Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Dr. Sama’ila Sambawa Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Idan ka ga nan a jahar Kabi,

Yara:    Dr. Sama’ila ya aiko ×2

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

Kai za ka yi gwamnan jahar Kabi, ×2

Yara:   Manya da yara suna addu’a,

Allah ya yarda da Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:  Jahar Kebi ba wargi ce ba,

Tana da d’imbin al’umma,

Ku za’bi mutum cimcimtace×2

Irin Sama’ila Sambawa,

Dun kar ku yarda da jemage,

Yara:    Ko yaushe kai na suke yake,

 

Ba za ya yarda da kowa ba.

 

Amshi:  Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:   Sake jikinki in don ‘yan k’wak’wa,

Wannan karon ba na su ba ne,

Yara:      Dr. hana masu ‘ba’batu.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:  Sake jikinka in don APP,

Wannan karo ba nasu ba ne,

Yara:     Dr. hana masu ‘ba’batu.

 

Amshi:  Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:   Dogo mijin Hajiya Baraka,

Ka k’ara matsawa don Allah,

Yara:     Duk mai gaya ma shi wane ne,

Dr. gwada mishi hilinai.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

 

 

Jagora: Dogo mijin Hajiya A’i,

Ka k’ara matsawa don Allah,

Yara:    Duk mai gaya ma shi wani ne,

Dr. gwada mishi hilinai.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:  Dogo mijin Hajiya Adama,

Ka k’ara matsawa don Allah,

Yara:    Duk mai gaya ma shi wani ne,

Dr. Gwada mishi hilinai.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Yanzu duk mai gaya ma shi wani ne,

Yara:    Dr gwada mishi hilinai.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/sani-rabo-magatakadda-gwamna-marinjayi/

Jagora: A jahar Kebbi kowa ya waye,

Ba su koma za’benka ‘barawo,

Ya kwashe kud’in talakawanai×2

Ya je k’asar waje ya ‘boye,

Yara:    Har na ji mutane suna hwad’in,

Olle raga muna nerori.

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Mulkinka wane mulkin banza ne,

Mulkinka ba ya da tasiri,

Tun randa wane ya zam gamna,

A jahar Kebbi kowa na kuka,

Talakawa sun damu da kai,

Na ji har suna rok’on Allah,

Yara:   Yada mun ka ga hwarkon mulkinka,

Ya Allah gwada muna k’arshe nai.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Duk wanda yake ANPP,

A jahar Kebbi kowa ya katce×2

Yara:    Don sun san ba su da majority,

In ga Sama’ila Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Duk yada aura ya kai k’arhi,

Ba ya shiga d’akin kura, ×2

Idan ba da bindiga ya zo ba,

Yara:    Koda da bindiga ya zo ma,

Kare ba ya i mata wa a shi.

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:  Nijeriya a bar ma Obasanjo,

Yara:     Jihar Kebbi a bar maka Sambawa×2

 

Amshi:  Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Wani ya ga alamun ya hwad’i,

Can nis same shi D’anwarai,

Ya d’auko shata babban mota×2

An shak’e mai ita da albasa,

Yara:    Ya ce a kai mai a Ibadan,

Can za a kai ta a saisam mai.

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: APP kun ‘bata shirinku,

Kun kada girman sarakuna,

Ga wanda ya gadi sarauta,

Sai d’ai ku kar’be rawani nai,

Yara:    Ku d’auka ku ba maginin laka.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Wani ya ci tuwonsa na shinkahwa,

Ya d’auki pure water ya sah,

Sai ya gano bawan Allah,

Mai cin tuwon dussa kullum,

Ya ce ya hana masa dussatai×2

Ku al’umma na tambaiku,

Shin wannan shi ne adalci?

Yara:    Wannan ya yi babban zalunci,

Ko ba a ce masa komai ba.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: PDP babbar jam’iya,

Wanda yake yin PDP,

Ba ya kissa ba ya munahwuci,

Sai dai ya yi maka alheri,

Yara:   Ka ci arziki ka ji dad’inka,

Don ba a yo ma mutun k’eta.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: A Maiyama can lokal gwaman,

Ni ‘Danba’u na tambai ku,

Wa kuka son ya zame gwamna?

Yara:   Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

 

Jagora: A wa kuka shawar ya zame gwamna,

Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Na je a Jega can Lokal gwamman,

Ni ‘Danba’u na tambai ku,

Wa kuka shawa ya zame gwamna?

Yara:   Sun ce Sam’ila Sambawa.

 

Jagora: Garin Gwandu can lokal Gwamman,

Na isko mutane sun taru,

Ni ‘Danba’u ni tambai su,

Wa kuka shawa ya zame gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Aleiro gari lokal gwamman,

Ni ‘Danba’u na tambai ku,

Wa kuka shawa ya zame gweamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Wa kuka shawa ya zame gwamna,

Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

 

Jagora: Birnin Kebbi can lokal Gamman,

Ni ‘Danba’u taibaiku,

Wa kuka shawa ya zame gwamna,

Sun ce Sama’ila Sambawa.

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: A garin Kalgo can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambai ku,

Wa kuka shawa ya zame gwamna,

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Birnin Bunza can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:     Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Amshi:  Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

Jagora: Garin Kokoma lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:   Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Garin Bagudu logal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Garin Zuru can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: A garin Argungu can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: In garin Augi can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:   Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Yelwa Yauwi lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora:  In garin Shanga ma lkal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:     Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Sai Ingaske lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

 

Jagora: Garin Zuru ma lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Birnin Fakai lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna? ×2

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: A Kangiwa lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Birnin Kamba ma lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Amshi: Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takara gwamnan Kabi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

 

 

 

 

Jagora: Danko Wasagu lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Birnin Ri’ba can lokal gamman,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Duka malammai na jihar Kabi,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: Sarakuna namu da a Kabi,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

Jagora: In talakawa na jihar Kabi,

Ni ‘Danba’u na tambaiku,

Wa kuka shawa ya zame Gwamna?

Yara:    Sun ce Sama’ila Sambawa.

 

 

 

 

 

 

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.