Ita
kuma wata ɗabi'a
ce mummuna da ta zama dole mutum ya guje ta a matsayin shugaba ko abokin aiki. Za
ka taras wani kullum cikin hanzari ne "Don Allah wane ɗan riƙe min wuri kaza ina son
na yi kaza..."
Ko ka ji yana cewa "Don Allah yau ba...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 21: Ƙoƙarin Kawo Gyara
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
In kana son kawo gyara a
ma'aikatarka ko wurin sana'anka na yau da kullum dole ne ka riƙa sanya ido, duk kuma wanda ya yi
kuskure a gyara masa, sai dai gyarar kan yuwu ne wajen nuna masa kuskurensa,
galibin abin da muke yi shi ne in mutun ya yi kuskure a dinga zaginsa da harshe
can sama kowa na ji, ko matarka da ka auro in dai za ka juri daga mata murya za
a kai lokacin da za ta shiga ramawa, samun mutum a kebe cikin natsuwa gyara ne,
yi masa kwarwa cikin mutane kuwa kunyatawa ne.
.
ƘARFAFA
GWIWA DA KALMOMI MASU DAƊI
In har kana da masu aiki a ƙarƙashinka
ka zama mai yawan raha a tsakaninsu amma ta wurin yin amfani da kalmomi masu
dadi yadda mataimakanka ba za su damu ba, aƙalla
za su ruƙa dariya ne a duk lokacin da ka cakali
wani, irin su "Katafila sarkin aiki" ko "Agogo da aiki aka san
ku" da dai sauran kalmomi masu dadi waɗanda
suke ƙarfafa gwiwa, to bare kuma in wani
sha'ani na gama-gari ya taso kamar Azumi ko Salla babba ko ƙarama, ka daure a yanka dabba, in babban
wuri ne ana samun kudi a raba wa ma'aikata danyen nama, in ƙaramin wuri ne a yanka rago a soye shi
yadda kowa zai ci ya san ya ci nama, wannan ƙarfafa
gwiwa ne, ka yi ƙoƙari ka halarci duk wani taro irin
wannan.
.
TA'AZIYYA, BIKI KO SUNA
A matsayinka na babba ka
daure ka halarci duk wani wurin farin ciki ko baƙin
ciki na ma'aikatanka, kai babba ne, wannan tabbas ba ja, amma duk wani ƙaramin da ya gan ka a wurin wani abu
nasa zai ji dadi sosai ba kadan ba, masamman abin da ya shafi baƙin ciki kamar mutuwa, asarar dukiya da
sauransu, to bare kuma a ce ka ɗan guntsila wani abu ka miƙa masa, kar ka raina ƙanƙancin
abin da za ka yi, ka duba girman tasirinsa ne a zuciyar wanda ka ba wa, nakan
ji ana cewa "Alhaji fa ya zo" wani za ka ji ana cewa "Ai
dabi'arsa ce, lamarin ma'aikatansa nasa ne" in da zai yi tunani duk
wahalar da suke sha duk da cewa suna samun abin rufin asiri ƙarshe dai komai wurinsa zai dawo, ba
domin gudummuwar da suke badawa ba komai cak zai tsaya.
.
SANYA GASA A TSAKANIN
MA'AIKATA
Ka yi ƙoƙarin
sanya wata gasa a tsakanin ma'aikatanka, lura da waɗannan
'yan bokon, duk da cewa muna kallon su marowata ne, amma abin da suke yi yana
yin tasiri sosai a zuciyar ma'aikatansu, sukan yi wasu 'yan alluna a ƙarshen shekara su rubuta sunan mutum su
ba shi a matsayin wata lambar yabo da take jinjina masa a kasancewarsa wanda ya
fi kowa zuwa da wuri, ko rashin fashi, ko tsafta, ko ladabi da biyayya, ko aiki
tuƙuru da sauransu, irin waɗannan
kyaututtuka suna da tasiri ba ƙarami
ba a zukatan ma'aikata, kowa zai yi ta hanƙoron
a ce ya samu, ba kuma zai samu din ba sai ya aikatu, da haka sai aiki ya bunƙasa, to bare a ce ana saya wa mutane
motoci da mashina ko talabijin da wayoyin hannu da sauransu.
.
Wanda bai samu kyauta ba bai
dage ba kenan, in babban kamfani ne ko saudiya sai a kai wani, duk da cewa
mutum daya ya samu, amma zai zaburar da sauran ma'aikatan idan suka ji cewa
dagewarsa ce da jajurcewa silar samun kujerarsa, in ƙaramar ma'aikata ce za a iya saya wa
talaka ƙaramin buhu na shinkafa, ko galan din
manja ko na man-gyada, ko dai wani abin da zai jawo hankalinsa, wannan ya fi
masa wata lambar yabo, da yawammu ba mu san ƙimarta
ba, ba mu cika wani lura da cewa nan da nan za mu murtsuke ci ya ƙare kenan ba.
.
ƊORA
WA MUTANE NAUYI
Ita kuma wata ɗabi'a ce mummuna da ta zama dole mutum ya
guje ta a matsayin shugaba ko abokin aiki. Za
ka taras wani kullum cikin hanzari ne "Don Allah wane ɗan riƙe min wuri kaza ina son na yi kaza..." Ko ka ji yana cewa "Don Allah yau
ba zan sami damar zuwa ba amma wane ɗan kama
min kaza" in hakan ya fara yawa ko ka nema ba mai kula ka, za ka taras duk
wanda ka kama yana zillewa saboda an maimaita ba daya ba ba biyu ba, ko shugaba
ne ya yawaita dora wa ma'aikatansu wasu ayyuka a wajen abubuwan da suka san sun
zama musu dole tabbas za ka taras sun noƙe,
ko in suka ji motsinsa kowa ya kama gabansa, ba laifi ya faru sau daya ko biyu
amma ba a hade ba kuma kar ya yi tsawo, in ka dora wa mutane aiki to yagar musu
wahalar aikinsu ka matsa su karba koda sun ƙi,
shi ne zai ba ka garantin ka nema wata rana.
.
Idan kuma ka shugabanci wani
bangare na jama'a a cikin ma'akata, taka ce ko aiki aka ba ka, ka yi ƙoƙari
wurin tabbatar da an yi aikin cikin nishadi, a maimakon ka zabo wanda ka raina
ka labta masa kaya ka jira ya yi shi kaɗai,
yi ƙoƙari
ka kira taro, koda ka san yadda za a yi ka ɗan dakata,
ka fito da aikin sarari, ka nemi shawarar abokan aikin naka kan yadda za a
tafiyar da shi, a maimakon mutum guda ya yi shi kaɗai,
wanda hakan kuma zai ɗauke shi wani ɗan lokaci,
ka yi ƙoƙari
ka kasa musu yadda kowa zai yi da kyau, kuma cikin nishadi sannan a ɗan ƙanƙanin
lokaci, buƙata ta biya kenan,
sannan shugaba ya riƙa
samun lokaci yana zaunawa da ma'aikatansa yana tattaunawa da su.
.
Abin da ya fi komai
mahimmanci ma ya riƙa
shiga cikin aikin, in zai yuwu kar ya bari a sami wani bangare na kamfanin
wanda ba ya shiga a yi da shi ko a ce bai san kansa ba, wannan sifar shugaba na
ƙwarai kenan wanda tabbas nasarar yake
nema kuma aiki yake yi tuƙuru
don isa gare ta, ba wai mutum ya yi ofishi a gefe sai dai a riƙa kawo masa takardu yana cikewa ko
tattaunawa da abokan ciniki ba, na yi karantarwa a wata makaranta wace
hedimastan lokaci-lokaci yakan hutar da wani malami shi zai koyar don ya ga
fahimtar 'yan ajin da duk inda suka tsaya a karatunsu, ɗan lokaci
kadan za ka gan shi a ƙofar
tagarka yana kallon abin da kake yi wa daliban, in ya ga kuskure za ka ji kira
a ofis, ya gyara maka cikin tsanaki.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.