Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 22: Me Ya Dace?


    Duk lokacin da mutum ya yi karo da wani abu mai kyau ya san cewa ba abin da yake dauwamamme. Wata rana zai ga abin da ba shi yake so ba, sai ya yi…


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 22: Me Ya Dace?

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah
    Kowa da ka ni yana da abin da yake damunsa, kuma abu ne sananne ba zai taba yuwuwa a ce mutum ya boye duk abin da yake damunsa ba, ko bakinsa bai fada ba wani lokaci fuskarsa za ta bayyana, mukan boye amincewarmu ta bayyana kamar yadda take hankatso damuwarmu, amma wani sa'in dole sai mutum ya yi ƙoƙarin shawo kan zuciyarsa da abin da yake damunsa, don kar harshensa ya riƙa kubucewa ya debo masa aikin da bai shirya masa ba, na ga wani mutum da abokan kasuwancinsa suke gudunsa a dalilin abubuwan da suke damunsa, ba wai fada yake yi da mutane ba ko zage-zage kamar mahaukaci, a'a.
    .
    Da ka É—an zauna da shi na wasu 'yan daÆ™iÆ™oÆ™i zai fara fado maka matsalolinsa, wallahi ban da lafiya, duk  kuÉ—ina na kashe su a magani, wurin aikina kaza-kaza, 'yan uwana duk masu kudi ne ba sa taimaka min, na yi asarar kaza da kaza, kudi duk in na samu sai su watse a banza, wane ne ya yi min baki, mahaifana kaza da kaza, mutane sun riga sun saba da shi, ba wani abu yake nema a wurinsu ba kuma ba wani abu za su ba shi ba, amma ba sa son jin irin waÉ—annan koke-koken marasa kan gado, da wahala ka ji mutum yana yi wa kansa fata ta gari, a kowani lokaci sai yi wa kansa mummunan fata yake.
    .
    Wani kuwa iya abin da zai iya gaya maka shi ne "Alhamdu-lillahi" wani ya ce maka "Harkar ce sai godiyar Allah!" Ko zai ƙara maka wani abu sai dai ka ji ya ce "Abubuwa duk sun tsaitsaya amma in sha Allah komai zai gyaru, akwai alamun alkhairi nan kusa ba da jimawa ba" haka zai fara kallo wasu hanyoyi da za abi a fita, ya fara tunanin kawo sauyi a harkar, ko dai ya canja wurin zama, ko ya sauya kayan ko dai ya ƙawata ta ta wurin shigo da sabbin tsare-tsare, irin waɗannan ba su cika dauwama a halin ni-'ya-su ba, don ba su yarda da cewa akwai abin da bai da mafita ba, ba su yarda da cewa lamarinsu yana hannun wani dan-adam ne ba bare ya takura su, rayuwa kullum a birgimar hankaka take, wata rana ka ga fari wata rana ka ga baƙi.
    .
    Duk lokacin da mutum ya yi karo da wani abu mai kyau ya san cewa ba abin da yake dauwamamme. Wata rana zai ga abin da ba shi yake so ba, sai ya yi masa shirin ko-ta-kwana, in zai zo din ma yakan zo masa da sauÆ™i, wanda yake ganin cewa wani zai iya yi masa wani abu to duk lokacin da mummunan abu ya same shi zai ce wannan mutumin ne, a maimakon ya fara tunanin cewa jarabawa ce wace hanya zai bi ya cinye ta sai ya fara tunanin wane ne ya yi masa kaza dole ya rama, kuma  ya ce "Shikenan ya gama da ni sai dai Allah ya isa kawai" ko ya ce za a yi musu hisabi a ranar Æ™iyama, batun neman mafita kuma ya Æ™are.
    .
    YA ZA KA KALLI MATSALOLINKA?
    Duk wanda ka kalla yana da fuskar da yake kallon matsalolinsa, yana da hanyar da yake tunani ta daban, wani za ka taras addini ya yi masa tasiri, duk abin da ya same shi ko yake son yi zai kawo Allah a matakin farko, irin waɗannan ba su cika rigima da mutane a kan abu ƙarami ba, cikin sauƙi za su warware babbar matsala su ce maka "Ba komai, haka Allah ya so" su ma din akwai bangaren da sukan yi kuskure, abin da ya kamata su dauki mataki don kare faruwar abin a gaba ga shi sun bar shi ya wuce sakaka, wasu kuma ba sa son ka kawo musu Allah a duk lamarin da ya shafi san'arsu, a tunaninsu maganar Allah a addini kawai ake samunta ba ta hada hanya da kasuwanci ba, in mutum ya yi daidai ya ga daidai in ya yi kuskure ya taba ya ji, da yawa waɗannan ba sa cin nasara a rayuwa.
    .
    Haka za ka sami kowa da fannin da yake tunaninsa, to kai abin da ya kamace ka shi ne ka kalli mutum da sifar da ta dace, ka kalli hanyar da yake tunani, ka kalli wayewarsa da iliminsa, ka kalli komai nasa, mace ce ko namiji, yaro ne ko babba, ya matattararsu take? Bai yuwuwa kai da aka haife ka a Kano ka tashi a cikin Hausawa, ƙila ma mahaifinka ne limamin masallacinku, ka sami wannan tarbiyyar, ka ce abokin sanarka ko mai maka aiki da ya taso a Kudancin Kaduna ba ma musulmi ba ne kana son ya yi maka irin ma'amallar da kai ka taso a ciki, kuma kana da tabbacin ba wahayi za a yi masa ba, za ku yi ta samun sabani ne, in maigidanka ne ƙila ka rabu da shi, in ɗan gidanka ne ƙila ka kore shi.
    .
    Ba yadda za a yi mutum ya riƙa kallon kansa wurin yanke hukunci a kan wasu, ba dole ba ne a sami fahimta iri guda, amma kallon mutum a dabi'arsa zai taimaka, wata abokiyar aikina, daga kudancin Kaduna, ba a yi wata ba take gaya min irin wahalar da ta sha da mahaifiyarta, ina son na ba ta haƙuri ta dibo ashar ta hado da mahaliccin gaba daya sai da na girgiza a lokacin, ba arziƙi na yi ƙoƙarin kulle hirar gaba daya, ita da kanta ta fahimci ban ji dadin maganar ba sai ta fara ƙoƙarin gyarawa, na tabbata in ba subutar baki ba ba za ta ƙara irin wannan a gabana ba, hanzarin da na yi mata ita ba musulma ce ba, ba ta da kawaici irin namu na Hausawa, ba ta da tarbiyyar girmama uwaye, shi kansa Allan ma ba su bi hanyar da za su kaɗaita shi ba bare su ba shi sauran sifofinsa da ya kebantu da su.
    .
    To bayan wannan ma a matattarar da muke ma, ko ciki guda ne akwai abin da ake kira Kebantattun Halaye ga Kowa, wato "Individual Deferences" a Turance, ko "Fruuƙ Fardiyya" a Larabce, irin waɗannan halaye ko ciki daya yara suka fito, wato 'yan biyu za ka taras kowa da dabi'unsa, in haka ne kuwa dole sai mun riƙa yi wa juna hanzari, in mutum ya kwabsa maka a matsayinka na shugaba ka kalli sauran ayyukan da yake yi kawai ka yi masa rangwame, in kuma kai ne yaron gida to ka yi masa hanzari, ka gane irin halin wadatar da yake ciki da matsayinsa, wanda in kai ne ba za ka yi haka ba, shikenan ya wuce sai a kalli gaba kuma.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.