaita su ba a nan. Duk da haka, bakandamiyar
ma’ana ta kalmar magani da Bunza, (1989)[10]
da kuma (1995)[11]
ya kawo, ya dace a kawo ta a wannan aiki. Masanin ya kalli ma’anar magani da
cewa:
“Magani wata hanya ce ta
warkarwa ko kwantar da, ko rage wata cuta
ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu daga haɗari; ko kuma neman
kariya ga cutar abokan hamayya ko cutar da su
ko neman ɗaukaka
ta daraja ko ta buwaya, ta hanyar siddabaru da
sihiri na ban al’ajabi.”
Wannan ma’ana da masanin ya kawo, a bisa haƙiƙanin gaskiya
ta dace kuma ta zaunu musamman idan aka yi la’akari da cewa ta taɓo muhimman abubuwan da suka shafi
magani. Duk da haka na fahinci cewa masanin bai kawo zancen magani da ake yi
don neman sa’a a sha’anin sana’o’i ba, wato ina magana ne dangane da tsaraka.
Masanin wataƙila da gangan ya yi haka domin kauce wa tsawaita ma’anar, kuma ai
ina ganin lamarin tsaraka zai iya shiga cikin ɗaukaka daraja a fakaice, domin idan sa’a ta samu, daraja na iya ɗaukaka.
A fahimtata, magani na nufin:
Duk wata dabara ta neman kariya
ko waraka daga cuta kowace iri, da kuma wani
wani lokaci cutar da wasu, da neman biyan wasu
buƙatu na
rayuwa kamar sihiri
neman sa’a, da ɗaukaka wanda wani lokaci sai an haɗa da sihiri ko Tsafi domin
sihiri ko Tsafi domin haƙa ta cimma ruwa.
2.0 Ma’anar Ciwon Sanyi
Sanyi wata damuwa ce da ke raunana lafiyar jikin mutum,
sakamakon ciwon da ake iya ɗauka ko kamuwa da shi domin yawaita shiga ruwa ko yin sammako a
jeji lokacin damina musamman a lokacin da ake samun raɓa sosai ko yawan tu’ammali da abu mai
sanyi. Haka ma ana ɗaukar
ciwon sanyi sakamakon saduwa ta fuskar jima’i da mace ko namijin da ya harbu da
cutar. Cutar sanyi idan ta daɗe a jikin mai fama da ita, takan shafi hanyar mafitsara da ƙoda, ta
raunana su yadda ba su iya aiki yadda ya kamata.
2.1 Ire-Iren Sanyi
A mahangar Sarkawa, ciwon sanyi nau’i biyu ne kuma sun kasa shi ne
ta hanyar la’akari da abin da ke haddasa cutar. Nau’ukan ciwon sanyin kuwa
su ne sanyin fadama da kuma sanyin mata. Nau’i na biyu wato sanyin mata ya kasu
gida biyu, farin sanyi da kuma jan sanyi. Wannan rabe-raben sanyi ya kasance
kamar haka:
Farin Sanyi Jan sanyi
2.1.1 Sanyin Fadama
Sanyi ne da ake
kamuwa da shi sakamakon yawaita shiga ruwa na gulbi ko tafki ko ƙorama ko dai duk wani
ruwa da ke
kwance ko mai gudu.
Haka kuma yawan zama a fadama musamman safiya da kuma yamma yakan sa a
kamu da cutar
sanyi. Haka kuma yawan sammako a gona lokacin da ake raɓa ga
damina,
musamman wajajen watan Agusta zuwa Satumba,
kan sa a kamu da ciwon sanyi. Galibin mutanen da wannan cuta ta fi addaba su ne
Sarkawa da masunta da kuma masu noman lambu a cikin fadama.
2.1.2 Sanyin Mata
Cuta ce da mutum ka
iya kamuwa da ita sakamakon saduwa ta fuskar jima’i da wanda ko wadda ta harbu
da ƙwayar
cutar
sanyi. Wannan nau’i na cuta ya kasu gida biyu. Akwai farin sanyi da kuma jan
sanyi. Kowane daga cikinsu ana ɗaukar sa ta hanyar jima’i. Idan aka kamu da farin sanyi,
zakari zai riƙa fitar da wani farin ruwa mai kama da ruwan ƙurji. Jan sanyi kuwa
jini yake fita daga al’aurar namiji yayin da yake fitsari ko kuwa bayan ƙare fitsarin tare da
wani raɗaɗin ciwo a zakari.
