Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 29: Kwaɗayi Ma Dalili Ne


Wani abokina na kusa ya taba gaya min cewa ya yi mu'amalla da wata 'yar gabashi, har ya kusa zuwa gidansu sai ta gaya masa cewa ita fa ba sa zama da kishiya. Ya ce to da ma yana da mata biyu. Sai ta ce ai da sauƙi tun da ba su kai 3 ba, kuma za ta iya riƙe yaran gaba ɗaya. Da ya tambaye ta ma'anar maganarta, sai ta ce ya sallami sauran matan kawai ta ishe shi komai! Auren da ba a yi ba kenan, domin ta kai ga uwayen tsohuwar matar sun...


Zan Ƙara Aure // 29: Kwaɗayi Ma Dalili Ne

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Koda-yake kwadayi kala-kala ne, akwai na sama da na ƙasa, na saman kan kasance kwadayin nau'o'in sanadari da ababan masarufi, na ƙasan kuma ido a kan 'yammatan dake gilmawa ko matan da suka sha ado ko yanayin halittarsu, na sha ganin masu mata guda-guda wadanda ciyar da su ma matsala ce, amma kyakkyawar yarinya ko wace ta san matsalar maza na gilmawa sai ta dauke hankalinsu ka ji suna buƙatar ƙarin aure, shi ya sa za ka ji mata da dama a wannan lokacin  suna ta laluben hanyoyin da za a hana maza ƙarin aure sai an tabbatar cewa za a iya riƙe su gaba daya.
.
Shekarun baya ne aka yi wani abin kuwa a daya daga cikin jahohinmu na Arewa, inda wata yarinya ta tallata kanta tare da cewa za ta tallafa wa mai aurenta da gida da mota, haka samari da masu neman ƙarin aure suka yi dandazo kowa na ƙoƙarin ganin shi ya lashe wannan gasar ya dauke ta, da a ce ba ta yi maganar tallafi ba ƙila da zancen aurenta bai shigo tunanin manemanta ko kadan ba, kenan kwadayin abin hannunta shi ne sila, na sha jin samari na cewa "Don Allah in aka sami wata hajia mai neman miji a tuntube su" kar ka ce ko suna neman su yi aure a bagas ne, abin hannunta suke kwadayi.
.
Shi ya sa za ka yi mamaki idan na ce maka mata na yaudarar maza don su aure su, kamar yadda kowa ya san maza kan yaudari mata, wallahi yanzu mace talaka za ta gyangyanda da ƙyar ta sayi mota da kayan ƙawa, ta sami namijin da ya yi mata ta yi masa ƙaryar arziƙi, ta nuna masa tana da kudi da dukiya mai dimbin yawa amma custom sun riƙe, da dai sauran maganganu, sai ta samu ta aure shi daga bisani ya gane cewa ashe ba da gaske ba ne ga shi kuma ya riga ya kama kansa dole ya haƙura, kwadayi ya zama dalilin ƙara aure.
.
Da yawa mazan dake neman yaran masu kudi ba don tsabar sha'awa da soyayyar dake tsakaninsu ba ne kawai, har ma da lissafin cewa in mutum ya auri wance to fa ya warke , na taba jin wata hajiya da wani matashi ya tsaya sai ya aure ta, ba ta ƙi shi ba, sai dai ta gindaya masa wani mummunan sharadi ne na sai ya rabu da matarsa, wato uwar 'ya'yansa, ya jujjuya maganar kuma ya yi shawara da abokai da iyaye a ƙarshe aka tsaya kan ya haƙura kawai tunda iyalinsa ba su yi masa komai ba, abin baƙin ciki ya yarda kan ya haƙura din, sai kuma can daga baya ya sake dawawa ya saki matarsa ya auro ta.
.
Wani abokina na kusa ya taba gaya min cewa ya yi mu'amalla da wata 'yar gabashi, har ya kusa zuwa gidansu sai ta gaya masa cewa ita fa ba sa zama da kishiya. Ya ce to da ma yana da mata biyu. Sai ta ce ai da sauƙi tun da ba su kai 3 ba, kuma za ta iya riƙe yaran gaba ɗaya. Da ya tambaye ta ma'anar maganarta, sai ta ce ya sallami sauran matan kawai ta ishe shi komai! Auren da ba a yi ba kenan, domin ta kai ga uwayen tsohuwar matar sun taka masa burki gami da gaya masa irin matakin da za su ɗauka matuƙar ya saka musu 'ya. Allah ne dai Masani. Wata ƙila ba su ne kaɗai dalilin fasa auren ba.
.
A hadisin Annabi SAW dai mun fahimci cewa dukiyar mace ma kan zama babban dalilin da kan sa mutum ya yi aure, koda yake ba wannan ne shahararre a matattararmu ba amma tabbas yakan faru, wasu kan ƙara aure a dalilin abin hannun mace, ba wai don suna da buƙatar ƙarin auren ba, har ma ka ji abokansa suna masa murna wai ya auna arziƙi, wasu ma sukan yi sha'awar a ce sun sami wannan damar koda kuwa abokansu ba su ji dadin nasu auren ba.

Post a Comment

0 Comments