Ticker

6/recent/ticker-posts

Masarautar Bakura A Daular Zamfara

 Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na huɗu da Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ta shirya a kan Daular Zamfara. Wanda aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Farfesa A.H. Amfani a  Zauren Lacca na Tsangayar Fasaha da ke Jami’ar, a ranar 26-2-2020.

zamfara

Masarautar Bakura A Daular Zamfara

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

TSAKURE

Sanin abubuwan da suka shuɗe ta kowace fuskar rayuwar ɗan Adam yana da muhimmancin gaske. Wannan ne ya sa masana tarihi ke iƙirarin cewa duk wanda bai san abin da ya faru kafin haihuwarsa ba, zai zama tamkar jinjiri har abada. Domin zai kasance da ilimin abin da ya sani ko ya gani, ba tare da fahimtar musabbabin wanzuwarsa ba. Tarihi yakan ɗauki fuskoki mabambanta kamar na ƙasa ko al’umma ko addini ko managartan magabata da taƙadirai. A waɗannan fannona, tarihi yana amfani wajen ilmantar da al’umma yanayin cikin da jiya ta ɗauka, domin sanin abin da gobe za ta haifa da kuma daraja ko ƙasƙancin abin da aka haifa zai samu a cikin rayuwa. Ganin an yi wa tarihin wasu al’ummomi riƙon sakainar kashi a farfajiyar ƙasar Hausa, alhali kuwa irin waɗannan al’ummomi ne suka aza harsashen abubuwan alheri da ‘yan baya suka riska har suka kasance suna cin moriyarsa. Dalilin haka ne wannan maƙalar ta ƙuduri aniyar kawo bayanai game da asali da ma’anar kalmar Bakura da yanayin ƙasar da iyakokinta da asalin mutanenta tare da bin diddigin asalin sunan masarautar da al’ummarta. Za a kuma zo da abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasar masarautar da sarakunanta da dangantakarsu da masu masaukinsu.

1.0 Gabatarwa

            Taskace tarihin kowace al’umma abu ne wanda ya wajaba a wuyan ‘yan asalin al’ummar, matuƙar sun mallaki ilimin karatu da rubutu1. Sau tari ta hanyar rubutun ce ake adana tarihin al’ummomin daban-daban don kare tarihin daga gurbacewa. Duk da haka al’umma kan zaɓi wasu rukunin al’umma da aka tabbatar da suna da kaifin basirar kiyaye abubuwan da suka ke wanzuwa a tsakanin al’umma, a ɗora musu alhakin taskace su cikin ƙwaƙwalwarsu maganin ko taka taso a sakamakon salwantar kundin tarihin al’ummar saboda ta’adin gobara ko harin yaƙi ko ambaliyar ruwan sama2. Zuwan Turawa ƙasar Hausa wanda ya haifar da yaƙe-yaƙe, ya zama sanadin salwantar kundayen tarihin wasu al’ummomi, musamman Musulmi. Wasu kayan Turawan Mulkin Mallaka ne suka kwashe su, su kai ƙasar Turai, musamman waɗanda aka taskace cikin harshen Larabci da rubutun ajami. Abin da ya rage gun ‘yan ƙasa sai waɗanda ke taskace a ka da abubuwan da Turawan suka rubuta domin biyan wasu buƙatun kansu. Domin ƙoƙarin adana ɗan abin da ke cikin ƙwaƙwalwar fasihan magabata, wannan takarda ta yi ƙoƙarin kawo taƙaitaccen tarihin wannan al’umma, kamar yadda aka ambata a cikin tsakuren da ya gabata a sama. 

2.0 Bakura: Asalin Kalmar da Ma’anarta

            Akwai ra’ayoyi da dama dangane da asalin samuwar wannan suna na Bakura. Sai dai kowane ra’ayi da aka bayyana za a tarar cewa, masu ra’ayin sun yi ƙoƙarin bayyana hujjar da za ta iya tabbatar da nasu ra’ayi. Daga cikin irin waɗannan ra’ayoyi akwai wanda ke nuna cewa, an samo asalin sunan “Bakura” daga sunan wanda ya kafa garin, kuma shugaban Ɓurmawa na farko mai suna Muhammadu Kura, wanda Turawan Faransa suka yi wa laƙabi da mayaƙi wato ‘WARRIOR’.

            An nuna cewa sunan Bakura ya samo asali ne a yayin da jama’ar Muhammadu Kura ke ƙoƙarin bayyana rasuwarsa, sai suka ce, “Ba Kura” a madadin su ce, “Kura ya mutu ko ya rasu”. Masu wannan ra’ayi sun bayyana cewa daga waɗannan kalmomi ne guda biyu aka haɗe suka koma kalma ɗaya wato “Bakura”, wadda aka yi amfani da ita aka laƙaba wa mazaunin Muhammadu Kura, kamar yadda Bunu (2003) da Muhammad (1988:16) suka bayyana.

             Idan aka dubi wannan ra’ayi za a ga ya sami gindin zama ta la’akari da al’adar ƙasar Hausa a inda akan yi amfani da kalmar girmamawa da nuna tausayi ga duk wani babban mutum da Allah ya yi wa cikawa. Domin a kunnen ɗan ƙasar Hausa da ya ji an ce: “ Wane ya mutu” zai ɗauki an nuna hutsanci da rashin ladabi da rashin nuna tausayi ko damuwa, musamman ma idan wanda Allah ya yi wa rasuwa shugaban jama’a ne.

            A wani ra’ayi na daban kuma an bayyana cewa, sunan Bakura ya samo asali ne daga sunan wani mafarauci da ake kira “BAKKU”, kamar yadda Harris (1938:93) da Johnson (1953:3) da Malam Yahya (2003) suka bayyan. Masu wannan ra’ayi sun nuna cewa, “an samo wannan suna ne a lokacin da Ɓurmawa suka yi ƙaura daga Tukunawa3, suka dawo mazaunin da garin yake a halin yanzu. A nan ne suka sami mafaraucin da ake kira “Bakku”, wanda ke zaune kusa da hanyar da Fulani ke wucewa in za su je mashayar dabbobi. An ce a duk lokacin da za su ɗaukar ruwa, sukan ce, “Ra – Bakku”, wato “ga Bakku”. An ce daga nan sai kalmomin suka yi musayar gurbin wurin zama, sai suka dawo “Bakku – Ra”. Daga baya sai aka haɗe kalmomin guda biyu tare da shafe harafin “K” da aka ɗaura a gaɓar farko Bak, sai ta dawo “Ba+ku+ra”, daga nan sai aka sami sunan “Bakura” da ake kiran wannan ƙasa ta Ɓurmawa da shi.

            Yayin da a wani ra’ayi aka nuna cewa, sunan “Bakura” ya samo asali ne, alokacin da aka fara kafa mazaunin da Bakura take, a inda ake son a bayyana wa sauran jama’a cewa wurin lafiyayye ne ba ya da kuraye, sai aka ce “Ba kura”, kamar yadda Marafa Alh. Bello Yusuf III (2003) ya bayyana. An ce daga waɗannan kalmomi ne guda biyu aka haɗe suka zama “Bakura”. Masu wannan ra’ayin sun nuna cewa, kafin a kafa garin a wannan wurin, ya kasance mai yawan kuraye. Amma a yayin da al’umma suka soma kai musu farmaki, suna farautarsu, sai duk kurayen suka watse. Don haka, a wajen ƙoƙarin nuna sun watse ba sauran da suka rage, shi aka taƙaita aka ce “Ba kura”, wanda daga waɗannan kalmomi ne aka game su waje ɗaya suka bayar da asalin sunan garin “Bakura”.

            Ta kowane irin hali dai za a iya fahimtar cewa, an kafa wannan gari mai albarka tun wajen farkon ƙarni na goma sha bakwai (ƙ.17). Kuma sunan garin ya samo asali ne tun daga wancan lokacin.

3.0 Yanayin Ƙasar Bakura Da Iyakokinta

            Kasancewar Allah ya yi mutanen wannan ƙasa zarumai ne, shi ya haifar da maƙwabtansu na kusa da na nesa suke yi wa wannan gari kirari da cewa:

            Bakura garin Jandamo

            Garin Na-abu da Ɗankwai

            Garin da ba a haihuwar ɗa raggo.

Garin Bakura na ɗaya daga cikin manyan garuruwa masu cikakken tarihi da aka kafa a farfajiyar Daular Zamfara, ya kuma kasance cikin jahar Zamfara ta yanzu. Yana tsakanin Sakkwato da Talata Mafara, kimanin nisan kilomita 105 ne daga Sakkwato zuwa Bakura. Daga Gabas ta yi iyaka da Ruwan Gizo da ke cikin ƙasar Talata Mafara. Daga Arewa kuwa ta yi iyaka da ƙasar Gandi. Ta yi iyaka da ƙasar Rara ta wajen Yamma, sannan ta yi iyaka da ƙasar Anka ta ɓangaren Kudu, a inda ta gangara ta faɗaɗa har ta kai Gulbin Rangam. Yayin da a Kudu Maso-Yamma ta yi iyaka da Tureta.

            Yamma arewa gabas  Zahirin Taswira Ƙasar Bakura (gamers, Aug 11,2018).

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Taswirar Jahar Zamfara, Nijeriya

Garin Bakura na ɗaya daga cikin manyan gundumomin Zamfara guda goma sha huɗu da suka haɗu suka yi yankin Sakkwato ta Gabas a lokacin mulkin mallaka. A wannan zamani kuwa tana ɗaya daga cikin manyan masarautun jahar Zamfara masu daraja ta farko.

            Ƙasar Bakura, ƙasa ce shimfiɗaɗɗiya wadda take kan tudu. Ba ta da yawan kwazazzabai, haka kuma ba ta da duwatsu, sai dai akan sami tsaunuka jefi-jefi a wurare daban-daban kamar: Dutsin Damɓo da Dutsin Yami da Dutsin Jauga. Gulbin Sakkwato ya ratsa ƙasar ta Bakura, wanda ya fito daga Gusau ya zarce zuwa Sakkwato. Shi wannan gulbin ya saki fadamu da dama a ƙasar, saboda wasu ƙoramu da suka haɗe da shi a cikin yankin, kamar na Ɓoɓo wanda kan kai wa tabkin Natu ruwa. Haka kuma tana da yanayin ƙasar noma mai albarka, tudu da fadama. Ƙasar da ke kan tudu akasari jigawa ce wadda ake iya noma kayan abinci da na sayarwa. Kayan abincin da ake nomawa sun haɗa da gero da dawa da maiwa (dauro). Su kuma kayan sayarwa waɗanda ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, sun ƙunshi auduga (kaɗa) da gyaɗa da wake. Fadama kuwa kamar yadda aka sani tana da ƙasa mai laka da damɓa-damɓa, wadda ake amfani da ita wajen noman rani da na damina, a inda akan shuka shinkafa da rake da masara da rogo da dankali da sauran kayan lambu. Hasali ma kusan noman rani da ake yi a madatsar ruwa ta Bakalori kusan kashi sittin da biyar a ƙasar Bakura ake gudanar da shi.

            Irin wannan yanayi na ƙasar noma mai albarka shi ya jawo hankalin wasu mashahuran mutane har suka zo Bakura suka yi gonaki, cikin su kuwa akwai Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato. Haka ma Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta gina wata haraba a Bakura domin nazari da binciken dabaru da hanyoyin noma na zamani. Allah Ya albarkaci yankin da wadatattun ruwan ƙarƙashin ƙasa fiye da sauran makwabtanta.

            Ƙasar Bakura tana da daji mai yawan gaske, sai dai bai cika sarƙaƙiya kamar na ƙasar kurmi ba. Amma akan sami namun daji a cikinsa can ba a rasa ba. Haka kuma ƙasar tana da itace da ke taimaka wa jama’ar ƙasar wajen inganta tattalin arzikinsu, kamar itacen kuka (murna ko miyar kaɗi) da ɗorawa da tsamiya da mangwaro da bagaruwa da kaiwa da kaɗe da ɗunya da sauransu.

4.0 Asalin Mutanen Bakura

            Akwai saɓanin ra’ayi dangane da takamaiman ƙasar da mutanen ƙasar Bakura suka fito da dalilin ƙauratowarsu daga ƙasarsu ta asali da yadda aka yi har suka iso a mazaunin da suke a halin da ake ciki. Duk da haka, ba za a rasa madafa ba, domin kuwa masana sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayoyinsu gwargwadon hujjojin da suka zo a hannunsu.

            Da farko, an nuna cewa, asalin mutanen Bakura Barebari ne da suka ƙaurato daga Barno5 a farkon ƙarni na goma sha huɗu (ƙ.14), kamar yadda Bakura District Assesment Report (1916:9) da Bakura District Note Book; SSHCB Sokoto (1980:22) suka nuna. Suka zo suka zauna a yamma da mazaunin da suke zaune a yau. Bisa wannan ra’ayin an nuna cewa ba wani mahaluƙi da ya taɓa zama a wurin kafin zuwansu daga ƙasar Barno. A da can ana kiran mutanen Bakura da sunan Barebari ne, sai daga baya aka yi musu laƙabi da Ɓurmawa.

            A wani ra’ayi da Harris (1938) da Magatakardan Sarkin Ɓurmin Bakura, Malam Yahaya suka bayar, ya nuna cewa, Ɓurmawa sun yi ƙaura ne daga wani wuri da ake kira LARABA-GARDA a can cikin ƙasar Barno, ɗaruruwan shekaru da suka shuɗe. Wannan ya faru ne a sakamakon wata rashin jituwa da ta auku saboda neman sarautar da ta faɗi. Domin kauce wa wulaƙanci da tsangwama daga Sarkin da ya hau karaga, sai abokan takarar su uku suka yi ƙaura tare da mabiyansu. A kwana a tashi har Allah ya kawo su mazaunin da suke yanzu. A wannan bayanin an nuna cewa, su waɗannan mutane uku ‘ya’yan sarki ne, hasali ma uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya da wanda ya hau karagar mulki, wanda kuma shi ne babbansu. 

