Tarihin Malam Babba Na Ƙofar Gabas


    Maƙasudin wannan aiki shi ne gano ko sanin tarihin malam Babba na ƙofar gabas wajen sanin haihuwarsa da kuna tarihin rayuwarsa da kuma irin buwayarsa da ya yi. Maƙasudin wannan aiki shi ne domin gano ko sanin tarihinsa da muhimmancin sana’arsa da kuma tashinsa da ya yi da ƙwazonsa da kuma irin shaharar da ya yi a ƙasar. Tarihi ya nuna cewa duba shi ne aikinsa, wanda ta wannan hanyar ne ya shahara kuma aka san shi a duniya wanda da wannan hanyar ne yake samarwa kansa abinci da kuma abin biyan buƙata ta yau da kullum. Irin ficen da ya yi a wannan ɓangare ya sa ake yawan neman tarihinsa na rayuwa domin amfanar da al’umma. Domin cimma manufar wannan aiki an kasa shi kamar haka: Gabatarwa, Dabarun bincike, Ra’in bincike, farfajiyar bincike, tarihin rayuwar Malam Babba ba ƙofar gabas da sana’arsa da buwayarsa da amfani da ya samu a rayuwarsa.


    Tarihin Malam Babba Na Ƙofar Gabas

    Ibrahim Mohammed
    0 806 028 7141
    Gabatarwa
    Allah Ubangiji maɗaukakin sarki, Ya wajabta duka jinsin mutane su karanci Alƙur’ani mai girma gwargwadon iko, kana kuma su san kaɗan daga  ƙa’idojin addinin Musulunci ta yadda za su bauta wa Allah ba bisa jahilci ba, saboda haka, sai ya zamana abin da ake yi a ko’ina cikin duniyar Muslmai shi ne da zaran yaro ko yarinya sun fara girma, sai a sanya su a makaranta don neman sanin Alƙur’ani mai girma tare da koyan rubutu da karatu, daga baya kuma sai a shiga sanar da shi ko ita hukunce-hukuncen addini. Wannan kuwa ya danganta ne da irin yadda Allah Ya so ya sauwaƙe wa mutum, wani Allah Ya kan ba shi ƙwazo da fasaha har ya haddace shi, kuma ya yi zurfi wajen sanin wasu fannonin ilimi, iri-iri, wani kuma Allah bai sanya da rabo sosai ba tun daga farko abin zai ƙi shi, sai kawai ya watsar ya shiga wata harka daban. To wanda ya tsaya ya karanta sosai, ya iya to shi ake ce wa Malam.
                Amma a ƙasashen Hausa tsarin neman karatu ya sha bamban kaɗan da na wasu wurare ko ƙasashe na duniya. Galibi a ƙasar Hausa farkon makarantar da suke fara sanya yara ita ce makarantar Alƙur’ani wadda aka fi sani da makarantar allo. A nan yaro zai fara karatu har ya sauke alƙur’ani, idan akwai hali ma har ya haddace wani kuma da ya sauke shi ko kuma ya yi karatu wato ya san baƙi, ta yadda zai iya rubutawa da karantawa, sai kawai a fitar da shi kuma a mayar da shi ta ilimi, inda zai koyi hukunce-hukuncen addnin Musulunci. Saboda haka, wannan ya nuna mana cewa,a tsari karatun Hausawa akwai manyan makarantu guda biyu kamar haka: (i( MakarantarAlƙur’ani ko makarantar Allo. (ii) Makarantar Ilimi ko makarantar littafai, daga cikin waɗannan makarantu guda biyu duk wadda mutum ya halarta in dai ya ƙware ana iya kiransa malam, balle ma wanda ya ƙware a duk biyun ko kuma ma yana koyarwa. A wasu lokuta ma har da wasu ƙarin girmamawa gwargwadon karatun mutum, Alal misali, wanda ya ƙware sosai a game da karatun Alƙur’ani to bayan kasancewar malam, ana kuma iya kiransa Alaramma ko gwani ko gangaram da dai sauransu. Haka kuma shi ma wanda ya ƙware a bisa fannonin ilimin addini, to shi ma dai bayan kasancewarsa malam ana kuma iya kiransa Ustaz ko Shehi. To su dai malamai a kowace irin al’umma abin girmamawa ne, musamman a cikin Hausawa, don kuwa ya kasance ba a iya taɓuka komai na sha’anin da ya shafi rayuwa ba tare da malamai ba., kamar abubuwan da suka shafi sarauta da mulki da aure ko ciniki da sana’o’i balle ma uwa uba abin da ya shafi addini. Kuma su malamai, suna da tasirin faɗa a ji da ƙwarjini, don haka ya kasance lallai ne a karɓi shawarwarinsu a game da harkokin rayuwa. Kuma su gidajensu ya zama makaranta wajen neman sani da gyaran addini, haka kuma sun zama tamkar asibiti wajen neman waraka daga cututtuka da kuma biyan buƙata.
                Ganin irin yadda mutane ke daudala a ƙofar gidan malamai don neman biyan buƙatu, shi ya sanya ya zama dole ga wasu malamai su koyi wasu fannoni ilimai, musamman wanda suka shafi matsalolin taimakawa mutane wajen warware matsalolinsu na rayuwa kamar ilimin harrufa, da na hisabi, da na bugun ƙasa da na taurari, da na sunaye da ayoyi da dai makamantansu. Kuma su waɗannan su ne ilimin da ake kira ilimin tsibbu.
                Amma kuma wani abin sha’awa da lura a nan shi ne komai, sanin da mutum ya yi na ilimi tsibbu tare da fahimtarsa ba a kiransa malamin tsibbu natuƙar ba yana ta’ammali da shi ne ba sai kawai a ce ya san tsibbu. Kamar dai mutumin da ya iya jan mota ko ya iya kaɗa ganga, to, ai ba a kiransa kowanensu direba ko makaɗi, matuƙar dai ba sun mayar da su sana’a ba ne, sai dai kawai a ambaci cewa wane ya iya mota, ko ya iya kiɗa. Haka kuma sau dayawa mutum zai ga cewa wani daga cikin malaman allo ko kuma na addini, sukan ɗan bayar da taimako a wasu lokuta da addu’a ko da wasu `yan laƙulƙuna da addu’a kamar rubutun sha, ko laya ko wani magani da dai sauransu. To su ma ba a kiran su malam tsibbu, tun da dai ba sun ɗauki haka ta zama sana’arsu ba ne.

    Ire-Iren Malamai
                Bisa ga wannan akwai malamai kashi daban-daban haka kuma a ƙasar Hausa akwai sunaye iri-iri da ake kiran malamai da su. Akwai malaman sunna da malaman bidi’a da malamin malamai da shehun malamai da kuma waliyin malami ga taƙaitaccen bayani a kan kowannensu.
    Malamin Sunna: Shi ne malamin da ke da ilimin addinin Muslunci gwargwadon, kuma yana karantar da shi ga jama’a. Bugu da ƙari, yana da taƙawa da nutsuwa da tsantseni da gudun duniya na innanaha kuma ba shi da tsoron faɗin gaskiya a kan komai da kowa. Haka kuma bai damu da fushin wani ba wajen faɗin gaskiya. Ire-iren waɗannan na da wuyar samuwa. Amma ana samun su domin bayin Allah nagari ba su ƙarewa.
    Malamin Bidi’a: Shi ne wanda yake da ilimin addinin Musulunci kuma yana koyar da shi ga mutane, amma yana da ƙwaɗayin abin da ke hannun mutane da kuma tsananin son dukiya a zuciyarsa.
    Malamin Tsibbu: Shi ne malamin da ya shagaltu da ba maras lafiya magani ta hanyar amfani da ayoyin Alƙur’ani mai girma da yin layyu kuma yana bugun ƙasa don ya faɗa wa mutane alherin da za samu ko cutar da za ta same su to akan kira shi da malamin tsibbu.
    Sarkin Malmai: A wasu wurare cikin ƙasar Hausa, in malamai na da yawa sarkin garin yana naɗa musu shugaba. Shugaban malamai a gari ko a ƙasa shi ne sarkin malamai wanda yake ba dole ne ya zama ya fi dukkan malaman garin ilimi ba. A halin yanzu akwai sarkin malamai a Sakkwato.
    Malamin Malmai: Idan malami ya shahara ƙwarai da gaske a kan ilimin addinin Musulunci, har wasu malamai da almajirai na zuwa daga nesa saboda neman ilimi a wurinsa, akan kira wannan malami da laƙabin malamin malamai. Hausawa sun sami wanann sunan ne daga Larabawa da ƙirƙirar wasu malamansu da laƙabin ‘Sharrl al shuyuki ‘al-allamat’ a nan nufin da wannan laƙuba babban malami wanda babu na biyunsa a ƙasa ko a zamaninsa.
    Shehun Malamai: Shehun malamai shi malamin da ya yi zurfi a cikin ilimin sufanci da ɗariƙun waliyan magabata. Haka nan kuma akan kira irin wannan malamai da sunan malamin ɗariƙa, wani lokaci in malami ya tsufa ƙwarai har ya ba shekara sittin baya a kan kira shi shehun malami.
    Waliyi: wani lokaci a kan samu malami mai tsoron Allah da natsuwa da gudun duniya da yawan ibada da ilhama har ma in ya yi magana a kan wani abu da zai auku, sai abun ya auku yadda ya ba da labari malamai masu irin wannan siffofi da aka zana a kan yaɗa cewa su waliyai ne. abin da ake nufi da waliyi shi ne bayan Allah da Allah ke so, wanda za ya shiga aljanna. Hausawa sun ɗauka cewa waliyi yana da ikon nuna karama yadda ya so, kuma a lokacin da ya so. Sun yi imani cewa, waliyi na iya abin da sauran mutane ba za su iya yi ba, kamar tafiya a kan ruwa ba tare da jirgi ba, ko tafiya wuri mai nisa a cikin lokaci ƙanƙani, ko kuma rayuwa wata da watanni ba tare da ci ko sha ba, da makamantansu.
                A ƙasar Hausa akwai malamai da yawa waɗanada suka shahara da walittaka mutane da yawa sun ɗauka su waliyan Allah ne, waɗanda za su shiga Aljanna kai tsaye ba tare da wata wahala ba daga cikinsu akwai Wali Ɗan marina da Wali Ɗan Masani da Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo. Haka kuma akwai karamomi iri-iri da aka danganta da kowannensu.
    Malamin Allo: Shi ne malamin dake karantar da yara Alƙur’ani mai girma da allo, shi ne ake kira malamin allo. Sau da yawa malamin allo almajiri ne. bayan yara sun tashi daga makarantarsa yakan tafi wajen babban malaminsa wanda ya fi shi sani don ɗaukan ilimi.
    Malamin Zaure: Malamin zaure akan kira shi malamin allo in ya kasance yana karantar da yara karatun Alƙur’ani da allo, kuma yana karantar da manyan litttafai kamar su: Ahalari da Ishimawi da Iziya da Risala da sauaransu.
    Alaramma: Wannan shi ne laƙabin da malami da ke da sanin Alƙur’ani sosai. Asalin kalmar  a Larabci (Allahu Yaharmuku) ma’anarta, Allah shi rahamshe ka, kafin a kira malami Alaramma sai ya haddace Alƙur’ani mai girma kuma yana iya rubuta shi da ka. Haka ma kuma yana iya bayanin tsarinsa da rabe-raben sururorin Alƙur’ani da ka.
    Malamin Gafaka: Wannan shi ne malami wanda ke yawo da almajiransa daga wani wuri zuwa wani wuri. Ba shi da sana’ar neman abinci ban da karantar da yara Alƙur’ani mai girma. Ya dogara ne a kan sadakan da mutane kan ba shi da kuma hidimar da almajirana kan yi masa.
    Ustazu: Hausawa kan kira mutum Ustazu in sun ga alama cewa yana yin shiga irin ta malamai kuma yana da ra’ayin riƙau game da sha’anin addini alhali kuwa ba shi da isasshen ilimin addnin Musulunci. Haka kuma akan kira mutum Ustazu in malami ne shi amma ba ya ɗariƙa, kuma ba ruwansa da ilimin sufanci wani lokaci a kan kira irin wannan malamin malamin Izala.

    Manufar Bincike
    Manufar wannan bincike/aiki shi ne a bi diddigin tarihin Malam Babba na Ƙofar Gabas ta fuskar irin ficen da ya yi a aikinsa na duba a ƙasar Hausa ganin cewa ya yi fice wajen aiwatar da aikinsa na duba da bugun ƙasa, haƙiƙa wannan aikin zai taimaka ƙwarai wajen gano tarihinsa da yadda ya sanu wajen aiwatar da aikinsa, wanda sakamakon haka ɗalibai da kuma manzarta za su samu wani ƙarin haske game da tarihinsa da ayyukansa ta fannin ilimi da kuma ƙarin samun wasu hujjoji da suke da muhinnancin gaske.

    Ra’in Bincike
    An zaɓi ɗora wannan bincike a kan ra’in ƙwaɗaitarwa (Motiɓation Theory) kalmar ‘motiɓation’ ta samu fassara daga masana da dama Garba, (2012:65) ya fassara kalmar ‘motiɓation’ a matsayin zaburarwa wadda ya ce, hanya ce da ake sanya mutum ƙaimin cimma wata manufa.
                Wannan ra’i an fi danganta samuwarsa daga MC Dougall (1871-1838) a wani littafi nasa mai suna An Introduction to Social Pschology, ya bayyana cewa zuciya da tunanin mutane na da wani halittaccen ko hali wanda ke da ƙarfin ingiza  yin duk wani tunani ko aikata wani aiki.
                Ado, (2017) a maƙalarsa mai taken, “Sarkin Gardin Sarkin Katsina Alhaji Amadu Na Lado: Gwarzon da ya yi fice a sana’ar Gardanci A Ƙasar Katsina wadda ta fito a littafin The Heros nad Herroines of Hausa land, ya ce shi dai ra’in ƙwaɗaitarwa,  Motiɓation Theory ra’i ne wanda yake yin bayani kan ɗabi’a da halayyar ɗan Adam ta fannin bayar da dalilin da ke sanya ko a zaburar da ɗan Adam a lokacin da yake jinƙawa ko sha’awa ta musamman, na aikata wasu ayyuka ko wani ƙuduri ko nua wata buƙata ta rayuwa. Don haka an ɗora wannan aiki ne a kan wannan mazhaba ta ƙwaɗaitarwa da jajircewa tare da burin malaman Babba na ƙofar gabas na yin fice a aikisa na duba da bugun ƙasa.

    Dabarun Bincike
    Manyan dabarun da aka yi amfani da su yayin aiwatar da wannan aikin binciken su ne bitar ayyukan da suka gabata, da kuma tambayau, da hirarraki da dangi da abokai domin cimma manufofi.
                An yi bitar ayyukan da suka haɗa da kundayen digiri da muƙalu da littatafai. An bibiyi ra’ayoyin masana da marubuta game da tarihin Malam Babba Na Ƙofar Gabas, bayan haka an zanta da `ya`yansa da masu unguwanni da manyan mutane wajen yin hira da su don samun ingancin aikin tare da hujjoji don fito da sahihin tarihin Malam Babba na ƙofar Gabas da kuma irin buwayarsa da ya yi a doron ƙasa.

    Farfajiyar Bincike
                Dangane da wanan aiki an sanya ƙudurin yin nazari mai zurfi ta hanyar bin diddgi rayuwar Malam Babba Na ƙofar Gabas da ayyukansa Buwayarsa tun farkon rayuwarsa har zuwa lokacin da ya komawa Ubangijinsa. Don haka ya zamo wajibi muhallin da za a gudanar da wannan aiki ya karkata ga dukkan wuraren da ake sanya tsammanin za a samu duk wani bayani da ya dangance shi don ganin wannan ƙuduri ya cika, wannan nazari ya taƙaita ne kan tarihin Malam Babba na Ƙoafar Gabas da kuma irin aikace—aikacen da ya yi.

    Taƙitaccen Tarihin Malam Babba na Ƙofar Gabar
    An haifi Malam Babba na ƙofar Gabar a garin Katagun mai kaba cikin ƙaramar hukumar Zaki da ke cikin jahar Bauchi, babu takamaimai shekarunsa na haihuwa domin kuwa ba a rubuta lokacin da aka haife shi ba, wannan ba shi da mamaki domin kuwa a ƙasar Hausa ilimin boko bai yawaita a lokacin haihuwarsa ba, hasali ma ana ƙyamar bokon ne tare da waɗanda suka kawo shi wato Turawan Mulkin mallaka.
                To, Sai dai duk da wannan cikas ɗin ana iya bin wasu hanyoyi a yi ƙididdigar shekarun mutum. Misali ana iya auna shekarun mutum da wani gagarumin abin da ya faru a cikin tarihi a daidai shekarun ko kafinsa ko kuma bayansa, an haifi Malam Baba na ƙofar Gabas a wani lokaci da ake ƙira kakan yunwa a daidai lokacin da ake tonowa gidan tururuwa domin a samu abincin da za a ci.
                A binciken da na yi a wajen ɗansa ya ce min ya rasu yana da shekara cas’in wanda ya yi daidai da 1917, sunan mahaifinsa Waziri Abba ɗan Malam Muhammadu Mai Gizo dukkansu mutanen Katagun Mai Kaba ne wadda take cikin ƙaramar hukumar Zaki, sunan mahaifiyarsa Hajiya Amina kuma iyayensa maza Barebari ne na Zaki wato wadda ake yi musu laƙabi da Larawa.
                Malam Babba na ƙofar Gabas ya zauna a gaban mahaifinsa ya fara karatunsa daga nan mahaifinsa ya rasu sai ya dawo wajen yayan babansa a gari Azare mai suna Baba Sabo, wuraren da ya zauna Malam Baba na ƙofar Gabas ya zauna a garin Kano a wata anguwa da ake ƙiran ta unguwar Durumin Iya a na cikin garin Kano

    Laƙabinsa na Suna
                Sanannen abu ne cewa a ƙasar Hausa ana sawa mutum laƙabi wato wani suna da za a iya ƙira suna na biyu, dalilin sunansa na Malam Babba na ƙofar Gabas ya samo sunan ne daga gidansu, wato ana kiransa da Malam Beji kalmar Barbarci ne, wadda take nufi babba, shi kuwa na ƙofar gabas dalilin ya zauna ne a ƙofar Gabas domin kuwa sarkin garin ne mai suna Sarki Abdulƙadir ya ba shi gida kyauta a ƙofar Gabas ya zauna a cikinsa har tsawon rayuwarsa. Suna Malam Babba na ƙofar Gabas na yanka shi ne Muhammadu Aminu.

    Zuriyarsa
                Malam Babba ya yi auren farko ne a cikin garin Kano a unguwan da ya zauna mai suna unguwar Durumin Iya a na cikin garin Kano. Matar da ya aura ita ce uwargidansa, wato matarsa ta fari mai suan Hajiya A’isha, haka kuma ya auri wata mata mai suna Hajiya Ummi a garin Azare ƙaramar hukumar Katagun. Allah ya azurta shi da `ya`ya maza da mata shidda, maza biyu, mata huɗu. Ga suannayensu kamar haka:
    1.      Muhammaadu
    2.      A’isha
    3.      Faɗima
    4.      Talatu
    5.      Zainabu
    6.      Inuwa
    Sana’arsa
          Malam Babba ya taashi ne a gidan karatu, don haka sai da ya yi karatu a makarantar allo a gaban babansa da yayan babansa gabanin ya buɗe ido da kowace sana’a, daga cikin abin da ya yi shi ne noma.
    Buwayarsa
    Kafin na shiga cikin buwayarsa  yana da kyau na ce wani abu game da duba, bugun ƙasa da kuma tsibbu.

    Ma’anar Duba
          Kalmar duba a harshen Hausa tana da ma’anoni masu tarin yawa tun daga ma’anarta ta harshe zuwa ma’anarta ta fannu. A ma’anar duba ta harshe wato lugga, duba yana nufin kallo ko gani da ido ko karonta. Misali ya duba aiki, ko ya duba littafi ko kuma ya duba ni” (CNHH 2006:108).
           A ma’ana ta haƙiƙa ko ta wani fanni na ilimi duba na iya zama ɗayan wɗannan:
    -          Duba wato gaisuwa kamar ta marar lafiya
    -          Duba wato sassauci kamar Allah Ya dube mu da idon rahama
    -          Duba wato ilimin sanin wasu abubuwa da ke ɓoye ko bugun ƙasa.
    Ma’anar duba a wannan nazari, ita ce binciko ɓoyayyen al’amura waɗanda suka shafi rayuwar ɗan Adam ko abubuwa ko dabbobi da makamantansu. Kuma irin waɗannan abubuwa ɓoyayyu suke ake kira gaibu.

    Musabbabin Duba
    Kowane abu da ɗan Adam yake gudanarwa a rayuwarsa ta yau da kullum, akwai dalilin da suka sanya shi yin haka. A ƙasar Hausa mutane suna da buƙatar sanin abubuwam da suke e aikatawa a rayuwar yau da gobe. Mutane sukan yi tambayoyi na su gane abin da zai iya yiwuwa ko ba zai yi yiwu ba kuma ko akwai alheri a ciki ko babu kuma ta hanya abin zai yiwu, kuma ya ya ƙarshen zai kasance?

    Kashe-kashen Duba
                Idan aka kalli al’amarin duba bisa jumlarsa za a iya kasa shi zuwa manyan gidaje guda biyu waɗanda suka haɗa da duba na gargajiyar Hausawa da kuma na zamani wanda Hausawa suka fahimce shi bayan zuwan Musulunci.
    1.      Duba na gargajiya: Hausawa sukan yi amfani da hanyoyi mabambanta waɗanda suka samar wa kansu na gargajiya wajen yin duba, amma duk da haka sun fi dogara ne da yarda da abin da matsafa da `yan bori da bokaye suka sanar da su. Haka kuma ɗaiɗaikun mutane sun ba sha’anin duba da binciken gaibi muhimmancin gaske ta yadda ta kai sun fi yarda da abin da bincike ya nuna bisa dukkan komai misali ɗan sarki zai so ya san zai gaji mahaifinsa ko ba zai gaje shi ba.
    Irin waɗannan abubuwa ne suka ingiza al’ummar Hausawa wajen neman wanda zai dinga warware masu matsalolin da suka taso musu. Daga cikin hanyoyi na gargajiya da al’ummar Hausawa suke aiwatarwa daga cikin su akwai bori da tsafi da bokanci da magori da zane-zane da wuri da makamantansu. Hanyoyin da `yan bori ke bi wajen gudanar da duba sun haɗa da hawan Aljani, wannan kuwa wata hanya ce da kowanne ɗan bori yake bin ta, ta haka ake iya kiran kowanne Aljani a yi magana da shi. Kuma ya bayyana abubuwan da ake buƙatar sani a ɓoye daga cikin fitattun Aljanu da suka fi ma’amala da su wajen duba akwai wasu kamar haka: Nakada da `Yar mairo da Barahaza da Babuk da Sarkin rafi. Kuma har ila yau ban da ta hanyoyin Aljani su `yan bori suna gudanar da harkokin duba ta amfani da wuri.
          Daga cikin abubuwan da matsafa kan yi amfani da su wajen gudanar da duba, akwai amfani da dabbobi ko sassan jikinsu. Yana kuma amfani da wuri da kyauro da kuma lura da mafarki ta haka matsafi zai harhaɗa abubuwansa kuma ya yi ta wasu gwalan-gwalon yana tofawa a wani ɗan koko bayan ya zuba jinin wata dabba a ciki yana tattauna goro ko barkono yana zazzare ido yana mazurai. Sai ya shiga yin bayani game da abin da aka tambaye shi, yana magana yana nuna kamar yana magana ne da wani daban. A wani lokacin ma matsafin ya kan yi shiru. Wata dabba da take tare shi ta dinga bayani kamar mage ko kare ko damo ko kaza ko wata tsuntsuwa da sauransu. Ta haka matsafi yakan yi duba ga duk wanda ya je wajensa neman bayani game da wata matsala da ta taso masa ya Allah ta aure ce ko ta sa’a ko ta lafiya. Bokaye a wajen Hausawa mutane ne waɗanda ake masu da’awa ta laƙantar hanyoyi na binciko abubuwan gaibi waɗanda suke ɓoye bisa kuma matakansu bambanta. Ta haka ne Hausawa suke yin tururuwa gare su domin neman waraka bisa matsalolinsu daban-daban masu tarnaƙi da dabaibayi.
    2.      Duba na Zamai: A bayanan da suka gabata an yi tsokaci ne game da duba na gargajiyan Hausa tare da fito da ire-irensa da kuma masu gudanar da su. A nan kuma za a yi magana ne dangane da duba na zamani wanda Hausawa suka samu bayan da suka karɓi addinin Musulunci.
    Ilimin sanin gaibu wato duba yana daga cikin sassan na ilimai waɗanda Hausawa suka sami rabauta da su bayan zuwan addinin Musulunci. Haka kuma Hausawa sun sami littafai da yawa a kan ilimi na duba, har inda Hausawan a daidai ƙarni na goma sha takwas (18) suka wallafa nasu ayyukan akan fanni na duba lokacin da Hausawa suka ƙaru da ilimin duba a zamanace sai suka fahimci hisabi da ilimin nujumu da ilimin alfaku da kuma ilimin bugun ƙasa.
                Ilimin hisabi – Ilimi ne wanda ya danganci hanya ta amfani da haruffa ana sarrafa su don a cimma biyan wasu buƙatu. A ilimin hisabi akan sanya haruffa su wakilci wani adadi na ƙidaya. Ta haka kowane harafi yana zama a gurbi na adadi daga ɗaya zuwa dubu.
    Ilimin Nujumu
                Kalmar Nujumu da harshen Larabci tana nufin taurari wannan ilimin na Nujumu yana magana ne a kan falala da taurari. A wajen Hausawa suna kiransa ilimin Nujumu da ilimin taurari kuma suna ba shi matsayi irin wanda Larabawa suka ba shi na zamantowa ilimi wanda ya shafi taurari da falaƙi. Ilimin taurari yana bincike ne game da sararin samaniya wato rana da wata da taurari ta fuskar jujjuyawar su da tafiyarsu da adadin taurari da sanyi da zafi da ruwa da kuma kisfawar rana ko na wata yanayin taurari na dare da na rana da na bazara da na kaka da na damina tare da amfaninsu game da rayuwar `yan Adam. Su kansu taurari suna da matuƙar yawa ta yadda babu wanda ya san adadinsu sai Allah maɗaukakin sarki kuma mahaliccin abubuwa.
                Taurarin da ake gudanar da harkokin duba da su ne suke da alaƙa ta kusa-kusa da ɗan Adam tun daga ɗaukar cikinsa har zuwa ranar haihuwarsa da kuma sauran harkokinsa na rayuwa zuwa mutuwa. Su waɗannan taurari su kuma suna tafiya tare da burujai guda goma sha biyu (12) na watanni, sannan kuma ko wane mutum yana da nasa burujin wanda ya dace da rana ko watan da aka haife shi a ciki. Kuma kowanne buruji na mutum yana da suna da wata sifa ko wata alama da ta bambanta shi da sauran burujai.


    Bugun ƙasa da Siffofinsa
    Asali da wanzuwar bugun ƙasa
                An sami ra’ayoyi mabanbanta dangane da asalin ilimin bugun ƙasa. Akwai malamai waɗanda suke ganin ilimi ne wanda daga sama ya sauko, sai ƙasa ta karɓe shi da duk abin da yake cikinsa, sai ya zama tana bayyana abin da ya ƙunshi wani bayani Thhey, (196:24).
                Wasu malamai kuwa suna danganta ilimin bugun ƙasa da Annabi Idirisu Alahi’s Salam (A.S). An ce Annabi Idirisu Alaihi’s Salam, Allah Ya aike shi zuwa ga wasu al’ummu waɗanda suka shahara da sanin ilimin taurari. A wata rana shi Annabi Idrisu, Alahi’s Salam yana tafiya, sai ya zo wucewa ta gefen wani mutum mai kyawun sura shi Annabi Idris bai san shi ba, ama sai ya j mutumin ya ambaci sunansa, sai mamaki. Daga nan sai ya ce da wannan mutum yaya ka yi ka san sunana bayan ba mu taɓa haɗuwa da kai ba? Sai wannan mutum ya ce da shi na san ka ne ta hanyar wani ilimi da Ubangijina ya sanar da ni, ko kai ma kana so na koya maka ne? sai Annabi Idrisu ya ce ƙwarai kuwa ina so ka koya mini daga nan sai mutumin ya yi amfani da rerayi domin a lokacin babu takarda.
                To bayan wannan mutum ya koya wa Annabi Idrisu wannan ilmi, kuma ya ga ya fahimta, sai ya ce da Annabi Idrisu ya buga masa ƙasa da niyan gano Mala’ika Jibrilu a ina yake a halin da suke ciki? Sai ya buga masa ƙasa da wannan niyar, sannan ya ce da shi, ya kai wannan bawan Allah, idan dai wannan ilimi ya yi gaskiya to a halin yanzu Mala’ika Jibrilu ba ya sama yana ƙasa tare da mu. Da tafiya ta miƙa ta hanyar wannan ilimi Annabi Idirsu ya fahimci wannan ba mutum ne ba, kuma shi ne Mala’ika Jibrilu ya zo masa a surar ɗan Adam (Al-Buney, 1996:27).
                Daga nan, Annabi Idrisu, Alahi’s Salam, ya tafi wajen jama’arsa, ya ce da su zan sanar da ku wani ilimi da Allah Ya sanar da ni, wanda za ku san abin da ya wuce da abin da ake ciki da kuma abin da zai zo nan gaba, sai suka ce to ka sanar da mu. Sai Annabi Idrisu ya koya musu ilimi-al-ramli. Wato ilimin bugun ƙasa.
                Daga nan Annabi Idirsu alaihi’s Salam ya tafi wajen jama’arsa ya ce da su zan sanar da ku wani ilimi da Allah Ya sanar da ni, wanda zaku san abin da ya wuce da abin da ake ciki da kuma abin da zai zo nan gaba, sai suka ce, to ka sanar da mu. Sai Annabi Idrisu ya koya musu iliu-alramli. Wato bugun ƙasa.
                Bayan sun koya da ya ga haƙiƙa sun fahimci ilimin sai ya tambaye su shin Allah Ya aiko wani Annabi wato Manzo? Idan kuma ya aiko shi ya ya sunasa? Sai suka buga ƙasa fitar da wannan buƙata, kuma suka fahimci Allah Ya aiko Annabi, sannan sunasa Idrisu. Nan take suka ba da gaskiya ga Annabi Idrisu, alaihis-salam. Daga cikin waɗanda suka koyi ilimin akwai ɗan Annabi Idrisu alaihis-salam, da ake kira Ukhnuƙhin. Haka kuma aka yi ta koyon ilimin nan na bugun ƙasa aka yi ta gajejeniyar aiki da shi har zuwa yau Thuhty, (1976:15).
                An ɗora harsashin ilimin na bugun ƙasa bisa turaku gida huɗu domin kuwa sirrin wannan ilimi ya samu ne daga ɗigo wato haka (.) wanda yake nuni ko ishara da ɗaya ƙwal, kuma shi ne mafarin ƙirge da ɗaya da ɗaya biyu ke nan wato haka (..). Tun da an ɗora ilimin bisa yanayi na ɗabi’a huɗu ne wato wuta da iska da ruwa da ƙasa sai aka gina tushen ilimin bisa shakali kamar haka: Wato digon wuta.
    Mai bi masa iska, na ƙasa da shi ruwa, na ƙarshen ƙasa kuma ƙasa. Da kuma a ka lura sai a ɗora shakalai na bugun ƙasa bisa gidajen goma sha shida daidai, ba ragi ba daɗi.



    Sharuɗan Bugun Ƙasa
    Lokaci Keɓaɓɓe
    Lokaci wanda aka keɓe na yin bugun ƙasa shi ne wanda ba na hudowar rana ko lokacin faɗuwarta, ko lokacin na garjin rana ko lokacin tashin iska ko motsawar giza-gizai ko kuma zubar ruwan sama ko tsaknanin sanyi ko kuma tsananin zafi.
    Tsarki da Alwala
                Wajibi ne mai bugun ƙasa, a lokacin da zai buga ya kasance cikin tsarki na jiki wato ba ya tare da janaba ko jinin haila ko na biƙi ko kuma wata najasa a jikinsa ko tufarsa ko muhallin gudanar da aiki. Haka kuma wajibi ne ya kasance yana tare da alwala.
    Buƙatu muhimmai
    Sharaɗi ne mafi ƙarfi ba a gudanar da bugun ƙasa sai don wata buƙata muhimmiya, amma ba don tsegumi ko gwaji ko kuma wasa ba.
    Nutsuwa da tara hankali
    Wajibi ne ga mai gudanar da bugun ƙasa ya kasance cikin farin ciki babu ɓacin rai sannan ya nustu ya tara hankalinsa waje ɗaya, don kada a sami kuskure wajen aiki kuma ba zai yi magana da kowa ba wani ma ba zai yi masa magana ba har sai ya kammala bugun ƙasar kuma amsa ta fita.
    Damantawa
    Abin da aka fi so mai bugun ƙasa shi ne ya yi amfani da hannunsa na dama, sannan ta ɗan ya tsansa manuni wajen bugun ƙasa, amma idan ya yi amfani da na tsakiya ma ba laifi, kuma kada a yi bugun ƙasa a martabar hanya, amma ana iya yi a ƙarƙashin bishiya ko dutse da sauransu.
    Kalmar Tsibbu
    Ita dai wannan kalma “Tsibbu” asalinta Larabci ce, kuma a Larabce ana cewa “Ɗibbi” amma kuma kamar yadda aka sani ne cewa idan Hausawa suka ari wata kalma musamman ma idan daga Larabci ne, to baƙin “Ɗa’  ya koma ‘tsi’ sai wannan kalma ta zama tsibbu to amma don wannan misali ya daɗa fitowa fili sosai, ga jerin wasu sunaye masu baƙaƙen ‘ɗa’ da aka aro daga Larabci kuma suka koma cikin harshen Hausa suka sami canji
    Larabci -          Hausa
    Dalha               Tsalha
    ɗibbu               tsibbu
    Tsibbu shi ne bin wasu hanyoyi na addu’o’i da roƙon Allah, sannan da karance-karance da rubuce-rubuce tare da haɗe-haɗen abubuwa da nufin biyan buƙata (Al’Buney, 1970:543).

    Buwayarwa da Ayyukansa
    Malam Babba na Ƙofar gabas mutum ne da ya ta so tun ƙarami da hazaƙa da kuma kaifin ilimi da kuma basira domin kuwa wannan suna ma da ake faɗa masa Malam Babba, ya samo shi ne tun daga gida  a hanyar yarensu wato ana ce da shi Malam Beji wato Babba.
                Domin kuwa duk abin da aka faɗa masa ko kuma ya koya ya ɗauke shi ko kuma ya koye shi ne ake masa laƙabi da Malam beji wato da Hausa Malam Babba. Daga cikin abin da ya buɗi ido da shi shi ne karatu daga nan kuma sai ya shiga aikin duba a nan ne ya shiga kuma ya yi suna domin kuwa akwai wata baiwa da Allah Ya yi masa wajen aikinsa na duba idan ya yi wa mutum aiki kamar yakan wuƙa.
                Saboda haka lallai ya shahara wajen aikin duba domin daga kowane sashi na ƙasar nan ana zuwa wajensaa ya yi wa mutum daga kama daga kan `yan kasuwa, `yan siyasa, ma’aikatan gwamnati da makamanatansu.
                Daga cikin manyan `yan kasuwa da ya yi wa aiki kuma ya fice akwai irin su Chanchangi. Haka kuma a ɓangaren yin aikin duba a ɓangaren mata ko kishi sai da ya yi fice a ƙasar ko yanki baki ɗaya.
                Daga cikin buwayarsa Malam Babba na Ƙofar Gabas ya tona wata rijiya a ƙofar gidansa, wato anan ƙofar gabas wanda take taimakawa jama’a wajen hidimar ɗiban ruwa don yin amfanin yau da kullum. To abin al’ajabi shi ne game da rijiyar idan wani abu ya faɗa sai a same shi a wata rijiyar wato guri mai nisan gaske. Idanunta ya haɗu da wasu rijiyoyi masu nisa, wanda idan ya ce aje rijiya ta guri kaza a je a ɗauko da ana je sai a samu abin an ɗauko. Misali daga rijiyar tasa wato ta ƙofar gidansa dake ƙofar gabas sai a samu abin a rijiyar Nasarawa.
                Daga cikin buwayar Malam Babba na ƙofar gabas shi ne idan dai ya yi aiki na duba ko makamancin haka ba a samun tawaya ko rashin aukuwarsa a kan abin da ya yi aiki. Ta irin wannan baiwa ne da Alllah Ya yi masa wata rana Alhaji Mamman Shata ya zo garin Azare wajen wani bikin a wurin Malam Babba na ƙofar gabas wato mai suna Bello Galadiman Katagun suka haɗu da Malam Babba ya yi masa wani aiki wanda ya ba shi mamaki da abin al’ajabi, wanda ya kai sai da ya yi masa waƙa, da nufim girmamawa da kuma jinjina ba dan kuɗinsa ba, sai don buwayarsa kawai.
                Haka kuma a ta ɓangaren bugun ƙasa nan ma ya shahara kuma duk lokacin da ya buga ƙasa ba a samun kuskure wajen fito da batun da ake nema na samun mafita wanda ya shafi ɗaukan kayan wani ko kuma bayani game da yin wani aiki da ya shafi siyasarsa ko kuma magana da ta shafi yin aure ko shika ko haihuwa da sauran makamantansu masu tarin yawa.

    Siffofinsa Na Halitta
                Malam Babba mutum ne baƙi marar jiki kuma yana da ƙwarjini kuma mutum ne mai yawan sa bbar riga da kuma rawani, malam Babba ya yi ɗaki na ɗore, wanda ya yi kama da na Fulani a ciki yake yin aikinsa na duba da kuma bugun ƙasa, wani lokaci yana yin kwana biyu ko uku bai shiga gidansa ba ya na wannan ɗaki yana yin aikinsa.
                Kuma ya raba yin aikinsa  na ganin mutane, da safe zuwa yamma maza yakan kalla, daga magariba zuwa dare ne, yake ganin mata.

    Karamarsa
                Daga cikin karamar Malam Babba idan ya fito da hantsi yakan sanar da mutane da suke kewaye da shi, waɗanana abubuwa da za su faru a unguwarsa ko kuma a cikin garin Azare ko  kuma wani mutum ya faɗa masa wani abun da zai iya afkuwa da shi na gaba, kuma idan ya faɗa abin yana faruwa.

    Karancinsa
                Malam Babba na ƙofar gabas mutum ne mai yawan kyauta da kuma mutunta mutane. Abin hannunsa ba ya rufe masa ido yana da yawan kyauta kuma da ga cikin ɗabi’arsa shi ne a na dafa nama ko fura a fito da ita asha a waje kusan kowane lokaci.
                Abokinsa na wajen aiki shi ne Malam Joɗa, sai dai shi, Malam Joɗa malamin sarakuna ne, da kuma manyan masu arziki, shi kuwa Malam Babba yana yi wa kowa da kowa aiki. Malam Babba na ƙofar gabas ya sake shahara sosai a dalilinsa na haɗuwa da Shata a karo na biyu, wanda ya yi masa alwalanci na aure a garin Azare wadda shi Mamman Shata ya yi aure wato jikar Alhaji Shiri wanda ke rijiyar ɗanduwala da ke garin Azare, sunan matar A’isha wadda ake kiranta  Bukuci sun haifi `ya ɗaya da shi Shata sunan yariyar da suka haifa Rukayya, kuma sun haɗu da matar ne a wajen wani wasa.
                Daga nan sai Shata ya shirya wata waƙa mai suna/taken Baban Rukayya sawun Aisha daga nan kuma sai ya sake rera wata waƙa wadda take bayanin aikace-aikacen da Malam Babba na Ƙofar gabas yake yi. Daga baya shi ne Shata ya haɗa Malam Babba da ɗan Kabo a dalilin wata waƙa da ya yi mai taken Malam Babba ka duba mini ya kuma ƙwal-ƙwale irin aikace-aikacen Malam Babba, sannan kuma ya ƙara waƙa ya haɗa Malam Babba da ɗan kabbo.
                Bayan haka Mamman Shata shi ne ya tallata shi, har ma wasu suka fari yi masa waƙa, irinsu Amarmara Gilashi da sauransu. Dangantakar Ɗan kabo da Malam Babba na ƙofar gabas, har ta kai Ɗan kabo ya kai shi Makka da kuma wasu muhimman abu da ya yi masa a rayuwa. Daga cikin waɗanda Malam Babba ya yi wa aiki kuma aka ci nasara akwai irinsu:
    -          Malam Dattijo wani ɗan kasuwa ne a garin Azare.
    -          Malam Aminu Sale
    -          Sule Katagun
    Kuma Malam Babba yana da alaƙa da fadar Katagun, domin kuwa fada tana son yin hulɗa da irin waɗannan mutane, kusan kowane lokaci yakan je fada su tattauna da sarki, haka kuma fada, takan yi masa kyauta ta alfarma, hasalima tana da ba shi rago duk sallah da nufin yin layya.

    Kammalawa
    A wannan aiki an kawo tarihin rayuwar Malam Babba na ƙofar gabar da ta haɗa da nasabar haihuwarsa da dalilin samuwar sunansa na laƙabi ƙurciyarsa. iliminsa sana’arsa, zamantakewarsa da mahaifainsa, aurensa da iyalansa zamansa a garin Azare da kuma irin buwayarsa da aikace-aikacen da ya yi da kuma sauran abubuwa na ban mamaki. Har ya zuwa lokacin da ajalinsa ya yi wato rayuwarsa. Malam Babba na ƙofar gabas ya rasu ranar 18-07-2007.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.