2.2 Alamomin Kamuwa Da Cutar Sanyi
Ciwon sanyi kowane
iri aka kamu da shi wato ko dai na fadama ko na mata[12],
Sarkawa na bayar da magani wanda za a sha a sami waraka. Sarkawa masu ba da
maganin sanyi na la’akari da wasu alamomi a jikin marar lafiya don tantance ko marar
lafiya na fama ne da cutar sanyi. Alamomin su ne:
¶ Zazzaɓi mai
tsanani
¶ Bushewar leɓɓa tare da
yin kamɓarori.
¶ Jiki yakan bushe ya yi huri.
¶ Yakan haddasa kumburi, jiki ya yi haske.
¶ Yakan sa jiki rama, ciki ya yi ƙui-ƙui-ƙui yana walƙiya.
¶ Ana shan wahala wajen fitsari, wani zubin fitsarin kan fita tare
da jini.
¶ Yakan haifar da kumburewar
tsuwayya na maza.
¶ Tsuwayya kan bambanta ta fuskar girma, ɗaya kan rinjayi ɗaya a girma.
¶ ƙaiƙayi a matsematsi.
¶ Akan gudana a kai- a kai
wani lokaci ya zama kamar ɗiɗɗira.
¶ Akan yi bayan gida kamar na raƙumi.
¶ Ana samun yawan yin rihi (tusa) barkatai.
¶ Samun kasala a jiki musamman a ji rashin ƙarfi a gaɓoɓi.[13]
¶ Kan haifar da zogi a ƙafafuwa da guiwa.
2.3 Illolin Ciwon Sanyi
Ciwon sanyi idan ya
yi jinkiri a jikin mutum ba tare da an sami waraka ba, yana haifar da wasu
illoli a jikin marar lafiya mace ko namiji. Illolinsa su ne:
v Yana haifar da kumburin jiki musamman sanyi na
fadama
v Ciwon ƙafafuwa da rashin
kuzari
v Matsanancin ciwon
mara yawanci ga mata da ciwon ciki ga maza.
v Yana shafar al’adar
mata yadda za ta riƙa sassaɓa lokacinta ko ta riƙa yayyankewa.
v Raunana ƙarfin mazakutar
namiji.
v Hana wa mace samun rabo (ɗaukar juna biyu).
v Raunana yawa da ƙwarin maniyin namiji,
wani lokaci yakan kawo ƙafewar namiji.
2.4 Naƙalin Ciwon Sanyi A Mahangar Sarkawa
Sarkawa mutane ne da
suka shahara matuƙa wajen ba da taimako na maganin ciwon sanyi. Nau’in
sanyin ya haɗa da wanda ake kamuwa
da shi sakamakon yawan shiga ruwa, da sanyin aikin fadama da na raɓa da kuma ciwon sanyi da
ake ɗauka ta hanyar jima’i.
A taƙaice, farin sanyi da kuma jan sanyi. Maganin da sukan
bayar ya shafi sassan itatuwa daban-daban. Haka kuma akwai ciyayi da ganyaye.
Sassan na itatuwa ka iya kasancewa saiwa ko ɓawo ko sassaƙe ko ganyaye na
itatuwan, waɗanda ko dai ake
tsimawa ko tafasawa ko dakawa domin a sha a kunu ko a
fura ko kuma a sha ruwan maganin zalla, da nufin samun waraka daga cutar sanyi.
Yadda mutane suka
bambanta, haka magungunan da suke bayarwa suka bambanta. Maganin da wani ya
sani, wani bai san shi ba. Tun da haka abin yake, magungunan cutar sanyi da
sarkawa ke amfani da su wajen kawar da ita na da yawa kuma mabambanta ne. A kan
haka, za a ɗauko wasu misalai na
wasu magunguna a bayyana su a cikin wannan muƙala. Gabanin a kawo
su, ya kyautu a sani cewa falsafa ko dalilin Sarkawa na ɗebo itatuwan da suke
amfani da su shi ne ko dai ya kasance itatuwan suna rayuwa ne a fadama ko cikin
ruwa ba tare da sanyin ruwa ya kashe su ba, ko kuma idan aka ɗebi sassaƙe ko saiwan itatuwan
za a ga suna da sanyi sosai. Wani lokaci har ruwa yake zuba, idan aka sari
itatuwan. Tunanin shi ne, idan dai har sanyi da suke tare da shi bai cuta musu
ba, za su iya taimakawa wajen korar sanyi a jikin mutane. Juriyar da suke da
ita na sanyi ta samu ne sakamakon wasu sinadarai da ke cikinsu,
wanda shi ke hana sanyi cuta musu. Ana ganin sinadaran za su iya gusar da cutar
sanyi. Misalan magungunan kuwa su ne:
*
Magani na sanyin fadama da Sarkawa ke
amfani da shi kuma sukan bayar domin samun waraka daga cutar sanyi shi ne na
sayyun itacen farar taramniya. Akan karkare su, a kuma ɗebi lingaɓi na sansami ko ganye na itaciyar farar taramniya kimanin dunƙule uku.
Ana kuma ɗibar saiwa
na itacen taura, da kuma sassaƙen itaciyar gyayya. Waɗannan duka za a saka a tukunya domin a dafu su tare
da jar kanwa. Bayan sun tafasa sosai, a sauke
tukunya. Idan maganin ya huce, marar lafiya ya sha iya cikinsa. Za a ci gaba da
dafa maganin har tukunya uku sannan a zubar da shi.[14]
*
Wani misali na maganin ciwon sanyi da
Sarkawa ke bayarwa wanda kuma ke maganin sanyi na fadama da na sanyin mata
shi ne a sami sayyun itaciyar lukuci, tare da sayyun ƙaidaji[15],
a haɗa su da
sassaƙen itacen gyayya. Ana saka duk waɗannan a cikin tukunya tare da kayan koli kamar citta da kanufuri
da kimba da ‘ya’yan yaji da acibirma da gangaware, sai a dafa su tukunya biyu
zuwa uku. Idan maganin ya huce sai a sha sau uku a rana har zuwa
sati ɗaya. Idan
ya kasance an haifi marar lafiya da ciwon sanyin ne, to zai riƙa shan
maganin a duk lokacin da ya ji ƙishirwa wato ya kasance duk ya buƙaci shan ruwa maganin
zai ɗauko ya
sha.[16]
*
Ana kuma amfani da sansami ko ganye na
itacen gudai tare da sassaƙensa, a saka a tukunya, a dafa bayan an jefa jar kanwa a ciki. Dafa maganin
za a yi sosai, idan ya huce sai a riƙa sha.
*
Wani taimako na maganin sanyin mata da na
fadama, wanda Sarkawa ke bayarwa ga marasa lafiya shi ne akan sami sayyun
lalle. Bayan an wanke ƙasa da ke jikinsu, sai a saka su a cikin tukunya tare da balma. Dafa
wannan magani za a yi sosai sannan a sauke tukunya bayan an tabbatar da maganin
ya dafu. Ana shan maganin kimanin moɗa ɗaya bayan
ya huce. Maganin yana sa a yi zawayi sosai kuma ba a ba mace mai juna biyu
domin haɗin
maganin yana ƙunshe da sinadarai da ke sa ciki zubewa.[17]
*
Idan sanyin mata ne irin wanda ke sanya
tsuwayya (‘ya’yan marena) su
kumbura, suna ciwo, Sarkawa kan ba da magani. Misali na wani magani da wasu
daga cikin Sarkawa sukan bayar kuwa shi ne sai a sami tsiro na damaigi a ciro
shi gaba ɗaya har
saiwa. Ana kakkaɓe shi
sosai domin koyaushe ana tarar da cinnaka ko kiyashi tare da shi. Saɓa shi a turmi za a yi a kuma shanya ya
bushe, sannan a sake daka shi sai ya zama gari sosai. Wannan garin za a riƙa ɗiba kwatancin babban cokali ɗaya, a riƙa zuba shi a cikin
kunu ko fura, mai rashin lafiya ya riƙa sha sau biyu a wuni, safe da yamma.
Wannan magani yana da inganci sosai kuma ana samun biyan buƙata.[18]
Ciwon sanyi da aka haifi mutum da shi, ana maganinsa ta hanyar ɗebo wani hakin ruwa da ake kira yaɗiyar ruwa. Dafa ta ake yi tare da jar
kanwa da kuma ganyen itacen gwaiba, sai maganin ya tafasa sosai sannan a
sauke tukunya. Ana samun kashin ƙadangare, irin farin kashin nan nasa, sai
a jiƙa shi a moɗa sai ya
jiƙa sannan
a ɗan zuba
ruwansa kaɗan a cikin
wancan maganin da aka dafa, sai a sha. Idan ba da ciwon sanyin aka haifi mutum
ba, ba sai an saka kashin ƙadangare a cikin maganin ba. Haɗa maganin da kashin na ƙadangare yana sa a yi amai don haka ba a
kwankwaɗar
maganin da yawa.[19]
Wasu daga cikin Sarkawa na da ra’ayin cewa ciwon sanyi kan haddasa
ciwon ciki. Irin wannan ciwon ciki, ko da marar lafiya ya sha maganin ciwon
ciki irin wanda aka saba da shi ba za a sami sauƙi ba kuma ko da an
samu sauƙin, na wani ɗan lokaci
ne.[20]
Da yake cutar sanyi ta haddasa ciwon cikin, maganinsa sai ya haɗa da maganin sanyi. Domin samun waraka
daga wannan irin ciwon ciki, Sarkawa kan bayar da magani. Maganin da suke
bayarwa shi ne:
*
Ana samun saƙesaƙin zogala
wanda za a jiƙa a cikin ruwan tsagaro mai tsami, a saka jar kanwa a ciki sai ya
jiƙa sosai
sannan mai wannan rashin lafiya ya riƙa sha har sai ya sami sauƙi.[21]
Mara wani ɓangare ne
na jikin mutum wanda bagirensa ke tsakanin cibiya da kuma inda
al’aura take. Da yawa mata da maza kan yi fama da ciwon mara amma dai ciwon ya
fi yawaita a tsakanin jinsin mata. Wani lokaci ciwon jan sanyi ne kan haddasa
ciwon mara. Masu fama da ciwon za su riƙa jin kamar ana sukar su a mara, mara ta
riƙa murɗa. Wani lokaci za a ga
mace ta faɗi kwance
tana wulle-wulle musamman idan ciwon ya yi tsanani. Cutar kan haddasa al’adar
mata da suka saba da ita wata-wata ta riƙa sassaɓawa ga yawan kwanaki ko ta riƙa karkatsewa, ta riƙa ɗaukewa tana dawowa. Haka ma cutar kan sa
al’adar mace ta ɗauke,
mace ta ɗauki
dogon lokaci ba tare da ta ga al’ada ba. Uwa uba, cutar kan hana masu fama da
ita musamman mata samun rabo, wato ta hana mace ɗaukar ciki.
Sarkawa sun shahara matuƙa wajen
ba da taimako na maganin wannan cuta. Misali na wani magani da wasu kan bayar
domin samun waraka daga cutar ciwon mara shi ne:
¶ Ana ɗebo sayyu
na itaciyar farin ice, a yanka su guntu-guntu daidai yadda za a iya saka su a
cikin tukunya. Dafa sayyun za a yi tare da jar kanwa domin kunu za a yi na
maganin. Ana samun gero kimanin rabin tiya ɗaya, sai a surfe shi sannan a shanya shi. Bayan ya sha iska, sai a
dake geron tare da ƙwara huɗu-huɗu na barkono da citta da kimba, sannan a
tankaɗe shi.
Ana kuma samun toka ta murhu (habɗi), ita ma a tankaɗe ta sosai. Za a riƙa ɗibar tokar da yatsun hannun dama har sau tara, kowace ɗiba za a yi sai a yi ‘Bisimilla’, sannan a
haɗe tokar
cikin garin gero da aka tanada. Ana raba garin geron kashi huɗu domin za a yi kwana huɗu ana yin kunun maganin. Idan za a ɗora tukunyar maganin a wuta, ana zuba ruwa
kimanin tiya biyu a ciki, tare da saka jar kanwa. Lokacin da maganin ya dafu, sai a ɗauko kashi ɗaya na garin gero, a dama, a yi kunu da marar lafiya
zai sha. Haka za a yi har sau huɗu. A rana ta huɗu in aka fahinci cewa ruwan da ya rage ba ya isa yin kunu, sai a ƙara kohi ɗaya na ruwa cikin maganin sannan a yi
kunu.[22]
3.0 Sakamakon Bincike
Al’adance, maganin
gargajiya a al’ummar Hausawa abu ne na sirri wanda ba kowa ake
bari ya san gindinsa ba sai tsakanin iyaye da ‘ya’yansu.
Ma’ana sanin gindin magani gadon sa ake yi kuma abu ne da ake riƙewa a cikin sirri ba
a barin saninsa a sarari sai dai ɓoye. Ko a tsakanin iyaye da ‘ya’yansu,
ba a faye barin ɗa ya san tushen magani
ba sai ya yi biyayya kuma ya nace da tambayar iyaye. Wani lokaci ko da an yi
hakan, akan buƙaci ɗan ya ɗan bayar da wani ‘goro’ ko da ƙanƙani ne kafin a sanar
da shi wani tushen magani. Idan ba a sami ‘ya’ya masu kula da tambaya ba,
dattijo masanin magunguna masu muhimmanci, kan ƙaura, ya tafi da
iliminsa na magunguna, ya kasance al’umma ta yi hasarar gaske.
Idan aka yi la’akari
da yadda wannan hali yake, wannan muƙala ba ƙaramar nasara ta yi
ba wajen tattaro wasu muhimman magungunan gargajiya masu fa’ida wajen warkar da
cutar sanyi walau sanyin fadama ko na mata da kuma ciwon mara. Wannan ba ƙaramin taimakawa zai
yi ba wajen adana waɗannan magunguna wanda
yin haka zai kuɓutar da su daga haɗarin salwanta.
4.0 Kammalawa
A wannan muƙala an yi ƙoƙari wajen binciko
irin gudunmawa da Sarkawa ke bayarwa ga sha’anin kiwon lafiya na gargajiya a
cikin al’ummar Hausawa. Muƙalar ta karkatar da akalarta
wajen
cutar sanyi, yadda Sarkawa ke kallon ta da kuma yadda suke magance ta. Wannan
wani ƙaramin ɓangare ne daga cikin irin
fannoni da cututtuka da Sarkawa ke bayar da taimako a
gargajiyance domin magance su. Ra’ayin wannan muƙala ne cewa ta fuskar
kiwon lafiya na gargajiya, Sarkawa ba ƙashin jefarwa ba ne
domin akwai cututtuka da dama da suke taimakawa wajen warkar da su. Tun da haka
ne kuwa, ashe ke nan
akwai ruwa mai tarin yawa a ƙasa sai dai idan ba a tona ba. A kan
haka ne nake hasashen cewa idan aka zurfafa bincike a kan gudunmawar Sarkawa ga
kiwon lafiyar al’umma ta Hausawa, za a tarar cewa suna da muhimmayar rawar da
suke takawa a fannonin kiwon lafiya kamar riga-kafi da
ceton rayuwa idan aka sami haɗari a ruwa da bayar da maganin
waraka da suka haɗa da
wasu cutuka na fatar jiki da kafewar hakin kifi a maƙogwaro da maganin
iska. Haka ma a wajensu ‘yan masu ganye suke samun kitse da fatu na
wasu dabbobin ruwa da kifi, waɗanda ake haɗawa wajen magunguna
daban-daban,
musamman magungunan tsafi.
Ya dace ainun masana
kimiyyar
haɗa magunguna su haɗa guiwa da Sarkawa
domin sanin irin itatuwan da suke amfani da su wajen magance cututuka
daban-daban da nufin binciken sinadaran da magungunan suka ƙunsa da nufin gano ƙima na yawan maganin
da ya kamata marar lafiya ya sha, da kuma lokacin da ya kamata a ɗauka ana shan
maganin. Wannan ne abin da wani maganin gargajiya ya rasa kuma yin haka zai
kawo sauƙi da kiwon lafiya mai rahusa wanda zai haifar da cigaba
mai ɗorewa.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
[1]
Galibi mutanen da suka yi haye wato suka koyi sana’a daga baya ba tare da sun
gada daga iyaye da kakanni ba, ba su faye samun asiri na sana’ar ba saboda yawanci
sha’anin magani an fi yaɗa iliminsa ne daga iyaye zuwa ga ‘ya’ya da
jikoki.
[2]
Duba Jinju, M.H. 1990 Maganin Gargajiya
Na Afirka Tare Da Mai Da Ƙarfi
A Kan Nazarin Itatuwan Magani Na Hausa. Gaskiya Corporation Limited, Zaria.
Shafi na 12. Da Bunza, A.M. 1989 “Hayaƙi Fid Da Na Kogo (Nazarin
Siddabaru Da
Sihirin Hausawa)” Kundin Digiri na Biyu, Jami’ara Bayero, Kano. Shafi
na149-153.
[3]
Ana amfani da waɗansu kifaye da kitse ko fata na wasu halittun
ruwa domin haɗa maganin gargajiya ko dai na
waraka daga wasu cututuka ko kuma na yin maganin tsafi ko na biyan baƙatun rayuwar ɗan’adam.
[4]
Duba Alkali, M.B. (1969) “A Hausa Community In Crisis: Kebbi in the Nineteenth
Century.” M.A. Thesis, A.B.U. Zaria. Shafi na 29-30.
[5]
Bargery, G.P. (1934) A Hausa English Dictionary And English Hausa
Vocabulary. Oxford University Press, London.
[6]
Fito na nufin ɗibar mutane da kaya a
cikin kwalekwale ko duk wani jirgin ruwa domin tsallakar da su daga wannan
mashaya ta gulbi zuwa waccan, ko yin sufurin su daga wannan mashigin ruwa na
wani gari ko ƙauye zuwa wani mashigin ko mashawa. Wato dai wata hanya ce
zirga-zirgar sufuri ta hanyar ruwa.
[7]
An samo wannan bayani ne daga
Lisanul Arab Na Ibn Manzur a adireshin intanet https://ar.m.wikipedia.org/wiki. Dr. Aminu Umar na sashen
Arabic Medium, COE Maru ya fassara.
[8]
CNHN 2006 Ƙamusun Hausa Na Jami’ar
Bayero. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero ,Kano. Shafi na 81.
[9]
Bunza, A.M. 1989 “Hayaƙi Fid Da Na Kogo ( Nazarin
Siddabaru da Sihirin Hausawa)” Kundin Digiri Na Biyu, Jami’ar Bayero, kano.
Shafi na 132.
[10]
T.D.A.S. Shafi na 134
[11]
Bunza, A.M. 1995 “ Magani A Rubuce: Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu.” Kundin
Digiri na Uku, Jami’ar Bayero, Kano. Shafi na 45.
[12]
Wani zai yi matuƙar mamakin abin da ya kai Sarkawa ga ba da maganin cutar da ake ɗauka ta hanyar jima’i. Dalilin haka shi ne cutar
sanyi ko dai na fadama ko na mata duk sukan shafi hanyar mafitsara ne (Urinary
track infection). Tunanin shi ne, tun da wuri ɗaya
suke raunanawa, maganin wannan zai taimaka wajen gusar da wancan.
[13]
Na sami waɗannan a wurin Sarkawa da dama
kamar Fadaman Falale, Fadama shehu, da Sarkin Ruwan Romon Sarki, Mai Ruwa Bala,
a hirar da na yi da su a garuruwansu, lokata mabambanta.
[14]
Hira da mai Ruwa Bala Barga a garin Barga, ƙaramar hukumar mulkin
Tambawal, jihar Sakkwato. Ranar Assabar, 12/06/2010.
[15]
Ƙaidaji da lukuci itace ne da kan
fito galibi bakin rafi. Ƙaidaji yana da ƙaya a jikinsa kuma ya so ya yi kama da
gumbi ko ɗunɗu. Lukuci kuwa ba ya ƙaya kuma ganyayensa kan yi labe-labe ne.
[16]
Hira da Bala Mai Ruwa Romon Sarki, ƙaramar hukumar mulkin
Tambawal, jihar Sakkwato, ranar Assabar, 12/06/ 2010.
[17]
Wannan maganin na tarar da mahaifina yana bayar da shi kuma ana samun biyan buƙata sosai tun ma ba a ce ga mata masu fama da
ciwon mara ba.
[18]
Na sami wannan magani a
wajen yayana, marigayi Fadama Yahaya ( Allah Ya jiƙansa).
[19]
Hira da Alh. Hussaini Sa’idu Kesi,
unguwar Bajana a garin Gayari, ƙaramar hukumar mulkin Gummi,
jihar Zamfara ranar Assabar, 22/05/2010.
[20]
An sami wannan bayani a wajen Alhaji Maibirgi Falam da Alh. Hussaini Sa’idu
Kesi Gayari, a hirar da aka
yi da su a garin Falam da Gayari, ranar Lahadi, 06/05/2010, da kuma ranar
Assabar 12/06/2010.
[21]
An sami bayanin wannan magani a wajen Alhaji Maibirgi Falam a hirar da aka yi
da shi ranar Lahadi, 06/05/2010.
[22]
Hira da Sarkin Ruwan Bakura, Alh. Ibrahim Nabagudu a gidansa da ke unguwar Ɗangarke,
Bakura, jihar Zamfara ranar Talata, 06/06/2011.
Allah ya sakawa Malam da mafificin alherinsa.
ReplyDeleteLambar wayarkafa malam?
ReplyDelete