Ilimin ƙirar kalma abu ne da masana suka yi nazarce-nazarce da kuma rubuce-rubuce a wannan fage cikin harsuna mabambanta cikinsu kuwa har da harshen Hausa. Kalmomin Hausa waɗanda ana gina su ne ta hanyar amfani da baƙaƙe da wasula bisa ƙa’ida domin ƙera kalma, a gefe guda kuma ana shafe wasali a wata gaɓar ta kalma domin taƙaita kalmar ko domin zuwan wata ƙa’ida a wata jimla da aka gina. Cikin wannan bincike, an bayyana wasu kalmomi na Hausa aka shafe musu wasali; wanda wannan shafewar ya shafi tsakiyar kalma ko kuma ƙarshen kalma. Har wa yau, binciken ya gano shafe wannan wasali yakan shafi gaɓar kalma ɗaya kawai. An gano hakan ne ta hanyar karance-karance da duba kundaye da littattafai waɗanda suka shafi ginin kalma a Hausa.
Shafe Wasali A Kalmomin Hausa
Ibrahim Baba (Nayaya)
M.A Hausa (Literature) Student,
Department of Nigerian Languages and Linguistics, Bauchi State Uniɓersity, Gaɗau.
07066366586, 08125351694
Da
Abubakar Umar Akuyam
Goɓernment
Comprehensiɓe
Day Secondary School, Misau
08039093730
Da
Babayo Aliyu
Goɓernment Comprehensiɓe Day Secondary
School School, Misau.
07039231211
baliyumisau@gmai
1.0 Gabatarwa
Shafe wasali wani yanki ne na tsarin
sauti da ake kira ‘phonological processes’ a Turance, wanda akasari yana faruwa
ne domin samun sauƙin lafazi ko kuma a samu daidaito wajen tsirar wani
lafazin. (Glowacka, 2001; Uffmann, 2002; Frajzyngier, 2003; Hall, 2006) a cikin
(Maikanti da Ago, 2018:72).
Masana da dama sun gudanar da
bincike kan wannan batu a harsuna mabambanta, kama daga Turai da Latin, har
zuwa harsunan Afirika. Amma a cikin wannan binciken, an taƙaitu ne a shafe
wasali a kalmomin Hausa, wanda hakan zai sauƙaƙa lafazi ko kuma ya
tsirar da sabuwar ma’ana, musamman idan aka haɗe wasu kalmomi guda biyu waɗanda a cikinsu akwai
wadda aka shafe wa wasali. Shi wannan al’amari na shafe wasali, kowane harshe
yana da irin nasa tsari wajen shafe wasalin domin samar da lafazi mai ma’ana.
An samu rubuce-rubuce daga masana a
harsunan daban-daban da suka yi tsokaci game da shafe wasali. Misali, Oyebade (1998)
ya yi bayani kan shafe wasali, inda ya rinƙa kwatanta kalmomin
Yarbanci, amma shi a wurin sa ana shafe wasali ne yayin da aka samu wasula biyu
ko fiye waɗanda suka zo a ɓangarori daban-daban,
misali, idan za a haɗe kalmomin /ɔmo obìrì/ sai
ya koma [ɔmobírì] wadda ke
nufin ‘yarinya’. To a wannan misalign za a ga an shafe wasalin farko na kalma
ta biyu, wato /o/. Ko kuma kalmomin /gbè ɔmɔ/ sai ya koma [gbɔmɔ], wato ‘ɗauki yaro’. A nan
kuma, an shafe wasalin ƙarshe na kalmar farko wato /è/.
Shi kuwa Allison (2007) a nasa aikin, ya
bibiyi harshen Úwù, inda ya kwatanta wasu kalmomi ta yadda ake shafe musu
wasali yayin da aka haɗe kalmomi biyu suka
koma guda ɗaya. Misali, idan an
tashi haɗe kalmomin /anũì ùwa/
sai ya koma [anũùwa] wato ‘ƙofar ɗaki’. Ko kuma kalmomin /oɲĩni àta/ sai su koma [oɲĩnaťa], wadda ke
nufin ‘idon ruwa’. A waɗannan misalan za a ga
cewa an kalmomin farko an shafe wasalin /i/ wanda yake jikin kalmar farko,
yayin da misali na biyu aka shafe wasalin /i/ shi ma a kalmar farko.
Maikanti da Saleh (2018) sun yi wani
aiki da ya shafi shafe wasali a harsunan Hausa da Ingilishi. Misali, sun kawo
wasu taƙaitattun jimloli a harshen Ingilishi da kuma yadda ake
shafe wasalinsu. /that is alright] wadda ke nufin ‘wannan ya yi daidai’, sai a
mayar da ita /that’s alright/, ko kuma/let us go/, sai ya koma /let’s go’, wato
‘mu tafi’. Wannan shafe wasalin da yake gudana a matakin gamayyar tasarifi na
ginin jimla, akan maye gurbinsa ne da waƙafin sama kamar yadda
aka gani a misalan da suka gabata.
1.1 Ma’anar Wasali
Sani (1999:14) ya bayyana ma’anoni
guda biyu a matsayin ma’anar wasali, inda ma’ana ta farko ya bayar da ita a dunƙule wadda saƙon ciki bai isa ba.
“Wasali sautin magana ne baya ga baƙi”. Amma a gamammiyar
ma’ana, ya nuna wasali da cewa “Wasali sautin magana ne wanda a yayin furta
shi, iska ba ta samun tangarɗa wajen fita, sai dai karkarwa kawai da tantanin maƙwallato ke yi. Ba
kamar wajen furta sautin baƙi ba inda yake tilas ne iskar ta sami
tangarɗa koyaya, wajen furta
wasali babu wannan tangarɗa haka. Haka kuma
dukkanin wasula masu ziza ne, ba kamar takwarorinsu baƙaƙe ba inda yake wasu
masu ziza ne, wasu marasa ziza, wasu ma ‘yan-ba-ruwanmu”.
Ke nan, wasali ɗan’uwan burmin baƙi ne wajen gina
kalma, su biyun ne ke haɗuwa da juna cikin
siffa da ƙira mai kyau domin samar da gaɓa mai kyau, ita kuma
gaɓa ta samar da kalma,
yayin da taron kalmomi kuwa zai haifar da jimla.
1.2 Adadin Wasulan Hausa
Hausa tana da wasali iri biyu, akwai
tilon wasali da kuma tagwan wasali.
1.2.1Tilon Wasali
Shi ne wanda furucinsa ke da siga
guda ɗaya tak. In za a
kwana ana jan wannan wasali, wannan siga bat a canjawa. Misali, da za a kwana
ana jan [a], ko [i] ko [u], sigar ba ta canjawa daga [aaaaaa--], ko
[iiiiii---], ko [uuuuu----]. Hausa tana talon wasali guda goma, cikinsu akwai
gajeru guda biyar, akwai kuma dogaye guda biyar (Sani, 1999:14). Misali:
a. Gajeru:
[a] misali faɗa
[i] misali
“ jiki
[o] misali zato
[u] misali
“ uwa
[e] misali
“ mace
b. Dogaye:
[aa] misali baashi
[ii] misali “ jiika
[oo] misali
“ ƙoofa
[uu] misali
“ buuta
[ee] misali
“ geemu
1.2.3 Tagwan Wasula
Tagwan wasula su ne wasulan da
mabambanta wasula biyu ke haɗuwa wuri guda domin samar da wasali ɗaya. Wajen furta waɗannan wasula, akan
samu siga biyu, wato ana farawa da wata siga a ƙare da wata siga.
Tagwan wasula sun haɗa da:
[ai] misali aiki
[au] “ ƙauye
[ui] “
guiwa (Sani, 2015:19- 20)
1.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Aiki kan shafe wasali a Hausa nazari
ne da ya wakana ta hanyar bibiyi furucin wasu kalmomi a Hausa tare da auna
furucinsu a baka, da kuma ganin irin yadda ake furta su. An yi amfani da haɗe kalmomi guda biyu wuri ɗaya, hakan sai ya
sabbaba shafe waslin ƙarshen kalmar, ko kuma ta hanyar taƙaita wata kalma;
hakan sai ya janyo shafe wasalin ƙarshe na kalmar.
