Wata itaciya ce da ake shukawa ko dasawa a gida ko gona, wadda ake tsigar ganyenta ana dafawa a kwaɗanta a ci ko a yi dambu ko fate ko a yi miya da shi. Haka kuma akan yi danga da itaciyarta. Tana da furanni farare.Ana kuma yin yaji da saiwarta (Garba, 1990:167).Ita zogale matsakaiciyar itaciya ce, wadda girmanta ya kama daga tsawon mita biyar (5) zuwa mita goma (10). Saboda yawan amfanin da ake da ita ya wanzar da nomanta a duk kusan sassan duniya. Ana samun ta a yammacin duniyada ƙasashen Asiya musamman a  yankunan tsaunukan Himalaya da ƙasashen Indiya da Pakistan da Afirika da kuma ƙasashen Larabawa.     
                                            Dr. Adamu Rabi’u Bakura

1.0 Zogale

          Wata itaciya ce da ake shukawa ko dasawa a gida ko gona, wadda ake tsigar ganyenta ana dafawa a kwaɗanta a ci ko a yi dambu ko fate ko a yi miya da shi. Haka kuma akan yi danga da itaciyarta. Tana da furanni farare.Ana kuma yin yaji da saiwarta (Garba, 1990:167).Ita zogale matsakaiciyar itaciya ce, wadda girmanta ya kama daga tsawon mita biyar (5) zuwa mita goma (10). Saboda yawan amfanin da ake da ita ya wanzar da nomanta a duk kusan sassan duniya. Ana samun ta a yammacin duniyada ƙasashen Asiya musamman a  yankunan tsaunukan Himalaya da ƙasashen Indiya da Pakistan da Afirika da kuma ƙasashen Larabawa.
            Al’ummomi daban-daban kamar Romawa da Girkawa da Misirawa kan tatso mai daga ‘ya’yan zogale wanda sukan sarrafa shi wajen aiwatar da turare da man shafawa. A cikin ƙarni na goma sha tara (19), gandayen zogale da ke Yammacin Indiya sun fitar da man zogale zuwa ƙasar Turai domin yin turare da giris na na’urori.
            Al’ummomin ɓangaren ƙasar Indiya sun daɗe suna amfani da kwasfan zogale wajen abinci. Shi kuwa ganyen zogale ya kasance wani muhimmin abu da ake ci a duk farfajiyar ƙasashen Afirika ta Yamma da wasu sassan Asiya.Abin ƙayatarwa ne ƙwarai dangane da jerin nau’o’in magungunan da ake yi da zogale waɗanda ke ƙunshe da muhimman sinadarin gina jikin ɗan-Adam. Sakamakon amfanin da ake yawan yi da ita ne ya sa aka gano tana maganin cuwurwuta da dama. Wannan ne ya haifar da mayar da hankali wajen binciken irin cutar da take magani.

1.1 Zogale A Farfajiyar Ƙasar Hausa

            A farfajiyar ƙasar Hausa akan kira ta da sunaye dabam-daban. Wasu yankunan na kiran ta zogalagandi ko zogale ko kuma tamakka. A wani yanki na ƙasar Zamfara kuwa, kamar Bunguɗu da Maru suna yi mata  laƙabi da ɗanhaki. Yayin da  ake kiran ta dakable a yammacin ƙasar Gummi. A ƙasar  Ruwan Ɗoruwa da kewayenta ana kiran ta ‘yarmakka. A yankin ƙasar Nijar kuwa akan kira ta da sunan bagaruwar makka.
            Ana kyautata zaton wannan itaciyar ta zo ƙasar Hausa ne ta hannun mahajjata, kamar yadda sunayen da aka yi mata a ƙasar Hausa da ƙasar Nijar suka yi ishara. A wani hasashen kuwa, zogale ta zo ƙasar Hausa ne daga Misira. Tarihi ya nuna, ƙasar Masar na daga cikin ƙas ashen da aka fara kai zogale daga Indiya. Misirawa sun daɗe ƙwarai suna amfani da zogale wajen magungunansu na gargajiya, musammam ma maida ake samu daga ‘ya’yan zogale wanda aka ce Misirawa na shafa shi a fatar jiki don kariya daga illar da iskar Hamada ke yi wa fatar jiki.
            A ra’ayin Hambali Junju, Hausa ta samo asali ne daga Misira. To idan muka ɗauki wannan ra’ayin za a iya cewa, ke nan koda Hausawa suka zo ƙasar Hausa, sun zo ne tare da abarsu. Ai ko banza masara ma daga Misira ta zo ƙasar Hausa. Saboda haka baabin mamaki ba ne idan aka ce zogale daga can ta zo. Sai dai ba wani mahaluƙi da zai fito fili yace ga ƙayyadadden lokacin da ta zo ƙasar Hausa da kuma wanda ya fara shigowa da ita, sanin wannan sai Allah.

1.2 Asalin Zogale:

            Masana da dama kamar (Nickon & others, 2003) da (Ndong,2007) da (Agrawal & others, 2008) da (Busani & others, 2012) sun nuna cewa, zogale tun can asalatan itaciyar ƙasar Kudancin Indiya ce,  wato ƙasar Sirilanka. In kuwa haka ne, za mu iya cewa, Allah cikin ikonSa da hikimarSa da iradarSa, Ya samar da zogale a can ne domin  Annabi Adamu da zuriyarsa na farko su sami abin yin riga-kafi da maganin cututtuka da ita. Musamman idan aka yi la’akari da irin sinadiran ban mamaki da ta’ajibi waɗanda Allah Ya halicce ta da su, da ke da muhimmanci a cikin jikin ɗan-Adam, ta fuskar waraka da garkuwa daga wasu nau’o’in cuwurwuta da kan addabi jiki. Masana tarihi sun nuna an saukar da Annabi Adamu (A.S.) a farfajiyar ƙasa da ke yankin Sirilanka, yayin da Matarsa Hauwa”u aka saukar da ita a Jidda. In kuwa haka lamarin yake, za mu iya cewa, zogale na ɗaya daga cikin itatuwan Aljanna. Musammam idan muka yi la’akari da irin ɗinbin sinadiran da take kunshe da su, da kuma yadda take maganin cututtuka fiye da ɗari uku (300) tun ƙarnukan da suka shuɗe kamar yadda za a gani nan gaba. Sai dai sanin gaskiyar lamarin yana wajen Allah.
            Wata hujjar da ke tabbatar da hasashen itace,  za a tarar cewa, itaciyar zogale ta sha bamban da sauran itatuwa ta hanyoyi da dama. Da farko dai takan tsiro (toho) a lokacin rani da damina, muddun tana samun danshin sanyi. Haka kuma tsananin fari da sara bai haddasa ta mutu, sai ko in har an haƙe saiwarta gaba ɗaya. Bakamar wasu itatuwan ba. Abu na biyu da ya bambanta ta da sauran itatuwa shi ne tana rayuwa a ƙasashe masu tsananin zafi da matsakaita da masu danshi da ni’ima, har ma a cikin yankunan rairayi.

2.1 Bayyanar Cuta Da Magani A Tsakanin Al’umma

            Allah Buwayi Gagara Misali, Shi ne cikin IkonSa da IradarSa Ya halicci halittu masu rai da marasa rai, na ruwa da na tudu. Waɗanda ake iya gani da waɗanda ba a iya gani, kamar Mala’iku da Rauhanai da Aljannu da mutane da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da tsirrai da duwatsu. Ya kuma halicci ɗan-Adam Ya sanya ƙasa ta kasance mazauninsa a sassa daban-daban na doron duniya.Ya ƙagi cututtuka masu ɗinbin yawa tare da sanadin wanzuwar su a tsakanin al’umma.  Ya sanya magani ga kowace cuta, sai fa tsufa da mutuwa. Mai Tsira da Amincin Allah na cewa:
“Kowace cuta tana da magani. Idan aka yi amfani da maganin da
Ya dace, sai cutar ta kau (a warke) da izinin Allah (Abual Rub, 2003: 25).”
Manzon Allah  (S. A. W.) ya ce:
“Allah bai saukar da cuta ba, face sai da ya saukar da maganinta.”
Buhari da Muslim suka ruwaito wannan Hadisin, kamar yadda Abual Rub (2003:25) ya zo da shi.
An ruwaito cewa, Usamah bin Shuraik ya ce: “ Wata rana ina zaune tare da
Annabi (S.A.W.) wani Balaraben ƙauye ya ce: “ Ya Manzon Allah, ko zan
Nemi magani? Manzon Allah ya ce, E” ya kai Bawan Allah, nemi magani,
Lallai Allah bai ƙaga cuta ba face sai da ya samar da maganinta, sai cuta ɗaya.”
Sai Sahabbai suka tambaye shi, wace cutace? Sai ya ce: “Tsufa”.
Imam Ahmad ya ruwaito shi kamar yadda Abal-Rub (2003:26) ya nuna. A wata ruwayar cewa aka yi, Manzon Allah S.A.W. ya ce:
“Lallai Allah bai saukar da cutaba, sai da ya saukar da  maganinta. Duk wanda ya san maganin
Cuta, ya san shi.Wanda bai sani ba, bai san shi ba (maganin). Waɗanda suka jahilce shi, ba
Su san maganin ba.”
Nisa”i da Ibn Majah da Hakimu da Ibn Hibban suka ruwaito, kamar yadda Abual-Rub (2003:25) ya nuna.
            Waɗannan hadisai suna tabbatar mana cewa, dukkan cuta tana da magani, sai dai idan al’ummar da ke fama da cutar basu fahimce ta ba ko kuma ba su san maganin ba.

2.0 CUTA DA RABE-RABENTA

            Zai fi dacewa a kawo bayanai game da ma’anar Kalmar cuta kafin a zo da bayanai a kan rabe-raben cuta. Saboda yin haka zai ba mai karatu damar fahimtar inda aka sagaba a cikin sauƙi.

2.1 Ma’anar Cuta

            Kalmar cuta tana cikin jerin kalmomin jinsin mata, jam’i kuwa “cututtuka”, a wani Karin harshe a ce cuce-cuce. Kalmar na ɗauke da ma’ana iri biyu. Ma’anar zamba ko rashin gaskiya (Kano, 2006:81).
Adamu (1998:4) ya bayyana ma’anar cuta da cewa: “Wani nau’i ne na rauni da raɗaɗI tare da wahala da kan sami mutum a sakamakon kasawar wata halittar jiki ko damuwar zuci.”
Bunza (1989:132) ya bayyana ma’anar cuta da cewa: “ Cuta wata damuwa ce da ta shiga jikin ɗan Adam don raunana lafiyarsa. Ko kuma ta shafi zuciyarsa ta fuskar buƙatocinsa na jin daɗI ko ɗaukaka darajarsa da sunansa”.
            Ita duniya zaman ‘yan marina ce, don haka ne muke kallon  cuta a wata damuwa ko illa da ke  shiga cikin jikin mutun ta raunana masa wasu ƙwayoyin halitta da ke zama garkuwa a jikin ɗan Adam.

2.2 Rabe-Raben Cuta

            Cututtukan da kan kama (sami) ɗan-Adam iri biyu ne, kamar yadda Abual-Rub (2003) ya zo da su kamar haka:
1.      Cututtukan Sarari
2.      Cututtukan Ɓoye

2.2.1 Cututtukan Sarari

            Cututtuka ne da kan kama jiki saboda wata ƙwayar halittar jikin ɗan-Adam aikinta yayi rauni ko kuma ta daina aiki gaba-ɗaya. Sakamakon shigar wata illa (ƙwayar cuta) cikin jiki ta hanyar ci ko sha ko shaƙar iska ko kuma ta hanyar jima’i. Yayin da wata ƙwayar jikin ɗan-Adam ta kamu da wata illa,  sai jiki ya ɗauki zafi. Wani lokaci ana iya ganin cutar da ido ƙarara ko a fahimce ta. Amma akwai cutar da ba a iya fahimta balle a gan ta ƙarara da ƙwayar ido, sai dai wanda cutar ke addaba kawai ne zai ji jikinsa ya sauya ba ya jin wani sukuni.Wasu lokuttan har ya kasa moriyar komai. Don haka ana iya cewa, cututtukan sarari su ne na jiki, waɗanda ake iya gani da ido ko a taɓa ko a yi bayanin yadda ake ji a jiki tare da magance su kai tsaye.

2.2.1.0Kashe-Kashen Cututtukan Sarari

            Cututtukan Sarari, kamar yadda bayani ya gabata, su ne cututtukan da kan shafi jiki. Irin su nau’I biyu ne kamar haka:

2.2.1.1 Cututtuka Masu Tsayayyen Magani

            Rukunin waɗannan cututtuka, haka Allah ya halicci bayinSa (ɗan-Adam da dabbobi) da su. Kuma kowannen su ya san yadda zai magance su, ba sai ya nemi wani yaba shi magani ba. Cututtukan sun haɗa da: yunwa da ƙishirwa da gajiya da sanyi da sauransu. Ɗan-Adam da dabbobi da sauran halittu masu rai duk sun san yadda za su yi maganinsu da kansu da zarar sun kamu da su ( Abual Rub, 2003:20).

2.2.1.2 Cututtuka Masu Buƙatar Kulawar Mai Magani

            Cututtukan da suka danganci wannan sashe suna buƙatar tunani da binciken yanayin da marar lafiya ke ciki, wanda kan wanzu a sakamakon jin zazzafan zazzaɓI fiye da kima, ko jin sanyi ko bushewar fatar jiki ko kuma haɗuwar dukan alamomin, kafin a gano nau’in cutar, sannan a kai ga magance ta (Abual Rub, 2003:20). Sai dai akwai wasu abubuwa da ba cuta ba ne, amma fa idan aka ƙi gusar da su daga cikin jikin ɗan-Adam sukan zama cuta idan suka yi yawa. Irin waɗannan abubuwa sun haɗa da: maniyyi da maziyyi da fitsari da kashi da tusa da jini da amai da atishawa da hamma da gyatsa da barci da yunwa da kishirwa.Idan ɗayan waɗannan ya wanzu fiye da kima a jiki yakan haifar da cuta, ba za a samu zaman lafiya ba, sai an sami maganin kawar da shi.

2.2.2Cututtukan Ɓoye

            Cututtuka ne na zuciya, waɗanda damuwa da rashin kwanciyar hankali ne da kan samu ɗan-Adam a sakamakon sha’anin rayuwar yau da gobe. Wannan kan sa a wayi gari mutun ya kasance kamar maras lafiya, har sai lokacin da irin wannan yanayin yakau, zai sami lafiya.
            Yayin da irin waɗannan cututtukan zuciya suka taso wa ɗan-Adam, zai kasance cikin yanayi irin na maras lafiyar jiki. Kamar damuwa da rama da rashin bacci. Abubuwan da kan haifar da cututtukan ɓoye sun haɗa da: sha’awa da tsoro da soyayya da hassada da kishi da ƙiyayya kamar yadda (Adamu, 1998:10) da (Abual-Rub, 2003:19) suka nuna.

2.3 Magani: Ma’anarsa Da Asalinsa

            Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar Kalmar magani gwargwadon fahimtarsu. Kano (2006: 316) sun bayyana ma’anar magani da cewa:
“Magani, yana nufin duk wani abu da ake sha ko shafawa ko
Kuma ɗurawa a jiki ta hanyar yin allura, don neman samun
Lafiya ko kariya daga wata cuta”.
Shi kuwa Ahmad (1984) ya bayar da ma’anar magani da cewa:
“Magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya ko
kuma wata dabara da aka yi don gusar da cuta daga jikin
mutum ɗungurumgun ko kuma kwantar da ita don kawo
jin daɗI ga jiki ko ga zuciya da sauƙaƙa duk wata wahala
ga jiki da damuwa da ita cutar kan iya haifarwa”.
Bakandamiyar ma’ana ta magani ita ce wadda Bunza (1989:134) ya bayyana inda yake cewa: :
“Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata
Cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari. Kokuma
Neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka
Ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na 
ban al’ajabi.”

2.3.1 Asalin Magani

            Magani ya samu ne tun bayan da Allah Maɗaukakin Sarki Ya halicci Annabi Adamu A. S. sai  ya sanar da shi dangogin ilmomi masu yawan gaske cikin yardarSa ( Alƙur’ani, 2: 31). Daga cikin ilmomin kuwa har da ilimin cututtuka da yadda za a magance su. Haka ya halitta wasu tsirrai a doron ƙasa domin amfanin Annabi Adam da zuriyarsa. Aka kuma fahimtar da su hanyoyin sarrafa su a matsayin maganin yunwa da na cututtuka.
            Yayin da zamani ya shuɗe, mutane suka ƙara yaɗuwa zuwa sassa daban-daban, sai Allah cikin jinƙanSa da rahamarSa Ya jefa wa ɗan Adam, a ransa, in aka yi amfani da abu-kaza zai yi maganin ciwo kaza da kaza.
            Wasu lokuttan kuma a mafarki za a gayawa  ɗan-Adam, yayi amfani da wani abu don maganin wata cuta. Wani zubin kuwa, murya kawai mutun zai ji kamar daga sama, ana umurtarsa, yayi amfani da abu kaza domin magance cuta kaza.
            Akan kuma sami magani ta hanyar gwaji da kwatantawa, musamman ta la’akari da yadda dabbobi da tsuntsaye ke amfani da’ya’yan itatuwa da hakukuwa da ganyaye yayin da suke cikin yanayin rashin lafiya, da yadda suke nuna halin ko’inkula da su a lokacin da suke cikin ƙoshin lafiya ( Adamu, 2003:10).
            Yaɗuwar al’umma da nuna kyakkyawar biyayya, ya wanzar da ɗorewar mallakar asirran magani daga hannun masana magunguna na haƙiƙa. Kyakkyawar biyayya ta sau- da ƙafa kan sa a sanar da waɗansu daga cikin zuriya ko waɗanda suka yi barance, asirran magungunan da Allah Ya sanar da su. Ta waɗannan hanyoyi ne aka cigaba da gadon asirran magungunan gargajiya a ƙasar Hausa. Kuma ta irin wannan hanyace ilimin sirrin magungunan da zogale keyi ya cigaba da bunƙasa.

2.3.2 Dokar Bayar Da Magani Da Karɓarsa

          Kula da mai ciwo ta hanyar ba shi taimako da magani, lamari ne da ke buƙatar ilimin magunguna da na yanayin cututtukan ɗan-Adam tare da kyakkyawar ƙwarewa. Domin rashin sanin makamar cuta tare da jahiltar maganikan haifar da babbar illa ga maras lafiya fiye da cutar da ke addabarsa. Sakamakon haka kan haifar da salwantar rayuwar marasa lafiya.
            Akan samu wasu jinsin mutane da ke da’awar mallakar ilimin magunguna, har sukan yi kasadar bayar da shi. Alhali kuwa sun jahilce lamari. Ganin irin yadda irin waɗannanmayaudaran mutane ke cutar da al’umma ne, ya sa shara’ar musulunci ta shata dokoki domin samar da kariya ga rayuwar da lafiya da kuma dukiyar al’umma. Masu irin wannan yaudara sukan yi ne domin tara abin duniya kawai ta hanyar zalunci. Manzon Allah (S. A. W.) ya ce:
“Waɗannan da suke yin aikin bayar da magunguna, alhali ba su
mallaki iliminsa ba, alhakin aikinsu yana a kan wuyansu.”
Hakim ya ruwaito shi, kamar yadda Abuai-Rub (2003:124) ya nuna.
A wannan hadisi za a fahimci cewa, duk wanda ya jahilci aikin ba da maganin gargajiya ko na zamani, ya kuma yi kasadar bayar da maganin, zai ɗauki alhakin sakamakon abin da hannayensu suka aikata. Saboda sun gudanar da aikin da bas u mallaki iliminsa ko kuma ba su ƙware a kansa ba, har suka haifar da illa (lahani) ga al’umma, waɗanda suka cutar ta hanyar yaudara. Don haka duk jahilin da yay i kasadar ba da magani, shi zai ɗauki nauyin aikinsa da aikata ga lafiya ko kuma rayuwar al’umma, a haɗuwar malamai. Abin nufi a nan shi ne, idan majinyaci yam utu a sakamakon aikin jahilin mai ba da magani na gargajiya ko na zamani ko wanda bai ƙware ba, biyan diyya ya wajaba a kansa.
            Idan ƙwararren masanin magani y aba marasa lafiya magani, yana cikin halinsa na sani, sai maganin ya wanzar da wata illa, a nan shi ma zai biya diyya. Saboda bai tsaya ya ƙwaƙƙwaran bincike da nazari ba kafin ya bayar da maganin.
            Yayin da maras lafiya ya gabatar da kansa ga wanda ya san shi ba masanin magani ba ne, domin ya magance masa wata cuta da ke addabarsa. Idan har wata illar ta auku ga maras lafiyar, to babu wata diyya da za a ba shi. Saboda shi da kansa ya taimaka wajen halaka kansa.
            Idan kuwa ƙwararren masanin magani, likita ne ko na gargajiya ne wanda ya mallakin izinin gudanar da aikinsa, ya je wurin ƙoƙarin magance wata rashin lafiyar wani ɓangaren jiki, sai ya haddasa wata illa ga wani sashe na daban a sakamakon kuskure. A irin wannan yanayi za a biya diyya ga maras lafiya. Sai dai akwai ra’ayoyi guda biyu na biyan diyyar. Idan mai bayar da maganin ba musulmi ba ne, zai biya daga cikin aljihunsa. Idan musulmi ne, za a biya diyyar daga aljihun baitil malin musulmi (Abuai-Rub,2003:125).

2.3.3 Ababen Da Masu Bayar Da Magani Ya kamata Su Yi

            Wajibi ne mai bayar da maganin gargajiya ko likitan zamani su aiwatar da waɗannan abubuwan kafin sub a maras lafiya magani. Yin haka shi ya fi zama maslaha da kariya gare su da kuma waɗanda Allah ya ɗora musu haƙƙin kula da lafiyarsu. Abubuwan kuwa sun haɗa da:
1.      A binciki nau’I da asalin ciwo.
2.      A gano dalilan da suka haifar da faruwar rashin lafiya.
3.      A binciki maras lafiya bincike mai zurfi domin a gane jikinsa zai iya samar da kariyar ciwon ko cutar ta fi ƙarfinsa. Idan har maras lafiya yana cikin kuzarinsa sosai da sosai har jikinsa na iya yin tsayayya da cutar, a nan ba a buƙatar ba da magani.
4.      A bincikin matuƙar yanayin maras lafiya.
5.      A binciki yanayin sauye-sauyen da maras lafiya ke fuskant.
6.      A gano adadin shekarun maras lafiya.
7.      A binciki ɗabi’unsa da abin da ya saba da shi.
8.      A yi la’akari da sakamakon yanayin da ake ciki.
9.      A yi la’akari da asalin mazaunin maras lafiya.
10.   A duba yanayi da kuma lokacin da mutum ya kamu da rashin lafiya.
11.   A binciko ingantaccen maganin da ya dace wajen warkar da cutar.
12.   A nemo ingantattun hanyoyin da za a yi amfani da maganin da yadda ya dace a sarrafa shi.
13.   Mai bayar da magani bai taƙaita kawai ga magance cut aba, aikinsa ya haɗa da kare aukuwar cutar da fi haɗari a rayuwa.
14.   Zaɓe tare da rubuta magani mafi sauƙi.
15.   A yi kyakkyawan nazari har a gano cutar mai magani ce ko kuwa ba za a iya maganinta ba.
16.   Mai bayar da magani ya kasance ya mallaki ilimin cututtukan zuciya da na rayuwa tare da hanyoyin magance su.
17.   Ya zama mai rangwame da haƙuri ga maras lafiya.
18.   Ya kasance mai amfani da nau’o’in magunguna da waɗanda suka danganci ruhaniyya tare da amfani da tunaninsa.
Rabe- Raben Magani a Bahaushiyar Al’ada
          Kamar yadda aka faɗa a bay akaɗan, magani abu nemai daɗaɗɗen tarihi wanda al’ummomi daban-daban na duniya ke bin hanyoyi mabanbanta domin samar da shi da kuma amfani da shi. Nau’uka ko ire-ire ko rabe-raben magani abu ne da ya ja hankalin masana al’adun Hausawa, kuma sun yi tsokaci a kan wannan batu. Sarkin Gulbi (2014:86) ya kawo rabe-raben magani kamar haka:
i.                    magungunan riga-kafi.
ii.            Magungunan waraka.
iii.          Magungunan cutarwa
iv.           Magungunan biyan buƙata
v.            Magungunan camfi

3.0 Zogale A Fagen Magani

            Zogale, nau’in ice ne wanda Allah Ya tsirar da shi a bias  doron ƙasa domin amfanin mutane da dabbobi da Aljannu. Ita kanta ƙasa ma tana amfana da shi. Wani abin mamaki da ta’ajibi shi ne, irin yadda halittun da ke ruwa suke amfani da saiwar zogale da ke kusa da gulbi ko ƙorama.
,‘Yanmagori da bokaye da sauran wasu daga cikin masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da masunta da makamantan su, duk suna amfani da zogale a gargajiyance domin yin magunguna nau’i-nau’i a farfajiyar ƙasar Hausa da ma wasu sassan Nijeriya.

Rabe-Raben Magungunan Zogale
            Ana iya karkasa magungunan da zogale ke aiwatarwa ta la’akari da yadda al’umma ke sarrafa ta wajen biyan buƙatunsu waɗanda suka danganci rayuwar yau da kullum. Daga cikin irin waɗannan buƙatun akwai:
1.      Waraka.
2.      Kariya Da Buƙatar zuci.
3.      Biyan Buƙatun zuci.


Zogale A Fagen Maganin Waraka
            Zogale na taka muhimmiyar rawa waje kawar da dangogin cuwurwuta da ke addabar jikin ɗan Adam. Irin waɗannan cututtuka nau’I biyu ne. wadda ake iya gani da wadda ba za a iya gani ba, sai dai kawai maras lafiya ya ji wasu alamomi tare da sauyawar yanayin jikinsa. Daga cikin cututtukan da zogale kan yi maganinsu akwai:

Ƙaiƙayin Ido
            A fagen magance ƙaiƙayin ido, sai a nemo ganyen zogale ɗanye, amurtsuke shi, a sami auduga (kaɗa/ tauhwa) ko wani farin ƙyalle mai tsabta. A tsoma cikin ruwan ganyen, a tatsa (matsa) ɗigo uku (3) a idon har sau uku a rana (jinju,1990:19). Shaihin Malamin ya tabbatar da ingancin maganin ta hanyar gwaji shi da kansa.

Ƙaiƙayin Jiki
            Ta fuskar ƙaiƙayin jiki kuwa, sai a samu ɗanyen ganyen zogale cikin tafin hannu uku (3) a daka, a tarfa ruwa kimanin babban cokali huɗu (4). A tace da ƙyalle fari mai kyau. Ruwan ne za a riƙa shafawa a wurin da ke yin ƙaiƙayin. Za a shafa maganin ne sau uku (3) a rana har tsawon kwana bakwai (7) (Jinju, 1990:73). Malamin ya tabbatar da ingancin maganin tare da rashi wani lahani (aibu/cutarwa) a jikin ɗan Adam.

Ƙaiƙayin Al’aura
            Akwai wata cuta da ke addabar mutane musamman mata, inda sukan fuskanci matsalar matsanancin ƙaiƙayi a daidai farji ko dubura. Irin waɗannan mata kan fuskanci matsalar rashin son saduwa da maigida, a sakamakon mummunan ƙaiƙayi bayan jima’i. Sai a sami saƙe-saƙin zogale a dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. Sai a sha kofi ɗaya (1) safe da yamma, ta kuma riƙa yin tsalki da ruwan maganin( hira da Sahabi Kardaji, Gummi). Haka su ma maza masu fama da ƙaiƙayin matsematsi na iya yin amfani da wannan haɗin, don nema samun waraka

Ciwon Ido da Kunne
            Yayin da mutun ke fama da lalurar ciwo ido ko kunne, sai ya ɗebo ɗanyen ganyen zogale. Ya murza, ya matse ruwan ya diga ɗigawa a ido ko a kunne. Insha Allah za a samu lafiya.

Ciwon Kai
            Ga mai fama da lalurar ciwon kai, sai nemi ɗanyen ganyen zogale, ya murtsuka shi ya shafa a goshinsa. Da izinin Allah zai sami waraka.

Ƙurajen jiki
            Idan mutun yana fama da ƙuraje a jikinsa, sai ya nemi garin zogale, ya haɗa da man zaitun ya shafa a jiki. Zai sami waraka insha Allah.
            Idan kuma mutun na fama da kurajen jiki, sai ya nemi garin zogale ya haɗa da man zaitun, ya kwaɓa, sai ya riƙa shafawa  a jiki. Da ikon Allah zai sami waraka.

Ciwon Haƙora
            Shi kuwa wanda ke fama da matsalar ciwon haƙori, sai ya nemo ƙaron ( jirrai/ jillan) zogale, sai ya liƙa a inda ke ciwon (Jinju, 1990:23).

Ciwon Ɗankakkarai
            Ciwo ne da ke shafar yatsan hannu ko na ƙafa. A irin wannan yanayi yatsa kankumbura, ta riƙa ciwo da zogi (raɗaɗi) mai tsananin gaske, har sai wurin ya ja ruwa, wanda ke bayar da damar yin sakiya. Ana amfani da ganyen zogale wajen maganin wannan cuta. Mai fama da wannan lalurar sai ya samo ganyen zogale, ya mutsuka shi, sai a saka kanwa, sai ya kunsa a yatsan da ke ciwo, kamar yadda ake kunsa (ɗaura) lalle. Da izinin Allah, cikin ‘yan kwanaki kaɗan kumburin zai sace ya kuma daina raɗaɗI sai wurin ya ƙafe (bushe).

Harbin Kunama
            Idan kunama ta harbi mutun (Allah Ya tsare), sai a nemo ganyen zogale, sai a murmurza tare da turare sai a saka a daidai wurin da ta yi harbi. In Allah Ya so za ta faɗI ba tare da jinkiri ba.

Ciwon Sanyi
            Mai fama da matsalar sanyi, sai ya nemi ganyen zogale, ya dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. A tace, ya rinƙa shan ruwan moɗa (kofi) ɗaya, sau biyua (2) a rana ga babban mutun. Yaro kuwa ya sha rabin moɗa sau biyu a yini (Jinju,1990:66).
            Haka kuma ana tafasa furen zogale tare da albasa, a rinƙa sha kamar shayi, don magance ciwon sanyi.
            Idan ciwon sanyi ya yi yawa, yakan shafi hanyar mafitsara, sakamakon da kan haifar da wahala ainun kafin fitsari ya fito..wani lokaci ma fitsarin kan faskara fita. Maras lafiya na jin fitsari amma ko je ya duƙa (tsugunna) domin yin fitsarin amma abin ya gagara. A irin wannan yanayi, sai a nemi sayyun zogale, a wanke su sosai domin a tsabtace su. A kuma sami ruwan tsami da aka tsiyayo daga ƙullun gero, sai a jiƙa sayyun a ciki, idan sun jiƙa, sai maras lafiyan ya sha moɗa ɗaya (1) da izinin Allah cikin ɗan ƙanƙanin lokaci fitsarin zai fito ( Fadama,2014: ).

Ciwon Sanyin Mata
            Akan kamu da irin wannan cutar a sakamakon saduwa da mace. Idan namiji ya harbu da ƙwayar cutar, sai a nemo sayyun zogale wadda bata daɗe da tsira ba. Sayyun za a kwanɗare ɓawonsu, sannan a dake su cikin turmi tare da jar kanwa. A yi kunun dawa, sai a ɗebo garin maganin a saka a cikin kunun. Maras lafiya zai riƙa shan kunun domin maganin wannan cutar sanyi. (Sahabi Ƙardaji, Gummi).

Sanyin Ƙashi Da Kumburi
            Mai fama da lalurar sanyi ƙashi ko kumburin jiki, sai ya nemo ‘ya’yan zogale a soya, sannan a daka har su zama gari. Sai a haɗa garin da man kwakwa a rinƙa shafawa a wurin da lalurar take.


Sanyin Ƙashi
            A wannan nau’in kuwa, za a sami saiwar zogale da tafarnuwa a kirɓe su. Sai a dinga haɗawa da man tega ana shafawa a ƙafa sau uku (3) a rana, har tsawon kwana bakwai. Za a sami sauki da ikon Allah.
            Ana kuma kwaɓa garin zogale tare da manja, a riƙa shafawa a wurin da ake jin raɗaɗi.

Tsayar Da Zubar jini
            Ta fuskar dakatar da jini daga zubewa kuwa, zogale nan ma ba a baya take ba. Domin in mutun yay i rauni ta hanyar yaka ko sara ko tuntuɓe wanda har ya haifar da kwararar jini, sai a samiganyen zogale ɗanye, a murtsika shi, a shafa ruwan ganyen a wuri raunin. In Allah Ya so jinin zai daina zuba.

Rauni Ko Gyambo
          Wanda ya ji ciwo har fatar jikinsa ta fashe tare da zubar jini. Ko kuma yana wani miki (ciwo) a ƙafa da ya daɗe bai warke ba, lamarin ya kai yana fitar da mugunya (ruwan ƙurji mai launin fari). Sai a nemi garin zogale a zuba a kan raunin ko gyambon. Insha Allahu zai yi saurin warkewa.

Gyambon Ciki (olsa)
            A dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi don maganin gyambon ciki.

Ciwon Shawara
            A dafa ganyen zogale tare da kanwa ‘yar kaɗan. A ci, a kuma sha ruwan don maganin shawara.

Suga A Jikin Bani Adam
            Jikin bani Adam na buƙatar wani nau’in sinadarin suga da ake kira a turance “GLUCOSE” da ke cikin jinni domin gudanar da wasu muhimman ayyukan da suka danganci lafiyar jiki. Irin wannan nau’in suga na bayar da kuzari ga jiki wanda ake buƙata wajen narkar da abinci da kuma rayuwar ƙananan halittu ( cells ) da suka tattaru da yawa suka gina jikin ko halittarsa tamkar bululluƙa.   
Suga, shi ne makamashin da ke ba jikin ɗan Adam kuzari domin rayuwa. Ƙwaƙwalwa (BRAIN ), hanyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa a jiki wato ( NERVES ) da jajayen halittun jinni (RED BLOOD CELLS) duk suna amfani da wannan makamashi, wato suga(GLUCOSE) domin samun rayuwa. Ana samunsa ne daga nau’o’in abinci masu samar da kuzari kamar: shinkafa da dawa da gero da masara da sauransu. Yayin da ɗan Adam ya ci abincin da ɗauke da suga fiye da yadda jikinsa ke buƙata, cikin ikon Allah sai wani sashen daki da ake kira da suna: mikin ciki (PANCREAS), kamar yadda Jinju (1990:239) ya kira shi, wato saifa kamar yadda mahauta ( rundawa) ke kiranta, sai ta samar da sinadarin da kan sa jikin ya tsotse sugan (INSULIN).

Cutatar Ciwon Suga         
Akwai dalilai da dama da kan wanzar da cutar ciwon suga a tsakanin al’umma. Wannan kan faru ne a daidai lokacin da ɓangaren jiki wato mikin ciki (PANCREAS) ta samu matsala hart a kasa samar da sinadarin da ke maganin cutar suga (INSULIN) ,wanda kan sa jiki ya tsotse suga (GLUCOSE). To sai adadin da ke cikin jinni ya yi yawa ya haifar da illa ga jikin.
Ƙiba ma tana sa wuraren da ake tsotse suga a jiki su ƙI aiki. Saboda haka, idan babu wannan sinadari ko muhallin tsotsewar na da matsala, sai sugan ya taru a cikin jinni, har ya kawo illa ga wasu sassan jiki kamar ƙananan magudanun jinni ( jijiyoyi) na:
·         Idanu
·         Zuciya
·         ƙoda
·         ƙwaƙwalwa
·         Fata
·         ƙafafu da sauransu, a sakamakon taruwar suga a cikinsu. Yana kuma yi wa wasu jijiyoyin
Lakka aibu, kamar na dubura da hanji da sauransu. Irin wannan illar ke wanzar da yawan fitsari da jin ƙishirwa da zafin jiki da ciwon ƙoda da ciwon mafitsara.
            Yayin da suga ya yi yawa a cikin jinni har yakan buge mutum ya faɗI a some. Haka idan ya yi ƙaranci, musamman ga masu fama da matsalar. Wannan ne ya say a zama dole gare su das u diga zuwa ana daidaita musu suga don ya kasance tsaka-tsaki.
            Ana iya gadonsa. Saboda haka wanda iyayensa da kakanninsa suka yi fama da matsalar, shi ma sai ya rinƙa zuwa ana masa awon suga a ƙalla sau ɗaya a cikin shekara.  

Zogale a Fagen Warkar da Ciwon Sikari (suga)
            Itaciyar zogale na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar ciwon suga. Sai dai akan samu wasu lokuttan sai an haɗa tad a wasu abubuwan wani lokacin kuwa ita kaɗai ta wadatar kamar yadda za a gani.

Ciwon Sukari
            A nemi furen zogale a gama da citta mai yatsu a dafa, a rinƙa sha kamar shayi. Yin haka yana maganin cutar da ke haddasa yawan fitsari wato Diyabitis.
            A haɗa zogale da yaɗiya a dake, a dinga zubawa a ruwan zafi ana sha sau uku a yini, wato da safe da rana da dare. Aiwatar da wannan haɗin kamar yadda aka zayyana yana kawar da ciwon sikari da izinin Allah.
            Haka kuma, wanda ke fama da irin wannan lalurar, sai ya ɗebo ganyen zogale tun da safe kafin rana ta fito. A shanya shi a wajen da ba hasken rana har ya bushe. In ya bushe sai a rinƙa dafa shi kamar shayi ana sha da madara, sau biyu a rana. A kula da zuwa wajen awo.Idan ba sauran cutar sukari sai a daina sha.

Ciwon Hanta Da Ƙoda
            A nemo ganyen zogale da ‘ya’yan ɓaure, a daka su har sai sun koma gari. Garin nan za a rinƙa sawa a nono ko kunu, a sha sau uku a yini. Insha Allahu za a sami lafiya.

Tsakuwar Ciki (Appendis)
            A sami saiwar zogale a gama da ‘ya’yan kankana a dake su har su zama gari. Sai a rinƙa zuba garin a nono ana sha. Insha Allah za a sami lafiya.

Tsutsar Ciki
            Idan yaro na fama datsutsar ciki, sai a sami ɗanyen ganyen zogale, a wanke a ba mai fama da lalurar ya ci, sau biyu a rana.

Maganin Bugun Aljani
            Idan Aljani ya bugi mutun har ya faɗI, sai a sami garin zogale a shaƙa masa a hanci. Zai yi saurin sakinsa. Wani zubin ma aljanin kan yi Magana.

Kariya Da Buƙatun Zuci
            Magunguna ne da akan yi amfani da su don taimakon ɗan-Adam wajen kare lafiyar jikinsa tare da biyan wasu buƙatunsa da suka jiɓinci jin daɗin rayuwarsa. A wannan haujin ma zogale na taka muhimmiyar rawa. Musamman idan aka yi la’akari da amfanin da ake yi da ita ta ɓangarori kamar:

Hawan Jini Da Ƙarin Kuzari
            Sanya zogale cikin abinci ana ci, yana maganin matsalar hawan jinni. Yana kuma ƙara wa mutun kuzari a jikinsa.

Kare Kai Daga Cuta
            Magunguna ne da ke taimakawa mutun wajen kare lafiyar jikinsa daga cuta da ke haifar masa da wata illa a jikinsa. Akan yi amfani da zogale domin ƙoƙari dakatar da wata cuta daga shiga cikin jikin mutun, ko kuma hana cutar yaɗuwa. Don haka za a iya cewa zogale na maganin da ya danganci rigakafi tare da hana yaɗuwar cuta.

Hawan Jini (tashin jini)      
          A sami albasa, a kasa ta kashihuɗu, a yanka kasha ɗaya bias huɗu na albasar a gama da dafaffiyar zogale a ci. A aiwatar da wannan haɗI sau uku ko huɗu a wata. Yin haka na maganin hawan jinni, kamar yadda Jinju (1990:32) ya bayyana.

Magungunan Biyan Buƙatun Zuciya
            Magunguna ne da suka jiɓinci buƙatun rayuwar ɗan Adam. Ta wannan fuskar ma ana amfani da zogale domin neman samun biyan irin waɗannan buƙatun rayuwa. Misalai daga cikin irin waɗannan buƙatun sun haɗa da:

Ƙara Yawan Ruwan Mama ( nono)
            A sami furen zogale a dafa shi tare da zuma. Mace mai shayarwa ta rinƙa ci sau uku a yini. Yin haka na ƙara yawan ruwan mama.

Ƙarin Nishaɗi
            A sami zangarniyar zogale tare da ‘ya’yan da ke ciki, a haɗa da kanunfari da citta da masoro da kimba a dake su, har sai sun koma gari. Sai a riƙa sawa a cikin abinci ana ci. Yin irin wannan haɗin na ƙara wa mata ni’ima da nishaɗi.

Ƙara Ni’imar Kwanciyar Aure
            Haka kuma mata ma’aurata na iya samun garin ganyen zogale a riƙa haɗa shi da madara ko nono ana sha domin ƙarin ni’imar kwanciyar aure da maigida. Amfani da wannan haɗin na ƙarasa mace ta ni’imtu, kwanciyar aure da maigida ta  yi armashi sosai har kuma a kwaɗaitu da sake maimaitawa.

Sa Maigida Saubatu
            A haɗa sauyar zogale da sauyar kankana da kanunfari a dafa su. Idan sun dafu, sai a tace rowan. Kana a nemi mazarkwaila da zuma a zuba (saka) a cikin tataccin ruwan, sai a sake ɗora su kan wuta har sai sun dafu. Idan suka dafu, sai a juye a rinƙa sha safe da yamma. Za a ga mamaki. Wannan haɗin ya keɓanta ga mata kawai.

Rage Ƙiba
          A nemo ganyen zogale, a tsabtace shi, a tafasa a rinƙa shan rowan kullum. Insha Allah za a yi mamaki.

Ƙarin Ni’ima Da Kuzari Ga Maza:
          A nemo furen zogale tare da ‘ya’yanta, sai a shanya su cikin inuwa har su bushe, sai a haɗa da dabino a dake su su zama gari. Garin za a rinƙa zubawa a nono ko madarar peak ana sha. Wannan haɗin yana ƙara wa namiji yawan rowan maniyyi da kuzari. Ana yi wa haɗin laƙabi da karya gado saboda ingancinsa.

Tsaraka: Asali da Ma’ana
            Asalin Kalmar, Bahaushiyar kalma ce wadda ke cikin tsarin sunayen kalmomin Hausa, jinsin mace. Ana tunanin cewa Kalmar ta samo asali ne daga kalmomi biyu na Hausa wato tsara da kuma kayi (kai). Kalmar tsara na iya ɗaukar ma’anar shirya ko gyara. Kayi kuwa na nufin kai. Idan haɗa waɗannan kalmomin da ke cikin jerin kalmomin aikatau, za su bayar da lafazin shirya kai, ko kuma gyara kai. Da yake lafazin shirya kai da tsara kai, duk ma’ana ɗayace, yau da gobe ta yi halinta a sakamakon sassauyawar zamani da sauye-sauyen da shi harshen kan fuskanta, sai Kalmominsuka rikiɗa suka komatsaraka. Sanin kowa ne, tun kafin bayyanar musulunci, Bahaushe baya shiga kowane irin sha’ani sai ya shirya masa. Shirin da ake aiwatar kuwa, yakan haɗa da neman kare kai ko sa’a ko nasara ga dukkan lamarin da za a fuskanta.
                        Abin da ya ƙarfafa guiwar ɗaukar wannan ra’ayi shi ne, a Karin harshen Katsinanci, Kalmar tsaraka bayan ma’anarta ta neman maganin sa’a a fagen sana’a tana kuma ɗauke da ma’anar kwana a shirye, kamar yadda  Abraham (1962:878).
            Tsaraka wani tsiro ne wanda masu sana’ar sayar da dafaffen ganye da fura da nono da wasu abubuwa da dama kan ɗiba su saka a cikin sana’arsu da ƙudurin kiran kasuwa, wato neman sa’a a yi saurin sayar da abin da ake talla. Wannan haki na tsaraka, mata kan haɗa da shi wajen ɗaurin lalle domin samun kanwar hannu (samun sa’a ko kasuwa)  don haɓakar sana’a, da cin nasara a fagen kasuwanci.
            A luggace kuwa, Ƙamusoshin Hausa sun ba da ma’anar tsaraka kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:
Kano, (2006:453) ya bayyana tsaraka da cewa, maganin da mutum yake yi don samun kasuwa ta fuskar ciniki. A ma’anarsa ta biyu kuwa, sai ya bayyana ta da cewa, neman sa’a wajen kamun kifi. Hasali an kawo karin magana, wadda Hausawa ke cewa, “ Su babu tsaraka wanka ne”.
Ta yiyu, wannan ne ya haifar da wanzuwar keɓaɓɓar Kalmar fannu a cikin lamarin sarkanci wadda sarkawa ke kira gyandi wato addu’a ko maganin da ake aiwatarwa domin neman sa’a.
            Bargery, (1933:1030) ya kawo ma’anar Kalmar tsaraka da cewa, duk wani abu da ɗankasuwa ke yin amfani da shi a matsayin magani domin samun nasarar haɓakar kasuwancinsa. Ya kuma kawo wata ma’ana da ke cewa: “ Hango haɗari a kuma kauce masa.”
            Sai dai abin kula a nan shi ne, tsaraka na iya kasancewa addu’a ko ‘yan ɗebe-ɗeben ganyaye ko hakukuwa ko saƙe-saƙin itatuwa waɗanda akan murza ko a jiƙa domin shafa wa kayan sana’a ko aiki.

Zogale A Matsayin Tsaraka
            Hausawa na amfani da ganyen zogale wajen yin tsaraka da ƙudurin samun sa’a a fagen saye da sayarwa. Mata masu sayar da kaya iri daban-daban kan jiƙa ganyen zogale a cikin ruwa, in ya jiƙa, sai a ɗauki ruwan a yi wanka da su. Wasu kuwa, ganyen ne akan saka a cikin kayan sana’ar da nufin samun kasuwa, sai kuwa a samu biyan buƙata.

Amfanin / Muhimmancin Zogale A Ƙasar Hausa
            A ƙasarHausa ana kallon bishiyar zogale tamkar “ Nagge daɗi goma”. Wato komai na zogale abin amfani ne.Ta kasance abin moriya ta fannin rayuwa daban-daban da ake iya bayaninsu kamar haka:

Zogale don ƙawa ko kwalliya:
            Kasancewar bishiyar zogale mai yawan amfani kamar yadda bayani ya gabata, akan yi amfani da wannan itaciya a  kewaye harabar muhalli domin a yi wa gida kwalliya. Wannan wani ƙari ne na daga ribar da ake samu daga itaciyar.

Zogale don Magani
            Masana da dama sun gabatar da ayyukka daban-daban a lokutta daban daban kan gudummawar wannan itaciya mai yawan albarka kan abin da ya shafi magani.
            Tashin farko, bayani ya gabata kan  abin da ya shafi abinci. Wannan babbar nasara ce, kuma magani babba da har yake kauda yunwa. Yunwa masifa ce kuma cuta kuma zogale makami ce babba da ake amfani da ita wajen kawar da wannan cuta. Ba nan kaɗai ba akwai hanyoyi da yawa da ake bi wajen sarrafa zogale don yin magani.

Zogale Da Kimiyyar Zamani
            Kamar yadda zogale ke da suna nau’i-nau’i a harshen Hausa dangane da yanayin bambancin muhalli da kuma Karin harshe, haka take da sunaye daban-daban da ake ambaton ta da su, tun daga harshen Latin da Faransanci da Girkanci da Indiyanci da sauransu. Wannan ne ya haifar da wanzuwar sunaye daban-daban da aka kira ta da su a kundaye da ƙasidun binciken da aka aiwatar game da zogale. Misali ana kiran ta Moringa Tree, Moringa Oleifera. Akan kuma kira ta da suna: Drustick Tree, Horseradish Tree. Tana ɗaya daga cikin jerin itatuwan da Allah Ya albarkata da baiwa ta musamman wajen ƙara lafiyar jiki tare da kasancewa garkuwar jiki don hana shigar cuta a cikinsa.
            Binciken masana kimiyyar zamani ya tabbatar da kasancewar zogale rumbun sinadarai masu yawan alfanu wajen kiwon lafiyar  al’umma, wanda ke da sauƙin mallaka har ga matalauta. Ita ce mafi armashin zama kafar samar da sinadarin gina jiki da ƙara kuzari. A kimiyyance an tabbatar tana kwantar da cututtuka kamar: saukar da hawan jini tare da taimakawa wajen samun isasshen barci. Wani aikin da zogale za ta iya aiwatarwa ya haɗa da tace ruwa tare da tsabtace su. Kuma tana daskarar da abubuwa masu illa (lahani) a cikin jikin ɗan Adam.
            Yayin da al’ummomi suka cigaba da amfani da zogale a matsayin cimaka (abinci) don maganin yunwa da cuta a bisa al’adu mabanbanta a sassa daban-daban na duniya. Haka kuma Romawa da Girkawa da Misirawa kan tatsi (fidda) mai (oil) daga ‘ya’yanta wanda sukan sarrafa shi wajen yin turare da man shafawa. A ƙarni na 19 gandayen zogale da ke yammacin ƙasar Indiya sun fitar da man zogale zuwa ƙas ashen Turai don sarrafa shi wajen yin turare da giris don amfanin  na’urori. An tabbatar da irin fa’idojin da ke ƙunshe a cikin zogale ta hanyar binciken masana kimiyyar zamani. Ganyen zogale tun fil-azal Allah Ya halicce shi kunshe da ninkin sinadarai nau’i-nau’i kamar haka:
·         Sinadarin bitamin “SI” (c) ninki bakwai (7) fiye da wanda ke cikin lemo.
·         Sinadarin kalsiyam ninki huɗu (4) fiye da wanda ke cikin madara.
·         Sinadarin bitamin “E” (A) ninki huɗu (4) fiye da wanda ke cikin karas.
·         Sinadarin kanwa ninki uku (3) fiye da wanda ke cikin ayaba.
·         Sinadarin furotin ninki biyu (2) fiye da wanda ke cikin kindirmo.
Dr. Mercola ya bayyana cewa, zogale na ƙunshe da bitamin da ma’adanan gina jiki da muhimman tsamin amino , antioxidants da sauran su. Bincikensa ya tabbatar zogale na maganin ciwon suga (diyabitis) da maganin kumburi, Cholesterol-lowering, tana kare jiki daga cututtuka. ‘Ya’yan zogale kuwa za a iya amfani da su wajen tsabtace ruwan sha fiye da wasu sinadiran zamani da ake amfani da su. Ya kuma nuna cewa, gayen zogale yana tattare da sinadirai masu gina jiki, kamar furatainin da alli da beta da carotene  da bitamin “SI”( c ) da potassium.  Ana amfani da ita a matsayin abinci da magani fiye da shekara 4000 da suka shuɗe. Binciken nasa ya nuna zogale na tattare da abubuwa kamar haka:
·         Sinadarin gina jiki ninki tara (9) fiye da wanda ke ƙunshe a cikin kindirmo. (yoghut).
·         Sinadarin bitamin “E” (A) ninki goma (10) fiye da wanda ke cikin karas.
·         Sinadarin potassium ninki goma sha biyar (15) fiye da wanda ke cikin ayaba.
·         Sinadarin kalsiyam (calcium) ninki goma sha bakwai (17) fiye da wanda ke cikin madara.
·         Sinadarin bitamin “SI” (c) ninki goma sha biyu (12) fiye da wanda ke cikin lemo.
·         Sinadarin iron ninki ishirin da biyar (25) fiye da wanda ke cikin alayyaho.
Dr. mercola, ya ƙara da cewa, zogale na maganin ciwon sukari saboda irin muhimman sinadaran da ke ƙunshe cikin ganyenta waɗanda suka haɗa da isothiocyanates. Ya kuma bayyana cewa, duk matar da ta rinƙa shan garin ganyenzogale mai nauyin giram bakwai (7grm) a duk rana har tsawon wata uku, sukarin jikinta zai ragu da kasha goma sha uku da rabi  (13. 5) daga cikin ɗari (13.5%). Haka zuba garin ganyen zogale mai nauyin giram hamsin (50grm) a cikin abinci, ga masu fama da ciwon sukari, yana rage yawan sukarin da kasha ishirin da ɗaya bias ɗari (21%).
      Ya kuma nuna ganyen zogale da kwasfarta da ‘ya’yanta suna ƙunshe da isothiocyanates, flavonoids da kuma tsamin phenolic. Wannan ne yaba su damar mallakar sinadaran da ke magance kumburi.Saboda haka ne a gargajiyance ake amfani da zogale wajen maganin gyambon ciki (stomach ulcet). Manta yana maganin ciwon hanta domin yana kare ta daga kumburin sha-ma-jika. Hasali ma mai ne da babu  kamarsa. Ana sarrafa shi wajen kare abinci daga lalacewa da wajen toye-toye da haɗa salad.Yana maganin amosanin gaɓɓai da hana bushewar fatar jiki.
      A cikin Duniyar Intanet a shafin Madina Islamic Medicins, an bayyana zogale da cewa, itaciya ce mai ban al’ajabi wadda Allah Ya sanya albarka da waraka a cikinta.  Ita abinci ce mai romon sinadaran da ke ƙara lafiya a jiki. Don haka ne aka kira ta da suna Itaciyar Rayuwa (The Tree Of Life). Ganyen zogale na ƙunshe da romon sinadari mai tarin yawa na bitamin “E” (A) wanda ke ƙara wa idanun ɗan Adam lafiya da gani fiye da bitamin “E” (A) da ke cikin karas har ninki huɗu (4). Sun kuma nuna  cewa zogale na tattare da sinadarai masu yawan gaske kamar:
·         Sinadarin calcium  mai sanya ƙashi da haƙoran ɗan Adam ƙwari da lafiya ninki huɗu (4) fiye da wanda ke cikin madara.
·         Sinadarin bitamin SI (c) wanda ke ƙarfafa garkuwar jikin ɗan Adam don yaƙi da cututtuka masu kai farmaki ga lafiyar jiki, ninki bakwai (7) fiye da wanda ke cikin lemo.
·         Sinadarin bitamin “I” (E) da ke kyautata fata da lafiyar jiki.
Binciken masana ilimin kimiyya game da itaciyar zogale ya bayyana zogale na:
·         Daidaita sukarin da ke cikin jiki.
·         Rage hawan jinni.
·         Ƙara wa mace mai shawarwa ruwan mama (nono).
·         Kasha ƙwayoyin cutar bakteriyal.
·         Wanke ciki, idan aka ci kafin a ci wani abinci.
·         Kare lafiyar hanta da ƙoda.
·         Ƙara kuzarin jiki.
·         Rage ƙiba.
·         Gyara ƙwaƙwalwa da sauran su.

Zogale A Idon Duniya
            Itaciyar zogale ta shahara a ƙasashen Afirika, musamman ma a ƙauyuka. Masana ilimin kimiyyar tsirrai sun kira zogale da suna moringa.A ƙasashe da dama, da wannan  sunan aka san ta da shi.
            Masu magungunan gargajiya sun jima suna sarrafa ta wajen warkar da cututtuka da kuma matsayin abinci mai gina jiki. Bayyanar nazarin ilimin kimiyya da bunƙasarsa ya wanzar da bincike game da zogale a sassa daban-daban na duniya ciki kuwa har da Nijeriya. Sakamakon binciken ne ya haifar da gano kimar ta, a matsayin magani da abinci da kuma abin sarrafawa a masana’antu. A halin da ake ciki ana nomanta a nahiyoyi daban-daban kamar Afirika da Amerika ta Kudu da Amerika Ta Tsakiya da kuma ƙasasas ashenilanka da Indiya da Mexico da Malaysiya da Filipin. Zogale na da saurin girma da jure wa fari. Tana yi a wurare masu yalwatattun ruwan sama da kuma ƙarancinsu kazalika kuma da yankuna masu zafi har ma da wuraren da babu ingantacciyar ƙasar noma.Tana ɗaya daga cikin itatuwa da aka fi sanin ta da yawan amfani a duk faɗin duniya. Kusan komai na jikinta yana da amfani. Babu wani abun yasarwa a jikinta.
            Ƙasar Indiya ta zarce kowace ƙasa a duniya a fagen noman zogale. Ana noma kadada 38,000, inda ake samar da ɗanyen kwanson zogale mai nauyin ton miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya zuwa ɗari uku (1,100,000 – 1,300,000) a duk shekara.
            An kafa Babbar Cibiyar Ƙasa Da Ƙasa da ke gudanar da nazarin kayan lambuna, domin rage talauci da ƙarancin rashin isasshen abinci mai gina jiki a ƙasashe masu tasowa ta hanyar inganta hanyoyin samar da kayan lambu tare da sahihiyar hanyar amfani da su. Daga cikin ayyukkan wannan cibiya sun haɗa da binciken itaciyar zogale.
            Ana cin ganyen zogale da kwansonta da aka ɗebo tun yana da taushi. A ƙasar Indiya kuwa ana haɗa kwanson (ɓawon ‘ya’yan zogale) da wasu kayan lambu a yi salad da su. Ana cin ɗanyen kwanson ko kuma bayan an dafa shi.
            A ƙasashe daban-daban ana magani da ganyen zogale da ɓawonta da saiwarta da furenta da kuma ‘ya’yanta. Amfaninta bai taƙaita ga ci da yin maganin gargajiya kawai ba. Saboda muhimmin sinadarin da ke ƙunshe cikinta, ana safarar ta zuwa ƙasashen ƙetare domin sayarwa. Kwansonta ya ƙunshe da sinadari kamar PENICILLIN  masu kashe ƙwayoyin cuta waɗanda ake kira ANTIBIOTICS. Wannan ne ya sa ƙasashe kamar Ingila da Japan da Kanada da wasu ƙas ashen Gabas ta Tsakiya ke buƙatar ta sosai. Tun fiye da shekara goma da suka shuɗe, wani kamfanin ƙasar Indiya da ake kira da suna: “DRUM STICK INDIA’ yake safarar kayan da aka sarrafa da  zogale. Kamfanin ya shahara da yin hulɗa da kamfanoni da hukumomin aikin gona da na kayan abinci da na magunguna da kuma kamfunnan kayan kwalliya (ado).
            Fiye da shekara arba’in (40) da suka shuɗe, Hukumar Lafiya Ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi amfani da itaciyar zogale wajen kyautata lafiyar al’umma a ƙasashen da talauci ya yi wa katutu. Masana sun tabbatar da cewa an ɓoye itaciyar zogale ne, domin ɗimbin ribar da ake samu daga gare ta, ta hanyar sarrafa ta ta fuskar magunguna da kayayyakin  kyautata lafiya dangin bitamin (vitamins) da gishirin ma’adanai mai kare lafiyar jiki (miniral salts). Wannan ne ya samanyan kamfanonin magunguna ba kasafai suke son bayyana sinadarin da suke yin magunguna da shi ba, da kuma nau’in tsirran da suke tatso sinadiran.
            A nahiyar Afirika kuwa,  hukumomi da cibiyoyin nazari da bincike sun duƙufa haiƙan wajen nazarin itaciyar zogale (moringa). Dr. Nworo A. Ozumsa da ke Sashen Nazarin Ƙwayoyin Cututtuka Na Jami’ar Nmandi Azikiwe, Akwa, ya gudanar da wani bincike a kan zogale, ga abin da ya ce: “ Haƙiƙa,  a ƙididdigar baya-bayan nan da na aiwatar, na fahimci zogale na maganin cututtuka kimanin tamanin da ɗaya (81). Tana ma iya warkar da kusan dukkan cututtukan da ke addabar jikin ɗan Adam. A can baya, mu masana kimiyyar zamani mun sha famar sukar masu magungunan gargajiya da ke cewa, magani ɗaya yana warkar da cututtuka ishiri (20). Amm yanzu a ilmance mun gano gaskiyar lamarin, domin an gano ganyen zogale na iya warkar da cututtuka masu yawan gaske. Ganyen zogale na maganin ciwon sukari da zazzaɓin cizon sauro da rashin isasshen barci da dai sauran su.
            Shi kuwa Dr. Ozumba, ya shekara goma sha ɗaya (11) yana nazarin itaciyar zogale. Ya bayyana cewa: “ tun da na gane sirrin da ke kunshe cikin wannan itaciyar ban sake amfani da maganin ƙarin gishirin ma’adanai  da jiki ke buƙata (miniral salts) irin wanda kamfanonin magunguna ke sarrafawa ba. Saboda aikinsa bai kai ingancin wanda ke ƙunshe a cikin zogale ba. Masanin ya ƙara da cewa: A matsayinmu na masana masu bincike, nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne, mu yi azamar bunƙasa itaciyar zogale domin sarrafawa a masana’antu. Kuma  mu yi ƙoƙarin ƙara mata kima.
            Dr. I. M. Bugaje cewa ya yi: “ Amfanin zogale bai taƙaita ga fannin abinci ba, domin tana tace ruwa. Idan aka fitar da mai da sauran sinadaran da ake buƙata, tunkuzar ‘ya’yan zogale na iya tace ruwan sha da kawar da ƙwayoyin halitta (bacteria) masu haifar da cututtuka”.Ya ƙara jaddada cewa: “Muna iya tace ruwa ta amfani da ‘ya’yan zogale a maimakon alam (alib ko alimu) wanda Nijeriya ke kasha biliyoyin daloli domin sayo shi daga ƙas ashen waje. Bugu da ƙari, zogale ba ta da wata illa a jikin bil-Adam, don haka tana nan bias yanayinta na ɗabi’a. alhali kuwa an san cewa alam na haifar da cututtuka da dama wanda ya haɗa har da gurɓacewar jini.
            Babban Daraktan Kamfanin AVUCO Nigeria Limited Yohanna Dami cewa ya yi: “ Zogale tana maganin hawan jinida zazzaɓin cizon  sauro da ciwon sukari tare da sauƙaƙe zafin zazzaɓin da masu ciwon ƙanjamau suke fama da shi. Su ma ‘ya’yan zogale suna da mai (oil) mai daraja da ake sayarwa a  kan dalar Amirka goma($10) kowace lita ɗaya a kasuwar duniya.”
            Shi ma Babban Daraktan Cibiyar Bincike Da Bunƙasa Kayan Sarrafawa A Masana’antu (Raw Materials Research and Development Council RMRDC), Farfesa Peter A. Onuwalu cewa yayi:” Itaciyar zogale za ta taimaka wajen samar da man abinci tare da sauran tsirrai masu samar da mai. A lokaci ɗaya noman zogale da sarrafa ta zai kawo mafita ga matsalar  samar da guraben aikin yi da kuɗaɗen shiga tare da kyautata lafiyar al’umma ta hanyar samar da tsabtataccen ruwan sha wadatattu lafiyayyu.”.
            Yayin da Farfesa Charles Wambede yake nasa bayani cewa ya yi: “ Itaciyar zogale tana ƙunshe da wasu fa’idoji kamar haka:
·         Ganyen zogale yana ƙara ƙarfin garkuwar jiki.
·         Tana ƙara kuzari.
·         Tana taimakawa wajen zagayawar jini da bugawarsa.
·         Tana taimakawa aikin ƙoda da hanta.
·         Tana maganin gyambon ciki da sauransu
Masanin ya ƙara da cewa, ganyen zogale yana ƙunshe da sinadarai nau’i-nau’i, masu yawa kamar haka:
·         Ninki bakwai (7) na bitamin SI (c) fiye da wanda ke cikin lemo.
·         Ninki huɗu (4) na sinadarin kalsiyam, fiye da wanda ke cikin madara.
·         Ninki huɗu (4) na bitamin E (A) fiye da wanda ke cikin karas.
·         Ninki biyu (2) nafuratanin fiye da wanda ke cikin madara.
·         Ninki uku (3) nasinadarin potassiumfiye da wanda ke cikin ayaba.
Ya kuma nuna cewa ‘ya’yan zogale na ƙunshe da mai (oil) wanda yawansa ya kai kimanin
kasha 38 zuwa 40 bisa ɗari (38-40%). Wannan man yana ɗauke da sifofi irin na man zaitun wanda ya shahara wajen daraja. Zogale za ta taimaka wajen magance ƙarancin abinci mai gina jiki. Nomanta zai samar da aikin yi da hajar sarrafawa a masana’antu, wanda zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziki da rage talauci a ƙasashe masu tasowa.

Kammalawa
            Kamar yadda aka sani ne, zogale ko zogala ba baƙon abu ba ce, musamman a karkarar da ke farfajiyar ƙasar Hausa, domin tana cikin jerin abincin yau da gobe. Sannu a hankali, mutanen da ke zaune a alƙaryu da birane suka gano amfaninta, wadda tuni mutanen karkara suka daɗe suna amfani da ita wajen aiwatar da magani domin magance nau’o’in cuwurwutar da ke addabar su, sakamakon ɗinbin sinadarin da ke jibge cikinta wanda Allah Mabuwayi Gagara Misali Ya halicce tad a su. Irin waɗannan sinadiran ne ya sa take ƙarfafa garkuwan jikin bani Adam da ke yaƙin cututtukan da ke cikin jikin wanda duk ke amfani da ita. Kuma haƙora da gaɓoɓI da ƙasusuwan jiki su ƙara ƙarfi da inganci. Wannan bincike ya gano cewa, tana ƙarfafa gani tare da ƙara lafiyar ido. Tana gina jikin ɗan Adam fiye da yadda madara ke gina shi. Tana taimakawa wajen gyara fatar jiki.
            A taƙaice za a fahimci cewa, zogale na ƙunshed a fa’idoji masu tarin yawa. Daga cikinsu akwai:
·         Magance hawan jinni.
·         Ƙara rowan nonon mace mai shayarwa.
·         Daidaita sukarin da ke cikin jinni.
·         Taimakawa wajen narkar da abincin da aka ci.
·         Yaƙar tare da kasha ƙwayoyin cutar Bakateriya.
·         Wanke ciki.
·          Ƙara wa hanta da ƙoda lafiya.
·         Gyara ƙwaƙwalwa.
·         Rage ƙiba ko taiɓa.
·         Ƙara wa bani Adam kuzari.
Irin wannan alfanu da ke ƙunshe cikin zogale ne ya sa ake kallon bishiyar zogale a ƙasar Hausa tamkar: “ Nagged aɗI goma”. Wato komai nata abin amfani ne. ta kasance abin moriya ta fannin rayuwa daban-daban.   


MANAZARTA


Contact Us..