Ticker

6/recent/ticker-posts

Mishan Bad Da Musulmi: Tsokaci Kan Wasu Daga Cikin Ayyukan Adabin ‘Yan Mishan Cikin Hausa

 Mishan wata ƙungiya ce ta Turawa da ke da manufar gina adabin mishan a farfajiyar ƙasar Hausa, domin samar da talife-talife cikin harshen Hausa. Suna hangen ta wannan dabara ce za su sami hanya mafi sauƙi da arha da za ta taimaka musu a fagen yaɗa addinin kirista. A bisa ga irin wannan ƙuduri ne ya wanzar da dagewarsu tun a ƙasar Turai don ganin a samar da daidaitacciyar ƙa’idojin rubutun harsunan ƙasashen Afirika, ciki kuwa har da harshen Hausa. Sun kuma yi namijin ƙoƙarin sanya alamomi a wasu haruffan Romawa don su bayar da sautukan muryoyin Hausa da babu a abjadin Ingilishi. Suna sane nasararsu ta dogara ne kacokam a wuyan ‘yan asalin ƙasa da suka karɓi addininsu da hannu biyu, don da su ne za a gudanar da ayyukan yaɗa addinin, kuma shi ne ƙudurin da suka sanya a gaba da komai. Fahimtar haka ne ya sa wannan maƙala ta ƙuduri aniyar komawa fagen tarihi domin bin diddigin dabarun da nau’o’in makircin da Turawan Mishan suka ɗauka waje samun mabiya addininsu a tsakanin wasu al’ummomin Musulmi. Haka kuma an kawo dangogin adabin da suka samar a cikin harshen Hausa wanda ya haɗa har da adabin horaswa. Hasali ma Hausawa sun ce, waiwaye adon tafiya.

rubutu

Mishan Ɓad Da Musulmi: Tsokaci Kan Wasu Daga Cikin Ayyukan Adabin ‘Yan Mishan Cikin Hausa

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

1.0  Gabatarwa:

Bayyanar adabin mishan a ƙasar Hausa ba ya rasa nasaba da aƙidar‘yanɗariƙar Furotastan da ke ganin wajabcin iya karanta Baibul ga kowane kirista mai hankali, ya kuma fahimci abin da ya karanta, domin ya yi tasiri a rayuwarsu ta yau da kullun . Ba a hardace shi  cikin harshen da aka saukar da shi ba, domin ba littafi ne da za a riƙa karantawa ana sauraren amon sautinsa kawai ba. Sakamakon wannan ra’ayi ne, Cocin Furotastan ta shirya fassara Baibul cikin  harsuna daban-daban domin ba kowace al’umma dammar mallakar Baibul da aka fassara cikin harshensu ( Westerman, 1937:187).

            Kafa  ƙungiya mai suna: “ British and Foreing Bible Society” a 1804 ya taimaka wajen samar da ayyukan adabin mishan a cikin harsuna da dama, ta hanyar fassara da kuma wallafe-wallafen littattafan addinin kirista a cikin harsuna 250 da ke farfajiyar Afirka ciki kuwa har da harshen Hausa. Daga cikin ayyukan, wasu ƙungiyoyin mishan ne suka gudanar da su kai tsaye, wasu kuwa ta hanyar gudummawa da aka samo daga: “ Contenental and American Bible Society” . Mafi yawan tallafin  ya fito ne daga aljihun British and Foreign Bible Society, ( Westerman, 1937: 216).

            ‘Yan mishan sun kafa kwamitin ƙasa-da-ƙasa na majalisar mishan, domin tanadin littattafan adabin mishan. An ɗora wa kwamitin alhakin wallafa littattafai da mujallu tare da bayar da shawarwarin da za su taimaka  wajen bunƙasa adabin mishan a cikin harsuna daban- daban. Haƙar ba ta cimma ruwa ba, a sakamakon rashin samun ƙwararrun da suka naƙalci harshen Hausa. Saboda rashin naƙaltar harsunan da ilimin hikimomin al’umma da yadda suke gudanar da tarsashin rayuwarsu da tunaninsu da kuma yadda suke bayyana ra’ayoyinsu. Duk da haka sun yi ƙoƙarin samar da wani abin a zo a gani a fannin adabin Hausa.

            Dangane da haka ne, wannan maƙala ta ƙuduri aniyar kawo bayanai game da  irin ayyukan  adabi da ‘yan mishan suka aiwatar a ƙasar Hausa. Maƙalar za ta fayyace waɗanda ake kira ‘yan mishan da abin da ya kawo su ƙasar Hausa da abubuwan da suka yi da irin rawar da suka taka  wajen samar da adabin  a ƙasar Hausa. Haka an duba hanyoyin da sukabi wajen jan hankalin al’ummar ƙasar Hausa zuwa ga addininsu. Daga ƙarshe an yi tsokaci game da littattafan adabin Hausa da suka rubuta don amfanin ƙananan azuzuwan makarantun firamare.

1.0 Su Wane ne ‘Yan Mishan?

Kafin bayyana waɗanda ake kira ‘yan mishan, dole a fahimci ma’anar kalmar

Mishan. Kalmar mishan asalinta Baturiyar kalma ce, da Turawa ke kira  MISSION  suka kuma ba ta ma’anarta ta asali da suka zo da ita ƙasar Hausa. Kalmar na cikin jerin kalmomin suna gama-gari da ke cikin rukunin jinsin maza, kuma tilo, jam’i kuwa ana kiran sa “ mishan-mishan”. Kalmar na nufin  sunan wani mutun ko taron jama’a da wata ƙungiyar addini ta aika zuwa wani wuri don koyar da wata al’umma addinin kirista, ( Macmillan,2007:960). A ci gaba da bayanin kalmar an nuna cewa, tana iya ɗaukar ma’anar : “ Mutum mai yunƙurin juyar da wasu al’umma zuwa ga wata hanyar rayuwa ko aƙida ta daban”. A wani ɓangaren kuma an bayyana ta da ma’anar : “ Mai yaɗa addinin kirista”. A ma’anarsu ta ƙarshe cewa suka yi: “Mai halayya ta ɓatar da mutane, wato ya sa al’umma su aikata masha’a, ( Sa’id, 2006: 346). Su ma al’ummar ƙasar Hausa, da wannan ma’anar suka ɗauki kalmar. Saboda sun ga take- taken da Nasara suke yi wajen yunƙurin juyar da al’ummar Musulmi daga tafarkin shiriya zuwa ga tafarkin ɓata, wato aƙidar kiristanci. Wannan ne ya sa, Hausawa kan kira duk mutumin da ke da halayyar yaudarar al’umma ya sa su aikata abin da shari’ar Musulunci ta hana, da sunan mishan. Wani zubin sukan ƙara da ɓad da Musulmi.

            ‘Yan Mishan a nan, yana nufin: “ Tawaga ko ayarin Kiristoci da ke ƙoƙarin yaɗa addinin kirista a tsakanin al’umma. Yayin da tafiya ta miƙa, sunan ya haɗe da dukkan ilahirin mabiyan addinin Kirista. Wato bai keɓanta ga waɗanda ke ƙoƙarin koyar da jama’a addinin don yaɗa sa ba a tsakanin al’umma.

