Salon Sarrafa Harshe a Wasu Waƙoƙin Alh. (Dr) Mamman Shata

    Tsarkure: Wanan maƙala mai suna “Salon Sarrafa Harshe A Waƙoƙin Shata” ta ƙunshi nazari ne a kan salon sarrafa Harshe da tubalansa, waɗanda Alhaji (Dr) Mamman Shata ya yi amfani da su domin ya isar da saƙonninsa cikin sauƙi da burgewa da kuma nuna zalaƙar harshe, ta yadda zai jawo hankalin duk mai sauraronsa tare da gamsar da shi da kuma nishaɗantar da shi a lokacin da yake sauraron waƙoƙinsa. Nazarin ya mayar da hankali ne musamman a kan ‘Muhimman Tubalin Salo’, guda ɗaya cikin bakwai waɗanda masana irin su Thrall da wasu (1960) da Ɗangambo (1981) da kuma Yahya (2001), suka lura da su. Wannan Muhimmin Tubalin Salo ya shafi ‘Mallakar Kalmomi’, inda za a nazarci zaɓen kalmomi, da sarrafa baƙin kalmomi na Ingilishi da na Larabci, da kuma Karin harshe. Muƙalar ta ɗauki wannan muhimmin tubali ne guda ɗaya don binciken ya auna wasu waƙoƙin Shata na Fada domin nazartar yadda mawaƙin ya sarrafa shi. Binciken ya kawo misalan yadda makaɗin ya yi amfani da wannan tubali wajen gina salon sarrafa harshensa. Binciken zai gudana ne a cikin waƙoƙin makaɗin guda huɗu na Fada waɗanda suka haɗa da waƙoƙin Sarkin Daura Mahammadu Bashar guda biyu masu taken ‘’Mai Daura Bashar Ɗan Sanda”, da “Kwana lafiya mai Daura”. Sai waƙarsa ta Sarkin Zazzau Shehu, da kuma ta Malami Sarkin Sudan. An ɗora wannnan bincike ne a kan ra’in ƙawa (Eestethicism theory). Wanda ra’i ne da ya aminta da a nazarci kyau daga aikin fasaha ba tare da la’akari da tarbiya ko aƙida ko kuma dalilan siyasa ba.

    Salon Sarrafa Harshe a Wasu Waƙoƙin Alh. (Dr) Mamman Shata

    Rabiu Bashir

    Deparment Of Nigerian Languages And Lingustics,

    Kaduna State University

    rabiubashir86@gmail.com

    08035932193/08094378162

     1.0 GABATARWA

    Waƙar baka wani fage ne mai zaman kansa da yake ƙunshe da ɗimbin hikima da basira tare da taskace tarihi da al’adu da adabin al’umma, duk kuwa da sauyawar zamani. Hakan ya sa kullum ake samun sababbin rubuce-rubuce a ciki.

    Idan ana maganar waƙar baka a ƙasar Hausa kuwa, tarihinta ba zai cika ba, har sai an ambaci Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. An haifi Alhaji Mamman Shata a gundumar Musawa ta cikin lardin Katsina a jihar Katsina ta yanzu, kuma ainihin sunansa Muhammadu Lawal. Duk da ba za a iya tantance ainihin shekarar da aka haife shi ba, saboda a daidai lokacin ba a yin rajistar haihuwa, sai dai a yi la’akari da wani muhimmin abu da ya faru a wannan lokacin, kamar na yunwa ko fari ko yaƙi, amma ana ƙiyasta cewa an haifi Mamman Shata a shekarar 1923, shekarar da ake wa laƙabi da ‘shekarar mutuwar shanu’ (Sheme, da wasu 2006, shf. 43). Asalin mahaifin Shata shi ne Ibrahim Yaro, wanda Bafilatani ne, mai tarin arziki, kamar shanu da awaki da sauran dabbobin kiwo, kuma da yana zaune ne a cikin daji kafin daga bisani ya yi ƙaura zuwa Musawa, kuma duk da haka bai daina kiwo ba. Yana da ‘ya’ya guda uku, wato da Shata da yayarsa Yalwa, da kuma wani ɗan uwan haihuwarsu. Kenan a iya cewa Shata Bafilatani ne usulan, duk da dai baya jin fillancin. Sunan mahaifiyar Mamman Shata Lariya, kuma asalinta Bakanuwa ce daga garin Tofa, kuma kafin ta auri mahaifin Shata ta taɓa aurar wani mai suna Musa, kuma ta haifi ɗa namiji da shi, mai suna Ali. An sa Mamman Shata a makarantar allo tun yana ɗan shekara biyar da haihuwa, daga bisani Shata ya daina karatun allo, kuma bai shiga makarantar boko ba.

    Bayan Mamman Shata ya bar makarantar allo, sai ya kama sana’ar sayar da goro ta ‘yan hamsin. A dalilin wannan sana’a ta ɗan hamsin ne Shata ya fara waƙa, domin a wannan lokaci idan an je cin kasuwa, yamma ta yi sai samari su haɗu su shirya wasannin gargajiya iri iri, kuma a kowacce kasuwa akwai filin da ake taruwa don gudanar da irin waɗannan wasanni, kuma a wajen ne akan shirya gasa ta waƙa a tsakanin matasa na unguwanni daban daban. A wannan lokacin ba suna yin waƙar ba ne don kuɗi, sai dai don nishaɗi a tsakaninsu. Daga ire iren waɗannan wasanni ne har Shata ya fara shahara, inda yakan cinye gasar gari da gari, to sai aka fara kiransa da “Sarkin waƙa”. Bayan Alhaji Mamman Shata ya bar garin Musawa sai ya koma ƙetare da zama, daga nan sai ya koma Malumfashi, daga Malumfashi sai ya koma garin Bakori da zama, inda a nan ne ya yi auren fari ya auri wata mata mai suna Binta, wadda aka fi sani da Hajiya Iya. A zaman Shata na garin Bakori, ya bar abubuwan tarihi a rayuwarsa. Wato kasancewar a garin ya yi auren fari, kuma a garin ne ya fara gina gidan kansa (Sheme da wasu 2006, shf. 77).

     Allah ya yi wa Shata rasuwa a asibitin Malam Aminu Kano. Bayan rasuwarsa sai ‘yarsa Jamila, wadda ita ke jinyarsa, ta sa aka kai gawarsa garin Daura, inda a can aka yi masa jana’ida aka binne gawarsa a gidan Sarkin Daura Alhaji Mahammadu Bashar (Sheme da wasu, 2006, shf. 357).

    Duk da cewa wasu manazartan na kallon salo a matsayin wani abu mai wahalar fayyacewa, musamman ta fusakar ma’ana, Yahya (2001), da Adamu (2002), hakan bai hana masana bayyana abin da suka fahimta da salo ba. Misali Stephen (2000), ya nuna cewa salon fasihin waƙa shi ne yadda fasihin ke kulawa ko sarrafa hikimomin harshe da kuma ƙoƙari wajen zaɓen kalmomi da amsa-amo da Karin waƙa da raujinta da kuma yadda yake sarrafa su daidai da tunaninsa a waƙe. Wato dai salon sarrafa sifofin harshen a asali gwargwadon zurfin tunanin fasihi da kuma buƙatarsa.

    Shi kuwa Baldick (2004), ya bayyana salo ne a matsayin hanya ta musamman da wani fasihi ko zamani ko wata mazhaba ko wani fanni ya shahara da shi wajen sarrafa harshe.

    Yahya (2001), kuwa cewa ya yi salo na nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar.

    Gusau (1975 da 2003), ya bayyana salo a matsayin wata dabara wadda ake yi wa harshen waƙa kwalliya da ita. Wato a kan zaɓi kalmomi ne a zayyana waƙa da su, a ƙawata ta sosai ta yadda za a burge mai saurare a kuma jawo hankalinsa.

    Ɗangambo (1981), ya bayyana salo ne a matsayin hanya ko dabara ta isar da saƙo. Sai ya ƙara da cewa lalle ne salo ya ƙunshi zaɓi, kuma kyan salo ko muninsa ya danganta da yadda kowane mutum ya zaɓi abubuwan da ya yi amfani da su cikin rubutunsa, ko furucinsa don isar da saƙo.

    Idan muka yi la’akari da waɗannan ma’anonin salo da masana suka kawo, za a iya fahimtar cewa, babbar manufar salo ita ce, kyautatawa da ƙawata saƙo da sauƙaƙe hanyar isar da shi da kuma fahimtarsa. Haka kuma daga cikin muhimmancin salo a kwai kwarzanta waƙa ko mawaƙi, da nuna gwanancewar fasihi wajen isar da saƙo, da bambanta tsakanin mawaƙa da ita kanta waƙar, da raya harshe, da kaifafawa da kuma sarrafa tunani, da sosa zuciya, da kuma fayyace sirrin waƙa.

     2.0 Tubalan Ginin Salo

    Idan aka yi la’akari da bayanan da masana suka yi ta kawowa don ƙoƙarin fayyace dangantakar da take tsakanin harshe da salo, a iya cewa salo wani ɓangare ne na harshe, domin kuwa da shi ne ake isar da duk wani saƙon da ake buƙata a cikin waƙa. Sai dai shi salo ya fi mayar da hankali ne a kan ire iren hikimomi da dabaru da suka shafi isar da saƙo da kalmomi walau da baki ko kuma a rubuce. Kuma kamar yadda Leech da Shorts (1981), suka bayyana a gargajiyance an fi alaƙanta shi da ayyukan hikima. Haka kuma salo wani makeken fage ne wanda ke da ruwa da tsaki a kowane irin furuci na kalma ko jimla da za a furta a waƙa. Sannan salo a waƙa zaɓi ne na mawaƙi da yake amfani da shi wajen ƙawata harshen da yake Magana da shi, ko kuma saƙƙonnin da yake zubawa a cikin ɗiyan waƙa.

     Mukhtar (2004), yana ganin a iya raba manyan tubalan ginin salo aƙalla guda huɗu, inda za a iya nazartar salo ta hanyar nazarin tsarin ginin kalma ‘morphological schemes’, sai kuma ta hanyar nazartar tsarin ginin jumla ‘syntactic schemes’, sai kuma ta hanyar nazartar tsarin sauti ‘phonological schemes’, da kuma ta hanyar nazartar adon harshe ‘schemes of figures’.

    2.1               Mallaka/Amfani Da Kalmomi

    Mallakar kalmomi da iya sarrafa su ta yadda ya dace shi kan bambanta waƙa da zance na yau da kullum. Don haka masana irin su Muhammad (1978), da Ɗangambo (1981), da Yahya (1984), da kuma Gusau (2008), suka nuna cewa waƙa kan kasance cikin “Wasu kalmomi ne zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”. Wannan dalili ya sa mawaƙi yake buƙatar ya kasance fasihi wajen zaɓen kalmomin da zai yi amfani da su a cikin waƙarsa, domin salonta ya inganta har saƙonta ya isa ga waɗanda aka nufa da shi. Yahya (2001), ya bayyana cewa: Fasahar mawaƙi ga abin da ake nufi da mallakar kalmomi ita ce ƙwarewarsa da sanin kalmar da ta dace a wuri kaza, ta fuskar ma’anarta da kuma tasirin da za ta yi wajen fahimtar maganar (wato ɗango ko baiti ko ma waƙa ɗungurumgun) da ta fito daga cikinta. Saboda haka ashe Mawaƙi ko bayan kasancewarsa mai iya yin irin wannan zaɓi, tilas ne ya zamo shi kan sa rumbu ne na kalmomi masu sigogin ma’ana da ƙira iri ɗaya (Yahya 2001, shf 4). Shi kuwa Ɗangambo cewa ya yi: Amfani da kalmomi shi ne yin sharhi dangane da yadda mawaƙi ya yi amfani da kalmomin da suka dace, da kalmomi masu zurfin ma’ana da ninkin ma’ana da sauransu.

    Shi kuwa Kolawale (1997), cewa ya yi a nan ne ake lura da yadda mawaƙa su ke sarrafa kalmomin harshe dangane da ma’anoninsu na musamman, da yadda su ke sarrafa tsohuwar Hausa da ƙirƙirar kalmomi, da kuma sarrafa kalmomi masu alaƙar ma’ana.               

    2.1.1 Zaɓen Kalmomi

    Makaɗa sukan yi ƙoƙari su zaɓi kalmomi da za su yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu, saboda mabambantan turaku da suke amfani da su, kuma kalmomin da za a zaɓo a yi amfanin da su wajen kiɗan noma ko tauri ba za su dace a ɗauka a yi wa sarki waƙa da su ba.Haka kuma sarrafa kalmomin da aka yi amfani da su wajen kiɗan maza ko kirari, idan aka sarrafa su wajen yi wa attajirai waƙa ba za su dace da su ba. Kalmomin da ake iya zaɓe a yi wa sarki kirari da su sauƙaƙa ne ga zukata, amma masu faɗi da nauyi a fassara (Bunza 2009, shf. 134).

     Akwai hikimomi da dama da makaɗa kan yi amfani da su wajen zaɓen kalomomi. Gusau (2002), ya nuna cewa waɗannan hikimomi sun haɗa da na nuna dangantaka da na karimci da baiwa da kyauta da son addini da ibada da iya mulki da sauransu.

    Alhaji (Dr) Mamman Shata kan yi amfani da ire-iren waɗannan hikimomi na nuna kyauta da karamci da son addini da ibada da iya mulki da kuma dangantakar wanda yake waƙewa wajen zaɓen kalmominsa da ya kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa, kamar yadda za a iya ganin misalan hakan daga cikin waƙoƙinsa daban-daban.

     

    2.1.2 Zaɓen Kalmomi ta Fuskar Dangantawa da Asali :

    Misali a cikin waƙar uban gidansa sarkin Daura Muhammadu Bashar inda ya ce:

    Jagora:          Baba duk asalin Sarauta Daura,

                         Tun Kal’ana tun Lamarudu,

                         Tun ga Magajiya Daurama,

     Har kuma Ummarun Bagadaza,

                         Har ta zo garai ɗan Musa.

    ‘Y/Amshi:     Kwana lafiya Mai Daura,

                         Jikan Audu Gwauron Giwa (Waƙar Sarkin Daura, Ɗa na biyar).

    A wannan ɗan waƙar, Shata ya yi amfani da wannan hikimar ta danganta Sarkin Daura Mahammadu Bashar da magabatansa, waɗanda duniya ta sani kamar su ‘Magajiya Daurama’ wadda ta yi sarautar garin Daura tun da daɗewa kafin shi, don ya nunawa duniya cewa sarkin Daura ya gaji sarautarsa ne daga wurin kakaninsa. Haka kuma ya ce :

     Jagora : Daura taku ce ɗan Musa,

     Tun Kal’ana tun Lamarudu,

     Tun da Magajiya Daurama,

     Tun kuma Ummarun Bagadaza,

     Daurawa su ke Daurarsu,

     ‘Y/Amshi : Mai Daura Bashar ɗan Sanda. (Ɗa na shida).

     Jagora : Ina Mamman Waliyin Allah,

     Jikan waliyin Allah,

     Ya Allah jiƙan Ɗansammai,

     Da Mulka da Audu tsohon Sarki.

     Jagora : Baba jikan Ummarun Bagadaza,

     Da Mulka da Audu sai kuma Musa. (Ɗa na talatin da shida).

     ‘Y/Amshi : Kwana lafiya mai Daura. (Ɗa na sha shida).

     

    A waƙar Shehu Malami kuwa cewa ya yi:

    Jagora:          Bawan Allah mutumin kirki,

                         Alhaji Dattijo Ɗan Dattijo,

                         Malami jikan Mai Hubbare.

    Jagora: Mai ɗammarar yaƙi ɗan Bello. (Ɗa na ɗaya).

    Jagora: Na Aɗɗa kwan da shirin mulki ɗan Bello. (Ɗa na uku).

    Jagora: Bamamaki na Alhaji Macciɗo,

     Mai hana ƙarya na Sarkin Daura.

     Malami mai Allah ɗan Bello. (Ɗa na biyar).

    ‘Y/Amshi:     Malami Sarkin Sudan Shehu (Waƙar Shehu Malami Sarkin Sudan).

    Shehu ɗan Fodiyo (Mai Hubbare), sanannen mutum ne wanda ya sallama rayuwarsa wurin jaddada addinin Musulunci, don haka Shata ya zaɓi ya danganta Shehu Malami da shi a matsayin kakansa don ya wasa shi. Ya kuma danganta shi da Bello ɗan ɗan Shehun, da Sarkin musulmi Muhammadu Macciɗo, da kuma sarkin Daura.

    A waƙar Sarin Zazzau Shehu, Shata ya yi amfani da irin wannan dabarar, inda ya danganta Sarkin da wani kakansa, wanda shi ma ya mulki Zazzau a baya. Inda ya ce:

    Jagora: Gwauron giwa mai ban tsoro,

     Na Garba zakin Malam Sambo.

    ‘Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu. (Ɗa na bakwai).

    Jagora : Mani Shehu sadauki jikan Sambo.

    ‘Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

    Jagora : Shehu jikan Mujaddadi a wajen matarshi.

    ‘Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu (Ɗa na huɗu).

    A nan ya dangata shi ne da Shehu Usman Ɗanfodiyo, kasancewar sarkin na auren jikarsa.

    2.1.3 Zaɓen Kalmomi ta Fuskar Kyauta

    Haka kuma Shata kan zaɓo kalmominsa ta hanyar nuna yadda wanda yake wasawa kan bayar da kyauta domin, ya koɗa shi ya nunawa duniya cewa gwanin nasa ba marowaci ba ne. Misali:

    Jagora: Dattijo mai raba riguna ɗan Umar. (Ɗa na ashirin da shida).

    Jagora:          Mamman in tafiya ta kama,

                         Ko da da damina ko rani,

              Ko cikin dare ko rana,

              Yakan guzurin doki ɗan Ummaru,

                         Don ya rabas idan ya zauna.

    ‘Y/Amshi:     Mai Daura Bashar ɗan Sanda (Sarkin Daura Bashar Ɗan Musa).

    A wannan ɗan waƙan (Dr) Mamman Shata na koɗa ubangidan nasa ne, wanda yake nuna cewa duk halin da yake ciki shi mai kyauta ne, don haka ya zaɓo kalmominsa ta hanyar nuna yanayi da lokuta mabambanta waɗanda duk ya sami kansa a ciki ba sa hana shi yin kyauta, ko yana gida, kuma ko da tafiya ta kama shi cikin damina ko rani, haka kuma ko da rana ne ko kuma da dad dare kyauta yake yi, wanda yin irin hakan ko a cikin Sarakuna sai wanda Allah ya zaɓa.

    Sannan sai ya ƙara cewa:

    Jagora : Mai kyautar dawaki Mamman,

     Mai raba riguna ɗan Umar. (Ɗa na ashirin da bakwai).

    Jagora:          Mai kyautar mota ɗan Ummaru,

                         Mai raba riguna ɗan Sanda.

    ‘Y/Amshi:     Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

    Jagora:          Mai raba motoci Bashar ɗan Sanda x2,

                         Idan ya tashi yana alheri,

                         Har tausai nai nike ɗan Ummar x2,

                         Idan ya tashi yana raba kaya,

                         Tausai nai nike ɗan Ummar,

                         Baba idan ya tashi yana raba kurɗi,

                         Har tausan shi nike ɗan Ummar.

    ‘Y/Amshi:     Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

    A wannan ɗiyan waƙar kuwa, Shata ya zaɓi ya nuna ire-iren kyautar da gwanin nasa yake yi ne, wato, yakan raba motoci, da riguna, da kuɗi. Sannan yake ƙara nuna cewa saboda yadda gwarzon nasa yake raba kyautar, idan yana yi shi (Shata) har tausayin sa yake yi.

    A wata waƙar kuma ta Sarkin Daura Muhammadu Bashar, Shata cewa ya yi:

    Jagora:          Mai maka tambaya ɗan Sanda,

                         Komi nike so Mamman,

                         Tuntuni ka riga ka ba ni,

                         Kai ni ƙasar waje ɗan Ummaru,

                         Tun ban tad da tsohona ba. (Waƙar Sarkin Daura. Ɗa na talatin da ɗaya).

    Jagora : Ga ka kana da rai ɗan Ummaru,

              Ga ni ina da rai ɗan Ummaru

     Mamman ba ni kukan komai. (Ɗa na talatin da biyu).

    A nan Shata ya nuna cewa indai kyauta ce, to duk irin abin da yake buƙata, Sarkin Daura ya riga ya ba shi, ya rage kawai ya fitar da shi ƙasar waje ne don ya ƙara buɗe idanunsa tun kafin ya rasu. Sai ya nuna cewa idan Sarkin na da rai ba zai taɓa rasa wani abu ba, don zai bashi.

     2.1.4 Zaɓen Kalmomi ta Fuskar son Addini da iya Mulki da Haƙuri

    Har wa yau, Shata kan zaɓi kalmominsa ta hanyar nuna son addini da ibadar wanda yake wasawa. Misali inda ya ce:

    Jagora:          Ga ilmi kuma ya san Allah,

                         Malami Sarkin Sudan Shehu.

    ‘Y/Amshi:     Malami Sarkin Sudan Shehu (Waƙar Shehu Malami Sarkin Sudan).

    A nan shata ya bayyana gwanin nasa a matsayin mai ilmi kuma wanda ya san Allah, don haka sai ya ƙara cewa:

    Jagora:          Ga ilimi kuma ya san Allah,

                         Ba shi munafunci ɗan Bello,

                         Ba a yi mai baban Nana.

    ‘Y/Amshi:     Malami Sarkin Sudan Shehu. (Waƙar Shehu Malami, Ɗa na tara).

    Tabbas kamar yadda Shata ya bayyana, ga duk kan mutumin da yake da ilimin sanin Allah, to ba zai yadda da ya yi ko a yi masa munafunci ba, don haka Shata ya zaɓi ya bayyana gwarzon nasa da wanda ba ya munafunci kuma ba a yi masa.

    A wajen nuna iya mulki kuwa da sanin makamar aiki, ga waɗanda Shata ya waƙe, za a ga irin yadda mawaƙin ya zaɓo kalmominsa don fayyace gwanayen nasa, kamar yadda ya ce a waƙarsa ta Sarkin Sudan Shehu Malami :

    Jagora:          Ga ilimi da basirar aiki,

                         Kana ga asali gun mulki,

                         Malami jikan mai Hubbare.

    ‘Y/Amshi:     Malami Sarkin Sudan Shehu. (Waƙar Shehu Malami, Ɗa na sha huɗu).

     

    Shata ya zaɓo kalmomin da suke nuna ƙwarewa da gwanancewar gwanin nasa ne, a wajen mulki da tafiyar da jama’a, don haka ya bayyana Shehu Malamin a matsayin mai ilimi kuma mai basira wurin mulki, sannan don ya tabbatar da abin da ya faɗa, sai ya nuna cewa shi mulkin nasa ma na gado ne, kuma Bahaushe kan ce: “ɗan na gada ya fi ɗan na koya”.

    A wani ɗan waƙar kuma saboda iya mulkin Sarkin Daura da Shata ya nuna, sai ya zaɓi ya bayyana shi a matsayin dattijo mai tsayar da magana,wanda idan ya faɗi magana to fa babu abin da zai sa ya canza. Inda Ya ce:

    Jagora:          Ina Dattijo ɗan Dattijo,

                         Mai halin mutanen da can,

                         Bai da halin mutanen yanzu,

                         Domin su mutanen yanzu,

                         Kui magana da safe ku ƙulla,

                         Su rantse su ce ta zauna,

                         Yamma tai su ce sun fasa,

                         Su mai da mutum kamar ‘yan mata.

    ‘Y/Amshi:     Kwana lafiya mai Daura,

                         Jikan Audu Gwauron Giwa. (Ɗa na tara)

    Tabbas ko a zahiri haka abin yake, domin kuwa mutum ko da ba Shugaba ba ne, idan yana tsayar da magana, za ka ga mutane na matuƙar ƙaunarsa, kuma suna girmama shi, ballantana kuma ace Sarki ne.Wannan ya ƙara nuna mana a fili irin yadda Shata ya iya zaɓo kalmomin da zai bayyana wanda yake waƙewa don ya nuna ƙaye, don haka sai ya zabo kalmar dattijo ya laƙaba masa, sannan ya zaɓo kalmomin da suke nuna ɗabi’ar dattijon mutum, kamar tsayar da magana da cika alƙawari. Don kuma ya nuna halayen mutanen yanzu da yadda suke karya alƙawari ko da sun ɗauka, sai ya zaɓo kalmomin, ‘rantse’,da ‘ƙulla’,da ‘fasa’ da kuma ‘ ‘yan mata’ ya sarrafa su a waƙar.

    Don ya tabbar da iya mulkin nasa sai ya ƙara cewa :

     Jagora : Baba komi ya faɗi ta zauna,

     Idan garai da sauran kwana. (Ɗa na goma).

    Duk da cewa kalmomin da Shata ke amfani da su a cikin waƙoƙinsa mafi yawa sauƙaƙa ne, waɗanda jama’a ke amfani da su yau da kullum. hakan bai hana shi zama rumbun kalmomi ba, don kuwa idan aka duba yadda yake wasa da harshe wajen zaɓo kalmomi, abin sai dai son barka. Misali a waƙarsa ta Sarkin Zazzau Shehu yana cewa:

    Jagora:          Baba kai da garaje,

                         Ka ƙi garaje,

                         Na garba jikan Malam Sambo. (Ɗa na sha uku).

    A wannan ɗiyan waƙar Shata ya yi wasa da harshe wurin zaɓo kalmominsa, inda ya nuna cewa Sarki ba ya garaje kuma ba ya son a yi masa garaje cikin ƙawa.

    2.1.5 Zaɓen Kalmomi Masu Kambamawa

    Bayan zaɓen kalmomi da makaɗa kan yi amfani da su ta waɗannan fuskoki, har wa yau akwai kalmomi da makaɗan baka suke zaɓowa su jejjefa a cikin waƙoƙinsu, waɗanda kan kwarzanta da kambama wanda suke waƙewa, da nuna ƙasaitarsa, gami da nuna buwayarsa. Idan Sarki ne kalmomin kan nuna isa da ƙarfin mulki, da kuma iya tafiyar da jama’a. Ire iren waɗannan kalmomi sun haɗa da, ginshimi, da gwauron giwa, da bahagon gulbi, da bangon diniya, da gamji, da kutunkun ɓauna da dai sauransu. Alhaji Mamman Shata, makaɗi ne da kan zaɓo ire iren waɗannan kalmomi ya sarrafa su a cikin waƙoƙinsa, musamman waƙoƙin fada. Za a iya ganin misalan kalmomin kamar haka :

    A waƙar Sarkin Sudan Shehu Malami cewa ya yi:

     Jagora : Son da nake wa gwauron giwa,

     Malami mai Allah ɗan Bello.

    ‘Y/Amshi : Malami Sarkin Sudan Shehu.

    Jagora : Malami bango zaɓen Allah. (Ɗa na bakwai).

    ‘Y/Amshi : Malami Sarkin Sudan Shehu (Shata : Malami Sarkin Sudan).

    Idan aka duba za a ga yadda Shata ya yi amfani da kalmar ‘gwauron giwa’ a ɗan waƙar na farko, a ɗa na biyu kuma sai yay a zaɓo kalmar ‘bango’, don ya nuna yadda gwanin nasa yake a tsaye a harkar mulki.

    A waƙarsa ta Sarkin Zazzau Shehu, Shat aya zaɓo irin waɗannan kalmomi, ya sarrafa su don ya waƙe Sarkin. Misali :

    Jagora : Gwauron giwa mai ban tsoro,

     Na Garba jikan malam Sambo (Ɗa na bakwai).

    ‘Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

    Jagora : Mugun madambaci baban Jekada.

    ‘Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu. ( Ɗa na talatin da ɗaya).

    Jagora : Wandara maƙi sake ɗan Malam Mamman.

    ‘Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu. ( Ɗa na talatin).

    Jagora : Rimi adon gari baban Jekada.

    ‘Y/Amshi :Alhaji Sarkin Zazzau Shehu. (Ɗa na takwas).

    Idan aka duba kalmomin da aka ja wa layi, za a ga cewa kalmomi ne da ke nuna matuƙar ƙarfi na wanda makaɗin ke waƙewa.

    A waƙar Sarkin Daura kuwa, Shata cewa ya yi :

    Jagora: Faskara koyo bajimin Ummaru,

     Mamman maganin abu Allah.

     Giwa tafi da haƙo Bashar ɗan Sanda.

    ‘Y/Amshi : Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

    Jagora : Ƙi kabago Bashar ɗan Sanda.

    ‘Y/Amshi: Mai Daura Bashar ɗan Sanda. (Ɗa na ashirin da bakwai).

     

    Idan aka lura da irin yadda wannan fasihi ya bi hanyoyi daban-daban ya zaɓo kalmomi da sassaƙa su don ya gina waƙoƙinsa, ta hanyar nuna gwanancewa da kaifin basira, don ya isar da saƙonninsa, ya isa ya tabbatar mana da irin shaharar makaɗin wajen iya sarrafa kalmomin harshen Hausa, da kuma yawaitar rumbun kalmomin. Hakan nuni ne da kasancewarsa fasihi mai tarin basira da zalaƙar harshe, gami da iya yi wa harshen waƙoƙinsa kwalliya.

    2.2 Baƙin kalmomi

    Baƙin kalmomi su ne kalmomin da makaɗi ko mawaƙi kan iya amfani da su a cikin zancensa don ya isar da wani saƙo waɗanda ba na harshen da ake magana da shi ba ne. Harshen Hausa ya samu shigar wasu harsuna a cikinsa a kai tsaye ko kuma a kaikaice. Harshen Larabci da na Ingilishi suna daga cikin harsuna manya da suka yi kaka-gida a cikin harshen Hausa. Gusau, (2002, shf. 63).

    Makaɗa na aron kalmomi daga wasu harsunan su jefa a cikin waƙoƙinsu don su ƙara burge masu saurarensu, kuma su nuna cewa lallai fa ba wannan harshen da suke waƙa da shi kawai suka iya ba, a’a akwai wasu harsunan da ban.

    Ɗangambo, (1973), ya nuna cewa (Dr) Mamman Shata ba kasafai yakan yi amfani da baƙin kalmomi ba, sai dai abin da ba a rasa ba daga harshen Larabci ko Turanci, kuma ko da ya yi amfani da ararrun kalmomi daga wani harshen, za ka iske cewa kalmomin sun kusa zama na Hausa. Za a iya ganin misalan aron kalmomin kamar haka:

    2.2.1   Kalmomin Ingilishi

    Alhaji (Dr) Mamman Shata kan yi amfani da kalmomin Ingilishi a cikin waƙoƙinsa jefe-jefi, hakan na faruwa ne sau tari saboda irin mutumin da yake yi wa waƙar. Haka kuma kasancewarsa mai yin ma’amala da mutane da yawa ta kowane ɓangare, tun daga saraki da ‘yan kasuwa da kuma ‘yan boko, hakan kan yi tasiri a kansa. Za mu iya ganin misalai na yadda Shata ya yi aro dagar harshen Ingilishi kamar haka:

    A waƙarsa ta Sarkin Daura mai taken “Kwana Lafiya Mai Daura” cewa ya yi:

    Jagora:          Baba ɗan Kofur Haru da Haruna,

                         Da Amadu Malamin dabbobi.

    ’Y/Amshi : Kwana lafiya mai Daura, (Sarkin Daura Bashar, Ɗa na arba’in).

    Wannan kalma ta ‘Kofur’ wadda Shata ya yi amfani da ita a wannan ɗan waƙar, kalma ce ta Ingilishi (copral), mai nuna muƙamin ɗan Sanda mai igiya biyu, duk da dai a iya cewa kalmar ta Hausance.

    A wani wurin kuma cewa ya yi:

    Jagora:          Mahammadu zamani na Bature,

                         Ɗan Mamuda na Hakinci’

                         Ya yi zamani da siyasa,

                         Jikan Audu ya yi Minista,

                         Yanzu a zamanin Turawa,

                         Ɗan Mamuda ka zama Sarki.

    ‘Y/Amshi:     Kwana lafiya mai Daura,

                         Jikan Audu Gwauron Giwa. (Ɗa na ashirin da bakwai).

    A nan kalmar ‘Minista’ wadda Shata ya yi amfani da ita kalma ce ta Ingilishi mai nufin wani babban jami’in gwamnati.

    A waƙar Shehu malami kuwa, ya yi amfani ne da kalmar daba (Durba), wadda asalinta kalma ce ta Ingilishi, in da ya ce :

     Jagora : Daga kai kallo ya ƙare,

     Sokoto in an taron daba. (Ɗa na ashirin).

     

    2.2.2   Kalmomin Larabci

    Alhaji (Dr) Mamman Shata kan yi amfani da kalmomin Larabci a waƙoƙinsa, wanda yin hakan babu mamaki, ko don kasancewarsa Musulmi, kuma yawanci waɗanda ya yi wa waƙa Musulmai ne, duk da dai da yawan kalmomin da ya yi amfani da su, sun riga sun zama jiki a wurin Hausawa, watau a iya cewa sun Hausance.

    Misali:

    A waƙarsa ta Sarkin Sudan Shehu Malami inda ya ce:

    Jagora:          Ya Allah don Allah, Allah,

                         Don albarkar Manzon Allah.

    ‘Y/Amshi:     Amin don Rasulullahi. (Ɗa na sha shida).

    A wannnan ɗan waƙar, Shata ya yi amfani da kalmar ‘Allah’ da kuma ‘Rasulullahi’ (SAW), watau Ubangiji da kuma Manzo waɗanda duka daga Larabci suke, duk da dai suma sun Hausance.

    Haka nan kuma ya ce:

    Jagora:          Muhammadu yau Bashar ke mulki.

    ‘Y/Amshi:     Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

             (Waƙar Sarkin Daura Mahammadu Bashar)

    Shata ya yi amfani da kalmar ‘mulki’ a wannan ɗan waƙar, kuma kalma ce ta Larabci (Mulk) wadda ita ma za a iya cewa ta zama ta Hausa.

     Jagora: Muhammadu tunda Allah yai ka,

     Tabaraka yai ka sarkin birni.

     ‘Y/Amshi: Kwana lafiya mai Daura.(Ɗa na sha huɗu)

     

    2.3     Karin Harshe

    Harshen Hausa yana da kare-kare da dama, baya ga daidaitaccen kari wanda masana suka samar, wanda ake amfani da shi a hukumance da makarantu da kuma kafafen yaɗa labaru.

    Zulyadaini (2003), ya bayyana karin harshe da cewa shi ne yadda fasihan waƙa kan sarrafa Karin harshe a cikin waƙoƙinsu saboda dacewa da buƙatunsu na ƙawata ayyukansu na fasaha ko fita daga wata larura irin ta waƙa.

    Abba, da Zulyadaini (2000), sun kawo kare-karen harshen Hausa da suka haɗa da ‘Sakkwatanci’ da ‘Kananci’ da ‘Zazzaganci’ da Dauaranci’ da ‘Gudduranci’ da ‘Haɗejiyanci’ da sauransu.

    Shi kuma Gusau, (2003) cewa ya yi : Makaɗan baka suna aiwatar da waƙoƙi ne cikin yawancin kare -karen harshen Hausa da ake da su, tamkar Sakkwatanci da Gobiranci da Kananci da dauranci da Katsinanci da Zazzaganci da sauransu.        Amfani da karin harshe a cikin waƙa ya danganta ne daga nahiyar da makaɗi ya fito, amma duk da haka an ɗauka cewa karin harshen Sakkwatanci shi ne fitaccen Karin waƙar Hausa, ta yiwu don Sakkwatanci yana da isasshiyar balaga da rumbunan kalmomi masu ɓuɓɓuga da kuma sauƙin sarrafawa.

    Baya ga amfani da karin harshen ‘Sakkwatanci’ kamar yadda yawancin mawaƙan Hausa kan yi, a kusan dukkan waƙoƙinsa, Shata kan tsattsarma wasu karuruwan harshen Hausa, kamar ‘Katsinanci’ wanda shi ne karin harshen da ya girma da shi, kuma shi ne karin harshen mahaifinsa. Sai kuma ‘Kananci’, wanda bai rasa alaƙa da asalin mahaifiyarsa, wadda take Bakanuwa ce daga garin Tofa kamar yadda ya tabbatar da bakinsa a waƙar “Gagara Badau”, sannan ya ƙara tabbatar da hakan a waƙar Iro Sarkin Malamai.

    2.3.1 Karin Harshen Sakkwatanci

    Karin harshen Sakkwatanci, kari ne wanda mutanen yamma suke amfani da shi, waɗanda suka haɗa da Sokoto, da Zamfara, da Kabi da kuma Gobir. Za a iya ganin misalan karin Sakkwatanci kamar haka:

    A cikin waƙar Sarkin Daura ya yi amfani da Karin Sakkwatanci a inda ya ce :

     Jagora : Baba idan ya tashi yana raba kurɗi,

     Har tausai shi nike ɗan Umar.

     Y/Amshi: Mai Daura Bashar ɗan Sanda (Shata : Mai Daura Bashar ɗan Sanda).

    Haka kuma a cikin waƙar Sarkin Zazzau Shehu, nan ma za a iya ganin misalan karin Sakkwatanci kamar haka:

     Jagora: Shehun gusun da Sakkwato jikan Sambo. Sarkin Zazzau, Ɗa na sha takwas).

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : ɓauna sanuwar sake Usmanu na Zariya.

     Jagora : Naɗin sarautar zakin Zariya,

     Ashahura ya ban mamaki.

     Jagora : Zage zagi wa ab babbanku,

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu (Ɗa na sha tara).

     Idan aka duba kalmomin da aka ja wa layi a ɗiyoyin waƙoƙin za a ga cewa na Sakkwatanci ne. Kmar kurɗi daidaitacciyar kalmar shi ne (kuɗi), tausai (tausayi), gusun (kudu), sanuwa (saniya), Ashahura (Ashafura) da kuma wa ab (waye).

     

    2.3.2 Karin Harshen Katsinanci

    Har wa yau baya ga karin Sakkwatanci, Shata na amfani da karin harshen Katsinanci. Za a iya ganin misalai a waƙoƙinsa daban daban kamar haka :

    A waƙar Sarkin Zazzau cewa ya yi :

     Jagora : Tsaya bani shan ruwa in huje kohin.

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : Ranar karɓar sandar Sarki Asha hura ya ban mamaki.

     Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : Na ce mashi Asha hura Ala ma albarka.

     Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : A a Jakadiya kukan mi za ki.

     Aminu dai na nan bai kau ba.

     Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : Tsaya in Aminu ya kau an ba Shehu.

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : A ukkun ga wa za kui wa habaici.

     Mallawa dai dangi nai ne,

     Bare bari kuma dangi nai ne,

     Yo bare Katcinawa kakanninsa.

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu ( Alhaji Sarkin Zazzau Shehu Ɗa na arba’in da uku).

    A waƙar Sarkin Daura kuwa cewa ya yi:

     Jagora: Tahi baba ka gyaran tsohon birni,

     Inda Magajiya taz zauna.

     Y/Amshi : Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

     Jagoara : Cike hili na Daura baban Sa’i.

     Y/Amshi: Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

     Jagora : Mahammadu ba fasawa baban Baushi.

     Y/Amshi : Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

     ( Mai Daura Bashar ɗan Sanda, Ɗa na sha uku).

     A wata waƙar kuwa ta Sarkin Daura, ya yi amfani ne da Karin Katsinanci a wuraren da ya ce:

     Jagora: Ruwan zahi Bashar ɗan Sanda’

     Baka da gehe gwauron giwa

     ‘Y/Amshi: Kwana lafiya mai Daura,

     Jikan Audu gwauron giwa. (Ɗa na ashirin da bakwai).

     Jagora: Idan bacin Bashar ɗan Ummaru,

     Da na daina ɗan-ɗan-ɗan.

     Ga ka ina gani ɗan Ummaru,

     Mamman bani kukan komi. (Ɗa na ashirin da shida).

     

    Idan aka duba duk kan misalan da aka ja wa layi a ɗiyoyin waƙoƙin, za a ga cewa misalai ne na karin harshen Katsinanci. Misali kohi daidaitacciyar ita ce shi ce (kofi), hura (fura), mi (me), nai (nasa), yo (to), tahi (tafi), hili (fili), zahi (zafi), gehe (gefe), bacin (bayan),

     

    2.3.4 Karin Harshen Kananci

    Karin harshen Kananci, na daga cikin kare-karen da Mamman Shata kan yi amfani da shi a cikin waƙoƙinsa. Za a iya ganin misalai kamar haka:

     Jagora: Dattijo ruwan dafi ɗan Sanda,

     Da sannu ya kas kutukun ɓauna.

     Y/Amshi: Kwana lafiya mai Daura,

     Jikan Audu gwauron giwa.

     Jagora : Baba in kwan in gai da Sarki Buzu.

     Y/Amshi Kwana lafiya mai Daura

     Jikan Audu gwauron giwa. ( Ɗa na talatin da huɗu).

     Jagora : Baba kai ni ƙasar wajen ɗan Ummaru,

     Tun ban tad da tsoho na ba.

     Y/Amshi: Kwana lafiya mai Daura,

     Jikan Audu gwauron giwa ( Kwana lafiya mai Daura. Ɗa na talatin da uku).

    A waƙar Sarkin Daura kuwa cewa ya yi:

     Jagora: Mai guzurin doki ɗan Ummaru,

     Don ya rabas idan ya zauna.

     Y/Amshi: Mai Daura Bashar ɗan Sanda.

    A waƙar Sarkin Zazzau Shehu kuwa ya yi amfani ne da Karin harshen Kananci, a inda yake cewa :

     Jagora: Ran ba da sandar Sarkin Zazzau,

     Asha hura ya ban mamaki. (Ɗa na talatin da huɗu)

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora: Haji Asha hura Allah ma sakayya. (Ɗa na talatin da shida)

     Y/Amshi: Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     Jagora : Jakadiya zauna bari kuka,

     Aminu dai na nan bai kau ba. (Ɗa na arbain da tara)

     ‘Y/Amshi : Alhaji Sarkin Zazzau Shehu.

     (Shata : Alhaji Sarkin Zazzu Shehu).

    Kalmomin da aka ja wa layi na karin harshen Kananci ne, misali kalmar kwan, daidaitacciyar ta ita ce (kwana), rabas (rabar), yakas (ya kashe), gai (gaishe), tad da (tarar da), rabas (rabar), ran (ranar), haji (Alhaji).

    3.0 Kammalawa

    Ƙoƙarin wannan maƙala na ɗora salon sarrafa harshen Shata a bisa ma’aunin muhimman tubalan salo, don ya gano ire iren hikimomi da dabaru da makaɗin ya sarrafa. Binciken ya tabbatar da cikar fasaha da zalaƙar harshen fasihin, inda ya tabbatar da cewa Shata mutum ne fasihi wanda yakan gina harshen waƙarsa da salo mai burgewa kuma mai armashi. Haka kuma binciken ya tabbatar da cewa Shata makaɗi ne da ya gwanance wajen iya zaɓen kalmomin da yakan sarrafa. Maƙalar ta tabbatar da cewa Alhaji Mamman Shata na zaɓo kalmomi ya kuma sarrafa su ta hanyoyi da dabaru iri daban-daban. Sannan yakan aro kalmomi ya kuma sarrafa su daga wasu harsunan kamar Ingilishi da kuma Larabci. Haka kuma Mamman Shata kan yi amfani da Karin harshe daban daban kamar na Sakkwatanci da Katsinanci da kuma Kananci.

    MANAZARTA

    A tuntuɓi mai takarda domin samun manazarta.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.