Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanayin Zuwan Mafayyaciya Da Lokatak Da Dirka Cikin Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

HARUNA ABDULLAHI UMAR

BABI NA BIYAR

5.1    TAK’AITAWA


Duk wannan aikin ya yi Magana ne akan harshen Sakkwatanci dangane da mafayyaciya, yadda take zuwa a cikin jumlolin Daidaitacciyar Hausa, da kuma cikin harshen Sakkwatanci. Haka kuma ya yi magana akan lokatak’, yadda take zuwa a cikin jumlolin Hausa don nuna kammaluwar aiki ko ak’asin haka, da kuma yadda take zuwa a cikin harshen Sakkwatanci. Bayan wannan kuma aikin ya yi bayanin kalmomin dirka da yadda suke kasancewa a cikin jumlolin Daidaitacciyar Hausa, da kuma yadda suke komawa a cikin harshen Sakkwatanci in sun zo cikin jumla. Haka kuma, wannan aikin ya d’an yi tsokaci dangane da wasu Sakkwatattun kalmomi.

A babi na farko na yi bayanin bitar ayukkan da suka gabata, da kuma dalilin yin bincike, had’i kuma da hanyoyin gudanar da binciken wannan aikin, tare da muhimmancin bincike na wannan aiki.

A cikin babi na biyu na wannan aiki na yi k’ok’arin ganin na kawo ma’anar jumlar Hausa da kuma ire-irenta. Bayan wannan kuma na bi kowane kaso daga cikin wad’annan ire-iren jumlolin na Hausa daki-daki domin kawo d’an tak’aitaccen bayanin da ya danganci Sassauk’ar jumla, da jumlar tambaya, da jumlar umurni da kuma jumlar korewa.

Haka kuma, a cikin babi na ukku ne, na ba da makamantan wad’annan jumlolin a cikin Karin harshen Sakkwatanci, inda na yi k’ok’arin kawo d’an bayani tare da misalai na Sassauk’ar jumla, da kuma jumlar tambaya, jumlar umurni, da kuma jumlar korewa.

A babi na hud’u wato inda gundarin aikin nawa yake a nan ne na yi bayanin mafayyaciya da abin da ta k’unsa, tare da wasu misalanta a cikin jumlolin Daidaitacciyar Hausa, da kuma wasu misalan a cikin lokatak’ bisa ra’ayoyin magabata tare da ire-irenta, da kuma wasu misalai. Haka kuma a cikin wannan babi ne na d’an yi bayani dangane da kalmomin dirka game da ma’anar su da kuma yadda suke zuwa a cikin jumlolin Daidaitacciyar Hausa, da kuma harshen Sakkwatanci. Bayan wannan kuma, na kawo wasu daga cikin Sakkwatattun kalmomi masu bambancin furuci, amma ma’ana d’aya, da kuma masu ma’ana d’aya, amma sauti bamban.

5.2    KAMMALAWA


Hausawa na cewa duk abin da ya yi farko to lallai hakika zai yi k’arshe. Wannan babin, babin kammalawa ne ga wannan d’an aikin nawa. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, akwai ‘bangarori uku, wato ‘bangaren nazarin harshe da kimiyar harshe, da ‘bangaren adabi da ‘bangaren da ya shafi al’adu. Abin da aka yi tsokaci a wannan aikin yana k’ark’ashin ‘bangaren nazarin nahawun harshe, wannan aiki mai suna “Mafayyaciya da Lokatak’ da Dirka, yadda suke a Daidaitacciyar Hausa da yadda suke zuwa a harshen Sakkwatanci”, da fatar Allah Ya sa ya amfani duk wani mai sha’awar harshen Hausa. Daga cikin masu sha’awar cigaban wannan harshe na Hausa akwai d’alibai masu bincike da rubuce-rubuce.

Wannan aikin ina fatar ya bud’e wa na baya hanya domin su ci gaba da bincike a wannan fage na nahawu mai matukar amfani da kuma sha’awa ga masu son ci gaban harshe.

5.3    NA’DEWA


A k’arshe, wannan babi na biyar shi ne babin da na tak’aita dukkan abubuwan da na tattauna a cikin wannan aikin. Na tak’aita dukkan babukan nan gida biyar. Na kuma ga cewa kowane babi da abin da ya k’unsa, amma a tak’aice. Da fatar Allah Ya sa wannan aikin ya kasance mai alfanu ga dukkan manazarta harshen Hausa, da mai sha’awar harshen Hausa, da kuma masu sha’awar sanin harshen Sakkwatanci. Haka kuma, ina kira ga ‘yan uwana d’alibai manazarta da su ci gaba da bayar da tasu gudummuwa a wannan fage mai ban sha’awa domin ganin wannan fage ya fad’ad’a.

 

Post a Comment

0 Comments