2.1  Me Ya kawo Su Ƙasar Hausa?

            Addinin Kirista ya zama addinin ƙasar Turai baki ɗaya, da suke hangen yaɗuwarsa da bunƙasarsa zai ƙara tabbatar da faɗaɗuwar ƙarfin mulkin ƙasashen Turai a kan yankunan da ya shiga. Buxton ya bayar da haske a kan lamarin inda ya ce: “ Ta hanyar ayyukan ‘yan mishan ne aka gina tsarin yanayin zaman al’ummar ƙasar Turai, bisa tafarkin bautar da marasa ƙarfi a zamanin da. Da fataucin bayi ya wargaje, sai aka maye gurbinsa da aƙidar yaɗa addinin kiristanci da cigaban yammacin ƙasar Turai” ( JH.SN, No.3, Dec., 1962: 283).

            Ya kamata a fahimci cewa, wayewar kan al’ummar yammacin ƙasar Turai da yaɗuwar addinin Kiristanci abu ne da ya zama tamkar jini da tsoka, da suka daidaitu don cimma manufa ɗaya. Manufar kuwa ba ta zarce kafuwar addinin kiristanci tare da samar da wani sabon yanayin da zai taimaka musu wajen bunƙasar rayuwar al’ummarsu da cigaban tattalin arzikinsu ta hanyar tabbatar da kafuwar mulkin mallaka a farfajiyar ƙasar Afirka, ciki kuwa har da ƙasar Hausa. A daidai shekarar 1800, aka samu wasu mutane da ke da manufar farfaɗo da lamurran addinin kirista da raya shi a ƙasar Turai, waɗanda suka nuna rashin gamsuwarsu game da yadda al’ummar ke yi wa lamurran addinin riƙon sakainar kashi a Ingila. Manufar waɗannan mazajen ta haɗa da:

1.      Kafa ingantaccen harsashen da zai taimaka wajen yaɗa addinin kiristanci a nahiyar Afirka, da ma ƙasar Hausa.

2.      Samar da kyakkyawan yanayi ingantacce a nahiyar da zai tallafa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasashen Turai, ( Afolalu, 1981).

Daga wannan za a iya fahimtar cewa, Turawan Mishan sun zo ƙasar Hausa don juyar da al’ummar ƙasar zuwa ga addinin kirista domin su sami ɗimbin mabiya. Hasali ma daga bayanan da suka samu a hannun ‘yan leƙen asiri, an nuna musu cewa, al’ummar ƙasar Hausa, al’umma ce wayayyi masu ilimi da al’adu da kyawawan ɗabi’u ga kuma sanin ya kamata, tare da tunani da basira kwatankwacin na Turawa. Sun fi sauran al’ummomin da ke bakin gaɓar Teku ta kowane hali. Wannan ne ya sa suke hangen in har Hausawa suka shiga addinin kirista ba ƙaramar ƙaruwa ba ce ga addinin da kuma mabiyansa da ke ƙasar Turai, a ce an wayi gari a ga al’ummar ta kasance mai bin addinin mishan.

            Wani dalili da ya kawo su ƙasar Hausa ya haɗa da bayanan da Edward Wilmot ya yi, inda ya nuna cewa, jama’ar ƙasar Kano sun yarda  da yawancin abubuwan da addinin kirista yake magana a kai. Wato sun yarda da dawowar da Annabi Isa zai yi ( zuwansa na biyu ), wanda su ma hakan suka tabbatar zai faru. Blyden ya ƙara da cewa, irin waɗannan mutane za su fi sauƙin juyuwa zuwa ga addinin kirista fiye da sauran al’ummomin da ke bakin ruwa ( Ayandele, 1966 :120 ).

            Ire-iren waɗannan dalilai ne ya haifar da kafa wani kwamiti a Manchester a shekarar 1886 da aka danƙawa alhakin duk tafiye-tafiyen da za a yi zuwa ƙasar Hausa don yaɗa addinin mishan. An haɗa ƙungiyar jami’an Turawan Mishan a ƙarƙashin jagorancin Graham Wilmot Brook, wanda ya riya a ransa cewa, kafin wata shida duk ilahirin al’ummar Nijeriya ta Arewa za su zama mabiyan addinin kirista cikin ɗan lokaci ƙanƙani.

2.2 Me Suka Yi a Ƙasar Hausa ?

Yayin da Turawan Mishan suka zo ƙasar Hausa sun riƙa yin wata shigar ɓad da bami, suna naɗa rawani su sa doguwar taguwa irin ta Larabawa, su kuma sanya takalma fyaɗe ( ka fi Malam) a ƙafa. Har ma in sun sami taron mutane, a zazzaune, sai su yi musu sallama.

            ‘Yan Mishan da dama sun kamu da matsananciyar rashin lafiya, a farfajiyar ƙasar Hausa, wadda ta yi sanadiyyar salwantar rayukansu. Misali, ƙungiyar farko da aka turo ƙasar Hausa don yaɗa addinin mishan a ƙarƙashin jagorancin  G.W. Brooke, wasu daga cikinsu sun mutu, wasu kuma suka fice daga cikin ayarin. Shi kansa madugun tafiyar a rahotonsa da ya rubuta a 1892 ya nuna cewa, “lallai na hango rigima na tafe, domin daga dukkan alamu addinin Musulunci zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske nan gaba”, ( Ayandele, 1966: 122 ).

A daidai farkon mulkin Lugard, Turawan Mishan sun yi ƙoƙarin neman Hausawan da za su mayar zuwa ga addinin mishan, amma ba su ci nasara ba, ( Muhammad, 1991 : 92). Sun kuma kafa gari nasu na kansu, a zamanin mulkin Lugard, nan kusa da ganuwar birnin Zariya. Haka ya ba su damar zama a wani ƙauye da ake kira Gimi a wajen Zariya (Jumare,1982:34).

3.0 Mishan Da Adabin Hausa :        

Fahimtar da ke akwai na cewa ba yadda za a yaɗa addinin mishan a cikin al’ummar da ba 

a san ciki da wajenta ba, shi ya tilastawa Turawan mishan duƙufa wajen fagen nazarin harsunan al’ummar nahiyar Afirka. Daga cikin harsunan da aka fi mayar da hankali wajen nazarinsu sun haɗa da  harshen Larabci da Hausa tare da ba su kulawa ta musamman. Wannan ne ya sa ƙungiyoyi daban-daban na ƙasashen Turai suka turo waƙilansu ƙasashen Larabawa da wuraren da suka zama matattarar Hausawa don su koyi harshen Larabci da na Hausa. Sun yi hakan ne don masaniyar da suke da ita game da yadda addinin Musulunci da ilimin Larabci suka yi tasiri ga rayuwar Hausawa, musamman ma kasancewar an saukar da Alƙur’ani Mai Tsarki cikin harshen Larabci.

            A tsakanin ƙarni na 18 da na 19 ƙungiyoyin mishan suka tashi haiƙan wajen turo jami’ansu don gudanar da bincike a kan al’adu da harshe da addinin ƙasashen Afirka. Shahararru daga cikin waɗanda aka turo sun haɗa da:  J.F. Schon, da C.H. Robinson, da Hanns Vischer, da G.P. Bargery, da W.R. Miller, da sauransu, ( Malumfashi, 2009 :36). Schon ya tafi Saliyo a shekarar 1832, ya shekara 7 yana aikin yaɗa addinin kirista, tare da koyon harshen Hausa a tsakanin ‘yantattun bayi. Ya fahimci Hausa a dalilin shaƙuwarsa da yaran da likita Barth ya tafi da su Ingila. Haka  ‘yan mishan kamar Robinson da Miller da Richardson  sun koyi harshen Hausa a Turabulus ( Tripoli). Wannan ne ya ba su damar naƙaltar harshen Hausa har suka sami sukunin gina adabin Hausa.

