Hoton Zuci Ganau a Waƙoƙin Maza : Nazari daga Waƙar ‘Yan Jabanda ta Kassu Zurmi

     TSAKURE: Waƙoƙin maza ko waƙoƙin jarumta waƙoƙi ne na musamman da ake shirya su ga wasu jinsin mutane da suka keɓanta daban ta fuskar jarumta da ƙarfin hali. Da irin wannan keɓantar tasu ne Magaji (2016), ya bayyana duk wanɗanda ake yi wa irin waɗannnan waƙoƙi jarumai ne waɗanda ko a cikin maza sun yi zara, domin sai jarumi ne zai iya bari a yanke shi ko a sare shi, sai jarumi zai iya shiga cikin ruƙuƙin daji domin farauta. Haka kuma sai jarumi ne zai iya bin dare ya tafi har wani gari domin ya yiwo sata. Wanan maƙala mai suna Hoton zuci Ganau a Waƙoƙin Baka: Nazari daga Waƙar ‘Yan Jabanda ta Kassu Zurmi ta ƙunshi nazari ne a kan salon Hotancin zuci ganau (visual imagery) a cikin waƙar ‘Yanjabanda. Wannan ɗaya ne daga cikin nau’o’in hotancin zuci na bayani. Maƙalar ta yi ƙoƙarin fayyace ko mene ne “Hotancin Zuci ganau”. Maƙalar ta kawo tarihin makaɗa Kassu Zurmi a taƙaice, sannan ta nazarci yadda fasihin ya sarrafa wannan nau’i na salo a cikin waƙar tasa. Ta yadda zai jawo hankalin duk mai sauraronsa tare da gamsar da shi da kuma nishaɗantar da shi a lokacin da yake sauraron waƙar.

    Hoton Zuci Ganau a Waƙoƙin Maza : Nazari daga Waƙar ‘Yan Jabanda ta Kassu Zurmi

     

    Rabiu Bashir

    Deparment Of Nigerian Languages And Lingustics,

    Kaduna State University

    rabiubashir86@gmail.com

    08035932193/08094378162

     

    1.1 Gabatarwa

    Waqa ba ƙashin yarwa ba ce, kuma xaya ce daga cikin fagage na hikima da Bahaushe ke da su wadda yakan ci karensa ba babbaka a ciki, wajen nuna gwanancewarsa a kan harshen nasa da kuma havaka al’adunsa gami da adana tarihi. Waqa, a iya kallon ta a matsayin wata hanya da ake bi domin a isar da saqo gami da bayyana al’amuran rayuwa na yau da kullum cikin wani yanayi mai burgewa da xaukar hankali. Waqa takan gudana cikin wani tsararren zance mai rauji wanda kuma ya sava da zance na yau da kullum. Ko waqar wani harshe ne na duniya wanda mawaƙa ke amfani da shi don su bayyanar da tunaninsu cikin kalmomi tsararru masu daɗi da kama jiki. Nau’o’in waqa guda biyu ne, a kwai waqar baka, wadda tun asali aka buxi ido da ita, sai kuma rubutacciyar waqa, wadda ta samu bayan Bahaushe ya iya karatu da rubutu. Duk da cewa kowanne fanni na waqar Bahaushe, watau ta baka ko rubutacciya, na xauke da abubuwan qaraswa na rayuwar al’umma, amma waqar baka ita ce mafi daxewa a wurin al’ummar bisa ga wannan takan kandame kusan duk wani nau’i na adabin Hausa. Su kuwa waƙoƙin maza wasu waƙoƙi ne da ake shirya su ga jinsin mutanen da suka kasance jarumai, waɗanda ayyukansu sun shafi ayyuka ne na jarumta wanda ba duk mutum ba ne zai iya aiwatar da irin waɗannan ayyukan sai jarumi kuma wanda ya shirya. Ire-iren waɗannan ayyukan su haɗa da farauta da dambe da kokuwa da sata da sauransu.

    Nazarin salo wani ƙaton fage ne da yake buƙatar a ci gaba da bibiyarsa don ƙara fayyace wa tare da zaƙulo irin azanci da fasaha da Allah ya yi wa zaɓaɓɓun bayinsa ta fuskar harshe. Masana sun tabbatar da cewa jigon waƙa ko turkenta kan isar da saƙo, amma ba kamar salo ba, domin kuwa da salo ne makaɗi kan isar da saƙonsa ya kuma jawo hankalin mai sauraronsa tare da birge shi. Yahya (2007:2), ya kira salo da cewa shi ne ‘asirin waƙa’. Haka kuma da fahimtar salo ne za a iya gane makaɗi mai azanci ne ko mara azanci. A kuma iya gane waƙa mai gishiri ce ko waƙa ce ‘lami’. Da wannan dalilin ya sa manazarta irin su Leech (1968), ke gwada cewa ba wani abu ne ke sanya waƙa ta yi armashi, ta kuma sanya mawaƙi ya shahara ba, illa iya sarrafa salo.

    Hotancin zuci a iya cewa shi ne ƙashin bayan salo, domin kuwa da shi ne makaɗi kan zayyano hoton abu muraratan a cikin waƙa, har ya sa mai saurare ya riƙa kallon abin da idon zuciyarsa ta yadda zai ga kamar ga abin nan a gabansa yana kallo ƙuru ƙuru da idonsa na zahiri. Sannan kuma hotancin zuci yana tafiya ne da sarrafa muhimman sassan jikin ɗanadam wajen isar da saƙo, kamar su ido, da kunne, da harshe, da hannu, da kuma uwa uba ƙwaƙwalwa wadda ita ce ke sarrafa dukkan wani tunani na mutum. A zahiri da za a cire hotancin zuci daga cikin salo sai a iske cewa salon ya raunana ta yadda ba zai gamsar ba, ballantana ya tsaya da ƙafarsa har ya ƙayatar tare da burge mai saurare. Hotancin zuci na bayani ya kasu zuwa a ƙalla gida bakwai, wanda shi hotancin zuci ganau ɗaya ne daga cikinsa.

     

     

    1.2 Hotancin Zuci (Imagery)

    Alal haƙiƙa, masana sun taka rawar gani irin yadda ya kamata a wajen ƙoƙarin nazartar salo kamar yadda muka faɗi a baya, kuma hakan bai rasa nasaba da fahimtar cewa da salo ne a kan iya tantance balaga da hazaƙa da kuma basirar makaɗi, kuma da fahimtar salo ne ake iya fahimtar manya da ƙananan saƙonni da kuma dukkan abin da waƙa ta ƙunsa. Sai dai duk da kasancewar hotoncin zuci ginshiƙi ko koma a ce ƙashin bayan salo, bai samu wata kulawa ta musamman ba daga wajensu, musamman ma a harshen Hausa. Nazarce-nazarce a wannan fanni sun yi matuƙar ƙamfa, domin kuwa ayyukan da aka iya gabatarwa a ɓangaren ba su wuce a irga su ba, kuma ko suma za a iske cewa sun ɗan taɓo wani abu ne na daga cikinsa ba tare da zurfafa bayani ba, ko kuma sun ɗan taɓo wani nau’i daga cikin nau’o’insa ba tare da tantance menene shi kansa hotoncin zucin ba. A wasu lokutan za a iske cewa manazartan sun dai iya bayyana hotoncin zuci a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da mawaƙa kan bi su isar da saƙonninsu, musamman a lokacin da suke ƙoƙarin bayyana salo da kuma ainihin ƙumshiyarsa, ba tare da mayar da hankali a wajen ganin an fayyace menene hotoncin zucin ba. Hotancin zuci na bayani kamar yadda Damanhuri (2011:2-5) ya bayyana ya kasu zuwa gida bakwai, inda ya nuna cewa hoton cin zuci na bayani kan wakilci sauti, (auditory imagery), ko ƙamshi ( olfactory imagery), ko ɗanɗano (gustory imagery), ko taɓawa kamar tauri ko taushi ko laima ko zafi ko kuma sanyi (tactile imagery), ko ji a cikin jiki kamar yunwa ko ƙishi ko tsoro (organic imagery), ko motsi da jiki ( kinesthetic imagery), sai kuma hotoncin zuci Ganau (Visual Imagery).

     

     Muhammad (2014), a matsayin na farko farko da ya yi bakin rai bakin fama wajen ganin ya fayyace tare da kawo kyawawan misalai na abin da hotancin zuci ya ƙunsa a harshen Hausa, duk da cewa shi kansa wannan aikin bai iya tantance ko mene shi kansa hotoncin zucin ba ballantana ya zayyano nau’o’i’nsa, sai dai kawai ya mayar da hankali a kan wani nau’i na hotoncin zuci (Hotancin zuci ganau), wanda ɗaya ne daga cikin nau’o’in hotancin zuci na bayani guda bakwai kamar yadda masana suka tabbatar.

     

    1.3 Ma’anar Hotancin Zuci

    Masana wannan fanni na nazarin salo sun bayyana fahimtarsu wajen ganin sun fayyace ma’anar Hotancin zuci da kuma ƙunshiyarsa. Misali Cuddon (1977:413), ya bayyana hotancin zuci a matsayin ‘samar da kwatanci’. Sannan ya ƙara da cewa kalmomin hoton zuci da hotoncin zuci na da ma’anoni da dama. Ya nuna cewa a dunƙule hotancin zuci ya ƙunshi yin amfani da harshe don a baiyanar da wani abu ko aiki ko wani abu da aka ji a jiki ko wani tunani ko ra’ayi ko matsayin zuciya da kuma dukkan wani abu da jiki ka iya ji ko ya iya tunanowa. Ya ƙara nuna cewa, mafi yawan hotancin zuci, ba duka ba ana isar da su ne ta hanyar amfani da wata siga ta adon harshe a matsayin kwalliya, ko tamka ko, mutuntarwa, ko kuma da kalmomin amsa kama. Haka kuma ya nuna cewa hotancin zuci kan iya kasancewa wanda za a iya gani da ido (visual), ko a shaka da hanci (olfactory), ko a taɓa da hannu (tactile), ko a ji da kunne (auditory), ko a ɗanɗana da harshe (gustatory), ko a hakaito da ƙwaƙwalwa (abstract/ intellect), ko kuma a motsa da dukkan gangar jiki (kinaesthethic). Ya jaddada cewa sau tari ba a iya rarrabe wani nau’in hotancin zuci ba tare da wani ba, domin sukan yi shigar giza gizai a tsakaninsu ko kuma su haɗe da juna, inda misali hotancin zuci wanda ya shafi motsi da jiki kan iya kasancewa wanda za a gani da ido.

    Baldick (2004:121), kuwa ya bayyana hotoncin zuci ne a matsayin wata hanyar isar da saƙo da ta ƙunshi amfani da harshe a aikin adabi wadda kan sa ƙwaƙwalwa ta kwaikwayi wani abu da aka kawo cikin wasa da harshe ko a zahiri kamar wani aiki ko matsayi. Ya nun cewa hotoncin zuci a cikin aikin adabi ya ƙunshi sarrafa sura ko hoton zuci ne, wanda ba dole ya kasance da ido kawai za a iya ganinsa ba, ya shafi amfani daƙwaƙalwa da hankali da sauran wasu sassan jikin mutum. Sau tari a kan baiyana hotoncin zuci a matsayin adon harshe ne da aka sarrafa a cikin aikin adabi, musamman ta sigar tamka da kwalliya.

    Shi kuwa Holman (1986:56), ya nuna cewa ne hotoncin zuci na ɗaukar ma’anoni guda biyu, watau zai iya ɗaukar ma’anar yin amfani da hotuna kai tsaye a cikin waƙa domin a kwatanta wani abu, ko kuma yin amfani da adon harshe kamar kwalliya ko tamka ko mutuntarwa domin a kwatanta wani abu da wani a fakaice, kuma domin a ƙara fayyace wannan abu ƙarara ta yadda mai sauraro zai riƙa ganin hoton abin a zuciyarsa. Su kuwa wasu masana da suka haɗa da Didac da kuma LL Orense, sun baiyana cewa waƙa cike take da hotoncin zuci, duk da cewa zai yi wuya a iya gane shi saboda sau tari yakan zo ne tare da sarrafa adon harshe kamar su kwalliya, da tamka, da kuma alamci da sauransu. Sun ƙara da cewa wannan dalilin ya sa yawancin ƙamusu na adabi idan za su kawo ma’anar hotoncin zuci sai sun haɗo da ma’anar hoton zuci. Sai suka jaddada cewa hoton zuci da kuma hotoncin zuci na daga cikin abubuwan da mawaƙa ke yawan sarrafawa a cikin waƙoƙinsu, sai dai ba a iya fahimtarsu yadda ya kamata don haka zai yi wahala a iya tantance amfaninsu.

