Ticker

6/recent/ticker-posts

Birgima A Cikin Wak’ar Mu’azu Haɗeja: Nazarin Jigon Waƙar Yabon Ubangiji

Wannan muƙala ta ƙunshi wani ɓangare daga cikin ɓangarorin adabi wato waƙa kuma rubutacciya. Ganin yadda waƙa take da matuƙar amfani ga jama’a kuma ta kasance wata hanya ta isar da saƙo a cikin sauƙi ga...


________________________________________________
Na
Haruna Umar Maikwari
+2347031280554
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya, Gusau. Jihar Zamfara
________________________________________________

1.0 TSAKURE

Wannan muƙala ta ƙunshi wani ɓangare daga cikin ɓangarorin adabi wato waƙa kuma rubutacciya. Ganin yadda waƙa take da matuƙar amfani ga jamaa kuma ta kasance wata hanya ta isar da saƙo a cikin sauƙi ga alumma. Marubuta na wancan lokaci sun yi amfani da waƙa wajen isar da saƙwannin su ga jama’a. Bayan wannan ma shahararrun malaman nan da suka jaddada addinin musulunci wato su Mujaddadi Shehu Usmanu ɗanfodiyo da ƙanensa Abdullahin Gwandu da ɗansa Muhammadu Bello da ‘yarsa Nana Asma’u da dai sauran almajiransa sun yi amfani da waƙa wajen isar da saƙonsu ga alumma. Wannan ya sa masana da manazarta suka yi aiki a kan wannan ɓangare. Don haka mu ma zamu ɗan duba wani ɓangare da ya shafi nazarin waƙar don samun ƙarin haske ga wani abu da ya shige wa jamaa duhu.  

1.0.1 GABATARWA

Fagen adabi fage ne mai tarin yawa wanda masana da manazarta da yawa suka gudanar da aiki a kansa, kuma har a yau suna a kai wajen gudanar da bincike na duk wani abu da ya shafi adabi. Wannan muƙala ba wai ta ƙunshi dukkan ɗaukacin adabi ba. Amma za ta bayar da ƙarfi a kan rubutacciyar waƙa. Ba rubutacciyar waƙa za a nazarta gaba ɗayanta ba. Za a dai ɗan yi tsokaci ne dangane da abin da ya shafi Jigo da Gajerce Jigo da Warwarar Jigo, duk a cikin rubutacciyar waƙar nan ta Mu’azu Haɗejia ta Yabon Ubangiji.

2.0.2 Jigo

ɗangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai.

Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da saƙonsa ga jama’a. Sarɓi, (2007:71).

Da wannan muke gani Jigo a matsayin igiya maɗaura kayan kowane rubutu da aka yi a fagen adabi ta kowane ɓangare wato Zube da Waƙa da Wasan Kwaikwayo in ba da shi ba to kayan za su kwance. A nan jigo na nufin burin zuciyar mawaƙi ko marubuci wanda yake son jama’a su fahimta.

 

Kaftin Suru Ummaru ɗa, Allah ya jiƙansa da rahama yana faɗa a waƙarsa mai suna Jigo. Ya ce:

Kay yi waƙa ba jigo,

                             Ya yi riga ba taggo,

                             Yai awaki ba faggo,

                             Ga amarya ba ango,

                                 Ban ga amfani nai ba.

Wannan ya nuna ke nan in aka yi waƙa ba a san jigonta ba to tana da rauni. To abin lura a nan shi ne, ba waƙa kaɗai ba koma wane irin rubutu ne in dai babu jigon da ya sa aka yi shi to aikin banza ne bai da wani amfani.

 

A waƙar Mu’azu Haɗeja ta Yabon Ubangiji, da muka nazarta mun gano cewa Jigon wannan waƙar dai shi ne TAUHIDI.

 

Galibi idan mai rubutu bai fito a fili ya faɗi jigon waƙarsa ba to mai nazari yakan yi la’akari da wasu muhimman kalmomin fannu da waƙa ta ƙunsa don ya gane inda aka dosa. Wannan ya ba mu damar zaƙulo babban jigon wannan waƙar ta amfani da wannan hanyar. Ga kuma hujjar daga waƙar:

 

Baiti na (2)  “komi ka gan shi duniya farko gari,

 

                          Ko ka gaya mini Rabbu waf fare shi?”

 

          Ko shakka babu idan mutum ya kalli baitocin waƙar zai ga cewa duk TAUHIDI take magana a kai, kamar dai yadda za a gani a gaba cikin warwarar jigo da zai biyo baya.

2.0.3 Gajerce Jigo.

 

        ɗangambo (2007:15) ya ce, “A nan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da mawaƙi yake faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi, bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Misali ana iya cewa a baiti na 1-3 ya ƙunshi yabon farawa, baiti na 4-7 ya ƙunshi gabatar da Jigo.

 

Idan aka yi la’akari da abin da magabata suka faɗa dangane da Gajerce Jigo za a ga cewa, wannan wurin yana buƙatar a fito da hoton bayanin waƙar a taƙaice ana iya ɗaukar ɗiya ko baitoci na waƙar rukuni-rukuni a fito da muhimman abubuwan da take magana a kai.

 

        Anan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da marubucin waƙar ya rubuta/faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi ko bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Ga dai yadda abin yake a wannan waƙar ta Yabon Ubangiji.

1.       Mabuɗin waƙar: Ya fara da ambaton sunan Allah Ubangiji a baiti na 1

2.       daga baita na 3-7, 19-21, 61-65, da na 70 suna bayani ne a kan kaɗaitar Ubangiji.

3.       Baiti na 18 da 68-69 suna nuna buwayar Ubangiji.

4.       Baiti na 22-32, 54-60, da 71-73 suna bayanin ƙarfin ikon Allah Ubangiji.

5.       baiti na 33-38 suna bayanin wadatuwar Ubangiji.

Yadda mawaƙin/marubucin waƙar yake nunawa cewa Allah Shi ne da arziki kuma idan mutum yana alfahari ya ba ka arziki to sila ce Allah Ya ga dama.

6.       Baiti na 39- 40 suna bayanin siffofin Ubangiji, kamar yadda marubucin ya kawocewa Allah mai haƙuri ne kuma mai ji ne Yana kuma gani.

7.       Baiti na 41-45 suna bayani ne a kan Mala’ikkun Allah haka dai marubucin waƙar ya ci gaba da kawo mala’ikkun Allah, kuma ya bayyana cewa duk abin da mutum ya aikata suna rubutawa.

8.       Baiti na 46 da na 47- 49 suna bayanin tashin alƙiyama. Bayan ya kawo Mala’iku, sai ya kawo zancen Lahira da yadda ake karɓar sakamako.

9.       Baiti na 48- 50, suna bayani a kan Tawassuli.

10.     Baiti na 51- 52, suna tsarkake zati Ubangiji.

11.     Baiti na 53 yana bayani a kan kyautar Ubangiji.

12.     Baiti na 54 - 60, suna bayanin ikon Ubangiji.

13.     Baiti na 66 - 67, suna bayanin adalcin Ubangiji.

14.     Baiti na 74 - 75, suna gargaɗi ga masu girman kai, saboda girman kai abu ne maras kyau.

15.     Baiti na 76 - 78, suna yabon Manzon Allah (SAW).

16.     Baiti na 79, marubucin ya faɗi sunansa.

17.     Baiti na 80. ya yi ƙoƙarin rufe waƙarsa tare da kawo yawan baitocin waƙar. A nan ne kuma ya dakata.

2.0.4 Warwarar Jigo

Anan za a yi sharhi ne kan Jigo gaba ɗayansa. Za a duba shi dangane da jawaban jigo, da kuma abin da waƙar ta faɗa a taƙaice. To amma muhimmin abin shi ne za a duba lungu-lungu na waƙar dangane da jigo tare da ƙarin bayani daga dukkannin abin da za a iya danganta waƙar da shi. Misali ana iya kawo ƙarin bayani don kafa hujja da misalai daga Alƙur’ani, Hadisi, littattafai, muƙalu, da ra’ayoyi iri daban-daban da dai sauran bayanai da za su taimaka wajen gane abin da waƙar ta ƙunsa da inda aka dosa. ɗangambo, (2007:16)

A ɗan tunaninmu a nan mai nazari yake da babban aiki kuma ja! Domin ana son ya tsattsafe bayanan da waƙar ta ƙunsa ya fito da su daki-daki. Sannan kuma yana da kyau a kalli waƙar ɗaka da waje wato dangantakar waƙar da Alƙur’ani Mai Tsarki ko Hadissai ko wani tarihi na musamman ko ambaton ayyukan ci gaba, ko wata magana mai matuƙar muhimmanci, da dai duk abin da mai sharhi zai iya gano asalinsa ta fuskar waƙa. Ashe ke nan ana son a yi nazarin ƙwaƙwab ga waƙar. Wannan fili ne na faɗin fahimtar mai nazari dangane da abin da ya gano game da waƙar da yake sharhi a kai.

A nan za a yi sharhi na gaba ɗaya tare da fitowa da saƙwannin wannan waƙa daki-daki domin ganin yadda abin yake wakana. Yanzu bari mu mayar da homa ruwa don ganin iya abin da za mu kamo na wannan sharhin da ya ƙunshi Jigo da Gajerce shi da Warware shi. Ga yadda abin yake.

Mawallafin wannan waƙar ya fara buɗe waƙarsa da cewa:

Baiti na (1)  “Na fara talifi da sunan Ubangiji,

                             Subhanahu Mannanu babu kamar Shi.”

Wannan tana ɗai daga cikin hanyoyin da mafi yawan marubuta waƙoƙi suke amfani da ita.

Bayan mawaƙin ya fara da sunan Allah a baiti na farko, sai ya fara gabatar da gundarin jigon waƙar a baiti na biyu, wato TAUHIDI, inda yake cewa:

Baiti na (2)  “Komi ka gan shi a duniya farko garai,

                             Ko ka gaya mini Rabbu waffare Shi?”

Wannan yana nuna Shi Allah babu wanda ya halicce Shi, kuma komi ka gani a duniya Allah ne ya halicce shi. Wato Allah Shi ne na Farko kuma Shi ne na ƙarshe, kamar yadda ya bayyana a cikin sunayenSa 99 “Al’Auwalu, Al’Akhiru”.

A baiti na 3 ne mawallafin ya fara warwarar wannan jigo inda ya ce:

            (3)  “Duk wanda ya yi farko ƙarshe garai,

                             Sai Rai guda ne babu mai kaushe Shi.”

Daga baiti na 4-15, ya ci gaba da warwarar wannan jigo yana nuna kadaituwar Allah (SWT) yana cewa , “Shi ba Shi da ɗa, ko uba ko uwa ko mata ko wani mataimaki , ko abokin shawara ko abokin aiki ko mai yi Masa wata hidima. Kamar yadda ya tabbata a cikin Alƙur’ani mai tsarki a cikin Suratul Ikhlas (SWT) kamar yadda yake cewa a wasu baituka kamar haka:

Baiti na (9). “Rayin da bai gajiya bare Shi yi gyangyaɗi,

                             Hali na gajiyawa yana ga wanin Shi.”

Baiti na (11). “Rayin da babu uwa gareShi bare uba,

                                  Shi ba shi da ɗa balle a san jikanShi.”

Baiti na (15). “Albaulu, ga’iɗu ko jima’i ba shi yi,

                                 Shi hadisi ne ajizi mai yin shi.”

Daga baiti na 17- 23 mawallafin ya yi bayanin buwayar mulkin Allah (SWT) inda yake bayanin cewa baya saye baya sayarwa, kuma ganinSa ya buwayi dukkan ‘yan’Adam. Haka kuma yana bayanin cewa Allah (SWT) ba ya da mataimaki a cikin mulkinSa, wato ba ya da waziri ko Hakimi ko Alƙali ko wani mai taimako kamar yadda ya tabbata a cikin wasu Hadisai na manzon Allah (SAW) cewa Shi Allah (SWT) Wahadahu ne La sharikalahu, wato Shi kaɗai yake ba ya da abokin tarayya. A wani wurin kuma Yakan ce Subhanahu Wa Ta’ala (SWT) wato tsarki ya tabbata a gare Shi kuma mulkinsa ya ɗaukaka. Haka kuma ya bayyana cewa mulkin Allah (SWT) Shi ya mallaki dukkan mulkin waninSa, kamar yadda yake a baiti na (19)

Baiti na (19). ‘Sarkin da ba Shi Waziri ba Shi da Hakimi,

                                 Shi ba Shi da Alƙali balle a san MuhutinShi.”

A baiti na 24-31, ya yi bayanin irin kyauta da kuma adalci na Allah (SWT) yana nuna cewa Shi Allah (SWT) Shi ne mai ba da kyauta ga wanda ya so, kuma Ya hana wanda ya so, a lokacin da Ya so a duniya da lahira., kamar yadda yake a cikin “Bismillahir Rahmanir Rahim” wato “Da sunan Allah Mai Rahama (kyauta) Mai jinƙai.”  Kuma da kyautarSa ne mai kyauta ke yin kyauta. Kamar yadda yake a baiti na 24.

Baiti na (24). ɓa ya ganin ƙyashin abin da ka mallaka,

                                Ko me ka samu Shi ya ba ka don son Shi.”

A baiti na 32, da 54-60, ya yi bayanin ikon Ubangiji Allah (SWT) cewa Shi ke aikata yadda ya so a lokacin da ya so, babu mai cewa don me? Kamar yadda ayar Al’ƙur’ani Mai tsarki ta nuna, “Fa’alun Liman Yurid” wato Shi Allah Shi yake aikata abin da ya ga dama. Haka kuma a cikin wata Ayar ta Al’ƙur’ani Mai tsarki yana cewa, “ Inna Laha Ala kulli shai’in Ƙadir” wato Shi Allah yana da iko a kan komai. Mu dubi waɗannan baitukan don gani yadda Marubucin ya ce.

Baiti na (32)          “Shi ne ke aikata yadda ya so Wahidun,

                             Don babu mahalukin da za shi kwaɓe Shi.”

Baiti na (58)          “Duka duniya idan sun ka so ka da arziki,

                             Idan ya sa ma faƙru babu mai ba ka shi.”

Daga baiti na 33-37 ya ci gaba da bayanin kyautar Allah (SWT) inda ya ce kamar hasken Rana da Wata ne, ya wadaci duniya baki ɗaya.

Daga baiti na 39-40, ya yi bayanin wasu daga cikin sunaye da siffofin Ubangiji inda yake cewa:

Baiti na (39). “Shi ne Sami’un, Basirun Mai ji Mai gani,

                                  Komai Ya ɗarsa a zuciya Ya san shi.”

Baiti na 41-45, Mawallafin ya yi bayanin Mala’iku da Allah ya sa ga kowane ɗan’Adam domin su rubuta dukkan ayyukansa masu kyau da marasa kyau. Waɗannan mala’iku ba su ci ba su sha, ba su barci, aikin su kawai suke yi kuma ba su saɓon Mahaliccinsu. Duba wannan baitin.

Baiti na (41)          “Hairan da sharran wanda duk ka aikata,

                             Da mala’iku da suke rubutu don shi.”

          A baiti na 46-49, ya yi bayanin tashin Alƙiyama da yadda hisabi zai kasance, wato wanda ya yi aikin ƙwarai zai karɓi littafinsa da hannun dama, wanda ya yi mumunan aiki kuma zai karɓi nasa littafin da hannun hagu. Ga dai yadda abin yake a cikin baitukan.

Baiti na (46)          “Kowa abin da ya aikata ran lahira,

                             Ran nan ake jimilla a ba shi abin shi.”

Baiti na (47)          “Wani za a ba shi kitabihi bi yaminihi,

                             Wannan rabon aljanna ne a gare shi.”

Baiti na (49)          “Wani ko ta ƙirji za a hudo zaharihi,

                             Hannun hagun sannan a ba shi abin shi.”

A baiti na 52-53, ya yi bayanin yadda Allah (SWT) yake haƙuri da bayinSa, da kuma himmatuwa a wajen roƙonsu. Misali.

Baiti na (52). “ Sarkin da ba Shi fushi balle Shi yi ɓaɓɓaki,

                                     Haƙuri gare Shi Ubangijin Al’arshi.”

Baiti na (53).“ Mai bai wa kowa ba a cewa Ya hana,

                                     Kowa ya ce bai ba shi ya saɓe shi.”

A baiti na 61-67, marubucin ya ci gaba da bayanin kaɗaituwar Allah (SWT) da kuma wadatuwar Shi da zatinSa, cewa ba ya buƙatar komi wurin kowa kuma Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, har ya ba da misali daga Suratul Ikhlas (Ƙulhuwal Lahu) ga dai abin da ya ce:

Baiti na (61)          “Can suratul Iklasi ga ayarSa nan,

                                      Shi wahidul-Ƙaharu ba na biyun Shi.”

A cikin baiti na 68-73, marubucin waƙar ya ci gaba da bayanin buwayar Ubangiji a kan mulkinSa, cewa Shi ne yake da iko a kan komai, kuma ba shi da wani tamka a cikin mulkinSa, sannan babu wani abu da yake da kama da Shi.

Daga baiti na 74-75, yana yin gargaɗi ga mutane masu girman kai cewa duk wanda ke taƙama da girman kai to lallai zai hadu da taɓewa. Ya ƙara da tunatar da masu saurare/karanta waƙar cewa kowane mutum ya dogara ga Allah ba ga waninSa ba. Kuma a daina yin girman kai. 

A baiti na 79-80, Mawallafin waƙar yana ƙoƙarin rufe waƙarsa da ambaton sunansa, tare da bayyana wa jama’a adadi/yawa baitocin waƙar.

Baiti na (79). “Ni ne Mu’azu Haɗejia ni na yi wallafar,

                                      Haza a ƙallu minal ƙalili yabon Shi.”

Baiti na (80). “ Baiti tamanin ne a nan muka dakata,

                                      Ƙirga shi sosai don ka san jimlar shi.”

3.0 KAMMALAWA

A cikin kalen nazarce-nazarcen da aka yi dangane da abin da ya shafi adabi. An gano cewa a kowane rubutu na wannan ɓangare, jigo shi ne ƙashin bayansa. A ɗan nazarin da aka yi a wannan waƙar wadda Mu’azu Haɗejia ya rubuta mai suna “Yabon Ubamgiji” an gano cewa Babban Jigon waƙar shi ne TAUHIDI. Muƙalar ta ƙara da Gajerce Jigon don sauwaƙawa ga mai nazari. Ba nan abin ya tsaya ba, sai da har aka Warware Jigon domin mai nazari ya ƙara fahimtar waƙar ciki da waje. An kuma kafa hujjoji da baitukan waƙar dangane da abin da marubucin ya faɗa a waƙar, da fatar wannan zai amfanar da al’umma baki-ɗaya. 

 MANAZARTA

Post a Comment

0 Comments