https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314
https://www.amsoshi.com/game-da-mu/
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ga d’an Galadima Horo,
Jikan Galadiman Horo×2
Sai kai Galadima,
Yara: In d’au iyalinmu in koma Horo.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: A sai kai Galadima,
In d’au iyalinmu in koma Horo.
Jagora: Ka gama da tsohon kolo,
Wane ya bar gida nai, ×3
Yara: An ce yanzu kullun yana loja kwance.
Jagora: Na yi marmari Haji ‘Danba’u,
In je in k’ara wak’a Shagari.
Jagora: Na san karo da kai,
Ba ya da dad’i,
Kai ji wane ya sha kaye,
Don na gane shi can malisa,
Yara: Ya tara leda yana k’ullin magi.
Jagora: Don na gane shi can malisa,
Yara: Ya tara leda yana k’ullin magi.
Jagora: Wawa!
Yara: Ya tara leda yana k’ullin magi.
Jagora: Saga!
Yara: Ya tara leda yana k’ullin magi.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Yanda kai mani na gode ma,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: A in dai kana nan Shagari,
In maida wak’a Shagari.
Jagora: Yau da gobe kyauta sai Allah,
Yara: Sai kai ciyaman Shagari. ×2
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ga d’an Galadiman Horo,
Jikan Galadiman Horo,
Sai kai Galadima,
Yara: In d’au iyalinmu in kuma Hora,
Jagora: A in kai galadima,
Yara: In d’au iyalinmu in koma Hora.
Jagora: A kwana a tashi dattijo,
Sai kai Galadima Horo.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Na ji har mutane suna hwad’i,
Ko yau siyasa ta dawo,
Yara: Kai za a za’ba Shagari.
Jagora: Ka gyara birnin Shagari,
Ka gyara birnin Shagari,
Yanzu ga wuta kuma ga famfo,
Da k’auyukka ka gyara su,
Ha na ji mutane suna yabo,
Ko yau siyasa ta dawo,
Yara: Kai za a za’be Shagari.
Jagora: Ko yau siyasa ta juyo,
Yara: Kai za a za’be shagari.
Jagora: Tun da sun yi dai sun has wahala,
In kuma siyasa ta dawo,
Yara: To ba za su za’ben mai cuta.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Rabbana ya k’ara kiyaye ka,
Allah ya k’ara tsare man kai,
Rabbana ya ja zamanin Mamman,
Kullun inai ma addu’a,
Yara: Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Kullun inai ma addu’a,
Yara: Mamman ciyaman Shagari.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Gai da Mai’akwa Jared’i,
Yara: Tunda hairan ya ban ya amfanan×2
Jagora: Ma’akwai k’anen Modi sadauki,
Yara: Hairan ya kai ya amfanan.
Jagora: Kansi Bashar na gode ma,
Hairan ya kai ya amfanan.
Jagora: D’an Muhammadu na Lambara,
Yara: Hairan ya kai ya amfanan.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Yaro: Wani ciyaman na nan mai rowa,
Da du ya gane ni ya sha toka, ×2
Wani mai idanun ‘yabin,
Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ina mai idanun mussoshi,
Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.
Jagora: Mudun ka ga ne ni a Shagari,
Yara: Mamman yake murna in je×2
https://www.amsoshi.com/2017/06/30/sani-mai-halin-mazan-jiya/
Jagora: Na gode ciyaman na Yabo,
Bala Musa d’an Ahmadu,
Yara: Hairan yakai ya unhwanan.
Jagora: Na gode ciyamanmu na Yabo,
Bala Musa d’an Amadu,
Hairan ya kai ya unhwanan.
Jagora: Godiya ni kan Sani sanata,
Hairan yakai ya unhwanan×2
Jagora: Godiya nikai Haji Bello ciyaman,
Birnin Bod’inga,
Yara: Hairan yakai ya unhwanan.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji D’an’ige d’an dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Wani ciyaman ne,
Sarki rowa,
Sai son a zo a yi mai wak’a,
To ba ni yin aikin banza,
Yara: Na daina yin wak’a kyauta.
Jagora: Wawa!
Yara: Na daina yin wak’a kyauta.
Jagora: Saga!
Yara: Na daina yin wak’a kyauta.
https://www.amsoshi.com/2017/06/30/sani-mai-halin-mazan-jiya/
1 Comments
[…] Wak’ar Ciyaman D’in Shagari Alhaji Madu Galadima Horo Ta Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai […]
ReplyDeleteRubuta tsokaci.