Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausa Cikin Hausa Martabar Hausawa Da Mai Karatun Hausa



Barazanar da lokaci ke yi wa al’umma ga ci gaban rayuwarsu musamman idan aka kalli mutuwa a faifan nazari, za a ga ba ƙarami ba ne. Magabata managarta maɗaukaka mafifita mahanga nesa, da ƙyallaro baya, da suka yi wa Hausa aikin a zo a gani an fara ƙamfarsu a ƙarninmu. Idan gaba ta fara ba da baya, baya ba ta da sauran kwanciyar hankali. Kasancewar na gaba idon na baya, idan ya faku, na baya ya rasa idon ƙyallaro gaba. Matuƙar bagiren da sanuwar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta tsoma bakinta. To! Idan ta ƙi tsoma bakin za a ce da lauje cikin naɗi. Danƙwairo ya tabbata mana gaba ta riga ta wuce baya ke da saura. Idan haka ne, gaba sunanta gaba, na baya na….
Hausa Cikin Hausa Martabar Hausawa Da Mai Karatun Hausa



Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, Nijeriya
Waya: 0803 431 6508
Ƙibɗau: mabunza@yahoo.com



Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa domin karrama Marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju mai taken: The Challenges of Teaching African Languages and Association des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) due da Nigerian Indegenous Languages Writers Association NILWA suka shirya, ranar 19-21 Febrairu, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic haɗe da bukin ranar Harshen Uwa International Mother Language Day (IMLD) da UNESCO ta ƙaddamar


Gabatarwa

Barazanar da lokaci ke yi wa al’umma ga ci gaban rayuwarsu musamman idan aka kalli mutuwa a faifan nazari, za a ga ba ƙarami ba ne. Magabata managarta maɗaukaka mafifita mahanga nesa, da ƙyallaro baya, da suka yi wa Hausa aikin a zo a gani an fara ƙamfarsu a ƙarninmu[1]. Idan gaba ta fara ba da baya, baya ba ta da sauran kwanciyar hankali. Kasancewar na gaba idon na baya, idan ya faku, na baya ya rasa idon ƙyallaro gaba. Matuƙar bagiren da sanuwar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta tsoma bakinta. To! Idan ta ƙi tsoma bakin za a ce da lauje cikin naɗi. Danƙwairo ya tabbata mana gaba ta riga ta wuce baya ke da saura. Idan haka ne, gaba sunanta gaba, na baya na nan baya, sunansa ɗan baya. Magabatanmu da suka assasa karatun Hausa cikin Hausa, sun aza Hausa a tafarkin cigaba. Nasararsu a fili take ko ba a yi gwari-gwari ba. Taken wannan takarda kirarin ne gare su, da tabbatar masu da goyon bayanmu bisa ga hasashen malamin kiɗi Narambaɗa:
Jagora: Ga abu nan a hwaɗi,
Yara  : Babu mai hwaɗi
Yara  : Sai ƙus! ƙus! ƙus! Akai da shi
Jagora: Wa ka hwaɗi?
Yara  : Kai ɗan baka hwaɗi,
Jagora: Wai, baya ka ƙwazon tunkuɗe gaba
Yara   : Shi Allah ba yarda shikai ba
Yara   :  Mai sharri shi ɗai yaka biya
Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci,
Yara   :  Karen ɓuki bai ɗan shawararka ba,
Yara   :  Shi maganar giwa yake tsare
Jagora : Ka ce wa biri duk dabbar da ac cikin daji,
Yara   : Giwa taka biya.
Jagora: Aaahn!
Gindin: Ya ci maza ya kwan shina shire
              Gamda’aren Sarkin Tulu Alu[2].       

Karatun Boko
Karatun boko ba wahayi ba ne, ba kuma wani keɓaɓɓen ilmi ne da aka keɓe domin wasu mutane na daban ba. Asalin karatun boko sana’o’i da al’adu da fasahohin da Allah Ya albarkanci mutane da su, a kowace nahiya ta duniya suke. Hore muna harshen sadarwa da aka yi shi ya bunƙasa su. Dabarar rubutu da Allah Ya saukar wa mutane ita ta taimaka ga ƙara yaɗa su da bunƙasa su da taskace su. To! Daga nan boko ya fara a duniyar mutane[3]. A wajen Hausawa yake “Boko”, kowace al’umma da yadda take kallonsa ta fuskar sunan da ta ba shi[4].
Masana ilmin harsuna da bazuwarsu sun tabbatar da cewa, harshe na bunƙasa, yana masassara, yana doguwar suma, yana ƙaura, yana balaguro kuma yana mutuwa[5]. Abubuwan da ke bunƙasa harshe, su ke hana shi masassara. Dalilan da ke sa ya yi masassara su ke haddasa doguwar suma. Cikin magagin suma ake samun ƙaura ko balaguro. Mutuwar harshe kwatakwata abu ne mai wuya, amma masana sun tabbatar da shi a rubuce[6]. Don haka, al’ummomin da suka fara samun cigaban karatu da rubutu da harshensu na asali a rubuce, suka yaɗa ilmin takarda mai suna “Boko” a Hausa[7]. Duk wata al’umma da ta bunƙasa da wannan salon adana ilmi a rubuce wannan shi ne tushen “Boko” gare ta.

Asalin Magana:
Asalin magana ga kowace al’umam ga harshe ake danganta shi. Harshen ɗan Adam ke sarrafa sautukan da bakinsa ke gurzawa bayan da ƙwaƙwalwa ta gama saƙa tunaninsu. Asalin basirar a zuciya take gine, ƙwaƙwalwa ke jujjuya su gwargwadon ƙarfin basirar mai magana. Don haka, basirar magana ta sarrafa sautuka da ita ake haihuwar ɗan Adam[8]. Masanan da ke da wannan tunanin sun ce, ai ba ɗan Adam kawai ke da harshe ba. Wasu halittu sun fi shi harshe mai girma, da tsawo, da faɗi, amma ba a ba su martabar magana ba. Duk da irin faɗin baki da girmansa da darajarsa ta sarrafa abinci, harshe ya fi shi daraja da martaba a fagen magana. Harshe ne madugun kula da ɗanɗano da jujjuya yawu a baki. Don haka, a tunanin gargajiya na magana ana cewa harshe “baki”[9].  Waɗannan abubuwa da aka hanga ya sa nake da ra’ayin cewa, magana ginanniya ce a jikin mai ita daga wanda ya ƙaga shi. Haka kuma, ita wannan maganar, ita ce ake kira Harshe.

Dole a girgiza wa masana ilmin harsuna a kan hasashe-hasashensu na asalin harshe ga ɗan Adam. Wasu na ganin asalin amgana daga tsuntsaye da dabbobi ne[10]. Domin tabbatar da wannan tunanin, sai an tantance, wa aka fara halitta daga cikinsu? Wa ya halitta su? Ina aka samu labarin wannan halitta? Hasashe-hasashen masana a kan asalin harshe idan aka ɗora su a kan waɗannan tambayoyi uku, za a gane wurin da salka ke tsatsa. A taƙaice, zamu gane cewa, a tarihin samuwar harsuna, babu harshen da ya fi wani daraja da ɗaukaka. Da akwai wani harshen da za a fifita a kan wani, da harshen da mutum na farko da ya riga kowa fara rayuwa a doron ƙasa shi ya kamata a fifita. Wane harshe ne? A wace ƙasa mai shi ya rayu? Wa ya koyar da shi harshen? Ire-iren waɗannan hasashe-hasashe sai a naɗe ƙasa a dangane ba a kai ga haƙiƙanin bayanin da za a bai wa mutum a gansar da shi sosai ba. Idan ana tare da ni a kan wannan za a ga:
i)                   Masu harshe ke ɗaukaka harshe ba harshe ke ɗaukaka kansa ba.
ii)                Ɗaukaka wani harshe a kan wani harshe bisa hankalin tuwo wani irin tiƙeƙen jahilci ne da bai kamata a samu masu shi a wannan ƙarni ba.
iii)             Duk harshen da ke da masu magana da shi yana da hujjar gwada tsawo da kowane harshe, domin babu wani ma’aunin ilmi da ya nuna wani harshe ya fi wani.
iv)              Duk wani harshen duniya da baki ake sarrafa sautukansa, kuma ‘yan Adam ke sarrafa shi ba dabbobi da tsuntsaye da ƙwari ba. Harshen da ya ci nasarar samun karɓuwar dabbobi da tsuntsaye da ƙwari babu laifi ya yi bugun gaba a ji shi. Wanda duk bai kai ga wannan martabar ba, ba ya da wata hujja ta yin kirari in ba kirarin matsoraci ba.
v)                Waɗannan ‘yan dalilai guda huɗu (i-iv) su suka ba ni damar ƙaga sunan wannan takarda da yanke hukunci na kai tsaye cewa: kowane tsuntsu ya yi kukan gidansu, sai dai, ban ga laifin shege ba, ya yi kukan uban wani domin ya rasa uba.

Rubutun Hausa A Tarihi
Gajeren tunanin wasu ke ganin wai, Hausa ba a fara rubuta ta ba sai bayan zuwan Turawa. Wannan shi ya sa ake tuƙe bokon Bahaushe ga tarihin zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. A tarihin bazuwar Bahaushe a duniya, da tarihin bazuwar wasu al’ummomi ƙasar Hausa, za mu ce, fara sarrafa harshen Bahaushe a rubuce ya soma ne tun zamanin:
i)                   Kakamin Gobirawa na farko da suka fara ratsu ƙasar Hausa daga Masar. An ce, sun zo da saukakken addini na Nasara. Abin sani shi ne, duk saukakku addini yana da azancin rubutu[11].
ii)                Bazuwar Hausawa a ƙasar Hindi tun gabanin zuwan Turawan mulli-mallaka yake. Hindi sun daɗe da ilmin rubutu da lisafi. Ba za a ɗebe ɗanmaha ba idan aka bi diddijin tarihi[12].
iii)             Girkawa da suka bazu a uwa duniya, an samu ɓirbishin shigowar su ƙasar Hausa a birnin Kano. A rijiyar Akwa an samu rubutun Hausa cikin sautukan Girkanci[13].
iv)              Barebari a diddigin tarihin rubuce-rubucensu na tarihin tafsiransu cikin harshensu, ajaminsu ya fi shekaru ɗari bakwai. Dangantakarsu da Hausawa irin ta jini da tsoka ce. Tabbas! Ba a rasa wani abu ba, na ba da misali ba[14].
v)                A tarihin Bahaushe, tun fil azal, kowace zuriya daga cikin zuriyarsa tana da tsage-tsagen fuska na gargajiya da za a iya rarrabe ta da ita. Babu wanda zai musanta kasancewar tsagar fuska rubutu, idan za a bi diddigin ma’anar rubutu[15].
vi)              Wangarawa da suka shigo ƙasar Hausa tun wajen ƙarni na tara zuwa goma, su kimanin ɗari huɗu, a Kano suka yada zango mai tsawo. Da suka assasa addinin Musulunci, salon karatunsu da ƙidan baƙinsu ne Bahaushe ya ara. Don haka, ba za a ɗebe ɗanmahan rubuce-rubucen harshensu (na Mali) Wangaranci  da aka aka adana Hausa a ciki ba, haka kuma, ba za a rasa Hausa rubuce a cikin harshensu ba[16].
vii)           Rubutun Ajami da shi Hausa ta yi fice da zara ga dukkanin harsunan Afirka a kundin tarihi. Don haka, Hausa a rubuce take gabanin bayyanar boko[17].
Harshen da ya kai ga ire-iren waɗannan martabobi ba ya buƙatar dafa kafaɗar kowane harshe domin ya tashi tsaye. A tsaye aka farar da shi. A tsaye aka san shi. A tsaye aka rabu da shi bayan da aka sadu da shi. A tsaye aka bar shi, bayan da aka fice shi. Haƙiƙa babu harshen gida da ya riga shi wayewa a duniayr rubutu. Yadda duk Turanci ya aro tsarin Romawa a fagen rubutu, haka Hausa ta aro tsarin Larabawa ta ɗora bisa ga nata. Abin mamaki a ce, ɗalibin harshe ke ganin wai, sai Hausa ta roƙi roƙaƙƙe da roƙo ya rarake domin ta ciyar da harshenta gaba. Yaushe ne hankalin karatu zai yarda da cewa:
i)                   Muna da namu, mu watsar, mu je mu yi aro. Ka ce dai da kuɗinmu, mu ɓoye, mu ciwo bashin da babu ranar biya.
ii)                Wace hikima ke ga aron aro? Turawa dai ga Romawa suka aro rubutu. Muna da namu, muka ƙara da na Larabawa. Me zai sa mu yi daɓin daɓakuna?
iii)             Kai! Ina ganin lokaci ya yi mu sake yin nazarin Rubutun Tafi da masana suka binciko na Hausa mu yi tunanin inganta shi[18].


Hausa A Karatun Bokon Nijeriya:
Turawan Ingila da suka ga ƙwal uwar bari, dole suka ba da kai bori ya hau, aka bar Hausa a tsarin ilmin boko. Tun a makarantun firamare, ake fara nuna wa yara Hausa. A da, a zamanin ‘yan bokon farko da Hausa za a dinga koyar da yaro komai har zuwa aji huɗu da biyar[19]. Daga nan, idan bakinsa ya yi taushi, fasaharsa ta ƙaru, a fara sa Turanci. A makarantun Sakandare da na horas da malamai da manyan kwaleji da jami’o’i duk Hausa na da kaso mai tsoka. Sai dai, domin a kare mata fikafikai za a sakaɗa ta ƙarƙashin sunaye irin su:
Department of Languages
Department of African Languages
Department of Language and Linguistics
Department of Literary Studies
Institute of African Studies.

Duk da haka, martabar Hausa ba ta ragu ba. Za a taras malaman Hausa da karatun Hausa da ayyukan Hausa da gudunmuwar Hausa sun fi yawa a ciki. A da, a karatun boko Hausa na a matsayin Vernacular[20], wato harshen marasa galihu. A wasu lokuta, a sa ta cikin ‘local languages[21]’ wai, wasu ‘yan tsirarun harsuna na ƙwarorin mutane. Idan ana son a kawo misalanta a rubutun ilmi, wasu su ce, mother tongue[22], wasu su ce, first language[23], ga su nan dai. Duk waɗannan abubuwa an rasa yadda za a yi a muzanta harshen da ake ganin ya gagari a ɗaƙile shi. Cikin wannan guni da kishi da zunɗe da harara da tsaki da ƙyacci da gwalo da ƙyashi da hasada, Hausa ta ci gaba da rayuwa da yaɗo da haihuwan nagartattun ‘ya’ya wandon robo daidai da kwankwason kowane irin zamani.
A cikin karance-karancen boko a Nijeriya, Hausa ta yi yaɗo kane-kane cikin ilmin harsuna. Ta yi babban biga cikin tarihi da walwala da ilmin siyasa. Ta yi zurfi cikin nazarce-nazarcen kimiyya da ƙere-ƙere da ilmin kiyon lafiya. Tsare-tsaren tattalin arziki da tsaro da kimiyyar ƙere-ƙere Hausa na ciki tsundum! Manyan ‘yan boko da suka yi digiri da manyan digirori cikin waɗannan fannonin da bazar Hausa suka yi rawa wajen rubuta kundayen digirorinsu. Butulci ne babba bayan an ci moriyar ganga a ce mata koren banza. Babbar magana kan ta ita ce, masu kukan a koyar da Hausa da Turanci sun manta da cewa, hatta da masu karatun Turanci da Hausa suke garkuwa ga kundayen digirinsu. Wannan ya tabbatar da kasawar Turanci ga biya wa Hausawan da suka ƙware ga Turanci wadatacen bagiren bincike. Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu. Hausawa sun ce, hankali ke gani ba ido ba. Haƙiƙa, mai hankali idan ya ga kurma a guje, taya shi gudu zai yi, ba tsayawa zai yi tambayarsa me ya faru ba? Dalili kuwa, shi ne, shi kurma gani ya yi, ba ji ya yi ba.

Koyar da Wani Harshe Ciki Wani Harshe
A fagen ilmi, kowane harshe gashin kansa yake ci. Bisa ga ƙa’ida, ba za a bai wa ɗalibi takardar shaidar ƙware wa ga harsunan Afirka ko Asiya ko Turai gaba ɗaya ba. Dole a ware harshe ɗaya da aka koyar da shi a ba shi. Bisa ga tsari, kowane harshe yana da sautuka da yadda ake furta su. Yana da tsarin furucin sauti da wasula da yadda za a gwama su, su gina kalma. Haka kuma, ba zai rasa yadda za a sarrafa kalmomin su ba da jimloli ba. Waɗannan albarkatu na harshe kamar zanen hannu suke kowa da nasa daban. Ko da dukkanin harsuna na duniya sun yi ittifaƙin a ce wa “ruwa” “suna” ne babu saɓani. To kuwa kowanensu ba “ruwa” zai kira shi ba. Wani ya ce “water”, wani “ruwa”, wani “maa’u”, wani “miri”, wani “diyan”, wani ya ce “akwa”, wani “omi” wani ya ce “eyin”[24]. Daga waɗannan misalai za mu ga cewa, koyar da wani harshe cikin wani harshe a ƙarshen dabirtar duk ga fasara za ta tsaya. A tsarin ilmi, fasara wani harshe zuwa wani harshe, ba shi ne koyon harshen na haƙiƙa ba, domin masana cewa suka yi, fasara ita ce, ƙoƙarin bayar da makusanceyar ma’ana, da za a iya fahimtar abin. Don haka suka kasa fasara zuwa:
a)       Fasarar baƙi-da-baƙi
b)      Fasarar mai ‘yanci
c)       Fasarar nan take
A cikin ilimin fasara, kowace irin fasara masani ya zaɓa, ba zai fito da ruhin madarar ma’anar harshen asali ba, sai dai a yi hasashe. A ƙarshe, za a taras da tsofafin kalmomi da kalmomi na al’ada da kalmomi na fannu/sana’a da ɓoyayyun kalmomin karin harshe da daɗaɗɗun kalmomin aro da kalmomin batsa da tsokana da wasannin motsa jiki da waƙe-waƙe da kirari da karin magana da salon magana da gatse da barkwanci su kasa samun yalwatacciyar fasara da ta fito da ruhinsu[25]. Idan tussan magana na adabin gargajiya sun lahanta, nahawun kowane ɓangare na harshe zai samu taɓuwa, a wayi gari kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabulu. Dubi waɗannan ‘yan misalai da ruhin ma’anonin fasarar da suka samu:
Larabci:       Wabilun
Hausa:         Ruwa kama da baƙin ƙwarya
Turanci:      It rains cats and dogs

Larabci:       Laisal khabaru kal iyaani
Hausa:         Gani ya kori ji
Turanci:      Seeing is believing
A cikin waɗannan misalai, rashin samun jituwan kalmomi bi-da-bi wajen fito da ma’anarsu a harsunan shi ya tabbatar da cewa, ma’anar fasara gajeruwa ce. Wani harshe ba ya biya wa wani harshe buƙata domin Alhaji Ɗanmaraya Jos cewa ya yi:

Jagora: Yaro ba ya ɗaukar yaro
          : Sai dai rungumanni mu faɗi
A irin hasashen da na gabatar, a ɗauka ana son koyar da Bature ko Balarabe ko Buzu ko Bayarbe Hausa, yaya za a fasara masa waɗannan ya samu ƙoshin ma’ana wadatacciya yadda Bahaushe zai ji?
·         Jarƙaniya
·         Tsakin tsakuwa
·         Kirɓin gumbar makauniya
·         Tumu/daƙuwa/ƙuli-ƙuli/baduhu /zana/kau-da-bara/ƙago/sagau/gaabaa
Idan aka tunkari taskar harshe ta sautuka da kalmomi masu yi wa juna shigan gizagizai za a samu salon magana, gagara Gwari, ko ƙarangiya. Duk yadda aka nuna ƙwarewar harshe, fasara ba ta bayar da gansasshiyar ma’ana mai ruhi irin ta harshen asali. Idan aka bijiro wa Bahaushe da wannan Turanci yaya zai mayar wa Bahaushe da gami a ji tangam! Irin na mai zuwa Haji da ya gamu da Annabi (SAW) a ji harafin “f” yadda take kaɗawa a Turanci?
·        First Friday, February fifteen fifty five further Frances fride four festival fish for four fathers from France.
Yaya za a bai wa Bature ma’anar wannan. Cikin lugudan harafin “k” yadda yake a Hausa?
·        Da Kalla da abokin Kalla sun ta fi kallon kalangu, sai aka kalle Kalla mari wajen kallon kalangu, aka gaya wa abokin Kalla, “Maza kalla gida da gudu ka gaya wa matar Kalla ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu”. Ya kalla da gudu ya kalla wa matar Kalla kira da cewa, ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu ta kallo kara, ta kallo da gudu da kallabi, domin ta kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu. Ta kalli taron kallon kalangu domin kallo wanda ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu, da ganin ta da kallanlen kara ya kalla da gudu, kallo ya koma ga Kalla da abokin Kalla da kallallen karan da ta kallo domin kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari.
Kaɗan ke nan daga cikin wahalolin da ba za a kai matsayar yadda za a fice su ba, idan aka nace ga koyar da mai harshe harshensa cikin wani harshe.

Mafarin Koyar da Hausa Cikin Turanci
Cikin manyan harsunan duniyar wajen ƙasar Hausa ba Turanci kaɗai Bahaushe ya fara cin karo da shi ba. Wace martaba Turanci zai gwada wa Larabci da Girkanci da Latinanci da Hindi da Urdu da Faransanci? Masu waɗannan harsuna sun riga Bature leƙa ƙasar Hausa, sun riga shi sanin albarkatun da ke cikin ƙasar na ƙasa da jama’a da sauransu. Me ya sa, ba su mamaye harshen Hausa ba, suka maƙure shi, suka shaƙe shi, suka cukuikuye shi a keji, suka hana shi ‘yancin yawo da ƙafafunsa? Dalilan da suka sa haka kaɗan daga cikinsu, su ne:
i)                   Turanci ya zo wa ƙasar Hausa da fuskoki daban-daban. Fuska ta farko an zo da niyyar buɗe ido cikin rigar leƙen asiri. Wanda duk ke son ya miƙe ƙafafunsa, ya yi munafunci da azuzanci da makirci da maƙarƙashiya da zagon ƙasa ga wata/wasu al’umma, dole sai ya koyi harshensu. Haka kuma, zai tilasta a koyi harshensa domin ya riƙa jin wainar da ake toyarwa[26]. Wannan shi ne babban mafarin ruɓaɓɓen tunanin.
ii)                Muradun Turawa su bazu, al’adunsu su mamaye ƙasa, a Turance mutane da harshe da al’ada. Cikin wannan dabarar ce za a cusa musu addinan Nasara su rungume shi hannu biyu domin an fi ƙarfinsu. To! Cikin rigar addini za a shimfiɗa mulkin mallaka cikin ruwan sanyi. Littafin Allah a hannu dama, a hannu hagu bindiga, a zuci mulkin mallaka. Haka ko aka yi[27].
iii)             Cunkoson da ƙasashen Turai suka yi da kaya jibge babu masaya. Yunwa da fatara da rashin aikin yi na yi wa mutane barazana, shi ya haifar da neman mafaka a ƙasashen Afirka ido rufe. Don haka, an fito cin ranin da babu ranar komawa, ko’ina aka ga wurin zama za a yi mannanu ƙuda ya faɗa ƙwaryar alewa. Ashe ke nan, dasirar koyar da Bature Hausa domin ya samu mafaka, ita ce ta haifar da koyar da Hausa cikin Turanci domin Turawa su amfana da nahawunta, ba don amfanar da Hausawa ba[28].
iv)              Rahotannin da Turawan leƙan asiri ke rubutawa cikin harshensu suke rubutawa. Waƙilansu da ‘yan barandarsu da suka koya wa harshensu domin su farauto asirranmu a rubuce a adana musu. Asirranmu cikin harshenmu suke. Dole a fasara su, a rubuta su cikin Turanci. Mai fasara dole ya ƙware ga harsuna biyu: harshen asali da harshen bayar da fasara. Tushen koyar da Hausa cikin Turanci a nan ta samo asali, domin Turawan leƙen asiri su tabbatar da cewa abubuwan da aka fasara musu a rubuce daidai suke[29].
v)                Bayan da ‘yan leƙen asiri suka gama aikinsu, tunanin kutsowa ƙasashen Afirka ya zo a zuciyar Turawa. Tunanin ya haifar da kafa sansanin koyar da harsunan Afirka a Turai musamman Ingila, Jamus, Faransa da Rasha. Hausa na daga cikin harsunan da ke sahun gaba a wannan tunanin. Sojojin yaƙi da ‘yan leƙen asiri da Mishon da Ma’aikatan hukumar mulkin mallaka aka fara koyar da su Hausa tun a ƙasashen Turai. Waɗannan abubuwa ba don ceton harshen Hausa aka tsara su ba, don ceton masu son su cuci Bahaushe ne. Asalin koyar da Hausa cikin Turanci domin amfanar da Turawan da ke koyon Hausa ne. Kai da ke da harshenka, wace dambala za ta sa a aro wani harshe a koyar da kai shi, in ba renin wayo da rashin kishi da rashin sanin ciwon kai da ɓata tunani da mayar da gaba baya da ɗaure wa ƙarya gindi ba?

Uzurin Masu Ra’ayin Aron Hannu:
Ɗalibai da ke da ciwon koyon Hausa cikin Turanci ban ga laifinsu ba, domin kowa da bukin zuciyarsa. Duk da haka, tilasta mutum ya ciwo bashin abin da yake da shi, ko ya yi aron abin da ya mallaka, wata irin dambala ce makusanciyar manomin da ya saya abincin da ya noma da kuɗin aljihunsa, ya biya kansa da kansa. Daga cikin uzurran da masu ganin dole a koyar da Hausa cikin Turanci ke faɗa akwai:
i)                   Turanci ne harshen ƙasa, dole kowa ya rungume shi a kowane aiki da ya danganci hukuma. Karatun Hausa na cikin tsarin hukuma, dole a yi shi a Turanci[30].
ii)                Babu wani takamammen aikin nahawu na Hausa da aka yi a rubuce, don haka, dole a ari na Turanci a isar da saƙo[31].
iii)             Idan ana son a koyar da Hausa cikin Hausa, za a ci karo da matsalolin fasarar wasu kalmomin ilmi (fannu) da babu yadda za a sarrafa su zuwa Hausa[32].
iv)              Karatun Hausa ilmi ne kamar sauran ilmuka, dole a koyar da shi a harshen da ake koyar da sauran darusan karatu a makarantunmu. Wai! Yin haka, zai sa ta samu karɓuwa a fahince ta[33].
v)                Sun ce, akwai ƙarancin wadatattun kalmomi na Hausa da za su iya wadatar malamin Hausa ya koyar da Hausa cikin Hausa[34].
vi)              Ana hangen barazanar kimiyya da cigaban ƙere-ƙere zai baro Hausa da Hausawa a baya idan aka nace da koyar da Hausa cikin Hausa[35].
vii)           Uzurin wasu masu koyar da Hausa cikin Turanci shi ne, malaman da suka ba su digiri ko suka duba babban digirinsu ba Hausawa ba ne, sun fi son abin cikin Turanci. Daga nan suka zaƙe suka fi mai kora shafawa[36].
viii)         A gaskiya, da yawa daga cikin masu son a koyar da Hausa cikin Turanci ciwo biyu ke damun su. Na farko, a ce sun iya Turanci. Na biyu, ka da a ce, ba su iya Turanci ba. Na uku, suna ganin sun waye, yin Hausa gidadanci ne[37].
ix)              Wasu sun ce, wai! Hausawa sun kasa tsayi su yi wani takamammen aiki na yadda za a fuskanci karatun Hausa cikin Hausa. Dole idan yadda aka so ba ta samu ba, a yi yadda ba a so, a zauna lafiya[38].
x)                Wata hujjar rashin hujja ita ce, wai akwai harsunan Nijeriya barkatai da babu littattafan da za a koyar da su da harshensu na asali. Idan aka ce, a koyar da Hausa cikin Hausa, su kuwa yaya za su yi? Domin a daidaita tunanin haɗa kai, sai a koma Turanci gaba ɗaya, in ya so a yi marus, haihuwan guzuma ɗa kwance uwa kwance[39].  
xi)              Ga alama, hatta da malaman Hausa akwai masu jin taƙaicin Hausa saboda sauƙin ta, da saurin fahintarta da ake yi. Zama ɗaya a iya ta, a fahince ta, a samu manyan digirin ƙoli ciki, abin na ci musu tuwo a ƙwarya. Da an bijiro da maganar koyar da Hausa cikin Hausa, sai idanu su yi ja, a dinga tayar da jiyoji, da karya gumi, hasada ta rufe ido, a dinga zubar da hawaye wai wasu za su ci arziki cikin ruwan snayi. Kaico! Ai rabon kwaɗo ba ya hawa sama[40].
Ban ce, waɗannan su ne kaɗai ra’ayoyin masu ganin a koyar da Hausa da Turanci ba. Duk da haka, su na iya kalatowa da rairayowa yayin da nake fafitikar harhaɗa wannan muƙala. Ko da da wasu daban, mu a Nijeirya ta Arewa waɗannan su ne jigajigan hujjojin. Idan muka yi riƙo da hujjojin su irin hasashen wasu abubuwa da na yi wa taken:

Hasarorin da Aron Hannu zai Haifa
A tsarin koyar da harsunan duniya, ba baƙon abu ba ne harshe ya ɗauki nauyin kansa a fagen koyar da duk abin da ya shafe shi. Baƙon abu shi ne, koyar da nahawun wani harshe cikin nahawun wani ba shi ba. Idan aka ce, a nace ga aron hannu, dole a shirya karɓar hasarar da ba za a san ranar gama jajenta ba. Abin da mu ɗaliban harshen Hausa da malamanmu suka hanga shi ne, za mu yi hasarar:
i)       Ruhin harshenmu na asali da ke ƙunshe cikin nagartattun kalmomin gado. A ƙarshe, kalmomin da suke gama gari ga ma’ana kawai za a riƙa amfani da su a watsar da waɗanda sai ‘yan gado suka sani. Da sannu harshenmu ya shiga cikin harsunan da ake yi wa suna “harsunan da ke cikin haɗarin salwanta”.[41]
ii)      Sautukan harshenmu da suke taƙadaru ga waɗanda ba ‘yan asali ba, irin su tagwayen baƙaƙe da wasula da baƙaƙe masu ƙugiya za a durƙusar da su. Yadda duk aka samu dabarar samar da su saboda ana son magana da rubutu da Hausa a wancan zamani, haka za a ragaitar da amfani da su idan Turanci ya karɓi tutar koyar da nahawun Hausa[42]. Allah Ya tsare mu Ya tsare wuyan raƙuminmu in ji Buzu da ya ga mai maƙoƙo.
iii)     Za a ci amanar karuruwan harsunan Hausa da suka taru suka gina harshen Hausa suka shimfiɗa daular ƙasar Hausa. Cikin ƙoƙarin daidaita Hausa ta dace da buƙatun gwannati a fagen koyarwa da daidaita ma’anonin kalmomi da za su yi canjaras da na Ingilishi dole a kushe wani karin harshe a kan wani. Idan na asali su salwanta Hausa ta yi hasarar su[43].
iv)     Bunƙasar harshe da ƙara ɗaukakarsa da yaɗuwarsa tana tare da tsarin salon rubutunsa da yadda za a adana shi a rubuce. Idan za a koyar da Hausa cikin Turanci rubutun Turanci zai ɗaukaka na Hausa ya rushe a farfajiyar ilmi, daga nan sai sare-saren salwanta. Me ya ɗaukaka harsunan Turai ba salon rubutu da aka adana su da shi ba[44]?
v)      Harshen Hausa da al’adun Hausawa sun zama wa Turawa alaƙaƙai tun zamanin cinikin bayi da mulkin mallaka. Duk ƙasar da ta ratsi duhun jahiliyyar mulkin mallaka za ta yi hasarar harshenta da nagartattun al’adunta da asirranta. Wannan maƙasudin ya kasa cin gira a ƙasar Hausa. Duk da Turance Hausawa da aka yi da bokonta su, da bautar da su, da rikiɗa musu addinai, an kasa murƙushe harshensu da al’adunsu na gargajiya. Babu abin da ya taimaka wa Hausawa a kan haka face riƙo ga harshensu damaƙui. Yau da rana tsaka, bayan mun ci nasarar yaƙi, a ba mu kuturun bawa, kurma, maƙaho, mahaukaci gigitacce da shi. Matuƙar aka bai wa Turanci amanar koyar da Hausa to, Turanci ne ake koyarwa ba Hausa ba[45].
vi)     Sunan wata babbar hasara ɓanta-ɓakatantan, ba a ga tsuntsu, ba a ga tarko. Masu koyar da Hausa cikin Turanci matuƙar ba Turawa ba ne, ba nagartaccen Turanci ɗan asali za su koyar da yara ba, yaye-yaye ne cikin kuri da gayanci, a wayi gari yara ba su iya nahawun Turanci ba, su manta da nasu na asali na Hausa. Bahaushe na cewa, ba ka bayar da abin da ba ka da. Turanci ba harshenka ba ne, ya ya za ka aro shi ka koyar da masu harshe harshensu da harshen da ba nasu ba? Da kai, da su, duka baran uwar Nuhu kuke yi. Assha! Wannan ita ce musibar da ke damuwar ɗaliban nazarin Hausa a ƙarƙashin wannan ruɗaɗɗen sabon tunani[46].
vii)    Fahintar harshe a ilmi shi ne, a naƙalci nahawunsa a magana da sarrafa shi a  rubuce cikin ƙoshin kalmominsa na asali. Idan za a koyar da Hausa da Turanci ɗalibin Hausa zai yi hasarar ɗimbin kalmomin Hausa masu wadatattun ma’ana ya faɗa cikin ƙaddarar ƙila-wa-ƙalan Turanci. Idan aka shiga wannan yanayi babu makawa sai an yi saki zari kama tozo. Wanda ya karanto harshe ya rasa wadatattun kalmomin da zai yi rubutu ya isar da saƙo a cikinsa bai amfanar da harshen da komai ba. Amfanar da harshe shi ne, raya kalmominsa, da adana su a adabi da rubutu. In babu ƙira me ya ci gawai? Masassara ke nan daga nan sai doguwar suma sai baƙuntar kushewa[47].
viii)   Wata hasara ita ce, renon takaici cikin takaici a rayar da takaici. Turanci kishiyar duk wani harshe ne da ya yi wa mulkin mallaka. Turawa kuwa ba su taɓa ganin kan wanda suka mallaka da gashi. A koyaushe uban gida son yake a ce, bawansa ya riƙa kwaikwayonsa domin ya tabbata bawa. Da wace hujja za mu rayar da harshen wasu wanda da shi aka zalunce mu, mu watsar da namu? Koyar da Hausa cikin Turanci rayar da harshen Ingilishi ne da daƙusar da martabar Hausa da Hausawa. Haba! Lokaci ya yi a doki garwa belbelu su tashi su san wurin da dare ya yi musu.

Bazar Hausa a Farfajiyar Ilmin Ƙarni na 21
A tsarin karatun Hausa na matakai masu zurfi an haɗu a kan ɓangarori uku. Al’ada, Adabi da Harshe. Kowanne daga cikinsu wani babban kandami ne da za a iya yi wa suna, daji ba ka da gambu. Tattare da haka, a imaninmu na ɗaliban Hausa da malamanmu masu kishin cigaban harshenmu, duk aikin da aka yi a kan wata fasaha ta harshen Hausa ko Bahaushe, Hausa aka yi wa aiki kuma aikin na nan a cikin farfajiyar karatun Hausa. Ai ba Hausa kaɗai ce harshe a Afirka ba. Ba ita kaɗai ce harshe a Nijeriya ba. Ba ita kaɗai ce harshe a Nijeirya ta Arewa ba. Ba ita kaɗai ce harshen da ake amfani da shi a cikin ƙasarta ba. Me ya sa ta fi su saura kere a fagen ilmi? Idan dai mun aminta da, karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani. To! Duk wani ƙwazon Bahaushe aka sarrafa cikin ilmi, Hausa ce ake yi wa aiki, ma’aikacin kuwa, Hausa ce ya karanto. Ku biyo ni, amma ku taya ni duba baya makaho ya so tsegumi:
i)       A ɓangaren harshen Ingilishi da Ilmin Harsuna fitattun kundayen manyan digirin Ph.D da Hausawan da suka karanto Ingilishi suka yi a kan Hausa sun ninka waɗanda aka yi a kan Turanci yawa. Mafi yawan Hausawan da suka karɓi digirin Ph.D na Turanci harshen Hausa suka yi wa hidima[48].
ii)      Haka kuma, waɗanda suka karɓi digirin Ph.D a fannin Ilmin Harsuna Hausawa da wasu maƙwabtansu Hausa suka yi wa hidima[49].
iii)     Malaman Hausa na farko da suka assasa karatun Hausa ba Hausa suka karanta ba, amma ita suka yi wa hidima a kundayensu na Ph.D. Suka dawo suka sauya akala don kishin Hausa.[50]
iv)     Sassan ilmi na fasaha irin Tarihi da Tattalin Arzika da walwala da sauransu. An yi fitattun ayyuka a kan Hausa da Hausawa[51].
v)      A kimiyya, an samu ayyuka da kimiyyar gine-gine da lissafi da sauransu[52].
Waɗannan aikace-aikace, sun isa su tabbatar da cewa, Hausa ta cancanci a koyar da ita cikin Hausa, domin Hausawan da suka ilmantu a fannoni daban-daban, da ita suka yi bara ga ayyukkansu. Ban yi zaton akwai wani harshe daga cikin harsunan Nijeriya da yake da wannan fice a duniyar ilmin wannan ƙarni ba irin Hausa. Ba wai harshen Hausa ba, yau babu wani fanni na ilmi da zai buwaya a Hausantar da shi ba, sai dai idan ba a so ba[53].
Bazar rawar Hausa cikin Hausa ta ci nasara a farfajiyar ilmin ƙarninmu. A halin yanzu, masu takardun shaidar Difloma da Ensi’i (NCE) a Hausa sun nunka na kowane harshen Nijeirya da ake koyo a matakan. Ban yi na babban mahaukaci ba, idan na ce, masu babbar takardar shaidar digiri (BA) na Hausa da digirin ilmi a ɓangaren Hausa B.A ed (Hausa) sun fi na kowane harshe yawa a Nijeriya. Babu shakka, ƙididdige masu digirin ƙwarewa na MA da Ph.D a Hausa, sai an nemi tiamakon hukuma. A matakin koyo na ƙarshe, Hausa na da Farfesoshi fiye da talatin ‘yan ƙasa, kuma ‘yan gida Hausawa da ke a Jami’o’i da Cibiyoyin nazari da bincike daban-daban[54]. Waɗannan dalilai su suka tilasta a koyar da Hausa cikin Hausa domin babu abin da Hausa ta rasa.

Hausa Cikin Hausa:
Babban matsalar da ke haddabar harsunan cikin gida ita ce, hana musu ‘yancin taka rawarsu da kansu a fagen koyonsu da koyar da su da rubuce-rubucen da ya shafe su. Farfesa Dalhatu Muhammadu Zariya[55] na daga cikin jigagan ganin dole Turanci ya sake wa Hausa mara a koyar da Hausa cikin Hausa. Yekuwarsa ta samu karɓuwa ga fitattun ɗalibansa, Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo[56]. Irin gudunmuwar da suka bayar na ƙwato wa Hausa ‘yancin koyar da ita cikin Hausa ita ce gajiyar da muke ci a yau. A nan, tilas a anbaci Farfesa Muhammadu Hambali Junju, wanda saboda tsananin kishinsa ya rubuta Rayayyen Nahawun Hausa[57]. Ɗalibansa Dr. Ahmadu Bello Zariya da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai kowanensu ya fito da littafin nahawun Hausa cikin Hausa[58]. Domin raya harshen Hausa cikin Hausa, Malamin Malaman Hausa, Farfesa Dauda Muhammad Bagari, ya wallafa gawurtaccen littafin nahawu mai take Bayanin Hausa. Waɗannan ayyuka sun rufe bakin masu ƙorafin rashin kayan aiki.
Hausa cikin Hausa ta yi tasiri a kundayen karɓar digirori na BA da MA da PhD. Jami’o’in Bayero da Ahmadu Bello da Usmanu Ɗanfodiyo da Maiduguri sun yi abin a zo a gani. Babban digirin farko na PhD da aka fara cikin Hausa shi ne na Farfesa Sa’idu Gusau (1989) na biyunsa shi ne, na Aliyu Muhammad Bunza, (1995) na uku, Farfesa Ibrahim Aliyu M. Malumfashi (1999). Daga bayansu an sami fiye da kundayen PhD talatin cikin Hausa. Wannan ya nuna an samu cigaba sosai, kuma cigaban sai daɗa ƙaruwa yake yi. Babu shakka, wannan na ba da haske gare mu cewa, fafitikar da ake ciki ta tabbatar da koyar da Hausa cikin Hausa, haƙa ta kai ga wadataccen ruwa. Abin da ya rage shi ne, a sake fito wa Turanci Hausance, a fara tunanin gabatar da darusan ilmin da ake tinƙaho da shi a ƙarninmu cikin Hausa.

Sakamakon Nazari:
Martaba da darajar ilmi na kowane fanni iri ɗaya ce, amfaninsa a fahince shi a amfana da shi. Daga cikin abubuwan da suka tanye ƙasashe masu tasowa ga cigaba akwai matsalar harshen da ake bayar da ilmukan da ke sa ci gaba. Tilasata wani baƙon harshe a matsayin harshen ƙasa da ƙoƙarin kururuta shi da fifita shi ga harsunan gado shi ya tauye banƙasar ilmi a ƙasashen da suka yi wa harsunan mulkin mallaka mabayi’a ta har abada. Wannan ɗan ƙwarya-ƙwaryan bincike ya hango:
i)                   Buƙatar sake jaddada koyar da Hausa cikin Hausa da rubuta kundayen binciken Hausa cikin Hausa. A fara tunanin bayar da kyauta ga kundin PhD mafi rubutuwa a tantagaryar Hausa
ii)                Akwai bukatar farfaɗo da, ko kafa hukumar fasara mai ƙarfi da za ta kula da ayyukan fasara na ciyar da fasara ayyukan kimiyya da ƙere-ƙere da kiyon lafiya domin a sama wa ‘ya’yanmu nagartaccen ilmi.
iii)             Binciken ya hango, babu harshe daga cikin harsunan Nijeriya da ke da masana da manzarta a fanninsa irin Hausa. Hausa ita ce kan gaba ga dukkanin harsunnan Nijeriya. Babbar matsalar kawai ita ce samun marasa kishinta daga cikin maciya gajiyarta.
iv)              Akwai buƙatar buɗa sassan karatun Hausa a jami’o’in ƙasashen Afirka ta Yamma musamman Nijer da Benin da Togo da Ghana da Senegal da Bokina da Mali. Yin haka, zai bai wa wasu ƙananan harsuna marasa galihu farfaɗowa idan suka dafi kafaɗar Hausa. Yadda za a sayar da wannan hajar shi ne, kiran tarukan ilimi na Hausa a ƙasashen domin su ji irin wainar da ake toyawa.
v)                A halin yanzu, a wannan ƙarni, lalurar koyar da Hausa cikinTuranci ta kau. Zancen rubuta kundin binciken Hausa cikin Turanci bai taso ga manazarci Hausa ba a sashen da ake koyar da Hausa ba. Duk malaman Hausa su tashi tsaye na ganin an kawar da duk wata matsalar da za ta yi wa koyar da Hausa ikin Hausa barazana.

Naɗewa:
        Hausawa na cewa, babu mai nunin gidansu da hannun hagu. Lallai ƙafafun wani ba su yi wa wani tafiya. Hakiƙa, kayan aro ba sa ado, domin komai ta daɗe ƙarshen ruwa kware. Na yarda da faɗar, tare da ni aka ci, ya fi gaba gare ni aka ci amfanin hanji. Tarihin saduwar Bahaushe da Turanci ba mai daɗin sauraro ba ne, domin kare jini biri jini aka rabu. To! Rabuwar da aka yi dutse hannun riga ina amfanin a ci gaba da renon musabbabinta? Buƙatar harshen na zama harshen ƙasa, ko harshen ilimi, dole ya kasance yana da jama’a na asali masu yawa da masu sha’awarsa. Haka kuma, ya kasance mai wadatattun kalmomi da za su wadatar a kowane bagire ake leƙo shi. Samun daidaitaccen tsarin rubutu wata martaba ce da ake so gare shi domin ilimi da siyasar rayuwa dole sai da rubutu. Me Hausa ta rasa a cikin waɗannan sharuɗa? Me Turanci zai yi wa Hausa doro a nan? Babu wani harshe na duniya da kalmominsa suka wadaci buƙatar zamaninsa. Babu harshen da ya bunƙasa ba tare da are-aren kalmomi da ƙirƙire-ƙirkirensu ba. Babu harshen da zai shiga zukata da hukuma ba tare da zawiyyar boko ba. Duk wani harshe da duniya zamaninsa ta ji zarmoɗarsa, sun yi auren zobe da ‘yan jarida. Duk wani baƙon harshe bai san budurcin Hausa ba. Larabci ya tarar da ita ɗakin mijinta. Rubutun ajami ya riske ta da tagawaye. Turanci da jikokinta ya gan ta. Samari! Ka da a ci ka da burga, idan za ka yi aure, ga shawaran makaɗa Ɗan’anace:
Jagora: Mai son miya ya auri Tsohuwa
          : Mai son shimfiɗa ya auri budurwa,
          : Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
                             (Waƙar Shago)
Na zaɓa maka isassa ita ce “Hausa”. Isassa na iya kasancewa da kowace irin sifa kake so.

MANAZARTA

Abdullahi, M.D. 2011. A Study of Writing and Development of TAFI,
Fatima Publishing, Katsina.

Adamu, M. 1975. Hausa Factor in West African History, Zaria: ABU, Press.

Amfani, A.H. (da wasu) 2012, Champion of Hausa Cikin Hausa A
Festschrift in Honour of Dalhatu Muhammad, ABU Press, Zaria.

Bagari, D.M. Bayanin Hausa, Rabbat, Morocco.

Bangbose, A. 1977. Language and Nation: The Language Question in Sub-
Saharan Africa, Edingburgh, University Press.

Birnin-Tudu, S.Y. 1990, “Nazari Kan Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa,”
Kundin digirin MA, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Bivar, A.D.H. 1960. “A dated Qur’an from Borno” Nigerian Magazine, No.
65, Lagos: Federal Ministry of Social Development, Youth, Sprots and Culture, Lagos.

Bunza, A.M. 2000, Rubutun Hausa, Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa,
Don Masu Koyo Da koyarwa, Ibrash, Lagos.

Bunza, A.M. 2008, Narambaɗa, Ibrash, Lagos.

Bunza, A.M. 2013. “Don Me Ake Karatun Hausa?” Cikin Harsunan
Nijeriya, Volume XXIII, 2011-2013 CSNL, BUK, Kano.

Clarke, P.B. 1982, West Africa and Islam, London.

Dressler, W. 1981, “Language Shift and Langauge Death, a Protean
Challenge for the Linguist”. Folia Linguistica.

Dorian, N.C. 1981a, Language Death: The Life Circle of a Scottish Gaelic
Dialect, Philadelphia.

East, R.M. 1952. A Vernacular Bibliography for the Languages of Northern
Nigeria. Zaria: NNPC.


Fagge, U.U. Ire-Iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni, Benchmark
Publishers Limited, Kano.

Fischer, S.R. 2000. A History of Writing, Reaktion Books.

Galadanci, M.K.M. 1976, An Introduction to Hausa Grammar, Longman
Nigeria.

Gazali, K.A.Y. 2005, The Kanuri in Diaspora, The Contributions of Kanen-
Borno ULAMA to Islamic Education in Nupe and Yorubalands, CSS Press, Lagos.

Jinju, M.H. 1981, Rayayyen Nahawun Hausa, NNPC Zaria.

Miller, W. 1971. “The Death of Language or Serendipity Among the
Shoshani.” Anthropological Linguistics 13:114-120.

Omar, S. 2013, Modibbo Kilo, ABU Press, Zaria.

Oyetade, S. 2007. “Language Endangerment in Nigeria.” Perspectives on
Akolo Languages of the South-West” Dorian, N. (ed) International Journal of Society and Language, 184, pp. 169-184.

Rufa’i, A. 1977 “Grammatial Agreement in Hausa”. PhD Thesis
Georgetown University, USA.

Rodney, W. How Europe Underdevelop Africa.

Sakkwato, A.B. 2011 Ginin Jimlar Hausa, Jagora ga Mai Nazarin Harshe,
Mathi Production Sakkwato.

Sani, M.A.Z. 2011, Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa, ABU, Press
Zaria.

Spender, D. 1980. Man Made Language, London Rutledge and Kegan Paul.

Tsafe, B.A da Sadi, S.A. 2010 Hanyar Binciken Ilmi a Hausa, Farin Batu
Press Gusau.

Ubah, C.U. 2001, Islam in Africa-History, Baraka Press, Zaria.

Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe, Garkuwa Media,
Services Sokoto.
Yar-Aduwa, T.M. 2008, The Syntactic adn Semantic Description of the
Hausa Quantifiers, Clean Impression Ltd, Kano.

Zariya, A.B. 1981, Nahawun Hausa, NNPC, Thomas Nelson, Nigeria
Limited.

Zaruƙ, R.M. Aikatau a Nahawun Hausa.


[1] .            Rashin Farfesa Muhammad Kabir Galadanci da Farfesa Ibrahim Yaro Yahya da Abdullahi Kafin
Hausa da Habib Alhassan Gusau da Malam Zarruƙ da Mahbub Alƙali da Malam Isa Kurawa
(Kakan Malaman Hausa) da Farfesa Muhammadu Hambali Junju ba ƙaramar giɓi ta bari ba ga
fagen nazarin Hausa.
[2] .            Don ƙarin bayani a dubi, Bunza, A.M. Narambaɗa, IBRASH, Lagos.
[3] .            A hasashen masana irin Farfesa Mahdi Adamu Ngaski Kalmar “boko” ‘yar gida ce, tun fil azal
Bahaushe na da “biri boko” da “amaryar boko”. Don haka, boko na nufin “ƙarya”. A hangen ɗaliban ɗalibansu irin su Aliyu Bunza, kamar “boko" Baturiya ce, asalinta daga Kalmar “book” ne da ake yawanta ambata a makarantar.
[4] .            A mafi yawar al’umma na Afirka da Asiya da wasu ƙasashen Larabawa ana ce da shi “ilmin
takarda”. Hausawa ma, ɗan takarda suke ce wa ‘yan boko gabanin Kalmar boko ta karɓe tuta.
[5] .            A dubi, Dorian, N.C. (1981a) Language Death: The Life Circle of a Scottish Gaelic dialect,
Philadelphia.
[6] .            A dubi, Dressler, W. (1981) “Language Shift and Language Death, a protean challenge for the
Linguist”. Folia Linguistica 15:5-25.
[7] .            Ba Hausawa keɗai ke da shi ba. Akwai shi a Igbo da Kanuri da Yoruba da Igala da Nupe da duk
harsunan Nijeriya da suka rungumi Turawa.
[8] .            Nassin Alƙur’ani Ya tabbatar da cewa, Allah Ya ƙagi ɗan Adam kuma Ya saka shi a zuriyar
zuriya da ya arzuta su da harsuna domin su san junansu.
[9] .            Idan ya ƙware da iya tsara magana ko yana da yawan surutu akan ce yana da “baki”.
[10] .           Waɗannan ra’ayoyin suna komawa ga irin fahintar da Darwin ya yi wa halittar ɗan Adam ta cewa
daga birai aka fara. A dubi Tarikh vol. 1 No. 3.
[11] .           A dubi, Alhaji Sa’ad Haruna Gobir, (1982) Kunna Ya Girmi Kaka. Ingantaccen Tarihin Hausa.
[12] .           A dubi, Sa’adiyya Omar, 2013, Modibbo Kilo ABU, Press, Zaria.
[13] .           Ɗan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule ya yi hira da gidan Rediyon BBC, 1982 da 2000 ya
ambace shi. Mal. M.S. Ibrahim ya ƙarfafa maganar da shi da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya.
[14] .           Mun gano wannan a wani binciken haɗin guiwa da na yin a wani masanin ajamin Barebari
Dmitry da muka haɗu a SOSA, 1997. Mun samu tabbacin haka a wani Ƙur’ani da muka samu a
hannun Wazirin Gwandu na yanzu (2014) takardun rubutun Ƙur’anin sun kai shekara ɗari bakwai
a tarihi.
[15] .           Don ƙarin bayani a dubi, Bunza, A.M. Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa don
Masu Koyo da Koyarwa.  IBRASH, Lagos.
[16].            Don ƙarin bayani a dubi, Clarke, P.B. 1982. West Africa and Islam, London da C.U. Uba, 2001
Islam In Africa-History, Baraka Press Zaria.
[17] .           Don ƙarin bayani a dubi, Birnin Tudu, S. (1990) Nazari Kan Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa, M.A.
UDUS.
[18] .           A dubi, Musa D. Abdullahi, A Study of Writing and Development of TAFI, Fatima Publishing,
Katsina.
[19] .           Hira da Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, Shugaban ƙasar Nijeriya a Jamhuriyya ta biyu a
gidan Talabijin na Tarayya Sakkwato (2010).
[20] .           A wata fasara ana cewa “Vernacula” harshen bayi.
[21] .           Da an ce wa abu “Local” a Turanci an so a ƙasƙantar da shi a takura faɗinsa da bazuwarsa.
[22] .           Ana faɗar haka domin ana ganin ga uwa ake fara koyon harshe. A wajen Turawa wani awon renin
wayo ne ga harshen da ba a ganin kansa da gashi.
[23] .           Idan an ji haka a fagen nazarin harsuna na ilmi ake faɗar haka.
[24] .           Waɗannan misalai duk daga cikin harsunan Nijeriya aka ciro su. Ina ga an ce a samo misalai daga
sauran harsunan? Za a ga iya adadin harsunan, iya adadin sunan ruwa da za a samu.
[25] .           Ko an yi fasara mai kyau ma’anar ba ta shiga jikin mai harshen fasara kamar yadda za ta shiga
jikin mai harshen asali.
[26] .           Da aka matsa kashe Turawan mulkin mallaka a kudancin ƙasar nan, sun kawo dokar dole kowa ya
riƙa tafiya da fitilar a-ci-bal-bal cikin dare. Duk wanda aka kama babu fitila tana ci a hannunsa da dare za a hukunta shi. Wai! Don su gane makasan su. Laccar Aji II a Tarihi tare da S.U. Lawal, Sashen Tarihi Jami’ar Sakkwato, 1984.
[27] .           Wannan ita ta ba Turawan Mishon damar kiristintar da wasu ƙananan ƙabilu a Arewacin ƙasar
nan da Arawan jamhuriyyar Nijar da gundumar Argungu.
[28] .           Don ƙarin bayani a dubi, Walter, R. How Europe Underdeveloped Africa, Ibadan.
[29] .           Rahotannin Mr. Hamper ɗan leƙen asirin Ingila a Iran ya tabbatar da haka. Fasarar Hausa ta
Sa’idu Muhammadu Gusau.
[30] .           Idan haka ne, me ya sa ba a tilasta kowane ɗan ƙasa ya aje harshensa na gado ba ko a cikin
gidansa ya yi Turanci? Duk abin da bai sa aka yi wannan dokar ba, shi zai ba da damar karantar da Hausa cikin Hausa.
[31] .           Wayyo! Sun manta babu harshen da ya tarar da nahawunsa a rubuce. Kowane harshe a doron ƙasa
shi ya zauna ya tsara nahawunsa a rubuce. Ai Turanci bai tarar da ko littafi ɗaya na nahawun Turanci saukakke ba! Yaya aka yi? Yadda duk aka yi, haka za mu yi.
[32] .           Haka Turanci ya sha wahalar, har yanzu ya kasa ciwo kan matsalolin amma ya ci gaba da aiki.
Hausa ma ta shirya haka.
[33] .           Ƙasashen da ke koyar da ilmi da harshensu fa? Me ya fi daɗi da irin yadda ƙasashen Asiya da
Larabawa da Rasha ke koyar da ilmi da harshensu?
[34] .           Ƙarya suke yi, a tambayi Rev. G.P. Bargery a shekarar 1933 ya tara fiye da kalmomi miliyan
ɗaya ya tace ya yi babban Ƙamus. Shi ne gawurtaccen ƙamusun Hausa na farko.
[35] .           Ina! Wace ƙasa ta fi China da Rasha da Indiya da Masar da sauran ƙasashen duniya masu amfani
da harshensu ci gaba yau. Kai! Wawa hatta da wayar hannu yanzu China ke yi wa duniya Limanci ita da Japan.
[36] .           To, ai kai Bahaushe ne. digirin Hausa aka ba ka. Malaminka harshensa yake yi wa yaƙi. Kai! Me
zai hana ka yi wa naka? Shi ke nan, in Malaminka ya ga Annabi ka gan shi, in bai gani ba, kai ka ci bone?
[37] .           To! Wannan ita ce babbar hujja. Babu wata bayan ta.
[38] .           Ai ba Aljannu da tsuntsaye za su yi aiki ba. In kowa ya yi kamar yadda kuka yi, Hausa ba za ta
kawo yau da rai ba.
[39] .           Wannan ra’ayin Turawan mulkin mallaka ne aka ara musu. A gai da Mishon.
[40] .           Mun ga haka a bayyane. Allah Ya taya shanu cirri.
[41] .           Don ƙarin bayani a dubi, Yakasai, S.A. 2011, Jagoran Ilmin Walwalar Harshe Garkuwa Media,
Kaduna.
[42] .           Ta haka Turawa suka ɓata muna sunayen garuruwanmu: Dubi wai, Zaria, Kankia, Zagga,
Chafe/Tsafe d.s.
[43] .           Haka ake yi wa karin harshen Sakkwato da Arabci da Gimbananci da Gobarci da sauransu.
[44] .           Me ke aukuwa a yau ba haka ba?
[45] .           A dubi rayuwar ɗaliban Hausa da aka yi wa wannan cutar. Ba su iya Hausa ba, ba su iya Turanci
ba.
[46] .           Barka da samun nasarar tabbatar da gushewar sa a karatun Hausa a Nijeriya.
[47] .           Abin da ake so ke nan ga harshen Hausa. Allah Ya tsare ta.
[48] .           Irin Prof. Bello Bada, Prof Asabe Kabir, Prof Malami Buba, Prof. Tsiga sun taka rawar gani.
Allah Ya taimake su.
[49] .           Irin su Prof. Junaidu, Prof. Mukoshy, Prof. Mukhtar Prof. Adeyanju da sauransu.
[50] .           Irin su Prof. Dalhatu, Prof. Galadanci, Prof. Bagari, Prof. Hambali, Prof. Danladi Yalwa, Prof.
Audu Yahaya Bichi, Prof. Maikuɗi Ƙaraye da sauransu.
[51] .           An yi PhD a kan adashin Bahaushe a UDUS, a fannin tarihi aikin Bala Usman, Mahdi Adamu,
Bello Alƙali, Abdullahi Rafi Augi, S.U. Lawal da Baƙo duk kan Hausawa ne.     
[52] .           An yi PhD a fannin Mathematics kan hisabin Hausawa a ABU, Zariya. An yi PhD a University of
London kan gine-ginen gidan Bahaushe.
[53] .           Mun ga haka, mun tabbatar da haka a yau (2014).
[54] .           A fannonin Al’ada da Adabi da Harshe.
[55] .           Aikin da aka yi a kansa shi ne taken: Champion of Hausa cikin Hausa, A festschritt in Honour of
Dalhatu Muhammad, ABU, at 50.
[56] .           Su ne ɗaliban farko na Hausa cikin Hausa.
[57] .           Har Allah Ya karɓi Hambali ba a taɓa jin ya yi laccar Hausa cikin Ingilishi ba. Allah Ya gafarta
masa.
[58] .           Na ambaci na Yakasai a lamba ta (41) na Ahmadu Bello Zariya shin e: Nahawun Hausa, NNPC,
Zaria.

Post a Comment

0 Comments