            Ayyukan farko da ‘yan mishan suka gudanar a cikin harshen Hausa sun kasance ne ta hanyar tattara labarai da zantuttukan hikimomin al’ummar Hausawa, waɗanda suka ƙunshi karin magana, almara, kacici-kacici, zaurance, tatsuniyoyi, hikayoyi da dai sauransu. Sun same su ne ta hanyar shifta da aka yi musu da kuma wasu da suka kalato a rubuce cikin sigar rubutun ajamin Hausa, daga hannun wasu almajirai da suka nuna sha’awarsu a fannin adabin. Da irin waɗannan ayyuka ne aka gina harsashen nazari da koyar da harshen Hausa a ƙasashen Turai. Misali, J.F. Schon ya rubuta littattafai masu yawa da suka danganci adabin Hausa, daga cikinsu akwai:-  1866 :           African Proverbs Tales and Historical Fragment , London: Society For Promotion of Christion Knowledge. Littafin ya ƙunshi karin magana, da tatsuniyoyi, da wasu gutsuttsarin tarihin ƙasar Hausa. Muƙaddamar littafin ta ƙunshi wasu zantuttuka ne na Hausa da aka ciranto daga littafin “ Magana Hausa”.

1885 :  “ Magana Hausa” , London: Society For Promoting Christian Knowledge. Littafin ya ƙunshi gabatarwa da jerin haruffan Hausa da yadda ake amfani da su wajen gina kalmomi. An kuma zo da karin magana 117 daga shafi na 5 zuwa 9, wasiƙun da Dorugu ya rubuta shafi 10 – 17, daga shafi na 18 – 111 ya ƙunshi tarihin rayuwa da tafiye-tafiyen da Dorugu ya yi a ƙasashen Afirka tare da Dr. Barth. Shafi na 112 – 224 ya ƙunshi labarai da tatsuniyoyi da wasu bayanai da Dorugu ya yi wa Schon shiftar su. Shafi na 225 kuwa, bayani ne a kan yadda ake amfani da albasa wajen maganin dafin maciji. Bayani game da amfanin kare da shamuwa sun zo a shafi na 226 -227. Shafi na 228 – 230 ya ƙunshi bayanai a kan abokin Dorugu. Daga shafi na 231 – 268 kuwa, gudummawar da Rev. J.C. John ya aiko wa Schon daga Lakwaja, da ta ƙunshi bayanai game da harin kamun bayi a ƙasar Hausa da jerin tatsuniyoyi da tarihin wasu abubuwa da suka auku a rayuwa ta zahiri da suka jiɓinci ƙasar Hausa da Hausawa. Tun daga shafi na 269 har zuwa ƙarshen littafin wata gudummawa ce da Mr. G. A. Krause ya aiko wa Schon daga Turabulus, da ke ƙunshe da tatsuniyoyi da fassarar littafin ARSHADA da almar, da waƙar Ɗan Balkori da tsarin yadda ake gudanar da zaɓen sarki a Luragis ( Iwragos).

            Masana sun tafi a kan cewa abjadin da ya yi amfani da shi wajen rubuta Hausa, ya ƙunshi duk haruffan da ake amfani da su a yau, in ban da ‘yan atishawa da ‘yan zoza da hamzatattun. Ya kasa rarrabewa tsakanin ‘yan atishawa da ‘yan zoza na Hausa. Wannan ne ya sa yake yawan hautsuna su.

            A cikin abjadin da ya yi amfani da shi, babu waɗannan haruffa: /ɓ/ da /ƙ/ da /y/. wani zubin yana rubuta “gb” a madadin “b”. Haka ya kasa rarrabewa tsakanin ɗauri da gajeren wasali. Wannan ne ya sa yakan rubuta “baba” da “babba”, a wani wuri kuma yakan rubuta “dere” a madadin “dare”. Yakan rubuta “taffi” ko “teffi”  a madadin “tafi” (Newman, 1974:3-4). Wannan bai rasa nasaba da yadda Schon ya dogara kacokam a kan yaran da likita Barth ya ara masa ba, wato Dorugu da Abegga, domin su kansu ba su iya karatu da rubutu ba, a daidai lokacin da yake koyon Hausa gunsu. Masana sun tabbatar da cewa duk rubuce-rubucen da ya yi da kuma Hausar da ya yi amfani da ita ya ta’allaƙa ne gare su (Zarruƙ, 1980: 113). Hasali ma wannan dalili ne ya wanzar da taƙaitar amfanin aikinsa na nahawu ga ɗaliban da suka koyi Hausa a ƙasar Turai (Baldi, 1977: 9-10).

 

3.1C.M.S. Da Ayyukan Adabi:                                                                                           

            Ƙungiyar mishan ta C. M. S. na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin mishan da suka zo ƙasar Hausa domin ayyukan yaɗa addinin kirista a nahiyar ƙasar Hausa. Jagororin wannan ƙungiya sun taka muhimmiyar rawa waje haɓaka adabin Hausa. Wasu sun yi ƙoƙarin tattara adabin ne waje ɗaya suka taskace shi. Yayin da kuma suka samar da wani nau’in adabi da aka yi domin horar da karatu da rubutun Romawa a ƙananan Makarantu da kuma koya wa Turawa harshen Hausa. Irin waɗannan ayyukan an aiwatar da su ne  bisa ga umurnin ƙungiyar  ko kuma ƙungiyar  ce ta ɗauki nauyi wallafa su don ganin muhimmancin aikin gare ta. Wasu daga cikin irin ayyukan sun haɗa da :-

William, W. (1857), Prime of the Hausa Language,  London: C.M.S.

Schon, J.F.  (1877), Hausa Reading Book, With Grammar and Vocabularies and

                        Travellers Vade Mecum, London: C.M.S.

Robinson, C. H. (1896); Specimens of Hausa Literature.

            A cikin wannan littafin Robinson ya tattara tarihin asalin Hausawa da bayanin harshen Hausa, da ilimin hikimomin al’ummar tare da adabin Hausa. Ya kuma yi tsokaci a kan yadda adabin addinin Musulunci ya yi tasiri ga al’ummar Hausawa, musamman marubuta adabin Hausa. An zo da matanin aikin a rubuce cikin sigar Ajamin Hausa da kuma Hausar boko tare da fassara cikin harshen Turanci. Waƙoƙin da wannan littafi ya ƙunsa sun haɗa wa Waƙar Liman Ceɗiya ta “Zancen Ƙiyama”, da ta Malam Muhammadu Na Birnin Gwari, mai take: “Jabbaru Wahidi Sarki Allah”, da ta  almajirin Liman Ceɗiya, mai suna Halilu, wadda aka kira: “Wa haza alkitabu Sha’iri al’ajami”, da kuma ta Malam Muhammadu Na Birnin Gwari mai suna: “Alkitab Alrata Limansub”, da ta Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, mai suna: “Mu gode Ubangiji Sarkin Sarauta” da “Mu gode Jalla Sarki Mai iyawa”. Robinson ya kawo tarihin sarakunan Zazzau tun daga Malam Musa Babarbare har zuwa lokacin Sarkin Zazzau Usman.

Robinson, C.H. ( 1930); Hausa Grammar With Excercises, Reading and Vocabularies.

Miller, W. R. ( 1901); Hausa Notes,

Miller, W. R. ( 1933); Fatima ( A Hausa Novel).

Judd, A. S. (1932) ; Tushiyoyi Da Buƙatunsu..

C. M. S. ( 1941); Littafi Na Karantawa Da Fari. Wannan littafin adabin horaswa ne. Ya da shafuka 55. Hukumar Fassara ta ɗauki nauyin buga shi. Maɗaba’ar Church Missionart Society Bookshop, Lagos, West Africa aka buga shi a cikin shekarar 1932. A farkon littafin an gabatar da tattashiya tare da haɗa kalmomi. Haka aka cigaba har aka soma gina gajerun jumlolin Hausa. Daga nan sai aka fara gabatar da gajerun labaran Hausa. Irin waɗannan labarai sun haɗa da na:  Zabuwa da kaza,   Rashin gaski,  Daɗin Magana, Almarar wata mace da mazanta,  Almarar wani mutun da ‘ya’ya,  Almarar kuda da tubali da karmami da kwaɗo, da Almarar jemage, da Almarar makaho da gurgu, da Almarar yara masu yankan nonon dabino, da Almarar sarki da kwai, da Labarin wani yaro, da Labarin mai babban ciki da mai babban kaiu da mai siriran kafafu da mai ƙaramin kai, da Labarin alkali da tsofuwa. Haka kuma littafin ya kawo wasu labarai kamar : Labarin wani mutun da ya tafi garin kurame, da Labarin Bamaguje da mahauci Bakano, da kuma Labarin wani malami da kurege da kura, da dai sauransu. Duk labaran da almarorin suna ƙunshe da wasu darussan da ke koyar da dabarun zaman duniya. 

 

3 .2 Sudan Interior Mission ( S.I.M.)

            Wannan ƙungiya ce da ta shigo ƙasar Hausa a kan manufar yaɗa addinin Kirista a tsakanin al’ummar Nijeriya ta Arewa. Ƙungiyar kamar sauran ƙungiyoyin mishan , ita ma ta yi ƙoƙarin tsara littattafan adabin horaswa a cikin harshen Hausa don amfanin makarantun Elimantare da ke ƙarƙashin kulawarta. Daga cikin littattafan da suka rubuta tare da bugawa sun haɗa da:-

1926 : Abin da Ya Faru  ( littafin karatu).

1929 : Littafi Na Karatun Hausa, I

1930 : Littafi Na Karatun Hausa, II

1931 : Hausa, I

1933  Bishara Karatun Hausa.

1938:   Ka Ƙara Karatu.

1938: Ka Koyi Karatu.

1938:Ka yi ta Karatu.

4.0  Ɓad da Musulmi :

A sakamakon tsananin ƙiyayya da gabar da Yahudawa da Nasara da dai dangogin kafurai ke yi wa Musulmi da Addininsu na Musulunci, sun haɗa ƙarfi da ƙarfe waje ɗaya domin ƙoƙarin kawo musu shakku da ruɗu a cikin lamarin addininsu. Sun ƙaddamar da tsare-tsare da tanade-tanade iri-iri wajen ƙoƙarin ɓatar da Musulmi ko mallake musu hankulla ta hanyar shirya makirci iri daban- daban da sunan wayar da kan al’umma ko jinƙai. Irin tsarin da’awarsu da ƙungiyoyinsu, da ke aikin tura ‘yan mishan masu yaɗa manufarsu a ƙasashe dabab-daban musamman ma na Musulmi, yana daga cikin irin salon da suka ɗauka don ƙoƙarin karkatar da al’ummar Musulmi daga hanyar addininsu na Musulunci. Sun yi amfani da gina makarantu da asibitoci,  da kafa masana’antu ba don komai ba sai don ɗora Musulmi a kan muguwar hanyar da za ta kai su ga hushin Mahaliccinsu.

4.1  Kafa Makarantu :

            Ilimi wata muhimmiyar hanya ce da Turawan Mishan suka fake da ita wajen cusa aƙidojin addinin kirista a tsakanin al’umma. Sun gina makarantu da dama a sarari da ɓoye. Manufar ‘yan mishan wajen ilmantar da al’umma musamman maguzawa, ba ta wuce koyar da su aƙidojin addinin mishan don samun mabiyan da za su taimaka musu wajen yaɗa addini ba. Sun fahimci cewa, nasararsu ta dogara ne kan ‘yan asalin ƙasar da suka karɓi addinin nasu,(Fafunwa,1974:74- 85).

            ‘Yan Mishan na ƙungiyar C.M.S. sun fara kafa makaranta a yankin Nijeriya Ta Arewa a garin Lakwaja tun a shekarar 1865. Sun yi amfani da harshen Hausa da Nufanci a matsayin harshen koyo da koyarwa a makarantar, ( Fafunwa, 1974:101) da ( Ozigi & Ocho, 1981:15). Haka an bayyana cewa, ɗaliban sun kai kimanin 30 zuwa 40 a shekarar 1871. An buɗa makarantar ne don ‘yantattun bayi da ‘ya’yansu. Haka a cikin shekarar 1904 ƙungiyar C. M. S. ta buɗe wata makaranta a Bidda domin koya wa Alƙalai da Muhuti- Muhuti da Magatakardinnen Sarakuna, saboda samfurin rubutun zamani da ake son  a yi amfani da shi a wajen adana bayanan da suka shafi hukuma. An gudanar da darussan makarantar ne daga ƙarfe 7 na safe zuwa ƙarfe 9 na safe. Darussan da aka koyar sun haɗa da: Jugurafiyya da waƙe-waƙe da Turanci. Wajen koyar da karatu kuwa, an yi amfani da littattafan mishan da aka fassara cikin harshen Hausa da Nufanci. Misalan littattafan su ne: “ Labarin Allah”, da “ Labaran Baibul”. A wajen haujen ƙananan yara kuwa, an yi amfani da Baibul ne wajen koyar da karatu a makarantar. Janyewar  Alƙalai da Muhuti-Muhuti daga makarantar ya faru ne a sakamakon haɗarin da suka hango da ke tattare da karatun nasu. Kuma shi ne musabbabin wargajewar shirin koyar da malaman, ( Fafunwa, 1974:103) da (Ozigi & Ocho,1981:18). A shekarar 1903 C. M. S. ta buɗe wasu makarantu biyu, ɗaya a garin Kutugi gauraye da ɗalibai maza da mata, ɗaya kuma aWatney da ɗalibai biyar kawai. A shekarar 1906 kuma sun buɗa wata makaranta a Makwa, domin gudanar da karatun dare. Ɗaliban sun kai kimanin 25 zuwa 30. An koyar da rubutu da karatun Baibul a makarantar kamar yadda su Ozigi ( 1981: 22) suka nuna.

            Kusan duk muhallin da ‘yan mishan suka kafa sansani ko makaranta, ba inda suka yi a wajen da musulmi suke zaune tsintsa sai a birnin Zariya. Wannan ya faru ne a sakamakon gayyatar da Sarkin Zazzau Kwasau ya yi wa Likita Miller, don ya gudanar da ayyukan kiyon lafiya da bayar da ilimin zamani. Samun wannan dammar ke da wuya sai Miller ya yi amfani da ita wajen yaɗa addinin kirista a tsakanin Musulmin, ( Ayandele, 1966:132). Dr. Miller ya aiwatar da ayyukansa a Durumin Maigarke a birnin Zariya. Makarantar an gauraya ta maza da mata, a matsayin makarantar bacci, ( Jumare, 1982:29). An koyar da karatu da rubutu da lissafi. Manufar wannan makaranta, cusa aƙidar mishan a cikin zukatan ‘ya’yan musulmi.

            Buɗa wannan makaranta ta birnin Zariya ya haifar da karkatar da ‘ya’yan musulmi guda huɗu zuwa ga addinin mishan. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da:-

1.      John Tafida Umar

2.      Paul Yusuf Amfani

3.      Nuhu Bayero Daniya

4.      Da kuma Yeroson.

Biyu daga cikinsu jinin sarauta ne, ba ɗammanin talauci ko gudun tsangwama da kauce wa biyan haraji da makamantan haka, ya sa su yin ridda, amma an fi kyautata zaton kwaɗayin son sarauta ne ya sa su shiga addinin mishan, don hangen cewa, alaƙarsu da Turawan na iya zama sanadin cimma manufarsu ta hawan karagar sarautar Zazzau. Suna hangen Turawan mishan na da wata muhimmiyar rawa da suke iya takawa wajen naɗa sarki da fitar da shi, ( Jumare,1982:35). Musamman idan aka yi la’akari da irin rawar da Miller ya taka wajen fitar da Sarkin Zazzau Kwasau da kuma Sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi.

            Ƙungiyar mishan mai suna: “ Sudan United Mission”, ta gudanar da ayyukan bayar da ilimi a Wase da ke cikin masarautar Muri. Ta kuma kafa sansaninta a garuruwan Wukari da Donga, da Bukuru, da Gel, da Langtene da kuma tsaunukan Wase da Dampar da Ibi, da kuma Jen. Sun kula da gidan ‘yantattun bayi da ke Rumasha. A daidai lokacin, sun kafa makarantu a Ibi, da Wukari, da Donga, da kuma Langtene,( Ozigi & Ocho, 1981:23-24). Manufarsu a fagen ilimi ita ce koyar da ilimin sana’a da aikin gona tare da cusa aƙidar mishan.

            Haka ƙungiyar mishan mai suna: Sudan Interior Mission (S.I.M.) mai manufar haɓaka ilimin sana’a ( Industrial Education), ta kafa sansaninta a Pategi a shekarar 1903 tare da soma aikinta. A cikin shekarar 1905 ta faɗaɗa ayyukanta zuwa garuruwan Wushishi, da Bidda. Sun buɗa makaranta a Kaltingo a shekarar 1922. A kuma shekarar 1929 ne suka buɗa Bible College a Kagoro. A garin Kwai kuma sun buɗa makarantar sakandare ta ‘yan mata a 1945. A 1946 suka buɗa makarantar ‘ya’yan mishan a Miango. Sun kuma buɗe Titcombe Secondary School da ke Egbe a shekarar 1951, ( Fafunwa, 1974:102) da ( Ozigi & Ocho, 1981:17).

            Tun daga shekarar 1934, sai kafa makarantu ya zama sinadarin yaɗa addinin mishan a farfajiyar Daular Usmaniyya. Wannan ya sa wani jami’in ƙungiyar mishan ta S.I.M. mai suna Father Gately ya rubuta wa Razdan na Lardin Sakkwato wasiƙa inda yake nanata masa muhimmancin makarantu wajen yaɗa addinin mishan, (NAK/Sok.Pro./ c230/ 1934). An buɗa makarantu a garuruwan Tsafe, da Gusau da kuma Sakkwato. Haka sun gudanar da azuzuwan karatu a wuraren da suka kafa sansaninsu ( gidajen mishan). Makarantar da aka buɗe a Tsafe cikin shekarar1930 an tanadar mata da malamai, malaman farko da suka koyar sun haɗa da: Rev.Canon, da Halidu Muhammad, da Malam Yero, da Malam Bidan, da Mr. Gowan ( mahaifin Janaral Yakubu Gawon). A daidai shekarar 1935, makarantar ta kankama har ana turo mata ɗalibai daga sassan lardin Sakkwato da Katsina, ( Bunza, 2000:131). Yaran da aka tura makarantar ‘ya’yan majinyata ne da ke jinya a sansanin kutare da ke ƙarƙashin kulawar ‘yan mishan, kamar Gatawa, da Moriko, da Kuma Amanawa. Kuma hukumar mishan ce ta ɗauki ɗawainiyar karatunsu. Pasto Maidabo na Cocin ECWA da ke Tsafe na ɗaya daga cikin waɗanda suka zama kirista ta wannan hanyar, ( Bunza, 2000:131). Haka sun ɗauki nauyin tura waɗanda suka shiga addinin mishan, zuwa makarantar mishan don karɓar horo game da hanyoyin yaɗa addinin mishan a tsakanin al’ummar Musulmi. Misali, akwai: Mamman Barkeji, da Malam Kassu, da Gana Gusau, da Shibkau Gora, da Mamman Illela, da Samuel wanda aka fi sani da suna: “Haruna Matankari”.

4.2  Asibitoci:

     Ko da Turawan mishan suka zo ƙasar Hausa, al’ummar ƙasar na cikin yanayi na rashin ingantattun magunguna da kuma cututtuka da yawan annoba nan da can. Ga kuma ƙuncin talauci day a dabaibaye al’umma, a sakamakon mulkin danniya da cin zalu. Wannan ya taimaka wa ‘yan mishan wajen amfani da hanyar bayar da magunguna ga majinyata tare da ɗaukar takalihunsu. A yayin da suke da’awar yaƙi da cututtuka musamman a yankunan maguzawa da marasa gata daga cikin Musulmi, sai suka fake da shi suna jan ra’ayinsu zuwa ga addinin kiristanci.

            Turawa mishan sun fara buɗa  cibiyoyin shan magani a sansaninsu, daga baya suka faɗaɗa aikin zuwa gina ɗakunan shan magani a nesa da su. Suka kuma dinga ziyartar majinyata a gidajensu, kamar  yadda Miller, (1936:85) ya nuna. Sun nuna wa majinyata ƙauna da tausayi da jinƙai da rashin ƙyama. Ƙungiyoyin  mishan da dama sun gina asibitoci da ɗakunan shan magani, a matsayin wata kafa ta jan ra’ayin al’umma zuwa ga addinin mishan, ( Barkindo, B. da wasu, 1989:139). Misali, an kai wa Likita Miller wani yaro da ya yi mummunan rauni a fuska da ƙirji, amma, sakamakon kulawar da ya samu, cikin ikon Allah ya warke sarai. Wani kuma sukar sa aka yi a ciki, har hanji suka fito, amma ta hanyar ɗinki da kyakkyawar kulawa, Allah ya ba shi lafiya. Daga ƙarshe suka zama kiristoci, (Jumare, 1982:37). ‘Yan mishan sun shata matakai iri-iri a fannin kiwon lafiya, a ƙoƙarinsu na karkatar da al’ummar Musulmi zuwa ga addinin kiristanci. Daga cikin matakan sun haɗa da:

1.      Gina asibitin Wusasa da ke Zaruya.

2.      Samar da Makarantar Jinya da Aikin Unguwar Zoma, a Wusasa Zariya, a cikin shekarar 1938.

3.      Gina ƙananan ɗakunan shan magani a garuruwan Maska, a shekarar 1930, da Bakori, a shekarar 1930, da kuma Babban Dodo Zariya. A shekarar 1934 ne suka gina cibiyar kula da cutar kuturta a Kugu. An riƙa kula da masu kuturta da ke faɗin Nijeriya a wannan cibiyar, ( Jumare, 1982:82).

Duk waɗannan ayyuka ƙungiyar mishan ta C. M. S. ta aiwatar da su a ƙarƙashin jagorancin Likita Miller. Akan sa majinyata yin addu’o’in addinin kirista.

            Ƙungiyar  mishan ta S.I.M. ta yi amfani da fannin kiyon lafiya wajen karkatar da Musulmi zuwa ga addinin mishan. Wannan ne ya sa suka kafa asibitoci da ɗakunan shan magani a sassan ƙasar Hausa. Misali a cikin shekarar 1936 sun karɓi lamarin gudanar da aikin bayar da magani da ke zangon kutare a lardunan Kano da Sakkwato da Katsina daga hannun gwamnatin mulkin mallaka. Zangunan kutaren kuwa su ne: Tofa da Babbar Ruga da kuma Amanawa, ( Akanet, 1993:30-33). Sun kuma buɗa asibiti a Jos domin tunawa da Birgham a shekarar 1947, da kuma makarantar horar da jami’an kiyon lafiya, wato Medical Auxiliary Training School, a cikin harabar asibitin Jan Kwano da ke Jos, a shekarar 1959, ( Akanet, 1993:16).

            Asibitocin da aka buɗa a garuruwa kamar Moriki da Tsafe da Kalgo da Amanawa da ta Babbar Ruga da ke Katsina, duk sun kasance wuraren karkatar da al’ummar Musulmi zuwa ga addinin kirista, ( Kofar Bai, 1988:30). Mafi yawan Musulmin sun faɗa tarkon ne a sakamakon mu’amalar neman magani a hannun ‘yan mishan, ( Bunza, 2000:136). Turawan mishan sun yi anfani da hanyoyin jinyar marasa lafiya da bayar da magani wajen juyar da Musulmi daga addinin Musulunci zuwa ga addinin kirista, kamar yadda Robinson , ( 1915:54 ), da Miller, ( 1936: 43) da, Bunza, (2000:140) suka nuna. Ta irin wannan hanya ce, mutane kamar: Amadu Maiki, ya rikiɗa a zangon kutare na Moriki, haka lamarin ya kasance a kan Mamman Barkeji a zangon kutare da ke Amanawa a shekarar 1940, ( Bunza, 2000 :141).

4.3  Kafa Masana’antu:

            Bincike ya tabbatar da cewa, Turawan mishan sun taimaka wajen noma, musamman noma kayan da ake fitarwa zuwa ƙasashensu, kamar: auduga (kaɗa) da koko ( cocoa), da ƙwarar manja, da gyaɗa,  amma ba su bayar da wata kulawa ta a zo a gani a fannin noman kayan abinci ba. Haka ba wani taimakon kirki da suka yi ta fuskar kafa masana’antu ko wajen inganta su. Suna hangen yin haka tamkar zai haifar da gasa ne a tsakanin kayan da ake yi a ƙasar Hausa da na ƙasashen Turai, ( Falola da Adebayo, 1983: 49 &77).

            ‘Yan mishan sun yi ƙoƙarin amfani da ƙananan masana’antu da suke ganin za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin al’ummar da suke neman jan ra’ayinsu zuwa ga addinin kirista. Mr. Venn ya taimaka wajen kafa tsangayar koyar da Sana’o’i  a Abekuta. Daga baya aka faɗaɗa ta zuwa Anaca da Lakwaja, inda aka rinƙa horar da ‘yan ƙasa sana’ar sarrafa auduga. Sun kuma koyar da sana’ar gine-gine da shata tsare-tsaren gini irin na ƙasar Turai da sha’anin ɗab’i  da harkar magunguna ( M.S. Arch.). ‘Yan mishan sun kafa kamfanin gurzar auduga da kamfanin yin bulo ( Brick Industry) waɗanda J.M. Hardin ya assasa a garuruwan Iddo da Legas tun a shekarar 1886. Masana’antar bulo ta zama ita ke shata tsarn gine-gine da zayyane- zayyanen coci da gidajen mishan. Sun kawo masu sarrafa katako daga Saliyo waɗanda suka taimaka wajen gina ƙawatattun gidajen mishan da makarantu a Legas, ( Barkindo, da wasu, 1983:123).

            Idan aka cire masana’antar mazarƙwaila da ‘yan mishan suka kafa a Gimi, a sakamakon shawarar da Rev. W.A. Thompson ya ba Dr. Miller, ba wata masana’antar kirki da suka kafa a duk faɗin ƙasar Hausa. Sun sayo injinan tatsar rake da madafa ta zamani daga Amurka. Kasancewar Gimi na zagaye da wasu ƙauyuka da ake noma rake, ya sa ƙungiyar C.M.S. ta yi amfani da masana’antar domin jan hankalin jama’ar yankunan waɗanda suke maguzawa ne zuwa ga addinin na mishan. Masana’antar ta bunƙasa har ana odar mazarƙwailar daga wajen su ( Miller, 1936: 112), da ( Jumare, 1982:50).

            Tun a shekarar 1896 ne ƙungiyar mishan ta C.M.S. ta nuna sha’awarta a fannin kantin littattafai, sai dai lamarin bai haɓaka ba, sai a shekarar 1923, inda suka buɗa kantuna a garuruwan Zariya da Kano. Dalilin haka ne ya haifar da zuwan Rev.J.F. Cotton da maiɗakinsa a ƙasar Hausa a shekarar 1921. An buɗa kantunan ne domin samar da ingantaccen adabin mishan tare da yaɗa addinin mishan a ƙasar Hausa ( Miller,1936: 143).

             Su ma ƙungiyar mishan ta Sudan Interior Mission, sun buɗa kantunan littattafai a garin Jos a shekarar 1924. Suka kuma buɗa wata cibiyar koyar da sana’o’i a Kagoro a shekarar 1939. Sun yi amfani da kantunan wajen samar wa mutanen da suka shiga addinin mishan aikin yi, musamman waɗanda suka yi ridda ( 1936: 104).

            Haka sun bayar da horo ga masu fama da lalurar ciwon kuturta, a kan fannoni daban daban da suka haɗa da sana’ar saƙa, da noma da wasu sana’o’i da suka dace da su, domin su dogara da kansu, ( Jumare, 1982:87).

4.4  Adabin Mishan:

            Adabin mishan ya ƙunshi duk wani nau’in rubutu da aka yi cikin harshen Hausa da ke da manufar yaɗa addinin mishan. Rubutun yana iya zama ta hanyar fassara wani matani na littafin kirista ko kuma ta fuskar rubuta waƙa da ke ɗauke da jigogin yaɗa addinin mishan.

            Jami’an mishan na sane da cewa, wanda ya rubuta wani matani cikin harshen al’umma, tamkar yana magana da al’ummar da ke amfani da harshen ne, domin sun fi fahimtar abin da yake faɗa fiye da wanda aka rubuta a cikin wani harshe na daban. Kashi 80 na adabin mishan da aka rubuta a ƙasashen Afirka, an rubuta su ne a cikin manyan harsunan al’ummomin nahiyar. An yi haka ne domin masaniyar da ke akwai na cewa, coci ba zai wanzu a ƙasar Hausa ba sai da taimakon adabin mishan na farfajiyar ƙasar Hausa.

Turawan mishan da masu bayar da gudummawa a ƙasar Turai sun haɗa ƙarfi da ƙarfe waje ɗaya don samar da adabin mishan a ƙasar Hausa tare da rayar da shi cikin harshen Hausa. Ta haka ne suka gudanar da wallafe- wallafe da ke ƙunshe da aƙidojin addinin mishan ga mabiya addinin da ke jin harshen Hausa. Misali daga irin waɗannan ayyuka su ne:-

-          Letafen Musa Nabiu (Exodu), J.F. Schon, 1859.

-          Labarin Nagari Kamad Marku Ya Rubutasi ( St. Mark), J.F. Schon, 1878.

-          Letafi Na Yesaya, Annabi ( Book of Isaiah), 1881.

-          Bishara Daga Hannun Yohanna (St. John, in Ajami), 1898.

-          Labarin Allah ( Bible Stories) 1903.

-          WaƙoƙI da addu’o’i ( Hymn book) F.Wakefield, 1913.

-          Labarin Yaƙin Ran Mutum ( The Holy War), 1920.

-          Haske a Kan Hanya ( Selections from the Travellers Guide), 1924.

-          Koyaswa ga Masu Bidan Tafarki ( A Catechism) 1925.

-          Sabon Alƙawali ( New Testament)

-          Tsofon Alƙawali ( old Testament).

-          Labarin Masu Bin Isa na Kwanakin Da ( Stories of the Saiat) 1931.

-          Labara Mai Kyau ( Ajami) da sauran su ( East, 1941:29-31).

4.5  Fatima:

            Wannan littafi shi ne na farko da ‘yan mishan suka rubuta a kan ƙagaggen labarin Hausa. An buga littafin a Legas cikin shekarar 1933 , ƙungiyar mishan mai suna: “ Church Missionary Society” ta buga shi. Littafin ya na da shafuka 92. Kuma shi ne littafi na farko da aka fara samarwa a fannin ƙagaggen labari a ƙasar Hausa. Marubucin ya tsara shi a fasalin babi-babi har babi goma sha biyar. Duk da haka ba wani kanun labarai da aka ba kowane babi. Littafin bai samu karɓuwa ba ga Turawan mulkin mallaka,a sakamakon jigon da yake ɗauke da shi na ƙoƙarin janyo ra’ayin Musulmi masu rauni zuwa ga addinin Kirista; tare da nuna munin wasu halaye na Musulmi, da tabbatar da irin karamcin da addinin Kirista da mabiyansa ke nunawa ga al’umma.

Idan aka dubi littafin za a tarar tun daga farkonsa marubuci ya soma da sukar Musulunci ta hanyar nuna cewa addini ne na masu duhun kai waɗanda ba su waye ba. Misali ga abin da marubucin ke cewa:

Malam Ayuba mutumin bara ne: na kirki ne kwarai mai ibada

Kuma; yana da suna dattijo wurin dukan jama’a, amma ba ya

Gane al’amura na yanzu ba ko kaɗan. Ba ya yarda ya yi ma’a-

-mala da baƙI masu zuwa daga yamma ba; duk ya haɗa su gaba

ɗaya ya che da su “arna”. Ko da am ba shi labarin karatunsu na

Masihiyyanchi, ba ya yarda ba. chikin jahilcinsa yana tsammanin

Babu wani addini sai Muhammadiyya: babu karatu sai na Alƙur’an

Da Islama!....Kalmomi irin na da da farillai da rukunai na da su ya

Ya riƙe da iyakar ƙarfinsa; ba ya sani ba amfaninsu sun riga sun

Shuɗe…. (Miller,1933: 4-5).

Wannan shi ne babban dalilin da ya hana a ji ɗuriyar littafin, hasali ma ba a sa shi cikin jerin littattafan ƙagaggu labaran da aka samar na farko-farko a ƙasar Hausa ba. Da farko an soma kawo bayanin  al’adar nan ta neman aure a ƙasar Hausa. Daga nan sai lamarin ya suya kama ya koma ta fuskar suka da wa’azin Kirista, wanda ya haifar da karkatar jigon littafin zuwa ga ƙoƙarin yaɗa addinin mishan a tsakanin Musulmi.

4.6  Ka Koyi Karatu, da Ka Ƙara Karatu, da Ka Yi Ta Karatu:

            Bayan Turawan Mishan sun samar da littattafan adabin horaswa, da suka yi amfani da su a makarantun da suka kafa a sassa daban daban na Nijeriya Ta Arewa, har da yankunan da ba na Hausawa ba ne,( Westerman,1937:21). Haka sun samar da wasu jerin littattafan horaswa a sakamakon yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu da Hukumar Talifi a shekarar 1937. A yarjejeniyar an shata a rubuta littattafai waɗanda ba za a danganta su da wani addini ba. An buga littafan ne domin amfanin ƙananan azuzuwan makarantun Elimantare. Ƙungiyar Mishan mai suna “ Sudan Interior Missionary da ke Jos ta wallafa su a shekarar 1938, ( NAK/ 1029/ AND/1938).

“ Ka  Koyi Karatu:

            An wallafa wannan littafi a shekarar 1938, domin amfanin ƙananan azuzuwan makarantun farko da ke Nijeriya Ta Arewa. Kantin Sayar da littafai mai suna: “ Sudan Interior Missionary Bookshop” ya buga shi.  Littafin ya ƙunshi gajerun labarai da ke cusa halin ɗa’a da ladabi tare da hannunka mai sanda game da lamarin rayuwar zaman duniya. Littafin yana da shafi 30 ne, an shirya shi ne don amfanin ɗaliban aji biyu na Makarantar Elimantare. An yi amfani da hajjatu (tattashi) tare da kawo gajerun jumloli, ta yadda za su iya karatu, aka kuma zo da gutsuren labari don a gwada su. Misali , a shafi na 3 an kawo gajeren labari da ke nuni ga muhimmanci tafiya da makami don kare kai. A shafi na 9 kuwa wani gajeren labari ne da aka yi wa suna: “Dila Sarkin Dabara”. A nan an nuna yadda dila ya yaudari hankaka da daɗaɗan kalamai ta hanyar kambama ta, har ya kwace naman da ta samo. A shafi na 13 wani guntun labari ne da aka kira: “Amsa Kuwa”. A ciki an yi ishara ne da yadda murya (lafazi) mai taushe kan tafiyar da fushi da yadda kakkausar murya kan ruruta wutar fitina a tsakanin al’umma. A shafi na 15 an zo da labari mai suna: “Gada Da ‘Yarta” shafi na 18 kuwa an kawo labari mai take: “Hankaka Mai Hikima”. A nan an nuna dabarar da ya yi ta amfani da saka duwatsu cikin tulu har ruwa suka taso sama, ya sha. A shafi na 22 an zo da wani labari da aka kira da suna: “Bagwari”. Haka a shafi na 27 an zo da wani da aka ambata da suna: “Wayon Ɓera Ya Fisshe Shi”. A nan an nuna dabarar da ya yi ya kuɓuta daga hannun kyanwa. Sai shafi na 28 da aka zo da wani taken da aka kira: “Fyuu”. Labarin yana ɗauke da bayanin kaza da ‘ya’yanta takwas, wanda na takwas ɗin ya kasance mai taurin kai, bai bin umurnin uwarsa. Sakamakon haka , shaho ya fige ƙyeyarsa. A ƙarshen littafin ma an zo da wani labari da aka kira da suna: “Alheri Farke Nagari”.

“ Ka Ƙara Karatu” 

            Littafin ya na da shafuka 40, Kantin sayar da littattafai na Sudan Interior Missionary suka buga shi a 1938. Kamfanin Gaskiya Corporation ya sake buga shi. Littafin yana ɗauke da gajerun labarai ne masu koyar da tarbiyya da dabarun zaman duniya. Labarai 37 ne ke cikin littafin waɗanda suka haɗa da labarin: 1- Kare Da Kura Da Damo 2- Makaho Mai Fitila 3- KwaɗI Biyu 4- Kurege Da Bushiya 5- Mugun Alƙali 6- Dila Da Zalɓi 7- Sarkin Zafi Da Sarkin Bauɗiya 8- Ungulu Da Shaho 9- Rai Ya Fi Dukiya 10- Kaza Da Giwa 11- Matafiya Biyu 12- Hana Wani Hana Kai 13- Yaro Da Kare 14- Yi Taka Tsantsan Da Duniya 15- Bagwari Da Malami 16- Alheri Ba Shi Kaɗan 17- Gaba Da Gabanta 18- Kafin Ka Ga Biri Biri Ya Ganka 19- Kura Da Ganga 20- Sannu Ba Ya Hana Zuwa 21- Wani Ɓarawo 22- Hasara Da Riba 23- Sata Ta Saci Sata 24- Farke Da Yaro 25- Karambani Kauyen Hanya 26- Mafarauci Da Abokinsa 27- Kome Ka Samu Gode Allah 28- Kagon Allah Mai Wuyar Jinƙewa 29- Maci Amana Yana Tare Da Kunya 30- Samu Ya Fi Iyawa 31- Gasar Neman Aure 32- Ina Amfanin Baɗi Ba Rai? 33- Ɓeran Birni Da Ɓeran Daji 34- Maciji Da Kunama 35- Gatari Da Wuta Mai Wuyar Rataya 36- Gamo Da Katar 37- Wani Ɗan Sarki Da Alƙali. A ƙarshen littafi aka zo da wata matashiya da aka kira: “Malami Da Ɗam Makaranta”. Wannan matashiyar tana ƙunshe da faɗakarwa da ilmantarwa mai amfani ga wanda ya yi da ita.

“ Ka Yi Ta Karatu” 

            Sudan Interior Missionary Bookshop suka buga wannan littafi a 1938. Ba san sunan mawallafin littafin ba. Abin da aka sani, wai wata Baturiya ce ta rubuta shi tare da waɗanda aka ambata a sama, kamar yadda Ibrahim, ( 1979: 36) ya nuna. Littattafan sun taimaka wajen koyar da ƙananan azuzuwan farko na makaratun firamare. Shi ma ya cusa tarbiyya da sanin ya kamata a cikin zukatan yara. Littafin shafukansa 77 ne ƙunshe da kanun labarai 33 kamar haka: 1. Yawan shekara ba shi ne wayo ba. 2. Bikin mutuwar Jaba. 3. Gudun shekara da shekaru ya same ni. 4. Dabaru biyar na zaman duniya. 5. Basha ja gora. 6. Ashe kunya ba a ido kaɗai take ba. 7. Aminci da mara hankali yana jawo halaka. 8. Dawakin Fiti. 9- Na-hana Sarkin Rowa. 10- Fargar Jaji. 11- Rimayen Zariya. 12- Bakatsine mai kan ƙwarya. 13- Ga wanda ya tafi farauta aka farauce shi. 14 Irin auren Rumada. 15- Labarin Sarkin Gaskiya. 16- Kamun gwauraye. 17- Banza girman mahaukaci. 18- Allah ya san abin da ke cikin zukatan bayi. 19- Sharo. 20- Wa ya gaya maka Lahira da gumi? 21- Ɗan Zazzau da ɗan Kano. 22-Su. 23- Ba mugun Sarki sai mugun bafade. 24- Yabon kai jahilci. 25- Aikata alheri, sakayyarka tana wurin Allah. 26- Gwaska. 27- Gardamar Wali Ɗammasani da Wali Ɗammarina. 28- Baki mai jaye-jaye. 29- Kadara. 30- Asirin da Allah ya rufa. 31- Ƙunar Baƙinwake. 32- Babban Gwani, Muhammadu Durugu. 33- Ka san labarin da ya fi kowanne tsawo? Za a tarar cewa, daga cikin waɗannan kanun matashiyar littafin, 24 labarai 24 ne, yayin da tarihihi ya kasance 01, sai kuma tarihi 08. Duk suna ƙunshe da wasu darussa da suke cusawa a cikin zukatan ɗalibai.

5.0 Jawabin Kammalawa:

            Daga rubuce-rubucen da ‘yan mishan suka yi game da al’ummar ƙasar Hausa da harshensu, da ma abubuwan da suka shafi tarihi, yanayin halayyar rayuwar Hausawa da al’adunsu da tatsuniyoyinsu da waƙoƙinsu da sauran sassan adabin Bahaushe, har ma da adabin mishan; an fahimci sun yi amfani da karin harshen al’ummar da suke zaune tare da ita a yayin da suke gudanar da aikin. A wasu lokuttan, sukan yi amfani da karin da suka ga ya fi dacewa. Haka kowace ƙungiyar mishan ta yi amfani da  ƙai’dar rubutunta ne da keɓaɓɓun kalmominta na addini, a yayin da take gudanar da ayyukanta na adabi. Yawancin ayyukan da aka yi sun ƙunshi fassara ce, domin biyan wasu buƙatu kwai. Kuma mafi yawan waɗanda suka yi irin waɗannan ayyukan ba su da cikakkiyar ƙwarewa game da harshen Hausa. Wannan ya sa ayyukan sun kasance cikin gurɓatacciyar Hausa da rashin inganci. Haka an fahimci cewa, bayyanar coci-coci a ƙasar Hausa bai taimaka wa  kiristoci ‘yan ƙasa wajen mallakar adabin mishan  nasu na kansu ba. Galibin abubuwan da aka rubuta sun kasance waƙoƙin yabo, da abubuwan da ke koyar da aƙidar kiristanci. Wasu kuma fassara ce kai tsaye daga littattafan addinin mishan da ke ɗauke da tarihi ko bayanin yaƙe-yaƙe, da irin waɗannan abubuwa ne aka bunƙasa adabi da al’adun mishan a ƙasashen Afirka. Da su kuma aka yi amfani wajen koyarwa a makarantu cikin harsuna daban –daban har aka ɗora harsashin ginin marubuta adabi ‘yan ƙasa.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments