Ticker

6/recent/ticker-posts

Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar LabɗoAsalin Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci. A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa bayi, don haka a ƙasarsu aka fara yaga wasiƙar Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’ suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar Karbala abin kula ne.
Kakkaɓan Gara Ga: “Laccar Makirce-Makircen Shi’a Ta Farfesa Umar Labɗo

Aliyu Muhammad Bunza
Professor of African Culture (Hausa)
Faculty of Humanities and Education
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
Zamfara State
Tel: 0803 431 6508

Gabatarwa:
Kasancewar addinin Musulunci na ƙashe daga cikin saukakkin addinai na Allah, dole ya ci karo da wasu matsaloli na har abada. Dalilan da suka haddasa haka kuwa su ne; mai saukar da addinai (Allah) Shi Ya saukar da shi a ƙarshe, kuma Ya ce ya rufe addinai da shi. Na biyu, Musulunci ya riski addinan gargajiya masu ƙarfi da suka mamaye duniyar zamaninsu, irin su Farisa, Rum, Indiya, Makka, Sin, da duniyar baƙar fata. Tarkacen addinan ba su da littafe daga Allah, Musulunci ya ambace su da sunayen uku: Majusawa, Mushurikai, ko Kafirai. Masu saukakkin addinai idan suka bijire suna iya ɗaukar biyu daga cikin sunayen uku, wato ko dai Mushurikanci ko Kafirci. Ga alama, ta wannan hanyar Yahudu da Nasara suka kutso cikin Musulunci a makirce, suka haddasa ƙungiyoyi da aƙidoji da ɗariƙu da ke tarwatsa kan Musulmai da nisanta su ga sahihin tafarki. A tunanin wannan tattaunawa, ‘Ƙungiyar Shi’a’ na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da aka shaƙa wa wannan guba.

Mece Ce Shi’a? Wane Ne Ɗan Shi’a?
Bai kamata a ari bakin mutum a ci masa albasa ba, don haka, waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ɗaya daga cikin manyan Shehunan Shi’awa Muhammad bn An-Nu’man (Al-Mufeed) ya ce Shi’awa su ne:
Mabiya Ali (RTA) da suka yi masa mubayi’a, suka yarda da Khalifancinsa bayan Manzon Allah (SAW) kai tsaye babu wasuɗa tsakaninsa da Annabi (SAW); kuma suka ƙi khalifancin duk waɗanda suka gabace shi ga gadon Khalifanci, tare da imanin cewa; Ali (RTA) ya bi khalifofin da suka gabace shi a bayyane ba tare da biyayya ga cancantar khalifancinsu ba.[1]

A wannan riwayar ta babban shaihin Shi’a, za mu ce, ɗan Shi’a shi ne:
i.                   Wanda bai yarda da khalifancin Sayyidina Abubakar, Umar da Usman (RTA) ba.
ii.                 Wanda bai yarda da duk wani shugaba na Musulunci ba in ba ta hannun Ali (RTA) ya biyo ba.
iii.              Wannan aƙidar ita ce “Shi’a” wanda ya yi imani da ita shi ne “ɗan Shi’a”.

Tarihin Shi’a A Musulunce:
Masana tarihin Musulunci sun daɗa juna sani a kan tarihin Shi’a, musamman a kan madugun tafiyarta. Abdullahi bn Saba’ Bayahude shi ya assasa Shi’a, kuma malaman Shi’a sun ce, shi ya fara sunsuno Khalifanci Ali (RTA) da takale-takalen yi masa mubayi’a (tun gabanin su Abubakar, Umar da Usman (RTA). Abdullahi bn Saba’ shi ya fara cewa, Ali (RTA) Allah ne. A lokacin da yana addinin Yahudu shi ne ya fara cewa Yusha’ bn Nuh Allah ne. Ali (RTA) ya hukunta shi da kisa[2] a kan gagarumin kafircinsa na ce wa Ali (RTA) Allah. A taƙaice, za mu ce, tarihin Shi’a shi ne:
Ƙungiyar da Yahudawa suka assasa a cikin addinin Musulunci a makirce, da sunan goyon bayan wani gwarzo daga cikin gwarazan Musulunci Ali (RTA). Hukunta Abdullah bn Saba’ da kisa da Ali (RTA) ya yi, ya tabbatar da barrantar Ali (RTA) da dukkanin Sahabbansa a kan wannan aƙida.

Bazuwar Shi’a A Duniyar Musulunci:
Asalin Shi’a daga Yahudu ne, makamashin wutarta na asali ƙabilanci. A tarihance, mutanen Farisa sun ɗauki Larabawa bayi, don haka a ƙasarsu aka fara yaga wasiƙar Annabi (SAW). Babban takobin yaɗa Shi’a shi ne siyasa, a shiga rigarta a yi tashintashina da ta’addanci. Abubuwan da su Abdullahi bn Saba’ suka haddasa tsakanin Ali (RTA) da A’isha (RTA) da Mu’awiyya (RTA) da musibar Karbala abin kula ne. Tun a wancan lokaci jama’arsu suke hijira ƙasashen daban-daban, yau ana samunsu a Jordan, Syria, Yemen, Iran, Iraƙ, Baharain, Pakistan, India, Lebanon, Kuwait, Afghanistan, da Afirka musamman Nijeriya ta Arewa). A Nijeriya ta Arewa, sun fi mamaye Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi, Sokoto, da ‘yan ƙwarori a Kabi da Zamfara.[3]

Fuskokin Shi’a A Nijeriya Ta Arewa:
A tarihance, Shi’a ta yi amfani da wasu manyan fuskoki da za su sa a kalle ta da idon basira. Shi’a ta mamayi matasan Arewa ta fuskar boko bayan juyin-juya halin Iran na 1979. ‘Yan boko suka riƙa tallarta da sunan Musulunci da jihadi. Daga nan, jaridu da mujallun Iran, musamman Mahjuba, Echo of Islam, Digest, d.s. ana raba su kyauta ana turo wa yara ‘yan makaranta kyauta. Wannan dasisar ta ci Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai (MSS). Da haka wasu suka samu damar zuwa Iran karatu, aka buɗa Sashen Hausa a gidan Rediyon Ƙum. Wannan ta buɗe wata fuska ta tarukan wa’azi da laccoci wanda ya haifar da fassara wasu mujallu da littattafan Shi’a cikin harshen Hausa. Daga cikin littattafan da suka yaudari matasa akwai Shi’a da Aƙidojinta na wani mutumin Ghana wanda ya zaman sanadiyayr buɗa Masallacin Jumu’a na Shi’a na Legas. Na biyu, shi ne littafin Muhimman Fatawowi a kan Muhimman Matsaloli na Muhammadu Isa Talata Mafara, wanda ya nuna Shi’a Mazhaba ce daga cikin Mazhabobin Musulunci. Wannan littafi shi ne yaudara ta ƙarshe da aka yi wa ‘yan boko Musulmi da matasan Sakkwato, kuma shi ne sanadin ɗaure wa zagin Sahabban Annabi (SAW) gindi a Sakkwato da Kabi da Zamfara (Allah Ya kiyaye mu).[4]

Dasisar Laɓewa Ga Jihadi Da Yaƙi Da Yahudu Da Nasara:
Shi’a ta bayyana a Nijeriya bayan da tsarin mulkin Turawan Ingila na Kafirci ya kafa tuta a Nijeriya. Yaƙin da Khumaini ya yi a 1979 da ‘yan barandar Amurka, har aka tumɓuke gwamnatin Shaa, ya zama wani furen kallo ga matasan Arewa, aka mayar da hoton Khumaini wani Dala’ilul Khairati a gidaje, da motoci, da gaban riga da rawunna. Masu wannan alamomi su ne mujahidai, akasinsu a ce musu magoya bayan Yahudu da Nasara. Hulɗar ta ƙasaita har ta kai ‘yan Nijeriya zuwa Iran domin bukin ranar jihadinsu. Daga cikin waɗanda suka halarci bukin akwai: Ibrahim Yakubu El-Zakzaky, Bashir Aliyu Umar, Ibrahim Bello, Abubakar Jibril, Abubakar Tureta, Muhamamdu Isa Talata Mafara, Turi Hamza Lawal, Husaini Abubakar, Nuhu Yahya, Yakubu Yahya, Mannir Lawal Rimi, Nuhu Rimi.[5] A lokacin an ɗauka Khumaini da Kafirai yake yaƙi, don haka, dole a manta da duk wani bambancin Shi’a da Sunna a mara masa baya. A cikin wannan tafiyar, abu biyu suka faru masu razana Musulmi daga bakin Jagoran tafiyar Ayatullah Khumaini:
1.     Na farko, da aka kai masa ziyara, ya ji sunan Abubakar Jibril da Abubakar Tureta, ya ce, a gaya musu su gaggauta sauya sunan zuwa wani (domin ba su da sunan ƙwari).[6] Tun lokacin, Abubakar Jibril da Abubakar Tureta, suka gaya wa abokan tafiya, ba ta da sauran gyara, mai neman beli ya mari uwar alƙali. Anya Musulmin ƙwari na ƙyamar Abubakar?
2.     Na biyu, a shekarar da Khumaini ya karvi gayyatar Musulman Afirka ta Kudu. Da aka tarbe shi a filin jirgi, a jawabinsa na babban baƙo ya buɗa da cewa:
Idan na samu nasarar shiga Makka da Madina a matsayin mai cin su da yaƙi. Abu na farko da zan yi shi ne, in tone gumaka biyu da ke raɓe ga kabarin Manzo (SAW) Abubakar da Umar, ya tsine musu.
(Truth about Shi’ism, coɓer page)[7]

Tun a filin jirgi aka rabu dutse hannun riga. Musuluman Afirka ta Kudu suka ce ba su da rumfar da za a zagi Sahabban Annabi (SAW) a ƙasarsu.

Makirce-makircen Rusa Musulunci A Arewa:
Bayyanar gwagwarmayar Shi’a a Nijeriya ta Arewa daga 1979-2019, yau kimanin shekara arba’in (40) za mu fahimci waɗannan abubuwa:
1.     Cikin dasisa Shi’a ta kame matasan Arewa maza da mata aka dinga amfani da su wajen rusa Musulunci da Musulmai domin a idar da ayyukan da Turawan Ingila da ƙungiyoyin leƙen asiri ba su idar ba. Yaya muke ciki a yau? Me ya raba mu da Chechnya da Karbala da Afghanistan da Iraƙ da Libya? An mayar da tashintashina addini, mutuwa ciki shahada. Ina sauran zaman lafiya?
2.     A shekakarar 1979-1980 Shi’a ta fara sunsuna wa matasanmu Boko Haram da zanga-zanga. Matasanmu haziƙai suka fice daga makarantu wasu suka yayyaga takardun kammala karatunsu. Zanga-zangar Shi’a ta farko a Sakkawato aka yi ta a shekarar 1979. Tun wancan lokaci aka yaudari matasanmu aka saka su fitina har ya zuwa yau. Wasu sun mutu a kaso/kurkuku, waɗanda suka fito sun zama ƙwararrun ‘yan ta’adda. Har yanzu ba ta sauya ba.
3.     An dasa wa matasa mummunar tarbiyya ta ta’addanci na kisan kai a wuraren bauta da wuraren gudanar da karatu. Mun shaidi wannan a Kano kan kisan Shaikh Jafar, da Sakkwato, kisan Malam Umar ɗan Maishiya, da Kaduna, kisan Shaikh Albani. Wane malami ya yi tasirin Shaikh Jafar a Kano? A Kaduna, wa ya kai Shaikh Albani matasa? A Sakkwato, wace da’awa ta fi ta Umar ɗan Maishiya razana Shi’a? Duk wani masanin da za a fahimci Shi’a a karatunsa a ilmance, ba za su bar shi ba.[8]
4.     Daga cikin manyan dasisar Shi’a akwai rusa karatun zaure/soro/allo. Shi’a ba ta zo da karatu ba. Lacca da karatun mujallu da farfagandar siyasar duniya ta zo da su. Galibin jagororinsu ba su iya karatu ba, balle su san darajarsa da ƙimarsa. Matasan da aka jawo ta fuskar laccoci, laccocin ne makarantarsu ta farko. Da wannan dasisar, nagartattun makarantunmu na ilmi suka durƙushe. Dalili kuwa shi ne, matasa na wajen gudanar da zanga-zanga, manyan malamai na tsufa suna mutuwa; majiya ƙarfi na wajen ƙwadago da kasuwanci da aikin gwamnati. An yi ɓatan ɓakatantan ba a ga tsuntsu ba a ga tarko. Allah Ya isa!
5.     Daga cikin dalilan yaƙar Turawan mulkin mallaka a Nijeriya ta Arewa akwai tsoron gurɓata tarbiyar mata. A kowace ƙasa aka cire wa mata kunya, babu sauran zaman lafiya. Ƙasar da duk shegu suke da rinjaye, da ita da maƙabarta zozo-zozo suke. Tsarin salon ilmin Bature na cakuɗa maza da mata wuri ɗaya, ya rusa kunya a idon matanmu. A tsarin Shi’a, wannan ba komai ba ne. Budare da matan aure ke jerin gwanon zanga-zanga da bukin maulidi, da lacca da kallon finafinai da fita daga garin da ake zuwa wani gari na daban na tsawon kwanaki ba tare da kulawa da wane ne muharrami, wane ne ba shi ba? Cikin wannan yaudarar aka tallata musu auren mutu’a,[9] aka mutu gaba ɗaya. Matashi da matashiyar da ta saba da auren mutu’a ba ƙaramin kira ke sa su waiwayo ba.
6.     Bisa kyakkyawan zato, ba shauƙin wa’azi kawai ya juyar da hankulan matasanmu suka fantsama cikin wannan fitina ba. A kwana rawan atisaye, a yi tafiyar fanfalaƙi mai tsawo, a ɗauki makami a kashe mai salla, dole da lauje cikin naɗi. Babu wai, an sa matasa shan miyagun ƙwayoyi, wanda yake wani tsari ne na musamman da duniyar yau ta shirya domin rusa Nijeriya ta Arewa, wadda ake jin ita ce ta ɗaya a duniyar addinin Musulunci.[10]


Babbar Magana:
Ina kyautata zaton kashi 75% a cikin 100% daga cikin masu da’awar aƙidar Shi’a a Nijeriya ta Arewa da cewa ba su san Shi’a ba ta yarda da Alƙur’ani ba; ba ta yarda da Manzon Wahayi Jibril (AS) ba; ba ta yarda da wanda aka yi wa wahayin ba (Manzon Allah SAW). Wannan makircin na ilmi ne kuma a ɓoye yake cikin littattafan manyan shehunan Shi’a na duniya. Shehin Shi’a Abdullahi Shubbar ya ce: “Ƙur’anin da aka saukar wa Annabi (SAW) ya fi wanda ke a hannunmu a yau. Na hannunmu akwai maguɗi a ciki…”[11] Don haka, Shehunsu Al-Kalbi ya ce: “Ƙur’anin da Jibirilu ya saukar ga Annabi (SAW) ayoyinsa dubu goma sha bakwai ne (17,000).”[12] Shi’awa sun tabbatar da cewa ba ga Annabi Muhammad (SAW) aka aiko Mala’ika Jibril (AS) ba, ga Ali (RTA) aka turo shi da wahayi, ya yi kure, ya kai ga Annabi Muhammad (SAW). Don haka, a tafsirinsu Tafseer Al-Ƙur’an na Shaikh Jabir bn Yazeed bin Al-Haarith Al-Ja’fi Al-Kufi (ya rasu 127AH) suka kafirtar da Sahabban Annabi (SAW).[13] Idan Alƙur’aninmu ba cikakke ba ne, Manzonmu ba shi aka nufa da wahayi ba, kure Mala’ika Jibril (AS) ya yi, Sahabban Annabinmu (RTA) riddaddu ne ko kafirai, ina sauran Musulunci a bangon ƙasa? Gudun leƙo waɗannan abubuwa, Shi’a ta fito da dasisar ba kowa ya kamata ya yi karatu ba, muradi dai shiga Aljanna, don haka, a bar wa Shehunnai karatu, muridai su bi ido rufe ba tambaya. Anya! Shi’a ba wani addini ba ne?

Ina Mafita?
Matsalar da muke ciki a yau, ba ta muƙabala ba ce, ba ta faɗa ba ce, ba ta sa-in-sa da Shi’awa ba ce. Ruwa sun kawo a wuya, aiki ya yi wa kurege yawa. Ya kamata a ce, mun mayar da hankalinmu ga muhimman abubuwa da suka haɗa da:
1.     Bin hanyoyin farfaɗo da nagaratar karatun allo da rayar da karatun zaure da faɗaɗa shi. Gabanin yaranmu su buɗe ido da komai, su tashi da aƙidarmu a ilmance.[14]
2.     Mu inganta makarantun Islamiyya tare da gwama su da nagartaccen karatun boko, yaranmu su tashi wayayyi, yadda duniya duk ta juya suna kallon ta sara.
3.     Mu yayyafa wa wutar ƙungiyanci da ɗariƙanci da mazhabanci da ɓangaranci ruwa. Mu riƙa sara muna duban bakin gatari, yadda fahimtarmu take, da kowa haka take, da an daɗe da cigaba. Mu dai sa hikima ko ba a yarda da mu ba, mu samu ladar wa’azi.
4.     Yadda ƙasarmu take ciki yanzu, babban makami ga ahlil Sunnah, da malaman sunnah, shi ne a rage kwaɗayi, da son abin duniya ido rufe. A ƙaurace wa fadanci da bambaɗanci cikin da’awa. A nisanci miyagun kalamai da tonon silili da amayo kalmomi masu haƙorin cizo ga saɓanin da bai taka kara ya karya ba.
5.     Masu da’awar sunnah dole su cire rowa a zukatansu. Wajibi ne a nisanci makabtattar hasada. Tilas a yi jifa da son girma da biɗar a sani da bugun gaba da zaƙewa. Zaman jiran afafa (banza) da zakka da sadaka, ba na ‘yan sunna ba ne. Dole mu tanadi wasu hanyoyin da za mu ƙarfafa ma’abota sunna ka da bidi’a da shirka su farauto su ba da saninsu ba.

Naɗewa:
Akwai buƙatar mu sani cewa da’awar Shi’a a Arewa ta sa mun yi hasarar matasa a ma’aikatun tsaro da likitoci da injiniyoyi da ‘yan jarida da fannonin aikin hukuma da dama. Wajibi ne mu ƙarfafa yaranmu su shiga ayyukan tsaron ƙasarmu gadan-gadan. Ba mu da ƙasa bayanta, ba mu kore kowa a ciki daga cikin ‘ya’yanta, ba wanda ya isa ya kore mu. Saboda haka, tashi tsaye mu kare ta da karatunmu da makamanmu wajibi ne. Lokacin abu a yi shi, ka da mu ja baya ga zaɓen shekarar 2019, ka da mu yarda a saye ‘yancinmu zaman lafiya ya gagare mu. Mu zavi mai ƙaunarmu, mai ƙaunar ƙasarmu, mai kare mutuncinmu da na ƙasarmu. Ka da mu yarda a yi amfani da mu a yi maguɗi ko a tada fitina. Ku tuna, fitina ba ta taɓa rutsawa da manya ko ‘ya’yansu ba, sai dai mu talakawa. A karantarwar Musulunci, babu fitinar da ke da sahihin nassi.


[1] Shaikh Al-Mufeed, Awaa’il al Muƙaalat fee Almadhaahib al-Mukhtaarah, shafi na 35.
[2] Ahasan bn Musa An-Nubukhti, Firaƙ As-Shee’ah, shafi na 50.
[3] Suraj, A. D. “Historical Deɓelopment of Shi’ah, Its Activities and Implication to Muslims in Northern-West Nigeria”, PhD Thesis, 2012, p. 96-97.
[4] Marubucin wannan littafi yana raye, kuma ya gabatar da shi ga Shaikh Abubakar Mahmud Gummi domin ya yi masa ta’aliƙi, marigayi ya ƙi, ya kuma yi masa nasiha. Ya san haɗarin da ke ciki, kuma har yanzu bai musanta abin da alƙalaminsa ya tabbatar ba. Na samu wannan bayani daga Mal. Aminu Salihu Gummi, lokacin da na kai wa marigayi ziyara a gidansa na tarar da littafin na Muhammadu Isa Talata Mafara ajiye kan teburin Shaikh Gummi. Wannan littafin ya mamayi ‘yan boko da yawa suka shiga Shi’a, wasu suka ba ta goyon baya. Shiga sahun masu zagin Sahabbai da goyon bayan masu yi, duk abu ɗaya ne mai hukunci ɗaya. Allah Ya kiyashe mu. Amin.
[5] Duba lamba ta 3, shafi na 97.
[6] Shaikh Abubakar Jibril ya yi wannan bayani a huɗubar Masallacin Farfaru wajajen shekarar 1990. Shaikh Abubakar Tureta ya tabbatar da zancen a Masallacin Bello a Sokoto (1990?).
[7] An turo wannan littafi a ɗakin karatu na CIS, UDUS, 1988, na fassara shi zuwa Hausa, ban samu wallafa shi ba.
[8] Idan aka lura, waɗannan shaihunai da aka kashe bas a tu’assibanci da taƙalidanci ga kowace ƙungiya ko ɗariƙa. Zunzurutun karatunsu ake tsoro ya samu karɓuwa a samu kafa gwamnatin da Shi’a ba za ta samu sakewa ba. Allah Ya isa!
[9] Game da auren mutu’a, Imam Khumaini ya faɗa a littafinsa Tahrir al Wasiilah, (shafi na 112). Ya halatta a yi auren ɗanɗana (mutu’a) tare da mace mazinaciya, amma a ƙi shi a zuci, musamman idan an shaidi fitacciyar karuwa ce. Idan mutum ya yi auren mutu’a da ita ya gaya mata ta daina zina. Hmn! Hausawa sun ce ba ta mutu ba ta ɓalgace.
[10] A rahoton BBC na shekarar 2015 an ce Nijeriya ta fi kowace ƙasa a duniya ga rungumar Musulunci gadan-gadan ta tsayar da shi a aikace. A Nijeriyar ma a Arewa aka ce, abin ya tabbata. Don haka, maƙiya suka biyo mu da dasisar safarar ƙwayoyi ana haukata matasanmu. A halin da ake ciki, Kano da Katsina da Sokoto da Kaduna nan ake jinge Tramol da Babba Juji (Cocaine), da Tabar Wui-wui. Ana bai wa ‘ya’yanmu da sunan zikiri da wuridi da jihadi a ƙwazon aiki da ƙarfin jiki, daga nan sai a haukace.
[11] Almaazandiri, Mir’at Al-Uƙool fee Sharh Akhbaar Ar-Rasool, Juzu’i na 13, Shafi na 525.
[12] Usool Al-Kaaf, Juzu’i na 2, Shafi na 826.
[13] Abdulrahman bn Sa’ad bn Ali, Doctrines of the Twelɓe Shiite (Enƙuiry and Response), p. 33.
[14] Abin kunya ne Musulmi suna kallo ana ba kalmar ‘Almajiri’ fassarar son kai ta cin zarafi da cin irlin Musulmi da Musulunci. Dole mu tashi tsaye mu ga yadda za mu magance matsalolinmu da kanmu.

Post a Comment

0 Comments