            A wata faɗar kuwa an nuna cewa, mutanen Bakura malamai ne masu tsoron Allah da ke aiki da ilminsu, sun baro ƙasarsu ta asali wato Barno a sakamakon buɗin da Allah ya yi musu na busharar cewa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da zai bayyana a wannan nahiya ta ƙasar Hausa. Samun wannan fatahi, sai suka ƙaurato daga mahaifarsu, suka dawo wannan nahiya suna masu jiran bayyanarsa domin su taimaka masa wajen jaddada addinin Allah a bayan ƙasa. Wannan ya so ya yi kama da irin abin da kakan Barebari wato Tubba’u ya aikata dangane da imani da Annabi Muhammadu (SAW), tun kafin bayyanarsa fiye da shekara dubu (Gana, 1965:39). Su ma al’ummar wannan ƙasa haka suka aikata, musamman idan aka yi la’akari da yadda Sarkin Ɓurmin Bakura Wakaso ya bar sarautar na wani lokaci, ya tare wurin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo domin ya bayar da gudummawa wajen jaddada addinin Musulunci. Haka kuma wannan ra’ayi na iya samun madafa idan aka yi la’akari da yadda sauran al’ummar ƙasar suka tsunduma wajen neman ilmin addini da kuma yaɗa shi a farfajiyar ƙasar Hausa. Malam Yahaya ya ƙara da cewa, a lokacin da suka taso daga LARABA-GARDA tun a ƙarni na 14, sun fara yada zango a Kura ta ƙasar Kano. Daga can ne suka koma wani wuri a ƙasar Katsina5. Amma saboda fargabar hare-haren Katsinawa da rashin tabbas na samun kwanciyar hankali, sai suka yi ƙaura daga ƙasar Katsina har suka iso mazaunin da suke a yau.

            Da farko an bayyana cewa, sun fara zama ne a wani wuri da ake kira “AJI GISHIRINKA”, kimanin mil biyar daga garin Bakura a halin yanzu. Ganin cewa, wannan wuri ya zama mashiga ce ga dakarun Gobirawa, wannan ya tilasta musu yin ƙaura suka koma sabon garin Bakura. Daga nan kuma suka koma garin Jabo da ke cikin jahar Sakkwato ta yanzu domin su kare kansu daga hare-haren Kanta. Bayan shekaru da dama, sai suka yanke shawara a kan su dawo inda garin Bakura yake a halin da ake ciki yanzu domin su kafa mazauni na din-din-din.     

            Saboda haka za mu iya cewa al’ummar ƙasar Bakura sun zauna wurare daban-daban kafin daga ƙarshe su zauna a Bakura da Tureta. Sai dai tarihi ya bayyana mana cewa wani ɓangaren mutanen Tureta sun cigaba da yawace-yawace kafin daga baya su zauna a Tureta ta yanzu, kamar yadda Bakura District Note Book (1980:23) ya nuna. Daga cikin wuraren da mutanen Bakura suka yada zango sun haɗa da: 1. Ɗunɗaye, 2. Gumyu, 3. Gwamatse, da cikin jahar Sakkwato ta yau, daga ƙarshe suka zarce mazaunin da suke a halin da ake ciki yanzu.

            A wani ra’ayin kuwa ya nuna cewa tushen al’ummar Bakura daga wasu shahararrun mutane ne su huɗu, waɗannan mutane kuwa su ne: 1. TULU, 2. WARKU, 3. JANDAMO, 4. BUREMA. Waɗannan mutane sun ƙaurato daga ƙasar gabas6 ne, suka zo suka kafa garuruwa huɗu waɗanda duk sunan sarautarsu yana ɗauke da laƙabin Sarkin Ɓurmi. Hasali ma idan aka duba fuskokinsu za a ga suna da alama ta fashin-goshi, wadda ke bayyana al’ummar da suka fito daga cikinta. Garuruwan kuwa sun haɗa da garin Bakura da Tureta da Jabo da kuma Moriki.

            Lokacin da Bakurawa suka isa ƙasar da suke zaune a cikinta, sun tarar da wani ɓangaren ƙasar yana ƙarƙashin mulkin Kabawa, yayin da ɗaya sashen ke ƙarƙashin kulawar Zamfarawa7. Bayan sun yi cikakken nazari sai suka yada zango a cikin ƙasar Zamfara. A daidai wannan lokaci ne suka taimaka wa Zamfarawa a fagen fama a matsayin sojojin haya, wato lokacin da Zamfarawa ke yaƙi da Kabawa, kamar yadda Bakura Disstrict Note (1980:22) ya nuna. A sakamakon taimakon da al’ummar Bakura suka bayar wajen yaƙar Kabawa, wanda ya haifar da samun gagarumar nasara, wadda ta samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya, ya sa Sarkin Zamfara ya ba al’ummar Bakura wani ɓangaren ƙasar da suke zaune a ciki a matsayin ladar yaƙin da suka taimaka (‘Yarkufoji, 1994 : 45).

5.0 Asalin Sunan Sarautar Bakura Da Na Al’ummarta

            Abu ne mai matuƙar wuya, mutum ya fito gaba-gaɗi ya bugi ƙirji farar ɗaya ya ce zai bayyana asalin samuwar sunan wata al’umma da sarautarta, ba tare da ya waiwayi abin da magabata suka bayyana ba. Ko ba komai, ai Hausawa sun ce, da tsohuwar zuma ake magani. Saboda cimma wannan manufa ne, ya zama tilas a koma baya don kalato ra’ayin magabata.

            Sunan al’ummar Bakura wato “Ɓurmawa” ya samo asali ne tun kafin su yi ƙaura daga ƙasarsu ta asali, Barno. Masu wannan ra’ayin sun bayyana cewa, Galadiman Barno ne na wancan lokaci ya laƙaba musu suna “Ɓurmawa”, kamar yadda Harris (1938:119) ya nuna. Yayin da Danial (1916:9) ya ce Sarkin Kukawa. Masu wannan ra’ayin sun nuna cewa, da Sarkin Kukawa zai tafi yaƙi, sai ya bar wa jikansa alhakin kula da lamurran ƙasar. Sarkin ya kwashe tsawon shekara bakwai wajen yaƙi. Bayan ya dawo, sai ya tarar da jikan nasa ya huda (ɓurme) taskarsa ya kwashi wasu abubuwa daga cikinta. Daga lokacin ne ya kira jikan nasa Sarkin Ɓurmi.

            A wani ra’ayi an nuna cewa an samo sunan ne daga sunan ɗaya daga cikin shugabanninsu mai suna “Bureme”, kamar yadda Bakura District Note (1980:119) ya nuna,  wato mutanen Burema ko Buremawa. Da tafiya ta yi tafiya, sannu a hankali sai sunan ya sauya ya koma Ɓurmawa.

            Daga nan ne aka rinƙa kiran jagoransu da sunan shugaban Ɓurmawa. Daga bisani sai aka rinƙa kiransa Sarkin Ɓurmawa. Saboda tsawon zamani da sauye-sauyensa da aka samu, sai sauyin ya yi tasiri matuƙa har ya kai ga shafuwar tsarin ginin kalmar ta koma Ɓurmi. Sai aka cigaba da kiran jagoran al’ummar da suna “Sarkin Ɓurmi”. Ke nan wannan ra’ayin yana nuna mana cewa sunan al’ummar Bakura da na shugabansu wato “Ɓurmawa” da “Sarkin Ɓurmi”, sun samo asali ne daga sunan shugabansu na farko da ake kira da suna “Burema”.

            A wani ƙauli kuma an bayyana cewa Sarkin Zamfara ne da kansa ya bayar da sunan sarautar, ta “Sarkin Ɓurmi”, kamar yadda Yahaya (1993) ya bayyana a Rima Rediyo (‘Yarkufoji, s1994). Masu wannan ra’ayin sun bayyana cewa, Bakurawa sun taimaki Sarkin Zamfara a lokacin da yake yaƙi da Kabawa, inda suka nuna bajinta da jaruntaka, suka fatattaki Kabawa. Bayan Wari ya nuna bajinta ne, sai Sarkin Zamfara ya mallaka musu mazaunin da muƙamin “Sarkin Ɓurmi”. Sai dai su ma masu wannan ra’ayin ba su bayar da wata hujja da ta sa Sarkin Zamfara ya kira wannan sarauta ta Bakura da laƙabin Sarkin Ɓurmi ba.

            Wani ra’ayi kuwa ya nuna cewa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ne da kansa ya raɗa wannan suna na Ɓurmawa, sarkinsu kuma Sarkin Ɓurmi, kamar yadda Alhaji Shehu Bunu (2003) ya bayyana. Wannan ya auku ne saboda irin jaruntakar da Sarkin Ɓurmin Bakura Son-Allah da jama’arsa suka nuna wajen fasa rundunar abokan gaba a Tabkin Kwatto, a lokacin da ake yin jihadi (‘Yarkufoji, 1994 : 42).

            Saboda haka, idan aka yi la’akar da kalmar Ɓurmi, za a tarar an samo ta ne daga kalmar aikatau da ake kira da ‘Ɓurma’ wadda a luggance tana ɗauke da ma’anar ‘yanke daga ƙarshe’, haka kuma tana nufin “hudawa” ko “fasawa”, wato kamar a ce: “Ya ɓurma masa wuƙa a ciki”, ma’ana,  ya huda masa ciki da wuƙa, ko ya fasa masa ciki da wuƙa”.

Saboda haka, ta la’akari da ma’anar kalmar a iya cewa sunan ya samo asali ne bayan an ga irin yadda suka nuna jaruntaka ta wajen yi wa rundunar yaƙin abokan gaba, yankan batta. Domin kuwa a tsarin kalmomin Hausa akan samu sunan ma’aikaci daga sunan aiki. Kuma ina kyautata zaton cewa, ta haka ɗin ne aka samar da sunan al’ummar, wato Ɓurmawa, abin nufi masu iya karya kowace irin rundunar yaƙi ta abokan gaba.

            Ita kuma sunan sarautar, wato Sarkin Ɓurmi, an laƙaba wa jagoran Ɓurmawa ne domin kasancewar sa ƙwararre jarumi mai dabarun yaƙi iri-iri, wanda bai da fargaba in ya so ya fasa rundunar abokan gaba, ta yadda za su gigice, su tarwatse. Haka kuma idan muka yi la’akari da yadda Barebari ke yi wa mai suna Ibrahim laƙabi da Buraima ko Burema ko Bura, ma iya cewa an samo sunan ne daga sunan Sarkin Ɓurmi na uku wanda ya yi mulki daga shekara ta 1375 zuwa 1407. Hasali ma laƙaba wa al’umma sunan shugabansu don a nuna cewa su mabiyansa ne abu ne da ya daɗe, akwai Malikawa da Shafi’awa, waɗanda ake nuni da cewa mabiyan mazhabobin Imam Maliki da Shaf’i ne.

6.0 Haɓakar Garin Bakura

            Idan aka ce haɓaka, a nan ana nufin abu ya girma, ya bunƙasa, ya kai wani mataki na gawurta har ya zama ya ƙasaita kowa ya san da zaman abin.

Saboda haka, nan bayani ya zo ne game da yadda garin Bakura ya girma, ya gawurta har ya samar da wata ƙasaitacciyar masarauta da za a iya bayyana ta da shahararriyar masarauta da ta samar da manyan bayin Allah da suka yi fice a doron ƙasa. Wannan ƙasa ta samu yin fice ta fuskoki da dama da suka haɗa da fannin yaƙe-yaƙe da kuma fannin ilimin addinin Musulunci da ke tattare da tawali’u da gudun duniya.

6.1 Gina Ganuwar Bakura

            Ganuwa, wata babbar katanga ce da ake zagaye gari da ita domin bayar da kyakkyawan tsaro da kariyar rayuwa da dukiyoyi da mutuncin al’umma. Samuwar ganuwa ga kowane irin gari wata alama ce da ke iya nuna tabbatar da bayar da cikakkiyar kariya ga al’ummar da ke zaune a wannan gari, domin takan ƙara jawo masa haɓaka da Bunƙasa ta fuskoki da dama.

            A lokacin mulkin Sarkin Ɓurmin Bakura Mayaƙi 1691 zuwa 1736 ne aka fara gina ganuwar garin Bakura. Sarkin ya aiwatar da wannan aiki ne domin ya samar da cikakken tsaro da kwanciyar hankali ga al’ummarsa. Ganuwar dai tana da ƙofofi huɗu ne kamar haka:

·         Ƙofar Bai: Ita wannan ƙofa tana Gabas ga gari ne, ita ce mashigin mutanen Rini.

·         Ƙofar Acale: An yi ta ne a Yamma.

·         Ƙofar Baici: An gina ta ne a Arewa.

·         Ƙofar ‘Yan Sarki: Ita kuwa an yi ta ne a ɓangaren Kudu.

Samuwar ganuwa a Bakura ya sa aka rinƙa samun mtane suna ƙauratowa daga ƙasashensu suna zuwa Bakura domin su sami cikakkiyar kariya da kwanciyar hankali. Wannan ne ya haifar da wanzuwar Gobirawa da Zamfarawa a cikin garin Bakura. Zuwan waɗannan rukunin al’umma ya sa Bakura ta bunƙasa tun a lokacin da ake yaƙe-yaƙe ta hanyar amfani da ƙarfin cin hatsi.

6.2 Bunƙasar Masarautar Bakura Ta Fuskar Yaƙe-Yaƙe Da Zuwan Baƙi

            Sau tari idan aka sami wani shahararren mayaƙi da ya kai wa gari harin yaƙi bai sami nasara ba, wannan kan sa a sami wasu jinsin mutane su yo ƙaura daga mazauninsu na asali su dawo wannan gari domin su sami cikakkiyar kariyar rayuwa da ‘yanci da dukiya ta yadda za su sami walwala da kwanciyar hankali. Haka kuma idan aka kai wa gari harin yaƙi aka laƙume shi, sai al’ummar wannan gari su watse su je su nemi mafaka a wasu garuruwan da suka tabbatar za su sami kyakkyawar kariya da tsaro na duk wani farmakin mayaƙa da ka iya tasowa. Masarautar Bakura na ɗaya daga cikin ƙasashen da bajinta da gwarzontaka a fagen fama (yaƙi) ya kawo mata bunƙasa ta hanyar zuwan baƙi don su tsira da mutuncinsu. Hasali ma idan aka bi diddigin tarihi za a tarar cewa tun kafuwar wannan gari har zuwa lokacin Turawa ba wata ƙasa da ta taɓa cin ƙasar Bakura da yaƙi, sai dai ƙasar ta kuɓutar da makwabtanta daga harin fin ƙarfi.

            Wannan ne ya haifar da son wasu sarakuna na neman su ƙulla ƙawance da wannan masarauta, misali kamar ƙawancen Banaga Ɗanbature8 da Sarkin Ɓurmi Bahago9. Duk da kasancewar Banaga Ɗanbature ya shahara da sanin dabarun yaƙi iri-iri, amma yana shakkar Bahago, don haka, sai ya rinƙa aika wa Sarkin Ɓurmi Bahago da wasu wurudda domin ya ƙara tabbatar masa da ƙaunar da ke tsakanin sa da shi. Banaga ya yi haka ne kamar yadda bincike ya nuna, domin Sarkin Ɓurmi da jama’arsa su ba shi haɗin kai wajen yi wa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo tawaye (Bagobiri, 1985).

            Jaruntakar Bahago da yawan roƙon Allah sun sa har Bawa Jangwarzo ma bai taɓa izgilin kawo wa wannan masarauta yaƙi ba. Hasali ma har an yi lokacin da Sarkin Ɓurmi Bahago ya ƙwaci al’ummar Tureta daga hannun Bawa Jangwarzo, (Bagobiri, 1985). Don haka muna iya cewa, al’ummar wannan masarauta zarumai ne, kuma duk inda zarumai suka kai, su ma sun kai.

            Masarautar Bakura ta kafu ta kuma bunƙasa ta kuma wuce tsara da wasu siffofi da suka keɓanta ga al’ummar wannan ƙasa na zamansu zarumawa, ta hanyar nuna ƙarfin hali da juriya da son zumunta da riƙon addini tare da ƙoƙari yaɗa shi. Haka kuma ga su da tawali’u da tsoron Allah wanda ya sa musu gudun abin duniya. Irin waɗannan halaye sun taimaka musu ainun wajen kafa ƙasarsu tare da faɗaɗa ta har aka wayi gari ta kasance ta bunƙasa ta hanyar ciye wasu ƙauyuka da garuruwa da suke zagaye da ita, waɗanda yaƙe-yaƙe suka auku a tsakaninsu a yayin da suka takale ta.

            Daga cikin garuruwan da ta ciyo a zamanin da ake yaƙe-yaƙe, sun haɗa da: 1. Gandi, 2. Rara, 3. Nasarawa, 4. Damɓo, 5. Rini, 6. Ɗankadu, 7. Birnin Tudu, 8. Ruwan Ɓora,  da kuma 10.Gorar Daji, kai har ma sai da ta cinye rabin garin Talata Mafara, wanda ya kai har Ɗankura, bakin tsohon gidan sarautar garin, wannan ya auku ne a zamanin mulkin Sarkin Mafara Ɗambaƙi , kamar yadda Edgar (1911) da Bunu (2003) suka nuna.

Amma daga baya sai aka kafa iyaka a ‘Yargeda, maimakon a tsakiyar garin Talata Mafara kamar yadda sharuɗɗan yaƙi suka tanada. Wannan ne sanadin wasa a tsakanin Mafarfari da Ɓurmawan Bakura. Haka a karon batta da masarautar ta yi da masarautar Anka, Bakura ta fatattaki Anka a inda ta laƙume garin Damri da sauran garuruan da ke ƙarƙashinsa. Sai dai daga baya an sami ƙulla zumunta a tsakani, a inda Sarkin Ɓurmin Bakura Isan Na-Abu ya aurar da ‘yarsa mai suna Maimuna ga Sarkin Zamfaran Anka Abubakar Bawa Adam wanda ya yi mulki daga 1829 zuwa 1853. Ya samu haihuwa da ita ta ɗa namiji mai suna Muhammadu Farin Gani wanda ya yi sarautar Anka har sau biyu. Na farko daga 1896 zuwa 1899, karo na biyu daga 1928 zuwa 1946. Shi ma ya auro ma ɗansa da ake yi wa laƙabi da Sardauna Yaro, mata mai suna A’ishatu daga shahararren gidan nan na Magazawa Bakura. Matar ta haifa wa Sardaunan ɗa da aka sani da Malam Sulaiman Anka (Magatakarda Malam Sule Anka).

            Babu shakka, za a iya cewa al’ummar wannan masarauta ba kanwar lasa ba ce, domin sun nuna bajinta da ƙwazo da jaruntaka tamkar yadda Fulani suka nuna a ƙoƙarin da suka yi na tabbatar da kalmar Allah. Wannan shi ya sa har suka kai ga kafa garuruwa na ƙashin kansu tare da samun cikakken iko a kan ƙasashen da suka ci da yaƙi. Samun nasarar ragargaza ƙasashen da suka laƙume ya ba su damar maye gurbin gidajen sarautar da nasu, ta hanyar naɗa wasu sarakuna daga cikin zuriyarsu. Da tafiya ta yi tafiya sai aka rinƙa ƙulla dangantaka ta hanyar auratayya a tsakani. Saboda haka ne aka sami garuruwa guda takwas a cikin masarautar da suka zama suna da kusan asali ɗaya da jama’ar Bakura, har ma hakan ya ƙara taimakawa wajen samar da haɗin kai da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al’ummar da kuma sarakunan da ke wannan masarauta. Hasali ma sai aka wayi gari suna ganin sun fito ne daga tsatso ɗaya.

            A sakamakon tsawon zamani da wanzuwar mulkin masu jihadi da na Turawan mulkin mallaka sun haifar da rage faɗin ƙasar masarautar Bakura. Misali an fitar da garuruwan Gandi da Ruwan Ɓorai da Ruwan Gizo da Gorar Daji da Barikin Daji daga cikin ƙasar. Wasu aka mayar da su ƙarƙashin masarautar Talata Mafara, Gandi kuwa ta sami ‘yancin kanta.

6.3 Bunƙasar Masarautar Bakura A Zamanin Turawan Mulkin Mallaka

            Kasancewar masarautar Bakura na ɗaya daga cikin masarautun da ke ƙarƙashin Daular Usmaniyya tun kafin zuwan Turawa, kuma Sarkin yana daga cikin muƙaraban daular, ya sa Gwamna Lugga ya yi taro na musamman da muƙarraban daular, domin su fitar masa da wanda ya dace ya zama Sarkin Musulmi, bayan Sarkin Musulmi Attahiru na 1 ya yi hijira. Jagoran wannan masarauta, Sarkin Ɓurmi Ahmadu Bafillace yana ɗaya daga cikin waɗanda aka gayyata a wancan zama (Kani & Gandi, 1990: 31). Saboda sarakunan yankin sun kasance cikin Majalisar Sarkin Musulmi tun zamanin jahadin Shehu Usman har zuwa lokacin Sarkin Musulmi Abubakar III ya kawo wasu  sauye-sauye a 1945 da suka haifar da cire sarakunan da ke majalisar tun zamanin Shehu, kamar: Sarkin Ɓurmin Bakura Yahaya (1937-1960) da Sakin Katsinan Gusau Marafa Ibrahim (1945-1948) da Sarkin Kiyawa Muhammadu Asha (1929-1952).  Wannan ita ce farkon ƙulla dangantaka tsakanin Turawa da masarautar.

            Aikin farko da Turawa suka fara ƙaddamarwa a masarautar shi ne buɗe ofishin gunduma, wanda suka aika da jami’i don ya kula da ayyukan da sarakuna ke aiwatarwa. Haka kuma sun gina titin mota da ya tashi daga Bakura zuwa lamba wanda ya haɗe da babban titin da ya fito daga Sakkwato zuwa Gusau.

            Idan aka karkato ta ɓangaren ilimin zamani za a tarar cewa, a shekarar 1945 Turawa suka gina makarantar Boko ta farko a garin Bakura. Haka sun gina ƙaramin ɗakin shan magani don amfanin jama’ar da ke masarautar.

6.4 Bunƙasar Masarautar Bakura Bayan Samun Mulkin Kai

            al’ummar masarautar Bakura, su ma kamar sauran kowace al’umma suna sane da irin yadda Turawa suka fakaice da mulki domin tsotse arzikin ƙasa tare da yin katsalanda a harkokin da suka danganci addini da makamantansu. Wannan shi ya sa suka tashi gadan-gadan suka tsuduma wajen yunƙurin ganin cewa, Turawa sun bayar da mulkin kai. Domin sun fahimci cewa, ta hanyar fafutukar neman ‘yanci ne kawai za a iya samun bunƙasar tattalin arziki da cigaban addinin Musulunci a cikin wannan ƙasa. Wannan magana a bayyane take, domin kuwa Sarkin Ɓurmi Yahaya ya fito fili ɓaro-ɓaro ya bayyana ra’ayin al’ummarsa a yayin da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya ziyarci masarautar a cikin shekara ta 1955 (Yahaya, 1993) kamar yadda ‘Yarkufoji (1994) ya nuna. Sarkin ya gabatar da jawabinsa a inda yake cewa:

                                    Ni Sarkin Ɓurmi da mu da jama’armu, muna ba da

                                    goyon baya ɗari bisa ɗari a kan yunƙurin da kuke

                                    yi na ganin cewa, ƙasarmu ta samu ‘yancin kai.

Samun mulkin kai ke da wuya sai masarautar Bakura ta fara bunƙasa ta fannoni daban-daban. Misali a fannin ilmin zamani, an sami cigaba, domin kuwa an sami damar gina makarantar firamare a ƙarƙashin Ƙungiyar Jama’atul-nasru Islam. Ta ɓangaren gwamnati kuwa, a shekarar 1960 ne aka ɗaukaka makarantar farko da Turawa suka gina zuwa makarantar firamare ta cikin gari da ƙara gina wasu azuzuwa domin a sami damar ƙara yawan ɗalibai. Haka an sami damar giggina wasu makarantun a wasu sassa da ke faɗin masarautar. A cikin shekara ta 1975 ne aka kafa Makarantar Horon Malamai a cibiyr masarautar. Makarantar ta fara zaman wucin-gadi a Talata-Mafara.

            Haka huma an sake buɗe ƙananan makarantun sakandare guda biyu a yankin masarautar a cikin shekara ta 1980. A cikin shekara ta 1983 aka sake buɗe wata makarantar firamare a Sabon Garin Bakura. Haka kuma an buɗe ofishin ilmi don ya kula da yadda ake tafiyar da lamurran ilimin makarantun firamare.

            A fannin noma kuwa, idan aka duba za a iya cewa duk faɗin masarautun da ke jahar Zamfara ba wata masarauta da ta bunƙasa fiye da masarautar Bakura ta wannan fuska. Domin kuwa a wannan masarauta Sardauna ya yi gona wadda aka shuka abubuwan da a wancan lokacin ba gonar da za a same su a duk faɗin lardin Sakkwato, sai a gonar. Haka kuma an gina asibitin dabbobi a Bakura. Noman rani ya bunƙasa matuƙa a farfajiyar wannan masarauta a sakamakon gina madatsar ruwa da aka yi a masarautar Maradun. Wannan ya sa masarautar ta zama mafi rijaye daga cikin ƙasashen da ke noman shinkafa a duk faɗin jihar Zamfara. Manoman yankin ba sun tsaya kaɗai ga noman shinkafa ba ne, har da wasu kayan ci da na sayarwa, wato kamar masara da alkama da wake da rake da tumatir da dankali. Masarautar ita ce gundumar da ta fi kowace ƙasa noman dankali a duk faɗin Nijeriya. Ganin irin yadda noma ke haɓaka a wannan masarauta shi ya sa aka kafa makaranta don inganta noman rani a masarautar wadda ake kira da SCHOOL OF IRRIGATION AND EXTENTION SERVICES. An yi haka domin a koyar da manoma dabarun noman rani na zamani. Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta buɗe haraba ta Kwalejin Aikin Noma a cikin gundumar, daga baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta karɓi wurin domin nazarin kimiyyar fasahar noma ta zamani.

       Bayan samun mulkin kai, gwamnati ta yi ƙoƙarin inganta harkokin kiyon lafiya ta hanyar gina ƙananan ɗakunan shan magani a wasu sassan wannan masarauta. A cibiyar masarautar kuma aka gina asibiti domin kula da lafiyar al’ummar wannan ƙasa.

            Ta fuskar sufuri kuwa, abubuwa sun bunƙasa a inda aka sami hanyoyin mota da suka haɗa wannan masarauta da wasu yankuna da ke maƙwabtaka da ita. Misali an gina hanyar da ta fito daga Sakkwato ta biyo ta Raɓa da Gandi ta faɗo Bakura ta zarce lambar Bakura a inda ta haɗe da titin da ya fito daga Gusau zuwa Sakkwato. Yin titin ne ya haifar da wanzuwar gina gadar Bakura. A ɗaya hanyar kuwa da ta fito daga sashen ‘Yarkufoji da Birnin Tudu da Rini ita ma ta sami bunƙasa a inda aka gina gada tare da shimfiɗa wa wani sashe kwalta. Haka an zuba kwalta a cibiyar masarautar.

            Ta fuskar samar da abubuwan jin daɗi inganta walwalar jama’a, a cibiyar masarautar ta sami rijiyar burtsatse, haka kuma garuruwan da ke cikin masarautar sun sami fanfunan tuƙa-tuƙa, haka a mafi yawan ƙauyuka. Wani muhimmin abu da ya taimaka wajen haɓaka masarautar shi ne ƙirƙiro ƙaramar hukuma da aka yi. Da farko ƙaramar hukumar tana ƙunshe da masarautu biyu ne, masarautar Tureta da masarautar Bakura. Amma bayan ƙirƙiro jihar Zamfara, masarautar ta sami ɗaukaka a inda aka bar ta a matsayin ƙaramar hukuma ita kaɗai. Samar da ƙaramar hukuma ya wanzar da samuwar sashen ilmi da kuma wata sabuwar kasuwa. Duk waɗannan abubuwa da suka faru a wannan masarauta sun taimaka wajen haɓakarta ta kowace fuska da suka haɗa da ƙaruwar yawan al’umma da tattalin arziki da ƙarin shigowar baƙi. wannan ya sa masarautar ke ƙunshe da ƙabilu daban-daban da ke zaune a cikinta kamar:

Ɓurmawa (Barebari) da Fulani da  Zamfarawa da  Gobirawa da Buzaye da Yarbawa da Igbo (Inyamurai).

7.0 Gidan Sarautar Bakura

            Daga abin da muka gani za a lura da cewa, asalin sarakunan masarautar Bakura sun fito ne daga tsatso ɗaya tun ranar da aka fara sarautar Bakura. Shi wannan babban gida, Muhammadu Kura ne ya kafa shi, wanda Turawa ke yi wa laƙabi da WARIOR a Turance, wanda ke nufin “Gwarzo” ko “Zarumi” ko “Mayaƙi” ko kuma “Barde”. Abin kula a nan shi ne wannan gidan sarauta na Bakura ya sha bamban da wasu gidajen sarakuna da aka kafa su a lokaci ɗaya, domin an ɗora harsashinsa ne a kan tubalan addini da jaruntaka da kuma gado, musamman idan aka koma baya aka dubi tarihin kafuwar masarautar da samuwar sunan masarautar.

            Hasali ma ko da al’ummar ƙasar suka zo mazauninsu sun kasance Musulmi tsantsa da ke ƙoƙarin koyo da koyar da addinin Musulunci. Wannan shi ya sa har kwanan gobe al’ummar wannan masarauta suke cikin sahun gaba a wajen ilmin addinin Musulunci. Za a iya ganin haka a zahiri a cikin gida da kuma waje. Misali, mutanen Bakura sun tare a Tudun Wada Zariya a sakamakon gayyatar da Sarkin Zazzau Ibrahim ya yi wa jagoransu Malam Aliyu Ɗan Muhammadu Kayi ( Liman Alu) ta hannun Malan Sani Na-Ƙofar Doka, don neman yaɗa ilmi da bunƙasa shi10. Haka ma lamarin ya kasance a wasu garuruwan kusa da na nesa da al’ummar suka je, kamar Gusau, da Ƙaura Namoda da T/Mafara da  Kano da Katsina da sauransu.s Don haka neman ilmin addinin Musulunci kusan abu ne wanda talaka da Basarake kowa ke nemansa tun kafin su zauna dindindin a wannan farfajiya.

7.1 Salsalar Sarakunan Bakura

            An riga an fahimci cewa, Muhammadu kura shi ne wanda ya fara zama a wurin da aka kafa Bakura tun lokaci mai tsawo da ya shuɗe. kafin garin ya tabbata, sai da mutanen farko suka sha fama da gwagwarmaya domin ganin sun tabbatar da ‘yanci tare da samar da cikakkiyar walwala da jin daɗi ga zuriya mai zuwa. Tarihi bai bar komai ba a sake, domin ya tabbatar mana da abubuwan tunawa da ke nuna salsalar gidajen sarautar Bakura ya danganta zuwa ga mutum ɗaya ne. Ita wannan zuriya ta sarakunan Bakura tana tattare da abubuwan da suka aiwatar na tarihi da ba za a manta da su ba. Wannan ne ya sa a daidai lokacin da aka raba zarumawan Ribaɗi da aka ba Abubakar Atiku yanki Zauma (Zamfara) wadda Bakura na ciki, sai ya tare a garin Bakura saboda amincin da ke tsakaninsu da al’ummar ƙasar.

7.2 Tsarin Sunayen Sarakunan Bakura da Shekarar da Aka Hau Karagar Mulki:

1.      Sarkin Ɓurmi Zara                                                               1319    - 1337

2.      Sarkin Ɓurmi Wari                                                              1337    - 1375

3.      Sarkin Ɓurmi Ibrahim (Ilo)                                                 1375    - 1409

4.      Sarkin Ɓurmi warku Jan-Damo                                         1409    -1445

5.      Sarkin Ɓurmi Ango                                                             1445    -1493

6.      Sarkin Ɓurmi Dodo                                                             1493    -1529

7.      Sarkin Ɓurmi Tulu                                                              1529    -1574

8.      Sarkin Ɓurmi Alje                                                                1574    -1621

9.      Sarkin Ɓurmi Bagobiri                                                        1621    -1646

10.  Sarkin Ɓurmi Aliyu AL’aje                                                 1646    -1691

11.  Sarkin Ɓurmi Mayaƙi                                                                      1691    -1736

12.  Sarkin Ɓurmi Son Allah                                                      1736    -1794

13.  Sarkin Ɓurmi Wakaso                                                                     1794    -1825

14.  Sarkin Ɓurmi Bahago                                                                      1825    -1836

15.  Sarkin Ɓurmi Bawa Na-Maibarau                                     1836    -1856

16.  Sarkin Ɓurmi Yusufa Ɗankwai                                          1856    -1885

17.  Sarkin Ɓurmi Isa Na’abu                                                    1885    -1901

18.  Sarkin Ɓurmi Amadu Bafillace                                         1901    -1905

19.  Sarkin Ɓurmi Amadu Maijirgi                                          1905    -1909

20.  Sarkin Ɓurmi Manu Maikasada                                        1909    -1916

21.  Sarkin Ɓurmi Muhammadu Taude                                              1916    -1919

22.  Sarkin Ɓurmi Ibrahim Ima                                                 1919    -1937

23.  Sarkin Ɓurmi Yahaya                                                                      1937    -1960

24.  Sarkin Ɓurmi Yusuf II                                                         1960    -1970

25.  Sarkin Ɓurmi Muhammadu Mailafiya                             1970    -1981

26.  Sarkin Ɓurmi Yusuf III                                                        1981    -2001

27.  Sarkin Ɓurmi Engr. Bello M. Sani                                     2001    -2010

28.  Sarkin Ɓurmi Hasan Damri                                                            2010    -2011

29.  Sarkin Ɓurmi Engr. Bello M. Sani                                     2011    -

8.0 Kammalawa

            Daga waɗannan bayanai an fahimci cewa tushen  al’ummar Bakura ta samo asali ne daga wasu shahararrun mutane huɗu ne wato Tulu da Warku da Jandamo da Burema, waɗanda suka ƙaurato daga ƙasar gabas suka zo suka kafa garuruwan Bakura da Jabo da Moriki da kuma Tureta. Hasal i ma duk sunan sarautarsu na ɗauke da laƙabin Sarkin Ɓurmi. A sifa kuwa suna da alamar fashin goshi da ke bayyana al’ummar da suka fito daga cikinta. An nuna cewa a sakamakon gudummuwar da suka bayar wajen yaƙar Kabawa, ta wanzar da nasarar sarkin zamfara a kan Kabawa. Ita c eta zama silar ba Ɓurmawa ƙasar da ta zama mallakinsu a madadin ladar yaƙi. An kuma ji yadda aka sami laƙabin sarautar da ma na al’ummar. Akwai buƙatar manazartan wannan zamani su ƙara ƙaimi wajen taskace tarihin al’ummominsu da al’adunsu domin amfanin na baya. Zai kuma dace a samar da makamancin irin wannan fage da zai yi ƙoƙarin taskace tsofaffin al’adun bukukuwan daulolin ƙasar Hausa saboda fa’idar da ke tattare da su. Irin waɗannan abubuwa sun danganci jaruntaka da ƙoƙarin yaɗa addinin Musulunci, musamman idan aka yi la’akari da irin gagarumar gudummuwar da suka bayar a yayin da ake ƙoƙarin jaddada addinin Musulunci a zamanin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. 

 

Ƙarin Bayani

1.      Waɗanda ma bas u iya rubutu da karatu sukan taskace tarihinsu da “ka” su bayar da shi da baki, sai dai akan sami gurɓatar tarihin a sakamakon tsufan da ke wanzar da mantuwa ko dagulewar al’amurran tare da giɗimewa. Saboda haka, sahihiyar hanyar taskace bayanai it ace ta hanyar rubutawa.

2.      Saukar ruwan sama masu yawan gaske ba kafkaftawa kan haifar da cikowar magudanun ruwa, sakamakon haka kan sa gidajen al’umma su cika su batse saboda rashin wadatattun magudanar ruwa masu yalwa. Idan haka ta auku, an sami ambaliya ken an a sanadiyyar rowan sama (Abubakar, 2015:15).

3.      Tukunawa na Kudu maso Yamma da garin Bakura, ta sashen tsohon titin mota mai zuwa Lambar Bakura.

4.       Al’ummar Bakura na alfahari da zamansu Barebari da suka fito daga Barno tun a wajen ƙarni na sha huɗu (K14). Dalilin haka ne ma Ɗan Majalisar Dokoki mai wakiltar yankin ya gabatar da buƙatar neman ɗaga darajar sarkinsu domin su sami kyakkyawan wakilci a majalisar masarautu ta jaha. Ya kuma kafa hujjarsa da cewa, Sarkin Kiyawan Ƙaura yana wakiltar Filanin Alibawa ne, yayin da Sarkin Katsinan Gusau ke wakiltar Katsinawa. Sarakunan Anka da Gummi da Talata Mafara duk suna wakiltar Zamfarawa ne. Saboda haka su ma al’ummar Bakura ya kamata a yi musu adalcin da za su sami wakilci a majalisar masarautu ta jaha. Ke nan wannan ya nuna suna alfahari da zamansu Barebari.

5.      Tarin ƙasar Bakura bai faiyace muhalin ba, balle a san ƙaramar hukumar da yake a wannan zamani.

6.      Ƙasar Barno, tun a cikin ƙarni na goma sha huɗu (Ƙ14).

7.      Daular Zamfara ta kasance tun kafin zuwan Gobirawa a Unguwar Alƙali, muhallin da aka sani da Alƙalawa. Wurin ya cikin farfajiyar Daular Zamfara ne har zuwa abin da ya kai Sakkwato a inda suka yi iyaka da ƙasar Kabi wajen filin jirgin sana da ke Sakkwato. Hasali ma ƙasar Dacaɗi duk cikin farfajir Zamfara ce. Daular ta fara ƙarfi tun a ƙarni na 15 har zuwa na 16. Ta bunƙasa sosai a tsakanin 1650 zuwa 1750 lokacin da ta dinga gwabzawa da masarautar Kabbi da Kano da Azbin da Adar ( Nadama, 1977:214).

8.      Banaga Ɗanbature ya yi mulki daga ƙarshen ƙarni na 18 zuwa 1818 a lokacin da masu jahadi suka kasha shi. Ya kasance mafaɗacin sarki, mai yawan kai hare-hare da ƙone tungage da rugage. Ya kuma addabi masu jahadi da ke yankin Zamfara ( Jabaka,1985:4, Gusau da Gusau, 2012:26, Last,1967:68, Usman, 1981:135-137).

9.      Sarkin Ɓurmi Bahago ya yi mulki a farkon ƙarni na 19 zuwa 1836.

10.  Malan Aliyu ɗan Magaji Muhammadu Kayi, ya tafi Zariya a shekarar 1924, bayan ya yi karatunsa a garuruwan Gwadu da Katsina. A Gwandu ya yi karatu ne a wurin dangin kakanninsa. A Katsina kuwa ya yi karatu ne a wurin Malan Salihu Mai-gatarin Baƙi. Yayin da ya isa Zariya, ya sauka a gidan Malan Namalama da ke Tudun Wada Zariya. A daidai lokaci layi biyu ne kawai, daga Layin Sarki sai Layin Joji. Ya tafi Zariya ne sakamakon irin labarin da ya samu na ƙwarewar Malan Sani Na-Ƙofar Doka a fannin fiƙihu domin su tattauna wasu abubuwa da suka jiɓinci sashen. Malamin ne ya sanar da Sarkin Zazzau Ibrahim zuwan Malan Aliyu, kuma ya shawarci sarkin da ya riƙe malan domin yana hangen zamansa a Tudun Wada zai sa ƙasarsa ta bunƙasa. Sakamakon wannan shawara ne ya sa Sarkin ya nemi malamin da ya zauna a Tudun Wada. Ya kuma ba shi limancin wannan wuri tare da ba shi jejin (dajin) da ke wurin, don samun gida da gona, sai dai malamin bai karɓi kyautar ba. Sakamakon haka ne aka sami makarantar farko da ake koyar da fannonin ilimi a Tudun Wada Zariya wadda mutumin Bakura ya kafa. A makartar an koyar da ɗalibai masu ɗimbin yawa da suka halarci makarantar daga sassa daban-daban na nahiyar. Almajiransa sun kakkafa makarantu daban-daban a Tudun Wada da wasu ƙasashe. Daga cikin almajiransa da za a iya tunawa akwai: Malan Ibrahim Mai’yammakanta, da Shekh Malam Mu’azu Na-‘yarkufoji, da Malam Ibrahim Maigandi, da Sarkin Ɓurmi Muhammadu, da Tudun Birnin Tudu Alhaji Tukur, da Malan Ibrahim Bakura (Na’yarkuta), da Malam Sulaimanu Bakura, da Limamin Tudun Wada Liman Habibullahi, da Malan Abubakar Aliyu Fari. Har Malan Muhammadu Marwa (Maitatsine) ya yi karatu a gunsa, amma da ya ga take-takensa sai ya kore shi. Wannan makaranta ta taimaka wajen yaɗa ilimi da bunƙasa addini da kuma ƙasar Zazzau da ma Nijeriya baki ɗaya ( Habibullahi, 1989) da (Sa’adu, 1994) da (Ɗanbuzu,1994).    

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments