Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummuwar Mawakan Baka Da Marubuta Wakokin Hausa Ga Yekuwar Gwamnati Kan Shirin Ilimin Zamani

This paper attempts at glancing through the works of oral and literary compositions of Hausa singers and poets in order to establish their contributions to various government campaign for education. In the paper, it was found that both two compositions had ralied round the minds of Hausa community emphasizing upon them the importance and benefits that could be gotten when they embrace educational policies of governments and the debilitating effects of ignorance and evil consequences of shunning educational pursuits at whatever level.


Gudummuwar Mawaƙan Baka Da Marubuta Waƙoƙin Hausa Ga Yekuwar Gwamnati Kan Shirin Ilimin Zamani

Bello Bala Usman
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University Sokoto Nigeria


Abdurrahman Faruk
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa ‘Yar Aduwa University Katsina Nigeria

1.0     Gabatarwa
Waƙa fa kowace iri ce: Ta baka ko rubutacciya, ta wuce duk inda ake tunanin ta dangane da isar da saƙo ga waɗanda ko inda ake son isar da shi. Shi ya sa ma idan har ana so a isar da saƙo cikin sauƙi kuma nan da nan to, a yi amfani da hanyar isar da saƙo ta waƙa. Wannan bai rasa nasaba da daɗin sauraro da take da shi wanda da haka ta tsere wa abokan tagwaicinta a adabi wato labarin zube da wasan kwaikwayo. Da waƙa akan faɗakar ko a yi wa al’umma hannunka-mai-sanda dangane da wasu lamurran duniya, wato a sa mutum ya fahimci kuskurensa da kansa don ya gyara. Da waƙa akan yi wa mutane wa’azi cewa su daina wasu ayyukan assha su himmatu wajen aikata halaye na gari waɗanda al’umma mai tasowa za ta koya. Haka kuma, da waƙa akan ilmantar da wanda bai san wani abu ba, ya sami sanin abin, don ya yi masa amfani a zamansa na duniya wani lokaci ma har da zamansa na Lahira.
Dangane da yaɗa manufofin gwamnati kuwa da mawaƙa suka himmatu a kai, lamarin daɗaɗɗen abu ne. Za a iya cewa tun lokacin da aka sami ‘yancin kai a Nijeriya wajen shekarar 1960, gwamnati ke ta ɓullo da wasu shirye-shirye na gyaran zamantakewar rayuwa da bunƙasa yanayin rayuwar al’umma da yaɗa manufofin Turawa dangane da abin da suka kira wayewa ko zamananci. Idan irin waɗannan shirye-shirye suka samu ta ɓangaren gwamnati, sai a tara mawaƙan baka da marubuta waƙoƙin Hausa domin a yi musu bayani kan batun da ake so su yi waƙoƙi a kai domin jawo hankalin jama’a su fahimci alfanun shirin da gwamnatin ta ɓullo da shi, ko kuma su gane illar abin da gwamnatin ta hango domin su tsira daga faɗawa a ciki. Misali shirye-shirye irin su alluran riga-kafi ko shirin Ilimin Bai Ɗaya (UPE), tsaftar muhalli da dashen itatuwa dai sauransu.
Wani lokaci wasu shirye-shiryen ba ma sai gwamnati ta kira waɗannan mawaƙa ta faɗa musu manufarta a kan wani shiri na musamman ba, a’a ana samun wasu lamurra na ƙyama ko masu haɗari da sukan yi shigar burgun kutse a cikin al’umma. Nan da nan, sai mawaƙa su duƙufa wallafa waƙoƙi domin nusar da al’umma illar irin waɗannan lamurra da nufin kada su bari sai matsalar ta azabtar da mutane sosai yadda da wuya a shawo kanta cikin sauƙi. Misali karuwanci da daudu da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ko fataucin su, da bangar siyasa da dai sauran ayyukan ta’addanci.
Nazarce-nazarce irin waɗannan ba yau aka fara gudanar da su ba. Wato masana da dama sun sha gudanar da bincike-bincike a kan mawaƙan baka ko rubutacciyar waƙa dangane da yadda suke bayar da gudunmmuwa wajen raya wasu fagage na bunƙasa rayuwar al’umma. Misali, yadda aka yi bayanin wani ɓangare na tarihi. A cikin Waƙar Yunwar Shago ta Umaru Nasarawa, Wazirin Gwandu, Usman (1997), sai kuma irin yadda waƙa take kasancewa a tunanin yara ƙanana, Dunfawa (2005). Wani nazarin kuma fasahar mazan jiya ya duba da gudunmuwar Alhaji Mu’azu Haɗeja, Omar (2015). Sai kuma binciken digiri na uku a kan rayuwa da waƙoƙin Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu, Usman (2008). Akwai nazarin da aka yi a kan rayuwa da jigogin waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa, Bunza (2009). An yi binciken digiri na uku a kan yadda aka riƙa samun tankiya tsakanin jam’iyyun siyasa a jumhuriya ta farko da ta biyu, Birniwa (1987). Duk waɗannan nazarce-nazarce da bincike-bincike da masana da manazarta suka yi, yunƙuri ne na nuna muhimmanci da matsayin waƙoƙin Hausa na baka da rubutattu wajen bunƙasa rayuwar al’umma.
Manufar wannan maƙala ita ce, yin mayalwacin nazari a kan yadda mawaƙan nan na baka na Hausa, da ma mawallafa rubutacciyar waƙa suka tallafi shirye-shiryen gwamnati na ilimin zamani. Nazarin ya taɓo yadda mawaƙan da mawallafan kan faɗakar da jama’a dangane da muhimmancin ilimi musamman ilimin zamani ko kuma illar jahilci. An kawo misalai daga matanonin waƙoƙin mawaƙan da mawallafan domin kafa hujja.
2.0     Ma’anar Waƙa
            Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ya bayyana waƙa da cewa, “Wata tsararriyar magana ce da ake rerawa a kan kari ko rauji, ” (CNHN, 2006: 466). Kodayake, masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar waƙa. A ra’ayin wani masanin, ba kome ba ce waƙa, illa maganar fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman (Yahaya, 1988: 1). Shi kuwa Yahya a tasa fahimtar dangane da waƙa cewa ya yi:
Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba (Yahya, 1997: 4)
A ganin Umar:
Waƙa tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka waɗanda ake kira baitoci ko ɗiyoyi kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman (Umar, 1980: 3)
            Idan aka lura da ma’anar da Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ya kawo, za a ga cewa, ya kawo bakandamiyar ma’anar waƙa. Domin kuwa maganar fasaha da yake yi a cure. Ta yiwu maganar nan ta baka ce ko rubutacciya. Bayan haka, an nuna a cure za a yi maganar, ke nan idan za a warware ta, ana iya samun wani dogon bayani ke nan. An kuma yi maganar tsari na musamman cikin sha’anin waƙa, wanda ke nufin cewa waƙa ta yi hannun riga da zube, ita tana da tsari na musamman ba kamar zube ba wanda akan zuba shi kara-zube, ba tare da wata ƙa’ida ta musamman ba.
 Amma shi Yahya(1997) a tunaninsa waƙa fa dole ta kasance cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka zaɓa kuma dole sai an auna su don a ga yawan gaɓoɓi ko tsawon ƙafafunsu yadda za su dace da inda ake son a aza su, kuma a sami damar rerawa. Domin rerawa wani babban ginshiƙi ne a sha’anin waƙa ko wace iri ce.
            Ba kamar Yahya(1997) ba, shi Umar(1980) fahimtar da ya yi wa waƙa bai wuce kasancewar ta na gunduwoyi ba, ma’ana, waƙa ana shirya ta curi-curi wanda kowane curi ake ce da shi baiti a sha’anin rubutacciyar waƙa, ko kuma ɗa a fagen waƙar baka. Sai dai shi ma ya lura da muhimmancin rerawa kamar yadda sauran masanan suka lura da hakan. Ba dai za a ce an yi waƙa ba dole sai an ji ana faɗar ta cikin murya ta musamman mai daɗi da rauji mai yaudarar da zuciyar mai sauraro ko karatu, don ya amfanu da saƙon da take ɗauke da shi.
Ko ta ina aka jirkita waƙa, ba dai za ta tsira daga kasancewar ta zance na baka ko rubutacce ba, kuma dole ta ƙunshi baitoci ko ɗiyoyi, kuma cikin tsari na daban, a rere sannan ɗauke da saƙonnin da aka gina ta domin su.
2. 1 Rabe-Raben Waƙa
Ta fuskar yanayi, an raba waƙa zuwa gida biyu: Waƙar Baka da kuma Rubutacciyar Waƙa.
2. 1. 1 Waƙar Baka
Dangane da waƙar baka kuma, ita saƙo ne a cikin furuci da kuma lafazi mai azanci wanda ake gudanar da shi ta hanyar daidaitattun kalmomi waɗanda ake rerawa cikin kalmomi masu tsari da kuma ƙa’ida da sauran dabaru masu jawo hankali. Saboda haka, ita waƙa maganar hikima ce da nuna fasaha (Muktar, 2006:130). Muktar dai ya nuna ƙarara cewa, waƙar baka ita ce wadda ake rerawa da baka, a ji ta da kunne a kuma adana ta da ka. Waƙa ce wadda tsarinta ya kasance cikin tsarin ɗiyoyi da daidaitattun kalmomi kuma masu jan rai ga mai saurararo, shi ya sa ma ta zama karɓaɓɓiyar hanyar isar da saƙo.
2. 1. 2 Rubutacciyar Waƙa
            Masana sun bambanta waƙar baka da rubutacciya. Ita rubutacciyar waƙa wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomin da aka zaɓa waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci (Muktar, 2006:130). Sarɓi, yana da ra’ayin cewa:
Rubutacciyar waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango da kari da amsa-amo da sauran ƙa’idojin da suka danganci daidaita kalmomi da zaɓar su tare da amfani da su a rubuce, sannan a rera lokacin da ake buƙata. (Sarɓi, 2007:1).
Ɗangambo ma cewa ya yi dangane da rubutacciyar waƙa:
Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (Bahari), amsa-amo (Ƙafiya) da sauran ƙa’idojoin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓen su da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba (Ɗangambo, 2007:5)
 Kamar yadda Ɗangambo ya nuna, baiti da ɗango da amsa-amon harafi ko na kalma duk sigogi ne na rubutacciyar waƙa. Amma Ɗangambo ya ƙara da bayyana mana cewa akwai wasu ƙa’idoji waɗanda suka shafi daidaita kalmomi da zaɓensu kai har da ma wasu sigogin da idan a maganar yau da kullum ce, ba za a faɗi haka ko a yi amfani da kalmomin ba.
 Saboda haka, waƙa fa wata babbar hanyar isar da saƙon da ke cikin zuciyar mawaƙi wanda yake son ya isar ga jama’a. Da yawa daga cikin saƙonnin da mawaƙa kan isar da bakunansu ko alƙalummansu, wani lokaci na lamurran da kan faru ne a rayuwarsu ta yau da kullum. Ke nan idan mawaƙi ya ga wani abu ya ɗarsa zuciyarsa ta hanyar ba shi sha’awa ko tsoro ko mamaki ko haushi ko ya faranta masa rai ko ma ya ba shi takaici, waƙa na iya ɓulɓulowa daga bakinsa ko alƙalaminsa. Misali, dubi abin da ya faru ga Alƙali Haliru Wurno na haɗarin da ya yi da babur ɗinsa Honda, jimamin wannan lamari ne ya sa alƙalaminsa ya rubuto Waƙar Fanda. Kuma Sani Sabulu ma da ya yi waƙar “Mai Dadiro, ” ai lura ne ya yi da yadda tamɓelen rayuwa ya kwashi wasu mutane ne suke wahalar da kansu kan neman kilaki sai ya buga waƙar, “Mai Dadiro. ”
 Wani lokaci kuma, wani abin alheri ne mawaƙan kan lura da shi ya shigo a cikin al’umma, amma mutane sun kasa fahimtar alfanun da ke tattare da abin nan. Saboda haka, sai su duƙufa faɗakar da mutane a kan muhimmancin wannan abu har al’umma ta gane. Ko kuma lamarin ya shigo wa al’umma a hagunce, ma’ana wani abin ƙyama ne ya shigo a cikin al’umma misali wata haliyya wadda za ta lalata tarbiyyar manyan gobe (yara), ko ma iyayen yaran kamar karuwanci ko shan giya ko caca, da dai sauransu, to sai mawaƙa su shiga aikinsu na faɗakar ko wayar da kai ko gargaɗi a kan illolin waɗannan miyagun halaye ga jama’a.
 Daga cikin lamurran da mawaƙan baka da rubutacciya suke duƙufa wajen wallafa waƙoƙinsu akwai ilimin zamani. Lokacin da ilimin zamani da aka fi sani da ilimin boko ya shigo ƙasar Hausa, ya sha waƙe-waƙe daga mawaƙan ƙasar Hausa. Amma kafin nan, mene ne ilimin zamani?
3.0     Ma’anar Ilimin Zamani
 Sani musamman na shari’a ko na addini shi ne ilimi. Haka ma karatu na fannin kimiyya ko adabi shi ma ilimi ne. Ilimi na nufin ganewa ko fahinta (CNHN, 2006: 205). A ɗaya ɓangaren, zamani shi ne yayi ko lokaci. Zamani na nufin lokacin da ake ciki ko mai ci (CNHN, 2006: 489). Idan aka haɗa kalmomin biyu: “Ilimi” da “Zamani, ” za a sami “Ilimin Zamani” wanda ke nufin sanin kimiyya ko addini ko shari’a ko adabi ko zamantakewa da ma sauran ɓangarorin rayuwa waɗanda ake yayi ko suke faruwa a cikin lokacin da ake ciki ko mai ci. A taƙaice ilimin zamani bai wuce sanin sababbin fannonin dabarun zaman duniya da Turawa suka kawo wa Hausawa bayan samun ‘yancin kai ba. Wannan sani shi Hausawa suka yi wa laƙabi da ilimin boko.
 Mawaƙan Hausa daga mawaƙan bakan har masu rubuta waƙoƙin, sun wallafa waƙoƙi a kan ilimin zamani dangane da yadda yake da amfani da kuma ɗaga darjar rayuwar ɗan Adam gaba ɗaya, ba sai Bahaushe kawai ba. Daga cikin mawaƙan baka da suka rubuta waƙoƙi a kan ilimin zamani akwai Ɗanƙwairo, da Sani Inka Bakura da Ɗanmaraya Jos da Alhaji Dr. Mamman Shata. Mawaƙan rubutacciyar waƙa kuma akwai irin su Aƙilu Aliyu, da Alƙali Bello Giɗaɗawa da Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu, da Mu’azu Haɗeja da Hauwa Gwaram da dai sauransu. Yanzu wannan nazarin zai yi ƙwarya-ƙwaryan bayani dangane da irin tallafin da mawaƙan baka da kuma mawaƙan rubutacciyar waƙa suka bayar dangane da bunƙasa manufofin gwamnati na yekuwa a kan ilimin zamani.
4. 0 Gudunmuwar da Mawaƙan Baka Suke Bayarwa Ga Shirin Gwamnati Na
 Yekuwa a Kan Ilimin Zamani
            Mawaƙan baka su ne makaɗa da mawaƙan Hausa waɗanda suke haɗa waƙa da kiɗa. Mafi yawancin waƙoƙinsu suna bisa wasu turaku da tubala ne na musamman, misali sarauta, ko sana’a ko jarunta ko sha’awa da gargaɗi da dai sauransu. Irin waɗannan mawaƙa akasarin su sun mayar da kiɗa da waƙa a matsayin hanyar neman abincinsu, wato sana’a ce gare su. Da waƙa suke ci, su sha, su yi sutura, har su yi bikin duniya. Da ita suke ɗaukar ɗawainiyar iyalinsu. Irin waɗannan mawaƙa wasu daga cikinsu suna da iyayen gida waɗanda suke jiɓantar lamurransu, su riƙe mawaƙan kamar ‘ya’yan da suka haifa, kuma su riƙa ba su duk abin da suka nema na buƙatar rayuwa. Da haka, sai su mallaki mawaƙan har ya kasance su mawaƙan ba su da ikon yi wa wasu sarakunan ko iyayen gidan waƙa, har sai sun nemi izini daga iyayen gidan nan nasu, in sun aminta su yi wa wani waƙar, idan kuwa ba su aminta ba, shi ke nan ba za su yi wannan waƙa ba, ko nawa wancan zai ba su.
Mawaƙan baka sun bayar da gudunmuwa sosai wajen taya gwamnati yin yekuwa ga al’umma a kan a rungumi ilimin zamani wato ilimin boko ganin yadda mutanen Arewacin Nijeriya suka yi masa riƙon sakainar kashi, ba kamar yadda mutanen Kudancin Nijeriya suka ɗauke shi ba. A haka ne Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi wata waƙa a kan ilimin zamani mai suna, “Waƙar Ilimi. ” Tun daga gindin waƙar Ɗanƙwairo ya fara fito da muhimmancin ilimi:

Gindin Waƙa: Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Gusau, 2019)

Wannan gindin Waƙar Ilimi da Ɗanƙwairo ya kawo, yana kira ga ‘yan makaranta da su himmatu su ɗauri niyyar neman ilimin addini da na zamani, saboda ba wani farin cikin da ya wuce samun ilimin addini da na boko a duniya. Ɗanƙwairo ya nuna cewa, da neman ilimin da samunsa duk farin ciki ne ga ɗalibi. Daga nan sai ya ci gaba da kawo ɗiyan waƙa masu jawo hankalin ‘yan makaranta dangane da muhimmancin ilimi. Dubi ɗiyoyin:

Jagora : Kowa ya sami ɗa shi kai makaranta,
Y/Amshi : Don ilimi tushen arziƙi ne.
Jagora : Kowa yah haihi ɗa shi kai makaranta.
Y/ Amshi : Don ilimi tushen arziƙi ne.
 : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Tun daga duniya hal Lahira,
 : Ilimi babban gwaddabe ne,
Y/Amshi : Kwab bi shi ba ya kunya,
Jagora : Ta tabbata kwab bi shi ba ya kunya.
Y/Amshi : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Ba a sarauta sai da ilimi,
 : Ba a sana’a sai da ilimi,
Y/ Amshi : In ga ilimi ya fi kyawo,
Jagora : Ta tabbata in ga ilimi ya fi kyawo,
Y/Amshi : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Gusau, 2019. )

 Idan aka lura da waɗannan ɗiyoyin waƙa uku, za a ga cewa suna kawo muhimmancin ilimi ga rayuwar ɗan’adam. A ɗan farko, Ɗanƙwaro ya yi kira ga iyayen yara cewa, duk wanda ɗansa ya isa sa wa makaranta, to ya daure ya kai shi makaranta, saboda muhimmancin ilimi na kasancewa tushen arziƙi, wato duk wani arziƙi na duniya da Lahira yana samuwa ne daga ilimi. Idan a duniya ne, bayan ka yi ilimin boko ka kai wani mataki, sai ka sami managarcin aikin gwamnati mai albashi mai tsoka, to duk abin da ka samu na arziƙi, tushensa daga ilimin nan ne. Ko kuma a ce ka yi ilimin aiwatar da wani kasuwanci, wato ka sami fasahar ƙera wani abu, ko dabarun tafiyar da wani kasuwanci, ka sami arziƙi sosai, to idan ka natsu, za ka ga dai asali daga ilimin da ka yi ne.
Dangane da ilimin addini kuma, bayan mutum ya yi shi, zai san yadda zai bauta wa Mahaliccinsa yadda Ya tsara. Idan ya je Lahira Allah zai saka masa da gidan aljanna. Babu mai arziƙi kamar wanda aka gama hisabi ranar Lahira ya sami gidan Aljanna. Kuma shiga aljannar nan da mai ilimi ya yi, tushensa daga ilimin da ya yi ne, shi ne kuma ya ba shi wannan damar.
Bugu da ƙari, a ɗan waƙar nan na uku, Ɗanƙwairo ya sake kawo muhimmancin ilimi, inda ya nuna cewa shi ilimi babbar hanya ce da ya kamata bayin Allah su bi domin samun tsira daga wahalhalun duniya da Lahira. Kuma duk wanda ya yi ilimi ba zai ji kunya ba duniya da Lahira. Manufar wannan ɗan waƙa shi ne, babu hanyar rayuwa da ta kamata kowane Ɗan’adam ya bi domin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum kamar ilimi. Ilimi ne kawai zai koya wa Ɗan’adam gudanar da rayuwa yadda zai mori zamansa na duniya ya kuma sami rufin asiri daga Mahaliccinsa. Duk wanda talauci ya yi masa kanta a yau duniyar nan, to asirinsa ya tonu. Kuma mai ilimi da wuya ya yi talauci saboda hanyoyin yaƙi da fatara da talaucin da ke tattare da ilimi.
A ɗan waƙar nan na uku da ke sama, yana nuni da cewa sarauta, wato shugabancin mutane a gargajiyance da kuma sana’a duk ba sa yiwuwa sai da ilimi. Da ilimi ne ake sanin matakin jagorancin jama’a har a aza su bisa turba madaidaiciya. Sai shugaba ya san makamar mulki, sannan zai samu biyayya daga mabiyansa, a kuma sami ɗorewar zaman lafiya da yalwar arziƙi. Haka kuma, babu wata sana’ar da za a iya gudanarwa, ba tare da an san yadda za a yi ta ba, kuma a inganta ta. Inji Ɗanƙwairo, ko da za a iya yin sarautar ko sana’ar, sam! Ba za su yi ma wani armashi ba, sai da ilimi. Wato dai mulkin mai ilimi ko sana’arsa sun fi inganci fiye da na jahili.
Bayan muhimmancin ilimi, sai kuma Ɗanƙwairo ya kawo koma baya da naƙasu ko illar jahilci wato rashin ilimi. Saurari waɗannan ɗiyoyi:

Jagora : Wanda bai ilimin Ƙur’ani,
 : Sannan ba ilimin boko,
Y/Amshi : Wayo nai bai kammale ba,
 : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Marar Ilimi ba wayo garai ba,
 : Idan ɗan yaro yay yi ilimi,
 : Sai ka gane shi cikin dattiɓai,
Y/ Amshi : Dattiɓai na ba shi shawara,
 : Don sun san mai hankali ne,
 : Farin cikinmu mu sami ilimi
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya.

Jagora : Mai jahilci ba shi gwamna,
 : Mai jahilci ba shi Di’o,
 : Mai jahilci ba shi Rasdan,
 : Mai jahilci bai Uban Ƙasa,
‘Y/Amshi : Balle har ya zamo Kwamanda,
 : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya. (Ɗanƙwairo: Waƙar Ilimi)

Dangane da illar jahilci a waɗannan ɗiyoyi da Ɗanƙwairo ya kawo, za a ga cewa a ɗan farko, mawaƙin na nuna wa al’umma illar rashin yin ilimi. Idan mutum bai yi ilimi ba, al’umma tana yi masa kallon maras wayo, ko yana da shi dai kaɗan ne. A ɗa na biyu, ya ƙara jaddada illar rashin ilimi da takan haifar da rashin wayo. Sai kuma ya ƙara da cewa duk jahili bai isa ya zauna tare da manyan mutane ba, balle har su ba shi shawara ta gari wadda za ta ƙare shi a rayuwa. Duk wanda bai yi ilimi ba, dattijai da manyan mutane ba su yarda ya matso kusa da inda suke ba, saboda ba su ɗauke shi mai cikakken hankali ba. Amma wanda ya yi ilimi, sai ya shiga cikin manyansa babu wata matsala, ko da kuwa yana da ƙarancin shekaru saboda ilimin ya ƙara masa girma, daraja da martaba a idanunsu.
A ɗa na uku kuma, mawaƙin ya nuna illar jahilci na yadda yake hana mai shi ya kai ga wasu manyan muƙaman gwamnati na jan ragamar al’umma, kuma muƙaman kowa na so ya kai gare su. Daga cikin waɗannan muƙamai akwai Gwamna da Rasdan da Di’o da Uban Ƙasa. Babu yadda za a yi jahili ya riƙe waɗannan muƙamai na gwamnati, sai ya fita daga cikin duhun jahilci.
Bayan haka, Ɗanƙwairo ya kwatanta aikin mai ilimi da jahili, inda ya kawo labarin wasu matafiya, ɗaya yana da ilimin inda za su je, wato ya san wurin. Yayin da ɗayan bai sani ba, wato ya jahilci inda za su je. Ga Ɗanƙwairo da jama’arsa:

Jagora : Sanin hanya ko can ya ɗaram ma sauko,
 : Ga wanin nan yai sabkonai na banza,
 : Sannan yaɓ ɓace cikin daji,
 : Shi ko wanda yas san hanya,
 : Sai da safe yaf fita gari,
 : Hay ya riga shi inda za su,
 : Ya sha ruwa, ya sha hura,
Y/Amshi : Hay ya huta bai taho ba,
 : Hay ya huta bai taho ba,
 : Ka ga sani yai nashi aiki,
 : Farin cikinmu mu sami ilimi,
 : ‘Yan makaranta mui ta niyya.

A cikin wannan ɗan waƙa na sama, mawaƙin ya kwatanta tafiyar wanda ya san hanya da wanda bai sani ba. Shi wanda ya san hanyar zuwa wani wuri, idan ya tashi tafiya ba sai ya tsaya tambaye-tambaye ba, saboda haka zai isa da wuri ba tare da ya ɓata lokaci ba. Amma wanda bai san hanya ba, sai ya tambaya idan bai yi hankali ba yana iya ɓacewa a daji kamar yadda wannan mutum da Ɗanƙwairo ya ba da labarinsa a ɗan waƙarsa ya ɓace. To haka ayyukan mai ilimi da jahili suke. Kodayaushe mai ilimi ba ya shan wahalar aiwatar da lamurransa na rayuwa, sai ya yi su cikin nasara da kyau, su yi haske har al’umma ta amfana da su. Amma shi jahili kodayaushe cikin duhu yake, yakan daɗe bai gane yadda lamurran rayuwa suke tafiya ba.
Muhammadu Bello Gwaranyo a waƙarsa ta, “Jahilci Rigar Ƙaya, ” ya nuna tun a cikin gindin waƙarsa cewa jahilci tamkar rigar ƙaya yake. Gudun kada rigar ta sa mutum kafin shi ya sa ta, sai Gwaranyo ya ce:

Gindin Waƙa : Jahilci rigar ƙaya ne
 :Yara mu je makaranta.
(Muhammadu Bello Gwaranyo: Waƙar Jahilci Rigar Ƙaya)

A cikin wannan gindin waƙa da ke sama, Gwaranyo ya kawo muhimmancin zuwa makaranta ga ɗalibai, wato don su tsira daga saka rigar ƙaya, wadda babu mai son ya saka ta a rayuwa. Haka kuma, makarantar da Gwaranyo yake kira a je, makarantar boko ce da kuma ta Muhammadiya. A wani ɗan waƙa kuma sai ya soki jahilci wato ya kawo irin illolin da jahilci yake kawowa.

Jagora  : Wanda bai san nun-‘ara ba,
                        : Ebisidi bai iya ba,
                        : Ka tabbata jakin duniya ne.
(Muhammadu Bello Gwaranyo: Waƙar Jahilci Rigar Ƙaya)

Rashin ilimi ko jahilci yana rage ƙima da darjar mutum ya zuwa dabba. Dubi yadda Gwaranyo ya bayyana cewa wanda bai yi ilimi ba, da shi da jakin duniya darajarsu guda. Dangane da illolin jahilci kuma, sai Bello ya siffanta jahilci da rigar ƙaya, rigar da take mai matuƙar ƙunci wajen sakawa (Rambo da Haliru, 2018:449).
            Wani mawaƙin da ya taya gwamnati yekuwa a kan ilimi shi ne Abdu Inka Bakura. A cikin wata waƙa da ya yi mai suna, “Waƙar Mu Ɗau Ilimi Da Gaskiya. ” Mawaƙin ya ɗaga darajar makaranta da ilimi da ma ɗaliban ilimin gaba ɗaya. Ga Inka:

Jagora : Makaranta uwar ƙwarai ta,
                        : Kuma mai riƙon ɗiya,
                        : Ta riƙi ɗanta,
                        : Ta yi mai sutura ya shigo.
(Abdu Inka Bakura: Waƙar Mu Ɗau Ilimi da Gaskiya)

Tabbas Abdu ya fito da martabar ilimi a nan, tun da ya kira wurin neman ilimin da uwa mai tallalin ‘ya’yanta, ta ci da su, ta sha da su har ta yi musu sutura. Kuma lallai haka abin yake domin idan ilimi ya samu a makaranta, da shi ne mutum zai yi aikin gwamnati ya sami albashi, ya ci abinci, ya yi sauran hidimomin rayuwa. To ka gani kamar ta ba shi ke nan. Can gaba ya ƙara cewa a cikin wani ɗa:
Jagora : Makaranta uwar ƙwarai ta,
                        : Kuma mai riƙon ɗiya,
                        : Ta riƙe ɗanta,                          
                        : Ta yi mai mota ya shigo.
Y/Amshi : Gwamnati horo takai, mu ɗau ilimi da gaskiya.
(Abdu Inka Bakura: Waƙar Mu Ɗau Ilimi Da Gaskiya)
Darajar ilimi ta wuce ta samar wa mai ilimi ko wanda ya yi makaranta da sutura ko abinci, har tana samar masa da mota ta shiga. Duk mai ilimin da ya kai ga mota, to an hau wani mataki na jin daɗin rayuwa. Kowaɗanne irin iyaye ne a duniya suna son su haifi ɗa ko ‘ya’ya shiryayyu. Kuma wannan shiriya inji Inka ana samun ta ne a makaranta kuma a cikin ilimin da ake koyarwa.

Jagora : A kai yara su koyi ilimi,
                        : Makaranta ta gyara,
                        : Ta hora maka shi,
                        : Ta kuma shirya maka shiya,
Y/Amshi : Gwamnati horo takai, mu ɗau ilimi da gaskiya.
                                                            (Abdu Inka Bakura: Mu Ɗau Ilimi Da Gaskiya)

Wannan ɗan waƙa da Inka ya kawo a sama, yana ƙara fito da yadda ilimi yake zama hanyar shiriyar yara. Duk rashin ji ko janjanci na yaro, idan aka kai shi makaranta ya sami ilimi, ko bai daina ba kwata-kwata, insha Allahu zai ragu. Idan kuwa aka sami nasarar haka, ilimi ya zama babbar hanyar shiriyar al’umma.
Wasu daga cikin muhimman nasarorin da aka samu ta fuskar ilimi, ko a ce cin gaban da ilimin zamani ya kawo a cewar Audu Inka akwai irin su kayayyakin ƙere-ƙere na kimiyya da fasaha. A cikin wannan ɗan waƙa na ƙasa, ya jaddada hakan:

Jagora : Can dori da babu ilimi,
 : Dori abin hawanmu jaki doki muna suka,
 : Sai aka sami ilimi nana aka ƙera keke,
 : Sai aka ƙera fanda, keke ba ƙafa huɗu,
 : Fanda ba ƙafa huɗu,
 : Ga mu muna gudu da su da ƙafafu huɗu.
 : Zamani yana zuwa ilimi na ƙaruwa,
 : Sai aka ƙera mota mai ɗaukar mutum biyar,
Y/Amshi : Ku san ilimi nak kawo hakanga,
 : Mui aniya mu ɗau ilimi da gaskiya.
(Audu Inka Bakura: Waƙar Mu Ɗau Ilimi Da Gaskiya)
Wannan ɗan waƙa na sama ya bayyana yadda lamari ya faro kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa. Inka ya bayyana yadda Bahaushe yake amfani da dabbobi wajen sufuri. Yakan yi wahala da su, kamar ciyar da su da kuma kula da lafiyarsu. Kwatsam sai ga zamani ya zo, Turawa suka zo da sababbin kayayyakin kimiyya da ƙere-ƙere. Kuma aikin da kayayyakin ƙere-ƙeren za su yi wa Bahaushe ya fi wanda dabbobin nan za su yi. Tushen waɗannan ƙere-ƙere daga ilimi. Dole sai da aka koyi yadda za a yi su da yadda za a sarrafa su. Shi kansa Inka ya faɗa a cikin wani ɗan waƙa nasa yadda yake jin raɗaɗi a ransa da bai ilimin boko mai zurfi ba. Ga Bakuran:

Jagora : Abdun Inka na ji zafi da ban da ilimi,
 : Inda ina da ilimi,
 : Ko da ina ta jin Turanci kaɗan-kaɗan,
 : Da na ɗau kiɗa da waƙa,
 Y/ Amshi : Mu yi ƙetare mu zo mu ga Babangida.
Jagora : Abdun Inka na ji zafin kuma ban da ilimi
 : In da ina da ilimi,
 : Ko da ina ta jin Larabci kaɗan-kaɗan,
 : Da na ɗau kiɗa da waƙa,
 : Na zo ƙasar Iraƙi,
 : Na zo gidan Hussaini Saddam na ganai.
Y/Amshi : Gwamnati horo takai, mu ɗau ilimi da gaskiya.
(Abdu Inka Bakura: Waƙar Mu ɗau ilimi da gaskiya)
Kukan zuci ne Abdu Inka yake yi irin na mutumin da bai yi ilimin zamani ba. Inka yana nuni da cewa, idan mutum bai yi ilimin zamani ba, to zai zama kifin rijiya. Wato babu ƙasar da za ya iya zuwa, saboda kuwa ba ya jin harshensu, su ma ba sa jin nasa. Amma idan mutum ya yi ilimin zamani, zai ji harsuna iri-iri misali harshen Turanci da Larabci, wanda zai ba shi dama ya ziyarci ƙasashen Larabawa da Turawan. Amfanin ilimi ke nan.
Daga nan sai Inka ya waiwayo ga illar jahilci inda ya faɗa a cikin wani ɗan wannan waƙa:

Jagora : Ilimi uwa uba ne,
                        : Kwat tashi babu ilimi,
 : Ya girma babu ilimi,
 : Ko ya biɗa buƙata,
 : Yac ce a ba shi,
 : Ba a kulawa da shiya.
Y/Amshi : Gwamnati horo takai, mu ɗau ilimi da gaskiya.
(Abdu Inka Bakura: Mu Ɗau Ilimi Da Gaskiya)

Saboda muhimmancin da ilimi ke da shi a rayuwar ɗan Adam, ya sa Inka ya siffanta shi da mahaifiya (uwa), da kuma mahaifi (uba) ga kowane mutum. Rawar da iyaye ke takawa ga ci gaban rayuwar ‘ya’yansu, irin ta fa ilimi yake takawa ga ɗalibi. Rashin yin ilimi (jahilci) yana mai da mutum abin ƙyama a cikin al’ummar da ya tashi. Wannan ƙyama takan zo da muni har ta kasance idan ya nemi taimako wurin mutane, ba za a yi masa ba, saboda ana ganin cewa bai cika mutum ba.
            Daga cikin mawaƙan baka da suka taya gwamnati yekuwa a kan ilimi, har da Alhaji Ɗanmaraya Jos. Wannan mawaƙi, ya waƙe malamin makarantar boko. Kodayake, waƙarsa ba ya yi ta kai-tsaye a kan ilimi ba ne. Sai dai kawai ya yi wa malamin makarantar boko ne waƙa. To amma a cikin waƙar yana bayyana alfanun ilimi da masu koyar da shi, saboda ilimi ba zai yi tasiri ba, sai da mai koyar da shi wato malami. Ga abin da yake faɗa a ɗan waƙarsa:

Jagora : Wannan kiɗan tica ne,
 : Tica uban karatu,
 : Wo, tica uban karatu.
Jagora : Injiniyan gidaje,
 : Injiniya na hanya,
 : Da masu ƙere-ƙere,
 : Da masu zane-zane,
 : In ba akwai tica ba,
 : Da ya akai su koya?
 : O! Tica Uban Karatu,
             ( Ɗanmaraya Jos: waƙar Tica)
A nan Ɗanmaraya yana kawo irin muhimmancin da ilimi ke da shi ta hanyar koɗa tica. A cewarsa, duk wasu injiniyoyin hanya, da masu zana yadda za a tsara gidaje da hanyoyi, da masu ƙera kayayyakin kimiyya da na ƙere-ƙere, duk sai da ilimi wato sai malamin makaranta ya koyar da su.

4. 0 Gudunmuwar da Marubuta Waƙoƙin Hausa Suke Bayarwa Ga Shirin Gwamnati Na Yekuwa a Kan Ilimin Zamani
 Marubuta waƙa su ma kamar mawaƙan baka suke, suna bayar da gagarumar gudunmuwa wajen taya gwamnati yin yekuwa a kan ilimin zamani. Sun wallafa waƙoƙi sosai don faɗakar da jama’a a kan muhimmancin ilimi da kuma illar jahilci. Daga cikin marubuta waƙoƙin Hausa waɗanda suka rubuta waƙa a kan ilimi akwai Alhaji Aƙilu Aliyu. Ya rubuta waƙar, “Ƙalubale. ” Ita wannan waƙa ya rubuta ta ne sakamakon gasar rubuta waƙoƙin Hausa da gwamnatin lokacinsa ta sa tsakaninin marubuta waƙoƙin Hausa a kan muhimmancin ilimi. Wannan bayani na gasa ya fito tun a farkon baitin waƙar tasa.

                                    Ƙulun ƙulifit abu dunƙule,
                                                Ƙalau na ƙale ƙalubale.
(Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)

A ɗango na biyu na wannan baiti Aƙilu ya ce, “Ƙalau na ƙale ƙalu bale, ” wato “ƙalewa” a nan na nufin ya haye can saman abokan takara ke nan. “Ƙalau” kuma na nufin hayewa daidai kuma da tazara tsakaninsa da abokan hamayya. To daga nan sai ya ci gaba da salon tatsuniyar da ya fara da shi a ɗango na farko. Shi wannan salo, salo ne na tatsuniyar kacici-kacici, inda akan ce, “Ƙulin ƙulifita, amsar sai a ce, “gauta. ” Matar ƙulifita, amsar it ace, “yalo. ” Dubi yadda ya tsara lamarin:
                                    Kacinci ka ci: miye abin,
                                                Da ke yaɗo kuma dunƙule.
                                    Ya watsu ya barbazu tattare,
                                                Da rassa ga shi a mulmule.
                                    Kadan ka ture zuciya,
                                                Da ilmu ake ƙalubale.
(Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)

Kamar yadda sigar tatsuniyar kacici-kacici take a adabin Bahaushe, wani abu ake siffantawa da wasu kalmomi a buƙaci mai saurare ko mai karatu ya yi amfani da tunanin basira ya gano mene ne aka siffanta haka, ya kuma faɗi abin. Shi ne kuma a ɗango na ƙarshen baitocin nan uku da ke sama, Aƙilu ya faɗi amsar abin da yake nufi wato ilimi. Ke nan ilimi ne ke da waɗannan siffofi. Saboda muhimmancin ilimi ne ya sa Aƙilu yake ƙara wa mutane ƙwarin guiwa wajen neman sa har ma yake cewa:
                                   
                                    Abin da ya kyautu da mu yi,
                                                Mu himmatu kar mu kashangale.
                                    A Ofis ko a cikin sito,
                                                A kowane gu ya maƙalƙale.
                                    Mu je mu tsaya mu fito da shi,
                                                Mu jajjawo shi mu ƙwaƙule.
                                    Ina magana kan ilmu ne,
                                                A nan ƙumshinsa na walwale.
                                    Da kyau haka bai zama aibu ba,
                                                A kan ilimi mu zaƙalƙale.
                                    A cikin nema nasa kar mu ji,
                                                Kasala kar mu katangale.
(Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)

Duk waɗannan shawarwari da Aƙilu yake bayarwa na ƙwarin guiwa ne a kan a tsaya tsayin-daka domin neman ilimi. Duk wata wahala da aka yi wa ilimi, to ba a faɗi ba, saboda ya cancanci a yi masa hakan. Marubucin kuma ya kawo wasu jerin tambayoyi masu ƙara fito da darajar ilimi cewa a cikin wasu baitoicin wannan waƙa:

                                    A nan ya kyautu na tambaya,
                                                Abin da ya harɗu a walwale:
                                    A yau ƙoshi waye da shi?
                                                Mutan ilimi suka hamdale.
                                    Su waye masu faɗa a ji,
                                                Da sun magana ta daddale?
                                    Cikon girma wa ke da shi?
 Mutan ilimi suka kammale.
                                    Ashe masana su ne gaba,
                                                A komi ba su zama bale.
                                    (Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)
Waɗannan baitoci guda biyar masu ɗauke da tambaya da amsa, suna ƙara fito da irin alfanun da masu ilimi ke tsinkaya daga gare shi. Misali, mai ilimi ne ke samun wadataccen ƙoshin abinci, kuma idan ya yi magana sai a saurare shi ko da ba shi da rigar kirki, shi al’umma ke kallo da girma a idanunsu, kai shi ne gaba-gaba a kowace irin harkar arziƙi. To idan mutane suka fahimci haka, wa zai yi wasa da neman ilimi?
            Al’adar marubuta waƙoƙin ilimi ce, bayan sun bayyana alfanu da muhimmancin ilimi, kuma su zayyano illar jahilci da nufin tsoratar da mutane a kan hakan. Aƙilu Aliyu ma ya yi hakan a wannan waƙa tasa ta Ƙalubale. Ga yadda ya soki jahilci:

                                    Kadan da sani ba a tsiya,
Rashinsa ya sa a taɓalɓale.
                                    Marar ilimi ba ya gaba,
                                                A bar shi a baya masha-tile.
                                    Juhala noman Barka ne:
                                                Da baya da baya ya zoƙale.
                                    Marar ilimi dattijo ne,
                                                Irin na biri mai ɗan kwale.
                                    Cikin zarafi assha da tir,
                                                Marar ilimi ya zaƙalƙale.
                                    Wajen madalla ban da shi,
                                                Da an jawo shi ya zumbule.
                                    Fa duk sha’aninsa daban-daban,
                                                Marar nasara a jagwalgwale.
                                    A nan bana dai kam babu shi,
                                                Balle baɗi can ya taɓalɓale.
                                    (Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)

Da tsiya da fatara aka fara tsoratar da jahilai a farkon waɗannan baitoci guda takwas. Sai kuma mawallafin ya nuna marar ilimi ba ya ci gaba kwata-kwata a rayuwarsa. Ya kuma siffanta jahilci da noman Barka, wato yadda wasu ƙabilu a Jumhuriyar Nijar da ake kira Barka suke yin sa. Kamar noma ne na shiririta, tun da ta baya-baya ake yin sa, wato a maimakon a iza sungumin a gaba, sai a mai da shi baya, kuma wani lokaci ma sai ya kare. Kai sai ma Aƙilu ya siffanta jahili da dattijon biri: Ga tsufa, ga lalata. Ga shi dai jahili ya kuma manyanta, amma bai san daidai ba. Duk wani halin ƙyama ya tattara ga jahili, domin bai san abin da addini ko al’ada ko zamantakewa ya ɗora a bisa mizanin daidai ba. Ya ƙara da cewa, ko an jawo shi an nuna wa jahili, abin da ke daidai, saboda illar jahilcin ba zai iya fahimtar inda aka nufa ba. Wato jahilcin zai kasance gare shi wata katangar dutsen da za ta yi masa shamaki da gaskiya kome zaƙinta.
A waƙarsa ta “Kadaura Babbar Inuwa” ma Aƙilu Aliyu ya ba da gudunmuwa sosai wajen taya gwamnati yekuwa a kan ilimin zamani. Tun farkon waƙar bayan yabo ga Allah da gaisuwa ga fiyayyen halitta (Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), sai ya fito wa masu karatu a mutum, wato ya bayyana abin da yake son ya yi magana a kan sa a cikin waƙarsa. Ga yadda ya cicciɓa ilimi ta hanyar kawo irin muhimmancin da ilimi yake da shi :


Ɗan gargaɗi ne ƙwarya-ƙwarya zan yi,
                                    Ba mai yawa ba kaɗan nake gutsurawa.
                        Sannan na bar ku da shi ku dinga tunani,
                                    Wato a kan sa ku kai kuna komowa.
                        A mazanmu har matanmu yara da manya,
                                    Jama’a mu san ilimi muna tarawa.
                        Shi ne Kadaura ilmu babbar gayya,
                                    Inuwa mayalwaciya wajen hutawa.
                        Shin ko akwai wani namu ba ilimi ba,
                                    Mai kai mutum ƙolƙoliyar ɗorawa?  
                                    Ba wanda bai san fa’idar ilimi ba,
                                                In ban da mai gafala marar ganewa.
                                    Ba wanda bai san moriyar ilimi ba,
                                                In ban da mai hasada da mai kushewa.
                                    Ilimi ga mai shi ya fi babban rumbu,
                                                Domin hatsin rumbu yana ƙarewa.
(Aƙilu Aliyu: Kadaura Babbar Inuwa)

Saboda muhimmancin ilimi da Aƙilu Aliyu yake son ya nuna ne har ya siffanta shi da kadaura. Ita kuwa kadaura bishiya ce mai girma da inuwa sosai. Ai iccen maje ke nan kuma kowa ya san yadda yake yin girma ya yi rassa da ganye linkif ya samar da mani’imciyar inuwa. To, yadda wannan icce yake to, haka ilimi yake ga mai shi inji Aƙilu. Ya nuna kuma yadda ilimi ke kai mutum ƙololuwar daraja har ya sami moriya, duk a snandiyarsa (Auta, 2009: 45). A cikin wasu baitukan waƙar tasa ta Kadaura Babbar Inuwa, Aƙilu ya jero wasu muƙamai na aikin gwamnati da mutum zai samu a dalilin darajar ilimi, kamar su aikin shari’a da kashiyan banki da aikin jarida da likita da malamin makaranta da dai sauransu. Ga yadda ya yi jerin sarƙen:
                       
In ba sani ba za a san shari’a ba,
                                    Balle a san odar da ke shiryawa.
                        Ba za ka zam wani kashiyan banki ba,
                                    In babu ilimi da me kake kawashewa:
                        In ba sani ba ka zan dokta ba,
                                    Sai dai akwai ilimi ake aikawa.
                        Aikin tiyata masu ilimi suke yi,
                                    Mai hattara shi ne da ƙulla abawa.
                        Ba ka zamto malamin ofis ba,
                                    Sai mai yawan ilimi yake aikawa.
                        Ba za ka zamto malamin huji ba,
                                    In babu ilmu da me kake hudawa
                                    In ba sani ba za ka zam lauya ba,
                                                A’a haba mai ilmu ke lauyewa.
                                    Aikin jarida masu ilmu suke yi,
                                                Kasgi ƙumusgi ba shi fara tagawa.
                                     In ba sani ba za ka zam tica ba,
                                                Sai mai yawan ilimi yake koyarwa.
                                     Ba za ka zamto reliwen hanya ba,
                                                Fasinja mai ilimi yake tuƙawa.
                                     Ba za zamto malamin daji ba,
                                                Don kai da gwanki inji babu rabewa.
(Aƙilu Aliyu: Kadaura Babbar Inuwa)

Duk waɗannan ayyuka na gwamnati da Aƙilu ya zano, babu wanda za a iya yi ba tare da ilimi ba. Sai mai ilimi kawai yake samun dama da darajar yin su, ya aiwatar da su cikin burgewa da nasara, ya kuma amfanar da al’umma. Daga nan, sai kuma mawallafin ya shiga kawo wasu manyan muƙamai na jagorancin al’umma da shugabanci waɗanda ba a naɗa kowa irin waɗannan muƙamai sai mai ilimi. Muƙaman sun haɗa da Rasdan da Di’o da Gwamna da sauransu. Ga Aƙilu:

                                    Domin rashin ilimi ba kai Di’o ba,
                                                Balle zama Razdan da ba farawa.
                                    In babu ilmu ba a yi ma gwamna ba,
                                                Shumagabanci mai sani ke sawa.
                                   
Irin waɗannan muƙamai kamar yadda aka ambata a baya, muƙamai na gwamnati waɗanda sai an sami wani matakin ilimi ko takardar shaidar ƙare wani karatu a wata kwaleji ko Jami’a, sannan za a naɗa wa mutum su. Ke nan wanda bai je makaranta ba, da shi da irin waɗannan muƙamai sai gani sai hange, da angulu ta leƙa masai sai ta ce, “Garin daɗi na nesa. ” Shi kansa wanda bai yi ilimi ba, ba zai fara tunanin samun irin waɗannan muƙamai ba, don wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.
            Bayan haka, marubuta waƙa, kan yi amfani da damar tasu su soki jahilci wato su kawo illolinsa don al’umma su guje shi su yi nisa da shi. Alhaji Aƙilu Aliyu ya bi sahun ‘yan’uwansa marubuta wajen rattabo illolin jahilci a cikin wannan waƙa tasa ta Kadaura Babbar Inuwa. Nazarci waɗannan baitoci:
                                    Taro ka cinci-ka-cinci, ko a cinta,
                                                Wace ce ƙazamar rayuwa marar yalwa?
                                    Ƙamtaƙalai
                                                Gashe babu romo ko na ɗan lasawa?
                                    Zai zamto ƙungurmin baƙin makwaɗaici,
                                                Koko maɗauki tun gaban miƙawa.
                                    Yaro marar ilimi tasono ke nan,
Mai toshe hanci babu numfasawa.
                                    Ba inda jahilci yake amfani,
                                                In ban da ma cuta a kan cutarwa.
                                    Cutar rashin ilimi tana cutarwa,
                                                Mawuyaciyar cuta marar warkewa.
                                    Shin jahili wai ransa me ya daɗa ne?
                                                Da zamansa ɗin nan na ga gwara macewa.   
(Aƙilu Aliyu: Kadaura Babbar Inuwa)

Idan aka lura da baitocin nan na sama masu nuna illar jahilci, za a ga cewa marubucin ya siffanta jahilci da wata irin gagaruma kuma mawuyaciyar rashin lafiya wadda ba ta da magani, ya kuma ambace shi da tasono wato wata ƙazantar cikin hanci da takan hana numfashi, sannan jahilci shi ke tunzura mutum ya zama makwaɗaici ko ma ya zama ɓarawo in bai yi hankali ba.
            Shi ma Mu’azu Haɗeja ba a bar shi a baya ba wajen taya gwamnati yin yekuwa a kan ilimi. Shi ma waƙarsa da ya yi wa laƙabi da, “Ilimin Zamani, ” ya kira ilimi da gishiri wanda idan babu shi babu miya. Matsayin ilimi a rayuwar Ɗan’adam, daidai yake da matsayin gishiri a cikin miya. Ga yadda ya kawo batun cikin baitoci:
                                    Gishiri in ba kai ba miya,
                                                Ilimi mai gyaran zamani.
                                    Ilimi shi ke gyaran ƙasa,
                                                Har a san ta a wannan zamani.
(Mu’azu Haɗeja: Ilimin Zamani)

Bayan kasancewar ilimi tamkar gishiri a miya, Mu’azu ya bayyana cewa, ilimin ne ke gyara ƙasa, ta bunƙasa dangane da tattalin arziƙi da yalwar al’umma da zaman lafiya da haɗin kai. Idan ilimi ya ba ƙasa irin waɗannan darajoji, tabbas za a ji amonta a cikin duniya. Wato za a san ta ko’ina. Daga nan sai Mu’azu Haɗeja ya fara nuna wa al’umma irin yadda zaman duniya ya kasance a yau cewa babu mai harka ko zaman lafiya da jin daɗin rayuwa, sai mai ilimin zamani. Saboda duniya ta bar yayin kome sai ilimi, da shi duniya ke yi wanda duk ya kuskure masa ya shiga uku:

                                    Maganar asali yau ta faku,
                                                Ta bi halin ilimin zamani.
                                    Maganar yau ni ɗan wane ne,
                                                Sai a bar ta a nemi biɗar sani.
                                    Ɗaukaka da mutunci duk suna,
                                                Gun sana’ar ilimin zamani.
(Mu’azu Haɗeja: Ilimin Zamani)

Haɗeja ya fito ƙarara ya bayyana a cikin waɗannan baitoci cewa, asali ko wani girman tsatso ta kau a wannan zamanin. Wani ɗan sarki ko ɗan attajiri ko wani ƙasaitaccen malami ko jarumi duk an bar yayinta. Abin da kawai ake dubawa a yau har a mutunta mutum shi ne ilimin da ya yi. Da shi ake auna girman darajarsa ko da kuwa ya fito daga gidan talakawa. Wani mataki na ɗaukaka darajar ilimi a rubutattun waƙoƙi da marubutan ke amfani da shi kamar yadda aka yi bayani a baya shi ne ƙara ƙasƙantar da jahilci. A waƙar nan ta Ilimin Zamani ma Haɗeja ya gwasale jahili da jahilci. Ga abin da yake cewa:
                                   
Yadda kaska ke tsotson jini,
                                                Haka jahilci gun zamani.
                                    Da tsiya da talauci duk suna,
                                                Gun da jahilci ya yi sansani.
(Mu’azu Haɗeja: Waƙar Ilimin Zamani)

Saboda tsananin ƙyama ga jahilci da yadda Mu’azu Haɗeja yake son al’umma su kalle shi a wulaƙance don su guje shi, ya sa ya kwatanta yadda jahilci ke zama ƙarfen ƙafa ga al’amurran zamani. A baiti na biyu ma sai ya nuna da tsiya da talauci suna tattare da jahilci, wato ke nan jahili ba ya arziƙi sai dai kullum cikin tsiya da fatara da talauci. Mu’azu Haɗeja ya sake fito da illolin jahilci sosai a cikin waƙarsa ta, “Mu Yaƙi Jahilci. ” Ga yadda Haɗeja ya nuna ma, duk wasu manya-manyan laifuka da ake aikatawa a bisa doron ƙasa, jahilci ne ke haddasa su. Jahili ne kawai zai kutsa cikin ɓarna yana ganin daidai ne saboda raɗaɗin rashin ilimi. Dubi yadda ya fasalta lamarin:
           
                                   
Zalunci gami da lalaci,
                                                Duka mai haddasa su jahilci.
                                    Yawan rikici da cin bashi,
                                                Duka mai haddasa su jahilci.
                                    Sata da fashi da yin caca,
                                                Duka mai haddasa su jahilci.
                                    Rashin haɗa kai, yawan hargitsi,
                                                Duka mai haddasa su jahilci.
                                    Yawan tankiya ga ‘yan iska,
                                                Duka mai haddasa su jahilci.
                                    Hawannafsi, ƙin zumunta mun,
                                                San mai haddasa su jahilci.
Yawan rantsuwa da Allah kan,
            Ƙarya ya laɓe ga jahilci.
Yawan fankama da girman kai,
            Duka caffarsu na ga jahilci.
Shiga zarafin mutane, yi,
            Da mutane yana ga jahilci.
Yawan tsegumi da kinibibi,
            Da yawan kwarmato da ha’inci.
Da gulma da yawan kisisina,
            Duka ususunsu na ga jahilci.
                                    (Mu’azu Haɗeja: Waƙar Mu Yaƙi Jahilci)

Kusan babu irin kaba’irar da Mu’azu bai ambata a cikin baitocin nan nasa na sama ba, kuma ya ce jahilci ne ke haddasa ta. Kamar yadda ya nuna, jahilci ne ke sa mutane saɓa wa Mahaliccinsu, su yi tawaye ga iyayensu, su ha’inci ‘yan’uwansu, su farraƙa tsakanin mutane, da son rai, da mutakabbiranci (girman kai), da sauran munanan laifuka.
            Daga cikin marubutan da suka rubuta waƙar yekuwa a kan ilimi akwai kallabi tsakanin rawuna wato Malama Hauwa Gwaram. Ta rubuta waƙa mai suna, “Yaƙi da Jahilci. ” A cikin waƙar tana bayyana muhimmancin ilimi. Ga abin da take cewa game da shi:
                                    Ku san igiyar riƙon ilimi ku san ta bari,
                                                Kowa ya bar ilimi ya sha wulaƙanci.
                                    Gabas da Yamma Arewa ka duba har da Kudu,
                                                Muka ƙirƙire duka domin ba mu jahilci.
                                    Da farin jini da mutunci za ka same su,
                                                In dai ka rinƙa zuwa yaƙi da jahilci.
                                    Ka zamo abokin mutane na da alheri,
                                                Kowa ya gano ka ya san ka yaƙi jahilci.
                                    Hankalinka zai gyaru kowa yai ta ƙaunarka.
                                                Ka ji gargaɗin malaman yaƙi da jahilci.
                                    (Hauwa Gwaram: Waƙar ‘Yaƙi da Jahilci)                           
Yekuwar da Hauwa ta yi a cikin waɗannan baitoci dangane da ilimi ita ce, yadda ta nuna duk wanda ya bar ko ya saki tafarkin ilimi, lalle zai sha wulaƙanci. Ta ce ai duk wani farin jini ko mutunci a idon mutane yana samuwa ne ta hanyar ilimi. Neman ilimi inji Hauwa zai sa mai yin sa ya haɗu da abokan arziƙi masu ɗimbin yawa. Mai ilimi kodayaushe yana burge mutane. Bayan cicciɓa ilimi da Gwaram ta yi, sai kuma ta karkato ga illar jahilci don a guje shi. Me take cewa a kan jahilci?
                                   
                                    Zama ki saurari amsa wacca zan ba ki,
                                                Domin takaici ake yaƙi da jahilci.
                                    Ku dubi Nomau wuyar da ya sha yana yawo,
                                                Ya ja wa kansa musiba saboda jahilci.
                                    (Hauwa Gwaram: Waƙar Yaƙi da Jahilci)
                                                 
A ƙoƙarinta na nuna illar jahilci, Hauwa Gwaram tana faɗa wa mata ‘yan’uwanta da ma mazan gaba ɗaya cewa, wanda duk ba ya da ilimi zai rayu cikin takaici da baƙin cikin rayuwa. To wannan baƙin cikin rayuwa da takaici zai sa mutum ya koma makaranta da girmansa ya koyi ilimi. Ta ce idan babu ilimi sai yawace-yawace na babu gaira babu dalili.
            Shi ma Wada Hamza ya bi sawun ‘yan’uwansa marubuta waƙoƙin Hausa, wajen taya gwamnati yekuwa a kan ilimi. A waƙarsa ta, “Neman Ilimi” ya kawo garaɓasar da ke cikin ilimi ta sanin yadda za a ƙera wasu kayayyakin kimiyya da na masarufi don amfanin al’umma. Sai ya ce:
A yanzu komai ka gani,
                                    Fen, tawada da magani,
                                    Mota, madubi na gani,
                                    Keke da babur ka sani,
                                                Duk yin su na gun ilimi.
Dafta da magani nasa,
                                    Joji da kotuna nasa,
                                    Injiniya cira masa,
                                    Malam a durƙusa masa,
                                                Ka ji muƙaman ilimi.
                                    Irin su saƙar gwaduna,
                                    Ɗinki da saƙar rawuna,
                                    Ƙarau da jeme fatuna,
                                    Harbi da aske kawuna,
                                                Duk sun bi layin zamani
(Wada Hamza: Waƙar Neman Ilimi)

Daga cikin falalar ilimin da Wada Hamza ya haska wa mai karatu a waƙar tasa ta Neman Ilimi akwai nuna yadda ilimi ya kasance sila ta samar da wasu kayayyakin kimiyya da fasaha da ma samuwar sana’o’in gargajiya na Bahaushe. Hanza ya yi bayanin cewa duk wasu kayayyakin da muke amfani da su muna gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum cikin inganci, sun ginu ne a sanadiyar ilimi. Sai da aka koyi yadda ake aiwatar da su sannan aka iya aka kuma samar da su ba tare wata matsala ba. Daga cikin sana’o’in gargajiyar da ya ayyano waɗanda ba su samuwa sai an koya sosai an ƙware, wato sai an yi iliminsu, akwai irin su aikin likita da alƙali da injiniya da saƙa da ɗinki da dai sauransu. Wada ya nuna yadda muhimmancin samun ilimi yake ga al’umma sosai. Ya gargaɗi mutane a kan su tashi su nemi ilimi don su tsira daga ƙangin jahilci. Ya yi amfani da salon kira a waƙar tasa inda ya ce:

                        Mai tafiya tsaya kaɗan,
                        Domin ka ji ni ɗan kaɗan,
                        Ga gargaɗi fa ɗan kaɗan,
                        Kila saninka yai kaɗan,
                                    Ruga ka nemo ilimi.
(Wada Hamza: Waƙar Neman Ilimi)

Alƙali Bello Giɗaɗawa yana cikin marubuta waƙoƙin Hausa da suka amsa kiran gwamnatin lokacinsu na yekuwa a kan ilimi. Amsa wannan kira ne da ya yi ya sa ya rubuta waƙar, “Darajar Ilimi. ” A cikin wannan waƙa, Giɗaɗawa ya kawo muhimmanci da irin darajar da Allah Ya yi wa ilimi. A ɗayan ɓangaren kuma, ya kawo illar jahilci da ma kira a kan a nemi ilimi a guji jahilci. Da yake yekuwa a kan muhimmancin ilimi, sai ya ce:
                                   
                                    Mai son ya ɗaukaka ba shi wargi kun jiya,
                                                Ilimi yake nema ya daina jidali.
                                    Don tara ilimi ya fi tarin dukiya,
                                                Samunsa shi ne yaf fi kowane jalli.
                                    Ɗibar sa ba ta rage shi ko da ƙanƙane,
                                                Sai ƙaruwa shika yi ka lura halili.
                                    Kuma ba ka neman masu gadi ka jiya,
                                                Kwanta ka yi kwananka babu jidali.
                                    Don ba sito kwanyarka can shika tattara,
                                                Ba ‘yan fashi balle ɓarayin gantali.
                                    Zai ba ka hairi duniya hal Lahira,
                                                Amma fa in ka aikata ga sabili.
                                    Ilimi ku san shi ne tudun taka-ka-hau,
                                                Kwah hau shi ya tsere ma duk wani zalli.     
(Alƙali Bello Giɗaɗawa: Waƙar Darajar Ilimi)

Alƙali ya bayyana ilimi da wani abu mai muhimmanci wanda ya kai duk mai neman ɗaukaka ta hanyar ilimi zai neme ta, duk wanda ya sami ilimi, tabbas ya samu ɗaukaka. Ya fifita ilimi da dukiya, ganin cewa ita dukiya tana ƙarewa, amma shi ilimi bai ƙarewa sai ranar da mutum ya rasu. Inda kuma ilimi ya fi dukiya shi ne ita dukiya ana ɗibar ta tana raguwa, idan ba ƙara ta ake ba, wata rana sai an wayi gari ta ƙare.
            Daga nan sai Giɗaɗawan ya fara kawo illar jahilci kamar yadda tsarin marubuta waƙoƙin ilimi yake. A ra’ayin Alƙali, illolin jahilci ba su ƙirguwa sai dai a kamanta. Waƙa bakin mai ita ta fi daɗi:
                                    Aibi na jahilci ku san bai ƙirguwa,
                                                Ɓannad da taz zaka duk iza ta ga jahili.
                                    Zai cuci kainai kun ga murna ɗai shikai,
                                                Mai hankali duk zai ji tausan jahili.
                                    Don shi ka shirme kodayaushe ga al’amar,
                                                Bai tuntuni bai shawara da su’ali.
                                    In jahili yat tsufa damewa shikai.
                                                Bai son masallaci biɗas shi ga dandali.
(Alƙali Bello Giɗaɗawa: Waƙar Darajar Ilimi)

Waɗannan baitoci na sama da Alƙali Bello Giɗaɗawa ya kawo, suna ƙara tsoratar da mutane a kan zama da jahilci. Ya nuna yadda jahili zai aikata wani abu da zai cuci kansa da kansa, amma saboda duhun jahilci, ba zai iya ganewa ba. Rayuwar jahili inji Bello, duk shirme ce, kuma shi ba ya iya yin tambaya kafin ya aikata wani abu, yana da ƙarancin zurfin tunani. Mai irin wannan halayya kuma kodayaushe yana tare da nadama. Wani lamarin ban tsoro da tsufan jahili shi ne tsufan kwando. Wato yana yin mummunan ƙarshe. Alƙali ya bayyana wa masu karatu cewa idan jahili ya tsufa, sai ya koma wani asharari, ya guje wa masallaci da duk wata hanyar ibada da za ta sa ya sami tsira a Lahira. A maimakon haka, sai ya faɗa wa ɓarna, ya riƙa halartar gidajen shagali da masha’a. Daga nan sai ya yi wa masu karatun waƙarsa gargaɗi a kan su rungumi ilimi:

                                    Wannan ishara babba ta don tuntuni,
                                                A tuna da ilimi shi ka jawo tafaluli.
                                    A tsaya tsayi na daka a sa himma garai,
                                                Wargi a bar shi a bar zama kan dandali,
                                    Niyya a kyauta kar a sa mata maguɗi.
                                                Kyauta ta aikin zai tafo ya yi ƙyalƙyali.
(Alƙali Bello Giɗaɗawa: Waƙar Darajar Ilimi)

Wannan gargaɗi na Alƙali ya ƙara fito da darajar ilimi cewa duk falala ta Allah tana shigowa ne ta hanyar ilimi. Al’umma su dage su nemi ilimi, kada a biye wa zaman dandali inda ba a ƙaruwa da komai sai gardama maras amfani sai kuma ashararanci.
            Yusufu Kantu ma ba a bar shi a baya ba, wajen yekuwa a kan ilimin zamani. Ya rubuta waƙarsa da ya yi wa take da, “Jahilci da Muninsa. ” Kantu ya soki jahilci da kakkausan harshe da alƙalami mai tsini. Kodayake, kafin ya shiga kawo illolin jahilci, sai da ya buɗe waƙarsa da yabo ga Allah Maɗaukakin Sarki. Sannan ya yi addu’ar cewa Allah Ya haskaka masa zuciya da ilimin gaskiya. Ya yi haka ne saboda irin falala da martabar da ilimi ke da ita ga Ɗan’adam. Ga yadda ya buɗe waƙar:

 Ya Ilahi Ya sarki ɗaya,
                         Mai sanin komi baki ɗaya,
 Rabbi Kai Ka san muna zuciya,
             Haskaka ta da ilimin gaskiya,           
                                                Ka cire mata duk jahilci.
 (Yusufu Kantu: Waƙar Jahilci da Muninsa)
Daga nan, sai marubucin ya ci gaba da abin da ya kawo shi, wato ya nufi babban jigon da ya mamaye waƙar tasa shi ne illar jahilci. Dubi yadda ya fallasa jahilci da jahili:
                                                Tun da shi jahilci aibu ne,
Aibi ko ba shi zai rine,
Jahilci mai cutar mu ne,                                                         
Ko fari ne mai shi zai rine,
In jahilci yai kauci.

Jahilci ya fi dare duhu,
Cuta tasa ta fi buhu-buhu,
Don shi kan jera ta sahu-sahu,
In ya dafa mai shi ya dafu,
Mai shi da ganinai sai ci.
Jahilci wanda ya wa yawa,
Wauta tasa ba ta ƙidayuwa,
Ko zance ya yi da faɗuwa,
A ciki sannan ga damuwa,
Ɗauri nasa ba sassabci.
Wanda duk yay yarda da shi ku ce,
Tun akwai rainai to shi ya mace,
Ba shi komi sai ya birkice,
Don basiratai duk ta bice,
Ba shi komi mai inganci.
Ka ga dai bai san Allahu ba,
Abada kuma ba zai san shi ba,
Tun da girman kai bai bar shi ba,
Tambaya a wurin ulama’u,
To ina zai san daidaici?
Jahilci na daɗa ƙaruwa,
Ƙin Allah na daɗa abkuwa,
Faɗin rai na daɗa yaɗuwa,
Ga yawan ganewa mai yawa,
Ga yawan riya ga sakarci.
(Yusufu Kantu: Waƙar Jahilci da Muninsa)

Waɗannan baitocin waƙa na Yusufu Kantu, suna tsoratarwa a kan illar jahilci. A zahiri, kushe jahilci tallar ilimi ne. Yayin da ake tsoratar da mutane a kan zama da jahilci, to lalle ana kuma ƙara ɗaga darajar ilimi ne, saboda kiyoshin juna suke. Abin da ya faru ke nan a cikin waɗannan baitoci da Kantu ya kawo. Ya nuna jahilci babban aibu har zai iya sauya wa mai shi launin fata daga fari da Bahaushe ya ɗauka shi ne mai kyau, zuwa baƙi.
            Saboda illar jahilci ga ɗan Adam Kantu ya ce yana iya dafa mutum kamar yadda ake dafa naman kaza a cikin tukunya ya yi laushi. Jahili wawa ne, jahili shashasha ne, jahili mai girman kai ne da ma sauran munanan siffofi da Kantu ya siffanta shi da su. Ya yi haka ne da nufin kushe jahilci da sa wa mutane a kan su guje shi, su himmatu wajen neman ilimi.
Daga cikin marubuta waƙoƙin Hausa da suka ba da gudunmuwa wajen yekuwa a kan ilimi, akwai Isa Mukhtar. A waƙarsa da ya kira “Waƙar Yaƙi da Jahilci” ya rattabo muhimmanci da alfanun ilimi, ya kuma kawo illoli da naƙasun jahilci, ya yi gargaɗi da kira ga al’umma a kan su tashi ka’in da na’in su yaƙi jahilci domin mugun ciwo ne. Yayin da yake zayyano muhimmancin ilimi ga rayuwa, sai ya ce:

                        Adalcin nan nufina ai ilimi ne,
                                    Da yaz zam dole ne yi nai ko a zuci.
                        Farilla ne cikin zance na dina,
                                    Ibadar tamu addinin salama.
                        Fa shi ilimi fa ya zamto farilla,
                                    Idan ka ƙi ka san ka yo butulci.
                        Karatu dole ne ko ka ƙi da ka so,
                                    To ko jika gare ka kai naci.
                        Batun ilimi ga babba ko ga yaro,
                                    A “U. P. E. ” da “Agency” Kanonci.
(Isa Mukhtar: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

Mukhtar ya bayyana a cikin waɗannan baitoci biyar na sama irin falala da muhimmancin ilimi. Cewa ya yi ma idan ka ji an ce, “adalci, ” to ilimi fa ake nufi, saboda duk wani adalcin duniya sai da ilimi ne yake tabbata. Ya kuma nuna cewa shi ilimin farilla (dole) ne ga rayuwar ɗan Adam. Karatun ilimi shi ne abin da ya kamata a ce kowane ɗa ya kama a rayuwa ya nace ya yi ta yi don amfanin gaba. Kamar yadda Hausawa ke faɗa a zantukansu na hikima cewa, “Gemu ba ya hana neman ilimi. ” Mukhtar ma ya tabbatar da hakan a waƙarsa inda ya ce a ɗan waƙa na biyar da ke sama cewa, ilimi ba ya da babba ba ya da yaro. Daga nan sai ya haɗe ilimin Ƙur’ani da na boko ya bayyana yadda suka yi tarayya wajen wahalar nema, sai dai in an samu, a daɗe ana cin moriyar su. Ga Isa da alƙalaminsa:
                       
                       
 Fa shi ilimin Ƙur’ani ko na boko,
                                    Fa kowanne ne ka tauna na da ɗaci.
                        Fa shi ilimi fa ko ƙaƙa ka samu,
Da ikon Rabbi kai neman abinci.
(Isah Mukhtar: Waƙar Yaƙi Da Jahilci)

A wasu baitocin waƙar, illolin jahilci ya kawo ya dage sai an guje su in ana so a yi rayuwa mani’imciya:

                        Marar ilimi da ka gan shi a titi,
                                    Da ƙyar ma zai yi huɗɗa babu ƙunci.
                        Talallaɓo fa ya kasa a dangi,
                                    Ya ci tuwon uwarsa yai ta bacci.
                        Marar ilimi da me ma zai kama ne?
                                    Da ka gan shi ka ce ma shi ne kumurci.
Ta yaya za a gane jahili ne?
                                    Da shashanci da yin kuma nunkufurci.
                        (Isa Mukhtar: Waƙar Yaƙi Da Jahilci)

Kamannun jahili kamar yadda Mukhtar ya ambata, kodayaushe ka gan shi cikin ƙuncin rayuwa, babu walwala tare da shi. Sannan duk wanda ka gan shi a cikin dangi, za a ga shi ne koma-baya. Wannan alama ce lallai bai yi ilimi ba. Wannan ya sa bai iya neman na-kansa sai dai ya zo ya ci tuwon gidansu wanda danginsa masu ilimi, ma’aikatan gwamnati suka nemo suka kawo. Saboda kaushin hali na jahili, Isa ya siffanta jahili da maciji. Ya nuna jahili shashasha ne marar wayo kuma miskili.
Umaru Nasarawa (Wazirin Gwandu) ma ya ba da irin tasa gudunmuwar wajen yekuwa a kan ilimi. A cikin waƙarsa ta, “Gargaɗi Ga ‘Yan Makaranta, ” ya kawo muhimmancin ilimi da illolin jahilci da kuma gargaɗi ga ‘yan makaranta a kan yadda ya kamata su kasance ga haliyya da tufafi da zamantakewa. Ga abin da yake cewa:

            Kyawon hali shi am mutum,
                        Sannan a so ilimi garai.
            A cikin aji in an shiga,
                        A ishe akwai himma garai.
            Da dare da rana duk a iske,
                        Hanƙurin nazari garai.
            Ga tufa da littattafansa har-
                        Ga jiki akwai tsafta garai.
            Wanki shikai wanka shikai
                        Ɗakinsa ko shara garai.
            `````````````````````````````````````````
Almajiri duka yaz zamo haka,
                        Arziƙi na nan garai.
            Kowa yana murna da shi,
                        Don ko halin girma garai.
(Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu: Gargaɗi Ga ‘Yan Makaranta)

Waɗannan baitoci da Umaru Wazirin Gwandu ya kawo, suna nuna falala da martabar ilimi. Ya bayyana cewa almajirin da ya zama neman ilimin yake yi da gaskiya, za a same shi da halayen ƙwarai irin su tsaftar abinci da ta wuri da ta tufafi da ta tunani. Ya kuma kasance yana da ladabi da biyayya. Ya ce idan almajiri (mai neman ilimi) ya kasance haka, to shi ake kira “almajiri. ” Amma duk almajirin da ya saɓa wa waɗannan siffofi, to jahili ne kuma ba zai sami ilimin da yake nema ba. Wazirin Gwandu ya yi masa laƙabi da:

                       
Almakiri na nan daban,
                                    Shi kam halin ƙyama garai.
                        Ibilisu na shaiɗanu na
                                    An gane taurin kai garai.
                        Mutakbbiri na makiri,
                                    An gane girman kai garai.
Ko an yi foro ba shi ji,
            Halin batsalci ag garai.
Babba da yaro ɗai garai,
            Duk babu mai girma garai.

``````````````````````````````````````````````````
Da cikin aji da cikin gari,
            Kowa shi nemi tsari garai.
Mugun hali ɓarnar mutum,
            Ko da akwai ilimi garai,
Balle daƙiƙi na balidi,
            Babu amfani garai.
A cikin aji in an shiga,
            Abada yawan barci garai.
(Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu: Gargaɗi Ga ‘Yan Makaranta)
                         
Wannan almajiri da Waziri ya kira Almakiri yana matsayin jahili ne kamar yadda Wazirin ya siffanta shi. Dalili kuwa ga shi dai a bisa tafarkin neman ilimi, amma sheɗanci da kaushin hali ya hana shi ya tsaya tsayin daka ya sami ilimin. A ɗayan ɓangaren halayen da ya faɗa Almakiri na yi, haliyya ce ta jahilci. Jahili ne kawai yake da taurin kai da girman kai da batsalci (baɗala) da rashin girmama manya da mugun hali da sauransu. Idan kuwa ɗalibi ya siffantu da waɗannan halaye na jahilci, tabbas daƙiƙanci zai sami wurin zama.

5. 0 Kammalawa
            Rawar da mawaƙan baka da rubutacciyar waƙa suke takawa wajen taya gwamnati yekuwa a kan ilimi, ba ‘yar ƙarama ba ce. A iya cewa ma, ba don waɗannan mawaƙa da mawallafa ba, to da manufar gwamnati na bunƙasa ilimin addini da na zamani ta yi ƙasa a guiwa. Domin duk lokacin da irin wannan buƙata ta taso ta son ƙara faɗakar da wayar wa jama’a da kai a kan ilimi, sai gwamnatin ta tattaro mawaƙan nan na baka da rubutacciya, ta aza musu wannan nauyi. Su kuma a matsayinsu na ‘yan ƙasa na gari sai su duƙufa, kowa ya yi amfani da hikima da baiwar da Rabbi Ya ba shi, ya isar da saƙon da ake son ya isar ga al’umma, ko kuma ya cika alƙawarin da ya ɗauka.
            Wani lokaci ma, ba gwamnatin ba ce kan buƙaci hakan, kawai dai su mawaƙan ne kan tunanin irin muhimmancin da ke cikin ilimin zamanin musamman ganin yadda mutanen Kudu suka yi ma na Arewacin ƙasar nan fintinkau a ɓangaren, kan sa su shirya ɗiyan waƙa ko su samar da baitoci masu kira ga alfanun ilimi. Da yake yayin da ake son nuna muhimmancin wani abu, sai kuma an riƙa kushe kishiyarsa, saboda a rairaye wa al’umma tsakanin aya da tsakuwa. Ke nan, yayin da mawaƙan suke kawo alfanun ko muhimmancin ilimi, a ɗaya ɓangaren kuma suna kawo illolin jahilci da raɗaɗinsa ga wanda ya kasa fitar da kansa daga zazzafar ƙunar jahilcin.
            Kamar yadda aka gani, wannan maƙalar ta yi nazarin waƙoƙin baka na wasu mawaƙan inda aka yi sharhin yadda sukan cicciɓa ilimi domin jawo hankalin mutane a kan su himmatu ga neman sa. Haka kuma, suka kawo wasu ɗiyan waƙoƙin masu nuni ga illar jahilci da yadda yakan zamo ƙarfen ƙafa ga jahilin. Wasu ɗiyan waƙoƙin ma har da gargaɗi suke a kan a guji jahilci. Yayin da wasu ɗiyan waƙoƙin kuma suke kwatanta darajar ilimi ko mai ilimi da jahilci ko jahili. Daga ƙarshe idan wannan maƙalar za ta yi wa mawaƙan ilimi adalci to, tana iya cewa, su mawaƙan baka da rubutacciyar waƙa na ilimi su ne kanwa uwar gami ko gishiri a miya wajen bunƙasar ilimi a yau.

Post a Comment

0 Comments