Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Habaici Da Zambo A Cikin Waƙoƙin Baka Wajen Bunƙasa Sarautun Gargajiya A Ƙasar Hausa

 Hanyoyin isar da saƙo a harshen Hausa suna da yawa musamman a ɓangaren adabin Hausa. Waƙar baka tana ɗaya daga cikin hanyoyin da Bahaushe yake amfani da ita domin ya isar da saƙonsa zuwa ga jama’a. Saboda haka fahimtar al’amurran rayuwar kowace al’umma ya dogara ne a kan yadda mutane suka ɗauki adabin al’ummarsu wajen harkokinsu na yau da kullum. Watau irin yadda al’umma ke gudanar da rayuwarta ya ta’allaƙa ne kacokan a kan adabi. Wannan takarda za ta yi tsokaci ne dangane da gudummawar da habaici da zambo suke bayarwa a cikin waƙoƙin baka na sarauta wajen bunƙasa sarautun gargajiya a ƙasar Hausa. Haka kuma da irin yadda sarakuna ke amfani da makaɗan Hausa wajen gano duk wata badaƙala da ‘yan adawa da ‘ya’yan sarakuna ke ƙullawa don su daƙushe kwarjinin sarki a idon talakawa da ƙasa baki ɗaya. Mawaƙan baka kan yi amfani da habaici da zambo su faɗakar da sarki irin zagon ƙasa da ‘ya‘yan sarauta ke yi a cikin waƙoƙinsu na sarauta.

Dangantakar Habaici Da Zambo A Cikin Waƙoƙin Baka Wajen Bunƙasa Sarautun Gargajiya A Ƙasar Hausa

 

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0 GABATARWA

Sarauta tsarin rayuwa ce ta shugabancin al’umma wadda ke buƙatar mutum mai hakuri da sadaukar da kai ga abin da zai kawo cigaban al’ummar da yake yi wa shugabanci. A.B Yahaya (1997). Da yake sarakunan Hausawa mutane ne da ke da sha’awar a kambama su, domin su sami dammar tafiyar da mulkinsu cikin walwala, ya sa suka ɗauki mawaƙan baka su riƙa rera masu waƙa. A cikin waƙoƙin da suke rera masu, su mawaƙan ke amfani da wasu kalmomi na habaici da zambo domin su soki abokan adawar sarakunan da suke yi wa waƙa, tare da harzuƙa sarakuna a lokacin da suke kambamasu.

 

Ganin yadda wasu mutane da sauran al’ummar Hausawa suke yi wa waɗannan kalmomi na habaici da zambo mummunar fahimta game da yadda mawaƙa ke amfani da su cikin waƙoƙinsu ne, ya jawo hankalina da in yi tsokaci game da saƙon da waɗannan kalmomi ke isarwa. Daga cikin saƙonnin da habaici da zambo ke isarwa akwai suka ga abokan hamayya musamman waɗanda suka yi takarar neman sarauta da sarki, da ‘ya’yan sarki da kuma sauran jama’a da ba su nuna goyon bayansu ga mulkin ba. Haka kuma su kansu mawaƙan sukan yi amfani da wannan dama su soki ‘yanuwansu mawaƙa ta hanyar habaici da zambo domin su burge sarkin da suke yi wa waƙa da nishaɗantar da masu sauraron waƙoƙinsu.

 

2.0 MA’ANAR HABAICI

Ɗangambo (1984); cewa ya yi, “Habauci magana ce mai ɓoyayyar manufa. Akan yi magana da niyyar nufin wani abu ga wanda aka yi maganar dominsa. Amma idan mutum bai san kan zance ba, ba kasafai ake gane wanda aka yi habaicin domin sa ba. Domin habaici akan laƙa shi ne ga wani abu da ya faru kan wani mutum da ya aikata wani abin da yake ba mai kyau ba. Misali idan an yi abin kunya, sai a yi wa mutum habaici don ya gyara”.

 

Bergery (1993); ya fassara habaici da cewa, “Habaici yin magana ne a kan halaye ko ɗabi’un wani a gabansa ba tare da an ambaci sunansa ba”. Calɓin (1990), cewa ya yi, “Habaici magana ce da wani a kaikaice ba tare da fitowa fili ba”.

 

A fahimtar da na yi ta kaɗan daga cikin bayanin masana da aka ambato a sama, habaici magana ce, ‘yar gajeruwa cikin taƙaitattun kalmomi da ake furtawa zuwa ga wani mutum ko wasu gungun mutane da nufin yi masu gargaɗi ko hannunka mai sanda ga illar aiwatar da wani abu da ya saɓa wa al’adar Hausawa. Har wa yau, habaici wani zance ne da ake furtawa a taƙaice a matsayin wanka- da jirwaye ko zuzar-zana ko zagin-kasuwa domin a musguna wa wani mutum ko a faɗarka da shi a kan wani ko wasu miyagun ayyukka da yake aiwatarwa da suka saɓa wa buƙatar mutanen da yake zaune tare da su.

 

Har wa yau habaici wata magana ce da ake yi wa wani mutum ba tare da an ambaci sunansa ko siffarsa ba. Ana furta maganar ta fuskar karin magana tare da yin amfani da wasu kalmomi kamar su; wani, wata, wane, wance, waɗansu, su wane, su wance, ɗan, yar, mai, mutum. Ta hanyar amfani da waɗannan kalmomi ne ake sa mai sauraro ya kasa fahimtar wanda habaicin yake faɗawa a kansa, sai fa idan ya san tarihin abin da ke gudana tsakanin mai habaicin da wanda ake yi wa shi. Watau duk wanda bai san abin da ke faruwa ba a tsakaninsu (mutum biyu), to babu shakka ba zai fahimci inda habaicin ya nufa ba. Mafi yawanci ko shi kansa wanda aka yi wa habaicin ba zai fahimci cewa da shi ake ba, sai fa idan ya san laifinsa ko kuma ya san cewa abin da yake aikatawa yana da alaƙa da abin da aka yi habaicin a kansa, sannan ya gane da shi ake yi. Ana samun habaici a cikin maganganun yau da kullum da kuma tsakanin masu sana’a iri ɗaya da masu sana’o’i kishiyar juna, da tsakanin mata kishiyoyin juna da kuma cikin waƙoƙin baka na Hausa wanda shi ne batun da nake son in yi magana a kansa.

 

3.0 MA’ANAR ZAMBO

Gusau (2008) da Yahaya (1997); sun bayyana zambo da cewa “magana ce wadda ake furtawa a matsayin kishiyar yabo”. Akan siffanta mutum da wasu siffofi munana waɗanda za su wulaƙanta shi ko su jawo mashi rashin martaba a idon mutane wala’allah yana da waɗannan siffofi ko ba shi da su.

 

Calɓin (1990); cewa ya yi, “Zambo magana ce wadda aka yi wa mutum don a ƙona masa rai”. Ɗangambo (1984) da Ɗangulbi (2003) cewa suka yi, “Zambo zagi ne na ɓatanci kai-tsaye idan an kwatanta shi da habaici”. Ana siffanta mutumin da ake nufi da duk siffofinsa da halayensa da ɗabi’unsa da danginsa da iyalinsa da duk wani abu da ya shafe shi wanda zai taimaka a gane da shi ake yi. Saboda haka bisa ga bayanin masana mun fahimci cewa, zambo wani zance ne na ɓatanci zuwa ga wani mutum ko wasu ƙungiyoyin mutane da aka ambaci sunayensu domin a muzanta su a idon jama’a.

 

4.0 DANGANTAKAR ZAMBO DA HABAICI A CIKIN WAƘOƘIN SARAKUNA.

A halin yanzu mun fahimci abin da ake nufi da zambo da kuma habaici, kuma mun fahimci cewa waɗannan kalmomi manyan jigogin adabi ne musamman a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Mawaƙa suna amfani da zambo da habaici a cikin waƙoƙinsu na sarakuna da kuma na yau da kullum. Abin yi a nan shi ne, mu ɗauki kowane daga cikin waɗannan manyan dangogin adabin baka mu ga irin gudummawar da yake takawa wajen bunƙasa sarautar gargajiya da kuma sarakunan ƙasar Hausa. Mawaƙan Hausa da dama suna amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su mai da martani ga mawaƙa ‘yanuwansu, ko su muzanta ‘ya’yan sarakuna ko ‘yan adawa da sauran mutanen da ke da alaƙa da sarauta. Haka kuma suna amfani da habaici domin su nuna ƙwarewa wajen amfani da harshen Hausa da kuma samar da nishaɗi ga masu sauraron waƙoƙinsu.

 

5.0 MUZANTA SARAKUNA

Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin mawaƙan sarauta wanda yake amfani da zambo da habaici don ya muzanta wani sarki a lokacin da yake aiwatar da sana’arsa ta waƙa. Ga abin da Sa’idu Faru yake cewa sa’ad da yake waƙe gwarzonsa, Sarkin Gummi, a cikin waƙarsa mai suna Gogarman Magaji.

Sa’idu Faru:               Dogon Sarki shina da ban shawa

                                    Ran da anka zo taro ya yi kyau da riguna,

Amshi:                                   Duk wanda ag gajere a aje shi gun rabon dawo

                                    Ya kai ma wanga dunƙule, ya kai ma wanga ɗunƙule

Sa’idu/Amshi           In wurin da mata ciki har tuman gada ya kai

Ɗan karuwa duk ɓaci kajjiya da kai nike.

 

Wannan zambo ya shafi asalin wanda ake yi wa shi domin kuwa mawaƙin ya bayyana matsayin wanda yake yi wa zambo da cewa shi ba a san ubansa ba domin karuwa ce ta haife shi. Mawaƙin ya ƙirƙira wannan matsayi ne ya jefa wa mahaifiyar ɗan sarkin da yake yi wa sharri don ya muzanta shi a idon jama’a, duk da cewa abin da ya faɗa ba gaskiya ba ne.

 

Ta fuskar habaici kuwa maƙaɗi Ɗankwairo yana muzanta wani sarki a cikin waƙar Ɗanmalikin Gabake, inda yake cewa:

Jagora:                        Ga wani sarki ya yo hawa

                                    Ya zo da ɗan doki nai bakwai

                                    Zagi nai ya yi lagen gwado

                                    Had da ‘yab butar-roba ya riƙe

Amshi:                                   Da dawakinai da kayan dokin in an haɗa

                                    Duk kuɗɗin ba su wuce fan bakwai

Jagora/Amshi:          Ni ko sai nicce mashi sarki in dai ka wuce

                                    Don Allah kar ka sake biyowa wajen.

 

Ɗankwairo ya yi wannan habaici ne a lokacin da aka gudanar da taron daba a Sakkwato don taya Sarkin Musulmi Abubakar na III murnar cika shekara arba’in (40) a kan karagar mulkin sarautar Sarkin Musulmi a shekarar 1983.

 

Hawan da Ɗanmalikin Gabake ya yi, ya ƙayatar da masu kallo, don haka wannan Sarki da ya biyo bayansa bai kama ƙafar Ɗanmaliki ba. Dalilin haka ya sa Ɗanƙwairo ya muzanta wannan sarki ta jifarsa da wannan habaici.

 

6.0 MUZANTA ‘YA’YAN SARAKUNA

Dangane da ‘ya’yan sarakuna kuwa mawaƙan baka na sarakuna suna amfani da hikimominsu wajen jefa kalmomin ɓatanci zuwa ga ‘yan sarakuna don su muzanta su a idon jama’a, musamman waɗanda suka yi takara da sarki mai ci. Idan aka dubi yadda mawaƙa ke yaba sarakuna ta fuskar kyauta da wasu halaye na gari, to haka kuma suke yi wa ‘ya ‘yan sarakuna habaici ko zambo dangane da wasu halaye ko ɗabi’u marasa kyau da suka nuna. Misali makaɗi Kwazo Bagega a cikin waƙarsa  mai suna Sarkin Bagega, ‘Bawa Dahiru, ya yi habaici kamar haka:

Jagora:                        Ɗan Sarki yana biyar gidan Fullani yana bara

Amshi:                       Sun mai sai mahaukaci

 

Har wa yau a cikin Waƙar Sarkin Ɗangulbi, Ƙwazo ya yi zambo da habaici kamar haka:

Jagora:            Ɗan Sarki da bunsuru ya jawo

Amshi:           Yana biɗar masu saye

Jagora:            Ɓarawo ne”

Har wa yau Ƙwazo na cewa a cikin Waƙar Sarkin Tumɓurku Alhaji Musa:

Jagora:            Sarki na zo ka miƙa min hwanda

                        Har ya yi nufin bayarwa

Amshi:           Durgun zakara ya soke

 

Misalan da suka gabata game da zambo suna nuna muzgunawa ne ga ‘ya’yan sarakuna waɗanda suka nuna wasu ɗabi’u ko halaye da suka saɓa wa al’adar gidan sarautun gargajiya. Irin waɗannan halaye ne ko ɗabi’u ke jawo hankalin mawaƙa su ƙirƙiri wani sharri su danganta shi da waɗannan mutane domin su ɓata masu rayuwa.

 

Idan aka koma ta fuskar habaici zuwa ga ‘ya’yan sarki, za a ga cewa mawaƙa na taka rawar gani wajen samar da nishaɗi da kuma kambama sarki ta fuskar abokan takara (‘ya’yan sarakuna) da ba su sami nasarar cin sarauta ba. Misali a cikin Waƙar Sarkin Zuru Alhaji Sani Sami ta Musa Ɗanba’u Gidan Buwai mawaƙin ya yi wa wani ɗan Sarki habaici, kamar haka:

Jagora:            Raggo na kallon gidan ubansa

                        amma ba ya zuwa cikinai

Amshi:           Cilas ya hanƙure ya yi kallo

                        mai ƙwazo ya shige gida nai

Ya ci gaba da cewa

Jagora:            Kai ku ji ga giwa ta nisa,

                        na ga itace na ƙallewa

                        ga Sarki Sani ya miƙe

                        ga ‘ya’yan Sarki suna gudu

Amshi:           Ga wani can ya faɗi ya kare

                        ya rasa wanda ka taimako nai.

Jagora:            Ga wani ya yi biɗa an kasai

                        Sai yat tashi yana ta kuka

Amshi:           Har mun ji yana wani zance

                        Ba ya da wanda ka son shi Zuru.

 

A cikin waɗannan baitoci biyu da Ɗanba’u ya yi amfani da su cikin Waƙar Sarkin Zuru, ya nuna irin martaba da kwarjinin Sarki Sani Sami a idon mutane. Don haka ya kamanta shi da giwa, idan ta miƙe duk wani abu mai karamin karfi ba zai yi motsi ba. To, haka martabar sarki take, idan ya miƙe tsaye to duk wani ɗan sarki dole ya kwanta. Ya yi wannan habaici ne ga waɗanda suka nemi sarautar Zuru tare da Sarkin Sani Sami, kuma ya kasa su.

 

7.0 MUZANTA FADAWA DA SAURAN YAN ADAWA

Za a jaddada cewa habaici da zambo tagwayen kalmomi ne da mawaƙan baka ke amfani da su a cikin waƙoƙinsu na sarakuna da makamantansu. Mafi yawan mawaƙan sarakuna sukan dubi yanayin da sarautar gari take ciki da irin mutanen da suka nuna goyon bayansu ga takarar kujerar tsakanin ‘ya’yan sarakuna da wanda Allah ya ba sarautar. Duk wanda ya yi nasara, to za ka sami mawaƙan sun duƙufa wajen kambama shi da kuma yi wa abokan takararsa habaici da zambo. Wannan zai sa sarki ya ƙara natsuwa tare da fahimtar halaye da ɗabi’un abokan adawarsa zuwa ga mulkinsa da kuma shi kansa. Dangane da haka su mawaƙan kan bayyana wa sarki masoyansa da kuma masu yi masa zagon ƙasa ta hanyar yi masu habaici da zambo domin sarki ya gane su.

Misali a cikin waƙar Sarkin Kaura Narambaɗa ya yi wa ‘yan -ba -mu - yarda ba, da ‘ya’yan sarakuna habaici. Ga abinda yake cewa:

Jagora:            In an so har in ba a so ba,

Amshi:           Mai abu dai shi adda abi nai

Gindi:             Giye bajinin Mamuda

                        Abu na Namoda shirarre

 

Haka ‘yan ba-mu-yarda ba da naɗin Sarkin Rwahi ba, wato, ‘yan adawa, sun sha habaicin Narambaɗa inda yake cewa:-

Jagora:            Gidan ga mutum biyu suna da haushi

                        Don Allah baƙin ciki kashe su

Amshi:           Ka ga su can da jan ƙuje

                        Da ɗanai

Gidi:               Masu gari mazan gabas tsayayye

 

Shi kuwa Sani Aliyu Ɗandawo a cikin waƙar Sarkin Yawuri Mamman Tukur, ya yi habaici kamar haka:

Jagora:                        Duniya akwai ƙarya da yawa,

                        Na ji wai tumaki na kwamiti,

Wai za su gidan giwa da faɗa, 

Wai su ce ma giwa kada ta wuce,

Amshi:           Bar su, ran da giwa tay yi hushi,

                        Duk suna sanin bayanta suke.

 

Waɗannan misalai na habaici zuwa ga fadawa da waɗanda suka nuna adawa ko rashin goyon bayan sarki sun nuna irin yadda mawaƙan baka suke amfani da hikimarsu wajen bayyana wa sarki halin da maƙiyansa da ‘yan – ba-mu-yarda ba suke. Don haka shi zai sa sarki ya ƙara azama wajen kyautatawa talakawansa don mulkinsa ya haɓaka, a koina ya yi suna.

 

Ta fuskar zambo ba a bar mawaƙan baka a baya ba domin sukan yi amfani da shi wajen aiwatar da kwatankwacin abin da suke yi a cikin habaici. Shi ma zambo ya yi tasiri wajen rayawa da bunƙasa masarauta a ƙasar Hausa. An fi yin zambo don adonta waƙa da samar da nishaɗi ga masu sauraro. Kuma makaɗan fada suna taka rawa ga yin haka duk da kasancewa wasu na ganin cewa zambo yana tozarta duk wanda aka yi wa shi. Akasari an fi yin zambo ga ‘ya’yan sarakuna, to amma su kansu fadawa da sauran jama’a ana yi masu zambo don a muzanta su, saboda kasancewar wasu daga cikinsu munafukai ne ko kuma marowata. Mawaƙan sukan yi amfani da salon jansarwa, wato su fito fili su bayyana siffar mutum ta hanyar dabbantawa ko abuntawa. Su zagi mutanen da suke so domin su muzanta su. Sukan faɗa masu maganganu na wulaƙanci domin kawai su faranta wa sarki rai da kuma samar wa jama’a raha da nishaɗi. Misali, a cikin waƙar Ƙwazo Bagega ta Sarkin Dangulbi mai suna Mijin Daga, an yi wa wani tsoho zambo da ya nuna rashin amincewarsa ga sarki, ga abinda Ƙwazo ya cewa:

Jagora:                        Garin biɗar girma na ga wane ya yanki kare

                        Na gangara ga gulbi sai nig ga ga mutum

Zaune zugum majina na ta zuba

Ai miyau na ta zuba

Amshi:           Babban mutum yana kuka

                        Ka sani wuya ta yi wuya

 

Har wa yau a cikin Waƙar Sarkin Ɗangulbi, Ƙwazo yana cewa

Jagora:                        Tsoho ya shigo rawa daɗa,

                        Ya faɗi, ya cira, ya yi tsaye,

Amshi:                       Tsoho wa ka ba ka sarki,

                        Koma gida dashen rogo,

                        Ko ka shuka doya mu saye.

Duk waɗannan zambo da habaici suna nuna wa jama’a cewa mawaƙan baka na Hausa mutane ne da ke amfani da hikimomi da hazaƙarsu wajen isar da saƙo cikin sauƙi zuwa ga jama’a. Idan aka dubi misalan da aka gabatar dangane da habaici da zambo za a ga cewa wasu hanyoyi ne da mawaƙan baka na Hausa ke bi wajen burge jama’a da kuma ƙara wa waƙoƙinsu armashi. Haka kuma su kansu waɗanda ake yi wa waƙa, wato sarakuna suna amfani da waɗannan hanyoyi su gano ‘ya ‘yan sarauta da fadawa da waɗanda ba su nuna goyon bayansu ga mulkinsu ba. Sarakuna suna ƙara ƙaimi wajen yin gyara ga gudanar da mulkinsu musamman idan sun tuna cewa ai akwai ‘yan adawa da sauran masu kallon yadda suke tafiyar da mulkinsu. Don haka zambo da habaici hanyoyi ne biyu da mawaƙan baka na sarakuna ke amfani da su don su bunƙasa daraja da kwarjinin sarakunan ƙasar Hausa ta hanyar suka da muzanta abokan hamayyarsu a idon duniya. A cikin Waƙar sa ta Mustapha Madawaki , Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yana cewa:

Jagora:                        Ni har yanzu jahili nika kallo,

Amshi:                       Bai san amana ba sai ta ci shi

 

KAMMALAWA

Bayanai a wannan takarda sun nuna cewa ana amfani da habaici da zambo a cikin waƙoƙin sarauta don a muzanta waɗan da abin ya shafa da kuma taimaka wa masu mulki su gyara tafiyarsu da kuma bunƙasa sarautun gargajiya a ƙasar Hausa.

 

Bayanai a wannan takarda sun nuna cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin habaici da zambo domin tagwayen juna ne a fagen gyaran ɗabi’u da samar da nishaɗi da raha a tsakanin waɗanda ake yi wa da sarakuna da kuma masu sauraron waƙa. Haka ma su kansu sarakuna da ake yi wa waƙar suna la’akari da hannunka mai sanda da mawaƙan ke yi masu dangane da abubuwan da suke aiwatarwa a lokacin da suke gudanar da mulkinsu.

 

A ƙarshe ina kira ga masu nazarin adabin Hausa da su lura da irin mihimmiyar rawar da habaici da zambo suke takawa wajen wayar da kan jama’a da koyar da tarbiya ta gari musamman hani ga aikata wasu ɗabi’u miyagu da al’umma take ƙyama, kamar yadda muka gani a baya cikin misalai.

 

Haka kuma waɗannan manyan jigogin waƙoƙin sarauta suna farfaɗo da martabar sarakuna da kuma raya al’adun masarauta da faɗakar da sarakuna game da abubuwan da ke faruwa a fadarsu. Wannan na taimaka masu wajen bayyana masu irin halin da talakawansu da ƙasarsu take ciki don su ɗauki matakin gyara, sannan su samu damar bunƙasa sarautunsu da nasarar gudanar da mulkinsu. Misali, yadda za su zauna da ‘ya‘yan sarauta da ‘yan adawa da talakawansu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments