Ticker

6/recent/ticker-posts

Huce Haushin Rashi A Kan Mai Samu


 
A fahintar ɗaliban al’ada, a kodayaushe akan tsinci al’adun mutane cikin harshensu da adabinsu. Al’ada kandamemen fage ne da babu wanda zai rayu a wajen ta, komai dabararsa sai an ga gurabunta a rayuwarsa. Don haka, ɗaliban al’ada ke ganin waƙoƙin baka wani babban rumbun kinshe al’ada ne da bai kamata a bari su salwanta ba a kowane zango na rayuwa. A rayuwar kowane mutum abu biyu ke tare da shi a cikin fafitikar rayuwarsa: ‘samu’ da ‘rashi’. Ga al’adar nema, tushen neman wani abu shi ne ‘rashinsa’. Ko dai babu shi, ana son a samo shi, ko kuma an same shi, ya ƙare, ko yana barazanar…
Huce Haushin Rashi A Kan Mai Samu

Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 0803 431 6508

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato Ranar, Talata 27 ga Nuwamba, 2012 da ƙ          arfe goma na safe a babban ɗakin taro na Tsangayar, a mazaunin din-din-din na Jami’ar.

Gabatarwa:
A fahintar ɗaliban al’ada, a kodayaushe akan tsinci al’adun mutane cikin harshensu da adabinsu. Al’ada kandamemen fage ne da babu wanda zai rayu a wajen ta, komai dabararsa sai an ga gurabunta a rayuwarsa. Don haka, ɗaliban al’ada ke ganin waƙoƙin baka wani babban rumbun kinshe al’ada ne da bai kamata a bari su salwanta ba a kowane zango na rayuwa. A rayuwar kowane  mutum abu biyu ke tare da shi a cikin fafitikar rayuwarsa: ‘samu’ da ‘rashi’. Ga al’adar nema, tushen neman wani abu shi ne ‘rashinsa’. Ko dai babu shi, ana son a samo shi, ko kuma an same shi, ya ƙare, ko yana barazanar ƙarewa, ana son a tabbatar da shi. A tsarin siyasar rayuwa, babu wurin da babu mai iko da talaka, ‘yantacce da bawa, mai akwai da marashi, baƙo da ɗan gida, ga su nan dai. A bisa ƙa’idar al’ada, cikin kowane kashe-kashe na al’umma, marashi da mai samu, sun fi fice da amo a zamantakewa. Ga ɗan bincikena, wannan shi ya sa adabi da al’adar kowace al’umma na kulawa da su matuƙa. Buƙatar wannan takarda leƙo yadda makaɗa Gambo ya fito da hoton yadda marashi ke kallon mai samu da irin hararar da suke yi wa junansu a zamantakewa.

Karan Gwajin Dahi:
A kowane sashe na adabi, ana samun yadda zamantakewar marasa da masu samu take. Wani lokaci a tarar an shirya musu bayani na musamman kamar waƙoƙin Ɗanmaraya Jos (na Kai Mai Akwai Ka Gane). A wani lokaci ya kasance matsiyatan kawai ake wasawa, kamar waƙoƙin ‘yan tauri. A wasu lokuta, a yi garkuwa da rashi, a yi zambo, irin yadda yake aukuwa a waƙoƙin fada. A wannan ɗan nazari, na zaɓi in mayar da akalar bincikena a kan tauraro ɗaya kacal, watau Alhaji Muhammadu Gambo Fagada.
Ga al’adar bincike, sai an fayyace fitilun kalmomi sosai ga mai karatu da masu sauraron karatun. Ɗan bincikena ya yi garkuwa ga waƙoƙin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada mai waƙar ɓarayi. An haifi Alhaji Muhammadu Gambo Fagada a garin Fagada Babba Ƙaramar Hukumar Maiyama, Jahar Kabi a shekarar 1947. Cikakken tarihin rayuwarsa da gwagwarmayarsa an taskace su cikin (Maiyama, 2008, da Gusau 2009, da Bunza 2011). Makaɗa Gambo ya yi fice wajen kiɗan sata. Ya yi luguden haushin da ke ga marashi a kan mai samu, da yadda za a hangi ƙurar takaicin a lafuzan marasa da ayyukansu.

Gurbin Sata A Al’ada:
A taƙaitacciyar fassara, sata na nufin ƙoƙarin mallakar abin wani ba da yardarsa ba, ba da saninsa ba, domin a amfana da abin, ko a lalata shi. Ma’anar sata ruwan dare ce ga al’ada, sai dai hukunce-hukunceta ya saɓa, daga ƙasa zuwa ƙasa, ko daga wani addini zuwa wani addini. A al’adance, sata abar ƙyama ce ga Bahaushe, abar kunya ce, mai fitar da mutum cikin mutane amintattu masu faɗa a saurare su a al’umma. Wannan ne dalilin da ya sa wa sunan mai aikata aikin baƙin jini, da ƙyama, ga duk wani mutumin kirki. Fitacci daga sunayen akwai: ɓarawo, mugu, matsiyaci, ɓare, mugun ɗa, ƙwaro, kura, duhu, macuci, fataken dare, maɗauki, gafiya, kare, da dai makamantansu. Kowane suna daga cikin waɗannan sunaye Bahaushe ya ji an kira mutum da shi zai nisanci mai sunan domin sanin ma’anonin da ke cikin sunan. Bisa ga ma’aunin al’ada, sata ba sana’ar da za a yi kirari da ita ba ce, domin al’ada ba ta yafe wa mai aikata ta. A al’adance, tana daga cikin manyan laifuka da Bahaushe bai tanada wa mai aikata su wurin zama ba a alƙaryarsa.

Me Ke Sa A Yi Sata?
A cikin kiɗin sata wannan takarda za ta kafa hujjojin da za ta kare iƙirarinta. Don haka, babu makawa, sai an fayyace abubuwan da ke sa Bahaushe ya ɗauki sata tafarkin rayuwarsa. Abubuwan da ke sa a shiga sata a wajen ɗaliban al’ada sun kasu gida biyu: na ɗaya na kira su ‘Azaliyya’ na biyu kuwa ‘Hali’. Azaliyya, ina nufin ɗabi’un da mai su, bai da hannu a kansu, da su aka haife shi, ko sun ci karo da shi riƙis! Wato abin da Bahaushe ke ce wa, ta tsaka mai wuyar sani. Daga cikin Azaliyya akwai: Ciwon sata, sammu ko jifa, gado (shan sata a nono) ko ga mahaifi. Waɗannan abubuwa uku, al’ada na ganin sun fi ƙarfin mai su ya kauce musu, domin ba da saninsa suka shige shi ba.
Muhallin ‘Hali’ ga sata shi ne, mutuwar zuciya wanda ke haddasa lalaci, da ragganci, mai kai ga, roƙo, da bara, da ɗauka, idan masu abu ba su ankara ba. Wanda ya ginu cikin wannan kashi, tushen satarsa daga rashi ne, idan aka zure, a gunguma, a wuce gona da iri. Ga al’ada waɗannan ɓarayi su ne, matsiyata ko marasa masu takaicin mai samu. Akalar takardarmu gare su zai ba da ƙarfi domin su suka sa kansu cikin halin da suke ciki, ba su suka fi kowa tsiya ba da rashin haƙurin zama a ciki. Idan kowane marashi sai ya yi sata, da ke nan, rukuni biyu kawai muke da su a zamantakewarmu, daga masu samu, sai ɓarayi. Assha! Da tarbiyarmu ba ta kawo yau da nagarta ba.
Idan muka faɗaɗa bayanin sata zuwa halin da muka samu kanmu ciki a yau, sai mu ce; abu biyu suka ɗaure wa satar biro da ta ɗauka-ruga gindi a ƙasashenmu: rashin adalcin shugabanni da rashin nagartaccen hukunci. Idan shugabanni sun kiyaye kansu a kan taɓin dukiyar hukuma, ba sai an ce wa talaka ya kama kansa ba. Idan shugabannin da talakawa duk jirgi ɗaya ya ɗauko su, tsaftataccen hukunci na sa dole a tsare gaskiya ko a sha kaifin takobin adalci. Rashin waɗannan abubuwa bala’i ne ga kowace al’umma komai wayewarta da ci gabanta.

Wane Ne Mai Akwai/Samu? Wane Ne Matsiyaci?
Kalmar ‘samu’ da ‘akwai’ suna da fassarori biyu: gajeruwa da doguwar fassara. Gajeruwar fassara ita ce, mutum ya kasance mawadaci ga buƙatun lalura na ɗan Adam. A samu mutum na da wuri irin na tsara. Yana da abinci irin na, ku zo mu ci a raga. Yana da sutura irin suturar da al’adarsu ke kira sutura. Idan mutum ya hau wannan fassara a al’ada yana cikin masu samu, don haka ya cancanci a kira shi ‘Mai Akwai’. Doguwar fassarar kalmar ita ce, a ƙara da gajeruwar fassara. A haɗa da abubuwan da ke ƙawata rayuwa, su fito da mai ita a sarari, a ƙara saninsa, ya gwada tsawo da zamaninsa. Wato ya kasance mai ilmi, ko mai ‘ya’ya da yawa nagartattu, ko mai wata alfarma ta musamman. Wanda ya samu wannan, ko da bai mallaki komai na duniya ba, ba ya daga cikin marasa, kuma ba za a ce masa, matsiyaci ko mai babu ba. Aƙilu Aliyu ya raba muna gardama a cikin waƙarsa Kadaura ya ce:
Sai ga mutum ba ilmu ba mulkin ba,
Shi ba kuɗi sha’anin akwai rikitarwa.
Ƙanta ƙalai gashe babu mai ko naso,
Dahe babu romo ko na ɗan lasawa.

Bisa ga al’ada, idan mutum ya kasa shiga cikin gajeruwar fassara  da doguwar fassara ta mai samu, to ya shiga cikin marasa ke nan, su ake kira ‘matsiyata’ na haƙiƙa. Idan mutum ya fi haɓar sama lafiya, idan bai shiga cikin fassarorin nan biyu ba, ya shiga cikin matsiyata. Tabbas! Idan ya fi dila wayo. In ya fi aula dabara; in ya fi biri azanci; in ya fi kowa hankali da zumunci a garinsu. Muddin ba ya da kuɗi da ilmi, ba muƙami, sunansa ‘matsiyaci’. Dangantakar waɗannan mutane da masu samu ita ce maƙasudin wannan ɗan rubutu.

Dangantakarsu Ta Al’ada:
Dangantakar mai samu da marashi ta ƙud-da-ƙud ce, irin ta jini da tsoka. A koyaushe, marashi wurin mai samu yake shan iska. A wajen mai samu za a bautar da jiki, a samu na shagali. Idan aka yi masa hidima ya biya. Abin da za a saya a more rayuwa, a wurinsa za a je a saya. Ya ba da bashi a saya dukiyarsa, a mayar masa da kuɗin da aka karɓa bashi gare shi. Ya ba da kyauta, a saya dukiyarsa da kuɗin, su koma gare shi. Ya yi sadaka, a saya dukiyarsa jallin da aka tara wajen bara ya koma gare shi. Idan ya yi arha ga kayansa ya ci riba, idan ya yi tsada dole a saya, ya ci riba da ribibi. A yi noma, a tara abinci a kaka, ya saya da arha kamar kyauta, ya ɓoye, sai rani ya kai rani ya fitar da abincin, waɗanda suka sayar da shi, dole su saya ko su mutu ko su bar ƙasar. Wai, duk wannan dangantakar mai sauƙi ce ga marashi domin ana yin ta ne da mai samun da ke tausayawa ne.
Wurin da ake hararar juna shi ne, wurin da mai samu ya kasance mai alfahari, marowaci, matsolo, macuci, mamugunci, marashi tausayi da tausayawa. Mafi rinjayen masu samu a wannan ɓangaren suka faɗo. Mai samu zai yi amfani da samunsa ya ƙwace wa moro (mataulaci) mata, ya ɓata ‘ya’yansa mata, ya kunyata ‘ya’yansa maza da kushili, ya haukata wasu, ta hanyar ba su kayan shaye-shaye, su yi masa banga a gari, da sunan siyasa, ko addini, ko ƙabilanci, ko barantaka. Bayan an bautar da marashi ga ƙwadago, a bautar da shi ta fuskar bashi da ruwa, tun bai gama biya ba, a bi shi da kamuwa. A koyaushe moro cikin ƙangi yake na masu gari da masu abin hannunsu.
Taimakon da wasu masu samu ke yi wa marasa, na dariya ne, da nuna, ga shi nan an san na fi ka. Idan za a ba shi sutura, taɓa-jiki za a ba shi, kowa ya san kuncen wane ce. Idan abinci za a ba shi, idan ya yi bara, saura za a ba shi, ya sha saleɓar yara. Idan dabba za a ba shi ya kiwata ya samu ta haifa masa, ramamma za a ba shi, ya sha wahalar kiwo, wasu a ba su juya, su gama kiyo a kai gidan mai abu a yanka a ci gajiyar wahalarsa, in ya yi sa’a, a ba shi fata da ƙassa. Idan aka ba shi gona ya noma, ba da abin da ya noma zai biya ba, sai ya je gandun mai gona ya kashe ƙarfinsa can gabanin ya dawo ya nomi nasa gaɓɓansa sun yi laushi ba zai noma abinda zai ciyar da kansa ba. Idan ya shiga wata matsala sai ya bayar da kayansa jingina zai fice ta. Ire-iren waɗannan abubuwa suka haifar da rashin jituwa, da samun natsuwa a fahinci juna tsakanin marashi da mai samu. A koyaushe marashi ganin yake, mai samu yake yi wa wahalhalun duniya, don haka daga nan ne ƙyashi zai shiga, takaici ya biyo baya, daga nan sai tunanin hanyoyin da za a huce haushin da aka ƙunshe shekara da shekaru. Wataƙila, daga nan ne wasu ke tunanin raba mai samu da samunsa ta kowace fuska, sai tunanin sata ya fara memen zuciyar marashi. Idan marashi ya kai ga wannan tunanin, ya kai bagiren da Bahaushe ke cewa, kome taka zama ta zama. Ashe gaskiyar wani mai bara da ke cewa:
Ranar da ba ka da shi,
Mai ba ka ba shi da shi
Rannann da kai da ɓarawo
Shawararku guda.

Hoton Takaici Da Haushi A Lafazin Mai Jin Su:
Babu wani ɗan Adam da ya kuɓuta ga shiga ƙunci na damuwa da zai haifar da takaicin wasu ko wani abu, ya ɗuru cikin hushin abin har ya yi ɓarin baki a gane a lafazinsa. Daga cikin abubuwan da suka fi bayyana a gane akwai takaici da haushi akwai:
i.                   Furucin takaici tsirara
ii.                 Kushewar samu kai tsaye
iii.              Muguwar fata ga samu
iv.               Zagi na fitar arziki
v.                 Mutuwar mai samu
vi.               Ganin hasara ga mai samu
vii.            Ƙyacewa da haƙewa

Furucin Takaici Tsirara:
Bisa ga al’adar magana, akan ɗan sakaya wasu abubuwa, ba sai an yi musu wuƙa zage ba. Idan marashi ya ga mai samu yana damawa a kan ingarmarsa ko motarsa sai ya ce: “Allah da Ya ba ku raƙumi Ya ba mu zakara”, an san ya sakaya, duk da yake ya furta abin da ke yi masa ƙaiƙayi. To, yaya za ka ce? Idan ya ce: “Allah da Ya ba ku raƙumi, Ya ba mu wuƙa, raƙumin ya ci ubansa.” Da ji, wannan lafazin ya fi wanda ya gabace shi zama tsirara. Dubi wannan lafazin na marashi ka gani:
          Jagora:        Ni dai ko da subahin ko da yamma
:In ishe mai kuɗɗi tsugunne
:In ga yana naso ga goshi
:Kama da kunama sun ka kauru
:Shi ɗebi gumi bay yo guda ba
:Gambo in ji awa na taki Arhwa
:Tun da mai abu ya koma matcaci

Mai samu ake son, in dai ya yini cikin baƙin ciki, irin na marashi, in ko ya kwana cikinsa. A ganin marashin, idan ya ga haka buƙata ta biya, domin su marasa sun ƙara yawa ke nan. A nan, ana zance ne kan wanda ya tara tsabar kuɗi ne, da aka zo ga mai ƙadara cewa aka yi:
          Jagora:        Gaya wa baƙauye mai tumaki
:Wai ya ga kiyo ya fara tcada
:Ya ga awa sun tara jalli
:Wallahi suna kwana matcata
:In je Mafara in iske Ja’e
:Shi gargaɗa ko ɗai bai ragawa

Babu shakka, a nan, haushin abin da aka tara ne marashin ke yi. Idan kiyo ya fara tsada, su marasa ba su da abin sayen bisashe ko da lalura ta riske su. Domin kakkaɓe wannan takaici za a kira Ja’e.
A waɗannan wurare duk, takaicin bai kai gaya ba, da aka bai wa Dikko Canda (ɓarawon bisashe da shanu) shawara cewa:
          Jagora:        In Canda na bin ta tawa
:Ana rasa ko bundi Kuwara
Ya kira marashin abokinsa (Canda) da cewa, ya samo kwari da baka irin na farautar namun daji, ya sa musu dahi irin na Bargu da an harba sun mutu, wanda ya ci nama ya mutu, ga faɗarsa:
Jagora:        Duk ka bi su ka harbe
:’Yan gaton uwa
:A bar su ga kolaye su canye
:Dikko ban yi hasarar ko kwabo ba

Takaicin ya fito tsirara, son ake, mai abu ya yi rashi, ya dawo cikinsu, a ƙara yawa. Kuwara can ne Madinar shanu a Nijeriya ta Arewa, duk wani Bafulatanin da ke jin ya taki ƙasa ga samu na dabbobi sai an je Kuwara za a tantancewa. To! A cikin Madinar shanun Arewa marashi ke son a rasa ko wutsiya. A lura ba Gambo ne ke magana ba, marashi ne ke furta takaicinsa a bakin Gambo. Dalilin haka kuwa masu samu suka sa aka ɗaure Canda ya yi hursuna, ya ƙare ya dawo. Don haka ake son ya rama abin da aka yi masa. Wa ya kai shi gidan Yari? Masu samu. Mene ne matsayinsa? Marashi. Me ya kamata ya yi? Huce haushi.

Kushe Wa Samun Kai Tsaye:
Irin nuna rashin tausayi ga marashi da masu samu ke yi, shi ke sa marasa ke nuna kushewa ga dukiyarsu. A al’adar huce haushi, idan ba a fito tsirara aka furta ba, ana nuna kushewa, da ko oho, ga mai samu. A fagen kushewa, ko da gaskiya aka faɗa, mai hankali zai gano cewa, akwai abin da ya sosa wa mai kushewar rayuwa don haka ya yi furucin. Nazarci wannan ɗan waƙa sosai:
Jagora:        In don waɗanga Musulmi na na yanzu
:Masu biɗan matan maƙwabta
:Musurmuƙa duk na ‘yan gaton uwa
:Kuɗin lukudi na ag ga shaggu
:A ɗunguma kowa ban hana ba

Tirƙashi! Daga cikin abin da ke ci wa marasa rai ga masu samun zamani akwai amfani da abin hannunsu su ɓata musu mata da ‘ya’ya. Haka kuma, suna ganin mafi yawan dukiyar ta tsafi ce da aka yi da ‘ya’yansu ko dabbobinsu. Wannan takaicin ke sa, ko an yi musu sata, ba a tausaya musu, domin ana ganin ɓarawo haƙƙinsa ne ya ƙwato da ƙarfi, kamar yadda aka yi amfani da wayo aka karɓe masa. Da Musulman na tsare haƙƙin amanar dukiya da mai bayarwa ya ba su, da ba su saɓa masa da ita ba. Idan suka yi masa ɗa’a da ita babu marashin da zai ji haushinsu bale ya huce haushin a kansu.

Muguwar Fata Ga Samu:
Idan takaici ya yi takaici, marashi buƙatarsa a yi marus, mai samu ya rasa kowa ya rasa. Da an yi fatar, ya rasa, wani ya tafi da samun, za a ce, da dama-dama. Makaɗa Gambo cewa ya yi, shi idan ya tunkari gari zai shiga ciki, ya dai san da samu ake kafa gari ba da rashi ba. Duk wanda ke cikin garin samu ya zaunar da shi. Don haka, yake son, ya tarar garin ƙurmumus da wutan gobara, kowa ya fita tsila, a faɗarsa:
          Jagora:        Ni dai ga irin magun nuhina
                             :In na tunkari gari
:Tun da shiga in taki toyi
:In ga labaye sun yi malle
:Gambo in ji awa na taki Arhwa
:Tun da mai abu ya koma talakka

Idan aka sa natsuwa sosai aka saurari Makaɗa Gambo ɗiyan waƙoƙinsa cike suke da ire-iren waɗannan kalamai masu nuni ga samun mai samu. Toyi yana nufin sauran hauɗin da wuta ta ci. Labaye su ne: sabara da geza da ƙananan tsirrai idan sun ci wuta sai su lanƙwashe ganye ya ƙone su yi sifar baka ko lauje shi ne “malle”. Malle wani abinci ne mai kara da ‘ya’ya irin na dawa idan ya nuna hogen sai ya lanƙwashe ya dubo ƙasa saɓanin na dawa da zai yi sama. Idan Bahaushe ya ce ‘an yi malle’ an soke kai ƙasa ke nan.

Zagin Fitan Arziki Ko Na Ɗiban Takaici:
Akwai zagin na haife ka, akwai zagin na grime ka, akwai zagin burgewa, akwai zagin kar ta san kar, akwai zagin fitan arziki. Zagin fitan arziki, na nuna takaici ne, da huce hushi a kan wanda ake jin haushinsa. Irin wannan zagin an fi yin sa ga iyayen wanda ake jin haushi, ko a ce ‘Shega’ ko ‘ɗan kazan uwa/uba’. Da makaɗa na ba Alu na Tambuwal shawarar yadda zai yi wa mai kuɗi fashi gidansa ya ce:
          Jagora:        Kak ka yi mai sata hina kwance
:Jijjigas shi in shege ya ta da kainai
:Tari bakin shege da bingida
:Ce, “In ba kuɗɗi ba ranka”
:Ai shi ka gwada ma wurin da duk suke
:Bai fitina bai tad da yaya

Da aka ɗauko Inuwa (fitaccen ɓarawo tauraron Gambo) da keke zuwa garin Romo aka tarar da Tsoho Tudu (buwayayyen tajiri) makaɗa ya ce:
          Jagora:        Nac ce Inuwa ga Tudun can
:Shegen tsoho ah hakan ga

Bayan makaɗa ya je ya wasa Tsoho da kirari ya dawo kan Inuwa sai ya ce:
          Jagora:        Inuwa ka jiya hwa
:Yac ce: “Mu je ka majiɗi kak ka damu”
:Wancan shege ni ka bi nai

Da Canda (fitaccen ɓarawon tumaki) ya kawo wa makaɗa ragunan layya. Makaɗa ya tambaye shi ina aka samo su? Ya ce:
          Jagora:        Uban wani yaɗ ɗaure su cana
:Sad da zai musu wanka
:Da sun ka ɗau dara
:Sai yag gilma nay yi ƙyacci
:Nac ce masa shege ba ka cin su
:Mai jinjina turaye ka cin su

Duk wuraren da aka yi amfani da kalmar ‘shege’ zagin ɗibar takaici ne ga mai abu. Wannan na nuna, an daɗe ana jin haushinsa, tun ba a kai ga dukiyarsa ba sai an zage shi an ɗebe takaici, idan aka je ga dukiyarsa, in ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai.
Idan aka samu tazara, za a yi zagin yankan ƙauna da za a kai ga iyaye kai tsaye. A nan, makaɗa ya fi amfani da kalmar “’yan gaton uwa” ƙarshen zagin ya kasance ‘shaggu’, jam’in ‘shege’. A cikin taken Dikko Canda, makaɗa ya san Dikko na sauya wa dabbobi launi. In baƙaƙe ne, su koma farare, in farare ne su koma jajaye, ga su nan dai. Komai wayon mai samu, ba ya kama dabbar da ba irin launin tasa ba, ko ya gan ta ga hannun sanannen ɓarawo Canda. Ba a bar mai abu da wahalar neman dabbarsa ba sai da aka ce:
          Jagora:        Mai biɗar akawal
:Bai kama danda
:Komai wayon ɗan gaton uwa

Da yake ba ɓarayin shiga ɗakuna shawara cewa ya yi:
          Jagora:        Ɗebo wuta sa ta ga bunu
:Har ta ruru
:Ka sa ta ga zauren ‘yan gaton uwa
:Lokacin da wuta tat turnuƙe sama
:Ba ta ɓarawo za a yi ba

Da makaɗa ya juya wajen masu kuɗi ya ce:
          Jagora:        Mai kuɗɗi in ba shi kyauta
:Sara nika dubin ɗan gaton uwa
:Don akwai ni da mai ɗiba ga bainai

Waɗannan zage-zage duka, na fitan arziki ne, na yankan ƙauna, ba a yin su, sai rai ya ɓaci, an ɗebe kunyar wanda ake sa-in-sa da shi. Bisa ga ma’aunin zamantakewa, mai furta su, wani ƙurjin takaici ne ya yi masa maruru a zuciya da babu wata sakiya da zai yi wa ƙololon, face furta zagin yankan ƙauna. Idan aka furta zagin sai a ji ɗan sanyi-sanyi na rashin da ake dambe da shi, sauran marasa su dara haushin ya rage.

Mutuwar Mai Samu:
Marashi ba ya da kowane irin tausayi ga mai samu idan ya tuna da irin wahalar da mai samu ke son ya gan shi a ciki. Da yawa za ka ji, idan lebara na faɗa da uban-gidansa, zai nuna bai ƙi uban gidan ya mutu ba. Wai shi a ganinsa, mutuwar mai samu ita ce mutuwar mai rai, amma ta marashi ai mutuwar matacce ce. Makaɗa ya ziyarci irin wannan ra’in wurin da yake nuna ba ya son a yi sata, a ƙyale mai samu ba a kashe shi ba. Buƙatarsa ita ce:
          Jagora:        Kway yi sata day yanzu
:Yab baro mai kuɗɗi da rainai
:Allah Ya isa min za ni cewa
:An yi ta ne don ta da yaya
:Kyawon sata ta satu
:Ba a ga kuɗɗi babu mai su
:In ishe tsohi na hawaye
:In ishe mata sun yi yakkwat!

Muradi dai a kashe mai samu kamar yadda ya kashe marasa da ransu. Takaicin ya kai ga ba kuɗɗin kaɗai ake son a raba shi da su ba, ransa ma dole a raba shi da shi, domin ka da a raba shi da kuɗi, ya rayu, abin ya sake dawowa, ya ci gaba da shan jinin marasa. A ganina, wannan takaici shi ne na ƙoli, domin Hausawa sun ce, ƙarshen tika-tika tik! Ashe gaskiyar Kassu Zurmi da yake cewa:
Jagora:        Mai abu ja, marar abu ja!
                   :Wallahi mai abu kauce
                   :Ka da wahala tai she ka

Ganin Hasara/ Ruɓushi:
A al’adar rayuwa, duk mai burin ganin hasara, bai mallaki abin hasara ba. Wanda duk ya mallaki abin da ba ya son ya yi hasara, ba ya son ya ga hasara. Irin wannan fahinta ce wasu ƙasashen duniya ke bi, su haɗa jari da talakawa da ma’aikata a gina gidaje, da kamfuna, a saka jarin kowa a ciki. Falsafar ita ce, ko da za a yi wa gwannati zanga-zangar ba-mu-so, ba za a yi ƙone-ƙonen gidaje da masana’antu ba, domin hannun kowa na a ciki. Don haka, babu mai son jawo wa kansa hasara. Marashi, saboda irin takaicin da yake da shi, ga mai samu, sai a ga yana ta ɗokin ya dai ga hasara, ya je ya ba da labari. Makaɗa ya tabbatar muna yana daga cikin marasan da ke da irin wannan tunanin ga masu samu. Nazarci wannan ɗan waƙa ka gani:
          Jagora:        Don ɗai in ga hasara
:An ka haihe ni
:In tahiya ta in da za ni
:Ba don wani daɗi mai yawa ba

A wani ɗan waƙa yana cewa:
          Jagora:        Ni dai in ga hasara ɗanya-danya!
:Ko ba a ban sisin kwabo ba,
:Gambo in ji awa na taki Arhwa
:Tun da mai abu ya koma matcaci

A wani ɗan waƙa irin wannan yana cewa:
          Jagora:        In dai ji hayagaga ina tsaye
:In ji gari ya ɗebi yaya
:In ji maƙwabta na hwaɗin: ‘Ar!’
:Mun ji awa an taki darni
:An taɓi soro an tumaye

A cikin waɗannan ɗiyan waƙa uku, babu wurin da makaɗa ya nuna abin da ya samu ko zai samu. Ya dai nuna, an riga an yi hasara. Wa ya yi harasa? Mai abu. Idan da bai mallaki komai ba, ba zai yi hasara ba. Tunanin marashi ga irin halin wasu masu miyagu, maƙetata, shi ya sa wasu marasa ke son ganin hasara a kan tunanin nan na Bahaushe da ke cewa: ‘In don kare a yi gobara, ya laƙe bundi (wutsiya) ya bi kassuwa.’ Karen bai samu komai ba, bai fita da komai ba. Haka marashi ke so ga mai samu ya dai gan shi:
          Jagora:        Ya yi saƙwamƙwan!
:Ya yi jangwan!
:In ga hawaye na zubo masa
:Ko na abin shan koko bai da
:Sai dangi sun ba shi rance
:Gambo in ji awa na taki Arhwa
:Don uban wani ya koma matcaci

Ƙyacewa Da Haƙewa
Tsakanin mai samu da marashi haka yake kamar dangantakar ɓera da kyanwa. A koyaushe marashi yana ƙyace wa mai samu, shi kuwa mai samu yana haƙe da shi. Idan takaici ya yi takaici, za a ji, wanda takaicni ya kai wa ko’ina ya yi na jaɓa (kulɓa) wato ƙt! A kowane baki waɗannan harufa suka fita, cikin ƙirjin da babbar magana ta takaici. Da makaɗa na hira da Tsoho Tudu gabanin su fara shiga manyan labaye cewa ya yi:
          Jagora:        Ga mu nan tahe da ni da baba
:Ƙemus-ƙemus! Ni da baba
:Rangai-rangai! Lahiya lau
:Hirab banza ta ni kai mai
:Nic ce: “Ƙt! Wallahi kana gane kurenka baba.”

Bayan an ƙyace wa baba, aka sake haƙe shi. Idan haƙewa, da ƙyacewa, suka haɗu, sai rai ya ɓaci fuska ta sauya, kamar dai yadda Gambo ya taras da Inuwa, bayan ya wasa tsoho Tudu yana cewa:
          Jagora:        Kan da in dawo in da Ɗanmoɗwacci
:Mugu na taunan haƙora
:Nag ga hina murza’ idanu
:Nag ga idanun sun yi jawur
:Yac ce: “Kt! mu je ki mashiɗi kak ka damu”
:Wancan shege ni ka bi nai.”

Ban musanta akwai ciwon sata ga Sani na Zauro (ƙwararren ɗan sane ne) ba, amma irin takaici da haushin da yake da shi idan ya ga mai kuɗɗi a kasuwa, ya kwararo shi, bai kai ga aljihunsa ya yanka ba, makaɗa na cewa:
          Jagora:        Mai kamas shi yi ƙwace
:Sani ɗan moɗen Zauro
:Aradu!
:In yak koro bai cika ba
:Sai ka cimma hawaye na zuba mai!

Modde ya’e! Haba! Ka san takaici ya yi takaici, ƙyacewa ta yi ƙyacewa, domin abin ya zarce ƙyaci, da cizon haƙora, da cizon yatsa, ya kai ga zubar hawaye, irin na mujahidi idan ya rasa shahada. Wallahi kowane mahassadi haka yake idan hasada ta zaburo masa, ba zai san ya yi ƙyaci ba, ko launin idanunsa ya sauya, wani lokaci hawaye kan zuba bai farga ba. Haka hasada kan tona wa mai ita asiri ba da saninsa ba, a gane shi.

Sakamakon Bincike:
Rashi wani abu ne mai muni da kowa ke gudu rayuwarsa. Samu wani abin so ne ga kowa ƙin wanda ya rasa. Yadda samu yake da wuya, a faɗar Bahaushe, kuɗi masu gida rana. Wani lokaci ya ce, “Kowa ya ci zomo ya ci gudu;” ko “Zomo ba ya kamuwa daga kwance;” ko “Babu maraye sai raggo.” Duk isharorin na nuna wa jama’a cewa, mai nema yana tare da samu. Duk irin wuyar da aka sha gabanin samu, irinta ce marashi ke ciki. Idan marashi na tunani da irin tunanin da al’adarsa da adabinsa suka tanada, batun ya shiga tunanin ya yi sata ba ta taso ba. Dalili kuwa shi ne, wanda duk ya samu, sai da ya sha wahala. Don haka, duk wanda zai raba shi da abin, sai ya sha wahalar gaske ta neman dabarun da zai bi, da yadda zai fita, idan ta rutsa da shi. Da yadda zai tsira da mutuncinsa, idan ba ta rutsa da shi ba. In haka ne, ai gara a yi tunanin yadda za a nemo na kai ya fi. Dukkanin tunanin da makaɗa Gambo ke yi, na nuna haushi da takaici, bai nuna wurin da ya yi ɗan yunƙurin neman na kansa ba. Da ya yi yunƙurin na kansa, da zai ci karo da samu, in kusa in da nisa. Abubuwan da ke tattara takaici da haushi a zukatan marasa zuwa ga masu samu su ne, rashin ƙoƙarinsu na tashi su nemi na kansu.
Duk da haka, Hausawa na cewa, idan an ga ta ɓarawo, a dubi na mai kaya. Nason mulkin mallaka da ya haɗo da hayaƙin gurguzu, da jari-hujja, da tsarin demukraɗiyya ya barbaɗa a daulolin ƙasar Hausa, ya ci zarafin tunanin Bahaushe ainun. Rashawa, toshiyar baka, alfarma, zurmuguɗɗu, da ci-da-ceto, su suka rikita ƙarshen zamanin da muke ciki. Mai bakandamiya ya yi wannan hasashe a ƙarshen zamani yana cewa:
          Mai akwai a hana masa godiya,
                   Mai babu ko a hana masa dangana.

A koyaushe, mai akwai buƙatarsa ya ƙara, a taru wajensa ana bauta. Marashi ya kasa dangana ya ari halin da ba nasa ba, ba na iyayensa ba, ya yi ƙaurin suna cikin mutanen alƙaryarsu. Wayyo! Da marasa za su ɗauki ƙaddara, su dangana su nemi ɗan abin da ya sawwaƙa, da sai mai samu ya rasa wanda zai bautar, ko dai ya yi kyauta, ko dukiyarsa ta ruɓe.

Naɗewa:
Kiɗan satar da Gambo ke yi, wata makaranta ce ta fayyace falsafar rayuwar duniyar da Bahaushe ya rayu cikinta. A bayanin Gambo, ɓarawo matsiyaci ne, maras zuciya, da kishin kai. Masu samun zamani kuwa, da yawansu musiba ne ga al’ummar da suka rayu a ciki. Da masu abin hannunsu na taimakawa, da ɓarayin ɗauka-ruga, ba su yawaita ba. Takaici da haushin da ke tsakanin mai akwai da marashi, a koyaushe zuba suke a bakin marashi, domin su zama hannunka mai sanda ga masu samu. Na jinjina wa Malam Muhammadu Gawo Filinge da ya yi wa talakawa gargaɗi da cewa:
          Jagora:        Talakka ba shi cin kifi soye
          Yara:           Balle ya sha roson zabbi
                             :Hi tai mahauta ga ƙiren hanji
:In yac ci guda biyu ya ƙoshi
          Gindi:          Ya Allah gyara
                             :Wahabu Ka taimaki ‘yan Nijar
          Jagora:        Miyal kuɓewa ba tau ta ba
                             :Mu samu dai yoɗonmu ya gyaru
Yara:           Mu samu wake da ruwan toka
Jagora:        Haka nan na!
Gindi:          Ya Allah gyara Wahabu
:Ka taimaki ‘yan Nijar

Matuƙar kowa bai tsaya matsayinsa ba, takaici da haushin juna, ba ya gushewa a zukata. Babu wani magani, face samun daidaitaccen tsari da zai tanada wa gaskiya wurin zama na gari. A ganina, shari’ar Musulunci kaɗai ce mafita.

Manazarta:
Aliero, H. M. 2000: “The Implication of Money Laundering on the Nigerian Economy”, paper, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Aliyu, A. Fasaha Aƙiliya, NNPC, Zaria.
Auta, A. L. 1988: “Gudummuwar Waƙoƙin Makaɗan Baka Dangane da Adana Tarihi.” Kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. 2009: Narambaɗa, Wallafar Lagos: IBRASH, Publishers.
Bunza, A. M. 2011: “Rashin Sani ya fi Dare Duhu.”: Jami’ar Umar Musa ‘Yar’adua.
Bunza, A. M. 2012: “Lalurar Kiɗa a Bakin Makaɗa” muƙala, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Bunza, A. M. 2012: “In ba ka San Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, kammalallen bincike ba a wallafa ba.
Burton, S. H. 1954: The Criticisms of Poetry, London: Longman.
Daba, H. B. 2006: Ɗanmaraya Jos in Hausa Folkloric Perspectiɓe, Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S. M. 2009: “Waiwaye a kan Tarihin Rayuwar Alhaji Muhammadu Gambo na Kulu Makaɗin Ɓarayi”, muƙala: Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad, D. 1977: “Indiɓidual Talent in Hausa Poetic Tradition a Case of Aƙilu and his art”, PhD, London: SOAS.
NNPC, Gangar Wa’azu, Zariya.
Rasmussen, D. 1974: Poetry and Truth, Paris: Monton.
Rodney, W. How Europe Under Deɓeloped Africa,
Tukur, T. 1984: “Mawaƙa da Matsayinsu a Al’umma” cikin: Studies in Hausa Language Literature and Culture, The First International Hausa Conference, Kano: Jami’ar Bayero.
Umar, M. B. 1977: Ɗanmaraya Jos da Waƙoƙinsa, Zariya: Hausa Publication Centre.
Umar, M. B. 1980: “Tattalin Arzikin Hausawa na Gargajiya”, Kano: Jami’ar Bayero.
Yahya, A. B. 1996: “In Praise of Theiɓes: An odd Category in Hausa Oral Poetry” Paper, Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Zurmi, M. A. 1986: “Rayuwar Alhaji Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa” Kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Post a Comment

0 Comments