Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaka A Garin Dakin-Gari: Tasirin Zamani A Kan Gargajiya (4)

NA

ABUBAKAR ALIYU
1310106004

KUNDIN DIGIRI NA FARKO NA HAUSA (B. A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NAJERIYA. JAMI`AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

BABI NA HU’DU


Tasirin Sassak’ar Zamani  a kan ta Gargajiya


4.0 Shimfid’a


A wannan bsbi mai taken tasirin sassak’ar zamani a kan ta gargajiya. Babin na da k’ananan sassa kamay yadda bayani zai biyo kamar haka:

A babin farko akwai shimfid’a a nan sashen zai kawo k’unshiyar babin  ne a tak’aice. Sai kuma ma’anar zamani. A nan sashen zai kawo muku ma’anar zamani da kuma yadda yake a tak’aice.

Baya ga haka sai kuma sashen babi mai suna kayan aiki da abubuwan da ake sassak’awa. A nan za a kawo jerin kayan aikin da abubuwan da ake sassak’awa a tak’aice.

Daga nan sai sashe mai suna tasirin zamani a kan sana’ar sassak’a. Inda a wannan sashe za a dubi irin tasirin da zamani ya kawo a cikin sana’ar sassak’a da kuma yadda yake tafiya da ita a cikin wannan zamani namu. Daga nan kuma sai sashe mai taken suna tasirin sana’ar sassak’a ga al’umma inda a wannan sashen za a dubi irin amfani da kuma illolin wannan sana’ar ga al’umma baki d’aya.

Daga nan sai sashe mai taken suna matsayin sana’ar sassak’a a yau. A nan wannan sashen zai dubi matsayin da sana’ar ta sassak’a take yau. Domin kawo muku ire-iren abubuwan da matsayin sana’ar a yau da kuma nan gaba a tak’aice. Daga nan kuma sai sashe mai taken suna makomar sana’ar sassak’a nan gaba. A nan wannan sashen zai dubi irin makomar wannan sana’ar ta sassak’a nan gaba domin kawo muku bayani irin yadda wannan sana’ar take sauyawa ta wasu ‘bangaren nata domin sigowar turawa da wad’ansu abubuwan zamani a cikin wannan sana’ar ta sassak’a da kuma dubin irin makomar wannan sana’ar nan gaba.

4.1 Ma’anar Zamani


Kalmar “zamani” ararriyar kalma ce daga harshen larabci wato daga “azzaman’ aka samota mai nufin lokaci da ake ciki saboda haka ne aka karkasa shi zuwa kashi biyu wato akwai “hali” kuma akwai “mak’ani”.

Shi kuma k’amusun Hausa (2006:489): ya bayar da ma’anar zamani da cewa: zamani shine yanayi ko lokaci. Haka kuma ya k’ara da cewa lokacin da ake ciki ko maici.

4.2 Kayan Aiki da Abubuwan da Ake Sassak’awa


Ko shakka babu duk sana’ar da aka ce sana’a ce da ake aiwatarwa da hannu sai an sami kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da ita.

       Saboda haka sana’ar sassak’a sana’a ce da ake yin ta da wad’ansu kayayyakinta da kuma abubuwan da ake samarwa a cikin wannan sana’ar kamar haka:

  1. Gatari

  2. Guru

  3. Kumbulu

  4. Mahuri

  5. Gizago

  6. Mazami

  7. Gatari: shine abu na farko da ake amfani da shi wajen yin wannan sana’ar kuma aikinsa shine a sare ice da shi ya fad’i kafin duk a soma wani aiki. Haka kuma gatari wani k’arfe ne da mak’era kan k’era wanda akan sanya shi a wata kussuwa ta k’ota domin dad’in rik’ewa.

  8. Guru: amfanin wannan abin aikin shi kuma ya ke’banta ne yayin da za a yi turmi wanda da shi ne ake amfani a yiwa turmi wannan ramin da ake zuba abin daka a ciki. Haka kuma guru wani k’arfe ne da mak’era kan k’era wanda ke da wata ‘yar tank’wara. Kuma ya na da fad’in baki sai dai bai kai girman kwasa ba sai dai ya yi kama da kwasa.

  9. Kumbula: tana d’aya daga cikin kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da wannan sana’a kuma ‘bota ce ta guru. Haka kuma ita kumbula tana da tank’wara a samanta kuma tafi sauran ‘bota mai girman aikin ta shi ne gyara turmi ta wajen sassak’e wajen zaman turrmi da kuma gyara shi wajen dai-dai tashi ta wajen tsayinsa da kaurinsa.

  10. Mahuri: wannan wani k’arfe ne dogo kuma mai tank’wara a saman shi wanda ake amfani da shi a hure turmi koma duk wani abin amfani da aka yi na wannan sana’ar.

  11. Gizago: d’aya ne daga cikin kayan aikin wannan sana’a kuma wannan wata ‘yar k’aramar hauya ce mai ‘yar ‘bota wadda kamar da ita ce ake saisaye duk wani abu da suka yi wanda ya danganci wannan sana’a tasu.

  12. Mazani: wannan wani k’arfe ne marar kauri kuma bai wuce tak’ar hannu biyu ba. Wanda ake amfani da shi a sanya shi wuta idan ya yi zafi sai a yiwa turmi zane amma ko turmin k’aramin turmi domin ba a yiwa babban turmi zane kuma suna amfani da shi su zane kujeri.


Abubuwan da ake sassak’awa sune kamar haka:

4.2.1 Turmi: wani abu ne wanda sakkarawa ke sassak’awa wanda mata ke amfani da shi a cikin gidajensu. Haka kuma tumi ya na d’aya daga cikin abubuwan da ake kaiwa mata amare a gidajensu lokacin da aka yi musu aure. Haka kuma turmi ya kasu kashi biyu: akwai babban turmi da k’aramin turmi. Babban turmi shi ne wanda ake daka da shi (wato surfe ko sussuka) k’aramin turmi shi ne wanda ake k’ulk’ule da shi (kamar k’ulk’ulen yaji ko k’uli-k’uli ko tumatur ko kuma wani d’an daka marar yawa).

4.2.2 Ta’barya: wata abace wadda masassak’a ke samarwa Ga mata a cikin gidaje. Da ita ne mata ke amfani wajen daka. Ita ma ta’barya ta kasu kashi biyu wato akwai babbar ta’barya da kuma k’arama. Babbar ta’barya ita ce wadda ake daka da ita kamar sussukar hatsi ko surfe ko kir’bin gumba da dawa da nakiya da dak’uwa. Ita ko k’aramar ta’barya da ita ne ake amfani wajen k’ulk’ule ko wani d’an daka marar yawa.

4.2.3 Akushi: idan aka ce akushi ana nufin abu ne wanda massak’a ke sarrafawa idan suka samo gunduwar icce sai su gyara shi da gizago. Idan suka k’are amfani da gizago sai su sa mahurinsu su k’ara gyara shi sai su rarake shi da kyau su mayar da shi tamkar kwanon cin abinci wanda idan mutum ya ganshi ba zai raba da kwano ba. Ana amfani da akushi wajen zuba abinci ko shan fura ko wankin surfe ko tuk’in tuwo da dai sauransu.

4.2.4 Kujerar Zama ta Mata: idan aka ce kujera ana nufin abinda ake zama akai galibi manyan mata ne suka fi amfani da ita a cikin gidajensu.

4.2.5 K’ota (‘Bota): ita dai k’ota wani icce ne da masassak’a ke sassak’awa domin ya zama marik’i ga wani nau’in kayan aiki. Akwai k’ota iri-iri kamar haka: k’otar kalme da k’otar gatari da k’otar hauya (kwasa) da k’otar magini da k’otar wuk’a (yuk’a) da k’otar gizago da dai sauransu.

Dukkanin wad’annan k’otocin masassak’a ne ke yin su (sassak’asu) domin su zama mafi sauk’i da kuma jin dad’in aiki ga nau’in mutanen da ke amfani da irin wad’annan kayan.

4.2.6 Ican Ganga: ican ganga wani nau’in abin kid’i ne na wasu makad’an da suke amfani da ita a wurin kid’ansu. Kuma sakkarawa ne ke sassak’a ican gangar ta kasu kashi uku (3) kamar haka:

  1. Icen gangar Noma

  2. Icen gangar Fada

  3. Icen Gangar Noma: ice ne babba kuma sosai kuma bakinta k’ato ne ita aje ta ake yi a k’asa sai a kama kid’awa. Bata d’aukuwa domin girmanta kuma makad’an manoma da ‘yan kokuwa ke amfani da ita a wajen kid’ansu.

  4. Icen Gangar Fada: ita wannan icen gangar sakkarawa ne ke yin ta da icen k’irya ko gawo sannan makad’an fada su rataya ta a wuyansu sau rink’i kid’awa.

  5. Icen Gangar Gardawa: ita wannan icen gangar sakkarawa ke yin ta da icem madobiya ko kawo ko d’unya sannan gardawa su suke amfani da ita a lokacin wasanninsu na gargajiya da suke yi kaman wasan kura ko dabo ko wasan birai ko kauda ido da sauransu.


4.2.7 Icen Kalangu: shi icen wannan kalangu masassak’a ne ke yin sa ta hanyar yi masa baki biyu wanda makad’a ke amfani da shi.

Kazalika shima kalangu ya kasu kashi uku (3) wato akwai:

  1. Icen Kalangu na Mahauta: wannan kalangu ya fi kowanne girma daga cikinsu.

  2. Icen Kalangu Na Manoma: shi kuma matsakaici ne ba ya da girma sosai.

  3. Icen Kalangu na Mafarauta: shi wannan icen duk ya fi su k’ank’anta domin k’arami ne sosai a garesu. Amma kuma dukkaninsu sakkarawa ke samar da iccen had’a shi.


4.2.8 Icen Kotso: shi ma icensa sakkarawa ke samar da shi haka yake kamar kalangu sai dai banbancinsa da kalangu shi baki d’aya gareshi. Shima sakkarawa ne ke sassak’a iccensa.

4.2.9 Icen Taushi: abin kid’a ne mai kamar kwanon shan ruwa da masassak’a ke sassak’a icensa kuma k’arami ne ba ya da girma sosai.

4.2.10 Icen Urya/Hurya: abin kid’a ne da masassak’a ke sassak’a icensa masu kid’a wanda suke amfani da shi a wajen bugun kalangu, kuma ya na da kai mai d’an fad’i.

4.2.11 D’angarafai: wannan kuma takalmi ne na sanyawa da sakkarawa ke yin sa da icce.

4.2.12 Icen Kwazagai: shi wannan shi ne d’ankililin da makad’a ke amfani da shi a wajen kid’ansu wanda Bahaushe na cewa “ba a kalangu sai da kwazagi”.

4.2.13 Iccen Wankin Hula: shi wannan iccen masassak’a ke sassak’a wa masu wankin hula shi domin su yi aiki da shi a wajen sana’arsu.

4.2.14 Muciya: wani icce ne da masassak’a ke sassak’awa masu sana’ar sak’ar gargajiya sai su sanya zare a cikin k’afafunsu sai su kama jan zaren ta amfani da wannan matcehi.

4.2.15 Cakalkala: ita ma wannan sakkarawa ke yinta ga masu sana’ar gargajiya. Amma ita tsawo gareta za su kwarkware ta dai itace ake sawa ga sak’ar gargajiya. Ana sassak’a shi daga iccen maje da kawo.

4.2.16 Sandar Rini: wannan sandar kamar ta’barya take massak’a ke sassak’awa masu sana’ar rini ita. Da ita suke amfani wajen bugun tufafin da suka rina. Sannan ana sassak’ota daga iccen Dogonyaro ko Loda Marke da sauransu.

4.2.17 Iccen Gwahwa: shi ma wani iccen ne da sakkarawa ke sassak’awa ga al’umma domin a yi amfani da shi a wajen rataye wani abu. Kuma ana sassak’a shi da iccen Dogonyaro ko Maje ko Kanya da sauransu.

4.2.18 Muciyar Tuk’in Tuwo: wannan wani d’an icce ne da sakkarawa ke sassak’awa mai kamar d’an kulki wanda mata ke amfani da shi a wajen tuk’in tuwo. Kuma ana sassak’a shi daga iccen Dogoyaro ko d’unya ko kanya da sauransu.

4.2.19 Allon Karatu: wannan wani iccen ne da sakkarawa ke yi wa malamai da d’alibai domin karatun Muhammadiya (Arabic). Ana sassak’a shi daga iccen Loda ko Dogonyaro ko D’unya ko kanya da sauransu.

4.2.20 Lude: wannan wani icce ne da ake sassak’awa mai marik’i a hannu sannan mai baki da zurfi wanda ake amfani da shi a wurin shan su. Ana sassak’a lude daga iccen Dogonyaro ko Loda da kanya da d’unya d sauransu.

4.2.21 Kuyafa: wannan ita ma kamar lude take da ice ake yin ta sai dai banbancinsu guda ita a wurin yin miya ko d’ibar miya ake amfani da ita. Ana sassak’ota daga icen maje ko dogonyaro ko aduwa da sauransu.

4.2.22 K’afar Guragu: wani icce ne da sakkarawa ke sassak’awa guragu (masu k’afa d’aya ko wad’anda k’afafunsu ke da rauni wajen tafiya) wanda ta kan kasance ga gurgu a matsayin k’afarsa ta biyu. Ana sassak’a shi daga iccen Dogonyaro ko marke ko maje.

4.2.23 Wajin Mota: wannan wani icce ne da sakkarawa su ke sassak’awa mai matsakaicin girma dunk’ulalle haka marar tsawo wanda direbobin manyan motoci ke amfani da shi a lokacin da su ka tsaya sai su sanya shi a k’asan tayoyin mota domin gudun kada ta gangara ko ina. Ana sassak’a shi daga icen dogonyaro ko marke ko madobiya  ko kad’e.

4.2.24 Jirgin Ruwa: sakkarawa ne ke sassak’a shi inda za su je daji su sami k’aton iccen mad’aci ko loda ko aduwa  ko marke ko madobiya ko kawo ko turare sai su kayar da shi sannan sai su sassak’e raffansa daga nan sai su sa gatarinsu su kama saransa. Idan sun gama aikin da gatarinsu sai su sa gizagonsu su fitar da saitin abin da suke buk’ata (jirgin ruwa) daga nan kawai sai ka ga siffar jirgin ruwa ta fita lafiya lau.

4.2.25 Sirdin Rak’umi: wannan wani icce ne mai kamar iccen d’anko wanda masassak’a ke sassak’awa masu rak’uma domin su yi amfani da shi ga rak’umansu a lokacin da za su hau da d’aukar kaya. Ana sassak’a iccen daga dogonyaro ko turare ko maje.

4.2.26 Jolar Shanu: ita kuma wannan wata dogon ice ne da sakkarawa ke sassak’awa ga masu aikin daji da shanu wanda su ke aza wannan sandar (jolar) a saman wuyan shanun sai a d’aura musu galma su ja domin a yi noma ko a d’aura musu kura (tarko) domin su d’auki kaya. Wannan iccen jolar ana sassak’a shi ne daga iccen taura ko dogonyaro ko maje. 

    

4.2.27 Sandar Fulani: ita ko wannan wata sanda ce da masu sana’ar sassak’a ke sassak’awa ga fulani wanda take k’arama ce mai sul’bi wato mai dad’in sha’ani wanda su ke amfani da ita a wajen kiwon shanu da sharo (shad’i) kai harma a wajen fad’a su na amfani da ita. Ana sassak’a sandar daga iccen gora ko tsiriri ko lattu.

4.3 Tasirin Zamani a kan Sana’ar Sassak’a


Zamani ya yi tasiri a kan wasu daga cikin kayan da sakkarawa ke sassak’a misali ga wasu kad’an daga cikin kayan kamar haka:

  1. Akushi: ya samu sauyi ne ta fuskar amfani da kayayyakin da zamani ya zo da su irinsu: kwanon cin abinci da kula (cooler) da dai sauran kayan cin abinci daban-daban iri-irin na zamani. Haka kuma zamani ya yi tasiri a kan akushi domin kuwa yana kusa da ‘bacewa ko ma ya ‘bace gaba d’aya don haka a halin yanzu wani ma bai san shi ba balle nan gaba yara masu tasowa.

  2. Ludayi da Kuyafa: wad’anda sakkarawa ke sassak’a, a yanzu na roba da na k’arfe sun fi samun kasuwa (ciniki) bisa ga na icce.

  3. Kujerar Zama: wannan kujera sakkarawa suna sassak’a kujerar zama wanda yake a yanzu zamani ya kawo kujerun roba da na k’arfe wanda ta mamaye k’asar nan sa’banin da wanda ba mu san wata kujera ba in ba ta sakkarawa ba wannan ya nuna cewa zamani ya maye gurbin waccen ta sakkarawa.

  4. K’yaure (Gambu): zamani ya yi tasiri a kan sa domin wanda sakkarawa ke yi a wancan lokacin suna yin sa da icce amma a yanzu ana samun na k’arfe da na gilas wad’anda sune na zamani har ma sun ‘batar da wancan na gargajiya na sakkarawa.

  5. Kayan Kid’an Gargajiya: a yanzu an rage amfani da kayan kid’an gargajiya wad’anda sakkarawa samarwa domin amfani da su a yanzu an fi amfani da na zamani kamar su jita da fiyano.

  6. Jirgin Ruwa: ta dangane da hark’ar sufuri na k’asa da k’asa an fi amfani da jirgin ruwa wanda zamani ya kawo (samar) wato (Bature) ya zo da shi sama ga wanda sakkarawa ke sassak’awa.


Daga k’arshe akwai kayan da sakkarawa ke sassak’awa wad’anda zamani bai yi tasiri a kansu  ba domin kuwa har yanzu Allah bai bawa Bature fasahar da zai yi wasu kayayyaki da sakkarawa ke sassak’awa, irin su k’otar hauya (‘bota) da ‘botar kalme Da jola da sirdin rak’umi da dai sauransu. Duk wad’annan sakkarawa ne kawai ke yinsu har yau zamani bai zo da wani d’aya daga cikinsu ba.

4.4 Tasirin Sana’ar Sassak’a ga Al’umma


Dukkan abinda ake aiwatarwa za a taras da ya  na da amfani ga al’umma sai dai wani lokaci ana samun ‘yan matsalolin da ba a rasa ba.      

      Wannan sana’a sana’a ce da ke da tasiri k’warai da gaske ga al’umma baki d’aya, domin duk inda aka zagaya a k’asar Hausa ko ma a k’asar nan za a taras da mutane na amfani da irin wad’annan abubuwa da masu wannan sana’ar ke samarwa. Domin duk abubuwan da aka zayyana wad’anda masu wannan sana’ar kan yi ana amfani da su wajen aikace-aikacen yau da kullum. Haka su na daga cikin tasirin wannan sana’ar wato:

  1. Samar da kud’in biyan buk’ata ga masu sana’ar.

  2. Samar da kayan aikin musamman ga:

  3. Manoma: ‘Botar hauya, galma, kalme, gatari da sauransu.

  4. Matan Gida: turmi, ta’barya, kujera da sauransu.



  • Kayan farauta: ‘Botacin, gatari, wuk’a, da sauransu.



  1. Mawak’a: iccen ganguna, kalangu da sauransu.


Duk da cewa wannan sana’a sana’a ce da ke da tasiri ko amfani ga al’umma, to kuma ta na da matsala. Matsalar kuwa ita ce:

Domin wannan sana’a sana’a ce da ake aiwatarwa ta hanyar yin amfani da itatuwan daji, ana sare su kuma sai ga shi saren itatuwan daji abu ne maras amfani domin ya na haddasar da gurgusowar hamada ga k’asa.

Saboda haka duk da alfanun da ke ga wannan sana’a kuma sana’a ce da ke iya haifar da wata matsala ga al’umma.

4.5 Matsayin Sana’ar Sassak’a a Yau


Kamar yadda na yi hira da sakkarawa daban-daban iri-iri a wurarenmu wato D’akin Gari su na bayyana min da cewa matsayin sana’ar sassak’a a yau ta na nan yadda take tun a can dori ba ta samu wata ta’bar’barewa ba ko wata illa ko wani cikas ba tun wancan lokacin har zuwa yanzu. Dalili kuwa shine domin Bature bai shigo a cikin wannan sana’ar ba domin bai da mu da ita ba yadda suka gadi abinsu suna nan suna aiwatar da ita yadda take a gargajiyance ba ruwansu da Bature balle ya shiga a cikin ta har ya ‘bata sana’ar ko ya illantar da ita. Saboda haka ne su masassak’an ke yin aiki da kayansu na gargajiya ba tare da sun yi aro daga kowa ba a cikin wannan sana’a ta su ta yau da kullum.

4.6 Makomar Sana’ar Sassak’a


Makomar sana’ar koyaushe sai dai ci gaba zai ta yi domin kuwa ta na samun jama’a da dama suna shiga a cikin sana’ar sosai da sosai kuma suna sassak’awar kayayyaki suna sayarwa akai-akai. Kamar ga abinda ya shafi kayan aikin gona suna sassak’a kayan aiki ga manoma damina da rani ga manoma masu aikin damina da na rani (wato ka tashi). Haka kuma wurin samun icce a can da sai su (sakkawa) su tafi daji da k’afa su saro icce sai su d’auko shi da kai amma yanzu da mota ake zuwa ko mashin ko keke ko tarhou shanu saboda irin ci gaban da sana’ar ke samu. Sannan a da idan za a je daji saran icce da gatari ake zuwa amma a yanzu zamani ya kawo musu injin yankan icce wanda a cikin lokaci masassak’a za su yanka itatuwa da dama wad’anda za su yi aiki da su a cikin sauk’i to balle nan gaba. 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments