Gudumawar Zambo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Ga Bunƙasa Dimokuraɗiyya A Nijeriya

     Takardar Da Aka Gabatar A Taron Ƙarawa Juna Sani A Tsangayar Nazarin Harsuna Ƙwalejin Ilimi Ta Maru Ranar 15, Ga Watan Mayu, 2013

    Gudumawar Zambo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Ga Bunƙasa Dimokuraɗiyya A Nijeriya

    ALIYU RABI’U ƊANGULBI

    Email: aliyurabiu83@yahoo.com

    PHONE NO. 07032567689, 07088233390

    TSAKURE

    Harshen Hausa na ɗaya daga cikin Harsunan duniya da ake amfani da shi domin a isar da saƙo ga al’umma a harkokin yau da kullum. Adabi na daga cikin nau’o’in harshen da ake ƙoƙarin bayyana al’adu da dabi’un kowace al’umma. Dangane da haka ne yasa al’umma ke dogara da harshe wajen bayyana hikimominta, da fasahar ta da ɗabi’unta a cikin waƙoƙin baka da rubutattu. Bisa ga wannan tunani na al’umma ya sa wannan takarda za ta tattauna a kan rawar da zambo yake takawa a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa na siyasa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya a Nijeriya.

    GABATARWA

    Kowace al’umma ta duniya tana bin tsarin al’adu da ɗabi’unta da ke wajabta mata samun ƙarɓuwa a idanun sauran al’ummomi na duniya. Al’ummar Hausawa mutane ne da ke tafiyar da rayuwarsu kamar yadda al’adunsu suka tanadar musu.

    Dangambo (2008), ya bayyana adabi da cewa, walimace ko liyafa da mutane ke aiwatarwa a lokacin jahiliyar Larabawa. Amma bayan shigowar addinin Musulunci sai ma’anar adabi ta sauya zuwa ga ma’anar dukkan wasu hanyoyi na gyaran halaye, ko kuma abubuwa masu kyau, kamar ladabin cin abinci da ladabin zance da sauransu, da tafiya ta yi tafiya sai kalmar adabi ta ƙara faɗaɗa ta ƙunshi wasu dangogin ilimi kamar labarai da tarihi da waƙoƙin baka da harshe da sauransu.

    Calɓin (1990), fasahar labarai da waƙoƙi da wasannin ƙwaiƙwayo da baka ko a rubuce shi ne adabi, da waɗannan bayanai na ma’anar kalmar adabi da masana suka kawo ya sa na fahimci cewa kalmar adabi wata hanya ce ta rayuwar al’umma da ta shafi al’adunsu da ɗabi’unsu da hikimominsu a wajen aiwatar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Fahimtar yadda kowace al’umma ke gudanar da rayuwarta ba zai yi tasiri ba face ta dogara kacokam a kan waɗansu nau’o’in al’adun gargajiya kamar tarbiyar girmama manya da abinci da sutura da sauransu.

    Dangane da abubuwan da aka ambata a sama yasa wannan takarda za ta yi tsokaci a kan wani muhimmin nau’i na adabi da ya shafi rubutattun waƙoƙin Hausa. Wannan nau’i na adabi shi ne yin amfani da zambo a cikin waƙoƙi da marubuta ke yi musamman a cikin waƙoƙin siyasa.

     

    MA’ANAR ZAMBO

    Zambo kalma ce wadda ake amfani da ita a cikin waƙoƙi ko a cikin maganganun yau da kullum domin a muzanta wani mutum ko wasu gungun mutane kai tsaye. Ana amfani da zambo domin a nuna ɓacin rai ko damuwa game da wata matsala da ke gudana a tsakanin mai yin zambo da wanda ake yi wa zambon (Dangulbi 1996).

    Gusau (2008) da Yahya (1997), dukkansu sun bayyana zambo da cewa magana ce wadda ake furtawa a matsayin kishiyar yabo. Akan siffanta mutum da wasu siffofi munana waɗanda za su wulaƙanta shi ko su jawo masa rashin martaba a idon mutane, tare da kau da kai daga wannan mutum, wala’allah yana da waɗannan siffofi ko ba shi da su.

    Calɓin (1990), ya bayyana zambo da cewa “Magana ce wadda aka yi wa mutum don ƙona masa rai”. Shi kuwa Dangambo (1984), cewa ya yi “Zambo zagi ne na kai – tsaye, idan an kwatanta shi da habaici”. Ana siffanta mutum da ake nufi da duk siffofinsa, halayensa, ɗabi’unsa, danginsa, iyalinsa da dai duk wani abu da ya shafe shi wanda zai taimaka a gane da shi ake. Saboda haka bisa ga bayanin masana ya nuna mana cewa, zambo wani zance ne na ɓatanci zuwa ga wani mutum ko wasu ƙungiyoyin mutane da ake faɗa kai tsaye domin a muzgunawa wanda ake yi wa. (Dangulbi 2003).

    A takaice zambo wani zance ne da ake amfani da shi domin a muzanta wani ko zagin sa kai tsaye ta hanyar faɗar wasu siffofinsa ko halayensa da aka san shi da su, mata da ‘yan kasuwa da sauran jama’a suna amfani da zambo a cikin mu’amullarsu ta yau da kullum don su muzanta kishiyoyinsu ko abokan hulɗarsu ko abokan sana’arsu. Har wa yau mawaƙa kan yi amfani da zambo domin su ƙayatar da masu sauraro ko karatu a cikin waƙoƙinsu (Ɗangulbi 2003). Mawaƙan baka da marubuta waƙoƙi su ne suka fi yin amrani da zambo a cikin waƙoƙinsu na sarauta ko na jaruntaka ko na siyasa da sauransu. Babbar gaba, ko adawa (kiyayya) it ace ke haddasa zambo. Misali zambo a tsakanin mawaƙa da ‘ya’yan sarakuna da kuma mawaƙa da ‘yan siyasa. Misali Sa’idu Faru a cikin waƙarsa ta Tudun Falale yana cewa:

    Sa’idu Faru:                Dogon Sarki  shina da ban shawa,

                                        Randa an ka zo taro yayi kyau da riguna,

    Amshi:             duk wanda ag-gajere a ajeshi gun rabon dawo,

                                        Ya kai ma wanga dunƙule, ya kai ma wanga dunƙule,

                                        In wurin da mata ciki har tuman gada ya kai

    Sa’idu/Amshi: Ɗan karuwa duk ɓaci kaj jiya da kai nike

     

     

    MAWAƘAN SIYASA

    Mawaƙan siyasa wasu mutane ne da suke aiwatar da waƙoƙinsu musamman ga jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa. Mulkin siyasa, wani tsarin mulki ne da ke kawo gwamnati kusa da jama’a da kuma bai wa jama’a damar faɗar albarkatun bakinsu a cikin harkokin mulkin ƙasa (Dangulbi 2003).

    Akasarin mawaƙan siyasa suna bayyanar da ra’ayinsu ga jam’iyyun da suke sha’awa ko ra’ayi, ta haka ne suke tsayawa su fahimci manufofin jam’iyyunsu sannan su rera masu waƙa da nufin tallata su a idon jama’a domin su sami karɓuwa.

    Tun lokacin siyasar jamhuriyya ta farko aka sami marubuta waƙoƙin siyasa da dama suna amfani da basirar da Allah (SWA) ya ba su, suna rubuta waƙoƙi domin su faɗakar da al’umma akan muhimmancin mulkin farar hulla da zaɓen shugabanni na gari, mawaƙan da suka yi fice a fagen rubutattun waƙoƙin siyasa sun haɗa da Malam Sa’adu Zungur, da Malam Lawal Mai Turare da Malam Mudi Sipikin da Malam Gambo Hawaja, da Malam Akilu Aliyu da sauransu (Ɗangulbi 2003).

                Har wa yau akwai Malam Lawali Isah Bunguɗu, da Malam Aminu Kano, da Aminu Ibrahim Ɗandago Kano, da Shu’aibu yar Medi ƙaraye, da Malam Muhammadu Ɗan Musa Kano da sauransu, waɗannan mawaƙa kaɗan ne daga cikin mawaƙan siyasa da muke da su a Arewacin Nijeriya.

     

    RAWAR DA ZAMBO KE TAKAWA WAJEN BUNƘASA DIMOKURAƊIYYA

    Yin amfani da zambo a cikin waƙoƙin siyasa tamkar gishiri ne a cikin miya, zambo yana daga cikin manyan jigogin waƙoƙin siyasa da ake amfani da shi domin a tallata jam’iyya da kuma muzanta ‘yan takara da sauran jam’iyyun adawa. Idan waƙa bata da zambo a cikinta to takan zama tamkar maganar hirar yau da kullum ce, watau bata da armashi. (Ɗangulbi 2003). Marubuta waƙoƙi sukan yi amfani da zambo a cikin waƙoƙinsu domin su ƙosar da nishaɗi ga masu sauraro ko masu karatun waƙoƙin nasu.

    Abu na gaba dangane da amfani da zambi cikin waƙoƙinsu shi ne domin su ƙawata waƙoƙinsu, ko da yake mafi yawan zambo da mawaƙa ke yi a cikin waƙoƙinsu karya ce maras tushe da kuma ƙazafin ɓatanci. Mutane na cewa, “idan kana son ka san asalinka to ka shiga siyasa yanzu ka san daga inda ka fito, haka wannan Magana take, domin duk wani mugun ƙazafi ko lafazi maras kyau da ka iya ɓata sunan ɗan siyasa ka ji shi daga bakin mawaƙan siyasa.

    A cikin irin wannan zambo ne da suke ƙirƙirawa na ƙarya mawaƙan kan dubi siffar ɗan adawa ko ɗanbi’unsa ko halayensa sai su dangata shi da siffar wata halitta ta dabba ko kwaro, ko tsuntsu dan su muzanta shi a idon mutane, idan mawaƙa suka jefa zambo ga ‘yan adawa to zai ƙara wa ‘ya’yan jam’iyyar da yake yiwa waƙa ƙarfin zuciyar riƙe aƙidarsu don ɗaukaka jam’iyyarsu.

    Da waɗannan dalilai ne mawaƙa ke ƙara tabbatar wa ‘yan siyasa cewa zambo wani babban makami ne da ake amfani da shi a cikin waƙoƙi wajen bunƙasa jam’iyyun siyasa daban-daban da kuma ɗaukaka darajar ‘yan takara.

     

    ZAMBO DON TALLATA JAM’IYYU  

    Mawaƙa kan riƙa yin amfani da zambo domin su tallata jam’iyyunsu ta hanyar bayyana manufofinsu ga jama’a akan yin wa jam’iyyar adawa zambo dangane da manufofin da ta tsara na samar da abubuwan more rayuwa, ilimi, kiyon lafiya, tsaro, tattalin arziƙi da sauransu, idan jam’iyya ta kasa aiwatar da waɗannan manufofi da ta tsara, misali da yake tallata jam’iyyarsa ta U.N.C.P mai take “Matashiya da ke muka kamfe, mawaƙin wannan jam’iyya Alh. Garba Gwandu yana cewa:

    Patin duk da manyanshi ba su da hanƙuri

    Ba su kasha wuta sai su hazaguɗa tunzuri

    Kar ka shige shi Malam Bala ka tsaya wuri

    Ɗau Patin da kwana kaɗanna da hamzari

    Ƙasar ga ta zo ta bunƙasa, zo ka bi garkuwa

    A cikin wannan baiti mawaƙin ya yi wa patinas waƙa ne don ya tallata irin kwarjinin da ke akwai ga patin UNCP wanda duk masu ra’ayin sa mutane ne dattijai masu haƙuri, kuma masu sasantawa tsakanin ‘ya’yan jam’iyya idan wata hatsaniya ta taso, hakuri da dattako wasu ɗabi’u ne da ake son duk mai ɓuƙatar ya zama shugaba, to dole ne ya kasance ya mallaki irin waɗannan halaye. Dangane da haka ne Garba Gwandu ya yi wa wasu ‘ya’yan wata jam’iyya zambo dangane da halayensu na rashin haƙuri da rashin dattako da kuma ɗabi’ar hazguɗa tashin hankali. Kamar yadda ya faɗa cewa masu irin waɗannan ɗabi’u ba su kasha wuta, wato basu hana hargitsi, sai dai su ƙara hazguɗa shi to kasancewar wannan jam’iyya ta ke da irin waɗannan mutane bai dace a shigeta ba ga duk mai son ƙasa ta ci gaba, sai dai su zo su shiga jam’iyyar UNCP wadda ita ce jam’iyya ta mutanen ƙwarai, kamar yanda Garba Gwandu ya faɗa.

    Shi kuma Muhammadu Suleiman Ɗunɗaye, a cikin waƙarsa ta jam’iyyar NPN a jamhuriya ta biyu mai taken “Yan Santsi kun zama kaya”, mawaƙin ya yi wa PRP zambo inda yake kiran jama’a da su guje wa shigarta domin ‘ya’yan ta sun cika haufi (tsoro) da alfahari cewa su sukafi sauran jam’iyyu, dangane da haka ne mawaƙin ya ke cewa:

    “Ku guje wa ‘yan PRP

    Jam’iyyar ta cika haufi

    Da yawan cewa su sun fi

    Kowa sun mai sai wofi

    Bayan kuma sun gigita

    Har wa yau Muhammadu Sulaiman ya ƙara da cewa:

    PRP bata amana,

    ba alheri mun auna,

    kuma ba ƙwazo mun raina,

    sharri, ƙarya da hiyana,

    Ta firgita duk yayanta,

     

    Daga yau mun koma hanya,

    Ta aminci ba jayayya,

    Su Akinloye, kun e manya

    Haƙƙin duka yan Nijeriya

    Ku ne rainon ‘ya’yanta.

     

    Kada kui halin PRP

    Ku haɗe kai don ku kunfi

    Kai ni bana PRP

    Ban son mai son PRP

    A sani daga yau na barta

    A waɗannan baitoci da ke sama, marubucin waƙar ya yi amfani da kalmomin da suka tabbata kalmomin zambo ne, watau “haufi, da wofi da kuma gigita”, haka kuma kalmomi irin su rashin amana, da ragganci, da danne haƙƙin al’umma da ji da kai, duka waɗannan kalmomi siffofi ne da ke bayyana halin da ‘ya‘yan jam’iyyar PRP suke ciki na fargaba da shashanci da kuma rashin natsuwa da sauransu. Da ma an ce zambo yana nufin faɗar magana kai tsaye ga wani dangane da halayensa don a muzanta shi. Saboda haka Malamin yake kira ga mutane su guje wa shiga jam’iyyar PRP, saboda munanan ɗabi’u da ya ambata akan ‘ya’yan jam’iyyar PRP. Wannan ya nuna cewa duk mai tsoro ko mutumin banza ko gigitacce watau maras natsuwa ba zai iya mulkin mutane ba, idan aka zaɓe shi ba zai kawo wa jam’iyyarsa ci gaba ba balle ƙasa sa ta samu bunƙasa.

     

    ZAMBO DON MUZANTA ƊAN TAKARA

    Mafi yawa daga cikin zambace-zambacen da mawaƙa kan yi wa ‘ya’yan jam’iyya da kuma ‘yan takara ƙarya ce maras tushe domin suna yi masu ƙazafi ne don su muzanta su a idon mutane, mawaƙan siyasa kan kalli siffofin ‘yan  takara da kuma halayensu da ɗabi’unsu sai su yi amfani da wannan dama su riƙa jifar su da maganganu na ɓatanci su danganta su da wata halitta ta dabba ko tsuntsu ko ta wani ƙwaro, da zaran sun yi haka sai jama’a nan take su yanke hukunci cewa ga wanda ake yi wa zambo saboda faɗin wasu suffofi da aka san wannan mutum da su, su ce shi ake nufi da wannan zambo. Misali a cikin waƙarsa ta PDP Malam Shu’aibu ‘yar Medi Ƙaraye yana zagin wasu ‘yan takara na wata jam’iyyar adawa inda yake ambatonsu da siffofinsu, musamman wani ɗan takara wanda ya kasance gajere ne da wannan siffar tasa sai mawaƙin ya dangantashi da wata halitta watau kunkunu kowa yasan kunkunu halittace wacce take dunƙule a cikin wani ƙoƙo a duk lokacin da taga wani tashin hankale ko abinda bata aminta da shi ba sai ta maƙe ta maid a kanta cikin ƙoƙon nan dangane da haka yasa mawaƙin ya yi wa wannan ɗan takara zambo in da yake cewa:

    Na ɗau kunkuru zan yanka wuya nai ya ƙi fiddawa,

    Har nai shawarar zan jefar sai yara suke cewa,

    Ɗau gaushen wuta liƙa wa takashin ja’iri wawa,

    Sai ya fidda kai watsa masa reza kar ya ɓata ƙasata

     

    Wannan baiti da marubucin ya kawo ya bayyana irin siffar da wannan ɗan takarar wata jam’iyya yake da ita, ya nuna wa jama’a cewa bayan zamansa gajeren mutum sannan kuma ga shi ja’iri (shashaha) kuma wawan, saboda haka duk mai irin waɗannan siffofi da halaye yana da wuya a zaɓe shi ya shugabanci mutane. Don haka idan ana son a fitar da shi cikin sahun ‘yan takara dole sai ta hanyar yi masa zambo in da aka muzanta shi har mutane suka gane halayensa suka ƙaurace masa domin bai cancanta ya zamo shugaba ba, har wa yau mawaƙin bai tsaya nan ba sai kuma ya koma zagi wani ɗan takara na wata jam’iyyar inda ya ke cewa:

    Tsutsa sha jinni ki shige turɓaya kar su gane ki

    Ni na hau gadon ƙarfe da katifa bani yau baki

    Wai ‘yan shafa labari shuni su za su yaɗa ki

    Sai mun je akwati mu ɗau inuwar lema mazanmu da mata

     

    A nan mawaƙin ya siffanta wannan ɗan takara da tsutsar azure inda yara ko almajirai ke kwana a wasu shekaru da suka wuce, da ba’asan dabarar yiwa ɗaki ko azure daɓe ko shafen siminti ba, ita tsutsa takan shiga cikin yatsun mutane ko yara da ke kwana a azure a lokacin da suke barci ta riƙa tsotson jininsu, to shi wannan ɗantakara yana da ɗabi’ar cin amana idan an ba shi kuɗi ko wata dukiya ya raba wa talakkawa, kuma yakan riƙa biyar jama’a yana neman su ba shi taimako maikamon shi ya taimaka wa jama’a, saboda haka shi mawaƙin yake cewa ba zai koma kwana a ƙasa ba, balle tsutsa ta sha jininshi, ma’ana ba zai sake bin wannan ɗan takara ba sai dai ya koma ga wani ɗan takara na jam’iyyar da yake yiwa waƙa a halin yanzu, saboda akwai daula shi yasa ya kwatanta wancen ɗan takara da tsutsar zaure saboda yanzu ya samu gadon ƙarfe da katifa da zai riƙa kwantawa, ma’ana ya samu Jam’iyyar PDP wacce zata tallafa mashi ya samu wadata, a nan manufarsa itace ba zai koma zaben tsutsa ba, don haka masu kokarin tallata wannan ɗan takara ƙaryace suke yi bazasu iya tallatashi ba har ya samu karɓuwa ga jama’a saboda mutane sun fahimci cewa ba mai taimakon jama’a bane har ma in ya samu nasu ba zai bar shi ba. Shi kuwa Muhammad Sulaiman Ɗunɗaye yana cewa a cikin waƙarsa ta NPN inda yake yi wa ‘yan takara na jama’iyyar PRP zambo cewa:

    Dama ƙarshen su ɓaleri

    Jawo fitina asharari,

    Domin bakinsa da sheri,

    Tusatai mugun wari,

    Kuma duk jama’a sun ji ta

                           

                            Shi jatau shashasha ne

                            Da halinsa da gwaggo guda ne

                            Da biri ja duk daidai ne

                            Aiki nasa ma ɓarna ne

                                        Ga raini ga son mita

     

    Shi kuwa Aminu Ɗandago Kano yana yi wa wani ɗantakara zambo wanda ya kasa cika alkawali da ya ɗauka bayan day a sami biyan buƙata a wancen zaɓe, mawaƙin ya siffanta shi da mage domin ya muzanta shi a idon jama’a cewa duk alkawarin da aka yi da shi ya saɓa. Kamar yanda mage ke alkawalin bata koma kama ɓera ko kaji, amma kuma ta saɓa, ga abin da yake cewa ta ANPP:

    Baƙar mage abin tsiyarki yassa na yada ke,

    Dirakun da mukai mukai gini da suu ke kika tunɓuke,

    San da ta gane gininmu zai faɗi ta tsallake

    Babu mutunci a yau tsakaninmu da ni da ke

    Baƙar mage baƙar tsiyarki na gaji tsinanniya

    Har wa yau akwai Muhammadu Ɗan Musa Kano wanda ya yi wa APP waƙa yana cewa:

    Jan biri na gane nufinka

    Da ce nake mai son jama’a ne

    Ashe kiranka kiran jama’a ne

    Ja irin aka ba ka minista

    Sai ka karɓe ka mance na baya

    Wannan baiti yana siffanta wani minista ne da halittar biri shi dai Malamin yana son ya nuna wa jama’a cewa wani ɗantakarar wata jam’iyya da ya taɓa riƙa muƙamin minista bai taimaka wa kowa ba, a yanzu kuma shi wannan wannan minista ya sake fitowa takarar kujerar gwamna, amma saboda ɓarnar dukiya da almubazzaranci da halin ko oho da ya nuna wancen lokaci sai mawaƙin ya yi masa zambo inda ya siffanta shi da jan biri yana nunawa jama’a kada su sake zaɓen shi domin zaran a ka zaɓe shi, to zai manta da jama’a kamar yadda ya yi a loakcin da yake minista, wannan dalili ne yasa mawaƙin ya siffanta wannan ɗantakara da jan biri, wanda idan jan biri ya shiga gona yakan yi kaca-kaca da amfanin gona, saboda haka mawaƙin yana nuna wa jama’a illar zaɓen wannan ɗantakara a kujerar gwamna.

     

     

    ZAMBO TA FUSKAR ZAƁE

    Mawaƙan Hausa musamman marubuta waƙokin siyasa sukan ɗauki alƙalami su bayyana ra’ayinsu dangane da zaɓen shugabanni na gari masu gaskiya da riƙon amana. Idan aka dubi yadda siyasar ƙasar nan take gudana babu shakka akwai buƙatar samun shugabanni masu adalci da gaskiya da riƙon amana domin bunƙasa ƙasa ta fuskanci da dama, misali fannin ilimi, tsaro, kiyon lafiya, samar da muhalli da bunƙasa tattalin arziki da aikin gona da sauransu, duk waɗannan abubuwa ba za su samu ba sai da samun shugabnni na gari waɗanda ke da kishin ƙasa, ba masu yi wa dukiyar ƙasa wasoso ba, watau ‘yan mu arzuta kammu da ‘ya‘yanmu sauran jama’a kowa yayi takansa. Dangane da haka ne ya sa mawaƙan siyasa da dama suka duƙufa wajen wayarwa mutane da kawunansu game da yiwa kansu kiyamullaili su zaɓi mutanen da suka cancanta don ƙasa ta cigaba.

    Mawaƙa daban-daban sun yi wa ‘yan takara zambo dangane da ɗabi’u da halayen kowanensu wanda mawaƙan ke ƙoƙarin siffanta ‘yan takarar da dabbobi da tsuntsaye daban-daban domin mutane su fahimce su don ka da su yi zaɓen tumun dare. Malam Umar kwaren gamba, Sakkwato yana ɗaya daga cikin mawaƙan da suka taka rawa wajen yin amfani da zambo domin ya wayar wa jama’a kai dangane da zaɓen yan takara masu ɗabi’u na gari ba kamar masu ɗabi’u da halaye irin na dabbobi da sauran halittu ba. Daga cikin siffofin waɗannan halittu akwai masu kwaɗayi da ƙwace da fashi da makami da fisge da yaudara da almubazzaranci da sauransu. Misali mawaƙin siyasar yana cewa a cikin waƙarsa ta Muhimmanin mai da mulkin ga hannun farar hula:

    Kun ga ‘yan kwaɗan su yi mulki su cuci danginsu

    Irinsu ɗan kuregen dutse kar ku tsai da shi

    Masu tattalin sui mulki don ƙashin kansu

    Nufin sukai su hau mulki don cimma gurinsu,

    Irinsu karku tsai da su ga mulkin farar hulla

     

    Wannan zambo ya shafi wasu gungun rukunin mutane masu sha’awar tsayawa takara don a zaɓe su, su shugabanci jama’a, amma suna da wasu ɗabi’u daban-daban da mawakin yake son jama’a su fahimce su.

    Saboda haka sai mawaƙin a cikin waƙarsa ta mahimmancin mai da mulki ga hannun farar hulla, ya kawo sunayen daban-daba da tsuntsaye waɗanda aka sansu da irin waɗancen dabi’u da ya ambata a sama. Misali:

    Umar K/Gamba yana cewa:

    Kar ku tsaida gohon jaki mai baƙin baki

    Mai tuma shi halbi mutane shi take yan tsaki

    Wanda yassake yaz zaɓeshi shi kayin zaki,

    Irin su kar ku tsaishe shi ku koreshi nan take,

    Kar shi zo shi ɓata mana mulkin farar hula

               

    Har wayau Malamin ya ƙara da cewa:

    Wanda kun ka gane cewa ɓarawo ne

    Ba’a kaushi banki dan ya saba yin sane,

    Son shi kai shi ɗauka ko ga mai tsaro zaune,

    Wanda kun ka gane cewa wanga mugu ne,

    Kar ku bashi mulki ko yasa farar hula.

     

    Malamin ya danganta su da wasu mutane masu ɗabi’u kama da na waɗannan dabbobi da tsuntsaye inda ya danganta su da wasu mutane masu ɗabi’u kama da na waɗannan dabbobi da tsuntsaye. Dabbobi da tsuntsayen da ya kawo misalinsu babu shakka da zaran mutum ya ji sunayensu ya san halayen da aka ambace su da su sun cancancesu. Misali a cikin waƙarsa daga baiti na 17-30 Malamin ya jera sunayen dabbobi, da tsuntsaye kamar su kuregen dutse, gohon jakim da ɓarawo, da jaɓa, da zarɓe da bushiya da dila mashanciya, da zirnaƙo da sauransu domin ya danganta ‘yan takara da yake yi wa zambo da waɗannan halittu cewa ka da a zaɓe su a lokacin zaɓe. Babu shakka zaɓen irin waɗannan mutane ba zai kawo wa ƙasar nan ci gaba ba sai dai ya hassasa fitintinu da mulkin zalunci wanda talakka ba ya da ‘yancin walwala balle ya samu abinda zai more rayuwarsa. Daga ƙarshe Malamin ya jaddada wa mutane cewa su karɓi shawara da ya basu domin a sami nasarar zaɓen shugabanni na gari masu adalci da riƙon amana, domin a bunkasa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Yana cewa:

    Waga shawara ‘yan jama’iyyu ku duba ta,

    In abin ku ɗaukat ku riƙe kwa ci ribat ta,

    In mutum shina son hairi cikin ƙasa ga ta,

    Shawarag ga wadda na kawo ba shi soke ta,

    Sai fa wanda bai son ai mulkin farar hulla

     

    Babu shakka zambo ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa siyasa a Nijeriya. Saboda haka an samu al’umma da dama sun fahimci abinda muhimmancin zaɓen shugabanni na gari wanda shi ke kawo bunƙasar tattalin arziki da dimokuraɗiyya mai ɗorewa. Haka kuma zambo ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da, da kuma tantance jam’iyyu masu manufofi na taimaka wa al’umma musamman a halin da ake ciki da siyasar ƙabilanci da banbancin addini suka yi tasirin gaske a zukatan al’ummar Nijeriya.    

     


    KAMMALAWA

    Idan aka yi maganar mulkin farar hulla ko yaushe jama’a sukan tattara hankalinsu wuri ɗaya, su natsu su yi nazarin irin abin da ka iya bayowa baya, wajen tafiyar da tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da zaman lafiya da damar walwala, domin idan aka ce siyasa ana zaton tsarin mulki ne wanda ke bai wa kowa dama ya faɗi albarkacin bakinsa, watau mulki ne wanda yake kawowa gwamnati kusa ga jama’a kowa ya amfana da romon mulkin dimokuraɗiyya.

    Da yake ‘yan siyasa mutane ne masu alƙawali da tayarwa ya sa marubuta waƙoƙin da dama sukan yi amfani da barar da Allah (SWT) ya yi masu su kalli irin illar da rashin cika alkawali ke kawowa, sai su tsakulo wasu hanyoyin da za su wayar wa jama’a da kawunansu domin a sami masalaha ta yadda jama’a zasu a amfana da mulkin farar hulla. Bisa ga wannan manufa sai mawaƙan su yi ƙoƙarin yin amfani da zambo a cikin waƙoƙinsu domin su kakkaɓe hannun duk wani mutum ko wani ɗan takara na wata jam’iyya adawa da ba a aminta da cancantarshi ba wajen tsayawa takarar zaɓe, wannan ya sa Malam Umaru Kwaren Gamba ɗaya da ga cikin marubuta waƙokin siyasa yake kira ga yan ƙasa da su zaɓi mutanen da suka cancanta a zaɓesu su shugabanci jama’a koda kuwa ‘yan takarar sun fito wuri guda ne, yana cewa:

    Ku zaɓi ɗan ƙwarai mai kirki guda ku tsai da shi

    Wanda ya fito don su ƙara sai ku mai da shi,

    Gamu da bashi amsar cewa ɗan gida ne shi,

    Yanzu in guda daga cikinku an ka kada shi.

    Za mu samu cikas jam’iyyarmu ya hulla

    Watau a takaice dai ana buƙatar a zaɓi shugabanni na gari wanda yin haka shi ɗai kawo ci gaba da bunƙasar mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

    MANAZARTA

    Tuntuɓi mai takarda.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.