Misali: /#kwaana#/, sai aka shafe wasalin /a/, ya koma [kwan], wato ‘ya kwan
lafiya’, ko kuma /#zaa + ni#/ sai ya koma [zan] yayin da aka haɗe su. Haka zalika, ana
shafe wasalin tsakiya a kalma wanda hakan sai ya mayar da kalma mai gaɓa uku zuwa gaɓa biyu, misali
/wuridii/ sai a shafe wasalin tsakiya /i/, sai ya koma [wurdii].
2.0 Shafe Wasali a Kalmomin Hausa
Kamar yadda ya gabata, an yi tsokaci
a kan wasali da kuma bayyana wasulan Hausa. A nan kuwa, za mu yi bayani a kan
shafe wasali, ta hanyar bayyana ma'anar shafe wasali.
2.1 Ma’anar Shafe Wasali
Abubakar (2013:1) ya ce, shafewa
tana ɗaya daga cikin
dokokin tsarin sauti muhimmai guda huɗu, baya ga naso da saƙalawa da kuma rawar
yan mata.
Idan muka yi la’akari da bayanin
Abubakar (2013) game da shafewa a Hausa, za mu tarar cewa ana iya samun shafe
wasali a ƙarshen kalma ko ƙwayar ma’ana a
tsakiya da kuma farkonta. (Maikanti, da Ago, 2018: 73)
Ta fuskar bayyana ma'anar shafe
wasali kuwa, Abiodun (2007) a cikin Allison (2017: 20) ya bayyana shafe wasali
da cewa, “Hanya ce da take haifar da ɓacewar sauti, wanda kan iya zama wasali ko baƙi ko ma a matakin
maraka yanki”.
Sani, (1999: 40) cewa ya yi, “Shafe
wasali akasi ne na saƙala wasali. Abin da ake nufi takamaimai shi ne cire
wasali daga kalma don taƙaita lafazi”. A wajen ƙarin bayani, Maikanti
da Ago (2018: 72) sun bayyana cewa yin haka ba ya kawo sauyi ko bambancin
ma’ana ga kalmar da aka shafe wani ɓangare nata.
2.2 Shafe Wasali A Tsakiyar Kalma
Wannan yanayi na shafe wasalin
tsakiyar kalma a Hausa ya shafi akasarin kalmomin da ake fara rubuta su da
wasali ne. Wannan nau’i na shafe wasali ya taƙaita ne ga wasu
kalmomin suna da na aikatau a Hausa, waɗanda za a gani kamar haka.
i. Shafewa A Suna
Abubakar (2013) ya yi bayani cewa
Bergary (1934) da Wolf (1992) sun yi nuni da cewa ana samun wasu kalmomi na
Hausa waɗanda ake shafe
wasalin /u/ ko /i/ da ke zuwa bayan baƙin hamza /?/. Dubi waɗannan misalai:
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /?ingiritʃii/ /?ŋgyiritʃii/ ingirici hay
b. /?ungulu/ /?ŋgwulu/ ungulu
ɓulture
c. /wuridii/ /wurdii/ wuridi prayer
Idan aka yi la’akari da misalan nan
za a ga cewa wasalin /i/ aka shafe a kalmar /?ingiritʃii/ wanda ya zo a gaɓar farko. A misali na
biyu kuwa, wasalin /u/ na gaɓar farko aka shafe, a yayin da har-ila-yau aka shafe
wasalin /i/ na gaɓa ta biyu da ke
kalmar /wuridii/, sai ta koma [wurdii] (Maikanti, Ago, 2018:75).
2.3 Shafe Wasali A Ƙarshen Kalma
Kalmomin da ake iya shafe wasalinsu a
gaɓar ƙarshe sun haɗa da kalmomin suna
masu gaɓa biyu da masu gaɓa uku kamar haka:
i. Suna Mai Gaɓa Biyu
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /#káajìi#/ [kaj] kâi head
b. /#ƙóojìi#/ [ƙwoj]~[ƙwaj] ƙwâi egg
c. /#mâajìi#/ [maj] mâi oil
d. /#ráajìi#/ [raj] râi life
e. /#sáawùu#/ [saw] sâu leg
Idan aka dubu misali na ɗaya za a ga cewa gaɓar farko ta kalmar
/#káajìi# tana ɗauke da tsarin gaɓa na baƙi da dogon wasali mai
karin sautin sama (S), gaɓa ta biyu kuwa tana ɗauke da kinin wasali
/j/ da kuma dogon wasalin /ii/ mai karin sauti ƙasa (K). Shafe wannan
wasali na /ii/ aka yi aka kuma jingina kinin wasalin tare da karin sauti ƙasa jikin gaɓar farko. Hakan ya sa
aka sami tsarin gaɓa na baƙi da wasali da kuma
wannan kinin wasalin. Kasancewar a Hausa ba a samun dogon wasali a rufaffiyar
gaɓa, sai wannan wasalin
ya gajarce, karin sautin wasalin da aka shafe kuma ya haɗe da na gaɓar farko sai aka sami
karin sauti faɗau wanda hakan ya sa
aka sami kalmar [kâj]. Haka lamarin yake ga sauran misalai na ƙasa kamar haka:
ii. Suna Mai Gaɓa Uku
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari
a. /#ƙájƙájii#/ [ƙájƙaj] ƙaiƙai chaff
b. /#táwsájii#/ [táwsaj] tausai
mercy
c. /sáwsájii#/ [sáwsaj] tsautsai accident
Misali na farko yana bayyana cewa
kalmomin suna masu gaɓa uku-uku suna ɗauke da tsarin gaɓa na BWB.BW.BWW tare
da karin sauti Ƙ-Ƙ-S. A sakamakon shafe wasalin ƙarshe na ƙarshen gaɓa, sai aka sami
kalmomin suka koma masu gaɓa bibbiyu kuma kowace gaɓa ta tashi a matsayinta na buɗaɗɗiya inda ta koma
rufaffiyar gaɓa.
Har-ila-yau, akan sami wasu kalmomi
waɗanda gaɓoɓinsu na ƙarshe ba kinin
wasalin /j/ ba ne amma kuma ana shafe shi (wasalin ƙarshe) don samun sauƙin lafazi. Za a iya
kallon waɗannan kalmomin na ƙasa da aka ɗauko daga Abubakar
(2013) a matsayin misalai kamar haka:
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /#duká#/ [duk]~[duw] ~[du]: duk/du
all
b. /#ganìi#/ [gaŋ] gaŋ
saw/seen something
c. /#ƙasá#/ [ƙas]~[ƙar] ƙas ground/down
d. /#sanìi#/ [saŋ] saŋ knew/knowing something
e. /#tùkùnna#/ [tùkwuŋ] tukuŋ yet
f. /#wanzaamii#/ [wanzam] wanzan berber.
Idan aka yi la’akari
da misali na farko da na biyu za a fahimci cewa an sami lafuza mabambanta
sakamakon shafe wasulansu na ƙarshe, amma duk da haka, ba a sami
sauyin ma’anar kalmomin ba. Bambancin lafazin da ake iya samu kuma ba zai rasa
nasaba da karin harshe da ake da su a Hausa ba.
Baya ga shafe wasali a kalmomin suna
na Hausa, akwai kuma shafe wasali a wasu kalmomi na aikatau. Newman (2000: 667)
ya sami goyon bayan Abubakar (2013) wajen nuna cewa akwai wasu aikatau na Hausa
guda goma da ake shafe wasulansu na ƙarshe ba tare da an
sami sauyin ma’ana ba. Kalmomin kuwa su ne kamar haka:
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /#ɗaráa#/ [ɗar] ɗar eɗceed slightly
b. /#ɗawká:#/ [ɗaw] ɗau
lift
c. /#Φaaɗáa#/ [Φar] far fall on/attack
d. /#kárajá#/ [karaj] karai lose hope
e. /#kaʃѐe#/ [kas] kas kill
f. /#kwaana#/ [kwáŋ] kwan spend the night
g. /#sakáa#/ [saw]</sak/7 sau release
h. /#saamáa#/ [sam] sam get/giɓe a little
i. /#sajaa#/ [saj] sai buy
j. /#zamaa#/ [zam] zam
become.
Baya ga misali na huɗu duk sauran suna ɗauke da gaɓa bibbiyu ne, a yayin
da misali na biyar kuwa kore ganɗantawa aka yi wato inda sautin /ʃ/ ya koma [s] a
sakamakon shafe wasalin /ee/, yanayin da ya haifar a misali na shida ya sami
sauyi bahanƙe /n/ zuwa bahanɗe /ŋ/.
