Wasu Ɗabi’un Matasa a Matsayin Barazana ga Zaman Lafiyar Ƙasa


    Nowadays, the life of the youth has become catastrophic, in which Hausa culture that we inherited from our forefathers has been deteriorated by the alien cultures, which bring about some changes in the good attitude of our youths. The main objective of this paper is to discuss the attitudinal changes of the youths, its causes, and consequences to the well-being of the society. The paper discussed the Hausa youth in the ancient time, nowadays and the anticipation of their life henceforth. The paper brings about some bad attitudes that youths engage themselves nowadays and the causes of those bad attitudes that become the nightmare to the security, stability, peace, and harmony of the society. The discussion ended by suggesting the way forward in tackling this problem.


    Wasu Ɗabi’un Matasa a Matsayin Barazana ga Zaman Lafiyar Ƙasa

    Jibril Yusuf
                             Department of Nigerian Languages and Linguistics      
    Kaduna State Uniɓersity, Kaduna
                                                         +2347030399995, jibreelzango@gmail.com

    Musa Isah Abubakar
    Department of Hausa
    Jigawa State College of Education, Gumel.
    +2347064833646

    Tsakure
    Rayuwar matasa a wannan zamani ya zama abin takaici, kasancewar an yi sakaci baƙin al’adu sun yi wa al’adun Hausawa kutse, yadda har ta kai ga al’adunmu da muka gada tun kaka da kakanni sun fara yi mana nisa, kuma har ta kai ga sauye-sauyen sun fara barazana ga zaman lafiyarmu. Manufar wannan takarda ita ce gano sauye-sauyen ɗabi’u tsakanin matasa, da kuma irin barazanar da yake yi ga zaman lafiya. Takardar ta yi ƙoƙarin kawo bayanai kan matasa a jiya wato a rayuwar gargajiya, sannan kuma an kawo bayanai kan rayuwar matasa a yau da yadda zamani ya yi tasiri a kansu. Daga bisani an zayyano irin miyagun halayen da matasa kan tsunduma ciki da kuma abin da yake haifarwa musamman yadda ɗabi’un matasan kan riƙa yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma. Sannan kuma an yi ƙoƙarin gano dalilan da suke haifar da waɗannan sauye-sauyen ɗabi’un. A ƙarshe takardar ta yi ƙoƙarin bayar da shawarwari kan hanyoyin da ya kamata a bi domin magance waɗannan matsaloli domin samun kai wa ga tudun mun tsira.

    1.0 Gabatarwa
    Matasa su ne ƙashin bayan ci gaban kowace al’umma, kasancewar su wani rukuni mai muhimmanci a cikin al’umma. A kowane yanki, lungu da saƙo na duniya da matasa ake taƙama domin kuwa su ne ake yi wa kallon manyan gobe. Hakan ya sa ake wa rayuwarsu kallon kayan ƙaras, wanda sakaci kaɗan za a yi ya lalace.
    Kenan rayuwar matasa na da matuƙar muhimmanci kuma abin kulawa ce matuƙar
    gaske, kasancewar idan ta lalace to al’umma na cikin haɗari da rashin tabbas. A cikin wannan takarda an ƙuɗiri aniyar gano barazanar da sauye-sauyen halaye matasa ke yi ne ga zaman lafiya, ta hanyar hasko inda aka fito wato rayuwar gargajiya da kuma tasirin zamani kan rayuwar matasan. Haka kuma za a yi ƙoƙarin fito da dalilan da kan haifar da sauyi a cikin rayuwar matasan, da irin munanan halayan da suka afka da sakamakonsa.       Dangane da wannan takarda kuwa matasa na nufin wani rukunin al’umma ne waɗanda suka wuce zangon yarinta, waɗanda tunaninsu da hangen nesansu bai kai matakin na manya ba, waɗanda kuma ke cikin ganiyar ƙarfinsu.
    2.0       Matasa A Matsayin Wani Rukuni na Al’umma
    Kalmar matasa jam’i ne tilon kalmar shi ne matashi (namiji) ko matashiya (mace). Masana da manazarta sun yi musayar ra’ayi kan yadda kowannen su ke kallon kalmar; Piaget (1972: 108) ya bayyanamatasa da cewa “Wani rukuni ne na al’umma da suka fara samun bunƙasar tunanin daga ƙuruciyar ya zuwa girma, wanda kuma ya ƙunshi ɗabi’un ƙuruciya, kuma mataki ne da yaro ya fara nuna manyanta, wato ya fara yin dogon hangen nesa da kuma kyakkyawan tunani dangane da rayuwa”.
    Cole da wani (1989: 521) sun bayyana matasa kamar haka, ‘Wani lokaci ne da ƙarfin jima’i yake kan ganiyarsa a gare su, kuma ɗabi’unsu suka karkata a kansa”.
    Yahaya da wasu (1992: 76) sun nuna cewa “matasa su ne waɗanda suka wuce zangon yarinta, suka nufi kaiwa matsayin manyanta. Matasa su ne suke kan ganiyar balaga da kai ƙarfi, don haka lokaci ne na gwajin rayuwa da gwada ƙarfi ko juriya ko hakuri. Don haka, zangon matashi na farawa ne daga shekara goma sha uku (13) zuwa shekaru talatin da tara (39) wannan ya yi daidai da ra’ayin Bahaushe game da matashi”.
    A cikin kowace al’umma matasa ne ke dauke da kaso mafi tsoka. Sannan kuma matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen yin ayyuka na karfi da tabbatar da tsaro a cikin al’ummarsu. Sannan idan aka duba za a ga cewa matasa su ne a cikin manyan makarantu (Almajir da wani, 2013: 493). Rukunin matasa shi ne rukuni mafi muhimmanci a cikin sauran rukunan matakan rayuwa domin kuwa dukkan wani abu na ci gaba da bunƙasar rayuwa a wannan matakin ne ake gina shi, kodai ya kasance ta fuskar neman ilimi ko sana’o’i da tarbiyya da sauransu daga wannan yankin rayuwa ne akan jajirce domin ganin gobe ta yi kyau. Kenan rukunin matasa a cikin al’umma na ba da gagarumar gudumawa domin ganin al’umma ta samu ci gaba ta kowace fuska.
    3.0 Matasa a Jiya da yau
    Masu hikimar Magana ne cewa “Duk inda ka ga tsohon banza to asalinsa yaron banza ne”. Wannan ko za a yarda da shi idan aka yi la’akari da rayuwar matasa a tun farkon fari, wato za a yi duba ga yadda matashi ya gudanar da rayuwarsa ta samartaka wannan ne zai iya ba da haske kan irin halin da ya tsinci kansa a ƙarshen rayuwarsa. Nagartaccen matashi shi ne ginshiƙin samar da kyakkyawar al’umma. Hakika duk al’ummar da ke da ɗumbin matasa to ta yi wa Allah godiya domin kuwa wannan ne yake nuni da cewa za a daɗe ana damawa da wannan al’umma a fagen ci gaban rayuwa(Gwale, 2012).
    Tun can azalan  an nuna cewa Bahaushe na da wasu ɗabi’u na asali da aka san shi da su waɗanda a duk inda ka gan shi ba sai ka tamabaya ba matuƙar dai ka san shi. Waɗannan kyawawan ɗabi’un kuwa sun ratsa kowane rukuni na Hausawa tun daga ƙanan yara zuwa matasa har zuwa tsofaffi duk inda ka ga Bahaushe za ka gane shi. Waɗannan ɗabi’u sun haɗa da: kunya da kara da kawaici da gaskiya da riƙon amana da gudun abin kunya da girmama na gaba, da riƙo da al’ada ta fuskar sanya tufafi da cin abinci da bukukuwa da dai sauransu. Sannan kuma Bahaushe na rayuwa ne irin rayuwarsa ta gargajiya wanda ya gada tun kaka da kakanni.
    Kasancewar irin wannan tsari ne na zamantakawar Hausawa ya sa matasa a wancan lokaci suka zama nagartattu kuma tsayayyu sannan amintattu kuma fitattun lokacinsu.
    Bugu da ƙari, a da, matasa su ne aka sani kan gaba wajen neman na kansu ta hanyar kama sana’o’i da jajircewa wajen kare mutunci da ƙimar dangi domin kada a ce mutum ya yi wani abin faɗa da zai bar wa kansa da danginsa abin faɗa. Ta fuskar ayyukan ci gaban ƙasa matasan ne kan riƙa haɗa kai wajen gudanar da ayyukan gayya da sauransu.
    Ta fuskar tsaron ƙasa ma akan samu matasa su ne sojoji da kan tsaya wajen kare ƙasarsu daga mahara. Wannan matasa kenan a jiya, a rayuwa irin ta gargajiya ta asali. Da tafiya ta yi tafiya sai aka sami cuɗanya da baƙin al’ummu, wanda hakan ya haifar da sauye-sauye da dama a shafin rayuwar Bahaushe musamman ma waɗanda nazarin ya ta’allaƙa a kansu wato matasa.
    Al’ummar Hausawa sun sami cuɗanya da baƙin al’ummu waɗanda suka shigo ƙasar Hausa da manofofi mabambanta. Duk inda aka sami cuɗanya tsakanin baƙuwar al’umma da wata al’umma ta daban, dole ne a sami ɗaya ya yi tasiri a kan ɗaya. Musamman idan cuɗanyar ta ɗauki dogon lokaci ta hanyar saye da sayarwa ko ta hanyar mamaya ko yaudara da fifikon ƙarfin makamai na zamani tamkar dai yadda ‘yan mulkin mallaka suka yi a ƙasar Hausa. Irin hakan kan sa a wayi gari al’adun al’ummar da ta yi mamaya ta yi tasiri a kan na waɗanda aka mamaye. In aka yi rashin sa’a sai a wayi gari sannu a hankali kyawawan al’adu da dabi’un al’ummar da aka mamaye su suna gushewa ɗaya bayan ɗaya (Bakura, 2013: 217).
    Irin wannan shi ne abin da ya faru a ƙasar Hausa sakamakon cuɗanya da Turawa. Wannan ya haifar da cuɗanya da baƙin al’adu wanda ya haifar da sauye-sauyen dabi’u ta fuskokin da dama.
    4.0  Sauye-Sauyen Ɗabi’un Matasa
    Idan aka yi batun sauyi kalmar na nufin sake ko canja ko musanya wani da wani (CNHN, 2006: 394). Kalmar ɗabi’a ko ararriyar kalma ce daga larabci wadda Hausawa suka ara, wadda kuma ke nufin halin mutum ko al’adarsa (CNHN, 2006:116).
    Kamar yadda aka bayyana a baya, cuɗanya da baƙin al’ummu kan yi tasiri mutuƙa kan al’ummar da aka yi cuɗanya da ita, wannan ya sa ake ganin kasancewar al’ummar Hausawa da ke zaune a Arewacin Nijeriya sun samun irin wannan cuɗanyar tun a karon farko da ƙananan ƙabilun da ke kewaye da su, sannan daga bisani zuwan Turawan mulkin mallaka ya kara yin tasiri ga al’ummar wannan wuri. Kenan al’adun ƙabilun da ke zaune tare da Hausawa sun yi mutuƙar tasiri a kan matasa a yau ta yadda za a tarar da matasa sun tsunduma cikin miyagun halayen da a da ba a san Hausawa da su ba.



    Daga cikin irie-iren ɗabi’un da matasa kan tsunduma a ciki sun haɗa da:
              i.            Shaye-shaye: Wannan ya shafi shan kayan maye kamar ƙwayoyi da shalisho da tabar wiwi da magungunan tari na ruwa wanda ya zama ruwan dare tsakanin matasa maza da mata.
                 ii.            Sara-suka/Dabanci: Yawancinwaɗanda kan tsunduma kansa cikin harkar shaye-shaye ne ke shiga cikin irin wanna ɗabi’ar. Domin kuwa harkace da ta shafi rashin mutunci da cin zarafin mutane don haka sai an gusar da hankali yawanci kafin a yi irin wannan harkar. Haka kuma kashi casa’in da biyar cikin dari na masu yin harkar sara-suka matasa ne waɗanda shekarunsu ke farawa daga 15-35.
          iii.            Rashin Ɗa’a/Girmama na Gaba: Yawancin matasan da ke irin wannan harkar ba su ganin kowa da gashi, ba su jin maganar kowa ba su kuma sauraron nasiha. Yawancin sun yi sallama da gidajen iyayensu. Don haka ko iyayen nasu ma ba su faɗa musu su ji. Sannan idan ta kama za su iya ciwa kowa mutunci ba tare da la’akari da shekarunsa ko ƙimarsa ba.
          iv.            Sace-sace: A idon Bahaushe sata ta fi kowane irin mumunan hali illa ga mutum da zuri’arsa (Sarkin Sudan, 2013: 231). Duk da haka wasu matasa a yau sun mayar da sata tamkar sana’ar ƙwarai, ta yadda suka ɗauke ta hanyar ci da shansu. Yawanci shaye-shaye ya taimaka wajen yawaitar sace-sace ga matasa domin sukan kasance idan ba su sha ba to ba su jin daɗi, kuma yawancinsu ba sana’ar kirki ke gare su ba. Sai ya kasance idan ba su da kuɗin sayen kayan shaye-shayen sai su nema ko ta halin ƙaƙa.
            v.            Zinace-zinace: Zina tana ɗaya daga cikin abin da Bahaushe ya tsana tun can azal kafin bayyanar Musulunci kuma dukkan wanda ya aikata zina to yakan zama abin magana kuma abin kunya ga zur’iar wanda ya aikata. Yana daga cikin al’adun auren Bahaushe na can dauri wato tabbatar da ɗiyauci wadda har ya kasance akwai tsafe-tsafe da akan yi lokacin da aka yi aure kafin a kai amarya gidan miji, da wanda ake wa ango duk don a tabbatar ba su taɓa yin lalata ba (Sarkin Sudan, 2008:79). A yau zina ta zama ruwan dare tsakanin matasa. Inda har akan sami waɗanda sukan fita domin neman wanda zai yi zina da su, su riƙa jira a bakin hanya idan mutum ya zo wucewa su tambaye shi in yana da buƙata. Yammata ne kan tsaya a bakin hanya suna zuwa wurin duk wanda ya zo wucewa musammam a kan abin hawa (mota ko babur da sauransu) su tambaye shi ko yana da buƙata, in kuma ya tsaya ya saurare su har sai sun tambaye shi da cewa: “Short-time ne ko kwana?” Marubucin wannan takarda ganau ne ba jiyau ba. Allah ya wadaran naka ya lalace!
          vi.            Liwaɗi: Wannan ma wata mummunar hanya ce da matasa suka kama wanda kuma ke yaduwa cikin al’umma. Hanya ce da namiji kan bi namiji domin gusar da sha’awarsa. Wannan yana daga cikin irin mummunar tasirin da zuwan Turawa ƙasar Hausa ya yi wa al’umma. Domin kuwa Turawa sukan baro ƙasashen su, su shigo ƙasar Hausa da mummunar manufarsu, sannan su yi wata da watanni ko shekaru alhali sun baro matansu a can ƙasashensu, wasu ma daga cikinsu ko auren fari ba su yi ba, suka zo sai suka koya wa wasu ‘yan ƙasa liwadi (Bunza, 2015). Matasa da yawa sun faɗa cikin wannan mumunar ɗabi’ar.
        vii.            Maɗigo: Wannan ma na daga cikin irin munanan abubuwan da tasirin zuwan Turawa ya haifar, inda mace kan bi mace ‘yar uwarta domin gusar da sha’awarta saɓanin namji. A al’adance ko dabba ba ta bin ‘yar uwarta mace, amma yanzu a cikin matasan mata an samu har faɗa ake yi tsakanin mace da mace idan suka haɗa neman mace guda.
     viii.            Bangar Siyasa: Yana daga cikin irin sauye-sauyen da aka samu na ɗabi’un matasa shiga ɗabi’ar bangar siyasa.  Da dama daga cikin matasa sun zama ‘yan zaman kashe wando, ba su son tashi su wahala su nema ta hanyar kama sana’a, sai dai su zauna a bakin titin unguwa suna jiran ‘yan siyasa su zo su ba su na taba (sigari). Sun gwammace su bi taron siyasa suna jiri suna ihun sai wane, sai wane, da yamma a ba su naira hamsin ko ɗari ko dai ɗan wani abin da bai taka kara ba balle ya karya. Wanda wannan ya saɓa da hali da ɗabi’ar da aka san Bahaushe da shi na ƙoƙarin neman na kai ba cima zaune ba.
          ix.            Rashin Kunya: Kunya ta ƙunshi hana harshe yin munanan maganganu da hana gaɓɓan jiki aikata miyagun ayyuka (Isah, 2013:423). Rashin kunya kuwa shi ne “Aikata abin da mutum ya ga dama mara kyau a gaban mutane. Shiga cikin irin wannan yanayi ga mutum a al’ummar Hausawa yana zubar da girma a riƙa ɗaukarsa mutumin banza” (Sarkin Sudan, 2013: 230). Wannan kuwa ya riga ya zama ɗabi’ar matasa a yau, tayadda suke ganin ma idan mutum bai iya rashin kunya ba gani ake bai waye ba. Inda zaka ji matashi yana tutiyar cewa ya fi kowa iya rashin kunya koka ji budurwa na cewa “Ƙaryar rashin kunya kake yi”(Hira da Ahmed Loskey, 2/11/2015). Kenan wannan ba ƙaramar barazana ce ga zaman lafiyar al’umma ba, kasancewar maras kunya na iya aikata kowane irin ta’asa. Domin ko a addinance ma an nuna cewa duk wanda ba ya jin kunya to ya aikata abin da ya ga dama.
     Yanayin Sutura: Za a tarar da matasa a yanzu ire-iren tufafin da suke sawa ya saba wa al’ada da addini, domin kuwa za a tarar suturar matasun matse jiki sun fitar da duk surar mace, ta yadda da wuya a iske mata goma a sami guda biyu waɗanda ba su sanya irin waɗannan tufafin ba, wanda hakan shi ne yake haifar da yawaitar zinace-zinace da fyaɗe da sauransu.
    Ga maza kuwa wata ɗabi’a da suka ɗauko ita ce ta zazzago wando ya dawo rabin ɗuwawu (sagging) wanda yanayi ne da alama ta ‘yan luwaɗi, amma sai matasa suka dauƙa suka mayar da shi tamkar wani abin birgewa (Bunza, 2015).
    Waɗannan su ne ire-iren sauye-sauyen da wannan nazari ya iya ganowa ta fuskar ɗabi’un matasa, wanda ke yin barazana ga zaman lafiyar ƙasa.Duk da haka, bayan nazari da gano waɗannan sauye-sauyen a cikin ɗabi’un matasa, sai aka duba aka ga cewa; Ruwa fa ba ya tsami banza. Domin idan fa ɓera na da sata, to daddawa ma na da wari. Kada kuma a bar jaki a riƙa bugun taiki!
    4.1 Me ya Haifar da WaɗannanSauye-Sauyen?
    A nan za a yi bayanin dalilan da ake ganin sun taimaka wajen sauyawar ɗabi’un matasan ne ta hanyar kawo misalai daga dalilan da aka bayar.
    Ko da masu hakimar magana suka ga goro cikin miya cewa suka yi ‘Da walakin…’Domin dai an tabbatar banza ba ta kai zomo kasuwa. Halin ni ‘ya su da ta taɓarɓarewar ɗabi’un matasa da a yau ya zama ruwan dare ba haka nan kawai aka wayi gari aka ga matasan sun sauya farat ɗayaba. Sai dai akwai wasu dalilai da za a iya hassashen cewa su ne ummul haba’isin wannan saki reshe kama tozo da matasan suka yi.
    -Rashin Tarbiyya: Tun da farko akan sami sakaci wajen tarbiyyar iyaye, ta yadda iyaye kan yi wa al’adu riƙon sakainar kashi ba tare da nuna wa yaro abin da ya kamata ya yi ko ya bari ba. Inda akan nuna musu abubuwa kamar girmama na gaba, da nuna musu muhimmancin aiwatar da wasu abubuwa masu kyau kamar cin abinci da hannun dama da karɓa ko bayar da abu da hannun dama da yin tsarki da hagu. Ana kwaɓar yara wajen sanya baki a maganar manya da sauransu (Abdulƙadir, 2013:579). Kasancewar shi yaro kiwonsa ake tamkar dabba, domin duk abin da ya saba da shi to da shi yake tashi. Wannan ya sa sakacin iyaye na nuna wa yara abin da yakamata, da nuna musu tsananin so ya sa yaran suka kangare suka ƙi sarrafuwa. Masu hikimar zance kuwa sun ce; Icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi.
    - Rashin Ilimi: Ilimi gishirin zaman duniya. Riƙon sakainar kashi da waɗansu iyaye suka yi wa karatun ‘ya’yansu ya taimaka ƙwarai wajen jefa matasa cikin duhun jahilci wanda hakan barazana ce ga zaman lafiyar ƙasa. Kasancewar ilimi shi ne hanya ɗaya tilo wanda kan kai mutum ga tudun mun tsira tun daga duniya har lahira. Domin kuwa, sai da shi ake gane hani da horo da kuma hanyoyin ci gaban rayuwa. Kenan rashinsa babbar illa ce ga matasa har ma da al’umma baki ɗayanta. Hakan ya sa ake ganin rashin ilimi babbar barazana ce zaman lafiyar kowace ƙasa mai son ci gaba. Kenan neman ilimi babbar hanya ce da kan yi jagora ga zaman lafiya da ci gaban al’umma.
    - Bakin Iyaye: Yawancin iyaye kan riƙa yi wa ‘ya’yansu mugun baki tun ba su isa misali ba. A al’adance an yarda cewa dukkan abubuwan da iyaye kan riƙa danganta shi da ‘ya’yansu shi ne yakan bi su, kuma su tashi da shi har girmansu.  Wataƙila ma wannan ne ya sa masu hikimar magana kan ce fata na gari lamiri! Wannan ko haka yake ko a addinance ma an tabbatar cewa addu’ar iyaye ga ‘ya’yansu karɓaɓɓiya ce. Wannan ya sa rashin sani ga wasu iyayen sai su yi ta faɗin miyagun abubuwa suna danganta shi ga ‘ya’yan nasu ba tare da sun san illar hakan a gare su ba wanda kuma kan bi ‘ya’yan nasu idan sun girma su addabi al’umma.
    - Talauci: Ƙuncin rayuwa da al’umma kan tsinci kansu a ciki sakamakon talauci yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da kan haifar tashin-tashina a cikin al’umma. Domin kuwa, fitina da tashin hankali babu abin da yake haifarwa sai hasarar rayuka da dukiya. Wanda kuwa ya duba gaba ya duba baya ya ga cewa bai ajiye ba, bai kuma bai wa wani ajiya ba, to bai damu da ya tayar da husuma ba, domin ba shi da hasara. Misali; idan aka ɗauki matsaloli irin su; sace-sace da fashi da makami da ‘yan kashe-a-biya-ka (hire killers) za a ga cewa duk yawanci talauci ne kan kai su ka faɗawa ga miyagun ayyuka.
    - Hassada da Baƙin Ciki: Sau da dama akan sami wani ko wasu su riƙa baƙin ciki da samun wani, wato kamar yadda akan samu waɗansu Allah ya hore musu dukiya wasu kuwa ba su da shi. Sai waɗanda ba su da shi su ƙulla gaba da masu shi har ma su riƙa fatan wannan dukiyar ta salwanta. Wannan ne kan sa a wasu lokuta wani kan kashe ko ya yi sanadiyyar mutuwar wani. Kai a wasu lokuta ma akan samu rikici tsakanin wata ƙabila da wata, musamman idan suna zaune a wuri guda,sai ƙabilar da take ganin an fi ta arziƙi ta yi amfani da ɗan wani abu ƙanƙani ta tayar da husuma don su kwashi dukiyar waɗancan ko kuma su lalata. Sau da yawa kuma matasa ne ake amfani da su wajen tayar da ire-iren waɗannan fitintinu.
    - Rashin Aikin Yi: Zaman kashe wando da rashin ƙwaƙƙwarar sana’a ya taimaka kwarai da gaske wajen sauyawa kyawawan ɗabi’un matasa akala. A maimakon idan aka wayi gari matashi ya kama hanya zuwa wajen sana’arsa, sai kawai ya riƙa zaman daba. Rashin aikin yi babbar barazana ce ga zaman lafiya, domin kuwa duk wanda ba shi da aikin da yake yi don samun taro da sisi to kuwa ya ƙulla abota da talauci wanda yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da kan haifar da tashin- tashina.
    - Rashin Aure: Aure babbar hanya ce wadda ke kange mutum daga faɗawa tarkon zinace-zinace da alfasha. A wannan zamanin yawancin matasa ba su mai da hankali ga yin auren ba, wannan kuwa ba zai rasa nasaba da wasu abubuwa baƙi da aka shigo da su cikin lamarin auren ba,waɗanda kuma suka sanya lamarin auren ya yi tsanani. Har ya zamto samari na son aure, ‘yammata na so, amma babu yadda za a yi domin an tsananta. Wannan sai ya kai matasa ga faɗawa tarkon shaiɗan wanda ya kai su ga shiga zinace-zinace da liwaɗi da maɗigo. Wannan ya sa fitina ta yi yawa a ƙasa, domin malamai sun faɗa cewa; Dukkan al’ummar da alfasha ta yi yawa a cikinta to ta shirya zuwan bala’o’i.
    - Kallace-Kallace na Finafinai: Shigowar finafinan Turawa cikin al’ummarmu da barin tarbiyyar ‘ya’yanmu a hannun tauraron ɗan Adam (satellite) ya taimaka gaya wajen gurɓacewar tarbiyyar matasa a yau. Misali; yawancin finafinan Turawa suna nuna yaƙe-yaƙe da kashe–kashe da harkar dabanci da sauran nau’o’in ta’addanci, wanda hakan ya ɗarsu a cikin zukatan da yawa daga cikin matasa kuma ya yi tasiri kwarai ga rayuwarsu a yau. Wannan ya sa a yau ba abu ne mai wahala ba ka ji an ce wani ya harbe wani da bindiga ko ya soke shi da wuƙa da sauransu. Yaɗuwar waɗannan finafinan ya sa an samu yawaitar finafinan batsa waɗanda matasa kan riƙa kallo wanda kuma hakan ya haifar da yaɗuwar zinace-zinace.
    - Mutuwar Zuciya:Mutuwar zuciya na ɗaya daga cikin abubuwan da ke yin barazana ga zaman lafiya, dalili shi ne, yawanci matasa a yau sun fi son ci a ɓagas. A da, an san matasan Hausawa da ƙoƙarin neman na kai, saɓanin yanzu sai ka tarar matashi yana son jin daɗi da tara dukiya amma kuma ba ya so ya wahala. Hakan ya sa matasa suka tsinci kansu cikin sace-sace da fashi da makami da tsafi, kai har ma da luwaɗi da maɗigo, domin an ba su mummunar huɗubar cewa hanya ce ta samun dukiya. Haka ma abin da ya shafi bangar siyasa duk mutuwar zuciya ceke haifar da su.
    Waɗannan da ma wasu dalilai da dama ne ake ganin suka haifar da sauyin ɗabi’un                  matasa waɗanda ake ganin cewa su ne ke yi wa zaman lafiyar ƙasa barazana a yau.To ta yaya za a magance su?
    4.2 Ta Yaya Sauyi Ke Barazana ga Lafiyar Ƙasa ?
                Daga cikin abubuwa da ke sanya sauyi ke barazana ga lafiyar ƙasa ya haɗa da: rashin tarbiyyada da wajen iyaye domin sukan yi halin ko watsi da irn abubuwan da ya kamata yaro ya aikata ko ya bari. Sauran abubuwan sun haɗa da rashin ilimi da baƙin ciki  da talauci ko ƙunci da yawana kallon fainafinai da hassada ko ƙyashi da kuma mutuwar zuciaya.
    5.0 Shawarwarin Bincike
    A nan za a yi ƙoƙarin bayar da shawarwari ne waɗanda ake ganin za su taimaka wajen farfaɗo da kyawawan ɗabi’u ga matasa, ta yadda ake ganin idan an bi su za su kai mu ga tudun-mun-tsira.
    Kasancewar matasa su ne ƙashin bayan al’umma domin su ne masu jini a jika kuma su ne ke da buɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwa waɗanda za a yi amfani da su domin ci gaban al’umma. Kenan, ya zama wajibi a wayar da kan matasa ta hanyar faɗakar da su illar miyagun halaye, domin kuwa gobe tasu ce kuma su ne manyan gobe.
    Don haka ya kamata gwamnati ta yi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta sama wa matasa ayyukan yi gami da ba su tallafi don kama sana’o’i.
    Matasa su tashi su tsaya tsayin daka wajen neman ilimin addini da na zamani, domin ilimi yana ‘yanto mutum daga ƙangin bauta, sannan kuma duk wanda ya yi ilimi ana sa rai zai rayu cikin rufin asiri.
    Sassauta lamarin aure da kuma sakar wa matasa mara su yi fitsari, ta hanyar barin su su yi aure da zarar sun nuna buƙatar hakan. Wannan shi ne zai kawar da matsalar zinace-zinace da luwaɗi da maɗigo.
    Bugu da ƙari, iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.Matasa kuma su ji tsoron Allah kan duk wani abu da za su aikata. Su sani cewa duk abin da mutum ya aikata Allah (S.W.T) yana ji kuma yana gani, zai kuma tashe su ranar ƙiyama domin yi musu hisabi.
    A ƙarshe, ya kamata matasa su dangana su jira lokaci, kuma su fahimci cewa komai yana da lokaci, kuma jiran lokaci abu ne mai kyau. Su sani cewa ba wanda ya isa ya yi wa wani arziki sai Allah. Saboda haka, duk wanda ya dogara ga Allah kuma ya jira lokaci, to Allah ya isar masa.

    5.1 Kammalawa
    Rayuwar matasa a wannan zamani ta zama abin takaici, kasancewar an yi sakaci baƙin al’adu sun yi wa al’adun Hausawa kutse, yadda har ta kai ga al’adunmu da muka gada tun kaka da kakanni sun fara yi mana nisa, kuma har ta kai ga sauye-sauyen sun fara barazana ga zaman lafiyarmu. Tun da farko, manufar wannan takarda ita ce gano sauye-sauyen ɗabi’u tsakanin matasa, da kuma irin barazanar da yake yi ga zaman lafiya. Tun da farko an yi ƙoƙarin kawo bayanai kan matasa a jiya wato a rayuwar gargajiya, sannan aka kawo bayanai kan rayuwar matasa a yau da yadda zamani ya yi tasiri a kansu. Daga bisani an kawo irin miyagun halayen da matasa kan tsunduma ciki da kuma abin da yake haifarwa. Sannan kuma an yi ƙoƙarin gano dalilan da suke haifar da waɗannan sauye-sauyen ɗabi’un. A ƙarshe an kawo shawarwari da ake ganin su ne mafita ga waɗannan matsalolin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.