Fishing is an age long traditional occupation of a certain section of the Hausa people of Northern Nigeria which may be referred to as artisan fisheries. This occupational phenomenon falls under the cultural aspect of the life of Hausa people. Literature is said to be an art that portrays the imaginative vision of a people and the world in which they live, it therefore reflects the culture of a people. Folktale as one of the genres of literature is simply a traditional narrative, usually anonymous and is handed down to the younger generation by word of mouth. Its example includes fables, fairy tales, legends, etc. Since literature whether oral or written is a mirror which reflects the culture of a people, there is no gain saying the fact that a good number of Hausa folktales are embedded with contents that reflects traditional fishing. It is against this background that this paper wishes to explore the extent to which Sarkanci is reflected in the folktales of the Hausa people.

kamun kifi

Laluɓen Sarkanci a Tatsuniyar Hausa

DR. MUSA FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983

Tsakure

Sarkanci wata daɗaɗɗiyar sana’a ce ta gargajiya wadda wani rukuni na al’ummar Hausawa suka daɗe suna aiwatarwa a matsayin hanyar neman abinci da ɗan abin ɓatarwa don gudanar da rayuwa ta yau da gobe. Sana’ar ƙunshe take da al’adu da dama. Adabi wani tsani ne da za a iya takawa domin a ƙyallaro rayuwar al’ummar da ta mallake shi, domin kuwa shi ne madubi na wannan al’ummar. Tatsuniya kuwa na ɗaya daga cikin rukuna na adabin baka na gargajiya wadda take ƙunshe da ƙirƙirarrun labarai,waɗanda ake yi wa yara ta amfani da fatar baki, domin a koyar da su wasu halaye na gari da kyawawan dabi’u . Babu tababa, waɗansu tatsuniyoyi na Hausa suna ƙunshe da lamurra da suka jiɓinci harkar sarkanci. A kan haka ne wannan muƙala ta ƙuduri aniyar tsunduma cikin tatsuniyoyin Hausa da nufin lalubo yadda lamarin sarkanci ya yi fice da shige a ciki.

1.0 GABATARWA

 Yawa-yawan Hausawa suna zaune ne a karkara kuma galibi noma da kiwo su ne manyan sana’o’in da suke aiwatarwa. Wani rukuni na al’ummar Hausawa kuwa ba su da wata sana’a da ta shige sarkanci, wato kamun kifi, rani da damina. Galibi da rana mutane kan duƙufa wajen fafitikar neman abinci, amma da yamma, musamman lokacin hira, akan sami nishaɗi da ɗebe gajiya ta hanyar ba juna labarai da kuma tatsuniyoyi ga ƙananan yara. A irin waɗannan labarai da tatsuniyoyi ne yara kan koyi wasu halaye da ɗabi’u na gari waɗanda al’umma ta aminta da su. Misali, sukan koyi jarunta da dauriya da riƙon amana da ladabi da biyayya da guje wa yaudara da ɗauke-ɗauke, da abubuwa makamantan waɗannan.

Sarkawa mutane ne da suke taka muhimmiyar rawa a cikin al’ummar Hausawa. Sana’arsu ce take samar da kifi wanda ya kasance muhimmin abinci da ke ƙunshe da sinadarai masu inganci wajen ginuwa da inganta lafiyar mutane. Tare da haka, kifi yana ƙunshe da sinadari mai amfani sosai wajen magance wasu cututtuka, hasali ma sinadari ne na haɗa wasu magunguna da naƙulƙula da akan yi domin biyan wasu buƙatun rayuwa. Sarkawa suna taka muhimmiyar rawa a sha’anin kiwon lafiyar al’umma a gargajiyance. Suna ba da magunguna na cututtuka kamar ciwon sanyi. Suna aikin bayar da agaji da farfaɗo da wanda ya faɗa ruwa ya galabaita. Idan ƙayar kifi ta maƙale a baki ko maƙogwaro, su suke cire ta. Dubin irin tarin alfanun da sana’ar sarkanci da Sarkawa suke da shi a cikin al’umma, ba zai zama abin mamaki ba idan sana’ar da masu aiwatar da ita suka yi naso a cikin tatsuniyoyin Hausa. Wannan muƙala za ta yi koƙarin haskaka yadda sarkanci da Sarkawa suka yi tasiri a cikin tatsuniyoyi na Hausa. Gabanin yin haka, muƙalar za ta bijiro da bayanai dangane da ma’anar sarkanci da kuma tatsuniya.

 

1.1 Asali da Ma’anar Kalmar Sarkanci

 Bisa asali, kalmar sarkanci ba Bahaushiya ba ce. Asalin kalmar daga ‘Sorko’ ne, wata al’umma ta daular Songhai. Al’ummar Sorko mutane ne da suka shahara matuƙa ga sha’anin su a kogin Kwara wanda ya ratsa ƙasashe da dama na yammacin Afirka. Sana’ar su ce ta kawo wannan al’umma ta Sorko a daular Kabi. Sannu a hankali har suka saje da jama’ar da suka tarar a Kabi.[1]

 Domin a Hausantar da wannan kalma ta ‘Sorko’ an yi mata kwaskwarima ta hanyar cire wasalin ‘o’ a gaɓar farko aka musanya shi da wasalin ‘a’, wataƙila domin a sami sauƙin furuci. Haka ma an yi mata ƙarin ɗafa goshi na ‘ba’ ta yadda za a sami sunan wanda ya fito daga wannan al’umma ta ‘Sorko’, kafin daga baya ma’anar ta sauya zuwa ga duk wani mai gudanar da sana’ar, aka kuma cire wasalin ‘o’ na ƙarshe, aka musanya shi da wasalin ‘e’, aka sami “Basarke”. Dangane da suna na sana’ar kuwa tushen kalmar ne Ɗsarkɗ aka yi wa ƙarin ɗafa ƙeya na ‘nci’ aka sami kalmar ‘Sarkanci.’[2]

 Bisa ma’ana, masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da suke ganin ake kira sarkanci. Bargery, (1933:92) a ƙamusunsa ya bayyana wanda ake kira Basarke. Daga wannan kalma ta basarke za a iya tantance ma’anar kalmar ta sarkanci. A cewarsa,

 Basarke shi ne masunci ko mai fito da kwale-kwale.[3]

Alkali, (1969) ya bayyana abin da yake gani ake kira sarkanci a inda yake cewa,

 Tun farkon ƙarni na goma sha tara (19) kalmar sarkanci ta ɗauki

 ma’anar ƙwarewa kan sana’ar su, don haka duk Bakaben da ke

 yin wannan sana’a ake kiransa Basarke.[4]

 Wannan ma’ana da Alkali ya kawo ta yi daidai don kuwa ba kowane masunci ne ake kira Basarke ba. Basarke masunci ne ƙwararre, wanda ba ya da wata sana’a da ta shige ta su, rani da damina. Irin wannan masunci ne za a tarar yana iya sarrafa ruwa da ma halittun da ke cikinsa ta duk yadda yake so. Ta fuskar ba da magani kuwa, basarke ba kanwar lasa ba ne.

Da wannan, ana iya cewa sarkanci kalma ce da ke nufin sana’ar kamun kifi da farautar dabbobin ruwa da duk abubuwan da ke tafiyar da ita kamar ƙwarewa a kanta da iya sarrafa ruwa da halittun cikinsa da kuma ba da taimako na cututtukan da ake samu a ruwa har ma da haɗurra da ke iya aukuwa a ruwa.

1.3 Ma’anar Tatsuniya

 Ƙamus na Merriam Webster (1993:452) ya faɗa cewa tatsuniya labaru ne na baka, daɗaɗɗu, marasa tushe, waɗanda ake yaɗawa a tsakanin al’umma.

Ibn Manzur, (2002:576) cewa ya yi tatsuniya a harshen Larabci tana nufin zantutuka waɗanda ba su da wani tsari na musamman ko kuma zantutuka waɗanda suka yi kama da ƙarya.[5] Dawkins (1951) cewa ya yi ana iya bayyana tatsuniya a matsayin labari na kunne ya girmi kaka, wanda ake yaɗawa ta hanyar fatar baki.[6]

Koko, (2009:2) ta kalli tatsuniya a matsayin labarai da mutane ke ƙirƙirowa cikin azanci don su tarbiyantar da ‘ya’yansu tare da cimma wasu buƙatoci dangane da al’umma. Galibi labaran na baka ne don haka a ka ake adana su amma duk da haka an taskace wasu a litattafai.[7]

2.0 Karatun Sarkanci A Tatsuniyar Hausa

 Tatsuniya wani babban rukuni ne na adabin baka kuma shi adabi ya kasance wani madubi da za a duba domin a ƙyallaro yadda al’umma take gudanar da rayuwarta. Sarkanci sana’a ce ta gargajiya wadda take ƙunshe da al’adu daban-daban. Kasancewar Sarkanci sana’a da ta shiga jinin Bahaushe jiya da yau, samun ratsin Sarkancin a cikin tatsuniya ba wani abin mamaki ba ne. A cikin tatsuniyoyi da dama, ana samun lamurran da suka jiɓinci Sarkanci. Waɗannan lamurra na Sarkanci da kan bijiro a tatsuniyar Hausa ne za a bi domin fito da su sarari.

2.1 Sunayen Kifi

 Allah a cikin ikonsa da buwayarsa, ya albarkaci ƙasar Hausa da albarkatu na ruwa kuma a ciki ya rayar da halittu daban-daban, ciki har da kifi. Kifin yana da nau’uka da sunaye daban-daban. Idan dai mutum ba yana zaune a inda sana’ar Sarkanci ke wanzuwa ba, mawuyacin abu ne ya iya tantance sunayen kifaye daban-daban. A cikin tatsuniya, akan kawo sunayen kifi kuma cikin tatsuniyar, ana iya koyon waɗannan sunayen domin ko banza ai tatsuniya wata makaranta ce da ake koyon abubuwa da dama, tun kafin bayyanar Bature a ƙasar Hausa.

Misalin tatsuniya da ta ƙunshi sunayen nau’ukan kifaye daban-daban ita ce ‘Tatsuniyar Gizo da Zaki’. [8] A cikin wannan tatsuniya an kawo sunayen nau’ukan kifaye kamar gwando da rajiya da. kullume da sauransu.

 A cikin tatsuniyar, gizo ne ya yi su ya kama kifi ya zo yana yin banda sai ga zaki. Bayan sun gaisa, sai zaki ya ce Gizo ya sam masa kifi. Da aka sam masa ya ci, ya ji daɗi, sai ya ce a ƙara masa. Da sannu, da sannu har zaki ya cinye kifin gizo sarai, ba tare da ya raga masa komai ba. Gizo na cikin baƙin cikin zaluntarsa da aka yi, sai ga zabuwa ta zo tana kuka: kuker! Kuker!! Kuker!!! Gizo ya kalli zabuwa ya ce: “Ku ji ta da kurin banza! Sai ka ce ba ni ne na yi mata zanen da take kuri da shi ba! Zaki na jin wannan kalami na gizo, sai ya ce shi ma gizo ya yi masa wannan zane irin na zabuwa. Gizo ya ce wa zaki yin zanen yana da wuya sosai don kuwa akwai raɗaɗi. Duk da haka zaki ya nace da sai gizo ya yi masa wannan zane. Gizo ya ce da zaki ya kaso ɓauna babba domin da fatarta za a ɗaure shi a jikin wani babban ice. Zaki ya je farauta, ya kaso ɓauna ya kawo wa gizo. Gizo ya yi zaune ya feɗe ɓauna, fatarta kuwa ya yanka ta yadda zai iya amfani da ita wajen ɗaɗɗaure zaki. Zaki sai ya je ya sami wani ƙaton ice, ya bangaje shi ya ga ko kaɗan icen bai motsa ba. Ya dawo ya shaida wa gizo. Gizo ya ce to su tafi. Suna isa wajen wannan babban icen, zaki ya tsaya, shi kuwa gizo ya sa igiyar nan ta fatar ɓauna ya ɗaɗɗaure zaki sosai. Ya ce da zaki ya motsa da ƙarfi don ya ga inda bai ɗauru ba. Zaki ya motsa, sai gizo ya ƙara tattanke shi sosai ta yadda zaki har ba ya iya wani dogon motsi. Gizo sai ya hura wuta, ya ɗauko wani ƙarfe ya saka a wuta, ya riƙa hura wuta har sai da ƙarfen ya yi jajir. Ya ɗauko ƙarfen nan mai zafi, ya riƙa yin zane a jikin zaki. Tun zaki yana dauriya har ya riƙa yin raki. Shi kuwa gizo duk lokacin da ya ɗauko ƙarfe mai zafi ya ɗaɗara wa zaki a jiki sai a riƙa jin cui. Kowane lokaci, idan gizo ya yi ɗaɗara ƙarfe mai zafi a jikin zaki, sai a ji cui. A duk sa’ilin da gizo da ya ƙona zaki sai ya ce, kifina, cui! gargazata, cui! rajiyata, cui! kullumena, cui! gwandona, cui! giwar ruwata. Da haka, gizo ya bi jikin zaki ya zane shi sarai da wuta. Gizo ya kwashe naman ɓauna, ya gudu ya bar zaki a ɗaure cikin wahala. Zaki duk ya bi ya lalace saboda yunwa da raɗaɗin ƙunar wuta. Gara ce ta zo ta kwance shi. Da suka sake haɗuwa da zaki, sai gizo ya sake yaudararsa har ta kai zaki ya shiga tsoron gizo. Kan ƙurus kan kusu.

 

2.2 Dabarun Sarkanci

 Sarkanci sana’a ce wadda sai an bi hanyoyi na hikima da basira domin cim ma nasara yayin aiwatar da ita. Hanyoyin hikima da Sarkawa suke bi domin samun nasara a sana’arsu ne ake kira dabarun Sarkanci. Ana bin waɗannan hanyoyi ne domin koyaushe kifi ƙoƙarin bijire wa yunƙurin kama shi yake yi. La’akari da wannan ne ya sanya Bahaushe yake karin magana: ‘Kifi na ganin ka mai jar koma.’

 Dabarun kama kifi da Sarkawa kan yi amfani da su suna da yawa. Wasu dabarun da hannu kawai ake amfani, kamar lalube. Akwai dabarun da akan kwalfe ruwa domin kama kifin da ke farfajiyar da aka kwalfe cikin sauƙi. Akwai kuma dabarun haƙa tarko daban-daban, kama daga ƙugiya kamar mamari da gyaba, zuwa raga kamar kalli da gurar Mali. Ana kuma haƙa wasu kayayyaki da aka saƙa su da kaba kamar unduruttu da tsattsara da gura da dai sauransu. Ana kuma yin shinge a cikin ruwa sannan a haƙa kayan kamun kifi. Ire-iren shingen ya haɗa da tashi da ganuwa da saba da dumba da dai sauransu.

 Dabarun Sarkanci, wato hanyar da ake bi wajen kama kifi kan sami ambato a cikin tatsuniyoyi na Hausa. Babban misali ya zo a cikin ‘Tatsuniyar Gizo da Ƙoƙi da Botorami.’[9] A wannan tatsuniya, gizo da matarsa Ƙoƙi suke maƙwabtaka da Botorami. Botorami kullum yakan je su ya kamo kifi mai yawa ya zo gidansa ya gasa don ya ci. Wata rana Ƙoƙi ta yi ta ƙoƙarin hasa wuta domin ta yi girki amma abin ya faskara, sai ta ɗauki kasko ta je gidan Botorami domin ta roƙo wuta.

Ƙoƙi ta shiga ta roƙi wuta aka sam mata kuma aka ba ta gasasshen kifi. Ta ci kifin ta rage wa mijinta kifin ɗan kaɗan. Da gizo ya ci kifin ya ji daɗi, sai ya ɗauki kasko ya sallama gidan Botorami wai shi ma a sam masa wuta. Aka ba shi wuta aka kuma ɗebo kifi aka ba shi. Kafin ya koma gida sai ya cinye kifin, ya kuma kashe wuta, ya sake komawa gidan Botorami wajen roƙon wuta. Haka dai Gizo ya yi ta yi yana komawa gidan maƙwabcinsa roƙon wuta don a sam masa kifi har sai da Botorami ya gaji da halinsa. Gizo ya dai ya ce masa gaskiya yana so ne ya san inda Botorami yake samun kifi. Botorami ya yi masa alƙawalin gobe ya zo su tafi wurin su tare. Gizo ya kwana yana ɗokin gari ya waye su je wajen su. Gari na wayewa, Gizo bai zame ko’ina ba sai gidan Botorami. Suka shirya suka tafi wani kogi. Bayan sun isa bakin kogin sai Botorami ya ce wa gizo ya shanye ruwan wannan kogi duka. Gizo ya duƙa ya sha ruwa iya cikinsa amma ruwan yana nan kamar bai sha komai ba. Botorami kuwa sai ya duƙa ya zuƙe ruwan kogin duka, sai ga kifi a sarari, suka kama kifi mai yawa. Gizo ya so su rage kifin kada su kame duka amma Botorami ya ce su kame kifin duka domin ba koyaushe ake samun sa ba. Ƙarshe dai da Gizo ya ji daɗin wannan tafiya su, sai ya ce da matarsa Ƙoƙi su je kogi su kamo kifi. Da suka isa wani kogi sai ya ce ƙoƙi ta shanye ruwan kogin. Ƙoƙi ta sha ruwa iya cikinta ta ƙoshi. Gizo ma ya kwankwaɗi ruwa iya zarafinsa amma ruwan kogi yana nan kundum kamar ba a rage shi ba. Gizo da matarsa suka kasa taɓuka komai na kwalfe ruwan kogi don haka ba su kama kifi ko ɗaya ba.

 Wannan tatsuniya tana nuni da yadda Sarkawa kan bi hanyoyi daban-daban wajen kwalfe ruwan kogi ko na tafki ta hanyar datse ruwan sannan a sa wani abu misalin kwarya, a kwalfe ruwan sarai domin a kama kifi. A yanzu saboda cigaba da aka samu ta fuskar kimiya, Sarkawa suna amfani da inji wajen janye ruwa domin kama kifi. Wannan dabara ce suke kira kwalfe.

2.3 Sarrafa Kifi

 Kifi halitta ce da ke rayuwa a cikin ruwa. Bayan an kama kifi, ana sarrafa shi ta hanyoyi daban-daban domin samar da abinci. Yana da saurin lalacewa ainun, don haka ne ba a ɓata lokaci mai yawa ba tare da an sarrafa shi ba. Hanyoyin sarrafa shi ya haɗa da suya da gashi da dafawa da kuma banda. Dabarun sarrafa kifi kan fito a cikin tatsuniya. Misali, waɗannan tatsuniyoyi da aka kawo, ba kawai kawo sunayen kifi daban-daban suka yi ba, sun kuma kawo wasu daga cikin hanyoyin da ake bi wajen sarrafa kifi bayan an kama shi. Banda dabara ce ta busar da kifi bayan an ɗora shi saman wata waya ko ‘yan itatuwa da aka ɗora a saman wani murhu, ta yadda zafin wuta zai riƙa kai wa ga kifin har sai ya bushe. Kifin da aka bandace ne kan kasance a dunƙule kamar gammo kuma yana ɗaukar lokaci ba tare da ya lalace ba. A cikin tatsuniyar farko, an nuna cewa gizo ya kamo kifi, ya zo yana bandarsa ne zaki ya tarar da shi, har ya roƙe shi ya sam masa kifin. Tatsuniya ta biyu wadda ta gabata kuwa, tana ƙunshe da wata hanya da ake bi wajen sarrafa kifi, wato gasa kifi.

2.4 Waibuwar Sarkawa

 Sarkawa mutane ne da suka shahara matuƙa a fagen magani da siddabaru da sihiri. Sarkawa suna iya sa ƙayar kifi ta laƙe wa mutum, suna iya cire ƙayar kifi idan ta laƙe ga baki ko maƙoshin mutum. Suna iya yin dabon kifi kuma suna iya sa kifi ya ƙi nuna a duk lokacin da aka so dafa shi musamman idan aka ɓata masu rai. Sarkawa idan rayuwarsu ta ɓaci suna iya hana wa mutum ko wasu jama’a shan ruwa. Ire-iren wannan waibuwa ta Sarkawa kan fito fili a cikin wasu tatsuniyoyi na Hausa.

 Tatsuniyar ‘Tasalla Maikifi’[10] ƙunshe take da misali na irin waibuwar da Sarkawa kan yi. Wata mata ce mai suna Tasalla wadda take kiwon wani kifi. Tasalla ta shaƙu da wannan kifi nata sosai. Kifin, sakamakon shaƙuwarsa da Tasalla har tuma yakan yi, ya yi tsalle sai bisa jikin Tasalla. Saboda irin tarairayar da Tasalla take yi wa wannan kifi da kuma ƙwazonta wajen ciyar da shi, kifin ya girma sosai kuma jikinsa sai sheƙi yake yi. Ita kuwa Tasalla saboda sabo, ba ta son abin da zai raba ta da wannan kifi nata. Kwanci tashi Tasalla na nan tare da kifinta, ranar nan sai tafiya ta kama ta. Tasalla, cikin baƙin cikin rabuwa da kifi, ta kama hanya ta tafi, ta bar kifinta a gida. Mutanen garin ashe sun haɗiye wa wannan kifi na Tasalla yawu. Fitar Tasalla ke da wuya, sai suka kama wannan kifi nata suka daddatse shi, suka dafa, suka cinye. Ko da tasalla ta dawo daga tafiya, sai ba ta tarar da kifinta ba. Ta shiga tuntuɓar mutane domin ta gano wanda ya kama mata kifi. Kowa ta tambaya sai ya ce mata shi ba ya da masaniya a kan abin da ya faru. Tasalla ta yi matuƙar baƙin cikin wannan lamari kuma abin ya harzuƙa ta matuƙa. Da wannan baƙin ciki da mutanen garin suka haddasa mata, sai Tasalla ta ji haushi, ta yi wata waibuwa da ta sa duk ruwan garin ya ƙafe. Duk garin aka nemi ruwan sha aka rasa, ba ruwan wanka ballantana na wanki. Da mutanen garin suka rasa ruwan sha, sai suka shiga cikin wani mawuyacin hali. Da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya suka riƙa roƙon Tasalla ta taimaka masu da ruwa, ita kuwa sai ta tambayi yadda aka yi da kifinta, amma sai a ɓoye mata. Ita kuwa sai ta ƙi sauraren buƙatarsu na ta samar masu da ruwan sha. Mutanen garin suka shiga yin nadama a kan abin da suka aikata. Da mahaifiyarta ta zo, ta roƙe ta, sai Tasalla ta yi haƙuri, ta sakar masu da ruwan sha. Mutanen garin suka ji daɗin karimcin da Tasalla ta yi masu, sai suka ba ta wani kifin madadin nata. Allah ya sa wa wannan kifin albarka, ya girma sosai, ya yi ta hayayyafa har ya wadaci mutanen wannan gari. Kan ƙurus kan kusu.

 Wannan tatsuniya ba waibuwar sarkawa na hana jama’a shan ruwa kaɗai ta nuna ba, ta kuma nuna wata halayya ta kifi. Kifi halitta ce da aka san ta da yin tsalle. Kifin nan da aka sani da suna tsage, ya sami sunansa ne daga halayyarsa ta yin tsalle daga cikin ruwa, wani lokaci har ya faɗo a saman tudu.

2.5 Waibuwar Kifi

 Sarkawa sun haƙiƙance cewa iska ko aljannu kan shiga jikin kifi har kifin ya riƙa wasu abubuwa da suka gagari hankali ɗauka. Irin waɗannan kifaye kan buwayi wasu Sarkawa har su ɓatar masu da lissafi. Wani lokaci kuwa iska ce take rikiɗa, ta koma kifi ta yadda za ta riƙa yin waɗansu abubuwa na al’ajabi. Kifayen da aka fi danganta su da irin wannan halayya su ne ramboshi da yauni. A cikin tatsuniyoyin Hausa ana samun waɗansu da ke nuni da irin wannan hali. Misali, a cikin ‘Tatsuniyar Mahaukacin ɗansarki’[11] akwai irin wannan lamari.

 A cikin tatsuniyar, wani ɗan sarki ne hauka ta same shi. Haukarsa ba ta duka ba ce, ba ya zagin kowa kuma ba ya surutai barkatai. Haukar tasa ta kisan dabbobi ne, awaki da tumaki da kaji da duk wata dabba ta gida. Haukar tasa ta yi muni a inda ya daina kisan dabbobi ya koma kan ƙananan yara. Abin ya ishi talakawa har suka kai koke wajen Sarki wato mahaifin mahaukacin, a kan irin ɓarnar da yake yi na kisan yara. Sarki ya yanke shawarar a gina masa ɗaki amma a rufe ƙofa, sai a bar wata ‘yar taga wadda ta nan za a saka masa abinci. Bayan an ɗauki lokaci, sai Sarki ya yanke shawarar cewa a aura wa mahaukacin ɗansa mata, a saka masa a cikin ɗakinsa domin a gani ko ya warke hauka. Aka ɗaura aure da wata yarinya, aka zura ta a ɗakin mahaukacin. Da dare ya yi sai ɗan sarki ya kama amarya ya karya ta, ya raba ta biyu. Ko da aka zo da safe sai gawarta aka tarar. An sake ɗaura masa aure da wata matar karo na biyu da na uku amma duk sai ya kashe su, sai dai da safe a ɗauko gawarsu. Da aka ga haka, sai Sarki ya ce a bar shi har sai can gaba.

 A wannan garin, akwai wani mutum mai mata biyu, da bora da kuma mowa. Kowace daga cikin matan tana da ‘ya mace ɗaya tilo. Saboda mijin ba ya son Bora sosai, koyaushe ‘yarta ake sa wa aikace-aikace kamar wanke-wanke da share-share da ɗaukar ruwa. Ita kuwa ‘yar mowa ba a sa ta duk wani aiki mai wahala saboda mahaifiyarta ce baban ya fi so. Wata rana sai uban ‘yar bora ya ce ta je rafi ta kamo kifi domin a yi miya. ‘Yar bora ta je rafi, ta kamo kifi kamar yadda mahaifinta ya umurce ta. Aka yi miya da kifin aka cinye. Da safe kuma sai uban ya sake ce mata ta je rafi ta kamo kifin da za a yi miya. Nan take ta kama hanya sai rafi inda ta kamo kifi ta kawo gida aka yi miya. Wata rana sai aka sa ta kamo kifi amma da ta je rafi, sai ta kama wata babbar kifanya. Kifanyar nan sai ta ce da ‘yar bora don Allah ta sake ta domin ta je ta ba ‘ya’yanta nono sannan ta dawo ta kama ta. Saboda tausayi da Allah ya yi mata, sai ‘yar bora ta saki kifanyar nan ta koma ruwa. A jima kaɗan sai ga kifanya ta dawo ta ce wa ‘yar bora ta sake kama ta amma ‘yar bora sai ta ƙi kama kifanyar. ‘Yar bora ta ce wa kifanya ta koma wurin ‘ya’yanta. Kifanyar ta sake komawa cikin ruwa ta kamo wani kifi ta kawo wa ‘yar bora kuma ta umurce ta da cewa duk lokacin da ta zo kama kifi, ta shiga cikin ruwa wurinta za ta ba ta kifi. Daga wannan lokaci, koyaushe ‘yar bora ta je rafi kama kifi, sai kifanyar nan ta kawo mata kifi nan take.

 A kwana a tashi, ranar nan sai Sarki ya aika a kira masa uban ‘yar bora. Yana isa fada sai ya faɗi ya yi gaisuwa. Sarki ya shaida masa cewa yana son ya ba shi ɗaya daga cikin ‘ya’yansa domin ya haɗa su aure da mahaukacin ɗansa. Uban ya roƙi arziki wajen Sarki a ba shi dama ya shawarci uwar ‘yar da zai bayar. Da ya zo gida sai ya kira mowa ya ce da ita zai aurar da ‘yarta ga mahaukacin ɗan sarki. Mowa ta kafe ƙafa ga ƙasa kan cewa ba ta aminta a aurar da ‘yarta ga ɗan sarki da ke kashe mutane ba. Da haka sai uban ya koma wajen bora ya gaya mata cewa zai aurar da ‘yarta ga ɗan sarki. Nan take, bora ta aminta da haka domin a ganin ta, da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Uban ‘yar bora ya koma wajen Sarki ya gaya masa cewa ya aminta a ɗaura auren ‘yar bora da ɗan sarki, aka sa ranar buki.

 ‘Yar bora kuwa sai kuka ta riƙa yi domin ganin irin haɗarin da za ta shiga. Da ta je rafi wurin kifanyar nan, sai ta tambaye ta abin da ke damun ta har take kuka. ‘Yar bora ta kwashe labari duk ta gaya mata. Kifanya ta shaida mata cewa kada ta damu, za ta taimaka mata da maganin da ɗan sarki ba zai kashe ta ba. Kifanya ta gaya mata cewa wasu gasu ne guda goma na jikin ɗan sarki suke saka shi hauka. Don haka zan ba ki mayafi goma ta yadda idan dare ya yi, ɗan sarki zai riƙa tsinkar gashin jikinsa goma yana saka wa a wuta da ɗaɗɗaya. Duk lokacin da ya tsinki gashi ɗaya ya saka a wuta, ke kuwa sai ki jefa mayafi ɗaya a wutar. ‘Yar bora ta yi wa kifanya godiya ta koma gida aka yi buki. An saka ‘yar bora a ɗakin mahaukacin ɗan sarki bayan ƙare buki. Da dare ya yi, duk abin da kifanyar nan ta faɗa na game da ƙona gashi goma na jikin ɗan sarki ya kasance. Ita kuwa ‘yar bora ta ƙona mayafan da aka ba ta. Sakamakon haka, haukar ɗan sarki ta warke, suka yi zaman su cikin daula. Ƙurungus kan kusu!

2.6 Kifi A Maganin Gargajiya

 Bisa al’ada, akan yi amfani da kifi domin haɗa magungunan gargajiya daban-daban. Magungunan da kifi kan zama sinadari ko mahaɗi kan kasance magungunan waraka daga cuta ko magungunan tsafi ko na biyan buƙatun zuciya. Misali, a gargajiyance ana sarrafa kifi ko wani sashe nasa domin magance ciwon ido da ciwon kunne, ana amfani da fatar mijirya wadda ba a buga ba wajen haɗa maganin ba-sanyi. A cikin tatsuniyoyi na Hausa amfani da kifi wajen samar da maganin gargajiya kan bijiro sosai. Misali, a cikin ‘Tatsuniyar Ɗankutungayya,’[12]

 zancen kifi a matsayin mahaɗi na maganin gargajiya ya fito ne a inda dodanniya ta rikiɗa ta zama wata kyakkyawar budurwa. Yayan Ɗankutungayya ya sami sa’a ya aure ta. Dodanniya ta yarda da auren ne domin tana son ta yi ramuwar gayya a kan ta’asar da Ɗankutugayya (wani hatsabibin yaro) ya yi mata, ya sa ta kashe ‘ya’yanta. Da aka ɗaura aure, sai dodanniya ta ƙwaƙule ido ɗaya na angonta wato yayan Ɗankutungayya. Ɗankutungayya da ya ga haka sai ya rikiɗe, ya zama Bafillata mai sayar da nono, ya je gidan dodanniya da sunan tallar nono. Kullum dodanniya ta sayi nono wajen Bafillata ita kuwa sai ta yi mata arha sosai. Yau da gobe sai suka shaƙu sosai, aminci ya shiga tsakaninsu. Wata rana Bafillata sai ta shiga gidan dodanniya fusace, rai a ɓace. Dodanniya ta tambaye ta abin da yake damun ta, Bafillata ta shaida mata cewa wani lalatacce mai suna Ɗankumale kullum yake zuwa yana kashe masu shanu, yau ga shi har shanun sun kusa ƙarewa. Dodanniya ta ce da Bafillata ai ba Ɗankumale ne sunansa ba, Ɗankutungayya, lalatacce ne kuma mugu ne sosai. Ku yi hattara da shi domin ba shanunku ba kaɗai har ku ma sai ya kashe ku. Ni nan ‘ya’yana goma sha ɗaya ya sa na kashe. Yanzu haka ma na yi kusan makantar da yayansa domin kin ga idonsa da na ƙwaƙule. Bayan Bafillata ta yaba irin ramuwar gayya da dodanniya ta yi wa Ɗankutungayya, sai ta roƙa ta ba ta idon nan ko za su dace da ƙanenta wanda wai sanuwa ta harbe shi a ido har idon ya tsiyaye. Bafillata ta yi godiya sosai bayan da dodanniya ta aminta za ta ba ta idon domin a saka wa ƙanenta. Dodanniya ta ce wa Bafillata a nemo ƙwayaƙwayen kifi guda bakwai da hantar baƙin kare, da kiyashi guda bakwai da kaucin marke, a shanya su bushe, sai a niƙa, a rinƙa sa masa a ido tsawon kwana uku. A rana ta huɗu, a saka idon zai zauna.

Wannan tatsuniya haƙiƙa tana nuni da yadda al’adance ake amfani da sassan kifi wajen haɗa magungunan gargajiya. Ba a tatsuniya ba, har ma zahirance cin ƙwan kifi yana ƙara kyautata lafiyar ido da ƙara gani. Ba wannan kaɗai ba haka ma ana gasa hantar balli a ci domin magance ciwon dundumi.

3.0 Kammalawa

 Laluben Sarkanci A Tatsuniyar Hausa muƙala ce da ta yi ƙoƙarin fito da bayani a fili cewa adabi musamman na baka da aka yi waiwaye a kansa wata makaranta ce da za a iya koyon al’adar al’umma domin da adabi da al’ada suna da kusanci irin na jini da tsoka kuma al’ada takan yi tasiri soasi a kan adabi. Da wannan ne nake hasashe cewa idan wannan bincike ya nausa cikin wasu ɓangarora na adabin baka kamar waƙoƙin baka, za a iya duba yadda lamarin wannan sana’a ta sarkanci ta sami ambato a cikin waƙoƙi daban-daban waɗanda Makaɗa da Mawaƙan Hausa suka rera. Wannan zai ba da damar fitowa da bayanai na irin yadda sana’ar sarkanci ta yi naso a cikin waɗannan waƙoƙin. Ba wannan kaɗai ba, haka ma wasu rukuna na adabin baka kamar Karin Magana, za a iya duba ta a kuma fito da lamurran sarkanci a cikinta.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.[1] Duba Alkali,M.B.(1969)” A Hausa Community in Crisis: Kebbi in the Nineteenth Century.” M.A. Thesis, ABU Zaria. Shafi na 29-30.

[2] A duba Abubakar, A. (2001) An Introductory Hausa Morphology. Faculty of Arts, University of Maiduguri, Nigeria. Shafi na 23 – 27.

[3] Bargery, G.P. (1934) A Hausa-English Dictionary And English Hausa Vocabulary. Oxford University Press, London. Shafi na 92.

[4] Duba lamba ta ɗaya, shafi na 30.

[5] Ibn Manzur (2002) Lisanul Arab Vol. iv. Darul Hadith, Cairo. Shafi na 576.

[6] Dawkins, R.M. (1951) Folklore. Cikin Jstor Vol.62, No 2. Shafi na 417- 429.

[7] Akwai litattafai da aka wallafa waɗanda aka tattara tatsuniyoyi masu yawa a cikin su. Misalinsu ya haɗa da Edgar, F. (1911) Littafi na Tatsuniyoyi Na Hausa. Belfas da Fletcher, R.S. (1912) Hausa Sayings And Folklore London da Rattray, R,S. (1913) Hausa Folklore, Customs, Proverbs Vol.1&2 Oxford University Press da NNPC (1968) Labaru Na Da Da Na Yanzu Northern Nigeria Publishing Company, Zaria da Yahaya, I.Y. (1972) Tatsuniyoyi Da Wasanni 1-6 University Press Ltd. Ibadan. da Usman, B. (2010)Taskar Tatsuniyoyi ( Littafi Na ɗaya zuwa Na Goma Sha Huɗu A Haɗe) Gidan Dabino Publishers, Kano.

[8] Wannan tatsuniyar tana nan ƙunshe cikin Rattray, (1913: 74) Hausa Folklore, Customs, Proverbs, ETC. Vol.11 Oxford At The Clorendon Press. Tatsuniya ta 27, shafi na 74.

[9] Cikakken labarin wannan tatsuniya yana nan cikin littafin Bukar, U. (2012) Taskar Tatsuniyoyi Littafi Na Ɗaya Zuwa Na Goma Sha Huɗu. Maɗaba’ar Gidan Dabino, Kano, Nijeriya. Shafi na 602-605.

[10] Domin samun cikakkiyar wannan tatsuniya, a duba tushen bayani na 9 amma shafi na 360-362.

[11] Wannan tatsuniya tana nan cikin littafin Yahaya, I.Y. (19770 Tatsuniyoyi Da Wasannin Littafi Na Shida. Oxford University Press, Ibadan. Shafi na 45-58.

[12] Cikakkiyar tatsuniyar na nan cikinlittafin Bukar Usman (2012) Taskar Tatsuniyar Hausa Littafi Na Ɗaya Zuwa Na Goma Sha Huɗu. Gidan Dabino Publishers, Kano, Nigeria. Shafi Na 221-225.