Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Gimshiƙin Kafa Mulkin Adalci A Dimoƙuradiyya

 Al’amarin tafiyar da shugabanci a tsarin siyasa yana buƙatar mutane masu ƙwazo da himma da sadaukar da kai da kuma kishin ƙasa. Samun irin waɗannan mutane ya danganta ga yadda aka tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma domin su shiga, tare da zaɓen jam’iyyar da mutane masu manufofin gina ƙasa. Dalilin haka ya sa wannan takarda za ta tattauna a kan rawar da marubuta waƙoƙin siyasa suke takawa wajen yin amfani da salon sifantawa, da kamantawa, da alamtawa da mutuntawa da dabbantarwa da abuntarwa da kuma karin magana a cikin waƙoƙinsu, domin su faɗakar da jama’a dangane da zaɓen mutane masu mutunci da amana domin a kafa mulkin adalci da gina ƙasa a Nijeriya.

Salo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Gimshiƙin Kafa Mulkin Adalci A Dimoƙuradiyya

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0 GABATARWA

A duk lokacin da aka yi maganar salo, mutane za su riƙa tunane daban-daban a kan abin da ake nufi da salo. A mahangar marubuta waƙoƙin siyasa, salo wata dabara ce ta jawo hankalin al’umma ga su mai da hankali wajen iya zaɓen mutanen da suka dace. Dan haka ne ya sa marubutan sukan yi amfani da salo daban-daban kamar siffantawa da kamantawa, da alamtawa da mutuntawa da abuntarwa da dabbantarwa da  karin magana da sauransu domin jawo hankalin jama’a su zaɓi mutane na gari masu gaskiya da riƙon amana don a kafa mulkin adalci a ƙasa.

 

1.1 MA’ANAR SALO

Za a iya ba da ma’anar salo ba da ma’anar salo ba tare da ya kawo kalmar dubara ba. Babu shakka salo abu ne mai sauƙin bayyanawa, idan aka dubi yadda masana daban-daban suka yi tsokaci a kan ma’anarsa.

 

Bisa ga bayanin Ulman (1973:133) da Turner (1973) nazarin salo abu ne da ke cin gashin kansa kamar yadda nazarin ilimin harshe yake cin gashin kansa, wato nazarin salo yana da sashe-sashe kamar yadda nazarin ilimin harshe yake da shi.

 

Dangambo (1981) yana ganin cewa salo wani abu ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu. Kuma ya nuna cewa salo wani ƙari ne na daraja a cikin rubutu ko furuci, wanda ba lalle ba ne a same shi cikin kowane rubutu ko furuci. Ya ƙara da cewa, salo ya shafi kauce ma daidaitacciyar ƙa’ida a cikin kowane fanni na ilimi.

 

Har wa yau ya ƙara da cewa, salo harshen wani mutum ne, wato salon Audu yana iya bambanta da na Tanko. Mukhtar (1987).

 

A taƙaice dai salo wata dabara ce wadda kowane marubuci ke amfani da ita wajen sarrafa harshensa cikin rubuta ko furuci da ya shafi nazarin harshe ko adabi. Idan aka dubi yadda marubuta waƙoƙin siyasa suke amfani da salon sarrafa harshe cikin rubutattun waƙoƙinsu sai a fahimci cewa, bayanan da suka gabata game da ma’anar salo, sun yi daidai da yadda marubuta waƙoƙin Hausa suke amfani da salo wajen sarrafa harshensu cikin irin hikima da baiwar da Allah ya yi masu ta isar da saƙonsu a rubuce cikin waƙe. Saboda haka a fagen nazarin waƙa salo wani muhimmin abu ne da ke fitar da ƙimar waƙa a idanun masu sauraro ko masu karatu. Kuma ya jawo ra’ayinsu zuwa ga karɓar abin da ake so su karɓa ko yarda da shi hannu biyu. Haka kuma shi ne ke sadar da mawaƙi da masu saurare ko karatun waƙarsa.

 

Waɗannan hanyoyi da dabaru da ake magana a kansu sun shafi yadda mawaƙi ya yi amfani da harshen da yake yin waƙarsa cikinsa. Kuma wannan salo ya haɗa da yadda mawaƙi ya tunƙa tunanensa, da yadda ya gabatar da baitocin waƙarsa kan takarda. Duk abinda ya shafi azanci ta fuskar yadda mawaƙi ya sassaƙa kalmomi cikin waƙa domin ya jawo hankalin masu saurare don su ƙara sauraren waƙarsa, ko mai karatu ya karanta waƙarsa kuma ya fahimci saƙon da take ɗauke da shi, to shi ne ake kira salo Dangulbi (2003).

 

Da wannan ɗan taƙaitaccen bayani na ga ya dace in karkata akalar takardar tawa zuwa ga yadda marubuta waƙoƙin siyasa suke amfani da salo a cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran jama’a zuwa ga zaɓen mutane/ shugabanni nagari masu gaskiya da riƙon amana. Sannan haka zai kawo sauyi mai ma’ana a cikin siyasar wannan zamani da ake ƙishir ruwar adilan shugabanni domin samun cigaban dimokuraɗiyya a Najeriya.

 

2.0 IRE-IREN SALO A CIKIN WAƘOƘIN SIYASA

Akwai salailai daban- daban a cikin waƙoƙin siyasa da suka haɗa da siffantawa da kamantawa da alamtawa, da mutuntawa, da abuntawa da dabbantarwa da kuma karin magana. Za a ɗauki waɗannan salailai ɗaya bayan daya, domin a ga yadda marubuta waƙoƙin siyasa ke sarrafa harshensu wajen yin amfani da salo cikin waƙoƙinsu don jawo hankalin jama’a su fahimci irin mutanen da suka cancanta a zaɓa a lokacin jefa ƙuri’a domin a samar da shuwagabanni nagari.

 

2.1 SIFANTARWA CIKIN WAƘOƘIN SIYASA

Sifantawa na nufin kawo hoton abu kusa ga jama’a domin su fahimci yadda abun yake ƙarara. Yahya (1997). Ya bayyana sifantawa a cikin waƙoƙin siyasa da cewa wani salo ne da marubuta waƙoƙin ke amfani da shi domin su bayyana abu ko mutum ta yadda jama’a za su fahimce shi. Wannan salo ne da ke kawo hoton abu kusa ga jama’a domin ya fahimtar da mai karatu ko mai sauraren waƙa ga abin da yake so ya sani. Salon sifantawa hoto ne cikin bayani da kalmomi suka kawo tare da ma’anoninsu. Wato wasu surori ne da mawaƙi ya saka cikin waƙarsa, kuma kowace sura da mawaƙi ya ba abu ko mutum cikin waƙarsa za ta dace da ma’anar abin da yake son ya ce game da wannan abu ko mutum. Misali a cikin waƙarsa ta jam’iyyar P.D.P, Shu’aibu Yar Medi Ƙaraye, Kano yana cewa:

Ga ƙwaryar zuma ko da an wanke ba a zuddawa

Malam Shugaba Ibrahim in kun kasa ganewa

Malam Assalamu – Alaikum ya kayar da udawa

Al’ummar Malumfashi ta katse Malam mazanmu da mata

A wannan baitin ya sifanta jam’iyyar P.D.P da wani ɗanta da ƙwaryar zuma, kowa ya san cewa ƙwaryar zuma cike take da zaƙi wadda ko da an wanke ta ruwan nan ba za a zubar da su ba saboda zaƙinsu. Mawaƙin yana son ya nuna wa jama’a irin muhimmancin da jam’iyyar P.D.P da ɗanta suke da shi a cikin tafiyar siyasa ta lokacin da yake waƙar, wato Malam Ibrahim Lawal Assalamu Alaikum da jam’iyyar P.D.P suke da shi a ƙaramar hukumar Malumfashi wato ya sifanta jam’iyyar P.D.P da Malam Ibrahim Lawal Assalamu Alaikum da ƙwaryar zuma saboda irin halayensu da kuma gudummawar da yake bayarwa ga tafiyar Jam’iyyarsa ta P.D.P a karamar hukumar mulki ta Malumfashi, jihar Katsina a lokacin da ya riƙe kujerar shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi.

 

Shi kuma Aminu Ibrahim Ɗandago Kano a cikin waƙarsa ta jam’iyyar A.P.P, ya siffanta jam’iyyar da uwa ta gari mai tausayin ‘ya‘yanta wadda ta rungumi dukkansu ba tare da bambanci ba. Ga abin da yake cewa:

A masu muradi a jingine tamu waje ɗaya,

Jan gora sai uwar da taz zam mai juriya

Ga ta da hali da ba tunanen ‘yan danniya

Mai naira hat-talakka duka za a ci moriya

Don haka fito a tsaida tamu a Nierjiya

Malamin ya siffanta jam’iyyar A.P.P da uwa da ke jure wa jidalin ‘yayanta, wannan kuma salo ne da ke jawo hankalin ‘yan siyasa da masu sauraron waƙar cewa duk wanda ya shiga jam’iyyar A.P.P ko yake da niyyar shiga, to kada ya ji wani shakku domin ita uwa ce da ke da juriya ga irin ƙalubalen da ka iya fuskantar ta. Don haka kowa ya fito don a tsai da jam’iyyar don ta yi mulkin Nijeriya.

2.2 SALON KAMANTAWA CIKIN WAƘOƘIN SIYASA

Kamantawa wani salo ne a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa inda marubuci zai faɗi cewa abu kaza kamar abu kaza yake; ko abu kaza ya fi abu kaza; ko a ce abu kaza bai kai abu kaza ba. Dangane da bayanin da ke sama za mu iya kasa salon kamantawa ya zuwa gida uku kamar haka; kamancen daidaito, da kamancen fifiko da kuma kamancen kasawa (Yahaya 1997).

 

2.2.1 KAMANCEN DAIDAITO;

A wannan ɓangare za a kamanta wani abu dai dai da wani; wanda inda za a ce abu kaza ya yi dai-dai da wani abu, misali Shu’aibu Yar Medi yana cewa:

 

Ga Mamun na Baffa Zubairu gida lambarka sun taru

Ga Malam Balarabe Bello a PDP mun ƙaru

Duk mai son ƙasa ya taho a yi PDP a gyara ƙasata

 

Malam Mamun na Baffa Zubairu da Malam Balarabe Bello mutane ne da suke da kwarjini da daraja a idon mutane, saboda haka ne ya sa marubucin waƙar ya kamanta su da daraja daidai da junansu, saboda irin gudummuwar da suke bayarwa wajen cigaban jam’iyyar PDP. Don haka ne mawaƙin ya kamanta su a fagen bunƙasa jam’iyyar da kuma kashe dukiyarsu domin jawo ra’ayin ‘yan Jam’iyyar su zaɓi shugabanni na gari.

 

Har wa yau ya ƙara da cewa:

Duk mai son a shinfiɗa ƙyaƙƙyawan mulkin farar hula,

Ɗorarre da ba a zuwa ayi wasoso kamar galla

Tilas ne mu tashi mu ja ɗamara yak u farar hulla

Duk mai son ƙasa ya shigo inuwar lema mazammu da mata.

 

Mawaƙin ya kamanta jam’iyyar PDP da galla, wato wata ruwan darɓa ce wadda ta yi kama da ruwan zuma, wadda zaƙinta ya yi daidai da zaƙin zuma yayin da aka lasa shi. Don haka duk shugabannin da za’a zaɓa a mulkin ƙasa dole ne su zama masu dangana, ba waɗanda zasu tafi su yi wasoson dukiyar ƙasa ba kamar yadda ake wasoson ruwan galla.

 

Salon kamance abu ne da marubuta waƙoƙin siyasa sukafi yin amfani da shi domin su nuna wa jama’a irin dangantaka ta ƙwarai da ‘yan siyasa suke da ita ga duk wata jam’iyya da ke da manufa ta gina ƙasa.

 

 “Sai Malam Bala Mansa mai alheri kamar kaka

Shi ma ya shigo tafiyar P.D.P don a gyara ƙasata

 

Marubucin waƙar ya kamanta irin kyautar da Bala Ibrahim Birnin Kudu (Bala Mansa) yake yi dai-dai da kaka wato lokacin da amfanin gona ya kai kawo ya wadata, ba mai nema ga wani, domin kowa ya noma nasa.

 

2.2.2  KAMANCEN FIFIKO

Shi kuma wannan bangare ya bayyana irin fifikon da mawaƙi ke bayyanawa da cewa abu kaza ya fi kaza. A nan ma za a ga cewa kalmomi irin su fi, zarce, wuce, furce, zara, kan zamo kamar gadar da ke haɗa abubuwa biyu mabanbamta inda har ake gane cewa darajar ɗaya ta fi ta ɗaya. Muhammadu Ɗan Musa ya kawo irin wannan kamancen fifiko a cikin waƙarsa. Inda ya fifita mace bisa ga sauran mazaje. Misali a cikin waƙarsa ta jami’iyyar A.P.P mawaƙin ya kamanta, Hajiya Naja’atu Muhammad da Zakanya a cikin dabbobi inda ita Naja’atu ya ce ta fi mazan Kano a fagen siyasa; misali:

 

Ga jirgin zuwa Bahrul Aswad Tekun gabas waccan

B azan hau ƙwami ya kife ba da ni ‘yar ƙorama kui can,

PDP na ke so jam’iyya ba na cikin waccan

Duk mai son ƙasa ya fito a yi PDP mazammu da mata

 

Idan aka kamanta jirgin ruwa da ake fito da shi a teku babu shakka, ba za’a kamanta shi ba da ƙwamiba, ƙwami yana nufin ƙwale ƙwale da ake amfani da shi a ƙananan ƙoramu ko gulabe. Don haka Jam’iyyar PDP babbar Jam’iyya ce da ta yi wa sauran jam’iyyu zarra, don haka shigar ta ya fi shigar wasu jam’iyyu da ba su kai girmanta ba. Da yake ƙara jaddada darajar PDP da irin girmanta a ƙasa, sai ya kawo kamancen cewa faɗin rana ya fi tafin hannu, don haka idan ta bayyana to tafin hannu baya kare ta. Ga abin da ya ke cewa:

           

In rana ta bayyana tafin hannu baya kare ta,

            Ta haske gabanta da baya da ƙarfi ba a maida ta,

            PDP ƙasa duka yau kowa ya karɓi tsarinta

            PDP muke so don a yi alheri mazanmu da mata

 

Salon kamance abu ne da marubuta waƙoƙin siyasa suka fi yin amfani da shi domin su nuna fifikon daraja ko arziki na wasu fitattun ‘yan jam’iyya, bisa ga wasu ‘ya’yan wata jam’iyya. Misali Shu’aibu Zakari Yar Medi ya yi amfnai da irin wannan salo inda ya haɗa Shaho da ‘ya‘yan kwai ya kuma haɗa jaki da sauran dabbobi. Malamin ya nuna irin fifikon da ke akwai tsakanin Shaho da sauran tsuntsaye, ko duk wani da aka same shi ta hanyar saka kwai. Misali yana cewa:

 

Shaho yai jawabi don haka duk ɗan kwai ya saurara

Jaki yai kiran ‘ya’yan dabbobi sun shigo saura

In ga al’umma sun zo talakawa sai mu saurara,

Ga Dallatu ga Rimi ga Lawal Kaita ku sa su gaba

P.D.P ƙasa duka mun amsa don a gyara ƙasa

 

Irin wannan salo na fifiko wani salo ne na kamance da mawaƙan siyasa suka fi yin amfani da shi domin su nuna fifikon daraja ko muƙami ko arziki na wasu fitattun ‘ya‘yan jam’iyyarsu. Don haka wannan mawaƙin ya yi amfani da wasu mutane daga cikin jam’iyyar P.D.P inda ya nuna fifikon da suke da shi a cikin jam’iyya. Mawaƙin ya nuna fifikon waɗannan yayan jam’iyya bisa ga sauran ‘ya’yan jam’iyyar, kamar yadda ya kamanta shaho da sauran tsuntsaye ko ‘ya’yan ƙwai.

 

 

2.2.3 KAMANCE KASAWA

Idan aka dubi kamantawa ta wannan hauji sai a ga cewa babu shakka marubuta su na taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da salo domin su tallata yayan Jam’iyya da kuma ita kanta jam’iyyar da suke yi wa waƙa domin ta sami karɓuwa ga mutanen ƙasa. Don haka a wannan nau’in salon kamance kasawa ne akan ce abu kaza ya kasa abu kaza ko kuwa bai kai kaza ba. Mafi yawan kalmomin da ake nuna irin wannan salo masu kore samuwa ne (Yahaya 1997). Wato kalmar “Ba” ta zo kafin da kuma bayan kalmar samuwa. Misali Shu’aibu Yar Medii yana cewa a cikin waƙarsa ta P.D.P.

 Mai son ratsa teku ka hau jirgi domin ya fidda ka,

In ko ka ƙi sai ka nutse a ciki ƙarshe a manta ka

Ɗan Nijeriya ka bi jam’iyya mai baka haƙƙinka

Duk mai son ƙasa ya shigo inuwar lema mazammu da mata.

 

Mawaƙin ya kamanta jam’iyyar PDP da jirgi da cewa ita kaɗaice za ta fitar da mutum idan ya zo ƙetare teku. Idan kuwa ya shiga wata jam’iyya ba ita ba, to kamar ya shiga ƙwale ƙwale ne wanda ba zai iya ratsa teku ba. A ƙarshe yana iya nutsewa a ruwa ya halaka ya halaka duk wanda ya ke cikinsa. Haka kuma duk jam’iyyar da ba PDP ba tana kasa kai ‘ya’yan ta ga samun nasarar kafa mulki. Don haka sauran jam’iyyu darajarsu ba takai ta jam’iyyar PDP ba a fagen yawan jama’a da kuma karɓuwa a ƙasa baki ɗaya.

 

2.3 SALON ALAMTAWA

Salon alamtawa wani salo ne da ya yi kama da kinaya har ma wani lokaci ba a iya bambanta su. Alamtawa da kinaya dukkansu suna sifanta mutum ko wani abu ta hanyar amfani da kalmomin da ba sunansa ba. Salon alamtawa yana amfani da wani sashi na mutum ko wani abu domin wannan sashi ya wakilci mutumin ko abin. Misali Musa Baban Bege Giɗaɗawa Sakkwato a cikin waƙarsa ta P.D.P yana alamta asibiti da ɗakin shan magani; Misali yana cewa:

Ɗaki a gina na shan magani

Ƙauyukka gami da birni

A ce musu ungo ga magani

A raba shi ga sansani-sansani

Haka ne fatarmu yan jam’iyyar P.D.P

 

A cikin wannan baiti maimakon mawaƙin ya fito fili ya ambaci cewa an gina asibiti, sai kawai ya alamta asibiti da ɗakin shan magani domin ya ƙara fayyace ma waɗanda ba su san asibiti ba da sunan ɗakin shan magani.

 

Har wa yau ita alamtawa tana amfani da wata kalma wadda ko bayan ma’anarta ta zahiri an ɗora mata wata magana tsayayya, idan aka ɗauki kalmomi irin su, kujera, goɓe, ɗakin magani da sauransu, za a taras cewa kowace kalma daga cikinsu tana wakiltar wani suna ne. Misali idan mawaƙi ya ce a ba shi kujera, yana nufin a biya masa Makka, haka yake ga kalmar gobe wadda ko bayan ma’anarta ta ranar da za ta biyo yau, to tana nufin ranar lahira kenan. Shi ma ɗakin shan magani yana nufin asibiti. Don haka salon alamtawa yana amfani da kalmar da mawaƙi ya kawo cikin waƙarsa domin ta tsaya a madadin wani mutum ko wani abu da yake magana a kansa cikin waƙar.

 

Marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa suna amfani da irin wannan salon alamtawa domin su ƙara fito da ma’anar waƙarsu a fili da kuma fayyace jigon da suka gina waƙar a kansa. Misali, Shu’aibu ‘Yar Medi a cikin waƙarsa ta jam’iyyar P.D.P har wa yau yana cewa:

 

 

 

Ɓauna saniyar sake mai ‘yar laya ba ya nuna ki

Balle yai tunanen kamawa tilas ya ƙyale ki

Tauraro turakin Adamawa ya zan abin ɗoki

Ga Bamanga ga Atiku kwashe kayan ɗan jaki

P.D.P akwai Jibril Farfesa masu gyara ƙasata.

 

A nan mawaƙin ya yi amfani da kalmomin “Tauraro” da kuma “ɗan jaki” domin ya nuna wa jama’a matsayin wani mutum da ya wakilci jama’a masu haiba da kwarjini a idon mutane. Ita kuma kalmar “ɗan jaki” tana wakiltar ƙasƙantattun mutane waɗanda ba su da wani amfani ga jama’a illa a ɗora masu kaya kamar yadda jaki yake a cikin dabbobi.

 

Wato mutumin da ba ya sawa ba ya hanawa a cikin al’umma, shi mawaƙin yake nufi da ɗan jaki, shi kuwa “Tauraro” yana nufin sanannen mutum wanda jama’a suke cin amfaninsa da kuma alfahari da samun irinsa a cikin al’umma, musamman a cikin jam’iyyar siyasa.

 

Har wa yau akwai wani misali da mawaƙin ya kawo inda ya alamta jam’iyyar P.D.P da “ruwan sanyi” wadda ke wakiltar kalmar “zaman lafiya”. Dukkan al’amari na duniya akwai buƙatar a sami zaman lafiya kafin a aiwatar da shi. Ta hanyar zaman lafiya ne arizikin ƙasa da ilimi da walwalar jama’a ke bunƙasa. Saboda haka a tunanen mawaƙin babu abin da ya fi “ruwa” lafiya. A kan haka ne ya alamta jam’iyyar PDP da “ruwan sanyi” wato jam’iyya ce ta zaman lafiya da take bai wa kowane ɗan Nijeriya haƙƙinsa ba tare da nuna zalunci ko fifikon ƙarfi ba. Misali mawaƙin yana cewa:

Zan je in ga Dallatun Fika Malam mun yi dafifi

P.D.P ruwan sha mai sanyi lokacin zafi,

Mai tsarki ka sha, ka yi wanka ba a nuna fin ƙarfi

Duk mai son ƙasa ya shigo inuwar lema a gyara ƙasata

 

A cikin wannan baiti mawaƙin ya alamta P.D.P da ruwan sanyi da ake buƙatar a same su a lokacin da tsananin zafi ya addabi mutane. Ma’ana ko da jam’iyyar P.D.P ta kafu a ƙasar nan, tana da manufar samar da zaman lafiya domin ƙasar nan ta cigaba. Don haka Malamin ya alamta ta da ruwan sanyi domin ta zo a lokacin da ake buƙatar jam’iyya da za ta iya ceto talakawan ƙasar nan daga uƙubar da suke ciki. Samun nasarar ceto ƙasar nan daga halin ni-‘yasu da take ciki ba zai yiwu ba face an sami mutane ƙwararru masu ilimi da kuma kishin ƙasa. Don haka ne jam’iyyar P.D.P ta rungumo Dalatun Fika, wato Malam Adamu Chiroma wanda ya taka rawa wajen tafiyar da jam’iyyar PDP tun farkon kafuwarta. Bayan da aka yi nasarar cin zaɓe a shekarar 1999, sai Shugaban ƙasa Olesegun Obasanjo ya naɗa shi a matsayin ministan aikin gona, haka dai ya ƙarawa jam’iyyar kwarjini, inda har mawaƙin ya alamta jam’iyyar da ruwan sanyi wanda ake sha domin a ji sanyi. Irin wannan gogewa da ƙwarewa da wannan mutum yake da su ya sa jam’iyyar P.D.P ta riƙa shi a matsayin babban jigo a cikinta.

 

Shi kuma Turakin Adamawa Atiku Abubakar wani ƙusa ne a cikin jam’iyyar P.D.P wanda har ya zama Mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin wannan jam’iyya. To da kasancewar irin waɗannan manyan mutane ƙwararru a sha’anin mulki da harkokin duniya shi ya sa mawaƙin ya alamta jam’iyyarsa da cewa ruwan sha ne mai sanyi lokacin zafi. Kuma ya ƙara da cewa ana sha a kuma yi wanka saboda samun sauƙin rayuwa.

 

 

2.4 MUTUNTAWA

Salon mutuntawa shi ne inda ake ɗaukar darajar mutum a bai wa dabba ko wani abu maras rai. Ga al’ada ta halitta, mutum aka sani da yin magana da dariya da kuma duk wani aiki na hankali da ɗan Adam zai iya yi da hannu ko da baki. Ita kuma dabba ba za ta iya yin magana ko aiki da hankali da mutum zai iya yi ba. Amma an san dabba da wasu ɗabi’u da suka haɗa da kuka, da nishi da gurnani da bodowa, da kuma yin ishara ga wani abu da take buƙata (abinci). Saboda haka za a iya cewa dabba kaza ta ce kaza, to a irin wannan hali da aka danganta dabba da ɗabi’u irin na ɗan Adam, to an mutumta ta ke nan tun da an ba ta muƙamin yin magana ko aiki irin na ɗan Adam.

 

Yin amfani da salon mutuntawa wani salo ne da marubuta waƙoƙin siyasa suke yi a cikin waƙoƙinsu domin su naƙasa ko muzanta wani ɗan siyasa ko ɗan adawa na wata jam’iyyar adawa. Misali a cikin waƙarsa ta Jam’iyyar APP, Muhammadu Ɗan Musa ya yi amfani da irin wannan salo inda yake cewa;

Jan biri na gane nufinka,

Da ca nake mai son jama’a ne

Ashe kiranka kiran jama’a ne

Ja’irin aka ba ka Minister

Sai ka karɓa ka mance na baya

 

Wannan baiti ya haɗu da lalurar waƙa wadda ta hana ta samu tsayayyen amsa- amo da ke tabbatar da matsayinta na rubutattar waƙa. Sai dai hakan bai hana saƙon da ake nufin isarwa ga jama’a ya cimma nasara ba. Malamin ya kawo wata daraja da ɗan Adam aka fi sani da ita, wato darajar hankali da yin magana da kuma riƙa muƙami. Malamin ya yi amfani da kalmomi da ɗan Adam kawai aka sani da aiwatar da su kamar “kira” son jama’a” “karɓa” da muƙamin Minister”. Marubucin ya bayyana yadda dabba ke magana inda take magana da baki har ta kira jama’a domin su amince mata. Wannan wata darja ce da ta kebanta ga ɗan Adam. Haka kuma riƙa wani muƙami don a shugabanci jama’a aiki ne na ɗan Adam mai hankali, to amma sai ga shi an bai wa biri wanda ya ke dabba ce. Danganta dabba da irin waɗannan halaye mutuntawa ne ga biri (dabba).

 

Haka shi ma Malam Shu’aibu ‘Yar Medi a cikin waƙarsa ta P.D.P ya mutunta tsuntsu inda ya ba shi muƙamin mutum mai sanya sutura da kamala irin ta ɗan Adam. Misali yana cewa:

Hankaka ina ɗamarar da ka ɗaura sakarai kwance,

Mai bunu a gindi idan ka ji a ne gobara kauce

Ka sayar yadda duk ka sayo amsar matar ɓarawo ce

Wannan lokacin na mutanen kirki ne mazanmu da mata.

 

An san hankaka tsuntsu ce, amma an ba ta daraja ta ɗan Adam inda mawaƙin ya ba ta aikin ɗaura ɗamara. “Ɗamara” wata rigar laya ce da mayaƙa ke amfani da ita domin neman kariya daga harbin kibiya ko wani makami da abokan gaba ke amfani da shi. A nan Malamin ya mutunta hankaka (tsuntsu) inda ya ba ta aikin ɗaura ɗamara kamar mutum.

 

Har wa yau Malamin bai tsaya ga mutunta dabbobi da tsuntsaye ba, a’a har ma da ita kanta jam’iyyar da yake yi wa waƙa. Ya nuna cewa jam’iyyar P.D.P mace ce kyakkyawa mai fara’a da ɗa’a da kuma girmama baƙi idan ka ziyarce ta. Don haka a duk lokacin da ta sami baƙo za ta yi maraba da shi ta kuma tarbe shi tana murna tana yi masa lale marhaba. Wannan hali ne na ɗan Adam wajen karrama baƙo. Amma saboda mawaƙin ya nuna ƙwarewarsa ga waƙa, sai ya yi amfnai da wannan salo na mutuntawa ya bai wa jam’iyyar P.D.P daraja da ɗabia ta mutane. Ga dai abinda yake cewa:

Malam Bello Isah Bayero ga saƙo a shaida ma

Fi-di-fi Maraba take ma al’ummarka, sun karɓa

Ya ya gaskiyarka da Bil’ama ya ce shi ya koya ma

Ni na san jinin Dabo bai zuwa gun masu ɓata ƙasata

 

Shi ma Ibrahim Aminu Ɗandago ya mutunta Jam’iyyar A.P.P inda ya ba ta darajar dan Adam. Ya ce A.P.P tana ‘shiri” ta kyautata wa talakawa. An san shiri ko tsari abu ne da ɗan Adam ke yi idan yana son ya aiwatar da wani aiki. Saboda haka bai wa A.P.P wannan matsayi na ta shirya wani tsari na aiwatar da cigaban talaka aiki ne na mutum aka ba ta, kamar yadda mawaƙin yake cewa:

A.P.P na shirin ƙasa talaka ya san hali

Ya sami sukuni ya ɗebi daularsa da cokali

Ba mai duban sa ko gida ko ko a dandali

Yai masa kallon maras kwabo ko maras hankali

Daidai da ƙasarmu jam’iyyar ‘yan Nijeriya

 

Kamar yadda baitin ya nuna jam’iyyar PDP ba mutum bace, amma an ɗora mata daraja irin ta ɗan adam, wato an bata irin aikin da mutum kawai ke yin sa, yin shiri idan za’a aiwatar da wani aiki mutum ne ke yin sa, domin Hausawa suna cewa In za’a a ke shiri ba sai an dawo ba, ka ga a nan an mawaƙin ya mutumta APP inda ya bata aikin shiri da ɗan adam ke yi, haka kuma mutum shi ke yin tsari idan zai aikata wani abu, abin mamaki sai gashi yin tsari da yin shiri duk mawaƙin ya ɗorasu ga jam’iyyar APP wajen tafiyar da harkokin samar wa talakawa jin ɗaɗin rayuwa a lokacin mulkin demokuraɗiyya idan har aka zaɓe ta.  Haƙiƙa wannan wani salo ne da ke nuna cewa marubuta waƙoƙin siyasa sun kan kalli yanayin da ake ciki da yanda abubuwa ke tafiya sannan su tsara waƙa ta yi dai dai da wannan yanayi domin su faɗakar da al’umma da ‘yan siyasa a cikin tallata jam’iyyarsu.

 

2.5 DABBANTARWA

Salon dabbatarwa wani abu ne da mawaƙan siyasa/Hausa ke amfani da darajar dabba ko aiki da dabba aka san ta da yin shi, a laƙa ma mutum ko a ambace shi da wannan hali ko ɗabi’a domin kawai a muzanta shi ko a ƙwarzama shi a idon jama’a. Marubuta waƙoƙin siyasa babu shakka suna amfani da irin wannan salo a cikin waƙoƙinsu domin su naƙasa ‘yan adawa da jam’iyyar adawa. Misali inda Muhammadu Ɗan Musa yake cewa:

Tun da zakonya tai ƙara

Ba ni shakkar ta murguɗe kura

Naja’atu zo ki yi mana gyara

Nan Kano sai mai ɗan kwali

 

 

A farkon wannan baiti a layi na ɗaya marubucin waƙar ya dabbantar da Naja’atu inda ya sifanta ta da zakanya, kuma ya ba ta hali da ɗabi’a irin ta dabba. Kalmar “ƙara” kalma ce da ke wakiltar ‘kuka’ da mutum kan yi. Amma Malamin sai ya yi amfani da ƙara da dabba ke yi, dabbar kuma zakanya don ya nuna irin kwarjini da tsoratarwa da ƙarar zaki ke razana ‘ya’yan dabbobi, kai har ma da yan adam. A nan Malamin ya dabbantar da Naja’atu inda ya ba ta ɗabi’a irin ta dabba don ya nuna wa jama’ar Kano irin kwarjinin da Naja’atu take da shi a fagen siyasa.

 

 

2.6 ABUNTARWA

Abuntarwa wani salo ne cikin waƙoƙi inda mawaƙi ke bai wa mutum daraja ko ɗabi’a ta wani abu maras rai wanda ba ya cikin mutane, kuma shi ba dabba ba. Misali Alhaji Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu a cikin waƙarsa mai suna Yadda Ya Kamata Nijeriya Ta Arewa Ta Zamo, yana cewa:

Yau ga kyauta su ce babu tamkakka ai,

Wane da su wane tauri sukai

 

A cikin wannan baitin waƙa a ɗango na biyu Malamin ya kawo maganar da ɗan raraka ya yi, ya nuna mana abuntawa a fili. Amfani da kalmar tauri da Malamin ya yi ya liƙa ta ga mutum domin ya sifanta shi da marowaci ya sa mai karatu ko mai sauraron waƙa zai fahimci cewa an abuntar da mutum ne. Irin wannan abuntarwa shi ne mawaƙan siyasa ke amfani da shi domin su muzanta ‘yan jam’iyyar adawa ko wasu muhimman mutane na sauran jam’iyyarsu masu adawa da tasu jam’iyyar. Misali inda Shu’aibu ke cewa:

Yau dai ga ni ga Sule Lamiɗo don in ɗauki ummurni

Sannan ba ni sake shiga jam’iyyar ‘yan guma ba ni,

Ba zan sake bin su ba tun da suna cancanza ummurni

In an ce su ba mu su sa aljihu sui ta ƙuƙuni

Yan ci babu ceto ba su da kowa su ka ɓata ƙasata

 

Malamin ya kawo kalmar ‘ƙuƙuni’ a cikin ɗango na huɗu na wannan baiti mai ɗango biyar, inda ya abunta wasu mutane da ke cikin jam’iyyarsa. Waɗannan mutane inji mawaƙin su ne suke danne duk wata kyauta da aka bai wa mawaƙin ba za ta kai gunsa ba. Idan an ba su sun karɓa sai su yi ta ‘ƙuƙuni’ wato su yi ta mutsu-mutsu da jiki da hannuwa suna ɓoye kyautar cikin aljihunsu. Ƙuƙumi kalma ce da take nuna wata ɗabia da kaza ke yi idan ta ɗauki ƙoto don ta ba ‘ya’yanta, sai ta riƙa yin wata ƙara tanayin ƙu-ƙu-ƙu, domin ta hana wa ‘ya’yanta da wasu kaji da ke biye da ita karbar abun da ke bakinta. To waɗannan mutane idan aka ba su kyauta su bai wa mawaƙin, sai su ɓoye wa kansu, suna ta yin ƙu-ƙu-ni don kada kowa ya samu. Irin waɗannan mutane su ne mawaƙin yake cewa ‘yan ci babu ceto.

 

2.7 SALON KARIN MAGANA

Karin magana wata dunƙulliyar magana ce wadda idan aka yi bayaninta za ta ba da ma’ana mai yawa; (Dangambo 2007). Salon karin magana a cikin waƙar siyasa abu ne da ya zama ruwan dare game duniya ga mawaƙan Hausa. Suna amfani da wannan salo na karin magana cikin waƙoƙinsu domin su nuna ƙwarewarsu ga harshe. Sannan kuma su yi wa abokan hamayya (‘Yan Adawa) habaici dangane da muƙamin da suke takara tsakaninsu. Wani lokaci marubuta waƙoƙin siyasa kan yi amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu domin su yi gargaɗi da hannunka mai sanda ga jama’a, dangane da mai da hankali ga zaɓen abin da ya fi muhimmanci da kuma ingancin ɗan takara. Misali don talakawa su kauce wa zaɓen tumun dare, a lokacin zaɓe, marubuta waƙoƙin siyasa kan yi amfani da karin magana su yi gargaɗi gare su bisa ga zaɓen mutumen da ya dace mai gaskiya da riƙon amana, wanda ba ɓarawo ba, ba kuma macuci ba. Malam Shu’aibu ‘Yar Medi da Aminu Ɗandago da Muhammadu Ɗan Musa da sauransu sun taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu na siyasa domin su faɗakar da talakawa game da muhimmancin zaɓen shugaba nagari. Misali Shu’aibu ‘Yar Medi yana cewa:

Hausawan garinmu suke cewa in za ka sai ƙwarya

Sai an ƙwanƙwasa ka ji ta ce ƙwar-ƙwar ƙwar a can baya

Jam’iyyun ƙasarmu ku tashi ku koma can ku ja baya

Fi-di-fi kawai jama’ar ƙauye domin a gyara ƙasata

 

Haka kuma yana cewa:

Dillalin jirajirai shi yas san kimar kuɗin wada

Mai neman farar akuya bari kallon tunkiyar Dada

In kau ka ƙi sai mu buge ka da hannu ko mu sa sanda

Jam’iyyarmu ce da Halimatu suya ban sayen ganda

Ko an babbake ta akwai ƙauri gara ma na ci gauta.

 

Babu shakka amfani da salon karin magana a cikin waƙoƙin siyasa ya taimaka ainun wajen wayar wa talakawa da ‘yan siyasa kai ta hanyar yi masu hannunka mai sanda ga zaɓen jam’iyyar da ta dace da manufofin gina ƙasa.

 

Shi ma Muhammadu ɗan Musa ya tofa albarkacin bakinsa inda yake cewa:

Zaƙin kiɗa sai kalangun Shata

Kyan gidaje a bar wa mata

Anti Hadiza na ƙauna ta

Zara’u ma tana ƙauna ta

Don ina waƙar talakawa


3.0 KAMMALAWA

Bisa ga bayanai da masana suka yi game da salo da amfani da shi a harkokin yau da kullum ciki har da waƙoƙin siyasa. Yana da kyau mu fahimci irin tasirin da salo yake da shi wajen warware jigon rubutattun waƙoƙin siyasa domin isar da saƙo zuwa ga al’umma. Yin amfani da irin waɗannan salailai a cikin waƙoƙin siyasa ya jawo wa jam’iyyun siyasa kwarjini da ƙarbuwa ga talakkawan ƙasa wanda ya assasa samar da shugabanni da suka ƙware a sha’anin mulki.

 

Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan tsari domin su nuna ƙwarewarsu ga harshe da kuma ƙoƙarin wayar wa jama’a kai dangane da abun da ya shige masu duhu game da manufofin jam’iyyu da kuma zaɓen ɗan takara na gari. A tsarin waƙoƙin siyasa salon sifantawa da kamantawa da alamtawa da mutuntawa da dabbantarwa da abuntarwa da kuma karin magana a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa wata babbar dabara ce da marubuta waƙoƙin siyasa ke amfani da ita domin su samar da kyakkyawan yanayin siyasa da ka haifar da tabbataccen mulkin adalci a Nijeriya.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments