Gudu A Bahaushen Tunani



    Tunanin mutane da ke bayyana a adabinsu na baka, da rubutacce wata fitila ce, ta ƙyallaro al’adun rayuwarsu. Ƙudurina a wannan bincike shi ne, in yi garkuwa da sassan adabin bakan Bahaushe, domin in leƙo irin gurbin da al’adarsa ta yi wa “gudu”; yadda yake, da yadda yake kallonsa. A cikin wannan tunanin, na gayyato mawaƙan baka (12) na sassan rukunin mawaƙa (5). Na sarrafa xiyan waƙoƙinsu (24) domin tabbatar da hasashena. Na yi wa hujjojina turke da karuruwan magana (27), na yave su da kirari (2); na ƙawata ginar da ƙagaggun labarai (2) da wassannin yara (1). Da jimillar waxannan hujjoji (67) na yi wa sakamakon bincikena turaku (6) nagartattu. Binciken ya tabbatar da gurbin “gudu” a al’adar…


    Aliyu Muhammadu Bunza
    Department of Nigerian Languages
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
    Waya: 0803 431 6508

    Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato ranar Laraba 12 ga watan Dismba, 2012, a xakin taro na mazaunin cikin gari na Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato.

    Tsakure:
    Tunanin mutane da ke bayyana a adabinsu na baka, da rubutacce wata fitila ce, ta ƙyallaro al’adun rayuwarsu. Ƙudurina a wannan bincike shi ne, in yi garkuwa da sassan adabin bakan Bahaushe, domin in leƙo irin gurbin da al’adarsa ta yi wa “gudu”; yadda yake, da yadda yake kallonsa. A cikin wannan tunanin, na gayyato mawaƙan baka (12) na sassan rukunin mawaƙa (5). Na sarrafa xiyan waƙoƙinsu (24) domin tabbatar da hasashena. Na yi wa hujjojina turke da karuruwan magana (27), na yave su da kirari (2); na ƙawata ginar da ƙagaggun labarai (2) da wassannin yara (1). Da jimillar waxannan hujjoji (67) na yi wa sakamakon bincikena turaku (6) nagartattu. Binciken ya tabbatar da gurbin “gudu” a al’adar Bahaushe; wurin da ake yin sa; abin da ake yin sa da shi, da dalilan da ke sa a yi shi. Don haka ake hangen yiyuwar saka ire-iren waxannan muhimman xabi’un rayuwa cikin manhajar koyar da Hausa a matakin ilmi mai zurfi. Haƙiƙa, babu sashe na rayuwar Bahaushe da gudu bai ratsa ba. Abin ban sha’awa, duk wata halittar da ke da rayuwa a bangon ƙasa, tana gudu, kuma ga shi, gudun ba koyonsa ake ba, cikin jiki yake gine.


    Gabatarwa:
            Tunanin xan Adam a koyaushe ba ya tsallake al’adar da ya tashi a cikinta. Fasaha da tunani da hankali makusanta ne a al’adance. Fasahar da aka koya, ko aka karanta, daban da wadda ginannan ce a jinin mai/masu aiwatar da ita. Tunani da hankali, da su ake haihuwar mutum idan ya ci nasarar samun su wadatacci. Da tunain da hankali, tabaran al’ada ke hango mizanin cikar su da batsewar su. Fasaha ko azancin da ke gine cikin jini wanda tunani da hankali ke gyara musu zama, sun haxa da irin ayyukan gavvai kamar dariya da murmushi da kuka da barci da kuwwa da susan jiki da waiwaya da ƙyalle da rego da bauxuwa da tagumi da gudu da dai sauransu. Waxannan abubuwa, al’ada ba ta tanado yadda za a koye su ba, bale keve wurin da za a koye su, da lokacin koyo. Don haka, xalibi na da damar ya dube su da idon nazari, domin rarrabe zare da abawansu. Don haka, na zavi in dubi “gudu” daga cikin ire-iren waxannan abubuwa:

    Gudu A Mizanin Nazari:
    Tunanina a nan shi ne, fayyace ganin cancantar gudu zama xaya daga cikin abubuwan da ya kyautu a xan waiwaya a farfajiyar al’ada. Gudu na daga cikin xabi’un da ke gine cikin jinin xan Adam da ba sai an koya wa mutum yadda zai yi su ba.[1] A tsarin matakan koyar da yara, a kan koyar da su zama idan sun iya a shiga xawainiyar koyon rarrafe. Idan an iya rarrafe, gwiwowi suka saba da karvar nauyin kwankwaso, sai a fara dafa ƙasa da hannuwa biyu, a xage gwiwowin sama, nauyin jiki ya sauka ga hannaye da ƙafafu.[2] Idan aka shiga wannan ajin, ƙafafu sun fara samun cikakken labarin nauyin jiki na gaba xaya. Daga nan, za a fara jarraba raba hannuwa da ƙasa a yunƙura a miƙe tsaye.[3] Bisa ga al’adar rayuwa, sai tsayi ya samu, za a yi tunanin yadda za a fara tafiya. Wasu cikin xan lokaci su saba, wasu kan ja lokaci gwargwadon yanayin da yaro ya samu kansa.[4]
    Iya tafiya, wani babban abin farin ciki ne da sha’awa ga kowane yaro. Wasu da sun fara tsayi, sai fara gudu kai tsaye, wasu kuwa, sai tafiyar ta samu, sai gudu ya biyo baya. Duk yadda halin ya kasance, ba koya wa yaro gudu ake yi ba. Ba zan musanta cewa, a kan kira yaro, a nuna masa wani abu, a ce da shi: “Rugo ka karva”. Wani lokaci a nuna masa wani abu a ce: “Ruga ka xauko”. A wasu lokuta a nuna masa abin ban tsoro, ko abin da ya so a ce: “Ruga ka je gida”. Wani lokaci a xauko bulala ko wani abin yi masa horo mamarsa ko yannensa su ce: “Wane gudu ga baba nan zuwa”. Wani lokaci a yi masa kukan kyanwa da baki: “Inyau!” idan ya nuna razana a ce: “Gudu, je gida, ga kyanwa nan.” Idan aka lura, waxannan matakan duk na koya wa yaro sanin hikimomin “ruga” da “gudu” ne.[5] Umurni ne ake ba shi, ba koyar da shi ake yi, yadda zai yi gudun ba. Idan ya yi gudun ya faxi, ba gaya masa yadda zai yi za a yi ba, sai dai a yi dariya, a sa masa ido. Idan ya yi gudun bai faxi ba, ba yaba shi za a yi ba da kalmomin ‘ka iya’, ko ‘yawwa haka’, ko ‘sannu da aiki’, dariya kawai za a yi, a sa masa ido. Wani lokaci ma a kau da huska, a ƙi kula da shi. Waxannan halaye ke nuna, ba koyar da shi ake yi ba, ana sa ran shi zai koya da kansa. Dalilin ko dalilan da suka sa Bahaushe ba ya koya wa yaronsa gudu suka sa, xalibin al’ada ya yi nazari a kan gudu ya gano musabbabin haka.[6]

    Ma’anar Gudu:
    A ganin Ƙamusun Hausa gudu ba ya da wani dogon bayani domin sananne ne. Maimakon ya fexe biri har wutsiya, misalan kalmomi ya ba da masu bayyana sigar gudu.[7] A wajen Larabawa, akwai sassaka akwai gudu, wanda a ma’anarsu gudu ya fi sassaka sauri.[8] Ta fuskar Turanci, gudu na da ma’anoni masu faxi. A fassararsu, gudu shi ne tsananka hanzari da anniya wanda ya zarce tafiya da sassaka.[9] Duk da haka, gudu a wajensu yana da ma’anoni fiye da tamani da biyar (85).[10] Fassarar Hausa ta gudu a ƙamusoshi da bayanan manazarta adabi bai yi wani dogon takin saƙa da ma’nonin da harsuna da muka gabatar suka faxa ba.[11] Haka kuma a Hausa akwai kalmomi kusan sittin da ake bayyana gudu da su a Bahaushen ma’auni.[12] A taƙaice, za mu iya cewa, gudu shi ne:
    Saka hanzari da uzuri, tare da kama jiki da anniya, wanda ya zarce sauri da sauri-sauri ya nunka sassaka, domin da jiki, da hankali, duk sun shagala ga aikin. Mafarin gudu shi ke fassara ƙwazon da aka saka ciki da gurbin hankalin mai gudu. Ƙafafu da hannuwa su ke riƙe da akalar mai gudu, xayansu duk ya kasa, hanzarin gudu zai koma sauri ko sauri-sauri ko sassaka.[13]

    Cikin wannan xan bayani, akwai abubuwan kulawa ga mai nazari. Ma’anar da muka tantance, tana bayanin gudun da ya shafi aiki da gavvai, a zahiri a ga gudun, a ga mai gudu, a san mafarin gudu, ko a ji mafarinsa, da niyyar yin sa. A al’adance, wannan ba ita kaxai ce ma’anar gudu ba. A wata fassara gudu kan xauki ma’anar:
    Tsoron wani abu a zuci da xaukar matakan kauce wa abin gwargwadon iyawa. Kauce wa wani abu, ko zuƙe masa, ko ƙin tsayara a shaide shi bayan an fara shi gaban idon mutum, duk yana xaukar ma’anar gudu.[14]

    Idan aka leƙa taskas al’ada, gudu na iya xaukar wata fassara ta uku. A fannin magani da warkarwa, idan Bahaushe ya yi amfani da kalmar gudu yana nufin “zawayi/zawo”. A al’ada, ana sakaya sunan “zawo/zawayi” da kalmar “gudu”. Idan aka ce, mutum ya kwana yana gudu, wato “ya kwana yana zawo/zawayi” ke nan. A vangaren zamantakewa, kalmar gudu na xaukar al’adar da mata budare ke yi, idan za a yi bikin aurensu su je gidan wani xan’uwa daga cikin dangi su voye, a bi su can a yi xawainiyar. Idan suka yi haka, akan ce: “sun yi gudu”. Za a iya fassara su kamar haka:
    Gudu kalmar sakayawa ce ga ambaton sunan “zawo” a Bahaushen lafazi, kuma takan kasance al’adar budare da suke yi a aurensu na farko.”[15]

    Ma’aunin waxannan fassarori uku na gudu, idan aka kalle su, kowannensu an gina shi a kan hujjarsa. Na raba waxannan ma’anoni daban-daban domin idan aka tabbatar da su[16] ana iya takura ma’anar ta gaba xaya ta kasance:
    Gudu a nahawu aiki ne da ya shafi gavvan ƙafafu da hannuwa wajen hanzartar da shi, ya xara sauri da sassaka ga anniya. Idan abin da zuciya ke tsoro aikatawa ko gani ne, da zuciya za a nuisance shi, shi ne gudun sa. Nannauyar kalmar “zawo” ana sakaya ta da kalmar gudu; a cikin sha’anin zamantakewar aure, kalmar na nufin gudun budurwar da aka sa wa ranar biki zuwa gidan danginta.[17]

    Ya kyautu a kula cewa, hawa da saukar murya cikin gavovin kalmar ‘gudu’ na sassauya ma’anoninta. Ga abin da nake nufi kamar haka:
    ·        Gudu -    guduu:         shi ne gudun da ƙafafu
    ·        Gudu -    gudu:          umurni ne na a yi gudu
    ·        Gudu -    gudu:          sunan gari ne da Shehu Xanfodiyo ya yi hijira da ya taso daga Xegel.[18]
    ·        Gudu -    guduu:        sunan zawo.
    A karin sautin waxannan, za a ji sun xan bambanta da juna ta yadda mai furuci zai iya ya rarrabe abin da yake nufi domin mai sauraro ya fahimce shi.[19]

    Falsafar Gudu A Al’adance:
    Gabanin kafa hujja da sassan adabi domin tabbatar da ƙunshiyar gudu a Bahaushen tunani, yana da kyau mu ga yadda Bahaushe ke kallon gudu gaba xaya. A hangen Bahaushe, gudu wani aiki ne da ya shagaltar da dukkanin jikin mai yin sa. Bahaushe na ganin duk lokacin da aka yi gudu:
    ·        Akwai dalilin da ya sa ake yin sa
    ·        Cikin gudu akwai alamun tsoro da firgita
    ·        Cikin gudu akwai neman kuvuta daga wani abu
    ·        Cikin gudu akwai gaggawan kai ga wani abu
    ·        Gudu uzuri ne, tilas a saurara wa mai shi
    ·        Hankalin mai gudu ragagge ne domin an shagaltar da shi
    ·        Gwargwadon abin da ya sa gudu, gwargwadon gudun da mai gudun ke yi
    ·        Gudu ba ya haxuwa da komai, da wani abu ya shiga ciki an  karya lagonsa
    ·        Idan tsoro da firgita suka  haddasa gudu, maƙurarsa samun ceto
    ·        Idan an yi shi don kuvutu, ko kai ga buƙata, maƙurarsa kai ga muradin yin sa
    A al’adance, duk gudu da ƙafa ake yin sa, kuma a ƙasa aka san da shi. Duk wani gudu da ba haka aka ko ake gudanar da shi ba, ya shiga cikin ma’anonin gudu biyu da muka gabatar. Tunanin Bahaushe a nan shi ne, dabbobi da ƙwari da tsuntsaye suna gudu irin gudun da mutane ke yi bisa dalili. Wasar doki komi tsananin gudunsa za a ce yana “sukuwa”, ko yana “kilisa” ko yana “suka”. Idan wata dabbar da ke iya kashe shi ko cutar da shi ko wata musibar gobara ta koro shi, ba za a ce yana kilisa ko sukuwa ko suka ba, za a ce yana “gudu”. Haka mutum idan yana gudu ba da wani dalili ba, ba tsoro, ko firgita, ko buƙata, za a ce, yana “motsa jiki”.

    Gudun A Faifan Adabi:
    Ƙololuwar tunanin kowace al’umma da fasaharta da falsafarta ana tsintar su a cikin adabinsu. Buƙatar da adabi ya yi wa fasahohin masu shi ba ƙarama ba ce. Da ba don adabi ba, da tarihinmu, da fasahohinmu, sun salwance mana. Taskace adabi cikin azancin labari da karin magana da salon magana da kirari da shaguve da barkwanci da gatse da baƙar magana da waƙa, shi ya sa al’adunmu na jiya suka wanzu a yau kamar ba su ratsi dogon zamani ba.[20] Ga xan waiwaye a kan wasu daga cikin waxannan sassan adabi da muka lafata:

    Karin Magana:
    Babu al’ummar da ba ta alfahari da karin maganganunta wajen daidaita al’amurran rayuwarta. Karin magana wani saƙo ne a dunƙule da ke buƙatar zazzurfan sani ga mai furta shi da mai fashin baƙinsa.[21] Duk wata matsala, ko wata haraka, ko wani abu, da al’umma ta xauka muhimmi karin magana zai ba da labarinsa.[22] Dubi waxannan misalai da “gudu” ya yi birgima a ciki:
           i.         Ruwa suna gudu aka shan su
         ii.         Hana ruwa gudu
      iii.         Ba a haxa gudu da susan baya
       iv.         Ƙafa me na ci ban ba ki ba?
         v.         Ya ci moriyar dugadugansa
       vi.         Ya sa hawan haki
    vii.         Kowa ya ci zomo ya ci gudu
    viii.         Zomo ba ya kamuwa daga kwance
       ix.         Abin da ya koro vera ya faxa wuta ya fi wutar zafi
         x.         In ka ga kurma a guje, kar ka tambaye shi, taya shi, gani ya yi, ba ji ba
       xi.         Barewa ba ta gudu xanta ya yi rarrafe
    xii.         Mutum ba ya ƙin ta mutane an ce wa varawo ya gudu
    xiii.         Iyakan gudu ƙuryar xaki
    xiv.         In ka ji ƙi gudu, sa gudu ne bai zo ba
     xv.         Banza gudun mai ƙararren kwana
    xvi.         In ba ka yi ba ni wuri
    xvii.         In ka ji: “Riƙa mini kayana” ba zawo ya koro mai kayan ba
    xviii.         Maganin ma ƙi gudu ban kashi
    xix.         Banza gudun harbabbe sai ya kai gawa nesa
     xx.         Ƙasa ta gudu ta je ina?
    Na xan tsakuro waxannan ‘yan misalai gudu ashirin domin a ga irin yadda Bahaushen karin magana ke duban gudu. Da za a tambayi masani, ko manazarci, ko xalibin karin magana, mene ne gudu a farfajiyar karin magana? Bayanin da zai bayar zai mamaye rassan gudu gaba xaya idan zai ce:
    ·        Ma’anar gudu: Wato kama jiki a uzurce kamar za a gangara daga kware ko tudu zuwa rafi irin na ruwan kogi ko gebe. Karuruwan magana na 1 da 2 sun nuna haka.
    ·        Gurbin gudu: Aiki ne mai cin gashin kansa, karin magana na 3 ya raba wannan gardama.
    ·        Da me ake gudu?: Madugai cikin gavvan jiki a gudu su ne ƙafafu, ko a ƙafar, dugadugai su ne gaba. Karuruwan magana na 4 da na 5 za su ba da haske.
    ·        Sifar gudu: Bahaushe duk zai yi wa bayanin gudu, ba a ba shi labarin zomo, ko gada ba, ba a fitar da shi duhu ba. Karuruwan magana na 7, 8, da 16 su ne turke a nan.
    ·        Dalilin gudu: Babu gudun da ba ya da mafari. Asalin mafarin gudu tsoro da buƙata da abin da ya yi kama da su. Dalilin da ke sa a yi gudu fili suke a karin magana na 9, 10, 12, 14, 15, 17, 18 da 19.
    ·        Bagiren gudu: Babu wurin da halittu za su yi gudu da ƙafafunsu sai a ƙasa. Dabbobi da ƙwari da ke sararin samaniya fiffikawa suke yi. Bagiren da ake gudu a fili yake a karin magana na 20.
    ·        Gurbin gudu: Aiki ne mai cin gashin kansa. Ba ya haxuwa da wani aiki. Karin magana na 2 zai kakkave wa tunani ƙura a nan.
    Ina ganin waxannan matakai bakwai da muka bi muka fexe ƙunshiyar gudu a karin magana, wani haske ne ga tunaninmu xalibai da masananmu cewa, gudu ya cancanci ya samu bagiren nazari cikin karatun Hausa. Tunanina ke nan na fara gabatar da wannan ‘yar ƙwarya-ƙwaryar takarda a matsayin zakaran gwajin dahi.
    Kirari:
    Bayan karin magana, babu wani sashe na adabin baka da ya kai kirari muhimmanci ga taskace jiya domin na yau su yi nazari. Duk da yake an rubuta muƙalu da dama a kan kirari, xaliban Hausa ba su taka kara suka karya ba a binciken kirari a matakan babban digiri.[23] Ga xan misalin abin da muke lalube a kirarin wani tauraron Garba Xanwasa Gumi yana cewa:
              Banza gudun kare mai tsoro
              Ko ya cika ba ya kama ba.

    A kirarin wani xan tauri na makaxa Xanbuga na Sabon Sara cewa yake yi:
              Kowa ya bar mu
    Don wuya ya bar mu
    Mu ka ba mattace kashi
    Mai rai da ya gani, to shi tsaya!
    Xan falgacen babban burar uba

    Waxannan misalai biyu za su ba mu hoton gudu a Bahaushen tunani. A kirari na farko, mun ga idan aka koro abu, da wanda aka koro, duk gudu suke yi. Wanda aka koro dalilinsa na gudu neman ceto, ko kuvuta. Wanda ya koro shi dalilinsa na gudu kai ga muradinsa. Kirari na biyu na gaya muna abin da mutum zai gani, ya gudu, ko da ba a ba shi shawarar gudu ba. Haka kuma, ko da a zahiri, ba a ce ya gudu ba, Bahaushe ya san gudu aka yi. Wa zai tarar da ana dukan wanda ya mutu ya tsaya? Yaya za a yi ya yi tafiya, bayan ya ba da baya? Tabbas! Ko bai san ya yi gudu ba, aguje yake, domin duk abin da bai ƙyale marigayi ba, ba zai ji tausan mai rai ba.[24]
    Ratsen Gudu A Azancin Waƙoƙin Baka:
    Azantaccen mutum, zai iya tsara azanci, a azantu da shi, har a ƙyallaro wani rumbun azanci a tsarin tunanin azancinsa. A fagen adabi, waƙa ita ce akalar azanci, duk wani azanci jaye take da shi, kamar yadda akala ke jaye da raƙumi ta hannun madugunsa.[25] Don haka, waƙoƙin baka wata hujja ce daga cikin hujjojin yadda al’umma ke kallon abubuwa. Cikin wannan bagire, waƙa ba ta raga muna hakin susa ba, ta fuskar yadda Bahaushe ke ganin gudu. Masana waƙa sun karkasa waƙoƙin Hausa zubi-zubi gwargwadon wurin da jigoginsu suka rinjaya; duk da yake akwai daxa juna sani a kan kashe-kashen da za mu xora tunaninmu a kansu.[26]

    Makaxan Maza:
    Ban gabatar da su domin komai ba, face don na ga sun fi sauran rukunin sarrafa kalmar gudu. Haka kuma, ma’anar gudu ta nahawu, da ta fannu, ta fi yawan bayyana a waƙoƙinsu.[27] Mawaƙan maza su ne mawaƙan da suka keve ƙwarewarsu ga yi wa mazaje ma’abota sana’a waƙa.[28] Ga kaxan daga cikin abubuwan da muka kalato:

    ·        Makaxa Bawa Xan’anace:[29]
    A cikin bakandamiyarsa ta dambe waƙar Shagon Mafara yana cewa:
            Jagora: Xan zomo shina gudu mun bi sai

    A wani xan waƙa yana cewa:
            Jagora: Wanda duk bai ga damben Shago ba
    :Na da sauran kallo
    :Ya dai zaka duniya kamab bai zo ba
    :Kamaz zuwan kare ga aboki

    Bisa al’adar wasan dambe, gurgusawa baya shi ne “gudu” kuma shi ke tabbatar da rashin mazakutar namiji. Xan’anace ya raxa wa wani suna Xanzomo saboda tsananin tsoronsa ga abokin wasa. Haka kuma, mun san da cewa, wanda duk ya je wajen abokinsa ziyara, zai so a xan zauna a sarara a cika zumunci a wuce. A ganin Xan’anace, kare ba haka yake yi da abokinsa ba. Gudane zai tarar da shi, gudane za a rabu. Da mai ziyara da wanda aka ziyarta babu wanda ya huta.



    ·        Kassu Zurmi:[30]
    A cikin waƙoƙinsa na tauri, ya sarrafa kalmar gudu da ma’anoni daban-daban. A cikin waƙar ‘Yan Jabanda, yana gaya wa, wani tauraro da ya taras an sassare ya voye a gindin bishiya wai zatonsa ya yi layar zana ko baduhu, Kassu ya ce masa:
            Jagora: Baduhu ba shi yi
    :Tashi sheƙa

    A wata waƙa da yake tayar da zakaransa cewa yake yi:
            Jagora: Gyaran-gyaran gudun mai goda
    :In ka ji gyangyaran ya faxi

    A cikin wata waƙar tauri ya ƙara da cewa:
            Jagora: Gudu na yara ne sai mata
    :In don am bak ku kwance
    :Duk ba komi


    A wajen ‘yan dambe, da ‘yan tauri, gudu abin kunya ne, amma in an ga ƙwal uwar bari, Kassu na ganin babu laifi a mazaya a mayar da iri gida.[31] A fagen daga, yara da mata ke gudu ba su kunyata ba. Buwayyaye barinsa kwance cikin jini a je a xauko gado, ko a binne can, shi ne suna.[32]

    ·        Garba Xanwasa Gumi:[33]
    A cikin waƙarsa ta tankiya[34] tsakanin Gumawa da Fulani ya fito da hoton gudu na tsoro da firgita ga Fulani da su da bisashensu yana cewa:
            Jagora: Ga shanu na gudu
    :Cikin fadama ko’ina
    :Ina makiyayansu?
    :mai takobi ya fallasa

    Gindi:          Mai sharanin bixan faxa
    :Ko ba nashi ba
    :Na sarkin Kabi Kaxo
    :Masu motsattsen hankali

    Tabbas! A nan, ana fassara gudu na matsanancin tsoro, da firgita, domin ga dabbobin makiyayi suna gudu ba a ga uban kiyon ba. Fassara a nan, ko ba a gaya wa mai sauraro ba, gudu aka yi. Wa zai gudu ya bar dukiyarsa, in bai ga wutar gashinsa ba? Dubi abin da yake faxa cikin wata waƙa:
            Jagora: In ishe Dikko na gudu
    :Kaxo kana biye
    :Rannan kowak kira shi
    :Ba za shi tsayawa ba

    Gindi:          Ya sa ‘yan maza gudu
    :Ba da lavewa ba
    :Zarnaƙo na Garba
    :Kai mai xamar fana(?)

    Garba ya tabbatar da cewa, cikin sha’anin kora, da wanda ya koro, da wanda aka koro, kowannensu gudu yake yi na kai ga muradinsa. Ya ƙara ba da haske kan gudu cikin wani xan waƙan da ke da harshen damo wurin da yake cewa:
            Jagora: Idonka idon Dikko
    :Yanzu malfa na faxuwa

    Gindi:          Mai sharanin bixan faxa
    :Ko ba nashi ba
    :Na sarkin Kabi Kaxo
    :Masu motsattsen hankali

    Wataƙila a nan, da ya arba da Dikko, Dikko zai ruga a guje har sai malfar da ya saka a kansa ta faxi bai tsaya ba, bale ya kula da ita. Haka kuma, tana xaukar fassarar an sare wa Dikko kai, dole malfa ta sauka ƙasa.[35]




    ·        Alhaji Mamman Narayau:[36]
    Makaxin dambe ne da ya makaro a gundumar Sakwkato da Kabi. A cikin waƙar da yake yi wa wani zakaransa Almu, yana horon sa da cewa:
            Jagora: Kai dai ban da gudu
    :Ko na gangara gebe na,
    Yara:           Ko da mutuwa za ta zo ta kwasa
    Gindi:          Ya sa maza lavewa
    :Almu ‘yan maza ka tsoro


    ·        Fanxararrun Waƙoƙi:
    Ban yi musu da wasu magabata ba da suka xora/saka su cikin waƙoƙin maza.[37] Ni dai a ganina, idan za a xora su a ma’aunin al’ada, za a ga sun fanxare.[38] Bisa ga wannan ƙiyasi na kira su fanxararrun waƙoƙi. Waƙoƙin da ke cikin wannan rukuni sun haxa da waƙoƙin sata da kwartanci da shaye-shayw da makamantansu. Dubi yadda Gambo ke kallon fassarar gudu ta fuskar tsoro da firgita:
            Jagora: Kaicon na kaina!
    :In nit tuna ban an zan tabbata ba
    :Sai raina ya vaci Gambo
    :Kaico ni gamuwar Gambo da Haliku
    :Ni gamuwar nan nai gudun ta

    Makaxa ya nuna irin tsoron da yake da shi na ranar haxuwarsa da Mahaliccinsa (Allah). Xanmotti Wababe a cikin waƙar Sarkin Varayi Ladan Nazaƙi ya fassara ma’anar gudu ta fuska biyu kamar haka:
    Yara:           Shi Nazaƙi na da satar raini
    :In yad xauko kayanka
    :Ya fi gaban gudu
    :Ba ya sheƙawa

    Gudun da Xanmotti ke son ya nuna a nan yana iya xaukar ma’ana biyu. Yana fassaruwa da gudun zuciyar mai kaya ko tsoron huce haushinsa a kan sa. Na biyu, yana xaukar gudu na cin moriyar dugadugai a xan zara sassaka kaxan, irin na ƙwararrwn mai laifi. Idan gudu ya cira wannan mataki, aka gantsare, da himma, an shiga ma’ana ta biyu ta “sheƙawa”.

    ·        Mawaƙan Sha’awa da Bandariya:
    Na haxe su wuri xaya domin ba a kansu nazarin yake ba, ba da misali za a yi da xiyan waƙoƙinsu. Bage Xansala[39] a cikin waƙarsa ta Sarkawa ya ba mu labarin wani matsoracin masunci xan haye[40] da ya je farautar kada (kado) a fadama. Yana cewa:
            Jagora: Wani shawarakin Sarkawa
    :Kullum da mashi sai gulbi
    :Ran nan da ya’ isa
    :Ya ishe karai baki gulbi
    :Ya yadda mashi yas sheƙo

    Yara:           Mata ka cewa: “Wane ina abin
    :Da kac ce ka kamo”
    :Yac ce: “Raba ni da wargi
    :Tai ga shi can kamo gulbi;
    :Hargin da kig gani  na xauko
    :Ai dole ta sa na yasai”

    Gindi:          Mu je mu iske Sarkawa
    :Su ban abincina kihi

    Ina laifi masu karin magana da ke cewa, in ka ji riƙa mini kaya ba zawo ya koro mai kayan ba? Bage Xansala na karantar da mu cewa, gudun uzuri na tsoro, ba a haxa shi da kowane irin aiki, ko wata lalura, ta rataya kaya ko xaukar su. Irin wannan lalura ta tava riskuwar Bala Maigumbe Bunza[41] a karonsu da Bagobiri wanda ake yi wa laƙabi da Xan Argungu Gumel.[42] Bagobiri ya yi wa Bala bugu biyu da hannu, na uku da kangarwan fitila[43] Bala bai kula da shi ba. Dalilin Bala na ƙin kulawa da shi, shi ne, Bala ya ga abokinsa ne, kuma bai kai Bala ƙarfi ba. Bala na ganin da wuya ya bugi wani ƙato da hannunsa, ya bar shi tsaye. Da Bala ya kasa jure bugu na uku ya ce:[44]
            Jagora: Naj jawo rankavau
    :Nak kaure Gumel
    :Yaf faxi yamma
    :Nas sheƙa da gabas
    :Ga ni yanzu sai garken Udulu
    :Gidan Ajayi nan nas share kwana
    :Daxa ga ni nan zuwa sagagan-sagagan!

    Da Bala ya sa hagunsa (rankavau) ya vatar wa Bagobiri da hankali, ya tabbatar da Gumel na ƙasa babu rai, sai ya yi amfani da kalmar “sheƙa”. Abin da aka yi, shi ya sa aka sheƙa irin gudun tashin hankali. Ba a daina gudun ba har aka zarce gidan Udulu da Ajayi[45] ana riƙe ba sakewa. Wannan matsalar muna iya kwatanta da irin abin da Garba Maitandu Shinkafi[46] ya gani a “Waƙarsa ta Kunama.”[47] Da kunama ta harbi wani malami (yaro) kuma xan gidan karatu, yana cikin karatu da allonsa, Garba na cewa:
            Jagora: Yaro xan Antu xan gidan malammai
    :Da tak kahwa mai bindi
    :Yay yi kwance yac ce man: “Ya mutu”
    :Bixo allo Garba naj ji ya ce:
    :“Baa da sin alif
    :Ban tava su sai in na samu ta yi sauƙi
    :Mugun dahinta ya kammin
    :Ga nib a ni alhwasha

    Yara:           ‘Yak kazan uba ‘yad danƙon uwa
    :Kunama keson uwaki
    :Ba ki ragowa ta kulva

    Yara:           Ta sa malam/yaro gudu
    :Ya bar allonai ƙasa

    Gindi:          Kunama zan wa kixi
    :Zama ciwo ag gare ta
    :Ta halban na jiya

    Jagora:        Malam Hamidu na Malam Isa
    :Xazu yana salla
    :Yay yi duƙe tah halbai
    :Yak katse Subahin sai yaz zuba
    :Malam ya ce: ‘a uzu billahi
    :Kaza uban ga ban kai kaka
    :Ku yi min shimfixa ku kau hwasa kuka
    :Rashin uba ya same ku
    … … … … …

    Yara:           Wanga ciwo ko ban mace ba
    :Sai kaina ya hwashe
    Gindi:          Kunama zan wa kixi
    :Zama ciwo ag gare ta
    :Ta halban na jiya

    Tirƙashi! A nan, kalmar “zuba” aka yi amfani da ita domin nuna irin gudun da aka yi na muzanta  da jin ciwo. Dubi ƙimar karatu da darajar allon da malamai ka gani, amma jifa aka yi da shi, kamar ba mai karatun ke da shi ba. Haka xabi’ar “gudu” take matuƙar ta rutsa da mutum, komai ya dakata, sai an gama da shi.

    ·        Mawaƙan Jama’a:
    Masana waƙa sun ce, su ne mawaƙan da kowa suna yi wa waƙa.[48] Ba su da zavi ga wanda suke yi wa, ko da kuwa suna da uban gida tabbatacce.[49] A cikin waƙar Sarkin Kano, Alhaji Musa Xanƙwairo na cewa:
            Jagora: Da an bugi kan xan Buzu
    :Dole shi koma gudu sai Tawa (Tahoa)[50]
            Gindi:           Ba takura kaurin gaba
    :Na yarda da Sarki Ado

    Babu shakka. Idan abin gudu ya kama mutum da ya ruga wurin da aka san shi can zai dosa. Ashe gaskiyar Hausawa da ke cewa, abin da duk ya yi kora shi ke gwajin hanya.[51] Wannan ya yi daidai da faxar Hausawa na iyakar gudu ƙuryar xaki.

    ·        Ƙagaggun Labarai:
    Tarihin ƙagaggun labarai ya soma tun daga tatsuniya har ya zuwa barkwanci da tarihihi da dai makamantansu.[52] Idan aka yi wa abubuwan duban tsanaki, za a ga ratsin gudu ko’ina a cikinsu. Wasunsu ma a kan “gudu” aka aza tubalin gina su. Labarin: “Gudun shekara da shekaru ya sami ni” ya isa ya zama abin misali a nan.[53] Haka kuma, labarin wasu ‘yan raraka da suka je raraka gidan wani tajiri, ya fito da bindiga[54] ya isa ya ƙara ba da haske.
    ·        Wasannin Yara:
    An ce, duk wasan da aka ga yara na yi, maza ko mata, rayuwar al’ummar da suke ciki ne suke ba da hotonta. Ga al’ada, duk wata xabi’a da yara suka fito da ita, akan camfa cewa, kul ba daxe abin zai wakana ga al’umma.[55] A cikin wasannin yara za a samu: Wasan Langa (sai an haxa da gudu), Wasar bareyi-bareyi,[56] Wasar tawayya,[57] Wasar yaƙi, ga su nan dai. A cikin wasannin yara na waƙe-waƙen Hausawan ƙasar Gwandu akwai:
            Jagora:          Kai ku xaga ga xan doka nan[58]
            ‘Yan karvi:   Ba mu gudu sai mun ga Nasara
            Jagora: Jah hula ba iko ta ba
            ‘Yan karvi:   Ko rawani ba iko na ba

    Dalilin da ya sa aka umurce su da su xaga a guje, wataƙila sun yi laifi, suka ƙi gudu. Dalilin ambaton xan sanda domin a saka musu tsoro ka da su haxu da hushin hukuma, duk da yake sun ƙi su gudu, sun ce, in sun ga Nasara suna gudu. Me ya sa suka gudu saboda Nasara? Saboda ta’addancin Nasara na yin xanyen hukunci ga wanda ba ya so.[59]
    Sakamakon Bincike:
    Na daxe ina tunanin gabatar da bincike a kan ire-iren waxannan fannoni da kan shiga duhu, a shafa da su, tattare da rayuwa ba ta yi sai da su. Hankalin bincike na xaliban bincike, da manazarta, ba ya ankara ga yin nazari a kan su, domin zato ake abubuwa ne busassu ba sa da maiƙon da za a laguda, a yi bincike a kai.[60] A wani lokaci a ce, mene ne fa’idar bincikensu?[61] Daga cikin fa’idojin da na samu cikin wannan nazari na ga:
    i.      Kalmar “gudu” Bahaushiya ce, gaba da baya, kuma ba ta da wani suna a kowane karin harshe na Hausa face gudu. Kalmar gudu kaxai ta isa ta zama wata fitila ta binciken asalin Hausawa.[62]
    ii.     Kalmar “gudu” a fagen ma’ana tana da harshen damo, ma’ana bayyananniya wato “gudu” na haƙiƙa, da kuma ma’ana ta nahawu nisantar abu ko ƙin sa. Waxannan ma’anoni biyu duka sun tattara a kan: “fargaba” da “buƙata”, duk wani gudu aka yi taliyo zai faxo cikin xayan biyun.[63]
    iii.    Kowane daga cikin sassan adabin Bahaushe, na baka ne, ko rubutacce, “gudu” na da babban turke a ciki kuma ya yi yaxo sosai a cikin sassan sa.[64]
    iv.    Yadda Hausawa ke kallon gudu a harshensu, haka nan manyan harsunan duniya ke kallonsa. ‘yan misalai daga Turanci da Larabci sun isa su ba da haske a kan haka.[65]
     v.    Ta tabbata cewa, dole sai mun sake nazarin manhajar koyar da Hausa, a manyan makarantu, da Jami’o’i, domin mu keve wa ire-iren waxannan daxaxxun al’adu ko mu ce tafarkin rayuwa bagiren da za a nazarce su.[66] Idan har guje-guje da tsalle-tsalle da duƙe-duƙe na zama wani fannin ilmi mai cin gashin kansa a mahaxar ilmi fannin Boko,[67] ban ga dalilin da zai hana a jarraba shi a Hausa ba.
    vi.    Taskace adabinmu na baka irinsu karin magana, salon magana, kirari, shaguve, baƙar magana, barkwanci, waƙe-waƙe, tatsuniya, da sauransu ya zama wajibi idan muna son mu kaxa miyar yau da gishirin jiya. Fito da hanyar taskace su, da kundace su, aiki ne ga dukkanin wuraren da ake koyar da harsunan Afirka.[68]
    vii.   Bahaushe ba ya buƙatar a ambaci gudu ƙiriƙiri a wurin da al’ada ta tanadi gudu. Da an ambaci dalilin gudu, akan ce: Yaz zuba, ko yac cira, ko ya xaga, ko ya sa kai, ko ya uzurta, ko ya sa aniya, ko ya gangara, ko ya vace, ga su nan dai.

    Naxewa:
    Nazarin al’ada fika-fikai biyu yake da su manya-manya. Fiffike na farko, fasahar hannu/azancin hannu (Material Culture); na biyu kuwa azancin tunani (Non-material Culture). Kowane xaya daga cikin waxannan fikafikai aka raunana, ko aka banzanta, tussan rayuwar al’umma zai salwanta. Nazarinmu na yau “gudu” yana daga cikin azancin tunani (Non-material Culture). Kuma azanci ne da kowace al’umma tana da shi.[69] Gudu, alamar nagarta ce ga wanda ya koro;[70] alamar kasawa ce ga wanda aka koro;[71] alamar rashin gaskiya ne idan ya haxa da waiwaye;[72] alamar buwaya ce, idan aka nemi a yi shi aka ƙi.[73]
    A duk lokacin da aka yi shi da dalilin yin sa. Mafarinsa yin sa, shi zai bayyana irin uzurin da ke cikin kama jikin mai gudun in ji Makaxa Amali:
            Jagora: Yana yi ma aiki kamag gudun ƙato
    :In ya hangi gobara
    :Muddin yas san gidansu tak kama
    :Ban san mai tare shi ba

    Yara:           Ran nan ko galvi an ka wa hanya
    :Sai dai yai ƙire biyu

    Gindi:          Ya riƙa aiki da gaskiyan Allah
    :Bai saba ba da zama
    :Aikau jikan Tayawa xan Mamman
    :Kunkelin fashin ƙasa

    Gudun uzuri, uzuri ake yi masa, domin ba ya kula da duk wani uzuri da zai gitta masa. Gudun da ƙato ke yi na ceton rai ne, gobarar rani mai cinye gida da abincin da aka kinshe ya gani. A irin wannan xanyar hasara: Amali ya tabbatar da, ko da sanke aka gilma a hanya, a irin yanayin wannan gudu, sai dai sanken (galvi) ya ƙire biyu, ko ƙaton ya ƙire biyu idan aka gamu, amma fa sai an kai ga muradi:
            Jagora: In ga tukunya, in ga tulu
    :Yadda a aki dut za ta faru
    (Gambo: Waƙar Tudu da Inuwa)

    MANAZARTA
    Adamu, M. 1978. The Hausa Factor in West African History. Zaria: ABU Press.
    Argungu, I. G. 2010. “Nazarin Salo a Waƙoƙin Bage Xansala”, kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
    Bada, B. D. 1995. “Literary Study of Themes, Functions and Poetic Divices of Hausa Karin Magana” PhD thesis Sokoto: Usmanu Xanfodiyo University.
    Bargery, G. P. 1934. A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University, Press.
    Bashinfar, S. A. 2003. Almugnii fi Fiƙhul Hajj wal Umra. Dar ibn Hazam.
    Birniwa, H. A. 2012. “Dangantakar Katsinawa da Sauran Al’ummomin Arewacin Nijeriya”, cikin Katsina A Dunƙule, wallafar Ƙungiyar Xaliban Katsina a Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato.
    Bunza, A. M. 2001. “Raxaxi da Zogin Cuta a Ma’aunim Bahaushe” cikin Hausa Studies: Readings in Hausa Language, Literature and Culture. Sokoto: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
    Bunza, A. M. 2006. Gadon Fexe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Ltd.
    Bunza, A. M. 2007. “The Role of Proverbs in Conflict and Crises Management”, in Promoting Peace Through Teacher Education, Baba, N. M. and Furfuri, M. M. (eds).
    Bunza, A. M. 2011. “Al’adun Hausawa Jiya da Yau, cikin KADA Journal of Liberal Arts. Kaduna: State University.
    Bunza, A. M. 2012. “In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, kammalallen kundin bincike, ba a buga ba.
    CSNL, BUK, 2006. Ƙamusun Hausa.
    Ganuwa, R. da Yabo, 1989. “Jigo da Salon Waƙoƙin Maza ‘Yantauri da Varayi”, kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
    Gusau, S. M. 2008. Waƙoƙin Baka na Ƙasar Hausa, Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers.
    Haour, A. Rossi, B. 2010. Being and Becoming Hausa Interdiscilpinary Perspectives, African Social Studies Series, BRILL, Leiden – Boston.
    Last, M. 1967. Sokoto Caliphate. Ibadan: Longman
    Magaji, A. 1979. “Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”, kundin digirin BA Kano: Jami’ar Bayero.
    Malumfashi, I. A. 2007. Adabin Abubakar Imam. IBM Printers, Kaduna.
    Mode, M. A. 2005. “A Stylistic Study of Hausa Toen Kirari (Epithec)” PhD thesis, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
    Newman, R. M. 1990. An English – Hausa Dictionary. Yale University Press. New Heaven and London.
    Oxford, Oxford Mini Dictionary.
    Salawu, A. M. 1988. “The Origin of Hausa States Revisited.” Depertment of History, Unisok.
    Sani, M. A. Z. 1999. Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. Ibadan: University Press.
    Sayaya, A. S. 2009. “Wasan Tauri a Ƙasar Katsina”, kundin digirin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo,
    Shinkafi, R. H. 2012. “Garba Maitandu Da Waƙoƙinsa”, kundin digirin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
    Tayson, L. 2006. Critical Theory Today A User Friendly Guide. Second Edition, Routledge Taylor and Francis Group, New York, London.
    Tsafe, I. A. 2010. “Farauta a Garin Tsafe”, kundin digirin BA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
    Usman, B. B. 1990. “A Sociolinguisitics Study of Taboos in Hausa”, MA thesis, Kano: Bayero University.
    Wurma, A. G. 2005. Daidaitacciyar Hausa da Ƙa’idojin Rubutu. ORP, Kaduna.
    Yahaya, I. Y. 1988. Hausa a Rubuce. Zaria, NNPC.
            1996. The New International Webster’s Comprehensive Dictionary of the English Language, Deluxe Encyclopeadic Edition.


    [1] Akwai wani labari na wani gurgu da aka ce, ya share shekara da shekaru ba ya iya tafiya, daga ɗaki sai ɗaki. Tun yana yaro, har manyanta ta shiga, aka sa wa Allah ido da ikonSa. An ce, wata rana, mutanen gida sun tafi gona ga hunturu, gobara ta kama gidan, har ta je ga ɗakinsa. Cikin ikon Allah, da aka hanzarto kashe wuta ɗakinsa aka fara. Gabanin a kawo ceto, ɗakin ya ƙone ƙurmumus! Aka yi ‘yan koke-koke, aka gaji, aka haƙura. Ana cikin karɓar ta’aziya, sai ga wani ya ce, ya gan shi saman wata ƙatuwar itaciya. Da aka je, aka tarar da haka ne gaskiya. Aka saukar da shi, ya hau ƙafafunsa lafiya lau. Duk jikinsa jini ke tarara, domin jijiyoyin jikin, an share fiye da shekara hamsin ba a motsa su ba, yau cikin ɗan lokaci, an buɗe da gudu da su. Wannan ya nuna ba a koya wa mutum tafiya. Ga gurgun da ko tafiya bai taɓa yi ba, ya balbala a guje, har da hawan doguwar itaciya. Aradu! In ka ji ƙi gudu, sa gudu ne bai zo ba.
    [2] Idan yaro ya kai ga haka, akan ce, “Ya fara dafa ƙasa.” Daga dafar ƙasa sai a tsayu a kan ta. Dafa ƙasa, ba rarrahe ba ne. Wani mataki ne mai nuna za a fara rarrahe.
    [3] A wannan mataki ne Hausawa ke cewa, a koyaushe mata masu juna biyu na addu’o’i biyu: ‘Na farko shi ne, Allah Ya mai da gaba baya.’ Cikin da aka ɗauka, a haife shi lafiya, a sake mayar da shi baya a goya shi. Haka kuma, sukan roƙi, ‘Allah Ya tayar da zaune tsaye.’ Jinjirin da ke koyon zama, Allah Ya nuna musu ya fara tashi tsaye da kansa.
    [4] A al’ada, wasu Hausawa kan danganta saurin iya rarrahen yaro, da iya tafiyarsa, ga irin basirar da yake da ita. A ganin Bahaushe, zama ake koya wa yaro, sauran biyun rarrahe, da tashi tsaye, da tafiya, da gudu, shi ne malamin kansa. Gwargwardon basirarsa, gwargwadon yadda zai iya aiwatar da su. An ce, masana kimiyyar zamani ma haka suka fahinci matsalar. Hira da Farfesa Abdulhamid Gwandu, ƙwararre ga lafiyar yara a Asibitin koyarwa ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Junairu 2010, a gidansa da ke Unguwar Gawon Nama, Sakkwato.
    [5] A tsarin koyon harshe, ambaton kalmar “ruga” ko “gudu” sun wadatar ga yaron, sai ya fara gudu kawai. Wani lokaci, idan ana son ya ɗaga aguje akan furta kalmomin motsin rai masu ban tsoro ga yaron irin su, “ish!” ko “ah!” ko “kayya!”ko “wayyo!” Yaron da wayonsa bai ji gishiri ba, da ya ji , sai ya fara gudu zuwa neman wurin ɓoyewa.
    [6] A cikin sana’o’in Bahaushe, ɗaya kawai ke buƙatar iya gudu sosai, ita ce farauta. Ɗan Adam tun farkon halittarsa da farauta ya fara, don ƙarin bayani a dubi, Tarikh. ɓol. 1 No. 3 Ɗabi’a ta biyu da ke buƙatar gudu ita ce “Sata”. Ita kuwa, babu mai son yaronsa ya zama ɓarawo. Don haka, Bahaushe ya bar gudu yadda ya tarar da shi, in buƙatarsa ta taso, a yi shi.
    [7] Don ƙarin bayani a dubi Ƙamusun Hausa. CSNL Jami’ar Bayero, Kano. Ya kawo: Gudu, fyalla ko ruga (2) kuɓuce ko tsinke (3) hanzarta (4) kauce wa abin da ba daidai ba. Shafi na 171.
    [8] A Larabci akwai kalmar “mashayu” mai ma’anar tafiya. Akwai “ramli” sauri-sauri, ko a ce ‘sassaka’. A ibadar Hajji, ana sassaka a ɗawafi sau uku. A Safa da Marwa, ana yi a duk lokacin da aka kai wurin wani koren haske. Wannan na nuna bambancin tafiya da sassaka a wajen masu Larabci. Don ƙarin bayani a dubi, Sa’id bn Abdulƙadir Bashinfar, (2003) Almugni fi Fiƙhul Hajj Wal Umra. Darul ibn Hazam, shafi na 170.
    [9] A fassarar Oɗford Mini Dictionary. Sun ce: Run 1. Moɓe at a speed faster than walking; 2. Moɓe smoothly; 3. (of a bus, train, etc) traɓel on a particular route; 4. Be in charge of; 5. Continue or proceed; 6. Function or cause to function; 7. (of a liƙuid) flow or spread; 8. Stand as a candidate in an election; 9. Smuggle goods. Da yawa daga cikin waɗanna fassarori sun yi canjaras da yadda Bahaushe ke duban “gudu”.
    [10] A dubi  The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of the English Language, deluɗe encyclopaedic edition, (1996) ya ce: 1. To moɓe by rapid steps, faster than walking in such a manner that both feet are of the ground for a position of each step; 2. To moɓe rapidly go swiftly; 3. To flee take flight; 4. To moɓe a brief or rapid journey: We run oɓer to Staten Island last night; 5. To make regular trips: ply, This steamer runs between New York and Liɓerpool; 6. (a) To take part in a race, (b) To be a candidate or contestant: to run for dog catcher; 7. To finish a race in a specified position, I run a poor last; 8. To moɓe or pass easily: The rope runs through the block; 9. To pass continuously and rapidly, elapse: The hours run by; 10. To proceed in a direction or eɗtent: This road runs north; 11. To moɓe in or as in a steam, flow; 12. To become liƙuid and flows, as a waɗ, also to spread or mingle confusedly, as colourse when wet. Shafi na 1101 – 1102, za a samu ma’anonin tamanin da huɗu (84).
    [11] Da Ƙamusun Hausa da English – Hausa Dictionary na Bargery da An English – Hausa Dictionary na Roɗana Ma Newman, duk ba su yi takin saƙa ba ma’anonin da suka yi fice a ƙamusoshin Turanci ba.
    [12] Don ƙarin bayani a dubi, G. P. Bargery, (1934) A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Ɓocabulary, shafi na 401 – 402 ya kawo: banka; burma; falfala; falla; famfara; fankaya; fyalla; gantsara; girba; girka; ƙalƙala; ƙarce; kasa; ƙunsa; kutsa; kwaɗa; ƙwala; ƙwalƙwala; ƙwanƙwala, nana; nema; noma; raka; ranye; rara; ruga; rutsa; share; shata; sheƙa; shirga; surmuƙa; surmuya; tantala; tattala; tsala; tsantsala; tsere; tsula; tsunka; ufa; wantsara; warta; yanka; zabura; zangaya; zuba; zuƙa; zunduma; zura; barje; buɗe; garzaya; gasa; hamce; gau; raɓa. Bargery ya kawo wasu jumloli da ke fassara gudu kamar haka: Ya yi noman bare, ya nomi gandun kare, ya nemi mabuɗi a hannun zakara, ya tsunka saƙar gizogizo, ya ci noma kuba, ya ci noma aura. Ba don Kalmar “gudu” na da muhimmanci ba, da wannan duk ba ta taso ba. Don haka, nazarin Kalmar wani tabbatarwa ne ga irin nauyinta a al’ada.
    [13] Sauri ya fi sauri-sauri uzuri, sassaka ya fi sauri da sauri-sauri. Na yi hasashen wannan ma’ana ne bayan da na nazarci fahintar mawaƙa da marubuta a kan gudu. Ko a wuri ɗaya ana sassaka. Yara masu bara suna waƙa da cewa:
                Kun ga rawan tuwo
                Kun ga sassakan miya
    [14] Wannan wata ma’ana ce ta furucin gudu a ma’anance. Za a iya cewa, “ɓarawo da ya ga ana yanka naman ɗan’uwansa sai ya ɓace.” A nan, ɓacewa ba ta baduhu ba ce, ta “gudu” ce. Haka za a ji Bahaushe na cewa: “Da muka halaka ɗayan cikin ‘yan adawa, muka waigo kan ɗayan, ƙasa ko bisa.” Faɗar “ƙasa ko bisa” yana nufin ya ruga a guje irin gudun fitan rai.
    [15] Ana camfa wasu abubuwa da fuskar ɓoye sunayensu na asali, a laƙaba musu suna maras nauyi. Zawo a ce “gudu”; Kuturta a ce “zafi”; hauka a ce “motsuwa”; mutuwar zakari a ce “kasawar gaba”. Haka ma sunayen ƙwari, maciji a ce, ‘maja-ciki’; kunama a ce ‘mai ƙari’. Don ƙarin bayani a kan harantattun kalmomi a dubi Usman, B. B. (1990) “A Sociolinguisitic Study of Taboos in Hausa”, MA, Kano: BUK.
    [16] Ƙamusoshin Turanci sun ba da ma’anonin gudu fiye da tamanin da huɗu (84). Na ga idan aka tattara hankali waje ɗaya, ana iya bayar da ma’anar da za ta haɗe waɗannan ma’anoni uku da muka bayar.
    [17] Wannan ma’anar na ga ya dace in bayar a kan abubuwan da na fahinta game da ma’anar gudu na gaba ɗaya. Ina zaton, idan aka taya ni gyare-gyare, za a kai ga daidaitacciyar matsaya.
    [18] Don ƙarin bayani game da hijirar Shehu Usmanu daga Ɗegel zuwa Gudu, a dubi, Last, M. (1967) Sokoto Caliphate, Longman.
    [19] Don ƙarin bayani a kan Karin sautin Hausa a dubi Sani, M. A. Z. (1999) Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa, Ibadan: Uniɓersity Press.
    [20]Don ƙarin bayanin ci gaba ko koma bayan al’adun Hausawa, a dubi Bunza, A. M. (2011) “Al’adun Hausawa Jiya da Yau” cikin KADA Journal of Liberal Arts, Kaduna State Uniɓesity, shafi na 249 – 259.
    [21] Don ƙarin bayani game da karin magana, a dubi Bada, B. D. (1995) “Literary Study of Themes, Functions and Poetic Diɓices of Hausa Karin Magana”, PhD thesis, UDUS.
    [22] Don ƙarin bayani a kan haka a dubi Bunza, A. M. (2007) “The Role of Proɓerbs in Conflict and Crises Management”, cikin Promoting Peace through Teacher Education. Baba, N. M. and Furfuri, M. M. (editoci) 2007, shafi na 154 – 166.
    [23] A iya sanina, aikin da aka yi na bayanan kan kirari shi ne, na Mode, M. A. (2005) “A Stylistic Study of Hausa Towns Kirari (Epithec)”, PhD thesis, Sokoto: UDUS.
    [24] Gudun da mai rai zai yi a nan shi ne, na ƙoƙarin ya tsere da nasa rai, domin ya san dukan da za a yi masa, ko ya mutu, ba za a fasa ba. Hausawa na cewa, a koyaushe ka ga mutum a guje, to kuɓuta yake son ya yi, ko ya kuɓutar. Babu wani abin da za a kuɓuta, ko a kuɓutar, da ya zarce ‘rai’. Wanda ya tarar da ana dukan matacce, a al’adar Bahaushe, idan ya ruga, ba za a ce “ya gudu” ba, sai dai a ce, “an neme shi, an rasa” ko a ce, “ƙasa ko bisa” ko a ce “ba a sake ganinsa ba”. Dalili kuwa shi ne, irin gudun da zai yi ba ya misaltuwa, irinsa sai ya faɗa a wata mutuwa bai sani ba.
    [25] Domin neman cikakkiyar balagar waƙa Bahaushiya a dubi, Mukhtar, I. (1985) “Nahawun Waƙa”, kundin digirn MA, Kano: BUK.
    [26] Don ƙarin bayani a kan rabe-raben waƙoƙin baka a dubi Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka na Ƙasar Hausa Yanaye-yanayensu Da Sigoginsu. Benchmark Publishers, Kano, shafi na 205 – 360.
    [27] Misali, a wasan dambe, wanda ba ya tsayawa a dake shi, ko a bugo ya ja baya, sunan ja bayan “gudu”. A wasan kokuwa, wanda ba ya tsayawa a sarƙe da shi sosai, ya zuƙe baya, sunan zuƙewarsa “gudu”.  A wasan tauri, idan ana kirari, matsoraci ya ƙi fitowa ya mayar da martani, za a ce, “ya gudu”. A wasan hawan ƙaho, barunjen da ke zamiya da baya idan sa ya tunkaro shi, sunan zamiyar “gudu”.
    [28] Ƙwararrun ga sana’a ina nufin, irin su: manoma, maƙera, mafarauta, masunta, ma’aska, masu dambe, masu kokuwa da dai makamantansu.
    [29] Cikakken sunansa Muhammadu Bawa Ɗan’ance ‘Yartsakuwa, don ƙarin bayani a kan rayuwar sa a dubi, Mahe, A. (1984) “Makaɗa Ɗan’anace da Waƙoƙinsa”, kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.
    [30] Cikakken sunansa Abubakar, don ƙarin bayani a kan rayuwarsa, da waƙoƙinsa, a dubim Magaji, A. (1979) “Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa”, kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
    [31] An ce, lokacin da Katsinawa suka kara da Gobirawa, da Gobirawa suka ga babu ci, maimakon su ce, a gudu, sai suka ce, “A mazaya a mayar da iri gida”. A dubi Birniwa, H. A. (2012) “Dangantakar Katsinawa da sauran Al’ummomin Arewacin Nijeriya”, cikin Katsina A Dunƙule. Wallafar Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Katsina a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, shafi na 17.
    [32] Da wannan dalili ne makaɗa Kassu Zurmi ke cewa:
    Jagora: Kyawon faɗa a yo accakwama
    :A kwaɓa ta baƙi ƙirin
    :Ta ƙare muku can
    Bahaushe ya fi son, ya taras da tauraronsa kwance, cikin jini, da a ce ya ruga a guje. A ganin Bahaushe, makashi maza, maza ka kashe shi. Don haka, babu hasara idan hasara ta ci hasara.
    [33] Fitaccen makaɗi wasan tauri ne a Lardin Zamfara da Sakkwato da Kabi. Manyan yaransa sun haɗa da Mamman Dogo, Ɗankurjan, Kogo, Bala Ƙonanne da dai sauransu. Don ƙarin bayani a kan rayuwar Garba Ɗanwasa Gummi a dubi R/Ganuwa da Yabo (1959) “Jigo da Salon Waƙoƙin Maza ‘Yantauri da Ɓarayi”, kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
    [34] Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya ne masanin al’ada na farko da ya yi musu suna “Mawaƙan Tankiya”. A ganinsa, bayan lafawan yaƙi, babu sauran kiɗin yaƙi. Ragowarsu ne suka koma mawaƙan tauri, da mawaƙan cin tama, da banga. A halin yanzu, sun narke cikin mawaƙan maza. Tankiya ita ce, ƙoƙarin tanka faɗa, ko rigima, hayagaga, tsakanin mutane. Takan ɗauki fassarar ta da zaune tsaye, ko tayar da fitina, wadda ta riga ta lafa. Mutum mai tankiya shi ne wanda yake da ja-in-ja ba ya sakewa komai ta banjama banjam.
    [35] A wajen masana Ilimin Harsuna, ƙa’idar nan ta “sake shiri” (deconstructiɓe criticism) tana taka rawa a wannan fassarar. Don ƙarin bayani a dubi Tayson, L. (2006) Critical Theory Today A User-Friendly Guide, Second Edition, shafi na 251 – 280.
    [36] Mamman na Rayau makaɗin bangaro (‘yan dambe) ne. ya shahara a Sakkwato da Kabi da Zamfara da wasu sassa na Katsina da Neja. Ban ci karo da kowane irin aiki da aka yi a kansa ba.
    [37] Magabata cikin nazarin waƙa wasu na saka su a cikin rukunin mawaƙan maza. Ni a fahintata, na kira su fanɗararrun waƙoƙi, domin sun fanɗare wa nagartattun al’adunmu. Waƙoƙin sata, kwartanci, shaye-shaye da zanga-zanga irin na waƙoƙin takkai. Waƙoƙin sata na Gambo da Kassu da Ɗanmotti Wababe da Bala Ƙarhe da Yahaya da Goloƙo da makakamantansu sun shiga ciki.
    [38] Duk wani ƙwazo da kirari da tamaza da ɓarawo ko kwarto ko wanda ya shayu da ƙwaya ko giya zai yi, ko ya yi, cikin kunya ne. Wanda duk ya san al’ada sosai, abin kunya zai ba shi ba sha’awa ba. A taƙaice, abin nasu ba yabo ba ne fassalawa ne. Don ƙarin bayani a dubi Bunza, A. M. (2012) “In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo” kammalallen bincike ba a wallafa ba. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ta aminta da ta wallafa aikin ƙarƙashin kwamitin Kulawa da Bincike da Wallafe-wallafe na Jami’a.
    [39] Don ƙarin bayani a kan waƙoƙin Bage Ɗansala a dubi, Argungu, I. G. (2010) “Nazarin Salo a Waƙoƙin Bage Ɗansala”, kundin digirin BA, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
    [40] Ɗan haye ana nufin wanda bai gaji abu ba, ya koye shi ne da sama. Donƙarin bayani a kan haye a sana’o’in Hausawa a dubi,
    [41] Bala Maigumbe fitaccen fasihi ne a garin Bunza. Waƙarsa “Rabbani Ahadun” ita ta fi fice, cikin waƙoƙinsa, a cikin waƙar ne aka saka, labarin damben da suka yi da shi da Bagobiri Gumel. Bala Maigumbe a zamaninsa babu namijin da ya kai shi tsayi, da zati, da auki, da ƙwazo; komai girmna namiji, sai dai a ce, kamar Bala Maigumbe. Yana yin gumbe ta takardar siminti ko takardar bagalibaho. Bagobiri Gumel ya rasu wajajen 1977/78. Bala na raye a halin yanzu da nake wannan bincike.
    [42] Ina zaton Bala ya ƙaga masa sunan nan na Ɗan Argungu Gumel. Gajere ne mai tsaga zube a kumuta irin ta Kabawa da Gobirawa. Yana da ɗan ja ga leɓe, da sanƙo ga kai, yana shan sigari mai zobe mai filita. Yana da fara’a da murmushi, sai dai saurin husata gare shi. A cikin tsohuwar kasuwar Bunza yake kwana kantin Marigayi Alhaji Ɗandare da ke ƙarƙashin kulawar Marigayi Mamo ƙanen Monde Gardaye. Da ya rasu, an rufe shi bayan gidan su Dashiri tsohuwar asibiti ta kasuwa.
    [43] Kangarwar Fitila ita ce, fitilar da babu baturi da gwalab ciki (wato fitilar hannu). Wani lokaci kangarwa ba ta da gilashi sai tasa kowai ke a kanta. A zamanin su Bala wani Malami mai suna Ƙassan Kura sai gara uban Balkisu, shi ke aje-ajen kangarwar fitilu yana ɗorin su, a yi mai cin batur goma. A ƙa’ida fitilar hannu baturi biyu ne kawai.
    [44] Ga al’adar mutum mai jiki bai cika saurin fushi ba. Don haka, yake cewa:

    Jagora: Ina ta ƙoƙarin in jure bugu
    :Yaran Kwadorko ka san ba su bari
    :Kuwwa sukai suna wayyo sagwaɓa
    :Singileti ketattar ki kike
    :Ɗan mace ko daɗai bai mai da bida
    :Ashe da nan Bala rai ya ci haki
    :In duba da yamma can sai ga Bagire
    :Can da arewa ga Ɗanjimma zuwa
    :Ga Shehu namu Ɗansandan Rahama
    :Nac ce” “In kuna rufewa sai ku rufe
    :In ba ku ko rufewa sai ku bari
    :Wallahi yau Bala zai rama bugu”
    Kwadarko sunan uguwar su Bala ce. Bagire, da Ɗanjimma, da Shehu, ‘yan doka ne na wancan lokaci a garin Bunza wajajen 1969 – 1975. Udulu da aka ambata a waƙar, shi ne, Udulu Tuntuɓe gidan da Bagori uban ‘yan tsalle ya yi zama. Ajayi kuwa, Shehu Ajayi ake nufi. Duk suna nan bayan shagon marigayi Alhaji Ɗandare Bunza. Amfani da Kalmar Sagagan-sagagan, tana bayyana irin jikin da Bala yake da shi, da zatinsa, da tsawonsa. Domin da dogo ne ba ya da jiki sosai sai a ce zalab-zalab! In gajere ne a ce, duƙui-duƙui!
    [45] An yi karon da Bala ke waƙewa can gefen tsohuwar kasuwa Bunza, daidai gidan marigayi Musa Yaro, wajen da Musa mai taba (taba gari) ke zama. Daga wurin, zuwa kantin Alhaji Ɗandare, akwai tazara. Gidajen Udulu da Ajayi su ne muka bayyana a tushen bayani na (44). Duk aguje aka wuce wuraren, ba ji, ba gani, bale waigawa.
    [46] Don ƙarin bayani a kan Garba Maitandu Shinkafi da waƙoƙinsa a dubi Shinkafi, R. H. (2012) “Garba Maitandu Shinkafi da Waƙoƙinsa” kundin digirin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
    [47] Kunama ta harbe shi ranar Lahadi, ya yi ɗan raki, aka yi masa dariya. Don haka, ya tsara waƙa, ya saka duk wani wanda kunama ta taɓa harbi a garin Shinkafi. Duk wanda ya yi masa dariya ya sa ‘yan’uwansa ciki. Gindin waƙar shi ne:
    Gindi:  Kuna zan wa kiɗi
    :Zama ciwo ag gare ta
    :Ta halban na jiya
    [48] Don ƙarin bayani a kan rabe-raben mawaƙa a dubi tushen bayani na (26).
    [49] Kamar Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun duk da yake yana da uban gida ‘Yandoton Tsafe, amma ya shiga cikin mawaƙan jama’a, domin ya yi wa jama’a da waƙa barkatai.
    [50] Tawa babban lardi ne a Jamhurioyar Nijar, can ne matattarar Buzaye fararensu da baƙaƙensu. Jiha ce a yanzu, mai gwamna na kanta. Ana rubuta suna haka “Tahoa” amma Hausawa na furta shi “Tawa”. Kano birni ne da ya tattaro al’ummomi iri-iri a bangon duniya. Asalin mafi yawa daga cikin mazaunanta bai salwance ba. Ɗanƙwairo ya san da haka, don haka yake nuni ga asalin wani ɗan siyasa da ke son ya ci idon sarki, ya ce masa “ɗan Buzu”.
    [51] A ƙa’idar gudu, wanda duk aka kora wurin da zai tsira zai dosa, kuma duk wurin da ya dosa ya san shi, ko ya ɗan san shi. Misalin da na bayar na Bala Maigumbe Bunza, wuraren da ya biya a guje, har ya kai gidan Fati, da Ɗankalmalo, duk hanyar zuwa gidansa ce. Ɗanƙwairo da ya ce, a bugi kan ɗan Buzu, bai ce ya yi Wudil ba, ko Bichi, cewa ya yi, sai “Tawa” cibiyar Buzaye. Wannan shi ne fassarar ma’anar karin maganan da muka ambata. Lallai duk abin da ya yi kora shi ke gwadin/nuna hanya.
    [52] Don ƙarin bayani a dubi, Yahaya, I. Y. (1988) Hausa a Rubuce. Zariya, NNPC.
    [53] Alhaji Abubakar Imam, ya kawo shi cikin rubuce-rubucensa. Asalim tarihin shi ne, wani ɓarawo ya je gonan wani ya sace masa riga. Da mai riga ya gan shi ya biyo shi a guje yana cewa: “Bawan Allah, ka tsaya ka ba ni layata, ka tafi da sauran tufafi na bar maka”. Ɓarawon bai kula ba, ya ci gaba da noman kare. Da ɓarawon ya kawo gonan wani matsiyaci ya sake ɗaukar rigarsa. Gogan naka, riga ɗaya kawai yake da ita a duniya, sai ya gaya wa maƙwabcinsa a gona cewa: “Matata tana da ciki in ka je gida ka gaya wa baba, in an haihu, a raɗa wa ɗan suna. In mace ce, in ta isa aure, a yi mata, don ni yau, gudun shekara da shekaru ya same ni.” Da ɓarawon ya ji haka, sai ya bushe da dariya, ya ce: “Matsiyacin banza ga abinka nan wofi”. Ya jefar masa da ‘yar rigarsa ya sha da ƙyar, da rigar wanda ba ya iya gudun shekara da shekaru.
    [54] An ce, wai wasu malamai ‘yan raraka suka je gidan wani tajiri sananne a Kano. Suna zaune cikin babban falonsa shi kuwa yana can gidan sama. Can suka ga ya sauko aguje da bindiga ɗure da albarushi, daga shi sai gajeren wando, alamar motsuwar hankalinsa ya tashi. Da ma an san shi da ita. Ya sauko falo, ya tarar da malamai zazzaune da carbi, ana salati. Ya ɗaga kansa ya dubi hoton mahaifinsa da ke rataye a bangon ya sa bingida ya harbe shi, ya warwatse falo ya ruru da hayaƙin albarushi. Ya dawo kan malamai masu jiran ya sauko ya ba da sadaka ya tambaye su: “Ko kun gana mini wurin da Annabi Musa (AS) ya biya?” Nan take suka ce, “Ga wurin da ya bi”. Suka rugo falo a guje, suka nuna masa hanyar da za ta zarce cikin gidansa, su ko, suka yi waje, in ba ka yi, ba ni wuri. Wannan labarin a kan gudu aka gina shi, ƙunshiyarsa “tsoro”. Hira da Malamina Farfesa Ahmad Haliru Amfani, 2010.
    [55] An camfa cewa, idan aka ga yara na wasan yaƙe-yaƙe, yaƙi ba ya nesa ga al’umma. Idan suna wasan guje-guje, yunwa ba ta nesa. Idan suna wasan kokuwa da dambe daminar da ke tafe za ta yi kyau. Idan suna wasan kuwace-kuwace da wuya ba yi gobara ba.
    [56] Bareyi-bareyi, wato wasan gudu irin na barewa. Za a dinga gudu ana laɓe wa juna kamar dai yadda barewa ke laɓewa ta dabirta karnan farauta da mafarauta.
    [57] Tawayya wasan ƙwallon tsumma (ragga) a jefa a sharɓe; a ruga a ɗauko. Haka za a ci gaba, har sai an gaji, ko an galabaita.
    [58] Ɗandoka su ne dogarai masu ɗaura jan rawani da yin ɗamare da jan ƙyalle. A da, su ke kula da dokokin ƙasa da sarakuna ke shatawa. Bayan zuwan Turawa ne aka yi ‘yan sanda, wato waɗanda ake ba sanda (ɗan kulki) da kayan sarki irin na yanzu. ‘Yan boko na yi wa sandar suna da “talk-true”. Wai da ita ake tilasta wanda ake tuhuma ya faɗi gaskiya. Don haka ake ce musu ‘yan sanda.
    [59] Don ƙarin bayani a kan yadda Bahaushe ke kallon Bature a dubi, Umar, M. S. (2005) Islam and Colonialism: intellectual Responses of Muslims of Northern Nigeria to British Colonial Rule. Leiden: Brill.
    [60] Rashin maiƙonsu shi ne rashin ƙwazonmu mu ɗalibai. Ai Hausawa cewa suka yi, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Bisa ga ƙa’idar karatu, kowa ya ci zomo ya ci gudu.
    [61] Haƙiƙa jahiltar da aka yi wa sani, shi ya kawo tunanin ganin rashin fa’idar binciken wani abu da ya shafe shi.
    [62] Wajen fafitikar binciken tushen mutane harshe ne babban makamin haziƙin manazarci, domin a ko’ina mutane suka sa kansu, harshensu na nan tare da su. Tattare da kare-karen harshe da ke ga Hausa, misali Kananci, Haɗejanci, Zazzaganci, Dauranci, Kurfayanci, Gudduranci, Kabanci, Gobarci, Arabci, Gimbananci, Gubanci da Yawuranci kowanannensu da Kalmar “gudu” yake amfani kuma ba ta da wani suna face “gudu”. Wannan zai iya buɗe ƙofar binciken kalmomi, domin tantance asalin masu magana da harshen. Domin ƙarin bayani a kan wannan a dubi.
    [63] Idan gudu bai faɗo cikin waɗannan rukunai biyu ba, ana sa ran “gudun motsa jiki ne.” Duk guje-gujen da muka lisafa a wannan takarda suna hawa kan “fargaba” ko “buƙata”.
    [64] Wannan takarta ta himmatu ga adabin baka kawai, idan da sarari, sai a ɗora wani bincike a kan yaɗuwar gudu a rubutaccen adabi.
    [65] Misalan da aka gabatar a tushen bayani na (10) ya isa ya wadatar.
    [66] Ina fatar za a sake duba yiwuwar a saka ire-iren al’adunmu, da suka yi naso cikin adabinmu, a cikin manhajar karatunmu. Zuwa gaba, za a samu al’ada cikin adabi, amma bayanin yadda take ya faskari manazartan lokacinta. Idan aka yi nazarin ƙwaƙƙwafi na waɗannan abubuwa za a ga amfaninsu zuwa gaba.
    [67] Wasannin yara na guje-guje da langa da bareyi-bareyi da tawayya da a-sha-ruwan-tsuntsaye da sauransu, su ne Bature ya tattara nasa ya samu suna Physical Education. Mu ma me zai hana mu yi amfani da wannan sunan mu cusa namu. Yaya za mu riƙe ƙahon nagge, wasu su yi tatsa, sai sun ƙoshi, su raga muna suɗi? Ƙarfin riƙon nagge aka fi mu ko dabarun tatsa? Wallahi! Babu maraya sai raggo.
    [68] Ina da fahintar, mu fara taskace waƙoƙin baka, kamar yadda Sa’idu Muhammad Gusau ya fara a Diwanin Waƙoƙin Baka. kowane fanni na adabi, da harshe, da al’ada, mu yi irin wannan yunƙuri, za mu samu nasara da yardar Allah.
    [69] Duk wani abu mai rai, mutum, ko dabba, ko ƙwaro, yana “gudu”; kuma ba koyawa ya yi ga wani ba. Haka kuma, dalilin da ke sa gudu iri ɗaya ne; ko zomo da gada akwai lokacin da za a tarar da su, suna tafiya, idan ba lalurar gudu ta cika da su ba.
    [70] Ai shi ne ya sa Garba Ɗanwasa ke ce wa zakaransa:
    Jagora: In ishe Dikko na gudu
                :Kaɗo kana baya.
    Ya yi namiji, ya koro Dikko aguje. Dikko in an yi haka, ya bar abin kunya ga na baya.
    [71] Wanda duk aka koro, wuya ta sa ya yi gudu, ko ya gan ta, ko ya ci ta, ko ya ji labarinta, domin makaɗa Narambaɗa cewa ya yi:
    Jagora: Kowac ce yana iyawa ga hili nan
    Yara:   Sai ya ƙetare gidania ba ban kwana
    Gindi:  Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
                :Baban Dodo ba a tamma da batun banza
    [72] Idan mutum na gudu yana waiwaye-waiwaye, ga alama, ya yi laifi. Idan ma gudun jama’a yake yi, ba ya son ya zauna cikinsu, mai laifi ne in ji Narambaɗa:
    Jagora: In ka ga mutum na gudun mutane
                :To, ba banza ba ya yi laifi
    Yara:   In ko sun ƙi shi ya ɓakalce
                :Sai ya yi zaune hanya shi kaɗai
    Gindi:  Tattaki maza ɗan Sanda na Iro
                :Gamda’aren Salau manzan ƙwarai
    [73] Ai Kassu Zurmi ya riga y ace:
    Jagora: “Gudu na yara ne sai mata
                :Don an bak ka kwance duk ba komi.”
                            (Waƙar ‘yan Jabanda)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.