Bugu da ƙari, ana samun shafe
wasalin ƙarshe na wakilin suna na ɗaya tilo {ni} da kuma na uku tilo
{ya}. Wannan lamari yana faruwa ne a matakin gamayyar tasrifi da ginin jimla,
kamar yadda za a gani a misali na gaba.
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /#záa + ni#/ [zâŋ] zan
I will
b. /#záa + ya#/ [zâj] zai
he will
c. /#báa + ni#/ [bân] ban giɓe me
Misali na farko na nuni da cewa
misalin /i/ na wakilin suna ‘ni’ akan shafe bayan da aka haɗe shi da manunin
lokaci mai zuwa na ɗaya (1st
ms) ‘záa’ yanayin da ya haifar da sauyawar bahanɗe /n/ zuwa bahanɗe [ŋ]. A misali na
gaba kuwa, wasalin /a/ na wakilin suna na mutun na uku tilo ne akan shafe. Wani
abin la’akari a nan shi ne, shafewar da aka yi na dole ne musamman idan ana
magana a kan daidaitacciyar Hausa.
Har-ila-yau kuma, ana samun shafe wasalin
/i/ na wakilin suna na ɗaya “ni”, musamman
lokacin da ya zo tare da jakada “ma”, kamar yadda za a gani a misali na gaba.
Ƙirar Ɓoye Lafazi Ƙirar Sarari Ingilishi
a. /#ma+ni#/ [miŋ] min
to me
b. /#ma+sa#/ [mar]/[mas] mar/mas to/for him.
Abin lura a misali na farko shi ne,
bayan da aka haɗa kalmomin biyu, sai
aka sami cikakken naso da kuma shafe wasali. A misali na biyu kuwa, bayan haɗe kalmomin biyu wuri
guda, shafe wasalin /a/ kaɗai aka yi. Za a iya ganin yadda buɗaɗɗiyar gaɓa ta koma rufaffiya
sakamakon haɗe kalmomin biyu da
kuma shafe wasalin ƙarshe. Mu dubi waɗannan jumloli da ke biye a misali na gaba.
A B
a. Yaa cirѐe miŋ Yaa cirѐe mani
b. Yaa buuɗѐe mas Ya
buuɗѐe masa.
Jumlolin da ke ɓangare na A ba su da wani
bambanci dangane da ma’ana idan aka kwatanta su da na ɓangaren B, in ban da
shafe wasali da aka samu a tsakaninsu. Idan ma har akwai wani tasiri, to bai
zai wuce samun sauƙi wajen lafazi ba.
3.0 Abin Da Bincike
Ya Gano
Wannan bincike ya gano
yadda aka samar da wasu cikin kalmomin da aka shafe wa wasali a harshen Hausa.
Binciken, ya yi nutso cikin kalmomin Hausa da kwatanta su a furuci, sannan ya
tabbatar da lalle akwai kalmomin da ake shafe wa wasali kamar a sauran wasu
harsuna irin Ingilishi, Yoroba da harshen Úwù.
An binciken, an gano yadda ake bi wajen shafe waɗannan wasula, da kuma irin muhallan da waɗannan wasula suke, da kuma yadda shafe wasalin ke taƙaita tsayin kalma. Wasulan da
binciken ya gano an fi shafe wa su ne /i/ da /a/, duk da kasancewar sauran
wasulan ma akan shafe su idan buƙatar hakan ta taso.
4.0 Kammalawa
Kamar yadda ya gabata a wannan
nazari, an bayyana ma’anar wasali tare da jero wasulan Hausa gaba ɗaya. A takardar, an
bayyana ma’anar shafe wasali bisa fahimtar masana, sannan aka kawo bayani a
game da shafe wasula. A cikin takardar, an kawo ayyukan da suka gabata daga
masana a harsuna mabambanta game da shafe wasali, misalign harshen Ingilishi,
Uwu da Yoroba. Wannan takarda ta taƙaita bayani a kan
yadda ake shafe wasula a kalmomin Hausa inda aka kawo kalmomi mabambanta kuma
aka shafe wasulansu.
Manazarta
Tuntuɓi masu takarda.
Tanbaya me ake Nufi da kinina kalma
ReplyDelete