Akwai
ƙananan
sana'o'i waÉ—anda masu kuÉ—inmu na yau duk sun yi su, amma sun yi
sana'o'i da yawa a bayansu. Na ga wani mai arziƙi aka ce
wanki-da-guga ne silar arziÆ™insa. Da na bincika sai na…
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 26: Kai ne Farko
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
In har za mu nemo hanyar cin
nasara a rayuwa kai ne farko, domin kai ne za ka fara laluben inda take ka hau
hanyar nemanta, wasu cikinmu suna ganin cewa in ka ji ana maganar nasara to a
neman aure ne ko wasan motsa jiki, tabbas an fi samun nasara idan akwai gasa,
amma wace gasa ce ta wuce mutum ya sami abin da yake so a rayuwa? Duk masu ƙoƙarin
cin nasarannan da kake ji kowa haƙilonsa
shi ne ya sami abin da yake so a rayuwa, na zauna da wanda bai da wani zance
sai ya zama mai kudi, ma'aikacin gwamnati ne, ya ƙi
komawa makaranta ya ƙaro
karatu, arziƙin mahaifinsa ya
karye bare a yi maganar gado, baida sana'a bare mu ga nau'in sana'ar da kuma
gudunta wurin isa ga nasarar da yake nema.
.
Akwai ƙananan sana'o'i waɗanda
masu kuÉ—inmu
na yau duk sun yi su, amma sun yi sana'o'i da yawa a bayansu. Na ga wani mai
arziƙi aka ce wanki-da-guga ne silar arziƙinsa. Da na bincika sai na ji ya yi wasu
sana'o'in barkatai a tsakiya, na ga wani matashin dakta a ilimi da na tambaye
shi yadda aka yi ya isa wannan matsayin, sai ya fara ba ni tarihinsa wanda na
ji har ƙasashen maƙwabtammu
ya zaga don neman nasara a rayuwa, ya sheda min cewa burodi yake sari yana
sayarwa, ya yi wasu sana'o'in kafin ya dawo ya riƙi
karatun da yake dogoro a kansa yanzu?
.
Kai dai ka lura wace sana'a
ce za ka fara don ta zama maka gada wurin isa inda nasara take? In ka tara masu
kudi kowa za ka ji hanyar arziƙinsa
saban ce, akwai shahararrun mawaƙa da
na gani suka ce daga almajirci suka zarce, ka ga dai kamata ya yi a ce sun zama
malaman Ƙur'ani, to ba su kaɗai
ba, na ma ga wasu masu abin hannunsu, arziƙi ya
kankama kuma suka ce daga almajirci suka fara, kowa kuma ya san almajirci ba
sana'a ba ne bare a fara tunanin yana kawo arziƙi ko
bai kawowa, uwayensu kan turo su ne sai yadda hali ya yi, ko karatu ko wani
abin, duk abin da yaro ya fara bude ido da shi to shi ne zai zama mafarin
tafiyarsa da zai riƙa
takawa yana hango nasara da shi.
.
1) Yanzu dai a matakin farko
ka fara amincewa kana son ka dogara da kanka, ba wai jira kake a raba gado ka
samu a sama ba, ko hakan ne ma ka sani in har aka ba ka kasonka dole ka riƙa ririta shi kana ƙara yawansa, ƙoƙarin
da za ka yi wurin ba wa dukiyar kariya ta rurin ƙara
yawanta ya fi wanda za ka yi a lokacin da kake neman na kanka wahala, don haka
yi ƙoƙari
ka kama sana'a, fitar da burin cewa za ka gaji kudi, ko tsammanin wani zai
taimake ka, yi ƙoƙari neman na kanka ya zama maka jiki
kafin ka riƙe wata dukiya da za
ta shigo maka daga baya, da za ka riƙe
kantinka da ka habbaka shi shi cikin shekara 17, ka miƙa shi ga wanda mai san kan sana'ar ba,
ka ba shi shekara daya tal ka dawo ka ga inda ya kai.
.
Yi ƙoƙari
ka gano inda ka fi rauni, in ba ka son abokanka su riƙa ganinka kana ƙananan sana'o'i to ka nemi irin sana'ar
da za ka zauna wuri guda kamar tela, tsaron kanti da sauransu, kar ka dauki
kabu-kabu ko yaron mota ko sayar da gwanjo wuri -wuri, ka amince wa kanka
tabbas kana son sana'ar, kuma za ka iya yin alfahari da shi a ko'ina ne, in
mace ce kake nema ka gamsar da zuciyarka cewa da sana'ar za ka ciyar da ita,
daganan sai tsarin yadda za ka tafiyar sana'ar ba tare da tsoron komai ko kowa
ba.
.
In ka fara sana'ar za ka ga
wasu matsaloli a tsakiya kar ka damu, ka sami ƙarfin
gwiwa kawai, ina yaro na yi sha'awar bara yadda na ga sa'o'ina yara suna neman
na kansu kuma suna iya yi wa kawunansu wasu abubuwan duk da cewa suna nesa da
mahaifansu, mu kuwa muna gaban uwayen ba iya tsinana komai, ranar farko da na
fita aka kama ni a gida na ji jiki, bayan wasu lukuta kuma na yanke zama yaron
mota, har na sami wanda zan riƙa
bi, amma da yaron gidansa ya zo haka ya ce min na sauka, daganan na karaya na
koma gida, banda wannan ma na taba zuwa gona na siyo rake na je kasuwa, don in
sayar in sami na rufin asiri, amma ni da kaina na saka rakennan a gaba na
shanye kayana, wanda na sayar kuma na
cinye kuÉ—in,
shi ma dai ban ci nasara ba.
.
Bayan na ƙara wasu 'yan shekaru sai na fahimci da
a ce na sauko da kaina ƙasa na
bi É—ayan
abokaina da yake É—ayan sana'o'in da na yi
dinnan, na koyi aikin sosai, na kuma san yadda zan yi manejin rayuwa ƙila da hakan bai faru ba, amma duk da
haka na gode wa Allah, domin na yi karatun rayuwa, wajen fadi tashina na sami
wurin da na maƙale har na kawo
matsayin da nake ciki yanzu, akwai wani yaro da ya yi rayuwa kusan irin tawa
amma ya fi ni natsuwa, ban san sana'o'in da ya yi a baya ba, amma na fara
ganinsa da 'yan faya-fayen bidiyo na wasan Hausa yana yawo da shi, da yake yana
samun ciniki a kasuwar unguwarmu sai ya yi wani É—an shago
É—an mitsili
wanda ko shi bai iya shiga, sai dai ya jera faya-fayen in za a saya ya ciro wa
mutum ya ba shi.
.
A hankali ya fara kawo man
shafawa da 'yan turarurrukan mata yana sayarwa, maganar da muke yi, ya kama
shago a daya hannun ya maƙare
shi da nau'ukan turare, yana kan hanyar nasara, akwai wata mata da na san ta
auri wani mutum, mu a waje muna kallon soyayyar da suke sha kuma tsuna burge
mu, amma a cikin gida auren na lilo yana ƙoƙarin balgacewa, ba abin da ta rasa na ci
da sha da sutura, kudi kuma sai dai ta ba wasu, komai take so gashinan, sai dai
tana da matsalar shimfida, 'yan uwanta ba su ganin wannan wani abu ne, na ce
ita ce da kanta za ta fara nemo wa kanta hanyar nasara.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.