Takardar da aka gabatar a wurin
taron ƙara ma juna sani a kan Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa A Yau. Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina, ranar Laraba 26 ga
watan Yuni, 2013.
Gudunmuwar Farauta ga Raya
Al’ada da Adabin Hausawa
ABUBAKAR SANI SAYAYA.
SASHEN WATSA LABARAI DA ƊAB’I
MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA.
08022671839
1.0 GABTARWA.
Al’umar Hausawa, al’uma ce wadda ta mamaye mafi yawan sassan Arewacin
Nijeriya da kuma kudancin ƙasar Nijar.
Masana da dama sun yi tsokaci dangane da wuraren da ƙasar Hausa ta mamaya, Funtua (2010), ya bayyana ƙasar Hausa da cewa ta
ƙunshi wani sashe na garuruwan
Zazzau da Zamfara da Kebbi da Bauchi da kuma tsofaffin lardunana Katsina da
Kano da wani sashe na kudancin Jamhuriyar Nijar, wato garuruwan Maraɗi da Tawa da
Tasawa da Damagarm da sauransu. Shi kuwa Abbas (2012), cewa ya yi, ƙasar Hausa yanki ne da a yau ya haɗa da jihar Katsina da tsohuwar
jihar Kano da jihar Sakkwato da Zamfara da Kebbi da wani ɓangaren jihohin
Kaduna da Bauchi a cikin ƙasar Nijeriya.
Haka kuma, ta haɗa da ƙasashen Ƙwanni da Damagaran da Tasawa da Maraɗi da Tawa da
sauransu, a cikin Jamhuriyar Nijar. Kamar sauran al’umomi na duniya, tun farkon
rayuwarsu Hausawa sun dogara ne ga farauta wadda ta wannan hanya ce suke samun
abinci kafin daga bisani su sami dabarar yin noma da kiwo da kuma sauran
sana’o’i da suka haɗa da ƙira da saƙa da sauransu. Gusau (2008). ya bayyana cewa hakika akwai
rubuce-rubuce da aka yi game da ƙasar Hausa ta
fuskoki daban-daban da suka haɗa da yanayin ƙasa da halayyar
mazauna wurin da abincinsu da suturarsu da aƙidojinsu da ayyukansu na tattalin arziki da sauran
abubuwan da suka shafi rayuwa. Hakika, wannan bayani ya yi matashiya dangane da
kayan cikin al’adar Hausawa, wadda a kan ta ne za mu dubi irin gudunmuwar da
farauta ke bayarwa wajen raya ta. Don haka kafin mu yi dubi, mu ga irin wannan
gudunmuwa, sai mun yi tsokaci a kan waɗannan kalmomi, wato “AL’ADA” da
kuma “FARAUTA” ta fuskar ma’ana. Dukkanin al’umomi na Duniya suna da ire-iren
hanyoyin da suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kulun, da suka tsira tun daga
haihuwa suka ratsa rayuwarsu har zuwa ga mutuwa. Ire-iren waɗannan hanyoyi na
gudanar da rayuwa su ne ake kira al’ada. Ubaidu (2013) ya bayyana al’ada da
cewa Kalmar Larabci ce. Hausawa sun aro ta ne kamar yadda suka aro sauran
kalmomi. Ma’anarta , halin rayuwa, ko abinda aka saba wanda al’uma ta amince da
shi. Shi kuwa Bunza (2006), bayyana kalmar ya yi da cewa, al’ada tana nufin
dukkanin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina
mutum ya sami kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a
wurin da ya rayu, ko yake rayuwa ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a
kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa face tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya
rarrabe ta da wata da ba ita ba. Haƙiƙa tun kafin Hausawa su fara cuɗanya da wasu baƙin al’adu Allah Ya albarkace su da ingantacciyar hanyar
rayuwa wadda ba sai sun jira samun ta wasu ba. Haka ya sanya har
kawowa wannan ƙarni, Hausawa ba su daina ba daɗaɗɗiyar
hanyar neman abicinsu, wato farauta muhimmanci ba.Buss (2011) ya kawo ma’anar
farauta da cewa, hanya ce da ɗan Adam kan bi waɗansu halittu masu rai musamman
namun daji da sauran ƙanana dabbobi domin samun abinci,
da motsa jiki da kuma kasuwanci. Kamar sauran al’ummomi na duniya, su ma
Hausawa sun sami kawunansu cikin fafitikar neman abinci domin ganin sun rayu a
bisa doron ƙasa. Hanyar farko da suka fara bi
domin samun abin da za su ci kuwa ita ce farauta. Wato kafin su sami dabarar
noma da kiyon wasu dabbobi domin samun cimaka sai su riƙa fita kewayen mazaununsu suna kama dabbobi ko tsuntsaye
domin su ci. Wannan dabara ta kaso naman daji a kawo gida ita ce ake kira
Farauta.
1.0 TAƘAITACCEN TARIHIN FARAUTA.
Gabanin Hausawa su sami dabarar
amfani da kowane irin makami, sukan
bi dabba a guje da ƙafa har sai dabbar nan ta gaji ta tsaya, ko ta faɗi don kanta
sannan su kama su zo da ita. Daga nan sai
dabara ta zo masu ta feƙa dutse, su yi
masa kaifi ya zama makaminsu. Sannan daga bisani fasaha ta ci gaba da zuwa masu har lokacin da
suka fara amfani da makamai na ƙarfe irin
su mashi domin suka, da wuƙa domin yanka, ko wani abu mai kama da takobi domin sara.
Kamar yadda Pagan (2012) yake cewa, a
yayin da mafarauta ko ‘yan tauri suka yi shirin fita farauta, sukan nuna irin
buwayarsu a kan duk wani makami na ƙarfe irin su wuƙaƙe, da adduna, da takubba, da
masu, da baka da kwari, da sanduna.Wannan daɗaɗɗiyar
hanyar neman abinci ta haifar da ƙaruwa da ci
gaban rayuwar Hausawa. Bayan da Hausawa suka kasance sun gina mazaunu na
dindindin tare da samun hanyar noma da kiwo da kuma sauran sana’o’i ne, sai
suka mayar da Farauta ta zama sana’a. Wato ta tashi daga hanyar neman abinci ta
dole, ta koma ta sha’awa da kuma nuna bajinta da karfin magani. Da haka har ta
kai an samu wasu makaɗa da mawaƙa suna bin masu
irin wannan sana’ar suna yi masu kiɗa da waƙa. Ta haka ne
farauta ta sami wani matsayi na daban a wannan zamani. A ƙoƙari wallafar wannan ɗan littafi an
kasa shi an kasa aikin zuwa sassa guda uku. Sashe na ɗaya ya ƙumshi labarin yadda ake farauta kai tsaye daga bakin wasu
fitattun mafaraua da suka taka rawa a fagagen Faraut daban-daban. Sashe na biyu
na ƙumshe da bayani iri gudummuwar da fFarauta ta bayar ga
rayuwar al’adar Bahause. A yayin da sashe na uku ya kasance bayanin iri yadda
Farauta ta taimaka wajen samuwar adabin bakan Bahaushe.
SASHE NA ƊAYA.
FARAUTA DAGA BAKIN
MASU ITA.
Ado Bahago Kunamawa.
A lokacin da nike ƙoƙarin tattara ire-iren waɗannan bayanai
nawa na tattauna da Malam Ado Bahago Kunamawa, wato Sarkin Taurin Yariman
Katsina, Hakimin Safana a ranar (
). Ga kuma yadda hirar
ta kasance:
T:To saraki mine ne asalin Farauta?
A:
Asalin Farauta shi ne neman abinci. Kuma duk wanda ya zo duniya ya tarad da
Farauta. Ta zamanto Farautan nan duk ɗaa namiji a can baya, idan bai yi
Farauta ba to me zai ƙaras? Lokuttan da ake zuwa
Farauta, wancan lokacin, sai rnai ya taho. Da damina mu tsaya mu yi noma. Da
kaka a yi huɗɗar abin da aka noma, amma idan rani ya yi sai a tafi a yi
Farauta. Ba a barin Farautan nan sai damina ta sauka.
T: Idan za a tafi Farauta ya ake kuna sani?
A: Idan
za a yi Farauta
Yadda ake fita Farauta.
Ire-iren makama da mafarauta ke amfani da su.
3.0 GUDUNMUWAR
FARAUTA GA RAYA AL’ADAR
HAUSAWA.
Ganin yadda farautar
nan ta yi tasiri ga hanyar neman abincin
Hausawa tun farkon rayuwarsu har kawowa yanzu,
da yadda ake aiwatar da ita ya sa ake ganin babu wani abu da ya taka muhimmiyar
rawa a wurin ginuwar al’adarsu. Wannnan ne ya sa suka ƙaru da wasu fannonin rayuwa da suka zama kanwa uwar gami,
wurin ginuwar al’adarsu. Wannan ne ya sa za a yi ƙoƙarin fito da waɗannan fannoni
domin a kakkaɓe su, a ga irin yadda suke. Daga cikin irin gudunmuwar da
farauta ta bayar ga raya al’dar Hausawa tun da farko, akwai:
3.1 SAMAR
DA ABINCI.
Kamar yadda Bass (2011) ya bayyana cewa binciken da aka samu ya nuna ƙabilun wancan zamani sun bi ta hanyar farauta ne a
matsayin matakin farko na samun abinci. Wannan ya nuna cewa su ma Hausawa a
wancan lokaci suna fita farauta ne domin
su samo abin da za su ci tare da iyalansu, wannan ya tabbatar da cewa farauta
ita ce hanya ta farko da ta taimaka
masu domin ganin sun rayu, domin
babu wani mai rai da zai rayu ba tare da ya ci abinci ba. Duk da cewa daga
bisani sun sami dabarar noma, da kiwon
dabbobi, da sauran sana’o’i, ba su san dabarar amfani da wani abu a matsyin kuɗi ba. Hanyar
kasuwancinsu ta farko ita ce ta furfure. Ta irin wannan hanyar ce su mafarautan
ke fita daji su kaso nama, su gyara su musaya shi ga masu buƙata a ba su wani nau’in abincin. Tabbacin hakan ya fito a
cikin Tarihin Ƙasar Hausa, A cikin Taskar Gidan Dabino (2009), inda aka
bayyana cewa irin sana’o’in da ake dasu sun haɗa da Noma, da
Kiwo, da Rini, da Ƙira, da Jima, da Sassaƙa da dai sauransu. Kuma a wancen lokaci ba su da wani abu
tsayayye da za a kira Kuɗi, illa iyaka ban gishiri na ba ka kanwa (cinikin
Furfure).
3.2
SAMAR DA WURIN ZAMA.
Daga cikin irin gudunmwar da farauta ta bayar ga raya al’adar Hausawa ita
ce ta samar masu da wurin zama. Kamar
yadda ɗan Adam ke buƙatar zama
wuri mai dausayi domin ya sami kariya da
abinci, to haka su ma dabbobi da tsuntsaye. Don haka duk wurin da za ka sami
Hausawa sun yi mazauni to asali za ka tarar cewa wuri ne mai yalwa, da wadatar
ruwa da kuma dazuka domin farauta. Tun farko idan mafarauci ya samu wurin da ya
gay a dace da shi sai ya share yak afa bukka tai ya zauna. Daga bisani ire-iren
waɗannan mafarauta sai da suka yawaita, sai suka riƙa kyautata zamantakewarsu da kiyaye hakkin maƙwabtaka da junansu. Da kuma sa da zumunci tsakani. Irin
wannan kusanci da mafarauta suka samu a tsakaninsu shi ya haifar da dabarar
gamewa guri ɗaya wanda ya sa tun mazaunnsu yana matsayin Tungaye har
suka koma a matsayin Ƙauyuka, daga bisani sai a samu
gari ya haɓaka. Misali idan muka dubi irin rawar da Dajin Rugu ya
taka wajen samuwar garuru da dama. Sayaya (2009), ya bayyana cewa, shi Dajin
Rugu, daji ne da ke da ƙoramu da yawa da suka ratsa
cikinsa. Dajin ya shahara ƙwarai ga
mafarauta. Hakan ya sa wurin ya zama
matattarar dabbobi, musamman namun daji wanda ya sanya aka samu
mafarauta da makaɗan farauta da dama daga cikinsu hard a shahararran makaɗin farautar nan
Alhaji Kassu Zurmi. Haka nan kuma dajin shi ne ya raba ƙasar Katsina da
Zamfara a halin yanzu. Kuma shi ne musabbabin samuwar garuruwa irin su
Kunamawa, da Kirtawa, da Mara, da Ɗantudu, da
Wagini da ke cikin ƙasar Katsina. A ɓangaren Zamfara
kum a akwai garuruwa irin su Birnin Magaji, da Shamusalli, da Jabanda da
sauransu. Kassu ya kawo wasu daga cikin waɗannan garuruwa
inda yake cewa:
Na tuna wasan da mun ka zo Kirtawa da Ɗantudu
Ina godiya
waɗan Kirtawa da Ɗantudu
Mijin Tudu komi akai
waɗan Wagini sun ma ni
Za ni gida
ku na ƙetare
kui ma ni gahwara sai wata rana
(Kassu Zurmi,
Wuya sa gayya kai na Iro mai Kansakalin hwaɗa).
3.3 SAMAR
DA TSARI NA
SHUGABANCI GA HAUSAWA.
Wasu masana suna ganin cewa asalin kalmar sarauta an samo
ta ne daga kalmar farauta wadda yawan furta kalmar ya sa harafn [F] ya
sauya ya koma [S] aka sami sarauta. Amma idan muka yi la’akari da irin
tsarin al’adar Hausawa cewa ba su yarda
da su zauna a wuri guda ba tare da sun sami wani wanda zai jagorance ba. Haka
nan kuma jagoran nan dole sai ya kasance gwarzo, jarumi, kuma namijin ƙwarai. Kamar yaddda aka bayyana a “Tarihin Ƙasar Hausa” a cikin Taskar Gidan Dabino (2011), cewa Akan
zaɓi wani dattijo a matsayin shugaba, kuma wani jarumi wanda
ya nuna ya fi kowa sadaukantaka, da jaruntaka, da dauriya. A sakamakon hakan ya sa daga
shugabancin farauta ne ake kyautata zaton samun wani barde ya kasance jagora. Ɓurɓushin haka ya fito a cikin waƙar Garu-garu na
Mande kamar haka:
Na Auta jan zakara
Ƙwazo na Mande uban tahiyat tauri
Katakoro zakaran burtu
A buge ka, ka mai da hwaɗa sabo
(Kassu Zurmi,
Garu-garu na Mande).
Idan muka dubi ɗiyan waƙar guda uku za mu ga cewa mawaƙin ya kawo kalmomi da suka haɗa da jan zakara
(Bahaushe ya ɗauka cewa jan zakara ya fi sauran zakaru faɗa da
juriya). Haka, a cikin layi na biyu ya
kawo batun shugabanci inda yake cewa uban tafiya (wato jagora ko shugaba ko
madugu) na masu farauta. Sannan a layi na uku ya kawo zakaran burtu. (Zakaran
burtu shi ne ke kasancewa a matsayin jagora a cikin garken waɗannan tsuntsaye).
Wannan ya nuna cewa lallai a cikin mafarauta akwai tsari na shugabanci, kuma
dole sai wanda ya buwaya yake zama shugaba. A cikin tsarin shugabancin
mafarauta akwai Sarkin dawa, da Galadiman daji, da Ƙaura da sauransu. aga cikin ire-iren wannan shuwagabanni
ne ake samun wanda zai jagoranci sauran al’umar Hausawa a wancan lokacin. Ɓurɓushin gaskiyar wannan zance ya fito a tarihin birnin Kano. Cikin littafin
HAUSAWA DA MAƘOBTANSU,(
littafi na biyu, shafi na 1), inda ake cewa “Shugabansu shi ne Barbushe, shi kuwa daga ƙabilar Dala ya ke.
Shi Dala mutun ne baƙi,
kakkaura, ƙaƙƙarfa, mafarauci. Domin shi yak an kasha Giwa da sandarsa,
ya ɗauko ta kansa ya yitafiya da ita”. Wannan ya nuna cewa asalin sarautar Kano ta fito daga
gidan wani shahararran mafarauci ne, wato Dala wanda ake ganin ɗansa Barbushe
shi ne sarki na farko.
4.0 GUDUNMUWAR
FARAUTA GA HAƁAKAR SANA’OA’IN
HAUSAWA.
Bayan da Hausawa
suka samu matsugunnai, suka kafa dauloli da garuruwa tare da samun dabarar noma
da kiwo da sauran sana ‘o’i, sai faruta ta tashi daga neman abinci ta koma
sana’a. Rimmer da sauransu (2009), suna cewa farauta tsohuwar sana’a ce. Can
da, kafin mutum ya gane dabarar riƙe fartanya, ko
saƙa, ko ƙira,
yawace-yawace yake yi yana neman abincinsa. To
bayan ya gane dabarar noma ya zauna wuri ɗaya ya fara
sana’oi, sai ya riƙa shiga daji yana neman nama. Da
haka dai har ya mai da farauta cikin sana’o’insa. Ta haka ne mafarauta ke shiga
daji, su kaso dabba su zo gari su sayar don su sami abin biyan bukatunsu. Daga
ciki irin wannan gudunmuwa ta farauta akwai:
SAMAR DA DABARAR
KIYON DABBOBI.
Asalin dabarar
kiyo ta samu ne a sakamakon lura da iri halaye da ɗabi’un ire-iren
dabbobi da tsuntsayen da su mafarautan ke kamowa idan sun je wurin farautar. Ta
haka ne suka fahimci cewa akwai nau’in dabbobin da ba su faɗa ko kuma
hatsari, kuma masu saurin sabo da jama’a. ta wannan hanya ce suke kamo su sa ɗaure su riƙa kiwonsu. Daga bisani sai su ire-iren waɗannan dabbobi da tsuntsaye suka saba da masu su,
kuma suka riƙa haihuwa har suka yawaita. Su
kuwa sauran dabbobin da ba su da saurin sabo sai dai idan an ci karo da su a
kaso su, ataho da naman gida. Daga cikin ire-iren dabbobi da ba su da sauri
sabo da jama’a sun haɗa da Zaki, da Damisa, da Kura, da Kerkeci, da Giwa, da Ɓauna, da Gwamki da makamantansu. Su kuwa ire-iren
dabbobin da aka fi sauri kiyon su a gida sun haɗa da Dawaki,
Jakuna, da Shanu, da Raƙumma, da Tumaki, da Awaki da
dangoginsu. Ta haka ne har kawowa wannan lokaci Bahaushe ya samu dabbobin gida
da na Daji (Namun dawa). A yayin da garke ya bumƙasa, dabbobin suka yawaita sai a riƙa sayarwa ga masu bukata domin su ma su samu na kiwo ko kuma
dan su samu nama. Wata muhimmiyar dabara da Bahaushe ya samu dangane da kiwo,
ita ce ta kiwon Kare domin ya kasance yana da da babban matsayi a gurin
mafarauta kamar yadda za mu gani.
MATSAYIN KARE GA MAFARAUTA.
Bayan da farauta ta ci gaba da kankam
sai al’umomin duniya suka fara samun dabarar
amfani da wasu dabbobi da tsuntsaye wajen farauta. Ire iren waɗannan dabbobi
kuwa sun haɗa har da Kare
wanda a ƙasar Hausa shine wanda suka fi
amfani da, domin kuwa shi yana da wasu halaye na musamman da suka dace da
zamantakewar ɗan Adam. Kamar yadda Bass (2011), ke cewa, a daidai
wannan lokaci na tarihi ne ɗan Adam ya samu abin da zai masa a wurin farauta a
sakammakon dabara day a samu ta mayar da wasu daga cikin dabbobin day a ke farautowa
da suka haɗa da Kare wanda ya
kasance mai hikima, da biyayya da kuma basira ta saurare da shakar kamshi. Har
kawowa yanzu ba a samu mamadin Kare a cikn dabbobi a gun farauta ba.
4.1 SAMAR
DA NAMA. (Asalin samuwar sana’r Fawa)
Tun da farko dai mafarauta su da kansu
suna amfani da naman da suka kaso a matsayin abinci sannan suna sayar da naman
da suka kamo ga masu so, domin samun kuɗin da za su biya buƙatunsu na yau da kullun. Waɗansu lokutta
kuma sukan sayar da naman ga masu sara, su sayar don samun riba. Irin wannan yanayi ne na kaso
dabba da samar da nama ya haifar da samuwar wasu waɗanda suka ƙwarai waje gyaran naman.
Ire-iren waɗannan masu gyara
nama sune daga baya suka rikiɗa suka zama Mahauta ko Runji. Wannan na daga cikin
dalilan da suka sa har yanzu daga cikin masu sana’ar fawa ake samun shahararrun
mafarauta a ƙasar Hausa. Haka nan kum an samu
masu wata sana’a ta daban da ke sha’awar farauta da ke zuwa su zauna gida Barunje da nufin samun ire-iren
magungunan da mafarauta tanada kafin su tafi Farauta, tare da makama daƙwarewar Farautar. Irin wannnan zaman ka sa har su waɗan da asalin ba
sana’ar fawa suke ba su koye ta. Tabbacin wannan ya fito a cikin wasu baitoci
na waƙar Kassu Zurmi da ya yi ma Ɗan’ikki a wurin da yake cewa:
“Duniya haka na tassaba,
Ɗan masu gari ya zan bawa,
Ba’azbine daɗa ya
zan bangaru,
Yana gidan Msau ya zanna,
Ha
an aza masa zanko Runji,
Ga wuƙa Barho an bas hi,
Hag
gas hi da ɗan Jantaɗi,
Yau daɗa ku ar Runji“.
4.2 SAMAR
DA FATA.
A mafi yawancin masana’antun Hausawa
musamman waɗanda suka gada kaka da kakanni za a samu suna amfani da
fata wuri gudanar da sana’o’in nasu, sukan yi amfai da fatar na a matsayin wasu
sassa na masana’antar, ko kuma su sarrafa fatar t hanyoyi daban-daban domin
samar da kayan aikace-aikace ko kwalliya, waɗanda Farauta ta
taimaka ƙwarai wajen samar da fatar nan.
Ire-iren masana’antun da mafarauta ke samar wa da fata sun haɗa da:
MAJEMA:
Sana’ar Jima wata
sana’a ce da Hausawa ke da ita ta saɓule gashin da ke jikin fatar dabbar da mafarauta suka
kaso a gyara ta ta yadda za’a samu sauƙin sarrafa ta
yadda ake bukata. Kum a sana’ar ta kasance ɗaya daga cikin
daɗaɗɗun sana’o’in da har yanzu Hausawa ba su bar gudanar da su
ba. Masu sana’r saɓule fata su
gyara ta su ake kira Majema. Su majema tun asali su kan samo fata daga gurin
mafarauta, su na gyarawa. Wani lokaci su kan yi shinfiɗa (Buzu) da
fatar domi shimfiɗa do zama ko kwanciya. Ko kuma wani su jeme fatar su yi
Warki da ita. Hasali ma su mafarautan warkin suke amfani da shi a yayin da za
fita Farautar, kamar yadda za mu gani a can gaba. Haka nan kuma su kan sarrafa
fatar su yi abubuwa daban-daban da suka haɗa Tandu na
kwalli ko na mai, da kayan adon dawaki da kayan wasan yara da makamantansu.
MAƘERA:
Ƙira wata sana’a ce da ake sarrafa
ƙarfe domin samar da kayan aiki wadda ta kasance ɗaya daga cikin
sana’o’in farka da Bahause ya fara yi tun da ya fara zama wuri ɗaya a matsayin
gari. Ta hanyar ƙiran nan ne Hausawa suka samu
makami da suke zuwa Farauta da su.
Makaman sun haɗa da wuƙaƙe, da takubba, da masu, da kibiya, da sauran madama. Haka
kuma ta hanyar ƙirann nan ne Hausawa suka sama
kansu saura kayan aiki na noma da makamantansu. Dukkan waɗannan kayan aiki
da madama an same su a sakamako Farauta. Haka nan kuma su maƙeran su kan yi amfani da fatar da majema suka samar wadda
asali daga Mafaraautan ne aka fara samu ta. Misalai, maƙera suna amfaani da fata su ɗinka Zuga-zugi
da suke zuga wutar da suke gasa ƙarfen ƙira.
DUKAWA:
Ɓatagarawa, (2013) na cewa Dukanci
sana’a ce ta taular fata da sarrafa ta a mayar da ita wani abu dao amfanin
al’uma. Fatar da majema suka jeme ce Baduku kan sarrafa ta ya samar da abubuwa
irin su rigar sirdi, da Ragama, da Lizzami, da Garkuwa, da maratayi, da Tandu,
da Salka, da Burgami, da Buzu, da Zug-zugi, da Taiki, da dai sauran abubuwa.
Tun da farko dai su Dukawa suna sayen fatar ne daga wurin mafarauta su yi
amfani da ita wurin yin ire-iren waɗannan abubuwa da aka zayyana a sama har ma da wasu da
suka haɗa da takalma, ko ɗinkin layu, ko
na ƙirra, ko ɗamaru, da kube da makamantansu.
FATAKE:
Fatauci sana’a ce saye da sayarwa, wadda
Hausawa kan yi tafiya ta kusa ko mai nisa domin su kai ire-iren kayayyakin da
suka da su domin sayarwa. Bayan sun sayar sai kuma su sayo irin waɗanda ake buƙata daga bangaren da su ka fito. Wannan nau’i na ciniki
ko kasuwanci da ake gudanarwa tsakanin garuruwa shi ake kira Fatauci, a yayin
da su kuma masu irin wannan kasuwancin ake kiransu Fatake. Fatake su ma suna
sayen fata daga wurin mafarauta domin su ɗinka Salka wadda suke zuba ruwan
sha a yayin da suke tafiya fatauci ko Taiki wanda suke ɗaukar hatsi da
sauransu.
4.3 SAMAR
DA ƘASHI.
Haka nan kuma su
mafarautan sukan samar da ƙashin wasu
dabbobi da ake sarrafa shi domin a yi
ado. Misali suna samar da hauren Giwa wanda ake yin kayan kwalliya musamman na
mata da shi. Haka kuma ana sarrafa ƙashin
Gwanki ko na Jimina a yi makami da shi.
Irin wannan makami shi ne ake kira wuƙar ƙashi. Wani lokaci sukan feƙe ƙahon dabbar da
suka kamo ya zama makami, ko su riƙa busawa.
4.4 SAMAR DA GASHIN DABBA KO NA TSUNTSU DOMIN YIN
WASU ABUBUWA.
Hausawa su kan yi
anfani da gashin wasu dabbaoni ko tsuntsaye da aka farauto domin samar da wasu
abubuwa kamar katifa ko matashin kai, ko abin shinfiɗa. Wani lokaci
kuma akan yi amfani da gashin wasu dabbobi wurin haɗi ko samar da
magani, misali akan yi amfani gashin baƙaƙen dabbobin daji a haɗa magungunan
siddabaru kamar layar zana da sauransu. Wasu kuma suna amfani da gashin
tsuntsaye su yi kayan ado ko mafeci da sauransu.
5.0 KYAUTATA
ZAMANTAKEWAR HAUSAWA.
Duk wurin da ka tarar da tarin al’umar
Hausawa, za ka samu san a kyawawan hanyoyin gudanar da rayuwarsu ta yau da
kullun. Idan muka dubi irin tasirin da
farauta ta yi wurin inganta
waɗaannan hanyoyi za mu ƙara sakakancewa da cewa, lallai Farauta ta game rayuwar
Hausawa. Hanyoyin kuwa sun haɗa da:
5.1 MOTSA
JIKI.
Motsa jiki babban al’amari ne ga rayuwar
Hausawa, domin kuwa shi ne matakin farko na samar da lifiyar jiki da juriya. Ko
a wannan zamani da muke ciki yanzu,wasannin da aka fi sani, su ne tafiya
(walking), da guje-guje (running) da kokawa
(wrestling). Sagagi (1994), ya bayyana cewa lokacin da ɗan Adam ya samu
fasahar noma da kiyon dabbabi, sai
Ta‘allaƙar rayuwarsa ga farauta ta sauya
ta koma wani dandali na motsa jiki na zamani yadda muka gani. Tuni idan mun
duba za mu ga cewa tun kafin zuwan wasu baƙin al’adu, Hausawa suna da ire-iren waɗannan wasanni
kuma duka a gurin Faruata ana aiwatar da su. Mafarauta su kan yini, su kwana
tafiya cikin daji domin neman naman dawa da za su kaso. Haka nan kuma duk naman
da suka ci karo da shi, da gudu za su bi shi har sai sun kaso shi. Duk lokacin
da suka kashe dabbar nan to ba jira ake yi ba, a ce a raba, a’a kowa ƙoƙari yake ya fizgi rabonsa. Irin
wannan hanya ta samun nama
ita ce
ake kira wawa, wadda ba ta da maraba da kokawa.
5.2 JURIYA.
Juriya na daga cikin muhimman al’adun
Hausawa domin kuwa Bahaushe bai taɓa yarda da ragganci
ba. Kamar yadda Hines, J. (2013) yana cewa wasu daga cikin mafarauta na wannan
zamani zuwa farauta ne domin jin daɗin tya ne. Suna amfana da abubuwa da dama a mamadin samar
da nama. Wannan garaɓasa ce kawai. Amma wasu suna sha’awa da jin daɗin yadda ake
farauta domin tana haifar da samun juriya. Ganin irin gwagwarmaya da accakwamar da ake yi a fagen farauta ne ya sa
ta, ta zama matakin farko na samuwa da
horas da mayaƙa a ƙasar Hausa. kamar yadda mawaƙan Farautar ke musalta ta, za mu iya tabbatar da cewa duk
inda mafarauchi yake ba raggo ba ne.
Dubi yadda shahararan mawaƙin Farauta nan
Kassu ya kawo irin gumurzun da aka sha a dajin Madohwa, inda yake cewa:
Yaƙi
noman Sarki, uwwui kukan Kura
Iro
Hwarautar da an ka zo ta Madohwa
Rannan
ka danƙara
ma arna kashi
Na
Labbo ɗan wani bai tahi gida ba daji yak kwan
A’a
rannan kau had da Kassu daji nak kwan
(Kassu Zurmi, Na Labbo ɗan namijin Duniya na Malan Ɗanja)
Juriyar da Bahaushe ke samu a sakamakon
farauta ta haɗa da juriya ta jiki da kuma juriya ta yanayi ko hali.
Juriya ta jiki da ake samu sakamakon fita farauta ta haɗa da jure ma
duka ko sara da makami, kamar yadda na Mande ya shanye sara a dajin Rayya, in
ji Kassu lokacin da ya gauraya da Dodo jikan Hure. Ga yadda yake cewa:
Ga wani
can tahe mai gahi
In yaz zo ko ku kashe man shi
Sun ka ce ku ɗaga man shi
Sai sun
ka yi mai bukkar Tauri
Bai
hwasa tahowa ba
Sheggun ba su hwasa bugu nai ba-2
Ko kahin a jima
Nag ga shi can ya shahe idanu nai
Tantirai
sun sassare shi
-------------------------------------------
Sun ka yi, sun ka yi bai kau ba—3
Rannan Garu-garu yai mani daɗi
Ɗan Sanda kamar na
dama zuma na sha
( Kassu
Zurmi, Garu garu na Mande)
A wasu lokutta a kan samu mafarauci ya
kasance ko da yause yana cikin daji, ba ya wannan daji yau, gobe ba ya wancan.
Bai damu da ya komo gida ya yi wata sana’a ba misali noma ko kiwo. Irin waɗannan mafarauta
su ne ke jure ma shiga cikin ƙunci na rashi kuɗi ko abinci.
Bature ɗan Fulani na daga cikin ire iren waɗannan mafarauta
kamar yadda Kassu ke cewa:
Bature
ɗan fullani rashi ya alalai
Mata
ta haihu ba gishiri, ba kanwa, ba yaji
Sannan
ba a ba shi bashi, ba a ba shi rance
Kuma
babu mai ba shi kyauta
Shiririta ta yi mai gida ba ƙwara
Bature ga ka
da ƙwazon
ciki babu Rago
(Kassu Zurmi,
Bature ɗan Fulani rashi ya alalai)
5.2
NISHAƊANTARWA.
Nishaɗantarwa na ɗaya daga cikin
al’adar Hausawa. A yayin da maza suka
nutsa cikin daji suka samo nama, suka ci suka ƙoshi, kowa ya samu na guzuri, to sai a sami wani fili ko
faƙo a cikin daji a kafa dandali inda makaɗan Farauta za su
fara kaɗa ma mafarautan take, suna yi masu waƙoƙi tare da tunatar da su irin
gwagwarmayar da maza suka sha a wurin wannan Farautar. A yayin da kowane mafarauci
aka kaɗa takensa sai ya fito tsakiyar fage yana kirari. Su kuwa
masu busa su riƙa busa taken wanda ya shigo
fagen. A gaba zamu ga irin rawar da Farautar ta taka a cikin kiɗa da waƙoƙin fararautar da makamantansu.
5.3 SA
DA ZUMUNCI.
Kudan, (2013) ya bayyan
zumunci da cewa wata alaƙa, ko
dangantaka, ko nasaba, ko jituwa ce da ka ƙulluwa ko haɗa mutane daban-daban kan harkokin da suka shafi rayuwa ta
yau da kullum. Son juna da sa da zumunci na daga cikin kyawawan al’adun Hausawa
wadda Farauta ta taimaka ƙwarai wurin
samar da shi da. Sa da zumunta na iya kasancewa tsakanin su mafarautan a
sakamakon buwaya, ko nemam magani, ko kuma haka nan daji ya haɗa su mafarautan.
Daga nan sai zumunta ta tsura a tsakanin su, inda har gano gidajen junansu su
ke yi, su riƙa ziyartar juna, wasu su zama
abokanen junansu, wasu kuma zumuntar tasu ta zama ta ubangida da bara, ko
auratayya ta kasance tsakanin su mafaratan ko ɗiyansu Tabbacin
hakan ya fito a cikin wasu waƙoƙin farauta kamar haka:
Ko Sarkin Dawan mutane
Ya zo ziyara wurin Bagi
Ko mai Gaba-gaba na cikin Zazzau
Ya zo ziyara wurin Bagi
Kuma ko shi Basakkwace Sarkin Karma
Ya zo ziyara wurin Bagi
Kuma tilas ne mu gai da Korau
(Ummaru jikan Bagwariya,
Waƙar Bagi Sarkin Karman Sarkin Katsina).
Shi ma Kassu ya kawo wani baiti a
cikin wata waƙa inda yake cewa:
Uban gidan na Ramatu
Sanda masu horo da wuta
Uban
gidan ɗan Magaya
Uban gidan ɗan Sharo
Uban gidan mai Mushe
Uban gidan su Mamman Kwasau na Kada
Iro
uban gidan su Goje Mani
Uban gidan Musaki Arzuka
Iro uban gidan Buhari na Asalamu
(Kassu Zurmi, Ibrahim Shaho
Bagobiri).
5.1 SAMAR DA TSARO.
Samar da tsaro na daga cikin irin gudunmuwar
da Farauta ta bayar ga al ‘umar Hausawa, domin kuwa a sakamakon irin magungunan
da mafarauta ke sha domin kariyar jikinsu da kuma rashin tsoro, ko fargaba ya
sa har kawowa yanzu su ne kan gaba wurin samar da tsaro a ƙasar Hausa. Idan ɓarawo ne su ke kama shi ko wani mahaukaci ya yi tunga da
makami su za su kamun shi. Haka nan kuma duk lokacin da aka samu wata dabba ta
buwayi al’uma to za ka tarar cewa Mafarauta ake kira don su zo, su kore ko kuma
su kama ta. A waɗansu lokutta su
ake sawa tsaron dukiyoyin sauran jama’a, ko in an fuskanci wani tashin hankali,
misali gobara da makamancin haka. Acikin waƙar Iro raƙumin gujiya,
Kassu ya tabbatar da haka inda ya ke cewa:
Ku ci magani ƙwarai
Ɗan Mamman, Ku yi ta taimako
Ku waɗanda Sarki ka kira ga mugun wuri
Hawan gangamin Maraɗi
sai kun je
Sai ku ji an ce ku kira Iro ko ba shi nan
(Kassu Zurmi, Jan Zakin garin Gatari).
5.4 SAMAR
DA MAGUNGUNA.
Allah Ya ba al’umar Hausawa wata baiwa
ta sanin magunguna daban-daban domin magance
cututtukan da ka iya damunsu. Ire-iren waɗannan magunguna
kuwa sun haɗa har da na cututtuka irin su zazzaɓi, da ciwon
ciki, da ciwon kai da na raunuka kamar
karaya, ko gocewar ƙashi, da targaɗe, da kuma na
riga-kafi, da sauransu. Sayaya,
(2009). Duk ire-iren waɗannan magunguna da aka ambata babu ma su samar da su, da
suka wuci mafarauta domin su ne ma’abuta shiga daji. Duk kuwa wanda ke shiga
daji shine mafi sanin tsurrai da itacen da ake haɗa magani kowane
iri ne. Su ne kuma suka san wuraren da ake samun waɗannan magunguna.
Hak nan kuma ya zame dole ga mafarauci ya sha magani domin kauce ma sara ko
duka daga abokanen Farauta. Kamar yadda a cikin wani baiti Kassu ke gargaɗi da a nemi
magani, yana cewa:
Ku sha magani banawa
Kada ƙato
ya ɗauki horon uban wani
Dan kak ku ce ana ba ku gaskiya
Daji
waɗanda sun ka gada ka birgima ciki
Ku kau dangi ku yanke walki ku sha tuwo
(Kassu Zurmi, ɗan datawa bai turkuna ni ba).
Wannan ya tabbatar da cewa sani da adanin magani na nan ga Mafarauta.
5.5 SAMARWA
DA ADANA MAKAMAN
HAUSAWA.
Tun lokacin da ɗan Adam ya fara
cin karo da haɗurra daga ire-iren dabboi da yake farauta a sakamakon
rashin ingantaccen makami da zai yi amfani da shi domin kaso nama cikin sauƙi, wani lokaci dabba na iya tasar masa ko kuma ta gudu ba
tare kaso ta ba ya say a fara tunanin wani abu da zai riƙa amfani da shi. Daga nan ne amfani da duste ko ƙashin dabbar da ya kasa a matsayin makami. Hines, J
(2013) ya bayyana cewa ɗan Adam ya fara amfani daƙashi da sanda, da duwatsu a matsayin makaman farauta. Daga nan ne ya ci gaba da samun dabarun feƙe wasu abubuwa da suka haɗa da itace, da
duwatsu makamantansu. Daga nan ne ya samu fasahar sarrafa ƙarfe ta hanyar ƙera wuƙaƙe, da kibau, da masu har daga ƙarshe suka kai ga ƙera bindiga.
Samuwar irin wannan fasaha ba ta tsaya ga al’uma guda ba ne. Don haka su ma
al’umar Hausawa ba a bar su abaya ba wurin samar da ire-iren nasu makaman ba.
Kamar sauran al’umomin duniya, Hausawa sun fara samun nau’o’in makamansu tun
lokacin da mafarauta suka samu dabarar ƙera makaman ne
waɗanda, da su ne suke amfani wurin kaso nama. Tun daga
wancan lokaci ne har kawowa yanzu Hausawa suke samarwa, da adana ire-iren waɗannan makamai da
suke farauta da su. Ire-iren waɗannan makamai sun haɗa da Mashi, da
Baka-da-kwari, da Takobi, da Gatari, da Gora, da sauran nau’o’in wuƙaƙe. Kasancewar Kassu ya shahara
wurin kiɗan Farauta ya sa bai yi
sake wurin zayyana ire-iren
waɗannan makamai ba. Yana cewa:
Kyawon
hwaɗa a zagi Takobi ai sharo
A sa Gorori ka ji rumuts
Wasu kau iya sa Gitta sukai
Wani
had da wuƙag
gutsu shi kai
Ka iske yana washe
ta
Wannan ba ka da mai jure ma shi
Amma Bindiga ba yaji ba ce
(Kassu Zurmi,
na Amadu kokirzon Kada).
Banda ire-iren makman da Kassu ya
ambata akwai waɗansu da suke ƙanana ne. Irin
su kuwa sun haɗa da Maguaji, da Kuikuiwa, da Sakamari, da Tasani, da
Gariyo, da Barandami da sauransu. Banda Gora a cikin makamai na itace akwai
Kere, da Kokara, da Ƙolo da makamantansu. Haka nan
kuma akwai makamai masu tsini da suka haɗa da Wuƙar ƙashi, da wuƙar Ɗunɗu, da kuma Ƙaho waɗanda Bahause ke feƙewa.
5.6 ADANA
TSOFAFFIN SUTURUN HAUSAWA.
Kamar yadda farauta ta kasance hanyar samar
da abinci ga ɗan Adam, haka nan ma ta kasance matakin farko na samar da
sutura ta hanyar amfani da gashi dabbobi ko fatarsu a matsayin abun ɗaurawa ko na
rufa. Gashi da fata sun kasance abubuwan samar da sutua ga ɗan Adam tun
lokacin day a samu dabarar yin farauta. Hines, J (2013). Wannan batu na Hines
tamkar tambihi ne ga al’dar Hausawa domin kuwa su ma tun kafin su fara amfani
da sutura da aka saƙa, da fata suke amfani a matsayin
suturarsu. Idan muka duba za mu ga cewa har yanzu mafarauta na amfani da irin
waɗannan suturu da ake yi da fata. Amma a wannan lokacin sai
idan za su fita zuwa wurin Farautar ne suke amfani da su. Kuma suna amfani da
su ne saboda rashin nauyinsu, dan haka ba su wahalar da su warin tafiya ko
gudu. Haka kuma suna zama a matsayin makari daga sara ko suka da wani ka iya yi
masu. Su kawa ire-iren waɗannan suturu da ake yi da fata sun haɗa da Warki
(walki) da Buzu.
5.6.1 WARKI (WALKI).
A zamanin da, lokacin da babu fasahar saƙa, mafarauta ba su da wata sutura sai
warki. Idan aka yanka dabba, masali
Akuya ko Tunkiya ko dabbar dawa irinsu Gada ko Barewa ko Mazau sai a kai ma
masu jima . idan aka jeme ta sai a riƙa ɗaurawa a ƙugu ko kuma a rataya a wuya. Warkin da ake ɗaurawa a gindi
ana kiransa “Tarezuwal”. Shi kuwa wanda ake ratayawa a wuya ana ce masa
“Karabbi”. Sayaya, (2009). Kassu ya kawo su a cikin wani baiti inda ya
ke cewa:
In za a Farauta
ba a zuwan ta da riga
Kai sai guntun Walki
Sai in ka yi tagguwa dan gilla
Sai ka ga tsoho yana ta kallo tahiyar
ɗa nai—3
Yanzu sai a taho gida da kaya a aje mai
Ga kayan ɗanka, wane ya cim ma iyaka
(Kassu Zurmi,
Ibrahim Shaho Bagobiri)
5.6.2 BUZU.
Wasu mafarauta suna amfani da fata wadda
ba a jeme ta ba. Ana gyara ta a buɗe kamar yadda ake buɗa fatar Rago a
yi buzu da ita. Su mafarauta sun fi amfani da fatar akuya ko ta wasu namun
daji, misali Bika, ko Kura, ko Damisa, da makamantansu. Shi irin wannan Buzu a
wuya ake rataya shi kamar yadda ake rataya Karabbi, kuma ana kiransa Gaba-gaba.
5.7 SAMARWA
DA ADANA KAYAN
KIƊAN HAUSAWA.
Mafi yawan lokutta idan za a fita Farauta ba fita
sai da kiɗa, kuma kayan kiɗan sukan bambanta daga wani sashe
zuwa wani, amma duka bori ɗaya su ke yi wa tsafi domin kuwa duk manufarsu a
zuga mafarauci ya kawar da tsoro. Kayan
kiɗan Farauta sun kasu kasha biyu da waɗanda ake kaɗawa da suka haɗa da Kalangu, da
Bishi, da Gangi, da Kurya. Su
kuma na busa sun haɗa da Ƙaho, da Shantu,
da Bindi da kuma Gyare. Su ma Kassu ya kawo su a cikin waƙa inda ya ke cewa:
Daga
ganga mai tsauri
Sai
Kalangu tamkakke
Sai
shantu sai busar gyare
Daji
ya ɓace na Auta
Rannan
har an ɗora kiɗin Kurya
(Kassu Zuri, Garu-garu na Mande).
6.0 GUDUNMUWAR
FARAUTA GA RAYUWAR ADABIN
BAKAN HAUSAWA.
Adabi madubi ne ko hoto na rayuwar al’uma. Abu ne daya game dukkanin rayuwar
ai’uma, musamman fasaharsu da hikimominsu. Fasaha da hikimomin al’uma kan haɗa da maganganun
hikima kamar Kirari da Take, da Habaici, da Gugar-zana, da Baƙar-magana, da Karin-magana, da Tatsunniyoyi, da Labarai,
da uwa, uba Waƙa.
6.1
WAƘOƘIN FARAUTA.
Waƙar baka wani
rukuni ne daga cikin rukunnan adabin baka wadda ta kansance wata taska ta adana
tarihi, da al’adu, da kalmomi, ma da sauran al’amurran da suka danganci
maganganun Hausawa gaba ɗaya. Kamar yadda Gummi (2013) ya bayyan waƙar baka da cewa wani zance ne na hikima ko magana wadda
aka shirya ta hanyar tsara kalmomi zaɓaɓɓu
kuma zaunannu, a rera su gutsure-gutsure cikin azanci da salon armashi, tare da
yin kiɗa da amshi da nufin isar da saƙo. Idan muka dubi yadda waƙa ta yi ka-ka-gida a cikin harkar Farauta za mu tabbatar
da cewa ba ƙaramar gudumuwa Farautar ta bayar
ba. Domin kuwa a cikin ire-iren waƙoƙin Hausa akwai waƙoƙin maza waɗanda a cikin su waƙoƙin Farauta su ake fara ambata duk lokacin da ake batunsu.
Gusau,(1993), yana cewa “Ko da yake an samu masana da suka taka rawa wajen kawo
tarihi ko asalin samuwar waƙa, amma wasu na
kyautata cewa Hausawa sun ƙagi waƙa ne ta hanyar Farauta da kirare-kirarenta”. Ban da waƙa kuma daga wurin Farauta ne aka samar da Take da kuma
Kirari. Waɗanda daga bisani suka mamaye sauran sassan adabin baknsu.
Ganin cewa waƙa ta samo asali ne tun daga lokacin da Hausawa suka fara
fita Farauta ya sa ya kasance
mawuyacin abu ne a tantance yawan wamaƙan Farauta da
ake da su a ƙasar Hausa. Amma daga baya-bayan
nana n samu wasu fitattun mawaƙa da suka taka
muhimmiyar rawa a fagen tsarawa da rera waƙoƙin Farauta. Daga cikin ire-iren
waɗannan mawaƙa akwai makaɗan Bishi da suka
haɗa da Ummaru Jikan Bagwariya, da Yado Shibdawa, da Dankazagi
Sanawa dukkansu a ƙasar Katsina. Akwai Dagajirau
Garinmalam mai kaɗa Gangi da Hamisu sarkin kiɗa a ƙasar Kano, da makaɗan Kurya irin su Garba Ɗanwasa a ƙasar Sakkwato da
kwaro mai Kurya a Doka ta ƙasar Katsina.
Haka nan kuma a samu maƙaɗan kalangu na Farauta
da dama musamman daga ƙasar Zamfara da suka haɗa da shahararrun
makaɗin Farautan nan wato Bature Nadadi da kuma Abubakar Kassu
Zurmi. Ta ɓangaran mawaƙan maharba akwai
makaɗan Garaya da suka haɗa da Ɗangalma Musawa da Iro mai Komo Kurfi. Waɗannan mawaƙa sun taa muhimmiyar rawa wajen samar da waƙoƙin Farauta. Wannan ne ya sa zai
yi wuya a kawo dukkan waƙoƙin da suka rera a zamanin rayuwarsu. Amma duk da haka ba
a rasa wasu misalai na ire-iren waƙoƙin ba. Kasancewa ba nazarin waƙa mu ke yi ba kai-tsaye amma ga misalan wasu baitoci nan
dan gane da turakun waƙoƙin dan kawo tabbacin samuwar waƙa daga Farauta. Daga cikinsu akwai:
Zuga.
Tsoro.
Faɗa.
Ta’addanci.
Juriya.
Magani.
Yabo.
Artabu.
6.1 TAKE.
Shi take kirari ne da makaɗan Farauta ke yi
ma iyayen gidansu ta hanyar gina gajerun jimloli da ke kunshe da hikima domin razana abokanen
gaba, kuma an fi yin sa da kiɗa ko busa. Ga misalin taken wasu mafarauta kamar haka:
(Ɗan Iya na Bala) “Ka
ƙi
gudu, ka hana mai gudu ya gudu”
(Sarki Muntari
Gurafe).“Hadari ɓullo
ta gabas ka ƙare
yamma”
(Bala Ƙosawa) “Gara
tsautsayi da zaman lafiya”
6.2 KIRARI.
Kirari shi ne jera
jimlolin adabi masu amfani da kalmomi waɗanda, ko dai su kasance masu
kaifin ma’ana ko masu zurfin ma’ana. Kuma waɗanda aka tsara
cikin salon siffantawa domin wasa, ko kumbura, ko ingiza mutum ko wani abu.
Dunfawa, (2004). A lokacin da Kassu ya kaɗa taken Shehu Ɓuraguji, da shehu ya fito ga yadda yake cewa:
Kassu
Wallahi ta yi yara da manya
Wallahi
ta yi daren Taure
Ka
ga manya-manya sashen Gamji
Yaro
zaɓi a goge ma kaihi ko tsini
Ka
ga na Baƙo ba
gida, ba daji
Kai
Kassu! Kai Kassu! Mai kiɗin ‘yan sababi
Bari
sai wuri ya ɓaci
Ko
wuri ya ɓaci sai Gada ta faɗi
Ko
Gada ta faɗi, sai ka ga ta yi yara da manya
Sannan
ka tambayo na Baƙo
kisago
Wanda
ba gida ba daji
6.3 HABAICI.
Banda waƙa da Kirari da Take, Farauta ta taimaka gaya wajen samar
da lafuzzan Habaici domin kuwa mafi yawancin sunayen karnukan Farauta, habaici
ne ake yi ma wani. Misali:
(Bi-su-Kare)- Mutunen da ba shi zuwa Farauta,
sai idan mata sun tafi daji ko gona ya bi
yana neman
su.
(Bar-su-ga-Allah)-Wani ne wanda ake zalunta bai ramawa sai ya ɗau
Kare ya sa masa
wannan
sunan.
(Mai-ɗan-wundi)-Wata mata ce ta cika yawan kwartanci, sai
wani mafarauci ya sa
ma Karyarsa
wannan sunan.
(A-sha-za ga)- Wani makaɗin Farauta ne ya sa wa Karen shi wannan suna, amma
yana nufin
wani ne wanda ba ya yi masa kyauta, kullun sai rowa.
Baya ga duk waɗannan sassan
adabin baka da muka gani, Har wa yau Farautar ta taimaka wurin ginawa da samar
da Karin maganar Hausawa. Idan muka dubi iren-iren Karin maganganu irin su:
Can ga su Gada, da Zomo ya ji kiɗin
Farauta.
Ba ni
na kashe Zomon ba, rataya aka ba ni.
Kuwwar banza, Sa-ranin marar Kare.
Tsufan sarkin baka, yana tsufa yana ƙara shiga daji.
Haka kuma wasu daga cikin marubutan litattafan karatun Hausa. Aƙoƙarinsu na samar da
abun karantawa sun yi amfani da Farauta sun gina labaransu. Ire-iren waɗannan
littattafai sun haɗa da ZAMAN MUTUM DA SANA’ARSA da LABARUNDA DA NA YANZU,
da wasunsu.
7.0 KAMMALAWA.
Ganin
irin yadda Farauta ta kasance magamin rayuwar Hausawa tun daga samuwarsu har kawowa
wannan zamani da muke ciki, za mu tabbatar da cewa ba karamar gudunmuwa ta
bayar ba ga raya al’adar Hausawa tun daga neman abinci, da samar da wurin zaman
su, da tsarin gudanar da mulkinsu, da samar da tsaro, da gudunmuwar da ta bayar
wurrin samar da kayayyakin gudanar da sana’o’in su. Haka nan ta wani ɓangaren kuma
farautar ta ba da gudunmuwa ainun wajen ginuwar Adabin bakansu ta ɓangaren da ya
shafi waƙa, da kirari da habaici, da karin-agana.
Duk da kasancewa samuawar isasshen abinci da nama ta hanyar noma da kiyo, har
kawowa yanzu farauta ta zama abar sha’awa ga mafarauta ta hanyar kwaikwayon
irin tsarin da ya gabata. Da haka ne nake ganin zai kyautu idan aka samu damar
gadunar kwakkwaran bincike domin tattara dukanin irin gudunmuwar da Farautar ta
bayar ga raya al’adar Hauswa domin kuwa zai yi wuya a gabatar da su a cikin ƙaramin lokaci irin wannan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.