Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Ciyaman Din Shagari Alhaji Madu Galadima Horo Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

 Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.
 
Jagora: Ga d’an Galadima Horo,

Jikan Galadiman Horo×2

Sai kai Galadima,

Yara:   In d’au iyalinmu in koma Horo.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: A sai kai Galadima,

In d’au iyalinmu in koma Horo.

 

Jagora: Ka gama da tsohon kolo,

Wane ya bar gida nai, ×3

Yara:    An ce yanzu kullun yana loja kwance.

 

Jagora: Na yi marmari Haji ‘Danba’u,

In je in k’ara wak’a Shagari.

 

Jagora: Na san karo da kai,

Ba ya da dad’i,

Kai ji wane ya sha kaye,

Don na gane shi can malisa,

Yara:   Ya tara leda yana k’ullin magi.

 

Jagora: Don na gane shi can malisa,

Yara:    Ya tara leda yana k’ullin magi.

 

Jagora: Wawa!

Yara:    Ya tara leda yana k’ullin magi.

 

Jagora: Saga!

Yara:    Ya tara leda yana k’ullin magi.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Yanda kai mani na gode ma,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: A in dai kana nan Shagari,

In maida wak’a Shagari.

 

Jagora: Yau da gobe kyauta sai Allah,

Yara:    Sai kai ciyaman Shagari. ×2

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Ga d’an Galadiman Horo,

Jikan Galadiman Horo,

Sai kai Galadima,

Yara:    In d’au iyalinmu in kuma Hora,

 

Jagora:  A in kai galadima,

Yara:     In d’au iyalinmu in koma Hora.

 

Jagora:  A kwana a tashi dattijo,

Sai kai Galadima Horo.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Na ji har mutane suna hwad’i,

Ko yau siyasa ta dawo,

Yara:    Kai za a za’ba Shagari.

 

Jagora:  Ka gyara birnin Shagari,

Ka gyara birnin Shagari,

Yanzu ga wuta kuma ga famfo,

Da k’auyukka ka gyara su,

Ha na ji mutane suna yabo,

Ko yau siyasa ta dawo,

Yara:    Kai za a za’be Shagari.

 

Jagora:  Ko yau siyasa ta juyo,

Yara:     Kai za a za’be shagari.

 

Jagora:   Tun da sun yi dai sun has wahala,

In kuma siyasa ta dawo,

Yara:     To ba za su za’ben mai cuta.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora:  Rabbana ya k’ara kiyaye ka,

Allah ya k’ara tsare man kai,

Rabbana ya ja zamanin Mamman,

Kullun inai ma addu’a,

Yara:    Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Kullun inai ma addu’a,

Yara:    Mamman ciyaman Shagari.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Gai da Mai’akwa Jared’i,

Yara:    Tunda hairan ya ban ya amfanan×2

 

Jagora: Ma’akwai k’anen Modi sadauki,

Yara:    Hairan ya kai ya amfanan.

 

Jagora: Kansi Bashar na gode ma,

Hairan ya kai ya amfanan.

 

Jagora: D’an Muhammadu na Lambara,

Yara:   Hairan ya kai ya amfanan.

 

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Yaro:   Wani ciyaman na nan mai rowa,

Da du ya gane ni ya sha toka, ×2

Wani mai idanun ‘yabin,

 

Yara:    Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.

 

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Ina mai idanun mussoshi,

Yara:    Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.

 

Jagora: Mudun ka ga ne ni a Shagari,

Yara:    Mamman yake murna in je×2

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/sani-mai-halin-mazan-jiya/

Jagora: Na gode ciyaman na Yabo,

Bala Musa d’an Ahmadu,

Yara:   Hairan yakai ya unhwanan.

 

Jagora: Na gode ciyamanmu na Yabo,

Bala Musa d’an Amadu,

Hairan ya kai ya unhwanan.

 

Jagora: Godiya ni kan Sani sanata,

Hairan yakai ya unhwanan×2

 

Jagora: Godiya nikai Haji Bello ciyaman,

Birnin Bod’inga,

Yara:   Hairan yakai ya unhwanan.

Amshi: Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari.

 

Jagora: Wani ciyaman ne,

Sarki rowa,

Sai son a zo a yi mai wak’a,

To ba ni yin aikin banza,

Yara:   Na daina yin wak’a kyauta.

 

Jagora: Wawa!

Yara:    Na daina yin wak’a kyauta.

 

Jagora: Saga!

Yara:    Na daina yin wak’a kyauta.

 

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/sani-mai-halin-mazan-jiya/

 

 

 

 

 

 

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.