Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Fina-finai a Kan Al’adun Hausawa: Ke’ba’b’ben Nazari a Kan WasuD’abi’u Na Musamman a Cikin Fina-finan Hausa

An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da saƙwanni ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin sun shafi ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka haɗa da Turawa, da Indiyawa da sauransu. Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da ƙwarƙwa kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da
_____________________________________________
Na
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
08035605024, 07087765510
Email Address: yagobir@yahoo.co.uk

Da
Department of Educational Foundations
Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
Phone No. 08133529736
Email Adress: abuubaidasani5@gmail.com
_____________________________________________


Tsakure

An dad’e ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da sak’wanni ga al’ummar Hausawa. Sak’wannin sun shafi ilimantarwa da fad’akarwa da nishad’antarwa. Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka had’a da Turawa, da Indiyawa da sauransu. Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da k’wark’wa kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da wata sauran alak’a da al’adun Hausawa. Wannan ya sa abin ya zama bambarak’wai nono da gishiri. Wannan takarda ta tarkato wasu daga cikin d’abi’u kamar yadda suke fitowa a cikin wad’annan fina-finai na Hausa. D’abi’un sun had’a da sutura da magana har ma da halayya. Hakan ya haifar da samuwar wasu miyagun d’abi’u tattare da rayuwar al’ummar Hausawa ta yau da kullum.

Muhimman kalmomi: Fina-finai, D’abi’u

Gabatarwa


Fina-finan Hausa sun sami gindin zama na sosai a tsakanin al’ummar Hausawa. Tuni harkar shirya fina-finai ta zama wani ‘bangare na rayuwar al’umma (Fage, 2004, Gidan Dabino, 2001). Harkar fina-finai ya kasance kasuwanci wanda jama’a da dama suka dogara a kansa domin samun abin sawa a baka. Sannan mutane da dama sun yi arziki ta dalilinsa. Wani abin burgewa dangane da harkar fim shi ne, rukunin masu sana’o’i da dama ne suke cin gajiyarsa. Sun had’a da mawak’a da taurari (‘yan wasa) da masu d’aukar hoto na kati da na bidiyo da masu kwalliya da masu shagunan sai da kaset da masu shagunan tura wak’ok’i da fina-finai zuwa ga wayoyi da ma wasu rukunonin masu sana’o’i daban-daban. A tak’aice harkar fim na da tasiri a kan tattalin arziki matuk’a (Gidan Dabino, 2001; Aminu, 2004; Larkin, 2004; Chamo, 2004).

A d’aya ‘bangaren kuma, fina-finan Hausa suna zaman figi-naka-na-figi-nawa ne tsakaninsu da al’adun Hausawa. Dalili kuwa shi ne, al’adun Hausawan na taka rawar gani cikin tsarin fina-finan. Yayin da a d’aya ‘bangaren kuma, su fina-finan ne ke jan akalar al’adun Hausawa zuwa wata k’urya ta daban. Za a iya ganin hakan idan aka yi la’akari da yadda fina-finan suke yin tasiri a kan rayuwar al’umma. Sukan samar da sara da sababbin d’abi’u da dama (Bunza, 2002; Iyan-tama, 2004; Ibrahim, 2004)

Wannan aiki ya bi sawun tarihin samuwar wasan kwaikwayo a tak’aice. Sannan ya waiwayi shigowar wasan kwaikwayo na zamani zuwa k’asar Hausa da kuma fara shirya fina-finan Hausa. Manazarta da dama sun gudanar da bincike game da lokacin da aka fara samun fina-finan Hausa. Sai dai sakamakon binciken manazartan yakan d’an bambanta saboda raunin tarihi. Manazarta da suka yi tsokaci kan tarihin samuwar fina-finan Hausa a cikin ayyukansu daban-daban sun had’a da; Yimi, (1981); gidan Dabino, (2001); Ali, (2004) da sauransu. Baya ga haka, aikin ya kawo wad’ansu d’abi’u da suka samu a dalilin fina-finan Haua. Muradin aikin ya ta’allak’a ne a kan nuna wad’annan d’abi’u ba tare da mayar da hankali kan yanke hukunci game da kyawu ko rashin kyawunsu ba.

Bayan wad’annan, aikin ya waiwayi tasirin fina-finan Hasau (kamar sauran ‘bangarorin adabin Bahausahe na zamani – zube da rubutacciyar wak’a), a kan rayuwar Bahaushe. Sakamakon yana nuni da cewa, adabin na mazaunin akala da ke sarrafa al’ummar Hausawa. Daga k’arshe kuma aikin ya kawo wasu shawarwari game da hanyoyi ko matakan da za su iya sanya fina-finan Hausa su kasance masu taka-rawar-gani wajen ci gaban al’umma baki d’aya.

Ma’anar Muhimman Kalmomi na Cikin Take


Fim: Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da ke d’auke da hotunan mutane, wato hotunan mata ko maza, yara ko manya ko kuma ma wanin mutane, wanda aka d’auka ko kuma hanyar yin amfani da na’urar d’aukar ta musamman, tare da bai wa mutane (kowannensu) damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa, a wani d’an lokaci da aka ke’be wanda shi wasan kwaikwayo yake d’auke da wani sak’o na musamman kan nishad’i da gargad’i da wa’azi da soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al’ummar duniya (Kiyawa, 2013).

D’abi’a: D’abi’a na nufin halin mutum ko al’adarsa (K’araye, da Yalwa, 2006). A wannar takarda, d’abi’a ta d’auki ma’anar duk wani hali na al’umma, tun daga magana, tafiya, sutura, cin abinci da ma sauran abubuwan da suka shafi rayuwa ta yau-da-kullum.

Tak’aitaccen Tarihin Wasan Kwaikwayo


          D’anjuma (2004) ya ce, wasan kwaikwayo na farko a doron k’asa ya samu ne tun zamanin Annabi Adam. Bayan da ‘ya’yansa biyu suka yi fad’a a kan mata, sai d’aya ya kashe d’aya. Wanda ya yi kisan ya shiga cikin damuwar yadda zai yi da gawar. A nan Allah ya turo da mala’iku a cikin siffar hankaki. Hankakin suka yi fad’a har d’aya ya kashe d’aya. A nan hankakan da ya yi kisan ya tona rami ya busne d’an uwansa da ya kashe. Wanda daga nan ne ‘yan Adam suka kwaikwayi wannan k’aramin wasan kwaikwayo ta hanyar busne ‘yan uwansu a duk lokacin da suka rasu.

Samuwar Fim a K’asar Hausa


          Tarihin fara fina-finan Hausa (harkar da ta fi kafuwa a Kano) yana da dangantaka ta kai-tsaye da tarihin fara fina-finai a Nijeriya baki d’aya (Ali, 2004). Fim kuwa a Nijeriya ya samu tun kafin samuwar Nijeriya a matsayin k’asa d’aya. An fara fim na farko a Nijeriya k’ark’ashin kulawar Herbert Macauly a shekarar 1903 (Alfred, 1979; Ali, 2004). A d’aya ‘bangaren kuma, ba a had’a Kudu da Arewa (a matsarin k’asa d’aya – Nijeriya) ba sai a shekarar 1914. Yayin da kuma aka ba wa Nijeriya ‘yancin kai a shekarar 1960 (Isichei, 1997; Douglas, 2004). Tsakanin shekarar 1903 zuwa 1970 an samu yunk’urin shirya fina-finai da dama. Ali, (2004) ya kira su da rukunin fina-finan farko na ‘yancin kai. Masu hannu a cikin wad’annan fina-finai sun had’a da Nuhu Ramalam da Adamu Halilu. Bayan nan kuma, kamfanoni sun d’auki nauyin shirya wasu fina-finai. Daga cikin wad’annan fina-finan akwai ‘Shehu Umar’ da ‘Amadi’ da ‘Salla Durba’ (Ali, 2004).

Fina-finan Hausa kuwa kamar yadda ake kallon su yanzu, an fara su ne tsakanin shekarar 1980 zuwa 1984 a Kano (Gidan Dabino, 2001). Fage, (2011) ya ce, fina-finan Hausa wad’anda aka fi sani da fina-finan Kanawa sun fara samun kar’buwa ne wajen 1990. A wannan lokaci an sami k’ungiyoyin fim guda uku da suka had’a da (i) Gwauron Dutse, da (ii) Karate, da kuma (iii) Gyaranya, wad’anda kuma duka sun wanzu ne a Kano. Fina-finan farko da aka fara gudanarwa k’ark’ashin wad’annan k’ungiyoyi su ne: ‘Hukuma Maganin ‘Yan Banza’ da ‘Yan D’aukar Amarya’ da kuma ‘Bak’ar Indiya’. Wad’anda suka d’auki nauyin wad’annan fina-finai su ne masu d’aukar nauyi na farko (first producers); Alhaji Hamisu da Muhammad Gurgu da kuma Sani Lamma (Gidan Dabino, 2001; Ali, 2004).

Zagari Game da Fina-finan Hausa


Idan aka yi la’akari da muhawarar masana da manazarta a kan alfanu da koma baya da fina-finai suke samar wa, za a iya cewa, fina-finan Hausa sun kasance hanjin jimina, akwai na ci a kwai na zubarwa. Hak’ik’a fina-finan suna taimakawa ta ‘bangarori da dama. Ali, (2004) ya ce, a tsawon k’arnuka biyu da suke wuce, samuwar fina-finan Hausa shi ne hanyar ha’baka tattalin arziki mafi girma da ya samu ga al’ummar Hausawa. Sai dai duk da haka, manazarta irin su; Iyan-tama, (2004) da Alkanawy, (2000) suna ganin samuwar finafinan Haua yana da illa ga al’ummar Hausawa. Wannan aiki ya kalli ‘bangarorin biyu kamar haka:

Amfanin Fina-finan Hausa


          Samuwar fina-finan Hausa ya zo da ci gaba ga al’ummar Hausawa ta fannoni da dama wad’anda suka had’a da:

  1. Samun Aikin Yi: Rukunin masu sana’o’i da dama suna cin gajiyar sana’ar shirya fina-finai. Wad’annan rukunnai na masu sana’o’i sun had’a da masana harkar fim, da marubuta da masu d’aukar hoto da masu shagon sayar da kaset da ma wasu masu sana’o’i daban-daban. Lallai ta nan za a iya cewa wannan ci gaba ne ga al’ummar Hausawa (Dumfawa, 2002; Malumfashi, 2002; Ali, 2004).

  2. Bunk’asa Al’adu da Adabi: Fim hanya ce da take taimakawa wajen bunk’asa al’adu da adabin Hausa. Wani abin mai da hankali a nan shi ne, fim na taka rawar gani wurin tallata al’adu zuwa ga baren al’ummu. Fina-finan Haua da dama sukan shiga hannun wasu al’ummu wad’anda ba Hasauwa ba da suke zaune a nan gida Nijeriya, har ma da na k’asashen waje (Nwuneli in Ali, 2004).
  3. Fad’akarwa: Hak’ik’a fim hanya ce ta fad’akar da al’umma game da lamura da dama. Akwai fina-finan Hausa da jigoginsu ke fad’akarwa kan abubuwa kamar illar zafin kishi, ko k’arshen mai munafurci, ko illar zato da zargi, ko cututtuka da ma wasu da dama makamantan wad’annan (Chamo, 2004; Yakub, (2004).
  4. Sada Zumunta: Fim d’in Hausa na taimakawa wajen k’ulla zumunci musamman tsakanin taurarin fim. Baya ga haka akwai fina-finai da suke jan hankali zuwa ga amfani da dacewa da buk’atar sada zumunta (Chamo, 2004).
  5. Koyar da Tarbiyya: Akwai fina-finan Hausa da dama da suke d’auke da jigon tarbiyya. Irin wad’annan fina-finai suna fad’akarwa zuwa ga biyayya ga iyaye (kamar fim d’in Linzami da Wuta), ko bin miji (kamar fim d’in Aljannar Mace) da sauransu (Chamo; 2004; Yakub, 2004).
  6. Nishad’antarwa: Hak’ik’a ana nishand’antuwa daga kallon fina-finan Hausa. Akai fina-finan Hausa da dama da aka gina jigonsu kan nishad’i. Babban tauraro a ‘bangaren fina-finan Hausa na nishad’i shi ne marigayi Rabilu Musa wanda aka fi sani da D’an Ibro (Chamo, 2004; Yakub, 2004).

Illolin Fina-finan Hausa


Masu iya magana suna cewa: “Kowane allazi da nasa amanu!” Haka abin yake ga fina-finan Haua. Manazarta da malaman addini sun dad’e suna nuni ga illoli da suke tattare ga fina-finan Hausa. Abubuwan da ake k’orafin kansu sun had’a da:

  1. ‘Batar da Al’ada: Za a iya kwatanta fina-finan Hausa da maganar Bahaushe da ke cewa: “Ana yabonka salla ka kasa alwala.” Duk da ikirarin da ake yi na cewa fina-finan Hausa suna ha’baka al’ada, wasu na ganin ko kusa ba haka abin yake ba. Sun tafi kan cewa, a maimakon fina-finan su taimaka wajen ha’baka al’adun Hausawa, sai ma suna k’ara dak’ushe su ne kawai. Fina-finan Hausa na dak’ushe al’adun Hausawa ta hanyoyin da suka had’a da:
  2. Harshe: Wato yawan amfani da Ingausa tare da fifita harshen Ingilishi a kan na Hausa.
  3. Sutura: Fifita suturun wasu al’ummu kamar Turawa da Indiyawa sama da na Hausa.
  4. Muhalli: Watsi da muhallin Bahaushe tare da fifita na wasu al’ummu sama da na Hausawan (Chamo, 2004; Al-kanawy, 2004).
  5. Shgaltarwa: Akwai manazarta da suke kallon fina-finan Hausa a matsayin hanya na shagaltar da al’umma daga wasu ayyuka da sha’anoni da suka fi dacewa. Wannan ya fi zama abin magana musamman idan aka kalle shi daga ‘bangaren addini wanda bai zo da wasa ko shagala ba (Al-kanawy, 2004; Iyan-tama, 2004).
  6. Fand’arewa: Akwai manazarta da suke kallon fina-finan Hausa a matsayin masu rud’i zuwa ga fand’arewa. Wannan na faruwa ne musamman idan aka duba irin shigar taurarin fina-finan wad’anda suka ci karo da addini da kuma al’ada. Sannan tsaurin ido ga na gaba da sauran halayen banza da ake nunawa a cikin fina-finan (Al-kanawy, 2004; Iyan-tama, 2004)
  7. Cud’anya Tsakanin Maza da mata: D’aya daga cikin manyan abubuwan da suka fi jan hankali, wad’anda kuma suke jawo sukar fina-finan Hausa shi ne cud’anya tsakanin maza da mata. Wannan ya kasance musamman idan aka kalli lamarin ta fuskar addini (Iyan-tama, 2004).
  8. Wak’a: Wak’a ta kasance a cikin fina-finan Hausa tamkar gishiri a cikin miya. Manazarta na kallon hakan k’alubale ne musamman idan aka yi la’akari da matsayin wak’a a Musulunci.

Manazarta da dama bayan wad’annan sun tafi kan cewa fina-finan Hausa suna taka rawar gani matuk’a wajen gur’bata al’adun Hausawa. Manazartan sun had’a da: D’angambo, (2013) wanda ya ce, a wani fim d’in idan da za a cire harshen da aka yi Magana a cikinsa (Hausa) to babu yadda za a iya danganta shi da Hausawa. Guibi da Bakori (2013) sun tafi kan cewa, telebishin na d’aya daga cikin hanyoyi mafi sauk’i da suke ‘bata tarbiyyar Hausawa. Kiyawa, (2013) ya kawo wasu hanyoyi wad’anda yake ganin ta nan ne fina-fina-finan Hausa suke ruguza al’adun Hausawa. Wad’annan hanyoyi su ne:

  1. Sun ci karo da koyarwar addinin Musulunci

  2. Rashin kyakkyawar wakilci ga al’adun Hausawa
  3. Lalata tarbiyyar yara da matasa
  4. Cusa bak’in al’adu marasa nasaba da Addini da al’ada
  5. Nakasa ruhin auratayya
  6. Samar da ‘barna
  7. Dogon buri (Kiyawa, 2013).

Baya ga duka wad’annan, akwai wasu tarin manazarta da suke da wannan ra’ayi. Sun had’a da: Mwani da K’ank’ara, (2013) da Mai’aduwa, (2013) da Sulaiman (2013) da D’an Maigoro, (2013) da Gwammaja, (2013) da Abdullahi da Maidabino, (2013) da Inuwa, (2013).

Wasu D’abi’u da Suka Samu Dalilin Fina-finan Hausa


Akwai d’abi’u da dama da wasu al’ummar Hausawa suka d’auka daga fina-finan Hausa. Za a iya kallon wad’annan d’abi’u ta fiskoki uku kamar haka:

  1. Sutura: An samu sababban salailan d’inki na maza da mata a dalilin fina-finan Hausa. A hirar da wannan bincike ya yi da Ubaida Usman (2016), (wata mai kallo da sharhi kan fina-finai a Sakkwato), ta nuna cewa, wad’annan d’inkuna na maza da mata sun had’a da:

  2. Wasila: A cikin fim mai suna Wasila, ‘yar wasar fim d’in (Wasila) ta saka wata riga. Rigar tana da fad’i sannan tana da yanka-yanka guna hud’u ta k’asanta. Daga wannan lokaci matan Hausawa da dama suka fara d’inka irin wad’annan riguna. Ana yi wa rigar lak’abi da

  3. A’isha/Bubu Kombineshin: Wannan wani d’inke ne da aka samo daga fim mai suna A’isha. A cikin fim d’in ne ‘yan wasa mata guda biyu suka yi amfani da irin wannar riga. Matan su ne Samira Ahmad da Hadiza Kabara. Riga ce mai tsawo sannan ta sama wani yadi ne da ake kira shuban/shugon. Ta k’asa kuma sai a sanya shadda.
  4. Jamila da Jamilu: Wannar ma riga ce ta mata. Rigar tana da tsawo. Baya ga hakan, hannunta d’aya dogo ne d’aya kuma gajere. An samo wannan d’inki ne daga fim mai suna Jamila da Jamilu. Tauraruwar fim d’in ita ce Jamila Nagudu.
  5. Cinko: Cinko wata irin riga ce ta maza wadda ake yi mata aiki na musamman. Adam A. Zango ne ya saka irin wannar riga a Fim mai suna Abban Sadik’. Daga wannan lokaci samari da dama suka rik’a dinka irin wad’annan riguna.
  6. Tsamiya: A fim mai suna Salma, A’isha Aliyu Tsamiya ta yi wata shiga. Ta sanya hijabi sannan ta jawo shi ta rufe ha’barta. Baya ga haka ta sanya tabarau ma ‘yar igiya a jikinsa. Igiyar tabarau d’in ya kasance a saman hijabin zagaye da wuyanta. Daga wannan lokaci mata da dama suna irin wannan shiga. Wasu suna kiran shigar da suna
  7. Fati Muhammad: Wannan wani salon d’aurin d’ankwali/kallabi ne wanda yake zagaye kai (kan goshi da k’eya), a bar tsakiyar kai kuma babu komai. An samo wannan salo ne daga fim d’in A cikin fin d’in ne Fati Muhammad da kuma Maijidda Abdulk’adir suka yi irin wannan d’aurin d’ankwali.
  8. Babban Yaro: Wannan wata shiga ce, ta maza, inda ake sanya d’amammiyar k’aramae riga da kuma wando d’amamme shi ma. An samo wannan shiga ne daga fim d’in Babban Yaro. A cikin wannan fim d’in ne Adam A. Zango ya yi irin wannan shiga. Daga wannan lokaci wasu matasa suke kwaikwayon shigar.
  9. Ali Nuhu: Wannar wata shiga ne ta maza. Bayan mutum ya sanya kaya (kowane iri) sai ya kawo kyalle ko rawani ya rataya shi a kafad’a. Wannan shiga an same shi ne daga Ali Nuhu. Ali Nuhu ya yi irin wannan shiga a fina-finai kamar su: Jarumin Maza da Sai Watarana.

    Sara: Akwai sara wad’anda suka samu a dalilin fina-finan Hausa. Wad’annan sara sun had’a da:
    Sai Bayan Kwana Biyu: Wannan wata sara ce da aka samu daga wani fim mai suna; Na Mamajo. An nuna mahaukaci a cikin fim d’in wana duk maganar da aka masa sai ya ce: “Ooo sai bayan Kwana biyu.” Mutane da dama sun d’auki wannan sara. Duk lokacin da wani ya tambayi a ba shi wani abu, sannan wanda aka tambaya ba shi da niyyar bayarwa, sai ya ce: “Ooo sai bayan kwana biyu!” Misali:

Musa: “Aminu don Allah ba ni aron d’ari biyar.”

Aminu: “Ooo, sai bayan kwana biyu!”
    K’ara’i: Wannar sara an samo ta ne daga fim d’in nan mai suna K’ara’i. a fim d’in an nuna yadda mutane suke duniyanci da sunan za su tuba daga baya. Daga nan ne al’umma suka samu. A duk lokacin da aka kwa’bi wani game da aikata wani abin da bai dace ba, sai ya ce: “K’yale ni na yi k’ara’i kafin lokacina ya wuce.” Sannan duk wanda aka ga yana aikata aikin banza, ana kwatanta aikin da k’ara’i.

    Wuta Sallau!: Wannan wata sara ce da aka samo daga fim d’in Rabilu Musa Ibro mai suna Wuta Sallau. A cikin fim d’in an nuna motar Ibro (Sallau) ta kama da wuta. Ana ta sanar da shi: “Wuta Sallau.” Amma ya d’auka yaba shi ake yi. Sai da abin ya yi k’amari sannan ya ankara, alhali ya riga ya makara. Daga nan duk lokacin da aka ga wani ya wahala ko yana wahala, sai a ce da shi: “Wuta Sallau!” Akwai ma wad’anda suka rik’a rubutawa a ababan hawansu.

    Basaja: Wannar sara an samo ta ne daga wani fim da ake kira A ciki Adam A. Zango ya fito a matsayin wanda ya k’ware a basaje sosai. Daga nan ne al’umma ta samu. Duk lokacin da wani ya yi basaje ko ya yi yaudara ko ya nuna wayo game da wani abu, sai a ce ai ya yi basaja.

    Gwaska: An samo wannan sara ne daga wani fim mai suna; A wannan fim d’in Adam A. Zango ya fito a matsarin ‘barawo mai tsananin fasa, wanda kuma yake taimakon talakawa da hana aikin ‘barna. A duk lokacin da ya yi sata, yakan bar alamar shi ne, ta hanyar rubuta sunansa (Gwaska). Da wannan ne wasu mutane (musamman yara a makaranta), suke d’auke littafi ko wani abu da ya daga wurin abokansu. Sannan su rubuta Gwaska a takarda su ajiye musu a wurin da suka d’auke abin.

    Su gayyar sod’i mun gode: Wannan sara an samo ta ne a fim d’in Ibiro mai suna Mai Ciki. Sai ta kasance a duk lokacin da wani ya shiga maganar da ba ta shafe shi ba, to masu maganar sai su ce da shi: “Su gayyar sod’i mun gode.”

    'Dan baba: Wannan ma an samo shi ne daga fim d’in Ibiro mai suna Mai Ciki. A cikin fim d’in an nuna yadda Ibiro yake matuk’ar son haihuwa. Saboda haka ne ma lokacin da matarsa ke da ciki ake ce wa d’an cikin d’an baba, tun ma ba a haife shi ba. Daga nan mutane suka samu, ake kiran d’an da ke ciki d’an baba.

    Halayya: Akwai wasu halayya da aka samu wasu Hausawa sun aikata kos una aikatawa, wanda kuwa asalin irin wad’annan halayya daga fina-finan Hausa suke. Sumayya Yahaya (wata ‘yar asalin Zamfara da ke zaune a Sakkwato, mai kallo da kuma sharhin fina-finai) ta ba da misalin halayya da Hausawa suka d’auka daga fina-finan Hausa:
    Akwai rikici da aka yi a wani fim mai suna D’akin Amarya. A wannan fim d’in Halima Atete (uwargida) ta farfasa kayan jeren d’akin amaryarta (A’isha Tsamiya), ranar daren farko na aurenta. Wannan binciken ya gano cewa, an yi wannan abu sak a Zamfara. Sannan a Sakkwato ma, unguwar Mabera an yi hakan a shekarar 2016.

    Mai zabo: Wannan wani aski ne da aka yi yayinsa. Akan aske gefe da gefen kayi sai a bar gashi a tsakiyar kai. An samo wannan salon daga wani fim da ake kira NASS. A cikinsa ne Adam A. Zango ya yi irin wannan aski.

    A’isha tsamiya: Wannan wata sark’a ce da aka yi yayinta. A’isha Aliyu Tsamiya ce ta yi amfani da sark’ar a fim d’in nan mai suna So. Daga nan mata suka duk’ufa wajen yayinta.

    Jamila sitayil: Wannan wani salon kitso ne wanda Jamila Nagudu ta yi a fim mai suna Jamila da Jamilu. Ana raba gashin kai biyu sannan a d’auki yawon kowane kaso zuwa baya.

Kammalwa


Ga bisa dukkan alamu akwai d’an bambance-bambance ga yadda manazarta ke kawo tarihin samuwar fina-finan Hausa. Wannan aikin ya waiwayi tarihin samuwar fina-finan Hausa a tak’aice. Hak’ik’a fina-finan Hausa suna da tasiri a kan rayuwar Hausawa. Wannan ne ma ya sanya aka samu d’abi’u da dama a dalilin fina-finan. Wad’annan d’abi’u sun shafi ‘bangaren cin abinci, da halayya da kuma musamman sutura. Aikin ya kawo wasu daga cikin d’abi’un da suka samu a dalilin wasannnin kwaikwayo. Wad’annan d’abi’u sun had’a da sarar gwaska da basaja da sai bayan kwana biyu. Bayan haka akwai sutura kamar; wasila da Jamila sitayil da babban yaro da dai sauransu.

Shawarwari

  1. Zai yi kyau masu hannu cikin shirya fina-finan Hausa su gane d’umbin tasirinsa a kan rayuwar al’umma. Wannan zai sa su sake mayar da hankali kan shirya fina-finai wad’anda jigoginsu za su kasance masu amfanarwa ga ci gaban al’umma ta gaba d’aya.

  2. Farfesoshi da daktoci da sauran masana da manazarta Hausa su kasance masu hannun sawa ko bakin magana a cikin harkar fina-finan Hausa. Wannan zai ba da damar jan akalar fina-finan zuwa hanyar da ta fi dacewa a ilmance.
  3. Gwamnati ta sanya hannu cikin harkar fina-finai ta hanyar tantancewa don hani ga miyagun ayyuka.

Manazarta



Post a Comment

0 Comments