Ticker

6/recent/ticker-posts

A Share Jini A Koma Wasa: Tasirin Tuba Da Sulhu Ga ‘Yan Ta’addar Zamfara

 Matsalar tsaro wata abu ce da take yi wa al’ummar jihar Zamfara barazana, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Malamai da shugabannin addini da hukumomi masu ruwa da tsaro a kan harkar tsaro sun yi iya ƙoƙarinsu don shawo kan wannan matsala, amma abin ya ci tura. Wannan takarda mai take “A share jini a koma wasa: Tasirin Tuba da Sulhu ga ‘yan ta’addar Zamfara” za ta yi tsokaci ne a kan musabbabin faruwar ta’addancin fashi da makami da satar mutane, ana garkuwa da su, domin karɓar kuɗaɗen fansa a Jahar Zamfara. Ta’addancin da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama da kuma dukiyoyin bilyoyin naira. Wannan sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin Maigirma Gwamna (Dr) Bello Muhammad (Matawallen Maradun, kuma Barden Ƙasar Hausa) da ‘yan ta’adda ya yi sanadiyar raguwar ayyukan ta’addanci duk da kasancewar har yanzu ana samun kashe-kashen gilla da satar dukiyoyi da lalata kayan gona da gidaje a wasu sassan jiha. Wannan takarda zata mai da hankali ne ga tasirin da tuba ta yi a sanadiyar sulhu da ‘yan ta’adda wajen samar da zaman lafiya da cigaban harkokin kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki a jihar Zamfara.

A Share Jini A Koma Wasa: Tasirin Tuba Da Sulhu Ga ‘Yan Ta’addar Zamfara

 

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0  Gabatarwa

Duk ƙasar da ba ta zaune lafiya, al’ummarta ba za ta taɓa samun cigaba ba ta kowane fanni. Ta’addanci yana daga cikin musabbabin rashin zaman lafiya a cikin kowace al’umma. Zamfarawa mutane ne da suka yi suna ta fuskar zaman lafiya da ingantaccen tsaro tun daga farkon mulkin shugabannin gargajiya har zuwa samuwar mulkin dimokuraɗiya a jihar Zamfara a yau. A halin yanzu da mulkin dimouraɗiya ya samu karɓuwa a wannan jiha da ƙasa baki ɗaya, sai ga shi ayukkan ta’addanci sun kurɗo kai cikin jihar Zamfara har ya kai irin zaman lafiya da tsaro da ake da shi a wannan jihar yana neman ya zama tarihi. Tunanin wannan bincike shi ne ya yi nazarin tasirin da tuba da ‘yan ta’adda suka yi wajen kawo zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara. Hausawa suna cewa, “Zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki”.

 

1.1 Manufar Bincike

Babbar manufar wannan bincike ita ce ta gano irin tasirin da tubar da ‘yan ta’adda suka yi ta fuskar zaman lafiya da samuwar walwala a jihar Zamfara. Haka kuma binciken yana da manufar binciko yawan al’ummar da suka rasa rayukkansu da ɗinbin dukiyoyin da aka yi hasara da gidaje a lokacin gwamnatin da ta gabata da kuma a wannan lokaci na gwamnatin Bello Muhammad (Matawallen Maradun – Barden Ƙasar Hausa), da kuma tasirin da sulhu ya yi a fannin cigaban tattalin arziki.

 

1.2 Dalilin Bincike

Hukumomin gwamnati da malaman addini da kuma masu ruwa da tsaki a fannin tsaro sun yi iya ƙoƙarinsu domin su tabbatar da an sami zaman lafiya da ingantaccen tsaro a jihar Zamfara, amma hakan bai kasance ba sai dai kullum ayyukan ta’addanci ƙaruwa suke daɗa yi. Don haka wannan bincike yana ƙoƙarin ya gano inda gizo ke saƙa, dangane da cigaba da ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara. Saboda haka wannan bincike zai yi zuzzurfan bincike a kan dalilan da suka sa aka samu raguwar ta’addanci da samar da zaman lafiya a sanadiyar sulhu da gwamnatin Bello Muhammad Matawalle ta yi.

 

1.3 Dabarun Bincike

An bi hanyoyi daban-daban domin samo bayanai masu inganci a kan matsalar tsaro da rashin zaman lafiya da jihar Zamfara ta sami kanta. Hanyoyin sun haɗa da duba littattafai da maƙalu da jaridu. Haka kuma an yi hira da masu ruwa da tsaki a kan matsalar tsaron Zamfara.

 

1.4 Farfajiyar Bincike

An taƙaita wannan bincike ne a jihar Zamfara kawai, domin nan ne ayyukan ta’addanci suka fi yin ƙamari wanda ya haifar da rashin zaman lafiya da hasarar rayukka da dukiyoyi da gidajen al’umma a yankin nan ƙarara na wannan jihar.

 

1.5 Tambayoyin Bincike

·         Mene ne ta’addanci?

·         Mene ne musabbabin ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara

·         Wace irin hasara ta’addanci ya samar a jihar Zamfara?

·         Wane mataki hukumomi suka ɗauka domin kawar da ayyukan ta’addanci?

·         Wane irin tasiri tuba da sulhu suka yi ga ‘yan ta’adda?

·         Wane sakamako binciken ya samu?

 

1.5.1 Mene ne Ta’addanci?

Ta’addanci wani hali ne ko ɗabi’a ko wani aiki da hannu zai aikata ko baki zai furta, wanda ya saɓa wa hanalin Ɗan’adam. Wato duk wani aiki ko furuci da zai saɓa wa tunanin zaman lafiyar al’umma ko yi masu barazana ga rayuwarsu da dukiyoyinsu. Bergery (1993) ya ce, ta’addanci shi ne aikata miyagun ɗabi’u ko halaye maras kyau a cikin al’umma. Misali a ɗauki wani abu ba tare da izinin mai abun ba. Ya ƙara da cewa ƙetare iyaka ga ayyukan yau da kullum”, shi ne ta’addanci. Fashi da makami, fyaɗe da keta haddin mata, da kisan gilla da ƙwace dukiyoyin al’umma duka ayyuka ne na ta’addanci da mutane maras kishin ƙasa ke aikatawa. Haka kuma satar mutane a yi garkuwa da su don neman kuɗin fansa shi kanshi ta’addanci ne.

 

Suleima (2013) ya bayyana fyaɗe a matsayin cin zarafi da keta haddin mata, wanda mutum guda ko fiye da haka kan aikata wa don fin ƙarfi ba tare da yardarta ba, shi ne ta’addanci. Aikata irin wannan ɗabia wani babban ta’addanci ne da ka iya jefa al’umma cikin yanayin rayuwar rashin zaman lafiya. Abbas (2013) shi ma ya bayyana ta’addanci a matsayin zalunci wanda Hausawa ke cewa “Rigar ƙaya” shi zalunci yana nufin saɓa wa tafarkin adalci, wato ajiye wani abu a bagiren da ba mahallinsa ba. Idan al’umma takasance cikin lamarin rashin adalci daga shugabanni, to dole ne a sami masu raunin tunani su riƙa nema wa kansu haƙƙinsu ko ta wane hali. Shi kuwa Umar (2013) ya ce, ta’addanci yakan faru a sanadiyar shugabanni maras adalci. Hausawa mutane ne masu biyayya da ladabi ga shugabanni, wanda hakan yakan sa idan shugabanni suka kasa yi wa talakawa adalci, sai ka ga su talakawan sun shiga yanayin damuwa da ƙorafe-ƙorafe, wato rashin bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa yakan kawo rashin zaman lafiya a tsakanin shugabanni da waɗanda ake shugabanta.

 

Tasirin salon mulkin dimokuraɗiyya da ke iƙirarin bai wa kowa yancin tofa albarkacin bakinsa da turawa suka kawo mana ya haifar da rashin ɗa’a ga shugabanni. Dalilin haka yasa aka sami mutane suka fara hamɓarewa suna ayyukan ta’addanci domin su biya wa kawunansu buƙatunsu daban- daban.

1.5.2 Mene ne Musabbabin Ayukkan ta’addanci a Jihar Zamfara

Rikicin ramuwar gayya da ƙabilar Fulani suka fara a shekarar 2012, shi ne musabbabin ta’addancin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar Zamfara. An wayi gari a shekarar da ake magana a kai. Fulani sun tsunduma cikin fashi da makami a hanyoyinmu, suna yi wa mata fyaɗe da satar shanu da sauran su. Domin a yi maganin wannan ta’addanci sai wasu masu aikin Banga (‘Yan Banga) suka fara kama ɓarayi suna yankewa, sannan su a za taya a gawarsu su ƙone. Kashe Alhaji Ishe, wani shugaban Fulanin Jihar Zamfara da Kebbi da Sokoto da ‘yan sa kai suka yi a ƙauyen Calin ta yankin masarautar Ɗansadau ya ƙara harzuƙa Fulani su kai harin ramuwar gayya na farko a garin Lingyaɗo a gundumar Binɗin ta ƙaramar hukumar mulki ta Maru, Jihar Zamfara. Da Fulani suka ga ɓarnar da ake yi masu ta fara yawa sai suka yi shawarar su kira taron yanuwansu don su sami mafita.

 

Duk waɗannan kashe-kashen Fulani ɓarayi sun faru ne a garuruwan Ɗangulbi da Lingyaɗo da Binɗin. Taron da aka yi a Binɗin ya nemi duk Fulani da ke zaune a waɗannan yankuna su ba da ya’yansu su shiga ƙungiyar yan ramuwar gayya ko kuma su ba da shanu a sayar a sayi makamai.

 

A sakamakon wannan taro sai suka tura shugabannin dabobi a kowane yanki, kudu da arewa, da gabas da yamma na jihar Zamfara. Hari na farko na ramuwar gayya shi ne wanda suka kai a garin Lingyaɗo inda suka kashe kimanin mutum 46 – 60. Wannan hari na Lingyaɗo ya zama mabuɗi ga ‘yanta’adda, daga nan sai suka ci gaba da kai hare-hare suna kashin mutane. Hari na biyu shi ne a garin Ɗangulbi nan ma sun kashe mutane 22 – 25. Abun ya ci gaba a garuruwan Kizara, da Kabaro da ‘Yargaladima, da Kangon Garaci, da Mayasa, da Birane da Birnin Magaji. Sauran garuruwan da ‘yan ta’addar suka kai hare-harensu sun haɗa da Ajja, da Wonaka da Munhaye.

Har wa yau sun kai hare-hare a Madaɗa, da Calin, da Magamin Maitarko, da Randa da Tasa, da Ƙememe, da kuma Ɓurma kai, haka kuma akwai hare haren da aka kai a garin Dole Moriki, da Badarawa da Kwaren Shinkafi da Galadi, da Ɗagwarwa, da Saka Jiki, da Bawar Daji da Kawaye, da Gando, Har wa yau akwai Magamin Diddi a yankin Maradun da Ƙaya, da Ajimmar Hausawa da sauransu. A waɗannan hare-haren an kashe kusan mutane dubu huɗu da ɗari takwas da sittin (4,860). Haka kuma an yi hasarar dukiyoyi da gidaje da amfanin gonad a kuɗinsu ya kai biliyan biyu (N2b) naira.

 

Waɗannan ‘yanta’adda suna samun makamansu ne daga hannun wani ɗansanda mai kula da ɗakin ajiye kayan yaƙi/bindigogi da ke nan Gusau, wanda ake kira Calɓin shi ne mai bai wa yanta’adda albarusai da bindigogi.

 

An fara shigowa da AK 47, guda uku, waɗanda aka rarraba wa manyan shugabannin daba irin su Buharin Daji a Binɗin, da kuma wasu manyan dabar Dumburun da yankin Ajja. Daga baya kuma da Libiya ta buɗe sai aka shigo da bindigogi 7, waɗanda aka sawo akan kuɗi Naira dubu ɗari da hamsin zuwa dubu ɗari da tamanin N150,000 – N180,000). Daga bisani kuma bindigogin suka kai kimanin Naira dubu ɗari uku da Hamsin (N350,000). Yadda makaman ke kai wa yanta’adda shi ne, shi Calɓin yane da gona a yankin Ɗansadau sai ya ɗora albarusai cikin jarkar da ake feshin maganin kashe haki kamar zai tafi aikin gona, sai ya kai masu waɗannan makamai.

 

Da kashe-kashen mutane da satar shanu suka yi yawa, sai ‘yan ta’addar suka fara ɗaukar mutane suna yin garkuwa da su. Tun lokacin da suka fara yin garkuwa da mutane an sami waɗanda aka yi garkuwa da su kusan su 525, daga cikinsu akwai ɗan Koriya ta arewa guda da ɗan Gana guda, da sauransu, zuwan gwamnatin Matawalle ya sa aka sako wasu da aka yi garkuwa da su, wasu kuma su ‘yanta’addar da kansu suka sako su, a dalilin sulhu da aka yi da su. (Hira da Kwamishinan Lamurran Tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Zamfara 13/3/2019).

 

1.5.3 Wace Hasara Ayyukan Ta’addanci Suka Samar a jihar Zamfara? 

An sami hasara mai yawa a sakamakon wannan ta’addanci da ya yi ƙamari a jihar Zamfara. Rayukan mutane da dama sun salwanta. Ana ha sashen an rasa mutane kimanin dubu bakwai (7,000) da kuma dukiyoyin da suka fi ƙarfin naira miliyan biyu (2m) naira. Haka kuma an yi hasarar buhunan hatsi da suka kai miliyan biyu ko fiye da haka da ‘yanta’adda suka ƙone a hare-haren da suka kai garuruwa daban-daban na jihar Zamfara. Daɗin daɗawa sun ƙone gidaje da adadinsu ya kai kimanin dubu saba’in (70,000) a duk faɗin jihar Zamfara.

 

A sanadiyar kuɗin fansa da ‘yan uwan waɗanda aka yi garkuwa da su, a yankin Ɗansadau kaɗai anyi hasarar kimanin naira miliyan saba’in da biyar domin fanso yan uwansu (75,000,000.00). Adadin hasarar da aka yi tun daga kayan amfanin gona da gidaje da shanu da sauran ƙadarori sun kai kimanin naira biliyon biyu ko fiye da haka N2b.

 

1.5.4 Wane Mataki Hukuma ta Ɗauka?

Ayyukan ta’addanci na boko haram da kashe-kashen gilla da ake yi wa waɗanda ba su ji ba, basu gani ba, da satar mutane ana yin garkuwa da su abu ne da yake dagula lissafin ko tunanin gwamnati da al’ummar ƙasar nan. Domin ganin a shawo kan matsalar rashin tsaro an yi amfani da matakai daban-daban. Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da ‘yansanda da sojoji da sauransu sun taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan wannan matsala a duk faɗin ƙasar nan, musamman a jihohin da wannan matsala ta yi ƙamari.

 

Jihar Zamfara tana ɗaya daga cikin jihohin da wannan matsala ta shafa. Kashe – kashen gilla da satar shanu da yin garkuwa da mutane ana neman kuɗin fansa sun jefa jihar cikin halin lahaula- walaƙuwata. Gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun yi duk abin da suke iya yi domin shawo kan wannan ta’addanci musamman a jihar Zamfara, amma abin ya ci tura. Daga cikin matakan da gwamnatin Abdul-Aziz ta ɗauka akai kafa kwamitin amintattu domin su binciko masabbabin waɗannan ayyukan ta’addanci. Rahoton da kwamitin ya bar shi ne, rikicin manoma da makiyaya ne ya haddasa haka. Wannan rahoto akwai siyasa a cikinsa domin gwamnati ta yi amfani da waɗannan yan ta’adda wajen samun ƙuri’u masu ɗimbin yawa da ya ɗora ta akan karagar mulki.

 

Sakamakon wannan rahoto da aka bayar, sai ‘yan ta’adda suka sami damar faɗaɗa kungiyoyinsu ta hanyar ƙara ɗaukar Hausawa da Fulani cikin ƙungiyoyinsu. Haka ya sa ƙungiyarjin sun ƙara ƙarfi inda har suka so su rinjayi jami’an tsaro. Yau idan an yi ta’addanci yankin Ɗansadau, gobe ka ji Dumburum ta yankin Zurmi ta ɗauka. Da haka lamurran suka yi ƙarfi a duk faɗin jihar Zamfara.

Duk da kasancewar siyasa ta shiga cikin lamarin rashin tsaro, gwamnatin Abdul-Aziz ba ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ƙoƙarin ɗaukar matakan shawo kan wannan matsala. Gwamnatin jiha a ƙarƙashin jagoranci Alhaji Abdul-Aziz Abubakar Yari ta:

-          Raba sababbin motoci ƙirar Toyota Hiluɗ da kuɗaɗen gudanarwa a kowane ƙarshen wata ga jami’an tsaro domin ba su damar gudanar da aikinsu

-          Ta samar da ofishi na musamman da wurin kwana ga sojojin da aka kawo don ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a wannan jaha.

-          Ta kafa wani kwamiti mai ƙarfin gaske tare da ɗora masa nauyin samar da hanyoyin shawo kan ayyukan ta’addanci da samar da zaman lafiya a jihar Zamfara.

-          Samar da bayanan sirri dangane da maɓoyar waɗannan ‘yanta’adda da masu kai masu rahoto kowace rana ga jami’an tsaro don su ɗauki matakin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jiha.

-          Gwamnati ta ɗauki kwaƙƙwaran matakin gyara wa jami’an tsaro motocinsu da wasu kayan faɗa domin basu damar shiga kowane lungu na mafakan waɗannan ‘yan ta’adda.

-          Gwamnatin jiha ta nemi haɗin kan jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da Kaduna da Neja da su rufe iyakokinsu domin hana zirga – zirgar/ shiga da ficen yan’tadda.

-          Jihar Zamfara ba ta tsaya a kan rufe iyakokin jihohi maƙwabta ba, a a har da na ƙasashe maƙwabtan Nijeriya; domin hana safara da shigowa da miyagun makamai a wannan jiha.

 

Duk da yunƙurin da gwamnatin da ta gabata ta yi na ɗaukar matakan amfani da jami’an tsaro da sojoji don shawo kan ta’addancin da ya yi sanadiyar hasarar rayukan mutane da ɗimbin dukiyoyin al’umma, ba a sami shawo kan matsalar ba.

Canjin gwamnati da aka samu a Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwarzo, haziƙin gwamna, Alh. Hon. Dr. Bello Muhammad (Matawalle Maradun), kuma (Barɗen ƙasar Hausa) sai al’amurran tsaro suka fara ɗaukar wani sabon salo. Matakin da wannan gwamnati ta fara ɗauka shi ne na kafa tsayayyen kwamiti mai ƙarfi a ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandar jihar Zamfara, tare da taimakawar Hon. Kwamishinan lamuran tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara, da wasu masu ruwa da tsaki a harkar tsaro su samo hanyoyin da za a bi a kawo ƙarshen matsalar tsaro da murƙushe ‘yan ta’adda da suka addabi al’ummar jihar Zamfara.

 

Bisa wannan aiki da kwamiti ya yi aka samu yan ta’adda da dama suka tuba, suka ajiye makamansu. Wato kwamitin ya ɓullo da salon yin sulhu da su ya ta’adda. Addinin musulunci, addini ne da ya aminta da a yi ssulhu idan matsala ta tusgo tsakanin mutane biyu ko fiye, ko kungiyoyi biyu masu gaba da junansu. A cikin Al-ƙur’ani mai girma, sura ta (49:9–10)

“Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaƙi, to ku yi sulhi a tsakaninku, sai idan ɗayansu ta yi zalunci a kan gudar, to sai ku yaƙi wadda ke yin yaƙi har ta koma zuwa ga umurnin Allah, to idan ta koma sai kuyi sulhu a tsakaninsu da adalci, kuma ku daidaita, lallai Allah na son masu daidaitawa.

 

Al-ƙur’ani mai tsarki ya ci gaba da ƙara kira ga Mumminai da su yi sulhu ga dukkan al’amurran da suka tsananta a tsakaninsu. Bisa ga haka a cikin Suratul Hujirat Allah ya ci gaba da kira cewa:

 

(49:10) Muminai yan uwan juna kawai ne, saboda haka, kuyi sulhu a tsakanin yan uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammaninku a yi maku rahama”  

 

1.5.5 Wane Tasiri Tuba da Sulhu suka yi ga ‘Yan ta’adda?

Tuba tana nufin yin nadama daga ayyuka maras kyau a koma ga masu kyau. Wato mai aikata wani aiki da ya saɓa wa al’ada ko addininsa ya gane cewa ya yi kuskure ga aikata haka, sannan ya yi nadama a lokacin da yake aikata wannan saɓo. Tuba ta gaskiya ita ce wadda mai saɓo zai yi nadama a lokacin da yake aikata wani abu da ya saɓa wa al’adar alummarsa ko addininsa, sannan ya yi niyar ba zai koma aikata irin wannan aiki ba a lokacin da yake aiwatar da shi. Sannan idan zalunci ne yake aikatawa, ya mayar da abin da ya zalunta na jama’a. Al-ƙur’ani mai tsarki ya tabbatar da haka a cikin sura ta (66:8) Allah (SWA) yana cewa;

 

“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku koma zuwa ga Allah komawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangijinku ya kankare muku miyagun ayyukanku, kuma ya shigar da ku a gidajen Aljanna. Ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu a ranar da Allah (SWA) ba ya kunyatar da Annabi da waɗanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, ‘ya ubangijinmu! Ka cika mana haskenmu, kuma ka yi mana gafara. Lallai kai, a kan dukan kome, mai ikon yi ne”  (ƙ66:8).

 

Dole ne duk mai aikata laifi ya tuba, wato ya bar ayyukan saɓo, ya koma ga ayyuka na gari, to Allah zai karɓi tubarsa, sannan ya kankare masa dukan laifukkansa. Malamai da sauran shugabannin addini da na al’umma sun taka rawar gani wajen yin kira ga masu aikata laifuka irin na ta’addanci, wato sace- sacen mutane da dukiyoyi da kisan gilla ga al’ummar Zamfara da su tuba su koma ga halaye na ƙwarai domin a samu zaman lafiya da ingantaccen tsaro. Wannan kira ya yi matuƙar mahimmanci domin an sami yanta’adda da dama suka yarda da kiran sulhu, suka kuma amince su ajiye makamansu.

Babu shakka wannan sulhu da aka yi da waɗannan mutane ya haiar da samuwar zaman lafiya da tsaro a wannan yanki na Zamfara. An sami raguwar zauna gari banza, kasuwanci ya bunƙasa, an sami walwale tsakanin baƙi da ‘yan asalin mazauna jihar Zamfara.

Wani mahimmin abu dangane da tubar ‘yan ta’adda shi ne, mafi yawan waɗanda suka tuba da su ake fafatakar ganin an murƙushe ayyukan ta’addanci wanda yake yi wa zaman lafiya da tsaro barazana. Hukuma ta rungumi tubabbi tana basu jari da muhalli, kuma da su ake zagaye lungu da saƙo ana ganawa da sauran ‘yan ta’adda da suke zaune a wurare daban- daban suna gudanar da rayuwar su ba kama hannun yaro. Da ma Karin maganar Hausawa na cewa “Mugu ya san makwancin mugu”, rawar da tubabbin yan ta’adda suke takawa wajen taimaka wa jami’an tsaro da shugabannin gwamnati wajen yin sulhu da ‘yan ta’adda ya zama abin alfahari ga ita kanta gwamnatin da mutanen da take shugabanta.

 

1.5.6 Waɗanne shawarwari ne za su taimaka a kawo ƙarshen Ayyukan Ta’addanci?

Muhimmiyar shawara ta farko da wannan bincike yake bai wa Hukuma da al’ummar jihar Zamfara shi ne, gwamnati ta yi ƙoƙari ta samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar kakkafa kamfunna da masana’antu domin samar da ayyukan yi ga matasa. Wannan babu shakka zai rage yawan raɗaɗin talauci ga al’umma wanda shi ne umul haba’isun faruwar ta’addanci da shiga bangar siyasa da matasa ke yi. Har wa yau gwamnati ta ƙarfafawa iyaye da su dage ga saka ‘ya’yansu makaranta su sami ingantaccen ilimi. Domin rashin ilimi yakan kawo raunin tunani wanda ke haifar da ayyukan fitsara ko ta’addanci a cikin al’umma. Garba Mai Tandu Shinkafi yana cewa:

Jagora: Mun gane sai da ilimi aka arziki

                        Mutane zaman duniya da gobe ƙiyama,

                        Ku tabbata kowaz zan ba shi da ilmi

                        Ba mu dai ga cin ribatai ba.

Amshi: Da shi da jaki, mi narrabasu

                        In ba zancen rashin bindin nan baa

(Waƙar Ilimi ta Garba Mai Tandu Shinkafi)

 

Kamar yadda Garba Maitandu Shinkafi ya faɗa a cikin wannan baiti da ke sama, lalle haka abin yake cewa babu bambanci tsakanin jahili da jaki wanda bai son kome ba sai a ɗora masa kaya. Jahilci shi ke haifar da rashin tunani ga ɗan’adam har ya kasa rarrabe abu mai kyau da wanda ba shi da kyau. Saboda haka uwaye da hukumomi su dage su bai wa ‘ya’yansu da matasa ilimi domin a rage zaman banza da rashin aikin yi a cikin al’umma, wanda ke haifar da faɗawa cikin ayyukan ta’addanci, su kansu ‘yan ta’adda da suka tuba a ƙarfafa masu su koma neman ilimi domin su san hukuncin da Allah zai yi wa masu irin waɗannan ayykan ta’addanci a doron ƙasa a gobe ƙiyama.

 

1.6 Sakamakon Bincike

Wannan bincike da aka gabatar ya samo bayanai masu mahimmanci a kan ayyukan ta’addanci da suka ƙi ci, suka ƙi cinyewa. Sanadiyar sulhu da gwamnati mai ci take yi da ‘yan ta’addan an sami sakamako kamar haka:

-          Maido da zaman lafiya da ceto mutanen da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su tun daga lokacin da suka fara satar mutane suna yin garkuwa da su da yawansu ya kai 525, tsakanin watan Yuli zuwa Disamba, 2019.

-          An miƙa dukkan waɗanda aka ƙwato daga hannun ‘yan ta’adda inji kwamishinan ‘yan sanda ga mai daraja Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Dr. Bello Muhammad (Matawallen Maradun, Bardan Ƙasar Hausa) a gidan gwamnati da ke Gusau kafin daga bisani a mai da su ga iyalansu.

-          An sami nasarar karɓe bindigogi kirar AK 47 kimanin 83 daga hannun ‘yanta’adda

-          Haka su ma ‘yan sakai sun ajiye nasu kayan faɗa domin samar da zaman lafiya bisa ga sulhu da aka yi da yan ta’adda a Zamfara.

-          Baya ga nasarar da aka samu ta rage yawan ayyukan ta’addanci, an sami raguwar ƙananan laifuka a cikin biranen jihar Zamfara da yandaba suke yi a unguwanni da gidajen al’umma a sakamakon samame da jami’an tsaro na haɗin guiwa da sojoji da yansanda da DSS da kuma Sibil Difens ke kaiwa a shiyoyin cikin birane.

-          Gwamnati tana ƙoƙarin samar da rugage a duk faɗin mazaɓun ‘yan majalisar dattawa uku da ake da su a jihar Zamfara domin gina wa Fulani wuri na dindindin da za su zauna da dabbobinsu da nufin hana su yawace- yawace da shiga gonakin manoma barkatai da yake haddasa tashe-tashen hankali tsakaninsu da Hausawa manoma.

-          Zirga- Zirgar kasuwanci ta komo yadda take da a duk faɗin jiha, wanda ya haɓɓaka tattalin arzikin al’umma.

 

1.7 Kammalawa

Zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki. Dangane da sulhu da gwamnatin Bello Muhammad (Matawallen Maraun, Barden Ƙasar Hausa) ta yi da ‘yan ta’adda an samu raguwar ayyukan ta’addanci da satar mutane ana garkuwa da su a jihar Zamfara. Wannan ya kawo raguwar hasarar rayukan mutane da dukiyoyi a sakamakon ayyukan ta’addanci da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, sanadiyar sulhu ya sa a halin yanzu waɗannan abubuwa sun yi ƙasa sosai, mutane sun sami walwala wajen gudanar da harkokin kasuwanci sun a yau da kullum. Sai dai har yanzu ana samun rahotanni na kashe-kashen mutane da satar shanu a wasu yankunan karkara da waɗanda basu tuba ba daga cikin ‘yan ta’adda suke aiwatarwa.

 


 

1.8 Shawarwari

·         Ya kamata gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen hukunta masu aikata ta’addanci idan ta samu nasarar cafke su, saboda tada tuba da suka yi.

·         Ta rage ba su kuɗaɗe saboda tubar da suka yi, domin da waɗannan kuɗaɗe ne suke sayen manya-manyan gidaje da manyan makamai suna ba sauran yaransu suna aikata wannan ta’addanci.

·         Yawancin ‘yanta’addan suna shigowa daga wata ƙasa ne don haka hukuma ta ƙara ɗauƙar matakin, kowa ya kashe a kashe shi. Idan aka yi haka za a sami raguwar wannan barna da ‘yanta’adda ke yiwa mutanen Zamfara.

·         A aika da jami’an tsaro ‘yan yaƙin sunƙuru, wato kungiyoyin tsaro na Operation Puff adder” na babban sifeton ‘yan sanda da “Operation Hadarin Daji” na haɗin guiwar Sojoji da sauran jami’an tsaro da kuma kungiyar “Operation Eage Gye” wanda aka ƙaddamar a jiha domin su kurɗa lungu da saƙo inda yanta’adda ke zaune domin su fatattake su, a sami zaman lafiya a jihar Zamfara.

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments