A cikin shekarar 1909 Gwamna Luggard ya umurci Hans Vischer wanda ake yi wa laƙabi da Ɗan Hausa, da ya sake buɗa wata makaranta a Kano. Domin a horar da malamai ‘yan ƙasa musulmi da za su yi aikin koyarwa (Graham, 1966:79). Da tafiya ta miƙa sai aka dinga buɗe makarantu a Lardunan jihohin Arewa.

Ruwan bagaja

Bin Diddigin Silalen Tubalin Ginin Littafin Ruwan Bagaja

Dr. Adamu Rabi’u Bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

1.0 Gabatarwa

            Ƙudirin wannan maƙala shi ne, ta binciko asalin zaren tunanin da Abubakar Imam ya yi amfani da shi a yayin da yake fafutukar tattara tubullan tayar da ginin littafin Ruwan Bagaja. Gasar ƙagaggun labaran Hausa da aka aiwatar a shekarar 1933 da ta zama sanadin ficensa a fagen rubutattun ƙagaggun labaran Hausa, har duniya ta san shi.

            Sai dai gurin wannan maƙala ba zai cika ba sai ta waiwaya baya. An shiga fagen tarihi, domin asami damar sanin abin da ya shuɗe, ta kowace fuska yana da amfani ga rayuwar ɗan adam, musamman manazarta. Dalili kuwa, masana tarihi sun ce, duk wanda bai san abin da ya wanzu kafin a haife shi ba, zai taƙaita ga sanin abin da ya ji ko ya gani, ba tare da gane sanadin aukuwar hakan ba. Wannan ne ya sa maƙalar ta bi diddigin tarihin kafuwar makarantu boko, da hanyoyin da aka bi wajen ɗabbaƙa rubutattun ƙagaggun labaran Hausa cikin sigar rubutun Romawa (boko). Haka an kawo dalilan da suka haifar da wanzuwar hukumomin inganta adabi a ƙasar Hausa da ƙas ashen ƙetare. An kuma nuna irin rawar da suka taka wajen tabbatar da muradinsu na aza harsashin ginin rubutattun ƙagaggun Labaran Hausa. Ko ba komi ai an ce “ Waiwaye adon tafiya”. Domin yin haka, zai bai wa mai karatu haske game da inda aka fito da inda za a dosa.

 

 2.0 Makarantun Boko Na Farko A Ƙasar Hausa.    

            Bayan Turawan Mulkin Mallaka sun kafa mulki a ƙasar Hausa.Daga nan suka shiga tunanin buɗe makarantu domin koya wa ‘ya’yan Hausawa karatun boko. An kafa makarantun ne don su sami waɗanda za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukkan mulki da suka shimfiɗa. A sakamakon haka ne, suka buɗe makarantar farko a Sakkwato cikin shekarar 1905 a ƙarƙashin shugabancin Mista Burden da mataimakinsa Malam Ibrahim wanda daga baya aka tura shi Ingila domin ya ƙaro Ilimi (Graham, 1966:59) da ( Taiwo, 1986:45). Da farko Razdan na Sakkwato bai sami haɗin kan sarakunan yankin ba game da sabon tsarin ilimin, don gudun kada ‘ya’yansu su zama kiristoci (Ibrahim, 1979:32).

            Da suka fahinci lamarin ba haka yake ba. Sai suka yi na’am da shirin bayar da ilimin. Wannan ne ya sa Sarkin Gwandu ya tura yara biyu, haka sarkin Tambuwal ya aika da yara biyu. Ƙoƙarin samun jerin sunayen ɗaliban farko na makarantar ya faskara. A daidai shekarar 1907 makarantar tana da ɗalibai 36, waɗanda aka tura daga gidajen Sarakunan Sakkwato da Gwandu da Argungu, kamar yadda ( Taiwo, 1986:45) da ( Malumfashi, 2009:36) suka bayyana. Wannan ya kawar da ra’ayin da ke cewa, makarantar farko an assasa ta ne a kano ba Sakkwato ba. Abin kula a nan shi ne, Razdan da ya buɗa makarantar ai wakilin gwamnati ne, ya yi haka a madadin gwamnatin. Hasali ma ba wani jami’i da ke sama da shi da ya taka masa birki kamar yadda aka yi wa ‘yan mishan a yayin da suke ƙoƙarin buɗa makarantunsu a yankunan musulmi. An kuma ci gaba da koyo da koyarwa, har an kawo wani akawu da ke aiki a sashen mulki da ya saba da aikin koyarwa, a matsayin ƙaramin malami domin ya taimaki Malam Ibrahim wajen koyar da ɗalibai darussa na tsawon awa huɗu a sati (mako). Ba wata rubutacciyar shaida da ta nuna an rufe makarantar. Makarantar ce aka ci gaba da faɗaɗawa tun daga makarantar lardi ta zama ta midil, ta koma kwalejin gwamnati har zuwa lokacin da ta kasance Kwalejin Nagarta a yau 2013. Don haka ne aka ɗauki cewa, ɗaliban makarantar boko na farko sun fito ne daga Sakkwato ba Kano ba. Akwai kuma tabbacin cewa, Sarkin Musulmi ya ɗauki ɗawainiyar bayar da kuɗaɗen gudanar da makarantar. An kuma sami bayanan da suka nuna ɗalibai uku na makarantar sun kamala karatunsu, sun kuma kama aiki a Ofishin Razda a kan matsayin mataimakan akawu a shekarar 1907 (Taiwo, 1986:45).

            A cikin shekarar 1909 Gwamna Luggard ya umurci Hans Vischer wanda ake yi wa laƙabi da Ɗan Hausa, da ya sake buɗa wata makaranta a Kano. Domin a horar da malamai ‘yan ƙasa musulmi da za su yi aikin koyarwa (Graham, 1966:79). Da tafiya ta miƙa sai aka dinga buɗe makarantu a Lardunan jihohin Arewa.

3.0 Matakan Samar da Rubutattun Ƙagaggun Labaran Hausa a Sigar Rubutun Boko 

            Bayan kafuwar makarantu boko da yaɗuwar ilimin zamani a Nijeriya ta Arewa. Abu na farko da aka fuskanta shi ne, matsalar ƙarancin litattafan karantawa a makarantun. Yayin da Hans ya tafi hutu Ingila a shekarar 1911, ya gudanar da tarurruka da masu ruwa da tsaki ga sha’anin mulkin ƙasar, domin ganin an samar da littattafan karatu don shiga sabuwar shekarar karatu cikin watan Oktoba (Graham,1966:83). Ya kuma fuskanci matsalar rashin takamaiman abjadin da zai mayyaze saututtukan harshen Hausa a sigar rubutun boko (Graham,1966).

            ‘Yan Mishan sun haɗu a Lakwaja, suka gabatar da buƙatar samar da tsayayyen abjadin  da zai ƙunshi wasu saututtuka, na harsunan Hausa da Nufanci da Yarbanci da harsunan da ke Lardin Binuwai. A harshen Hausa, sun amince da a yi amfani da haruffa 29, idan aka cire harafin “q” da “x” a wajen rubuce-rubucen adabin mishan (C.M.S., 1911/NN).

            A Nijeriya ta Arewa, Hans Vischer ne mutun na farko da ya fara shata ƙa’idodin rubutun Hausar boko. A tsarin abjadinsa ya amince da ayi amfani da haruffa 28, ya cire haruffan “c” da “q” da “v” da “x”. Ya yi tsokaci a kan baƙaƙe da wasulla da auren wasali kamar “ai” da “au” da wakilin suna, da zagi, da yadda ake samar da jam’i da lokuttan aikatau. Ya aminta da a rubuta kalmomin Larabci da suka danganci shari’a da addini kamar yadda ake furta su a harshen Hausa. Sunayen Larabci kuwa za a rubuta su kamar yadda suke. Kalmomin Ingilishi kuwa sai a fassara su da Hausa (Vischer, 1912:3) da (Graham,1966:86) da (Zaruk, 1988:116-7).

            George Parcy Bargery ya yi wa abjadin Hausa wasu gyare-gyare da suka haɗa da:

Watsi da tagwan harafin “ch” ya ɗauki  “c”. Ya amince da harafin “sh” da “ts”. A wajen ɗauri kuwa, ya yi amfani da “ssh” da “tts”, ba “shsh” da “tsts” ba.

Ya yi amfani da waƙafi a gaban hamzatattun baƙaƙe a madadin ɗigagga da ake sawa a ƙarƙashinsu, misali: ‘b, ‘d, k’.

            Abjadin Bargery ya fi kusanta da lafuzzan Hausa fiye da na sauran da suka gabace shi. Ƙa’idojinsa na raba kalma sun fi na sauran , kamar yadda Zarruk (1980: 117-8) ya nuna.

4. 0 Samar Da Hukumomin Inganta Adabin Hausa

            Bayan wannan, sahihiyar hanyar da aka fara bi domin ganin an samar da ingantaccen harsashin gina ƙagaggun labaran  Hausa. Haka kuma an yi azamar samar da wasu hukumomi a cikin gida, da ƙasar Turai da aka aza wa alhakin kyautata adabin Hausa da kuma haɓaka shi. Hukumomin da aka ratayawa alhakin tafiyar da wannan aikin su ne:

(i) Hukumar Ƙasa Da Ƙasa Ta Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka ( International Insitute Of African Languages And Cultures) mai cibiya a London.

(ii) Hukumar Fassara (Translation Bereau). Da farko a Ofishin Makarantar Ɗan Hausa, Kano. A shekarar 1930 ta sami ofishinta na dindindin a Ƙofar Tukur-Tukur da ke Zariya.

(iii) Hukumar Talifi (Literature Bereau) mai cibiya a Zariya.

(iv) Hukumar Yaƙi Da Jahilci (Northern Regional Literacy Agency (NORLA) mai cibiya a Zariya.

            Waɗannan hukumomi sun yi rawar gani ta haujin biyan muradun da suka sa aka kafa su, a cikin fasalin da ya dace.

 

 

5. 0 Tarihin Samuwar Gasar Rubutattun Ƙagaggun Labaran Hausa

            Bayan da Turawan Mishan da haɗin gwiwar gwamnatocin mulkin mallaka sun samar da Hukumar Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka. Hukumar ta aza harsashin ginin adabin Afirka cikin sigar rubutun boko, musamman rubutaccen ƙagaggen labaran Hausa, a shekarar 1929. A farkon shekarar ne hukumar tare da hukumomin da ke kulawa da lamurran ilimin ƙasashen Afirka suka shirya gasar rubutun ƙagaggun labaran Hausa, da wasu harsunan nahiyar (zube). An gudanar da gasar ne a London, inda akasarin waɗanda suka fafata malaman makarantar boko ne. A  gasar an gabatar da littattafai 37. Littattafai goma daga ciki na harshen Hausa ne, littattafai sha biyar sun fito daga harshen Suto. Littattafai tara daga harshen Ganda. Littafi biyu kuwa daga harshen Madingo suke. Littafi ɗaya a cikin harshen Mende aka rubuta shi.

            Ba wani littafi da ya zo na ɗaya. An sami littafai biyu da suka sami kyautar fam goma kowannansu. A harshen Suto ‘yantakara huɗu suka sami kyautar fam biyar. Haka kuma, wasu uku suka sami kyautar fam uku. A harshen Hausa kuwa, ‘yantakara biyar ne suka sami kyautar fam uku kowannansu. Daga cikin littattafan da suka sami kyauta a harshen Hausa sun haɗa da:

Hausa Stories            na        H.G.B. Nuhu,

Hausa Stories            na        Malam Dodo,

Zaman Dara  na        Malam Ahamet Metteden,

Littafin Karatu Na Hausa   na        Malam Bello Kagara,

Takobin Gaskiya      na        Malan Nagwamatse Ɗan M. Alƙali Sakkwato (Westerman,1933:102-3).

            Abin kula a nan shi ne, hukumar ba ta wallafa  waɗannan littattafai ba. Ta dai buƙaci hukumomin ilimi da ƙungiyoyin Mishan da lamarin ya shafa, su taimaka su buga. Sai dai har zuwa yau, babu wani rubutatcen bayanin da aka ci karo da shi mai nuna an buga littattafan.

 

5. 1 Littattafan Ƙagaggun Labaran Hausa Da Aka Fara Wallafawa

            Tun lokacin da aka fara ƙoƙarin samar da littattafan ƙagaggun labaran Hausa. Ba a sami littafi ko ƙwara ɗaya da aka wallafa ba, domin koyarwa tare da nishaɗantarwa ga al’umma. Domin har zuwa farkon shekarar 1933, ba wani wallafaffen rubutaccen littafin ƙagaggen labaran Hausa. Hana rantsuwa littafin Fatima  wanda Dokta Walter R. Miller ya wallafa, wanda Church Missionary Society Bookshop suka buga a Legas cikin shekarar 1933. Sai dai littafin bai yi fice ba, sakamakon jigon da ya ƙunsa na yaɗa addinin mishan.

            A cikin shekarar ne, gwamnati ta hango buƙatar wallafa littattafan ƙagaggun labarai cikin harshen Hausa, don amfanin masu koyon Hausar boko. Wannan buƙata ta sa R.M. East yin rangadin sassan Arewacin Nijeriya. An gana da ‘yan boko game da manufar da aka sanya a gaba ta shiga gasar rubuta ƙagaggun labaran Hausa. Kuma an yi alƙawalin za a bayar da kyauta ga wanda ya nuna hazaƙa a kuma buga littafinsa duniya ta san shi (Ibrahim, 1979:34). Wannan gasa ita ta samar da littattafan ƙagaggun labaran Hausa da suka yi fice, waɗanda suka  haɗa da:

Ruwan Bagaja                       na        Malam Abubakar Kagara,

Ganɗoki         na        Malam Bello Kagara,

Shaihu Umar na        Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa,

Idon Matanbayi        na        Malam Muhammadu Gwarzo,

Jiki Magayi    na        R.M.East da Tafida, da kuma

Iliya Ɗanmaiƙarfi     na        Malam Ahmadu Ingawa, kamar yadda (Ibrahim, 1979:34) ya nuna. Ayyuka da dama kamar, East, R.M. (1941), da Baldin, S. (1977), da Yahaya, I.Y. (1988), da Malumfashi, I..(2009) ,da Adamu, A.A.(2009) bas u sanya shi ciki sahun littattafan gasar farko ba. An dai nuna an wallafa shi a shekarar 1951, bayan shekara 17 da yin gasar.

            Duk da kasancewar waɗannan ne aka zaɓa a matsayin waɗanda suka sami nasara. An tsara wasu da aka yi ƙudurin wallafawa. Sai dai hakan bai samu ba. Littattafan kuwa su ne:

Boka Buwayi na        Malam Nagwamatse,

Yarima Abba na        Malam Jumare.

            Wannan ita ce gasa ta biyu, a cikin tarihin rubutaccen ƙagaggun labaran Hausa. Kuma ita ce ta zaƙulo mutane masu hikima da suka bayar da gagarumar gudummawa, wajen haɓaka karatun boko da rubutaccen adabin Hausa.

            Littafin Ruwan Bagaja, ya samu nasarar zama na farko a gasar.  Littafin yana ƙunshe da babi takwas ban da gabatarwa. Littafin ne ya fito da Abubakar Imam  fili har duniya ta san shi. Saboda irin yadda littafin ya samu karɓuwa a hannun Turawa. Ko kuma a ce,  alƙalan gasar, da suka yanke hukunci cewa, littafin ne ya zama zakara a kan wasu dalilai da za a iya gani nan gaba.

6. 0 Tubalan Ginin Littafin Ruwan Bagaja

            Abubakar Imam ya ƙaga littafin ne ta hanyar, tsakuro nan, da can, ya haɗa labaran da ke cikin littafin. Littafi yana ƙunshe da tubalai a ƙalla guda biyar, da mawallafin  ya yi amfani da su wajen gina littafin nasa. Tubalan kuwa su ne:

6. 1 Tatsuniyar Ruwan Bagaja :

            Idan aka ɗauki taken littafin ana iya cewa an samo shi ne daga tatsuniya mai suna “ Tatsuniyar Ruwan Bagaja”. Ita dai wannan tatsuniya ta ƙunshi labarin ‘yar bora, wadda aka yi wa ƙagen ta yi fitsari a ƙirgi. Don haka, aka tura ta kogin Ruwan Ruwan Bagaja wajen wanke ƙirgin. Tafiyarta kogin ya zama sanadin ta sami alheri mai yawa tare da martaba. Ta samu dukiya mai ɗinbin yawa. Ga yadda aka nuna a tatsuniyar: “Da ta fasa sai tag a mutane sun ci ado sun hau dawakai ana busa algaita ana yi mata kirari. A ɗora ta kan doki aka raka ta gida. Duk ƙamshin turare da bushe-bushe suka cika gari” (Yahaya, 1971:42 bk4). A ɗaya ɓangaren kuma, sarkin garinsu ya aure ta. Wannan ya faru ne sakamakon dangana da rashin kwaɗayi da tare da ladabin da ta nuna ( Yahaya, 1971:33, Bk4).

            A littafin Ruwan Bagaja, an nuna Alhaji ya tafi neman Ruwan Bagaja, a sakamakon cin mutuncin da sarki ya yi wa mijin mahaifiyarsa a bainar jama’a (Imam, 1994:5-6). Tafiyar ta zamar masa alheri. Ya samo zobe daga Sarkin Aljannu, wanda ke da wani bawa mai yin hidima ga zoben tare da biyan buƙatun wanda ya mallaki zoben. Ga yadda aka nuna “Da za mu rabu, ya kawo wani zobe ya ba ni na zinariya, ya ce shi ma yana da bawa kamar na takobin nan. In na ji na matsu, na goge shi sai bawan ya fito, don ban iya riƙon takobin nan” ( Imam,1994:40). A ɗaya haujin kuma, ɗan sarkin garin ya warke daga cutar da ke addabarsa (Imam,1994:42-4).

6. 2 Tatsuniyar Gizo da Hankaki

            Idan aka duba littafin Ruwan Bagaja, za a tarar akwai alaƙa a tsakaninsa da tatsuniyar. Domin a labarin, an nuna Alhaji Imam  ya tsunduma a cikin ruwa. Da ya nutse ya sadu da garin ‘yanruwa. Ga yadda aka nuna lamarin “..Yau ga yaran banza, sun dai mai da mutane makafi. Ai na san mun kawo. “sai na diro daga jirgi wai in faɗa ƙasa. Da faɗawata sai na nutse, na yi ƙasa! Abin ikon Allah sai na isa wani gida a ƙasan tabkin, na tarad da waɗansu irin mutane masu manyan kawuna. Ashe ‘yan ruwa ne, suka yi maraba da ni” (Imam,1994:16). Wannan ya auku ne sakamakon rashin godiyarsa ga yaransa guda biyu. Haka a tatsuniyar gizo da hankaki, an nuna gizo ya tsunduma cikin ruwa bayan hankaki sun gudu sun bar shi a kan itaciyar dabinon. A wani ƙaulin, ɓaure da ke tsakiyar ruwa. Ga yadda tatsuniyar ta nuna “…Sai ya faɗa cikin ruwa tsundum. Ya nutse can ƙasa. Sai kuwa ‘yan ruwa suka gan shi suka ce, “La, ga shi ya zo, ga shi ya zo” (Yahaya, 1974:7 bk1). Wannan duk sakamakon rashin godiyarsa a kan karamcin da hankaki suka yi masa tun da farko ta hanyar ba shi dabino. Irin waɗannan kamance da kusance ya sa ake zaton daga tatsuniyar aka gina labarin. Dalili kuwa, tatsuniyar ta riga littafin samuwa.

6. 3 Tatsuniyar Gizo da Fatalwa

            A cikin kayan cikin littafin an nuna Alhaji Imam ya karɓi san Zandoro ɗan Zantori a bisa sharaɗin, bayan kwana bakwai zai dawo a biya shi ta hanyar taɓa kansa. In ya kasa zai tafi da shi ya yanka ya ba gunkinsa jini ya sha. Ga yadda lamarin yake “..Wa zai amshi sana, in an yi kwana bakwai in zo ya taɓo kaina?” (Imam, 1994:16) Labarin bai da wani bambanci da abin da ke cikin tatsuniyar gizo da fatalwa, wadda aka nuna gizo ya karɓi saniyar Fatalwa bisa sharaɗin bayan shekara ɗaya za ta dawo ya taɓa kanta. In ya kasa za ta je da shi ta yanka ta sha jininsa. A tatsuniyar an nuna cewa “ Fatalwa tana yawo da santa cewa “ Wa zai karɓi sana, in shekara ta dawo in zo ya taɓa kaina?  (Rattray, 1913) Bambancin da ke takaninsu shi ne na suna. A littafin an ce Zandoro, a tatsuniyar kuma aka ce Fatalwa a wani ƙaulin aka ce Mutuwa. Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen kuɓuta duk kusan ɗaya ne. Domin kuwa, lokacin da Zandoro ya je a taɓa kansa ya sami Alhaji Imam na cikin ɗaki. Ya tsaya na tsawon lokaci yana jiran shi ya fito, har ya kai ga yi masa magana. Shi kuma Alhaji ya ce wai ya tsaya lallaɓe bangon ɗakinsa da ya tsage. Lokacin da Zandoro ya sunkuya ya leƙa cikin ɗakin ya ganar wa idonsa yadda ake ɗinke bango, sai Imam ya yi farat ya shafa kan zandoro ya ce na taɓa, mutane suka shaida ya taɓa. An nuna shi kamar haka a littafin, “…To fito, alƙawali ya cika!” Sai na ce masa, Dakata kaɗan, in gama lallabce bangon ɗakin nan da ya tsage da damina”. Ya ce, “Kai yaya ake ɗinkn bango? Na ce ba wuya a garinmu, leƙo ka gain.” Sai ya cuso kai don ya gain. Sai na yi farar na taɓa kansa, na ce, “ Ah na taɓa!” (Imam, 1994:16-17).   

            A tatsuniyar Gizo da Fatalwa ta irin wannan hanyar ce aka kuɓuta. Shi ma Gizon ɗaki ya shiga, Fatalwa ta yi ta jiransa har ta ƙagara ta yi masa magana. Sai ya ce, wai ruwan da ya zube ne yake tsinta. Jin haka sai ta sunkuya ta ga yadda ake tsintar ruwa. Da ga nan sai ya yi farat ya taɓa kanta. Shi ma mutane suka shaida ya taɓa. Ga yadda aka nuna a tatsuniyar “ To fito alƙawali ya cika!” Gizo ya ce mata, “ jira ni kaɗan ruwa suka zube, ina tsincewa ne” Sai ta ce, “ Kai yaya ake tsintar ruwa? Bari in leƙo in ga yadda ake tsintar ruwa”. Sai ta saka kanta ɗakin, sai ya yi farat ya taɓa. Ya ce, Eh! Na taɓa!   Duk waɗannan tatsuniyoyin sanannu ne a farfajiyar ƙasar Hausa. Sai ɗan bambancin da akan samu a cikin su. Saboda wannan kusanta ne, ake kyautata zaton cewa, da waɗannan tatsuniyoyi ne ya yi amfani wajen gina wasu sassan littafin Ruwan Bagaja.

6. 4 Ma’ul Haya (The Water of Life)

            Birniwa (1981-2) da Malumfashi (2009)  sun nuna cewa, an gina littafin Ruwan Bagaja a kan wani littafin Larabci da ake kira “MA’UL HAYA” wanda Turawa suka fassara da “ WATER OF CURE”. Masu wannan ra’ayi sun nuna cewa, Larabawa sun riga Turawa samun wayewar kai. Wannan ya sa, suka koyi harshen Larabci. Hakan ne ya ba su damar fassara wasu abubuwan Larabci ciki harshen Ingilishi. Ko ma tatsuniyar Ruwan Bagaja ana kyautata zaton daga Larabci aka samo ta. A lokacin da malaman zaure suka karanta irin waɗannan littattafai na Larabci. Su kuma suna gaya gaya wa mutane a yayin da ake gudanar da darussa. Wai daga nan ne ake jin tatsuniyar ta bayyana (Tsiga,1986).

            Ana kyautata zaton akwai wasu tubalai da aka ciro daga wani littafi mai suna The Brothers Grimm Fairy Tales musamman a labarin “The Water of Life”. Misali a littafin Ruwan Bagaja, an nuna cewa, Yarima ɗan sarki ba ya da lafiya, sai an kwantar an tayar. Liman, uban Imam ya bayar da shawarar a nemi Ruwan Bagaja a ba Yarima ya sha, zai warke. Shawarar ta baƙanta wa sarki rai har ya muzanta Liman a bainar jama’a. Wannan lamarin ne sanadin fitar Imam zuwa neman Ruwan Bagaja (Imam, 1994:5-6). A labarin The Water of Life kuwa an nuna sarkin ne ba lafiya, ‘ya’yansa suka damu matuƙa, har wani tsoho ya bayar da shawarar a nemo Ruwan Bagaja. Ga yadda aka nuna. “Wata rana, sai sarki ya tashi da rashin lafiya, sai a kwanta, sai a tayar. Ciwo ya tsananta, har an fitar da zuciya ga rayuwarsa. Rashin lafiyar sarkin, ta sanya ‘ya’yan nasa cikin yanayi na damuwa. Wata rana suna yawo a cikin lambun sarki, sai suka haɗu da wani tsoho. Tsohon ya tambaye su abin da ke damun mahaifinsu, sai suka bayyana masa. Tsohon nan y ace, “Na san maganin da zai warkar da shi, da za a sami Ruwan Bagaja ya sha kaɗan, da ya warke. Sai dai samun rowan ne ke da wahala”(Grimms, 1906:306). In aka dubi wannan a iya cewa, Imam ya sauya suna ne kawai domin babu wani bambanci a tsakani.

            A littafin Ruwan Bagaja, an nuna Imam ya fita neman Ruwan Bagaja. “Ya isa wani dutse mai kogo, inda ya sami wani tsoho a ciki yana ibada, wato wan Liman da aka muzanta. Tsohon ne ya buga ƙasa ya bayyana masa inda Ruwan Bagaja yake, wato hannun aljannu (Imam, 1994:4). Yayin da aka nuna  ɗan autan sarki ne ya haɗu da wadan tsoho a cikin dokar daji, wanda ya bayyana masa inda zai samo ‘The Water of Life’ da yadda zai same su. An nuna lamarin kamar haka “Ɗan autan sarki ya fita nema Ruwan Bagaja. Ya haɗu da wada a kwaren tsauni da cikin daji. Ya bayyana masa cewa, mahaifina bay a da lafiya, sai a kwanta, sai a tayar. Ina neman inda zan sami Ruwan Rayuwa. Dan Allah ka taimake ni , ka faɗa mini, idan ka san inda suke” (Grimms, 1906:309).

            Haka kuma, kamar yadda Imam ya gamu da abubuwa masu ban al’ajabi wajen shiga rijiyar Sinaini. Ya ga saniya tana tatsar Bafillatana, da doki bisa mutum, da kare na zagi, da sauran su. Haka aka zayyana ɗan autan sarki ya haɗu da zakuna baki buɗe. Ba su iya yi masa komi. Da wasu masu sarauta da ba sa iya cewa ƙala, da wani takobin tsafi da sauran su. Ga abin da ka bayyana, “Zan bayyana maka inda za ka samo ruwan. Rowan da kake nema suna cikin wata sammatatciyar rijiya ce. In Allah Ya so za ka isa wajenta salum alum. Zan ba ka sihirtatcen ƙarfe da yankan burodi biyu. In ka isa ka daki ƙyauren ƙofar da wannan ƙarfen sau uku, zai buɗe. Za ka tarar da miyagun zakoka buɗe da baki. Ka jefa musu burodin za su bari ka wuce” (Gramm, 1906:309). Duk waɗannan abubuwa ne da ake zaton Abubakar Imam ya tarkato, ya haɗa, ya tayar da labaransa bayan ya sauya musu kama.

 

6. 5  Alfun Laila Wa Laili 

            Duk wanda ya taɓa karanta Dare Dubu Da Ɗaya zai haƙiƙance an yi amfani da salon tsarinsa wajen gina labarin littafin Ruwan Bgaja. Misali, Imam ya soma gini littafinsa ta hanyar bayar da labarin wani mutun wai shi “Koje Sarkin Labari”. A ɗaya littafin ma da irin wannan salo aka soma. Inda Shaharuzadi ta yi ta ba sarki Sharuzaman labarai iri-iri. Aikin sarkin shi ne, kashe budurwa a daren da ya kawar da budurcinta. Duk da haka saboda hikimarta. Bayan ya sadu da ita. Ta ce za ta gaya wa ‘yar uwarta labarai wanda shi ma sarkin ya kwaɗaita da ya ji labaran (Edgar, 1970:1-11).

            A Ruwan Bagaja, Imam ya nuna cewa, cikin tafiye-tafiyen Alhaji, ya isa wani gari da ake kira Tambutu. Da ya shiga garin,  ya wuce fadar sarki, inda sarki ya saukar da shi. Daga baya ya shaƙu da wani tajiri, wanda ya yi wa ƙaryar cewa, shi falke ne, shanunsa na baya, alhali shanun wasu ne. Wannan ƙaryar ta sa tajirin ya amince da Imam har ya rinƙa ba shi bashi, a kan waɗancan shanun da ya yi ƙaryar mallaka (Imam, 1994:7). Wannan ya yi daidai da yadda Ma’aruf Baduku ya shirya wa sarki a cikin “Hikayar Ma’aruf Baduku da Matarsa Fatima” da ke cikin Alfu Laila (Mac, 1893:329) Malumfashi (2009) ya nuna. Shi Ma’aruf da ya sauka a garin, sai ya yi wa sarkin ƙaryar baro dukiya a baya. Har ya kai ga cin bashi wurin sarki a kan alƙawalin in dukiyarsa ta iso, sarki ya ɗebi duk abin da yake buƙata. Har Ma’aruf ya kai ga auren Gimbiya, ‘yar sarki a kan sadakin da ke ciki waccan dukiyar da ya yi ƙaryar mallaka.

            Kamar yadda aka zayyana cewa, Alhaji Imam ya je Ruwan Bagaja a rijiyar Sinaini. Yayin  da aka nuna Jaudaru ya je ɗauko kayan tsafi a cikin taskar tsafi. Haka ma, tamkar yadda aka nuna Imam ya ɓata wajen ƙirga ɗaki na biyar daga dama, ya shiga na shida. Sai ya ruɗe ya ƙirga na huɗu daga hagu, ya shiga na biyar. A Ruwan Bagaja Imam ya ce: “Da kutsa kai sai ya ji an ce, “ya yi kuskure ku buge shi! Aka same ni tatas aka jeho ni wajen gari duk da takobin nawa har na karye a ƙafa….(Imam, 1994:39)”. Wannan ya yi kama da yadda aka nuna Jaudaru ya yi kuskuren shiga ƙofofin taskar. Shi ma Jaudaru da ya isa ɗakin da mahaifiyarsa take. Ya kasa yi wa mata zindir tamkar yadda aka shata. Har ya haddasa ma kansa matsala. Nan take matar nan, ta fasa kururuwa da ƙarfin gaske, ta ce: “A aaah. Ooooh!! Ya yi kuskure ku buge shi! Haba ai sai aka rufe shi da bugu da mari da mangari kamar ruwan sama. Aka yi masa ligi-ligi, ba ya ko motsi, sannan aka jeho shi waje…..(Mac,1839:110) da Malumfashi (2009).

 

6. 6 Muƙamat al- Hariri 

            Idan aka yi wa littafin nazari na basira za a tarar cewa, marubucin ya yi amfani da salon da ke cikin littafin. Shi ma marubucin ya tabbatar da haka, a wata hira da aka yi da shi, a inda yake cewa: “Littafin Ruwan Bagaja wata dabara ce na samo daga wani littafi na Larabci mai suna Muƙamat al – Hariri. A labarin ya nuna mutum biyu ne, ɗaya yana ƙoƙarin ya wayance ɗaya a irin hanyar wayo da dabara na Larabawa. To ni kuma sai na ɗauki mutum biyu ta irin wannan salon, amma kuma na yi amfani da irin hanyar wayancewa ta Hausawa da dabarunsu a rayuwar Hausa (Kano, 1995:88)”.

            Malam Zurƙe da ya yi amfani da shi a cikin labarin , ba shi ya ƙago sunan ba. Domin akwai shi a wani lokaci da ya shuɗe a Katsina. Dokta Abubakar Imam ma ya tabbatar da wanzuwarsa a inda yake cewa: “ Amma shi Malam Zurƙe wani mutum ne mai ban dariya a kasuwar Katsina. Tun muna yara mukan so mu je kallon sa. Abin da yake yi shi ne, sai ya saka tsummoki yana bin kasuwa yana kiɗa yana rawa. Tun asali ba a san shi da Malam ba, ni ne na sa mishi Malam Zurƙe don labarin ya yi armashi (Kano, 1995:90).

7. 0 Kammalawa

A iya namu bincike mun fahimci cewa, littafin yana ƙunshe da wasu abubuwa da aka fassara daga littattafan Larabci da na Turanci. Haka kuma, an yi amfani salon juyar   ayyukan wasu. Shi ma Abubakar ya tabbatar da haka a inda ya ce: “Abin da kawai ya dame ni shi ne, in karanta wata dabara ta wasu marbuta in fahimci inda suka dosa, sai in ajiye in ci gaba da ƙirƙiro tawa dabarar ta hanyar hasken da na samu daga nasu dabarun” (Kano, 1995:88). Haka ya fito fili yana bayyana cewa: “… na kwaikwayi salon wasu labarai wani littafi na Larabci mai suna Maƙamat al –Hariri. A cikin labaran akwai sunayen wasu mutane su biyu, Abu Zaidi da Harisu, Su ne na mayar Alhaji Imam da Malam Zurƙe (Kano,1995:90).

Wannan maƙala ta bayar da haske game da kafuwar makarantun boko a ƙasar Hausa. Da hanyoyin da aka bi wajen shimfiɗa harsashen ginin  ƙagaggun Labaran Hausa. Ta kuma yi tsokaci a kan hukumomin inganta adabi, da tarihin samuwar gasar ƙagaggun labaran Hausa. An kuma bayyana jerin littattafan farko da aka fara bugawa. An yi haka ne, domin a ɗora tarihi a kan nagartatcen ma’auni. Musamman ganin cewa, wasu masana, Allah bai nufe su da samun damar  aza hannayensu a kan wasu rahotanni da Turawa suka taskace ba, da suka danganci rubutattun ƙagaggun Labaran Hausa.

Kamar yadda ya gabata ne, an fahimci cewa, an gina littafin Ruwan Bagaja, a kan abubuwa da dama. Daga cikin su akwai adabin baka na Hausa. Musamman tatsuniyar Ruwan Bagaja, da tatsuniyar Gizo da Hankaki, da tatsuniyar Gizo da Fatalwa, ko Mutuwa. Ma rubucin  ya yi amfani da wasu littattafan Larabci. Misali Littafin  Ma’ul Haya, da Alfun Laila Wa Laili, da Muƙamatul al-Hariri. An kuma yi amfani da barkwanci da waɗanda hankali bay a ɗauka. Bai tsaya kawai nan ba, har ya haɗa da wasu abubuwa day a gain a rayuwa ta zahiri, kamar Zurƙi.

Wannan wata manuniya ce, a kan yadda ilimin addinin musulunci ya yi tasiri ga rayuwar marubucin. Fatata ita ce, maƙalar ta zama sharer fage game da wasu sassan da ban taɓo ba, domin zurfafa bincike.   

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda