Ticker

6/recent/ticker-posts

Manufofin Jami’yyun Siyasa a Ƙarni Na 21: Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa


Kowace jam’iyyar siyasa da aka kafa tun daga samun ‘yancin kan Nijeriya zuwa yau an kafa ta ne bisa wasu ayyanannun manufofi da tsare-tsare waɗanda jam’iyyar za ta bi, kuma da su ne za ta riƙa tallata hajarta ga al’umma domin su amince su zaɓe ta. Yawanci waɗannan manufofin su ne kan zamo alƙawuran da ‘yan siyasa ke yi wa al’umma don neman ƙuri’unsu. Ire-iren waɗannan alƙawura ba su wuce hanyoyin kyautata rayuwar al’ummar ba. Kowace jam’iyya takan tsara manufofinta a rubuce, daga bisani sai a raba ga jama’a, wasu kuma sai dai idan an tafi yaƙin neman zaɓe za su ji manufofin jam’iyyar a bakin ‘yan takara ko ‘yan siyasa ko magoya bayansu ko kuma mawaƙansu da na jam’iyya. Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo manufofin jam’iyyar PDP daga bakin marubuta waƙoƙin Hausa, domin ganin irin rawar da marubuta waƙoƙin suke takawa wajen tallata jam’iyyun siyasa ga al’umma a wannan ƙarni da muke ciki, wato ƙarni na 21.


Manufofin Jami’yyun Siyasa a Ƙarni Na 21: Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa

Jibril Yusuf
Department of Nigerian Languages and Linguistics,
Kaduna State University, Kaduna.
Phone No: +2347030399995

Taƙaitattun kalmomi:
PDP- Peoples Democratic Party
G-18- Group of 18
G-34- Group of 34
EFCC- Economic and Financial Crimes Comission.
UNCP- United Nigerian Congress Party
DPN- Democratic Party of Nigeria
GDM- Grassroot Democratic Moɓement
NCPN- National Centre Party of Nigeria
CNC- Congress for National Concensus

1.0       Shimfiɗa
Kowane allazi na ga da amanunsa,
Sai da bindiga soja yake tsiyarsa,
Shi maƙeri mai noma ne gwaninsa,
     Haka jam’iyya sai da mawallafi ta ja daga.
(Waƙar Shegiyar Uwa ta Haruna Aliyu Ningi)
Nazari a kan rubutattun waƙoƙin Hausa ba sabon abu ne ba a fagen nazarin Hausa, musamman idan aka yi la’akari da irin rawar da masana da manazarta suka taka wajen fito da muhimman abubuwan da waɗannan rubutattun waƙoƙi suka ƙunsa. Masana irin su Hiskett (1975) da Yahya (1987) Birniwa (1987) da Birnin Tudu (2001) da Usman (2008) sun yi wannan nazari ne ta la’akari da yadda marubuta waƙoƙin suka baje kolin basirarsu ta hanyar jeranta zance cikin hikima da basira wanda suka kira shi zubi da tsari da kuma nazarin harshen waƙa wato salo, sai kuma nazarin irin saƙon da mawaƙi ke son isarwa ga al’umma wanda a harshen nazari aka kira shi jigo. Yawancin nazarce-nazarce da ayyukan da aka gudanar kan abin da ya shafi rubutacciyar waƙa an gudanar da su ne ta waɗannan hanyoyi, wato nazarin zubi da tsari da salo da kuma jigo. Irin wannan nazari kuwa ya shafi har da waƙoƙin siyasa, waɗanda su ma an yi ayyuka da dama kansu, kuma an fito da abubuwa masu yawa waɗanda duniyar nazari ke amfana da su[1].
Duk da irin yadda manazartan suka bayar da gagarumar gudunmawa kuma abin yabawa, kasancewar ilimi kogi, wannan ya sa ba a sami wani aiki da aka gudanar da ya fito da manufofin wata jam’iyyar siyasa guda daga cikin rubutattun waƙoƙin siyasa ba. hakan na daga cikin dalilan da suka sanya aka gudanar da wannan nazari. Wannan takarda mai taken ‘Manufofin Jami’yyun Siyasa a Ƙarni Na 21: Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa’ ta fito da abubuwan da suka shafi manufofin jam’iyyar PDP ne kamar yadda suke a cikin kundin manufofi da tsare-tsarenta, kamar dai yadda mawaƙan suka bayyana a cikin baitocin waƙoƙinsu. Amma da farko an waiwayi tarihin kafuwar Jam’iyyar PDP a taƙaice.
1.1       Kafuwar Jam’iyyar PDP
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1984 wanda ya kawo ƙarshen mulkin farar hula a wancan lokacin, sojojin ne suka ci gaba da jan ragamar shugabancin Nijeriya. Duk da cewa an samu wasu daga cikin shugabannin mulkin soja waɗanda suka yi yunƙurin gudanar da wani irin tsarin mulki mai kama da angulu da kan zabo, Misali; Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Sani Abacha, amma wannan yunƙuri nasu bai yi tasiri ba (Ɗangulbi, 2003).
An fara tunanin kafa jam’iyyar PDP ne daga wani dogon nazari da ƙungiyar waɗansu mutane mai mambobi sha takwas waɗanda suka kira kansu da suna G-18 suka yi kan irin yadda al’amuran Nijeriya ke tafiyar hawainiya a tsakankanin shekarar 1998 ƙarƙashin mulkin soja, wannan yananyin mambobin na ganin ya haifar da koma baya ga harkokin tafiyar da ƙasar. A watan Fabrairu na shekarar 1998, sai mambobin suka yanke shawarar rubuta wa shugaban mulkin soja na wancan lokaci wato Janar Sani Abacha takarda mai ɗauke da bayanan irin ɗimbin matsalolin da ƙasar ke ciki, da kuma irin halin damuwa da al’ummar ƙasar ke ciki na ƙuncin rayuwa. Haka kuma, takardar tasu ta ƙunshi bayanai da suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda Janar Abacha ya tilasta wa jam’iyyu biyar ɗin da aka kafa a lokacinsa tsayar da shi a matsayin ɗan takaran shugaban ƙasa, a wani yunƙuri nasa na komawa mulkin farar hula. Wannan ƙungiya ta G-18 sun bayyana a cikin takardar tasu cewa, idan har shugaban ƙasar na so ya yi mulki ƙarƙashin farar hula to sai dai ya sauka, ya kuma tsaya takara a ƙarƙashin ɗaya daga cikin jam’iyyun nan biyar[2].
Wata guda bayan wannan takarda da G-18 suka rubuta wa shugaba Abacha, sai suka ci gaba da tuntuɓar wasu masu ra’ayi irin nasu, kafin wani lokaci sun samu ƙarin magoya baya. Bayan nan sai suka sake rubuta wa shugaban ƙasa takarda, amma a wannan lokaci sun kai su talatin da huɗu, inda suka yi wa kansu laƙabi da G-34.
Ana cikin wannan yanayi ne, sai kwatsam Shugaba ƙasa Janar Sani Abacha ya rasu a ranar 8 ga watan Yuni, 1998, wanda hakan ne ya kawo ƙarshen yunƙurin wannan gwamnati na zarcewa da mulki a tsarin farar hula. Bayan Janar Abdulsalami Abubakar ya karɓi ragamar mulkin ƙasar a sanadiyyar rasuwar Janar Abacha, sai ya samar da hanyoyin tuntuɓar juna a tsakanin ƙungiyoyin siyasa daban-daban, wanda a ƙarshe dai aka samu matsaya kan miƙa mulki hannun farar hula. Shugaba Abdulsalami kuma ya kafa kwamitin da zai yi aiki har na tsawon watanni goma sha ɗaya wajen tsara yadda za a miƙa mulki, wanda kuma zai ƙare aikinsa ranar 29 ga watan Mayu, 1999. An sanar da rushe dukkan jam’iyyun siyasa biyar da tsohuwar gamnatin Abacha ta kafa, sannan aka ba da damar yin taruka domin kafa jam’iyyun siyasar da za su gwada ƙwanjinsu a zaɓen da za a gabatar a gaba.
Wannan ƙungiya ta G-34 ta ci gaba da yaɗa manufarta na fafutukar komawa ga mulkin dimokuraɗiyya, inda ta yi nasarar samun haɗin kan wasu ƙungiyoyin siyasa da dama. A ranar 19 ga watan Agusta, 1998 waɗannan ƙungiyoyi suka gudanar da taro a wani ɗakin taro da ke otal ɗin Sheraton a birnin Abuja, inda suka yi matsaya, kuma suka amince da zama ƙarƙashin inuwa guda ta hanyar kafa jam’iyyar siyasa wadda za ta shiga zaɓen shugaban ƙasa a fafata da ita. Ƙungiyoyi da dama ne suka dunƙule wuri guda. Fitattu daga cikinsu su ne: All Nigerian Congress (ANC) da Peoples Consultatiɓe Forum (PCF) da Social Progressiɓe Party (SPP) da People National Front (PNF) da wasu da dama ne su ne suka haɗu suka kafa jam’iyyar da aTurance ake kira Peoples Democratic Party (PDP)[3]. An yi bukin ƙaddamar da jam’iyyar ranar 31 ga watan Agusta, 1998 a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa (International Conference Centre) da ke Abuja, inda aka sanya Cif Dr Aleɗ Ekwueme a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa, sai kuma Farfesa Jerry Gana a matsayin sakataren kwamitin (Odunayo, 2016).
1.2       Su Wa Suka Kafa Ta?
Dangane da su wa suka kafa jam’iyyar PDP kuwa, kamar yadda aka bayyana a baya ƙungiyar wasu mutane ne da ake kira G-34 tare da wasu ƙananan ƙungiyoyi kusan guda 125 ne suka haɗu suka kuma amince da kafa jam’iyyar (Odunayo, 2016). Kodayake, yawanci an fi danganta kafuwar jam’iyyar ga mambobin ƙungiyar G-34, ba don komai ba sai kasancewarsu kanwa uwar-gami dangane da fafutukar neman komawa ga salon mulkin dimokuraɗiyya.
Waɗanda aka tabbatar su ne mambobin G-34, waɗanda kuma ake alaƙanta kafuwar jam’iyyar PDP zuwa gare su, su ne:
1. Abubakar ƊanMusa 2. Abubakar Olusola Saraki 3. Abubakar Rimi 4. Adamu Ciroma   5. Ahmadu Ali 6. Aleɗ Ekwueme 7. Aminu Wali 8. Ango Abdullahi 9. Atiku Abubakar    10. Audu Ogbe 11. Bamanga Tukur 12. Barnabas Gemede 13. Bello Kirfi 14. Bola Ige
15. Daniel Saro 16. Garba Nadama 17. Isiyaku Ibrahim 18. Iya Abubakar 19. Iyochia Ayu 20. Jerry Gana 21. Jibril Aminu 22. Jim Nwobodo 23. Lawal Kaita 24. Musa Musawa     25. Sani Zangon Daura 26. Solomon Lar 27. Sulaiman Kumo 28. Sule Lamido 29. Sunday Awoniyi 30. Tanko Yakasai 31. Tom Ikimi 32. Tony Aneni 33. Walid Jibril 34. Yahaya Kwande.[4]
Waɗannan su ne suka kafa jam’iyyar PDP.
1.3       Manufofi Da Tsare-Tsaren Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa
Kowace jam’iyyar siyasa da aka kafa an kafa ta ne bisa wasu ayyanannun manufofi da tsare-tsare waɗanda jam’iyyar za ta bi, waɗanda kuma da su ne za ta riƙa tallata hajarta ga al’umma domin su amince su zaɓe ta. Yawanci waɗannan manufofin su ne kan zamo alƙawuran da ‘yan siyasa ke yi wa al’umma don neman ƙuri’unsu. Ire-iren waɗannan manufofi ba su wuce hanyoyin jin daɗi da kyautatuwar rayuwar ‘yan ƙasa ba.
Kowace jam’iyya takan tsara manufofinta a rubuce, daga bisani sai a raba ga jama’a, wasu kuma sai dai idan an tafi yaƙin neman zaɓe ko a cikin waƙoƙi za su ji manufofin jam’iyyar a bakin ‘yan takara ko ‘yan siyasa ko magoya bayansu ko kuma mawaƙansu da na jam’iyya. Kamar yadda Shu’aibu Idris ‘Yammedi ya ce;
Jam’iyya masoyan Allah ka zo al’umma ga ta,
Jam’iyya a kan manufar alheri ta yi tsarinta,
Jam’iyyar da babu ruwanta da zaluncin mazalunta,
PDP farar aniya ta zo domin mazanmu da mata.
 (Shu’aibu Idris ‘Yammedi; waƙar Bakandamiya).

A wannan baitin, mawaƙin ya nuna mana cewa jam’iyyar da yake waƙewa fa tana da manufofi da tsare-tsare waɗanda ta shirya su domin jin daɗin al’ummar ƙasa baki ɗaya, don haka mawaƙin ya nuna cewa ya kamata ‘yan ƙasa su fito su rungume ta domin kuwa da manufar alheri ta zo.
A nan za a yi ƙoƙarin fito da manufofin da aka kafa jam’iyyar PDP ne a kansu daga cikin rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa, sannan a ga irin rawar da jam’iyyar ta taka wajen aiwatar da manufofin nata.
Kamar yadda aka bayyana, jam’iyyar PDP jam’iyya ce da aka kafa ta a kan manufofi da tsare-tsare waɗanda za a bi domin samun nasara a zaɓe da mulki baki ɗayansa. Daga cikin manufofin nata, jam’iyyar ta yi wa ‘yan ƙasa alƙawura da dama da suka haɗa da:
-          Tabbatar da kyakkyawan tsarin dimokuraɗiyya wanda ya ƙunshi kyautata tsarin zaɓe da tabbatar da zaɓen gaskiya da sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma tabbatar da mulkin gaskiya.
-          Samar da cikakken ‘yanci ga al’ummar ƙasa da kuma girmama ɗan’Adam.
-          Tabbatar da adalci da daidaito tsakanin al’ummar ƙasa ba tare da nuna bambancin yare ko ƙabila ko yanki ba.
-          Samar da ci gaban ƙasa ta hanyar:
a-      Kyautata fannin ilimi.
b-     Kiwon lafiya.
c-      Samar da isasshen abinci ga ƙasa
d-     Bunƙasa masana’antu.
e-      Samar da tsaftataccen ruwan sha.
f-       Samar da gidaje ga ‘yan ƙasa.
g-     Samar da aikin yi.
h-     Inganta fannin sufuri
i-       Samar da ingantaccen wutan lantarki da kayayyakin more rayuwa
j-        Tabbatar da haɗin kan ‘yan ƙasa ta hanyar kawar da bambancin addini ko ƙabila.
k-     Tabbatar da mulkin karɓa-karɓa daga wani yanki zuwa wani.
l-       Bai wa fannin shari’a cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu, ba tare da yi musu katsalandan ba.
m-   Bunƙasa fannin haƙar ma’adinai.
n-     Inganta fannin tsaro.
o-     Inganta fannin tattalin arziƙi, da sauransu.[5]
Waɗannan suna daga cikin irin tsare-tsare da manufofin jam’iyyar PDP waɗanda aka kafa jam’iyyar a kansu, sannan mawaƙan jam’iyyar da dama sun tabbatar da waɗannan [6]manufofi a cikin waƙoƙinsu, ta hanyar yabon jam’iyyar da nuna irin lagwadar da ke ƙunshe a cikinta wadda ‘yan ƙasa za su mora idan suka amince suka zaɓe ta.
Akwai mawaƙa da dama da suka taka muhimmiyar rawa wajen tallata manufofin jam’iyyar PDP musamman daga kafuwarta a 1999 zuwa 2015. Yawanci mawaƙan sun yi la’akari da manufofin jam’iyyar ta ayyana ne wajen bayyana su cikin waƙoƙinsu. Daga cikin mawaƙan jam’iyyar PDP da suka yi fice wajen tallata manufofinta akwai; Haruna Aliyu Ningi wanda haifaffen garin Ningi ne ta jihar Bauchi, kusan shi ne ya fara tallata jam’iyyar PDP da waƙoƙinsa irin su “Iyata Sarauniya” da “Waƙar Ƙalubale” har ta sa mu karɓuwa ga al’umma. Sannan akwai Lawan Inusa Gwarzo, mutumin Gwarzo ne ta jihar Kano, ya yi wa jam’iyyar PDP waƙoƙi da dama, cikinsu akwai waƙar “Himma Ba Ta Ga Raggo” da sauransu. Bari mu ga yadda manufofin jam’iyyar suka fito cikin baitocin wasu waƙoƙin nasu.
1.3.1    Samar da Zaman Lafiya da Tsaro
Babu wata ƙasa ko al’umma wadda za ta rayu, ta bunƙasa ta dukkan fannoni zamantakewa ba tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Wannan ne ma ya sa masu hikimar magana kan ce ‘Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki’. Samun zaman lafiya kuwa kan tabbata ne ta hanyar samar da ingantaccen tsaro ga al’ummar ƙasa, wanda ya haɗa da tsaron lafiya da na dukiyoyinsu. Ke nan, zaman lafiya shi ne ginshiƙin duk wani ci gaba da ake nema, wanda idan babu shi to ba za a taɓa samun ci gaba da zai amfanin al’umma ba. Misali; a cikin waƙar “Himma Ba Ta Ga Rago” ta Lawan Inusa Gwarzo, ya fito da manufofin jam’iyyar PDP domin ‘yan ƙasa su lura da irin garaɓasar romon dimokuraɗiyyar da za su samu idan suka zaɓi shugabanni a ƙarƙashin tutar jam’iyyar. Dubi abin da ya ce;
Duba ka gani hoton laima ce,
Mai ja da fari koren launi ce,
Mai ba jama’a dukkan haƙƙi ce,
Don ba da tsaro, ilimi da sana’u laima zan zaɓa.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago).

A nan mawaƙin ya fito da wasu muhimman manufofin jam’iyyar waɗanda suka haɗa da tsaro wanda ya ƙunshi na rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa, wanda sai ya samu ne sauran al’amuran ci gaba kamar su; ingantaccen ilimi da kuma sana’o’i don kashe zaman banza da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai za su iya samuwa.
Bugu da ƙari, ta fuskar tsaro wani mawaƙi ya nuna a cikin baitinsa cewa, jam’iyyar za ta kawar da duk wasu masu tayar da ƙayar baya, wanda hakan zai ba wa ‘yan ƙasa ‘yancin walwala mazansu da matansu kamar yadda ya fito a waɗannan baitocin;



Mai sa talaka ya samo ƙima,
Mai sanya matasa ɗaukar himma,
Don ba da tsaro ga dukkan al’umma,
Don kau da tsageranci a ƙasa laima zan zaɓa.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago).

A cikin baitin da ke sama, mawaƙin ya nuna cewa jam’iyyar PDP za ta magance tsagerancin masu tayar da ƙayar baya, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin ƙasa.
1.3.2    Samar da Abubuwan More Rayuwa
‘Rai dangin goro ne sai da yayyafi’. Kowace al’umma tana buƙatar rayuwa cikin jin daɗi da walwala. Haƙƙin kowace gwamnati ce ta tabbatar ta samar wa al’ummarta abubuwan da za su rayu da su cikin jin daɗi ba tare da matsi ba. Waɗannan abubuwa sukan kasance abubuwa ne waɗanda ɗan’Adam yake buƙatarsu domin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da wahalarwa ba. Waɗannan buƙatu sun haɗa da; tsaftataccen ruwan sha, da wutar lantarki da ingantattun hanyoyi (tituna) don sauƙaƙa sufuri da zirga-zirgan jama’a da samar da jari da sana’o’i ga ‘yan ƙasa da sauransu. Mawaƙan jam’iyyar PDP sun fito da waɗannan abubuwa a cikin wasu daga cikin baitocin waƙoƙinsu. Wani mawaƙi Lawan Inusa Gwarzo ya ce;
Don kau da matsi a cikin al’umma,
Don ba da wuta da ruwa mai dama,
Don ba wa manoma kayan noma,
Domin bunƙasa sana’un mata laima zan zaɓa.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago).

A sai mawaƙin ya nuna cewa manufar jam’iyyar PDP ita ce ta kyautata rayuwar al’umma ta hanyar kawar da halin ƙunci da ake ciki, da samar da wutar lantarki ingantaccce da kuma ruwan sha yalwatacce mai tsafta. Ya kuma nuna cewa, yana daga cikin manufofin jam’iyyar inganta fannin noma, hakan zai tabbata ne kuwa ta hanyar bai wa manoma kayan noma wanda zai taimaka musu wajen samun sauƙin ayyukan noman. Sannan kuma ya ce har mata ma ba za a bar su a baya ba, jam’iyyar za ta samar musu da sana’o’i domin dogaro da kawunansu.
Ta fannin sufuri da albarkatun ƙasa da muhalli ma Lawan ya nuna cewa duk jam’iyyar idan ta hau gadon mulki za ta kyautata su. Ya ce;
Don kyautata titi ingantacce,
Don yalwata fetur mai tatacce,
Sauya ƙasa tsari tsaftatacce,
Don ba taka jari da muhalli laima zan zaɓa.

Don kau da matsi a cikin al’umma,
Don sa jama’a bisa hanyar nema,
Domin sufuri a ƙasa ya yi dama,
Don gyaran dukkan masana’antunmu laima zan zaɓa.

Duk mai neman ƙasa a yi gyara,
Mai son yaninmu ya zarce tsara,
Don kauce a kwashe kuɗi a ci gara,
Don sanya ƙasa a tafarkin sauƙi ba ha’inci ba.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago)

A nan mawaƙin ya nuna cewa ai manufar jam’iyyar ita ce ta kyautata rayuwar ‘yan ƙasa ta hanyar sama musu ayyukan yi wanda za su dogara da kawunansu da hanyoyi masu kyau da yalwataccen man fetur a ƙasa domin kyautata sufuri. Za a tabbatar an kauce wa tsarin handama da babakere da rub-da-ciki da dukiyar ƙasa domin kawar da ha’inci.
Wutar lantarki yana daga cikin abubuwan da suka daɗe suna ci wa ‘yan ƙasa tuwo a ƙwarya, wannan ya sa daga cikin manufofin jam’iyyar PDP akwai samar da ingantaccen wutar lantarki a ƙauyuka da biranen ƙasar nan. Haka kuma daga cikin manufofin akwai samar da muhalli ga ‘yan ƙasa domin samun jin daɗin rayuwa. Sai kuma yaƙi da cin hanci da rashawa wanda ya zama ruwan dare a cikin a cikin ƙasar, wannan ya sa da kafuwar jam’iyyar PDP sai ta sanya shi cikin manufofinta cewa za ta tabbatar ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa da rub-da-ciki a kan dukiyar ƙasa. Wannan dalilin ne ya sa aka kafa hukumar yaƙi da cin hanci da zambar kuɗaɗe wato EFCC a Turance, kamar yadda za a gani a baitin da ke biye;
Wa ke gyaran nefa a ƙasata,
Wa ke jawo teku don gata,
Wa yai EFCC hana sata,
Domin inganta kuɗin jarinmu laima zan zaɓa.

Na tabbata laima ta fuce saura,
Gun kawo alheri ga gyara,
Ta ɗauki salon warkar da lalura,
Domin manufar samar da muhallai laima zan zaɓa.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago)

Fannin sadarwa ma ba a bar shi a baya ba, domin kuwa jam’iyya ta sanyo shi gaba-gaba cikin manufofinta inda ta nuna cewa za ta bai wa wannan fannin muhimmanci. Dubi wannan baitin;
Da batun ilimi, lafiya yana nan a rubuce,
Da noma, hanya, ruwa mayanci ni’ima ce,
Da kullum ƙaunarmu za mu samar a wadace,
Da sadarwa don mu rinƙa ɗan sa da zumunta.
 (Haruna Aliyu Ningi; waƙar Iyata Sarauniya)[7].
A cikin wannan baitin mawaƙin ya kawo manufofi da dama, inda a layin ƙarshe na baitin sai ya nuna cewa jam’iyyar za ta bai wa fannin sadarwa muhimmanci, domin kyautata zamantakewa ga ‘yan ƙasa.


1.3.3    Kiwon Lafiya
‘Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke’. Lafiya abu ne muhimmi a rayuwar ɗan’Adam, wanda idan babu ita to babu wani abu da za a iya aiwatarwa, kuma rayuwa ba za ta yi daɗi ba sai da ita. Yana daga cikin manyan haƙƙoƙin kowace gwamnati ta tabbatar ta kula da kiwon lafiyar jama’arta, ta hanyar giggina asibitoci da wadata su da magunguna da kuma samar da ƙwararrun ma’aikatan jinya, waɗanda za su riƙa kula da marasa lafiya.
 Ta fuskar kiwon lafiya, mawaƙan sun bayyana manufar jam’iyyar PDP na inganta wannan fannin. Sau da yawa idan mawaƙan za su ambaci manufofin jam’iyyar sukan haɗa da kiwon lafiya, wannan ya sa kusan duk baitin da aka kawo misali da shi akan samu an ambaci kiwon lafiya a ciki. Misali, Haruna Aliyu Ningi ya fito da wannan manufa fili a cikin wani baitin waƙarsa. Dubi abin da ya ce;
Ruwan shanmu da lafiyarmu ‘yanci ta tanada,
Ta ce ko ɓera ya samu ciwon kai a gwada,
A sa masa magani ya sha ya yi rangwaɗa,
Ya kece kewarsa ran bikin ‘yan Nijeriya.
(Haruna Aliyu Ningi; waƙar Ƙalubale)[8].

A cikin wannan baitin mawaƙin ya nuna cewa, manufar jam’iyyar PDP shi ne ta kyautata fannin kiwon lafiya, ta yadda ya nuna cewa za a ba wa fannin lafiya kulawa sosai, ta yadda ba ma mutane ba ko ɓera ne ya yi ciwon kai za a kai shi asibiti a gwada shi a san me yake damunsa, sannan a ba shi magani. Wannan ya nuna ta bakin mawaƙin yadda jam’iyyar za ta bai wa fannin kiwon lafiya muhimmanci ne.
Shi ma Lawan Inusa Gwarzo, a fannin kiwon lafiya, ya bayyana irin tsarin da jam’iyyar ta yi domin inganta fannin kiwon lafiya, inda ya nuna a cikin wani baitin waƙarsa cewa, jam’iyyar za ta ɗauki ma’aikatan jinya domin magance ƙarancinsu a asibitoci, sannan kuma za ta gina sababbin asibitoci domin rage cinkoso. Dubi yadda mawaƙin ya kawo manufofin a cikin wannan baitin;
Tsarin lafiya ɗibar likitoci,
Samar wa ƙasa sabbin asibitoci,
Fannin ilimin boko Larabci,
Samarwa da kulawa aikin jiyya laima zan zaɓa.
(lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago).

A nan ya nuna cewa idan jam’iyyar ta yi nasarar lashe zaɓe, za ta bai wa fannin lafiya muhimmanci ta hanyar ɗiban sababbin ma’aikatan jinya. Sannan kuma za ta gina wasu sababbin asibitoci domin kulawa da marasa lafiya.
1.3.4    Inganta Fannin Ilimi da Noma

            Ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa, da shi ne ake gane duk wata hanya ta daidai da kuma tafarkin ci gaba. Muhimmancin ilimi a cikin al’umma ya wuce a misalta, domin kuwa babu wata al’ummar da za ta ci gaba ba tare da bai wa fannin ilimi muhimmanci ba.
Noma kuwa daɗaɗɗiyar sana’a ce wadda ɗan’Adam ke gudanar da ita tun can azal. Shi ya sa ake yi masa kirari da ‘Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras’. Noma sana’a ce mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan’Adam, domin hanya ce ta samar da abinci ga al’umma. Kasancewar Allah ya albarkaci ƙasarmu Nijeriya da ƙasar noma, wannan ya sa gwamnatoci kan ware wani kaso don inganta fannin. Jam’iyyar PDP ita ma ba a bar ta a baya ba, domin kuwa daga cikin manufofin jam’iyyar akwai inganta fannonin ilimi da noma, inda ta tsara cewa, za ta samar da taki ga manoma domin inganta wannan fannin. Fannin ilimi kuwa za a tabbatar an kori jahilci ilimi ya wadatu kamar ruwa a cewar mawaƙin. A nan Haruna Aliyu Ningi ya fito da manufar jam’iyyar, inda ya ce:
Batun noma za a samu taki ba gardama,
Mu noma tumatira, gyaɗa da waƙe ga alkama,
A samar ilimi kamar ruwa don ɗaga al’umma,
Ta san inda take zama haƙiƙanta a duniya.
(Haruna Aliyu Ningi; waƙar Ƙalubale).

A nan mawaƙin ya yi ƙoƙarin nuna wa al’umma ne cewa, yana daga cikin manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar PDP a fannin noma samar da wadataccen takin zamani ga manoma wanda za a noma kayan abinci domin wadata ƙasa da abinci da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa. A cikin baitin nasa ya bayar da misalin kaɗan daga irin kayan noman da za su wadata sakamakon kulawar da gwamnatin PDP za ta ba wa fannin na noma.  Sannan kuma ya nuna cewa jam’iyyar in ta yi nasarar samun shugabanci, za ta kula da fannin ilimi domin bayar da shi ga ‘yan ƙasa, ta yadda kowa zai fahimci ‘yancinsa.
1.3.5    Tabbatar da Cikakken ‘Yanci Ga ‘Yan ƙasa da Kawar da Ƙabilanci
Daga cikin manufofin jam’iyyar PDP akwai tabbatar da ingantaccen tsarin demokuɗiyya wanda ya haɗa da bai wa ɗan’Adam cikakken ‘yancin rayuwa cikin walwala, sannan kuma jam’iyya tana da manufar kawar da bambancin yare ko ƙabila da kuma ƙoƙarin kau da mulkin zalunci da tabbatar da adalci. Waɗannan manufofi sun fito a cikin wani baiti wani kamar haka;
Laima manufar ƙasa ta yi ‘yanci,
Don kau da ƙabilanci bambanci,
Don kau da dukkan mulkin zalunci,
Don gyara ɗabi’un ƙasata laima zan zaɓa.
(Lawan Inusa Gwarzo; waƙar Himma Ba Ta Ga Rago).

Shi ma Haruna Aliyu Ningi ya bayyana a cikin wani baitinsa cewa;

                        Aƙidarmu ta kyautata wa mutane,
                        Ya sa ‘yanci har ta karɓu sosai ga mutane,
                        Idan ba ita jam’iyyar ƙasar duk matsala ne,
                        A yau mun muku tanadin ta kowa ya riƙe ta.
                        (Haruna Aliyu Ningi; waƙar Iyata Sarauniya)
A nan mawaƙin ya nuna cewa aƙidar jam’iyyar PDP ce kyautatawa ga kowa. Wannan ya sa jam’iyyar take da manufar samar da, yanci ga kowa domin samun kyautatuwar rayuwa da kuma kauce wa matsalolin rayuwa, wanda mawaƙin y ace jam’iyyar ta yi wa ‘yan ƙasa tanadin wannan ‘yancin.
A cikin kowace manufa guda akwai tsare-tsare da aka tanada waɗanda suke ƙunshe cikin manufar, waɗanda kan kasance ƙarin bayani ne kan yadda wannan manufar za ta yi aiki ko yadda za a aiwatar da ita domin ci gaban al’umma.
Kamar yadda aka bayyana a baya, kowace jam’iyyar siyasa akan kafa ta ne bisa manufa da kuma tsare-tsare, wannan ya sa jam’iyyar PDP ita ma ba a bar ta a baya ba wajen shirya waɗannan manufofin wanda kan zama wa jam’iyya tamkar ɗan jagora ne da zai riƙa yi mata jagora kan ayyukan da ta yi wa al’umma alƙawari. Da waɗannan jerin manufofi da tsare-tsare ne ake iya dubawa a gane inda aka fito da inda ake, wanda zai sa a gane inda aka dosa, wato za a iya tantancewa ko dai jam’iyyar ta yi nasarar aiwatar da manufofin nata, ko kuma ta kauce wa wasu, ko kuma ta yi watsi da manufofin nata baki ɗaya.
1.4       Naɗewa
Wannan nazari ya shafi rubutattun waƙoƙin siyasa ne. A ciki an yi ƙoƙarin fito da manufofin jam’iyyar PDP ne daga bakin marubuta waƙa. Daga cikin bayanan da aka kawo a cikin takardar an ga irin manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar da kuma inda marubuta waƙoƙi suka bayyana su a cikin waƙoƙin nasu. Tun da farko an kawo tarihin faɗi-tashin da aka yi wajen kafa jam’iyyar a taƙaice. Haka kuma an rattaɓo sunayen waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP. Sannan aka tsunduma cikin nazarin inda aka kawo wasu manufofin jam’iyyar daga cikin baitocin waƙoƙi na fitattun mawaƙa da suka haɗa da Haruna Aliyu Ningi da Lawan Inusa Gwarzo. An riƙa yi ana sharhin baitocin filla-filla domin fito da bayanan da suka ƙunsa a fili.


[1] Domin ganin irin waɗannan ayyuka da aka yi kan waƙoƙin siyasa sai a duba: Birniwa (1987) da Funtua (2003) da Ɗangulbi (2003) da Ɗan’illela (2010) da Sani (2012) da Idris (2016) da Yusuf (2018).
[2] Jam’iyyun su ne; UNCP da DPN da GDM da NCPN da CNC.
[3] A dubi kundin manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar PDP (manifesto of PDP), shafi na 6-8.
[4] Hira da Dr Aliyu Tilde ta waya ranar 19/Jan/2017 da misalin ƙarfe 5:17 na Yamma.
[5] A dubi kundin manufofi da tsare-tsaren Jam’iyyar PDP (Manifesto of PDP)
[6] Waƙar “ Himma Ba Ta Ga Raggo” an yi ta a shekarar 2007
 Amshinta shi ne; “ Zaɓe- in zaɓe ya zo laima zan zaɓa”
 Tana da baitoci 32 da ɗangwaye ƙwar huɗu.
[7] Waƙar “ Iyata Sarauniya” an yi ta a shekarar 1998
 Amshinta shi ne; “ PDP Jamiyyata,
    Abar so a zukata,
    Mutanen Nijeriya ku taso mu riƙe ta”
 Tana da baitoci 57 da ɗangwaye ƙwar huɗu.

[8] Waƙar “ Ƙalubale” an yi ta a shekarar 1999
 Amshinta shi ne; “ Mu kawo ƙarshen taƙaddamar mu ta jamhuriya,
                                      Mu ɗau PDP saboda ceto Nijeriya”
 Tana da baitoci 35 da ɗangwaye ƙwar huɗu.


Post a Comment

0 Comments