https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Rubutawa: Shehu Hirabri 

08143533314

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Mijin Hajiya Mariya mai karhi,

Uban Najib baban Ibrahim,

Barista Baban Barista×2

Yara:   Karo da kai arna suka tsoro.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga matawallen Sakkawato, birni,

Ga matawallen Najeriya kaf, ×2

Yara:   Tunda gidan Usmanu a nan anka,

Tabbatatat nan anka nad’a ka.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ka yi hawa biyu yau saura d’ai,

Ga ka sifikan Najeriya nan,

Aminu yau ka zan mutawalle, ×2

Na uku mu ba za mu fad’i ba,

Yara:   Mu bar ma ‘yan kallo su karanta.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

 

Jagora: In sun karanta su ba mu amsa,

Yara:    Mai hak’on tsuntsaye duk×2

Ba ya ta da hannu kar su hiraye.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

Jagora: Ga matalle Aminu Waziri,

Na gwamnan Sakwkato Ali Wamakko,

Da kai da shi Allah ya had’a k’u,

Yara:    K’asa, ga kowa ba ya raba ku.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora:  Ko a siyasa in ta tashi,

Mai jama’a shi ne aka za’be,

Kai wane kar ka fito a gane ka,

Bak’in jininka kare ya ‘baci,

Yara:    Ko da ka je ka buga fosta,

Ko a gida wani ba ya lak’a ta.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga ka sifika kai mutawalle,

Duk inda ka zo kar ka yi shakka,

Yara:   Je ka da karhi d’an waziri,

Duk inda ka je ba a tare ka.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

Jagora: Abin da duk kura ka buk’ata,

Ba haka sarkin fawa ka so ba,

Kura kwad’anki har ya ‘baci,

Ita dai kullun ta ci nama,

Yara:   Duk randa ta shiga ba daidai ba,

Sai ta sha kashi ga mutane.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga dogo mai hannun kyauta,

Ga dogo mai hannun kyauta,

Kyautarka ta fi jarin yaro,

Rai ya dad’e ma Kabiru Marahwa,

D’an uban k’asa Alkammu,

Yara:   Kabiru rini kere itace.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Sauraran ni Kabiru Marahwa,

Yara na sun yo mani sak’o,

Sun ce babura kaka ba su,

Yara:   Amma alfarmar mutawalle.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ba don kid’a mu da wak’a ta ba,

Yara:    Don daraja sabon mutawalle×2

 

Jagora: Ana ta fad’in Haji Kawo Sumaila,

‘Danba’u bai san ka ba sosai,

Allah gwada mini Kawo Sumaila,

Yara:   Ni in ganai dai ko da idona.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga jikan Usumanu Waziri,

Aminu tun yana yaronai

Kowa ya san shi da kirki,

Yara:   Ba ya walak’antar da mutane.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

Jagora: Habibu Isa mun gode mai,

K’anenka na hwama da mutane,

Muddin in ya gane mu ya ba mu,

Yara:   Bai ta’ba jin haushin jama’a ba.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Haji Aminu Bala Bod’inga,

Haji Aminu Bala na k’warai ne,

In dai kana wajen Mutawalle,

Na san abina ba ya ‘bacewa,

Yara:   Tunda miya in ta cika zak’i,

Na san da magi anka had’a ta.

 

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Amshi kakai na ba ni takaici,

Amshi kakai na bani takaici,

In za ka ban mu yi hannu da hannu,

Yara:   Ka ban rabona in tahiyata.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Kai bari dai in ta da gwanina,

Bari dai in wasa gwanina,

Aminu d’an waziri Umar,

Sai kai d’an Alhaji malam,

Mai hank’uri d’an Shehi Moyi,

Ga d’an Shehi Ibrahim,

Ga d’an Shehi Haruna,

Ga d’an Shehi Haji Isa,

D’an Haji Alu ka kyauta,

Mai hwarin jini daga Allah,

Mutan gabas duk kai suka hanga,

Arewacin duk kai suka hange,

Mutan Gusun duk kai suka hange,

Balle yamma da ta zama taka,

Yara:   Sun rantce sai kai mutawalle.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

 

Jagora: A d’an waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am mutawalle,

D’an waziri ka k’ara shirawa,

Yara:   Aminu yau kai am mutwalle.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga matawallen Sakkawato,

Ga matawallen Najeriya kaf, ×2

Yara:    Tunda gidan Usmanu a nan anka,

Tabbatatat nan anka nad’a ka.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Mijin Hajiya mai karhi,

Uban Najib baban Ibrahim,

Barista Baban Barista×2

Yara:   Karo da kai arna suka tsoro.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: Ga wani na neman mutawalle,

Kai k’wank’iro wa za ya nad’a ka,

Kowa ya san bai alheri, ×2

Yara:   Bai iya kyauta ba a yaba mai.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

Yaro:   Duk randa nish shiga Sakkwato birni,

In yi rawa in mik’e k’agwata,

Jagora/Yara:  Tunda ubana am mutawalle. ×2

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: K’anen Waziri Muhammad Waziri Bello,

K’anen Waziri Muhammad,

Mai hana k’arya d’an dattijo,

K’anen Hajiya Hafsatu mun gode,

Ga kanen Haji Abdullahi,

Gai da k’anen Haji Maccid’o kai d’a,

Yara:   Na gode sabon Mutawalle.

 

Amshi: D’an Waziri ka k’ara shirawa,

Aminu yau kai am Mutawalle.

 

Jagora: K’anen Muhammadu Maccid’o kai d’a,

Gai da k’anen Hajiya Hafsatu,

Yara:   Gai da k’anen Haji Abdullahi.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/