    Ƙamusun waƙa (2017), ya bayyana hotoncin zuci a matsayin sunan da ake ba wasu abubuwa a waƙa waɗanda ke haskaka wani tunani. Duk da cewa ma’anar hotonci na dai dai da sura, amma a waƙa hotoncin zuci ya wuce abin da za a iya gani kawai da ido, ya haɗa da dukkan abin da sauran muhimman sassan jikin mutum ka iya yi, wanda ya haɗa da saurare da taɓawa da ɗanɗanawa da kuma sunsunowa na dukkan wani abu ko yanayi ko tunani da mawaƙi ke ƙoƙarin faiyacewa. Ƙamusun ya ƙara da cewa hotoncin zuci ya haɗa da sarrafa adon harshe don a bayyana wani abu ko aiki ko kuma tunani ta yadda za su kasance tamakar muna ganinsu a fili ƙuru-ƙuru.

     Yahya (2001:88), kuwa, ya kira wannan salo na hotoncin zuci ne da sunan “zayyana”, wanda ya ce da shi ne mawaƙi kan suranta wani yanayi har ya kasance mai saurare ko karatun waƙarsa ya riƙa ganin wannan yanayi a cikin ransa ta amfani da idon zuciyarsa. Har wa yau, Yahya (2001:89), ya ƙara da cewa hotoncin zuci, na nufin amfani da kalmomi a cikin waƙa waɗanda tattare da sauran maganar da suka fito cikinta za su ƙirƙiro siffar abu ko yanayi a cikin zuciyar mai karatu ko sauraren waƙar. Ya ƙarfafa cewa, yadda me yin zane-zane ke dubin abin da ke a gabansa, ya yi amfani da alƙalamin zane ya zana surar abin nan da ke a gabansa, haka ne mawaƙi ke dubin abu ko yanayi da idon zuciyarsa ya kuma yi amfani da basirarsa da kalmomin harshen da ya mallaka (waɗanda su ne alƙalaminsa da tawadarsa), ya zana (wato ya zayyana) abin nan, ko yanayin nan da ke a gaban idon zuciyarsa. A taƙaice ya nuna cewa, hotoncin zuci salo ne da mawaƙi ke amfani da kalmomi domin ya ƙirƙiro hoton abin da ke a zuciyarsa ta yadda mai karatu ko sauraren waƙar zai ga hoton da idon zuciyarsa. Ya jaddada cewa mawaƙi ta fuskar salon zayyana, mai ɗaukar hoto ne ko mai zane.

    Idan aka duba fahimtar masana a kan hotancin zuci, za a fahimci cewa wani salo ne da ya shafi isar da saƙo ta hanyar jawo hankalin mai saurare ya gani ko ya ji wani abu ko yanayi da idon zuciyarsa kamar yadda fasihi ya zayyano masa ta hanyar zana masa hotuna cikin bayani ta yadda zai rinƙa jin kamar ga abin da aka nuna masa nan yana gani da idanuwansa na zahiri.

     

    1.3 Taƙaitaccen Tarihin Kassu Zurmi

    An haifi Kassu Zurmi ne a wani gari da ake kira Magarya ta ƙasar Zurmi wanda ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a wannan lokacin. Sunan Kassu na yanka shi ne Abubakar. Sunan mahifiyar Kassu Maimuna, mahifinsa kuma sunan shi Muhammadu Ganga, wanda makaɗin farauta ne. Kenan a wajen kiɗa da waƙa a iya cewa Kassu ya yi gado ne daga wajen mahifinsa, wanda shi ma ya shahara ne a kiɗan tauri. Duk da cewa Kassu bai yi ilmin boko ba a rayuwarsa, amma ya yi ilmin addini dai-dai gwargwado tun yana matashi, kafin daga bisani ya watsar ya fara bin mahaifinsa wajen yawon kiɗa. Abubakar Kassu Zurmi ya zauna ne a wani gari da ake kira Kadawa, mai nisan a ƙalla kilomita biyu daga Magarya, wato ainihin mahaifarsa, inda a nan ya rayu kuma ya yi aure har ya hayayyafa, ya auri mata huɗu da suka haɗa da Sadiya (Yaya), da Zuwaira (Auta), da Aishatu (Karɓa), da kuma Zainabu.Allah ya azurta Kassu da ‘ya’ya guda goma sha biyu, shida maza shida mata.

     Ta fuskar kiɗa da waƙa, kafin Kassu ya yi nisa a kiɗan farauta wadda ita ya gada, sai da ya taɓa kiɗan noma, kafin daga bisani ya tsunduma cikin kiɗan farauta, wanda a nan ne ya yi fice har duniya ta san shi. Makaɗa Kassu Zurmi yana amfani ne da kalangu a matsayin abin kiɗa, kuma shi kaɗai yake aiwatar da waƙarsa ba tare da ‘yan amshi ba. Bisa ga wannan dalili ne Gusau (2014: ix), ya bayyana tsarin rera waƙoƙinsa da cewa sun kasance ne kamar haka “ +Kaɗaita + Jagora + Ƙari +Taƙidi – Rakiya – Tarbe – Zagin Gindin Waƙa”. Abubakar Kassu Zurmi ya rasu ne a cikin watan Satumba, na shekarar 1980, a garin Kadawa, sakamakon rashin lafiya da ya yi ta fama da ita kamar yadda Magaji (2016:9-10) ya tabbatar.

     

    1.4 Hotancin Zuci Ganau a Waƙar ‘Yan Jabanda

    Hotancin zuci ganau ɗaya ne daga cikin nau’o’in hotancin zuci na bayani, wanda ya shafi hoton tunanin abin da za a iya gani ne da ido wanda makaɗi ya zano cikin bayani. Yawancin kalmomin da ake sarrafawa domin a isar da saƙo a cikin waƙa waɗanda za a iya gani ne da ido. Idan makaɗi ya tashi yakan kalli abu ne da idon zuciyarsa saboda haka sai ya yi ƙoƙarin zano hoton abin cikin bayani ta yadda mai saurare zai iya sarrafa nasa idon zuciyar ya kalli abin irin kallon da mawaƙin ke yi masa. Wato alhakin mawaƙi ne ya ja hankalin mai saurarensa ta hanyar zaɓo kalmomin da suka dace ya zana hoton abu ko yanayin da yake da buƙatar mai sauraren nasa ya iya gani har kuma ya fahimci wani abu na saƙon da hoton ke ɗauke da shi, kuma a wurin zano hoton ne zai yi amfani da kalmomi waɗanda za su nuna wa mai saurare hoton abin ya gan shi da idon zuciyarsa ya kuma iya tantance shi da idon sa na sarari.

    Hotancin zuci ganau ya ƙunshi zano hoton abu ne ko yanayi ta hanyar kwatanta wannan abun ko yanayin ga mai saurare ta yadda mai saurare zai yi amfani da wannan kwatancen ya samar da hoton wannan abin ko yanayin a cikin zuciyarsa. A lokacin wannan kwatancen da makaɗi kan yi zai iya kasancewa ta hanyar amfani da kala ko sauti ko tsari na sifa ko aiki wanda za a iya gani da ido. Ire-iren hotunan da mawaƙa kan zano cikin bayani ta hanyar kwatanta abu ko yanayi domin mai saurare ya gani da nasa idon zuciyar, har kuma ya rinƙa jin ga abin nan yana gani a zahiri su ake kira da hotancin zuci ganau. Ire-iren waɗannan hotuna mai saurare na amfani da idanuwansa na zuci ne da kuma na zahiri ya tantance su har kuma ya samu damar fahimtar saƙon da suke ɗauke da shi.

    Makaɗa Kassu Zurmi ya sarrafa hotancin zuci ganau a cikin waƙarsa ta ‘yan Jabanda a lokacin da ya tashi zano hoton yanayin halin da ‘Yan Rikudawa suka shiga a lokacin da suka gabza da ‘yan Jabanda a wurin da ya ce:

     Jagora:Ya ƙi ya ci ‘yan Rikudawa,

     :Haikau kwance,

     :Sani kwance,

     :Huri kwance,

     :Bobo kwance,

     :Inga nig ga an harbe shi.

     

    Kassu na ƙoƙarin zano hoton irin halin da ‘yan Rikudawa suka shiga ne bayan sun yi kaciɓis da ‘yan Jabanda sun gwabza faɗa a daji, wanda har ya kai ga an bubbuge su ƙasa. Saboda haka da ya tashi sai ya zano wa mai sauraro hoton yanayin da suke ciki ta hanyar bayani inda ya nuna cewa ga Haikau nan a kwance, ga Sani nan ma a kwance, suma su Huri da Bobo duk ga su nan su ma a kwance, shi kuma Inga an harbe shi ne gefe guda. Da zarar mai saurare ya kalli hoton wannan bayanin idon zuciyarsa zai kawo masa hoton mafarautan ne, ya gan su a kwak kwance kamar yadda makaɗin ya zano masa su da yanayin kwanciyar da kowanne ya yi, sannan kuma sai ya rinƙa jin kamar ga su nan yana ganinsu da idonsa na sarari a gaban shi. Kuma hakan ne zai sa ya fahimci cewa ai lallai ‘yan Jabanda sun fi ƙarfin ‘yan Rikudawa, wanda shi ne saƙon da makaɗin yake ƙoƙarin isarwa.

    Haka kuma da Kassu ya tashi fayyace irin sarar da ‘yan Jabanda suka yi wa abokan bugawarsu, sai ya sarrafa hotancin zuci ganau ya zano wa mai saurare hoton yanayin saran yadda shi ma zai iya gani da idanuwansa. Inda ya ce:

     

     Jagora:Da wanga shingi nag gabas,

     :Hak kai wanga shingin yamma,

     :Yaro in ka ga rijiya ga baya,

     :‘yan Jabanda nay yasa ta,

     :Ko tsayin wata,

     :Ko shan doguwa.

     

    Kassu na zano hoton ayarin abokan bugawar ‘yan Jabanda ne da ire-iren sarar da aka yi musu a lokacin da suka gauraya a cikin daji, saboda haka sai ya zaɓi ya zano wa mai saurare hotonsu cikin bayani ta yadda shi ma zai iya sarrafa idon zuciyarsa ya hange su da kuma ire-iren sarar da aka yi musu. Sanan kuma zai sarrafa idonsa na sarari ya ji kamar yana ganin su a gaban shi. Makaɗin ya yi zanen ne ta hanyar kwatanta wa mai saurare daga kan wannan mafarauci zuwa kan wancan,wanda idon zuciyar mai sauraren zai nuna masa su da nau’o’in saran da aka yi musu. Sannan ya zano masa nau’ikan sarar da aka yi musu. Inda shi kuma idon zuciyar mai saurare zai gano masa hoton su a wurin da aka zana masa su tare da nau’ikan sarar da aka yi musu, ta yadda zai ga wani saran a tsaye kuma da zurfi wani kuma a kwance kamar fitowar wata. Sarrafa hotancin zucin, shi zai sa mai saurare ya rinƙa jin kamar ga su nan yana ganin su da idonsa na fili ɗauke da raunukan da aka yi musu.

    A wani wurin kuwa makaɗin ya zano wa mai saurare hoton halin da Gado ne ke ciki a lokacin da ya haike wa ‘yan Jabanda, sai ya nuna shi ga mai saurare kamar haka:

     Jagora:Ina Gado Rana jikan Kolo?

     :Shi ma kwance nai iske shi,

     :Dangi na gadon ɗauka tai,

     :‘Yan Jabanda sun ɓata shi.

     

    A wannan ɗan waƙar Kassu na son kawo halin da Gado (wani mafarauci) ya faɗa ne a lokacin da ya faɗa wa ‘yan Jabanda su kuma suka buge shi, don haka sai ya zano hotonsa a kwance, ga shi dangin shi sun ɗauko shi a kan gado yare-yare. Yin hakan zai sa mai saurare ya yi amfani da idon zuciyarsa ya hangi Gado a cikin yanayin da Kassu ya zano shi, inda zai hange shi a kwance an taitayo sa cikin jini, sannan kuma ya riƙa jin kamar ga shi nan yana kallonsa a fili a lokacin da aka ɗauko sa ɗin baya ko iya motsawa.

     

    A wani wurin kuwa Kassu ya zano wa mai saurare hoton wurin da ‘yan Jabanda suka tare ‘yan Barkejawa ne suka far musu inda a nan ne suka fafata.

     

     Jagora:Jabandawa jar kuka sun ka tare su,

     :Suna cikin sagagi,

     :Kowanne zuciya na ci nai,

     :Jandau yam miƙe,

     :Ya ce to Sharu gyara dac can.

     

    Kassu yana bayyana wurin da ‘yan Jabanda suka tare ‘yan Barke ji ne a cikin daji, bayan da suka neme su da fitina a cikin kasuwa amma ba su kula su ba, don haka sai suka biyo su bayan gari suka tare hanya domin a yi ta a nan ta ƙare. Saboda haka da ya tashi sai ya zano wa mai saurare hoton wurin da kuma halin da su ‘yan Jabandan suke ciki na fushi da ɓacin rai ta yadda shi ma zai sarrafa idon zuciyarsa ya hange su. Makaɗin ya zano su a gindin iccen kuka ne a cikin sagagin ciyayi, sannan kuma ya zano hoton ‘yan Jabanda suna ta fushi ransu a ɓace. Sai kuma ya zano hoton Jandau (ɗaya daga cikin ‘yan Barkeji) a tsaye yana magana. Da mai saurare ya kalli hoton wanna kwatancen dam akaɗin ya yi, zai iya hangen wurin da ga iccen kuka nan sannan ga sunƙurin ciyayi, kuma zai ga yanayin da idon zuciyarsa, inda zai gano hoton waɗanda aka tare ɗin suna cikin damuwa da tashin hankali, sai kuma ya ga waɗanda suka tare ga su nan cikin fushi da ɓacin rai. Haka kuma zai riƙa jin kamar ga su nan yana ganin su a waurin da idonsa na fili.

     

    Bayan ‘yan Jabanda sun tare ‘yan Barkeji a cikin sagagi kamar yadda Kassu ya zano wa mai saurare hotonsu, sai kuma ya zano masa hoton hali da yanayin da ‘yan Barkejin suka kasance ya nuna su kamar haka:

     

     Jagora:Kahin a ƙara jimawa,

     :Sai ga Sharu an kirme shi,

     :Ga Bala can kwance,

     :Anne an bishi an tattake,

     :Sauran barwansu suka fasshage.

     

    Kassu ya zano wa mai saurare hoton halin da ‘yan Barkejawa suka shiga ne ta hanyar kwatancen yadda aka yi wa mutanen cikin hoto, inda ya zano masa hoton Sharu an kirme shi da hannu ya faɗi ƙasa, sannan ya zano hoton Bala a can gefe guda an buge shi yana kwance, ga kuma Anne can shi kuma an tattaka shi ya yi ɗai-ɗai ba ya ko iya motsi, ya kuma nuna sauran sun fashe a guje. Da zarar mai saurare ya kalli hotunan da aka zana masa cikin wannan bayanin, idon zuciyarsa zai kawo masa hoton ‘yan Barkejawan kamar yadda Kassu ya zano masa su, ta yadda zai gan su a zube an bubbuge su guda na gefe an buge shi, ga wani can shi kuma a kwance, sannan ga ɗaya can an tattake, sannan kuma har ya riƙa jin kamar ga su nan yana kallon su da idonsa na zahiri a cikin wannan yanayin.

     

    Da Kassu ya zana wa mai saurare hoton ‘yan Barkeji an watsa su, sai kuma ya zano masa hoton makaɗinsu cikin bayani ta yadda mai saurare zai hange shi a guje kamar haka:

     Jagora:Sai ga Roƙu kacau-kacau da kalangu,

     :An ka ruhe da hannun riga,

     :To bahago ne,

     :Sai nig gane ‘yat tahiya tai.

     

    A nan Kassu ya zano hoton makaɗin ‘yan Barkeji ne a guje ya ɓoye kalangunsa a cikin riga kada a gane shi, amma saboda kasancewar ya san cewa shi bahago ne sai ya iya gane shi daga irin tafiyar da yake yi. Zano hoton Roƙu da makaɗin ya yi cikin bayani, zai ba mai saurare damar ya sarrafa idon zuciyarsa ya hange shi kamar yadda makaɗin ya zano shi, inda zai gano shi a guje yana ƙoƙarin ɓoye kalangun nasa a cikin riga, har kuma ya riƙa jin kamar ga shi nan yana ganinsa sanda yake gudun da idanunsa na fili.

     

    Bayan Roƙu (makaɗin ‘yan Barkeji), ya sami kansa a gida, sai kuma Kassu ya zano hotonsa yana bayar da labarin waɗanda ‘yan Jabanda suka buge a cikin tawagarsu, inda ya ce:

     Jagora:Ka ga an bige Gandau?

     :Sai yai min na bisashe,

     :Yag girgiza man kai nai,

     :Roƙu Katakare sun ka sabatta?

     :Kuma sai ya kakkaɓa mun kai,

     :Kai ko duka da Garu-garu na Mande?

     :Yad dai girgiza mun kai nai.

     

    A wannan ɗan waƙar Kassu ya zano wa mai saurare hotunan Roƙu ne kala-kala, bayan ya koma gida yana bayar da labarin yadda aka kwashe tsakanin ‘yan Jabanda da ‘yan Barkeji, sai ya nuno shi ana masa tambaya na abubuwan da suka faru shi kuma yana bayar da amsa. Da farko Kassu ya zano hoton makaɗin ne ya girgiza kai na alamar amsawa bayan an tambaye shi ko an bige Gandau, sai kuma ya zano wani hoton daban yana kakkaɓa kai lokacin da aka tambaye shi ko an sabatta Katakare, sannan ya sake nuno wani hoton makaɗin yana girgiza kai da aka tambaye shi ko shi ma Garu garu na Mande an kashe shi? Mai saurare na kallon waɗannan hotunan da Kassu ya zano cikin bayani, idon zuciyarsa zai nuna masa Roƙu ana masa tambaya yana bayar da amsa a wurare daban-daban, sannan kuma zai riƙa jin kamar ga makaɗin nan yana gani ana masa tambayoyin yana amsawa a sarari.

     

    A wani wurin kuwa da Kassu ya tashi zai zano wa mai saurare hoton Sharu bayan ‘yan Jabanda sun buge shi ƙasa ya faɗi, sai ya sarrafa hotoncin zuci ganau ya ce:

     

     Jagora:Ashe Riɓa ɓarai yaɗ ɗaukai,

     :Bahillacan nan,

     :Yac ce ga kashi gudaji-gudaji,

     :A’a mai ƙarfi ka tutu ga tamba,

     :Maiso nai gudaji-gudaji.

     

    A nan Kassu ya zano wa mai saurare hoton Sharu ne ya nuna ga shi nan wani bafilatani ya ɗauko shi, inda har ya yi kashi mai guda-guda a cikin wandonsa saboda wahala, sannan kuma ga amai nan ya yi a gefe guda. Wannan hoton da makaɗin ya zano cikin bayani zai sa mai saurare ya sarrafa idon zuciyarsa ya hangi Sharu a cikin wannan mawuyacin halin da makaɗin ya zano masa shi, inda zai gan shi an ɗauko shi, ga kasha nan da ya yi mai guda-guda, a gefe guda kuma ga amai can da ya yi. Sannan kuma mai sauraren zai riƙa jin kamar ga mafaraucin nan yana gani da idonsa na fili a cikin amai da kashi.

     

    5. Kammalawa

    Salon Hotancin zuci ganau salo ne da ke ba makaɗi dama ya isar ga saƙonninsa cikin sauƙi da burgewa, ta yadda mai saurare zai iya fahimtar saƙo tare da ganin ainihin hoton abin da makaɗin ya zayyano masa cikin bayani ta hanyar amfani da idanuwan zuciyarsa. Makaɗa Kassu Zurmi ɗaya ne daga cikin fitatttun makaɗan maza da ya shahara wajen kiɗan tauri, wanda yakan yi amfani da hikimarsa ya waƙe tare da zuga ‘yan tauri. Wannan maƙala ta nazarci hotancin zuci ganau ne da yadda makaɗin ya sarrafa shi wajen ganin ya isar da saƙonsa ga mai saurare cikin hikima da zalaƙar harshe, ta yadda mai saurare zai sami damar fahimtar saƙon tare da kallon hotunan bayanan da makaɗin ya zano masa da idon zuciyarsa, wanda hakan zai sa saƙon ya shige shi ainun har kuma ya ji kamar abin ya faru ne a kan idonsa. Maƙalar ta tabbatar da cewa Makaɗa Kassu Zurmi ya samu damar isar da saƙon nasa ta hanyar sarrafa wannan nau’in na hotancin zuci, wanda hakan ya fayyace irin fasaharsa da kuma naƙaltar harshe.

     

    Manazarta

     

    A tuntuɓi mai takarda domin samun manazarta.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.