Kundin Ma’aurata 41: A Taƙaice


    14) Yi ƙoƙari ki san abin da yake so a wurinki, magana ce, ko motsi, ko ado da kwalliya ko abinci ko shimfiɗa. Manta da abin da sauran maza suke so....


    Kundin Ma’aurata 41: A Taƙaice

    Baban Manar Alƙasom
    Zauren Markazus Sunnah
      
    Mun zo ƙarshen abubuwan da za mu fadi a kanki saura na maigida, za mu yi bitar baya a taƙaice don ki yi saurin ganewa.

    1) Ki dauki maigidanki a koda yaushe a matsayin hanyar da za ki kusanci Allah SW.

    2) Kir ki yarda ku kwanta barci kina da matsala da shi ba ki warwareta ba.

    3) Ki dauki girman da Allah SW ya ba shi na jagora a matsayin shari'a ba zalunci ya sa ya ba kansa ba.

    4) In kika sami yana da dan sanyi-sanyi kar ki ce dama kika samu da za ki juya shi, wasa da wuta za ki yi ba ki sani ba, bare har ki je wurin bokaye kan haka.
    .
    5) In kika samu yana ibada ki dage ke ma ki yi, don kina matarsa bai nufin in ya sami aljanna shi kenan ke ma kin samu.

    6) Irin azumin da sauran ibada da yake yi ke ma ki yi, in ma ba ya yi to ki san kowa abin da ya aikata ne zai gani.

    7) In kin ga abin da ba ya so kar ki ce sai ya yi magana sannan za ki bari, wani sa'in yana ganin rashin ladabinki ne.

    8) In ya hana ki aikata wani abu, ki bari yananan ko ba yanan, kar in ya fita ki aikata.

    9) Ki yi haƙuri da yadda Allah ya yi shi tun da har kin aure shi, kudinsa, kyawunsa, iliminsa, ibadarsa da sauransu, haka Allah ya tsaga koda kuwa wasu sun fi shi.
    .
    10) Ki riƙa fadin kyawawan abubuwa ne gare shi, koda kuwa yana aikata munanan, yadda duk in kin fada masa abubuwan da yake yi munana zai san ranki ya baci, kar ki saba da haka sai lokaci-lokaci.

    11) Idan ba ya faɗa don kin tafi wani wuri, kar hakan ya zama dama da duk inda kika so za ki ba tare da izininsa ba, lallai ya san duk inda za ki tafi.

    12) Nisanci abin da zai baƙanta masa rai komai kasawarsa.

    13) Ki kiyaye kudinsa, kar ki taba sai da izininsa, koda kuwa ba zai ce komai ba.

    14) Yi ƙoƙari ki san abin da yake so a wurinki, magana ce, ko motsi, ko ado da kwalliya ko abinci ko shimfiɗa. Manta da abin da sauran maza suke so.
    .
    15) Ki dena yarda yana fadi kina fadi, in ya daga murya ke ki yi shuru.

    16) Ki daina sauraron ya yaba miki wani abu da kika yi masa, koda kwalliya ce ko daddadan abinci, da yawan maza ba sa magana.

    17) In ya yi subul da baka ba kaifi ki nuna masa kuskurensa amma ta hanyar da ta dace, maigidanki ne.

    18) Ki guji yawan fada, maza ba sa son mace haka, ke ma kina son ki zauna lafiya.

    19) In kin yi kuskure fada kawai kin yi, ki ba shi haƙuri, banda gardama, da yawan jayayya.

    20) Kar ki yarda na waje su riƙa sanin sirrorinki, tsirara za su riƙa kallonki ke ba ki sani ba.
    .
    21) Kar ki yarda a riƙa zaginsa a gabanki, ke ce shi, in ba za a yi a gabansa ba to kar a yi a gabanki.

    22) Kar ki riƙa kai ƙararsa wurin uwayensa a kan ƙaramin abu, ki sa ya zama zu ne za su tambaye ki, wani lokacin za su riƙa miki kallon maras haƙuri ba za su gaya miki ba.

    23) Ki nesanci duk abin da zai sa a riƙa shakkun abin da kika yi ko a zarge ki.

    24) In ya talauce, ko rashin lafiya, ko damuwa, dama ce kika samu da za ki nuna masa tsabar ƙaunar da kike masa ba ki guje shi ba.

    25) Ki yi haƙuri da halin da kuka sami kanku ba kullum ake kwana a gado ba.

    26) In ya sami karayar zuciya ki yi ta ƙarfafa masa gwiwa, kar ki yarda ya riƙa jin cewa ya gaza yanzu ba zai iya yi muku komai ba.

    27) Sanya shi ya saba da jin ƙamshin turare, kar ki bari ya riƙa ji a waje kawai.
    .
    28) Ki yi iya ƙoƙarinki ki riƙa tashi gabaninsa, kar ki bari ya tashi yana neman abin karin safe.

    29) Yi ƙoƙari ki tsaya a gabansa lokacin da yake sa kaya, kar ki bari ya fita da mummunar shiga, in bai sa turare ba ko bai shafa mai ba gaya masa.

    30) Kar ki bari ya fita da kaya ba guga, ko yagagge, ko mai datti, ko ya maimaita sama da daya.

    31) Ki ƙauna ci maigidanki sosai, ba wai ki riƙa gaya masa cewa "Ina bala'in ƙaunarka" ba, ya gani ne a aikace.

    32) Ki gamsar da shi cewa tarbiyar da za ki yi wa diyoyinki ta fi wace wani zai ba su.

    33) Ki ba shi kulawa ta masamman, aikinki bai fi shi mahimmanci ba.
    .
    34) Ki nuna masa kina da matuƙar buƙatarsa, ya zama abokin shawararki.

    35) In zai yuwu ki zama mai zaba masa kayan da zai sanya, kar ki bari ya riƙa daukar wanda ya yi masa.

    36) Kar ki yarda ya riƙa dawowa gida ba kyanan.

    37) Kar ki riƙa daura masa abin da ba zai iya yi ba, zai gaza.

    38) Kar ki yi ƙoƙarin tanƙwara shi sai ya dauki dabi'un da kika zabar wa kanki kina so.

    39) Ki nuna masa koda yaushe cewa za ki iya barin komai a dalilinsa.

    40) Ki kiyaye lokutansa, kar ki riƙa ƙirƙiro abubuwa a lokutan da kika san ba zai iya yi ba, kar abincinki ya riƙa shiga lokutansa, kuma ki matsa sai ya ci.
    .
    41) Duk kayan da ya shigo da su kamar takardu, littafai da sauransu, kar ki canza musu wuri yadda ba zai gani ba, amma ki adana su saboda yara.

    42) Ki dan riƙa nuna damuwa a abubuwan da suka dame shi, ki taimaka masa da abin da za ki iya, koda ke ba ki damu ba, misali in an ci Nigeria bal, ke ma ki yi ta tsaki in mai son ƙwallo ne, zai riƙa ba ki labari har ya manta zafin cin.

    43) In ya shigo gida ki bar duk abin da kike yi ki tarbo shi, koda kuwa kina magana da mahaifiyarki ne, ki yi zumbur ki ba ta haƙuri ki je a guje, ita ma za ta ji dadi.

    44) Ki tarbe shi cikin fara'a da murna, ki amshe in zai iya ba ki kayan.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.