Duk
lokacin da mutum yake ganin cewa shi fa zai rayu ko shi kaɗai
ne kuma ba ya buƙatar taimakon kowa to akwai matsala babba, amma abu mafi
girma a ciki shi ne son kai, wato ya kasance mutum komai shi kaɗai yake so ya kwashe
ba ruwansa da kowa. In kana da wurin sana'a
kar ka yarda a ce...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 20: Hannu Ɗaya ba ya Ɗaukar Jinka
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Haka Bahaushe yake cewa,
alokacin da ka so fara wata sana'a ko aiki naka na kanka ko kasuwanci dole za
ka buƙaci mutanen da za su taimaka maka wurin
cika burinsu, misali wani tsohon ma'aikacin banki da ya yi wani ƙwarƙwaryan
shago, ya dora wani makusancinsa don ya tafiyar masa da shi, ya kawo duk abinda
ake buƙata masamman na'urannan ta bankin tafi
da gidanka, wannan abu ne mai kyau matuƙa
tunda makusancinsa yana samu da shi, sai dai duk abinda da mutum zai tsara matuƙar zai nemi taimakon wasu to ya tabbatar
waɗanda
suka dace ne za a saka a wurin.
.
Taimakon na kusa da kai
wajibi ne, akwai halin ma da za ka kawo shi kusa don ya riƙa ba ka bayanin duk abubuwan dake
faruwa, amma dagewa cewa naka ne kawai za ka sanya a wuri matsala ce babba wace
za ta iya ruguza maka shiri, sai in ya cancanta da matsayin, wasu kan yi
sha'awar sanya 'yan uwansu makusanta a wararen sana'a da kasuwanci alhali 'yan
uwan ba su cancanci wurin ba, a ƙarshe
sai ka ga an ƙare da nadama, kodai
dan uwan ya aikata ma-sha-a, ko ya yi sama-da-fadi da dukiyar wasu ko handama
da babakere, duka dai munanan abubuwa ne, ko dan uwanka yana da takarda ka
tabbatar ya zauna a wasu wuraren dake da alaƙa da
aikin, ya naƙalci komai, kuma yana
da alƙawari.
.
BIYAYYA
Alƙƙwari a aiki da tattali da
tanadi koyonsa ake yi kamar yadda ake koyon aikin kansa, galibin masu kukan
cewa sun dauko 'yan uwansu sun cuce su za ka taras ba wata horarwa ta masamman
da suka samu kafin su shiga sana'ar, ba su koyi yadda za su yi ta'amuli da
dukiyar wani ba ko kadan, abinda suka sani kawai yanzu za su shiga kudin dan
uwansu, shi ya sa nan da nan sai ka ga abin Allah-wadai ya faru, a ƙarshe kuma su haramta musu ci gaba da
ma'amalla da su har abada, su ce bare ya fi dan uwa, alhali su suka yi kuskure
tun farko.
.
DAIDAI RUWA DAIDAI ƘURJI
A duk lokacin da ka ce kai
da abin hannunka kawai za ka yi harka kana da matsala, amma kimanin shekara 3-4
da suka gabata na taba ganin wani malami yana bayanin cewa kar mutum ya taba
karbar bashi a kan wata sana'a da zai fara, ya ririta abinda ke hannunsa kawai,
na ga kuma waɗanda suka yi masa raddi da cewa kashi 75
cikin dari na waɗanda suka ci nasara ba da
dukiyar hannunsu suka yi aiki ba, masamman masu manyan ma'aikatu da
masana'antu, to dai duk abinda mutum zai yi kar ya taba yarda ya sha ta fi
ciki, dole a ci bashi amma wanda za a iya biya ba wahala, kamar wanda za a
gyara wuri a ƙara jari da
makamantansu.
.
KULA DA MATAIMAKA
Duk lokacin da mutum yake
ganin cewa shi fa zai rayu ko shi kaɗai
ne kuma ba ya buƙatar
taimakon kowa to akwai matsala babba, amma abu mafi girma a ciki shi ne son
kai, wato ya kasance mutum komai shi kaɗai yake
so ya kwashe ba ruwansa da kowa.
In
kana da wurin sana'a kar ka yarda a ce kanka da iyalanka kaɗai
ka sani, yi ƙoƙari a ce hatta mai yi maka gadi yana da
matsayi a wurinka, kuma kana ba kowa haƙƙinsa
yadda ya dace, ko kwana daya mutum ya yi ba ka gan shi ba tambayi inda yake, za
a gaya masa cewa ka tambayi halin da yake ciki, in bai da lafiya ne kuma ba za
ka iya zuwa duba shi ba saboda wani zarafi yi ƙoƙari ka kira shi a waya, in kana da dan
wani abin hasafi ka yi masa, in ka matso kusa da ma'aikatanka ba za ka taba
ganin abinda zai dame ka ba, mutum yana son alkhairi koda kuwa ba yawa.
.
IN GORA TA CIKA BA TA ƘARA
Haka Hausawa suke cewa, in
ka ga mutum yana ji da kansa kuma yana nuna isa da fankama a wurin sana'arsa to
bai shirya aikin sosai ba, matso kusa da ma'aikatanka ka janyo su jiki, komai
ku riƙa yi tare, za ka ga duk abinda ya taso
sun iya samun ƙarfin gwiwar da za su
tuntube ka ko ku tattauna tare, kar ka zama kamar dodo kowa na tsoron ya yi
magana da kai, a irin wannan matsayin abubuwa da yawa za su yi ta faruwa ba ka
sani ba, yanzu an fara fahimtar amfanin haka, akwai wani mai neman gwamna da
mai neman dan majalisa da na gani, alla-alla suke yi su ji an yi rasuwa ko
taron biki ko suna a duk yankinsu ka gan su a wurin, mafi yawancin tarurrukan
da suke halarta ba gayyatarsu ake yi ba, amma suna so ne a gan su a yaba da ƙoƙarinsu
a ƙarshe a zabe su, dan majalisan ya ci,
mai neman gwamnan ya fadi, dukansu biyun dai sun dena abubuwan da suka fara, na
ce da sun sani su ci gaba, don gabar ta fi baya yawa.
.
MAGANIN MATSALA
Wasu fa ba su san yadda za
su magance matsalolinsu ba samsam, idan mutum ya yi kuskure a wurin aiki sai
maigidansa ya yi masa kaca-kaca a gaban jama'a, wani lokacin ma ya kore shi, na
ji wanda yake iya bakin ƙoƙarinsa wajen tsare hanyar cin abincinsa,
amma da ya yi kuskure daya, haka maigidan ya zazzage shi kuma ya kore shi, ko
aure mutum yake yin kuskure wajen gyara shi ko tantama ba na yi zai sami
matsala wajen zama da mace, a shekarun baya na yi hira da wani tsoho wanda yake
ce min ya yi aure so goma sha biyar, amma mata biyu na san shi da su, na ji
matar da aka ce masu zaman haya a gidanta ba sa yin shekara sun gudu, saboda
rashin iya ma'amalla, na ga wani mai sana'a duk wanda ya zo koyon aiki wurinsa
sai ya gudu, bai iya ma'amalla da su ba.
.
Na
ga malamin jami'an da ya yi hatsari dalibansa suke addu'ar Allah ya ƙarisa shi a asibiti, suka ce ina ma ya mutu tun
daga wurin hatsarin, na ga wanda wani mutum ya jawo shi don su yi sana'a tare,
amma ya munana ma'amallarsa, ya mayar da wurin nasa shi kaɗai,
a ƙarshe ya sallami wanda ya kawo shi, ba a jima ba
lamarin nasa balbalce, dole mu riƙa
kyautata alaƙarmu da masu yi mana aiki ko masu aiki a ƙarƙashimmu
ko dalibammu matuƙar
muna son ganin ci gaba a rayuwarmu.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.